UMM ADIYYAH CHAPTER 6 BY AZIZA IDRIS GOMBE
Www.bankinhausanovels.com.ng
MUN TSAYA
Duk gidan kowa ya kirata, banda wanda ta fi tsammanin kiransa, koda yake me zai sa ya kira? Tunda fatansa ta fadi, ta je ta yi aiki a kamfaninsa, inda zai fi jin dadiin ganinta cikin wuya. Duk da Adda Asma’ ta Ki ta yi mata bayanin komai a waya, wannan bai sa ta sauke tunanin cewa Yaya Zaid na son Adda Asma’ ba. Rubutaccen gwaji aka soma yi masu, sannan akai masu na baki, ta san dai a na
rubutun ne kawai, ta yi abin arziKi, amma na bakin kam sai a hankali, don banda “Pardon” ba abinda take ce masu, saboda hankalinta baya jikinta, daga baya suka ce ta matso da kujerarta gaba saboda ta rinKa jinsu da kyau. Har ta ji kunya, sai lokacin ne ta maida hankalinta garesu. Suna fitowa ta saki ajiyar zuciya, duk da ba ta san meye sakamakonta ba, amma ta sauke mai wuyan. Gidan Adda Zubaida ta koma tana ba su labarin yadda Interview din ya gudana. Suna zaune Asma’u ta kira, wannan ya sa Umm Adiyya ta yi wuf ta koma daki ta ce, “Don Allah Adda Asma’ yau kam ki fada min sunan Dee na gaskiya.”
ZAMU TASHI
“Haaa, ka ji min yarinya, yanzu ke ba abin kunya bane a gareki don Allah mijin Addarki ba ki san sunan sa ba, duk tsawon lokacin nan? Shekarunmu hudu tare fa.” A’a to ba ke bace ki ka sa masa Dee, kowa ma yake kiransa haka ba? Kuma ni yaushe ma na zauna a Abuja bare na sani?” “To yanzun me za kiyi da sunansa idan kin sani?” “Don Allah dai, wani surprise ne, ba yanzu zan fada miki ba.” “Ki fad min surprise din, sai na fada miki sunan.” Tsumewa ta yi, a ranta ko cikin damuwa take tsantsa, “To shi kenan kar ki fada, ai dai za ku buga katin daurin aure ko?”
Asma’u na dariya ta ce, “To sarkin wayo, sunan sa Www.bankinhausanovels.com.ng Usman Zunnurain, a office dinmu yake abokin Yaya Zaid ne kuma.” Wata irin wawiyar ajiyar zuciya Umm Adiiyya ta sauke, ba ta taba tsintar kanta a cikin
irin wannan yanayi na tsantsar jin dadin ba, irin na wannan lokacin, har take tsoron bude idanu kar ko mafarki take yi. “Alhamdulillahi, ba Yaya Zaid Adda Asma’ za ta aura ba.” A rashin saninta a bayyane ta yi furucin, kuma wayar ba a kashe ba. “Me ki ka ce?”
Cikin kidima ta bude idanu ta ce, “Ni? Ba… Bu… Ban ce komai ba.” “Tsaya ki fada min, wai ma tukun me yake damunki ne ki ka faye tunani da magana da kanki? Ko dai Yaya Zaid ne? Wani abu ya fada miki ko kuwa wani abin ya yi?” Da gaske ba komai, sai da safe.” Da sauri ta tsinke wayar tana cizan harshenta
cikin alamun kwafsi. Allah dai ya sa Adda Asma’ kar ta gane komai. Wannan shi ne fatan Umm Adiyya.
Bata taba ni’imtaccen bacci ba, irin na ranar a cikin tsawon shekaru uku, saboda yau ta san Yaya Zaid ba ‘yar-uwarta zai aura ba. Www.bankinhausanovels.com.ng
Washegari da sassafe Adda Zubaida ta sameta da ‘yar jakarta a falo ta yi shirin tafiya. “Haba ke kuwa sai ka ce ina korarki? Meye haka? Ba za ki jira sai a weekend ba ki koma? Ga Baban su Walid ma ran Juma’‘a zai je Abujan, ai sai ku tafi tare.”
“A’a Adda Zubaida, ba komai zan tafi din, kin san mun yi da Abba idan mun gama na koma, saboda AZ suna nemana.” Kai Yaya Zaid ba dama, duk kuma ‘yan Kannen nawa sai ya sa sun bauta masa ne? To Allah dai ya zabar da abinda ya fi alkhairi.” Numfashi ta sauke, yayin da Umm Adiyya ta dan dubeta a KaiKaice, domin ta san maganar da za ta dago mata sarai, “Saura maganar miji kuma…” “Maman Walid, don Allah ki bar wannan maganar. TJ din ma ya ce ya haKura ba shi kenan ba?” Wa ya janyo har ya haKura? Mutumin nan fa har kayan auren sa ya hada, ya kammala komai jira kawai yake yi ki amince masa, ya isa gida, amma ki na ta masa yawo da hankali, ai ba matan aka rasa a gari ba, amma ya ganki ya ce ke ki kai masa? Meye laifinsa, don ya ce yana sonki? Allah dai ya ganar da ke Wallahi.” Ta san duk bayanin da za ta yiwa ‘yar-uwarta, ba za ta gane ba, don haka ta yi shiru ta gama kwasan fadanta son ranta. Ba ta Kara awa guda a gidan ba, ta wuce tasha ta kama hanyar Abuja.
***********
Dagowa ta yi daga (Lapton) cinta inda ta samu littafin L.J. Smith(Vampire Diaries) tana karantawa, ba komai ya dauke mata hankalinta daga karatun da take yi ba, illa jin Kamshin, turarensa da ta yi, wanda ko a mafarki ta ji Kamshin, ta san mai shi,
bare a zahiri. Haka kawai ta samu kanta da sakar masa murmushi, sannan ta gaishe shi. Sannu da dawowa.” Ta fada Kasa-Kasa tana satar kallon sa, yau ma cikin Kananan kaya yake, daga inda take zaune, gashin kansa yana yalki da alamar bai dade da
yin wanka ba. Gefen fuskarsa kuma gashi ne a kwance tamkar wani baKin balarabe. Sannu Ummu.”” Ga mamakinta wuri ya samu ya zauna ya fiddo wayarsa da take ringing ya amsa, ta saman (Lapton) cinta take satar kallonsa. Ba ta san yaushe ya
kammala wayar ba, ai kuwa caraf! Ya kamata tana kallonsa. Ba shiri ta sauke ganinta, shi kuwa ya Kura mata idanu. Can ya ce, “Adiyya? Zo nan.” Www.bankinhausanovels.com.ng
Yadda ya yi maganar ne, ya sa ta miKe jikinta na rawa, ta isa kusa da shi ta zauna a Kasa. Sai da ya Kare mata kallo sannan ya ce, “Wani abu Asma’u ta fada miki ki ke kallona?” Da sauri ta dago, me Adda Asma’ kuma za ta fada mata? A’a ba ta fada min komai ba.” “To, me ya faru?” “Babu,” Ta fada a tsarge. Ki shirya Monday za ki fara zuwa office, zan ba ki lambar Fayemi ki same shi idan kin je. Zai ba ki duk abin da ki ke buKata, don ina ga by then, zan tafi US ba na gari.”Yaya amma…” Amma meye? Ke an fada miki aiki yana da arha ne? Na fada miki ga yadda za kiyi, kuma za ki ce min amma?” “To na gode, idan ECN suka nemeni fa?” Ta fada cikin Karamar muryarta tana kallon Kasa, ranta a cunkushe.
“Ki dai saurara tukun. Zan yiwa Abba bayanin komai.”
Godiya ta sake yi, sannan ta miKe za ta tafi daki, tsayar da ita ya yi yace, “Ki sama min wancan kunun naki.” Murmushi ta dan yi, ba kasafai ciye-ciye ya dame shi ba, amma haka nan yake son
Kunun semovitan da take yi. “Babu, amma bari na yi maka.” Ki barshi kawai, tunda babu.” A’a bayi da wuya ai. Yanzu zan kawo maka.” Ta fada, sannan ta wuce kicin, cikin minti goma sha biyu sai ga ta ta fito da mug cup, yana turiri da teaspoon a gefen saucer plate. Karba ya yi a hankali, ya yi mata godiya, yana shaKar Kamshin Vanilla da ke fita daga cikin kunun, za ta tafi ya ce, “Kin hadu da mijin Asma’ ne?”
Ta rasa dalilin tambayar, sannan yaushe Zunnu ya zamo mijin Asma’, tunda ba a daura auren ba?
“A’a tukuna, tana mana rowa dai. Wani abu ne?”
Ajiye kofin hannunsa ya yi kan dan saucer plate din, sannan ya ce, “Zauna na tambayeki.” A sanyaye ta zauna inda ya nuna kujerar da ke gefen nasa. “Kin ga alama tana sonsa sosai?” Hannayensa ya hade wuri guda_ yana sauraronta, “Yaya Zaid, kun fi kusa da ita, ai ya kamata ka fi ni sani. Amma dai iya abinda na sani, shi ne tana cikin farin-ciki. Amma me ya Sa ka tambaya?” Yatsina fuskarsa ya dan yi sannan ya ce,
Kawai dai. Ni sai na ke ganin kamar sun yi sauri, tun ba yau ba, ina fada mata.” “Yaya Zaid yanzu fa Www.bankinhausanovels.com.ng shekarar su uku, kusan na hudu suna tare, wane sauri ne a ciki? Ina tsammanin duk wani halin juna sun gama sani, ko shekara daya ne, idan har akwai aminci a tsakani, yaci ace an san halin juna. Ni kam ina ga sun dace, don yadda yake ji da ita, haka ita ma ta ke ba shi muhimmanci.” Hmm! I see.” Kawai ya ce tana ganin yadda fuskarsa ta sauya kamar akwai abin da zai sake fadi, sai kuma yace, “Shi kenan, na gode.” Ita dai tunda ta bar falon, tana mamakin kalaman Yaya Zaid, tabbas ta san da wani abu, idan har ba shi Adda Asma’ za ta aura ba, kuma ba shi take so ba, to kuwa tabbas Yaya Zaid ita yake so.
*************
Kai tsaye ta sameta da suka zo kwanciya ta ce, “Adda Asma’ ni me ya raba ku da Yaya Zaid ne?”
Cikin tsantsar mamakin kalaman Umm Adiyya, ta juyo hade da yaye bargon jikinta. “Wa ya fada miki daman muna tare bare mu rabu?” “Haba Adda Asma’ me ya sa za ki boye min, ni na san komai dai. Tun farko shi ne ko?” Murmushi ta yi sannan ta ce, “Ni babu wannan a tsakaninmu, shi dai kawai yake tunanin, dama akwai wani abin, amma ni kam na nuna masa babu komai.” “Anya kin tabbata ya fahimta? Don kuwa har gobe Yaya Zaid ke yake so.” Asma’ ta Www.bankinhausanovels.com.ng kwashe da dariya, har tana cewa, “Wayyo cikina. Yaya Zaid din ne ya fada miki haka, ko kuwa wani ki ka ji yana fada?” “Ni na ga hakan a tare da shi.”
“Ummu A, idan ba ki san wani abu ba, yau ki sani, idan har akwai abin da Yaya Zaid yake so duk duniya, to shi ne (AZ Consultants), wato kamfanin sa da komfutocinsa. Ni ban taba ganin mutum irin sa ba. Don haka duk randa zai so wata ‘ya mace, ina fada miki duk duniya sai sun sani. Saboda ba Bangaren sa bane wannan. Wai sai da na fada masa abokin sa ya ce zai turo tambaya gida, shi ne ya hau ni da
fada akan me ya sa abokinsa yana nemana, ba zan fada masa ba, sai da magana ta kai har kan tambayar aure? Wai shi a dole yana kishi, shi sona yake yi.” “Ke me zai ba ki tabbacin ba sonki yake yi ba?” “Saboda na san so, kuma ko kadan ba wannan bane a tare da Yaya Zaid game da ni, illa shaKuwa ta ‘yan-uwantaka. Sai dai tsaya me ya kawo wannan tambayoyin kamar wata ‘yar jarida?”
Da sauri Umm Adiyya ta shiga cire dan-kunnenta ta kau da kai ta ce, “Babu, kawai shi ne ya tambayeni dazu ko kina farin-ciki da zabinki.” Murmushi Asma’ tayi “Ummu A, yana da kirki sosai kin sani ko? Ki ba shi time komai zai daidaita.” Da sauri ta waiwayo tana duban ‘yar-uwarta. Ita kuwa ta lumshe mata idanu, “Haba, ‘‘yaruwa kin dauka tuntuni ban san me ki keji game da Yaya Zaid bane? Na san cewa kina sonsa. Na ga yadda ki ke kallonsa, idan kin dauka ba mai kula da ke, na ga yadda ki ke damuwa, duk sanda ya yi tafiya, na ga yadda ki ke kakkarwa, idan ki na aiki a gaban sa. You always look clumsy around him. Ke da komanki ki ke yinsa a tsanake, abu biyu ne zai sa hakan ko dai ki na tsantsar tsoronsa, ko kuma ki na matuKar sonsa ki na KoKarin boye hakan.”
A hankali ta zauna a bakin gadon, ta damKi zanin gadon a cikin hannunta, gaba daya sai ki daburce idan yana wuri.” Hawaye ya hau bin fuskarta, “Adda Asma’ ban san yadda zan yi ba, tamkar me ciwon hauka, na yi iyaka KoKarina na cire abin da na ke ji a raina, amma na kasa, har addu’a na ke yi sonsa ya bar ni zuciyata, amma ba abinda ya canza, sai ma Karuwa.” “Haba Ummu A, wannan ya sa ki ka shiga tsananin damuwa lokacin da ki ke tunanin ko Yaya Zaid zan aura?” Kai ta gyada mata a hankali. Www.bankinhausanovels.com.ng
Hannunta ta riKo ta ce, “Ummu A, kar ki sake yi min haka, yaya za ayi ki yi shiru kan wannan maganar? Ashe ba za ki fada min ba? To da yanzu hakan ne fa sai ki zuba idanu ki cutar da kanki har mu yi auren? Gaskiya ba ki kyauta min ba, kar ki sake yin shiru kan irin wannan al’amarin.” Adda Asma’u to yaya na iya? Tunda ni kuma Kaddarata kenan, kar ki manta bai ma
san ina son sa ba, sannan kwata-kwata ma hankalinsa baya kaina, ke yake so. Ke da bakinki kin fada yanzu.”
Asma’ ta sauke numfashi tace, “Ina tabbatar miki yadda hankalinsa baya kanki, haka baya kan kowa, saboda haka ke dai ki yi ta roKon Allah zabinsa, idan har da rabon za ku yi aure za ki ga cikin ikon Allah shi ma sai Allah ya saka masa soyayyarki a zuciyarsa. Ko ba komai, ku na shiri, wannan ma wani Karin sauKi ne, don haka ki daina damuwa.” “Adda Asma’ ni na dade da rarrashin zuciyata game da shi, saboda hakan ne ma bana bawa kaina fata na Karya, don na san ba abinda zai faru, ke dai ki min addu’a
kawai. Saboda al’amarin Adda Zubaida ya gwada min koda wasa kar ka sa kanka a cikin abinda ka ke tantamansa, ki ga irin rayuwar da ta fuskanta a gidan Isa. Ba zan iya yin irinsa ba, duk haKurina shi ya sa na yankewa kaina danne duk wani abin da na ke ji game da shi.” Tausayin Kanwarta ya kamata matuKa, haka suka raba dare suna magana. Ko Maami ba su bari ta san me yake faruwa ba. Abba ko yana gama jin bayanin Yaya Zaid. Ya amince Umm Adiyya ta fara aiki da su, idan wancan na Bauchin sun nemeta sai ta tafi.
***********((
Yau Talata yau ne. Umm Adiyya ta kammala shirinta na fara aiki da kamfanin (AZ Consultants), ta gama shiryawa tsaf! Cikin shiga na kamala, atamfa ce a Www.bankinhausanovels.com.ng jikinta sai hijabin da ya shiga da shi, kallo daya kawai za ka yi mata, ka dauka matar aure ce. Tunda ‘yan matan yanzu sun banbance yanayin shigarsu da ta matan aure, duk daa addinance kuwa, fasalin hijabi duk guda ne, ko ‘yan mata ko matan aure ko dattawa. Kai tsaye tana zuwa office din ta shige ciki kasancewar ta taba zuwa kusan sau biyu ko uku dalilin Asma’. Sai dai sai da ta hada da tambaya, sannan ta samu Fayemi, mutum ne kakkaura bai cika tsawo ba, yana da fara’a sosai, don nan da nan ya
washe mata baki ya fara, “Welcome, Ajiya”. A cikin harshensa da ka na ji, za ka fahimci shi bayarabe ne. Shi ya yi mata bayanin komai ya kuma nunata ga sauran ma’aikatan da suke nan. Asalin dakin ofishin da za ta yi aiki, su shida ne a ciki, daga ita sai wani wanda aka nuna mata shi sunan shi Oga Musa, sirirri ne fari da dan tabarau dinsa farare daga gani dai, Kabila ne, sai kuma Hasan, shi kam Bahaushe ne, bai cika tsawo ba, amma ya faye surutu kamar Aku, baya kwama bare fulstop. YaKe kawai Umm Adfiyya take masa, da ya shiga mata bayanai har da wanda ba ta
san manufarsu ba. Sai Oga Akim, wanda shi ne shugaban bangaren da take. Dadinta dai daya sun mata kyakkyawar tarba, sannan Jamila ita ma tana da faram faram. Hakan ya sa ta dan ji sauKi, zuwa washegari ta fahimci Oga Musa mutum ne mai
tsannanin tsabta da tsantseni, don baya sayan komai yaci. Daga gida yake kawo abincinsa, yawanci kayan marmari a yanke a robar take away. Minti kadan kuma zai murza man kariya daga Kwayoyin cuta (Hand sanitizer). Bai cika magana ba, wannan ya sa tasu tafi zuwa daya. Sai Ayo wanda maye ne wurin tsare-tsaren kwangila, don idan ya ritsa komfuta ko Charles Babbage (Mutumin da ya fara kirkiro komfuta) iyakaci, ance wataran a ofis yake kwana.
Kwanakinta hudu tana zuwa, kuma ba laifi ta fara gane kan komai, minti kadan wani daga cikin manyan zai leKo ya tambaya ko tana buKatar wani abu. Ko yadda suke mata, ta san hala Yaya Zaid ya fada masu ita Kanwarsa ce. Www.bankinhausanovels.com.ng
Sai dai duk yadda take son danne lamarinsa a cikin ranta ta boye, bai hanata jin kewarsa ba na tafiyar da ya yi tun ranar Asabar, yau kwanaki shida kenan. Yau kam da motar Maami ta fito ofis, ta zo shiga ne. Sai ga Oga Musa ma ya sauko ya bude tasa motar, ya yi mata murmushi sannan ya ce, “Have a nice Juma’‘ah.” Godiya ta yi masa ta shige cikin murmushi. Ba kasafai ya faye magana ba, sai ta kama dole.
Duk da kasancewar yau ba su yi wani aiki so
HMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG