UMM ADIYYAH CHAPTER 75 BY AZIZA IDRIS GOMBE
Www.bankinhausanovels.com.ng
Suna kammala wayar ne, ta fito falon Hajja
Ku, nan ta tarar ana shigewa daya dakin
da bokitai biyu masu tururi, sai kamshin da ke
tasowa daga hayakin.
“Hajja ce ta ce a shigo miki da shi, idan kin
shirya.” Mai aikin Hajja Ku ta fada.
“Idan na shirya me?”
Muryar Hajja Kubitto ta juyo tana cewa, “Yau
za a fara saka ki a lalle, ba kya dai
tsammanin mu kaiwa miji ke haka, ba gyara ba
kimtsi ko? Mu ba a mana haka ba,
don haka ba za mu sa idanu ayi miki haka ba.
Ga nan wadannan bokitan dafaffen
Lalle ne da ganyen magarya, masu kyau Www.bankinhausanovels.com.ng da
tsafta, ki surka ga ruwan turaren muski
nan zan ba ki. Idan kin yi wankanki na sabulu,
to wannan ruwan kuma shi za ki yi
wanka da shi a karshe. Hakan kuma za ki yi na
tsawon kwse anaki uku, kafin ki bar nan
gidan.”
Umm Adiyya kam ware idanu ta yi da baki
tana kallon Hajja Ku, tana jin bayanan da
kala-kala da