UMM ADIYYAH CHAPTER 61 BY AZIZA IDRIS GOMBE

UMM ADIYYAH CHAPTER 61 BY AZIZA IDRIS GOMBE

                    Www.bankinhausanovels.com.ng 



Mun tsaya 

Ina, sai dai ki gwada mata ja da mulmulewa.
You’re just too adorable (ke abar so ce, har ma
kin kure).” Www.bankinhausanovels.com.ng
Da ya gama ta kalli kanta, a madubi ta tuntsure
da dariya saboda guda biyu ya
kukkulla mata, suka yi kama da kahon rago.
Har yanzun da yake tuna wannan lokacin, sai
dai ya ji gudun zuciyarsa ya karu.
“Kin faye shiga rai Twinkle.” Ya fada hade da
shafe kan wayar, nan ya shiririce da
kallon hotunanta, wasu ya yi dariya, ya girgiza
kai wasu kuma ya yi tsam zuciyarsa
ta cika dam! Da abubuwa masu nukurkusa

wannan tsokar. Lokaci guda ya fita daga
wurin hotunan gaba daya. Ya runtse idanunsa
ya hadiyi wani abu hade da maida
kansa jikin filo.
“Good night, Twinkle.”
***********
Juyi ta yi a kan gadon, ta dago kanta cikin
saurare, gabanta ne ta ji yana yawan
faduwa. Wannan ya sa ta mike ta mutsuke ida
nunta ta shiga bandaki ta dauro
alwala. Nafila raka’a biyu ta yi ta dade tana ad-
du’o’l, cikin sujjadarta, bayan ta yi
sallama ne, ta yi addu’ar Istikhara. Sannan ta
koma ta kwanta.
********
Yau ce rana ta farko da suka yi da TJ. Zai zo gida
ya ganta. Kasancewar hutun da
aka yin nan tana Abuja gidan Abba. Gaba daya
zuciyarta gudun famfalaki take yi

Www.bankinhausanovels.com.ng
kamar wata karamar yarinya.
Ta kira Asma ya yi sau biyar a waya. “Adda
Asma to idan ya tambayeni wani abinda
ba na son na amsa fa, me zance masa?”
“Lalle Ummu A. Na yarda Yaya Zaid ya yi
miki shigar sauri. Ke wato ma kwata-kwata
ba ki san me ake fada ba a zance ko? Na zaci
kafin shi dai da kin taba kula wasu.”
“Ina kuwa zan sani Sarkin yaki ya zo farauta,
ai ba ya jira a soma Magana, yake cin
ganima.”
Adda Asma ta yi dariya har ta gode Allah, “Za
ki kulle min ciki, ina nan ina ta dariya,
kawai ki kasance kanki, ba wata yaudara,
kuma ki amsa masa duk abinda ya ke son
sani bilhakki, shi kenan fahimtar juna, shi ya fi
komai.”
“Na gode.”
Ita dai Asma’ mamaki ne ya isheta, wai yau
Ummu A. Ce mai kira a ba ta shawarar
yadda za ta kula wani mai sonta. Ita da tun tana
yan mata ma, kowa ya zo korarsa
take yi, ba ta sama da sati biyu da saurayi,
kankan ta dade wata daya ne za ta ce
bai mata ba, don har tunanin jinnu ne suka au-
reta ake yi, amma ashe ita soyayyar
Yaya Zaid ce ta yi mata yawa. To yanzu kuma
ga TJ. Fatan ta daya. Allah Yayi mata
zabi mafi alkhairi, ya kuma sa a kare lafiya.
Tana gama waya da Adda Asma’, ta shirya
cikin doguwar riga mai kama da siket da
riga, kasan siket din launin kkasan teku,
saman rigar ruwan madara an lullube shi
da leshi, ga dogin hannu a jikin rigar. Ta yi
kyau ta kara zama cacas! Da ita.
Tunda TJ. Ya iso kuwa, ta kula da yadda ya ji
dadin ganinta, ita ma dai yau kam ta
tsaya, ta dan kare masa kallo a fakaice, ka-
sancewar tana tsaye ne a farfajiyar
gidan, don ta shigar da shi falon da za su za-
una, cikin shekarar Abba ya yi gyara, ya
dan canza fasalin gidan nasu.
Yana da tsawo da faffadan jiki, kallo daya za
kayi masa, ka san yana wasannin
motsa jini, baki ne, fuskarsa kuma ba ta faye
fai ba, yana da siririn gashin baki da
kuma fararen idanu. Yadi ne ruwan toka a jikin
sa, ya sha aikin hannu, sai hular da
ta daidaitu a saman kansa. Tunda ya sauka a
mota kuwa, Kamshinsa ya mamaye
filin gidan.
Sai da tayi masa masauki a falon bakin Abba
ne ta ce, “Na dauka ka bata ne ai, har
zan sa a je cigiyarka.” Www.bankinhausanovels.com.ng
“Fadi gaskiya ke dai, kin zaku ki ganni.” Ya
fada yana kallonta ta kasan idanunsa.
Umm Adiyya tayi dariya ta ce, “Ka yi one
zero, kuma zan rama. Bare ma dole na
zaku ai, zuwa ne kamar ta shugaban kasa, tun
Karfe biyu aka ce za a zo, sai biyar
da rabi aka samu isowa.”
“Na zaci zan gama abinda na ke yi da wuri ne,
na nemi wayarki na shaida miki
sauyin shirin, sai kuma bai shiga ba.”
“Ba damuwa, daman ka na cewa biyu na ajiye
a shida, na ga kokarinka ma ai. An
samu ragin minti talatin.”
“Maman Walid dai tayi min shaidar latti, an
kuma kamani da shi. Yaya gida, yaya su
Maami?”
“Lafiyarsu kalau. Alhamdulillah.”
“Yau kam ga ki a garin shugaban kasa, na fara
tunanin zuwa na janyoki ai, sai Allah
ya taimaka suka dubi al’amarina suka ba ku
hutu. “
“Uncle TJ. Kenan.”
“Allah da gaske, har Hajiya ta fara cewa wai
kai yawon me ka ke yi ne kullum ka na
kan titi. Ba ta san dawar garin ba, amma
kusa ta shaida.” Murmushi ya yi mata
a
sannan ya ce, “Kwanan nan in sha Allah.”
“Lalala, ka rufa min asiri. Muna ‘yar mutumci
da Hajiya.” Kanta ta saddar kasa, ta ki su hada
idanu da shi.
“Akwai mutumci sama da batun aure ne? Ke
kin faye tsoro, ba daman a fara
Magana, sai ki fara yin kwana, yau ba zan bar
gidan nan ba, sai da amsa, gwamma
kin shirya ba ni guda.”
“Ga shi ba ka fada min ba, balle na shirya abin
faci.”
Kura mata idanu ya yi ya yi murmushi, “Ki
fada min Ummu Adiyya, me ya sa ba kya
son zurfafa maganarmu ta kai gaba ne?”
Rausayar da kanta ta yi gefe guda, “Har ma sai
ka tambaya?” Www.bankinhausanovels.com.ng
“Ki fada min, zan so na ji daga gareki, kar nayi
miki gurguwar fahimta.”
“Gaskiyar magana ita ce, ka na zaune lafiya da
iyalinka, rana tsaka na zo na fado
maku rayuwarku, ban son shiga hurumin mu-
tum, a dalilina ace rayuwarka da take
tsanake ta shiga wani hali a dalilina, ni dai
abinda ba zan so ai min ba, ba zan so ayi
wa wata ba. Kuna daidai gabar daya dace ku
na Kara sanin juna, ku duka sabbin
iyaye ne, ku kula da rainon Minaal dama
dalilai da dama…”
Ganin kallon da yake mata, ya ba ta tabbacin
bai gamsu da dalilan da ta ba. Don
haka ta kara da fadin.
“Sannan kuma Uncle TJ. Ba zan iya maka ba.
Ka na bani tsoro, and ba wai kai
kadai bane, maza gaba daya suna ba ni tsoro.”
Kada harshe ya yi ya ce, “Me yayanmu yayi
mana haka ne da har zai bata min
damata a karo na biyu? Duk da ma dai na ce za
mu cire shi a layin yayyin, idan ya yi
wasa. “
“Bai da gami da Yaya kawai dai..”
Wani gajeren murmushi ne ya ziyarci
labbansa, lokacin da ya kafa mata idanu, “A
tunanina za ki iya da ni, yadda ya dace. Fada
min me ki ke so da ni? Kin san ina da
hakuri, zan iya ba ki duk lokacin da ki ke
ganin ya dace ki dauka wurin gama
kimtsawa, ki shirya zuciyarki.”
Me ki ke yi Umm Adiyya, ki na ji, ki na gani
za ki
sake bari ki kwaba rayuwarki da
kanki, ba abinda tunanin rayuwarki zai had-
dasa miki, illa da-na sani.
“A shirye na ke yanzun ma kawai dai..”
“Kawai dai ni din ne? Oh TJ. Ka ga ta kanka.”
Dariya ta yi sosai, ganin yadda ya zuba tagumi.
“Nooo, ba fa kai bane.”
Sauke tagumin ya yi, fuskarsa ta washe hako-
ransa suka bayyana cikin murmushi.
“Wannan yana nufin ba ki dai da matsala da ni
kenan, da auren ne. Maza sun ga ta
kansu.”
“Ba ni da matsala da kai, ba ni da matsala da
aure.”
“To menene matsalar a nan?”
********** Www.bankinhausanovels.com.ng
BABI NA ASHIRIN DA TARA
*********
Kawai lokacin ne.”
Ki na ga zan iya canza miki ra’ayi mu tafi a
iya speed limit dinki?”
Yaya za ayi ya zuba mata idanunsa nan, ta iya
musa masa? “Sai dai mu gwada mu
gani.”
Hakan ya yi kyau, sannan ina so ki sani, ba ki
yi wa kowa kwace ba, tana da
huruminta da wurinta a raina, tamkar yadda ke
ma ki ke da na ki gurbin, saboda
haka stop feeling guilty (Ki daina jin dardar),
abin da ya fi muhimmanci, shi ne na
san cewa, kin amince na nemi aurenki wurin
Abba. Ummu Adiyya? Of course zan
nemi soyayyar ma a hankali, idan zuwa yanzu
ban yi tasiri ba, na san mutane sun
yaudareni shekaru ashirin da suka wuce zuwa
yanzu.
Ware idanunta ta yi ta ce, “Da aka yi yaya?”
Da suke kirana Material mana.”
“B a rabaka da abun ban dariya. Wani abu ne
hakan yake nufi?”
Ki tambayi su Mahmoud, idan kin gansu,”
“Bayan gani ga mai sunan?
“Ba komai bane, da ya wuce da na yi wasan
kwallo sosai, to duk bangaren da zan yi
wasa, sai suke kirana hakan, saboda a cewarsu.
Ni abun a ajiye ne ayi tattali. .”
“Hinyau, kai kuma sai kanka ya budu da suke
ce maka haka?”
“Ba da yawa ba, dan daidai haka. Mu bar wan-
can zancen, na kula ba ki ba ni
amsata ba, idan kuma shiru amsa ce, shi kenan,
gobe ma sai na zo da jama’a a
shafa Fatiha.”
Murmushi kawai ta yi, amma har yanzu wai ta
gaza yarda, duk kishinta har tana iya
cewa tana shirin karbar tayin soyayyar mijin
mutum. Rayuwa juyi-juyi kenan.
************
Har waje ta raka shi ta kofar falon bakin Da ta
tashi komawa ciki ne, ta bi ta babban
falon kasan. Kanta a sadde, tana nado zancen
da suka yi da TJ. Mutum mai saukin
kai, barkwance, ga hakuri, ga shi ya san
hakkin dan Adam. Ba abinda ya burgeta da
shi, illa yadda bai boye mata darajar matarsa a
wurinsa ba. Www.bankinhausanovels.com.ng
Sabanin wasu mazan idan sun je neman karin
mace, sai su yi ta aibanta ta gida,
suna nunawa mace ita ce maganin matsalolin
da suke da su. Su kuma matan abin
takaici, sai su zaci haka abin yake, sai sun
shiga su gan shi da matarsa tif da taya.
Cak! Ta tsaya tana kallon takalman, kafin ta

HMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *