UMM ADIYYAH CHAPTER 58 BY AZIZA IDRIS GOMBE

UMM ADIYYAH CHAPTER 58 BY AZIZA IDRIS GOMBE

                   Www.bankinhausanovels.com.ng 

Mun tsaya 

“Eh na san za a samu ‘yar matsala ta wannan wurin, ban sani ba. Kawai ku je ko

Baffa Mai-Kano ku samu da Yaya Nazeef din zan yi KoKarin na shigo nan da sati

biyu Inshaa-Allah.”

“Amma Zaid ina so ka sake tunani kafin dai a yanke komai.” Salisu ya facia daga

Claya Bangaren.

“Haba, dan group, ya kamata ka sani, ba na wata tantama, kai ma ai ka ganta and

ka ce ba matsala, na san idan na zo komai zai daidaita.”

“Ka san me na ke nufi sarai, ka daina kaucewa zancen nan, ni a tunanina ka na

dawowa za ka yi abinda ya dace?”

“Menene abinda ya dacen da ya wuce wannan?”

“Yanzu dai duk turirinku daga kai har Ummu Adiyya ya ci ace kun huce, ya kamata

ne ka yi KoKari ku daidaita, ba ka sake Haro wani sabon aiki ba.”

“Hmm! Salis kenan, da a ce ba ka san komai bane, sai na tsaya yi maka bayani,

amma ka sani. So, batun ka tsaya tambayata dalili bai taso ba, na sa iya Karfina,

lokacin da ya dace, me zan yi idan ni kadfai ke saka wannan yunkurin? Www.bankinhausanovels.com.ng

Ka na sane, na fada maka an je sulhu. Ko idanu na ta gagra kalla, bare ace ta amsa

wayoyin da nayi mata bayan watanni uku, a tunanina ta huce zuwa lokacin. Bayan

nan na cire sha’aninta a raina. kamar yadda ita ma ta cire. Ba ka ganin lokaci ya yi

da kowa zai kama gabansa? Akwai ababe da yawa na rayuwa da suka wuce

wannan.”

“Don Allah Malam ka bar maganar nan, kai ne fa namijin, ina ka taba jin anyi rarrashi

ta waya bare sulhu? Kai ya kamata ka yi Kwakkwarar motsi ka yi tattaki ka isa inda

take, ba ka tsaya yin abu baya-baya ba, ka na jin kanka.”

“Na amince da farko na janye, saboda kowa ya samu lokacin da yake buKata, amma

daga baya, bata bani dama ba,a taKaicet, ba ta taba nuna alamun tana so mu koma

ba. Ba ta damu ba, ta ci-gaba da rayuwarta yadda ya dace, babu ni a ciki, don haka,

No. Babu abinda ya rage. Na riga na yanke shawara. Ina zuwa za a ci-gaba da

batun aurena da na saka a gaba.” “Ka dai yi tunani.”

“Na riga na yi tunani, mutum yana Kokarin ya ceci alaKar da ya fahimci cewa, ana

son ya ceci wannan alaKar ne, a duk lokacin da na yi yunKurin hakan kuma sai na
ga ta sake subuce min. Www.bankinhausanovels.com.ng

Ban san yadda zan fadla maka cewa na kasance cikin mafi tsaka mai wuya na

rayuwana ba a wannan shekarar da ta shudle ba, kawai ka cauke shi a matsayin

Yasmeen za ta maida ni mutumin da ku ka sani a baya.” Ajiyar zuciya ya sauke, “Ka

zauna cikin shiri. Ina zuwa, za mu yi abinda ya dace, ina dawowa Inshaa-Allah.”

“Za ka yi da na sani Zaid, ina fada maka wannan ne a matsayina na abokinka.” Zaid yana jin kalaman abokin sa, wata jijiya a saman kansa ta yi motsi. Runtse idanunsa

ya yi, ya sauke hucin numfashi. Sannan ya kashe wayar.

Kansa ya kifa kan hannayensa da ke sargafe saman teburin da yake zaune. Bai ki

ya gan shi gaban Mama ba a wannan lokacin tana ba shi baki da kalamai tausasa,

hadle da masa adu’o’i masu inganci da tasiri.

Sai dai yanzu Mama gaba Claya ba ta, ta shi, wannan ya sa ya Claga waya zai kira

Adda Sadiya, abin mamaki, sai ya samu kansa
da kiran lambar Maami. Tunda ko ta fara ringing, sai bai katse ba. ““Assalamu-Alaikum?”

Shiru ne ya ratsa na dan lokaci, kafin ya ce, “Wa’alaikumussalam. Maami an wuni

lafiya?” Www.bankinhausanovels.com.ng

Take muryarta ta facfadia fara’a, “Zaid, lafiya Kalau, yaya ayyuka? Jiya ko Abba ke

maganar ka ce ka kusa dawowa.”

“Eh, mun kammala aikin da ya kawo mu, ina ga zuwa Sati na sama dai. Ayi ta saka

mu a addu’a.”

“Inshaa-Allah ana kai. Allah ya kade dukkan sharri, ya Kara kawo ci-gaba.”

“Na gode. A gaida su Faruk.”

“Za su ji, sai anjima.” Suna ajiye wayar, ya sauke numfashi. Saura kiris! Ya yi subul

da baka ya yi tambayar da za ta janyo masa jangwam! Wannan ya sa sai an Can

kwana biyu yake kirarsu a waya.

Halin da ya samu kansa a ciki na rashin kuzari,
ya sa ya fasa kiran Adda Sadiyar

ma, ya komar da hankalinsa kan abinda ya sa a gaba. Domin yanzu yana kiranta da

ma sauran jama’ar gidansu, to an samu matsala, ya rasa me yake damun jama’ar

gidansu? Musamman Baffa da su Anti su a dole har yau fushin shawarar da ya

yanke suke yi.

To banda abinsu, a wancan lokacin idan bai yi haka ba, yaya suke so ya yi? Wannan

ne babban musabbabin da yasa ya nisanci al’amuran gidan ma, lokaci dai zuwa

lokaci yana zuwa. Amma yanzu kusan watanni uku cif! Ya kwashe bai je gidan ba.

Kwanaki uku bayan nan, ya hadfa ya nasa ya nasa, ya nemi jirgin da zai tashi cikin

kwanaki biyu, domin bai yi tunanin zai iya kaiwa sati biyu nan gaba, bai san me yake

ciki ba kan abinda ya sa aa gaba.

3g 3 ok oh 2 ok ok ok of

Tunda TJ. Ya sake daura idanunsa akan Ummu Adiyya, ya san cewa tashi ta same

shi, domin duk wani abinda ya nade ya share ya tura a can Kasan zuciyarsa na

mancewa da ita ko kuma soyayyarta, ya koma sabo fil! Sai lokacin ya sake samun

sabon himma na tunkararta da batunsu, ya kwana da sanin komai da lokacinsa, Www.bankinhausanovels.com.ng

haka nan wani baya taba samun rabon wani a rayuwarsa.

“Material, kwana biyun nan fa ba na gane maka. Kullum ka na maKkale da waya.”

“To kuma ba dama na riKe waya sai wani abu ya faru?” TJ. Ya fad yana kallon

Mahmoud abokin sa.

‘Dole na yi magana, ka san idan dai Madam ce, ba zance wani abu ba, saboda na

san yadda abin yake, amma wannan gaba aya ka shiririce ka mance kanka, na yi

sallama sau uku shigowata nan wurin, kafin ka san anyi ruwana.”

“Wallahi ka faye sa ido, kamar wani abin nan. Ka yi abinda yake gabanka.” Hularsa

ya kafa a kansa yana KoKkarin mikewa, don ya kammala abinda yake yi na yinin
ranar.

“Na yi shiru ai koma menene za ayi walkiya. Mu je zuwa wai mahaukaci ya hau

Kura.”

TJ. Bai kuma tanka masa ba, baya ga murmushin da ya yi, suka sauka zuwa Kasa

inda suka shiga motarsa. Suna cikin hirarsu ne ya ce, “Za mu je Bauchi ne ranar Juma’ a?”

“Koda me za ka hacfani Wallahi, na san sirrin nan a Bauchi yake. lye Malam, cikin

sati uku ka je sau hudu, ko ka fada min ko kuma ba inda zan je kuma na hana ruwa

gudu.”

“Kai ka sani ai duk tsurkunka za ka yi ka gama.”

“To ka sauka lafiya.”

Wani kallo TJ. Ya sakar masa, “Sai ka je to, ko na tona batun sabuwar motarka.”

Ba shiri Mahmoud ya gintse fuska, ya juyo yana kallonsa, “Kai me ya sa ka ke haka

ne Material? Karfe nawa za a tafi?”

TJ. Ya tuntsure da dariya, ya san hanya sas
sauka da yake daure abokin sa. Allah

ya sanya masa haukar son motoci, idan ya ga mota tayi masa kyau, zai iya

sadauKar da komansa don ya mallaketa, kullum suna cikin fada da Ummansa akan

hakan, wannan ya sa duk lokacin da zai canja, baya fada, sai ta kwana biyu idan ta

gain, ta yi fadian, a wuce wurin. Www.bankinhausanovels.com.ng

Yanzu ta ba shi gargadli na Karshe, ko ya san na yi da rayuwarsa, ya bar yarinta ko

kuma ta fita sha’ aninsa.

TJ dai ji yake yi kamar Juma’a ta yi nisa, yana shiga gida, ya tarar da Rahma da

Minaal sun sha kyau cikin kyakkyawar shiga. Da fara’arsa ya isa garesu, ya Cauki

baby Minaal ya fara mata wasa, ita kuwa tana ganin sa ta fara KyalKyala dariya.

“Za ka zarar min da yarinya Wallahi. Wannan dariyar ai ta fi Karfin jinjira.”

“Wannan ce jinjirar? Ki na ga yarinya da wayonta, tana hira tana gayu tana zama, ki

wani ce mata jinjira, ai an mana demotion, ko bayb princess?”

HMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *