UMMI AISHA CHAPTER A

 UMMI AISHA CHAPTER A

Tasss ta bata wani kyakkyawan mari me tafiyar da mutum lokaci daya.. Sannan dayar wadda suke tare itama tasa hannu ta tunkudeta ta fadi akasan tiles din dake a parlor din dagudu Wata yar’madedeciyar mata tafuto daga kitchen da alama me aiki ce tana fadin”aunty lapia naji kara haka?!tana isowa parlor din taja tai turus ganin wa’enda suke a parlor din Se huci suke inda sabo sunsaba xuwa suyi haka wani lokacin har ita suke hadawa siwa lilis sosai tabo na a dukkan jikinta na dukan dasuke mata baxasu irguba ,”murya narawa ta tsugunna har kasa tana gaishesu ina wuninku addah surayya da addah

sadeeya?!wacce takira da “addah surayya tana wani sunce mayafin datai damara dashi a kugu Sannan ta yafa akanta tana huci kamar tsohuwar karya tareda kada idonta Ta aikamata da wata muguwar harara tajefawa yar’aikin. dabamu wuniba xaki ganmu yar’aiki?! Nayi tunanin yauma xaki shisshigin dakika saba kice xakisaka wannan hannun naki dayasha kanta kice xaki  rabiyar fadan wannan yar iskar tasa hannu Tana nuna matar dake kwance akan tiles da alama she’s unconscious kila ta suma ma.wannan juyar (wadda bata haihuwa)dan kwa juya xance tunda bata aikin Komi sede taci Tasha tacika masai da kashi Allah ya isan wanmu daya auro Tama Wlhy kila kyanta da kalar datake dashi yarude shi dama mata sekace aljana Dan Kyau.. shekara kusan 20 ba haihuwa kullum jiya’i yau da ike angama dashi tawanke tabashi yasha ai yakasa Komi kullum cikin fadar basu cire rai… Bata karasa maganar ba wacce aka kira da “addah sadeeya tace enough surayya kina bata bakinki kina wa yar’ aiki magana dallah xomu wuce mutafi dukan wani satin inya xagayo Ma seyafi wannan wallahi..Sannan suka fice ,itade yar’aikin bata tanka masu ba Se rufe kofar datai Sannan ta koma tana jijjiga matar dake kwance kan tiles din batako motsi”aunty,aunty..shiru kakeji bashiri tai kitchen tabude freedge tadakko ruwan gora me sanyi tabude ta yayyafa wa matar,,cikin ikon Allah kuwa matar tafara atishawa tana rike da kanta dan yadda yake sara mata kamar ze fado dan ciwo tarike kan tana salati Sannan tai addua tagoga akan..”dakyar tabude bakinta tace haule temakanni da pain killer cikin drawer jikin tv..da azama haule tamike tadakko takawo mata Sannan tace tadakko mata ruwa marar sanyi xatasha maganin dashi. Tasha maganin kenan tabude baki”tace haule temakanni nahau kan kujera Dan Allah .rufe bakinta keda wuya wani dattijon mutun yashigo ciki fari kyakkyawa yanada tsaho da jiki madedeci fuskarsa dauke da murmushi kamar kullum yashigo da dan trolley ahannunsa dakuma leda a dayan hannun “yadan daga murya Yana fadin Hajia Hafsat nadawo ai tafiyar nan baxata yiwuba yau..cak yatsaya da maganar lokacin da muryar haule me aiki ke reto akunnensa Tana fadin sannu da dawowa abba,ganin Hafsat dinsa kwance akujera goshinta yakumbura yayi suntum ga kuma parlor din yayi kaca_kaca da alama wani abu ya faru!

+
Bashiri yasaki trolley da ledan hannunsa akasa yanufi inda Hafsat din take Sannan yadagota yadora kanta a cinyarsa Yana duba goshin ga jikinta yadau zafi rau sosai daka ganta kasan batada lapia..”ahankali yace my Hafsat meya faru?!  dakyar “tabude baki tace hayatee(rayuwata,my life)bakomi bigewa nai da…setai shiru Tana naxarin da mexatace tabige Sannan tace ruwane yadan xube kan tiles shine na zume nikuma nabige da tiles dinnan Sannan Ta sunkuyar da kanta kasa Dan bata taba fadawa mijin nata cin kashin da yan’uwansa suke mata ba Sannan tace haule Ma karta soma fada sosai sunfi shekara 15 suna ci mata mutunci amma dede da rana daya bata taba fadawa mijin nata abinda ke faruwa ba.. Sosai yaji tausayinta Sannan “yace toh sannu my Hafsat kiringa lura pls shisa nace akaro wata wadda xata dinga kula dake kinki ,banasan kina wahala my Hafsat ..”Hajia Hafsat tai shiru azuciarta Tana yaba yadda mijin nata ke sonta baya san ganin bacin ran nata ko kadan yawanci idan tai masa maganar ya’ya yakance ita yakeso ya aura bawai danta haihu ya aureta ba,hakade yake yawan fada mata kyawawan kalamai masu sanyaya zuciya. ” my hafsat kinyi shiru’ “Hajia hafsat tace haule Ma kadai Ta Isa hayatee ,Sannan tadanyi murmushi Ina tafiyar kuma naga kadawo ?! Yai Daria da dimples dinsa suka lotsa Sannan yasa hannu Yana gyara mata gashin kanta “my hafsat wallahi wakili natura Dan wani bangare na zuciana Yana cemin Kai mijin hafsat kakoma gidah your Hafsat ba lapia kawai naji baxan iya tafiya nabarki ba shiysa nadawo ashe ashe  dagaske ne bakida lapia wannan tiles din yazumeki,gobe xansa acireshi asa marbles ma..Hajia Hafsat tai Daria calm down hayatee baruwan tiles dinnan ruwane yaxube fa,haka kwanaki fa daga tv yajani seda kacanxa TV sets din duka uhm uhm hayatee nide kabarshi Allah Bakomi nawarke..sosai sukai Ta Hiran soyayyarsu kaman basu manyantaba  ya Allah kabarmu damasu sonmu!ledan daya siyo yadakko kaji ne ciki soyayyu sekuma bracelet na azurfa mekyau dashi anrubuta*my hafsat *ajiki.sosai Hajia Hafsat tayiwa hayatee dinta godia danbaya gajiya da faranta mata rai.hugging dinshi tai tana hawaye “I so much love you hayatee Allah yabarmun captain adam dina amin…

STORY CONTINUES BELOW

WANENE CAPTAIN ADAM ABDULRASHEED?!

Shide asalin captain adam abdulrasheed Dan asalin garin hadeja ne,don dukkan iyayensa uwa da uban duk yan’  cikin garinne.amma yanxu iyayen nasa suna garin kaduna,ko ince mahaifiyarsa na garin na kaduna Dan mahaifinsa Malam  abdulrasheed yadade da rasuwa..suna zaune a unguwar dake kaduna wato Halliru dan toro dake malali GRA!

Itakuma mahaifiyarsa Hajia ateeka yar unguwar kasuwar kofa ce dake garin na hadeja ,aikine yakawo me gidan nata kaduna Wanda Allah yayi nanne wajen zamansu.

A nan garin kaduna suka haifi dukkannin ya’yan nasu sunada ya’ya guda 5 alhaji sameer shine babba Se Capt. Adam Wanda sailor ne se kuma kannensu mata wato addah surayya da addah sadeeya Se karamar su bilkisu.kafin rasuwar mahaifinsu yakasance business man ne Yana saro kaya Sannan sunada shagon saida laptops dakuma makaranta takoyarda computer ..babarsu itakadaice awajen babansu har Allah yakarba ransa.yakasance harkar da mahaifinsu keyi Ta computers ita babban Yaya wato alhaji sameer yakeyi ,Sannan kannensu mata duk sunyi aure inda dukkansu a Kano suke da xama Se karamar wadda akai bikinta bara Tana zaune kadunan ita.

Tunda captain Adam yagama karatunsa yanufi gidan abokin babansa dake kano ,anan yasamu scholarship yatafi karantar bangaren sailor a mariners university of birmingham dake England.bayan dawowarsa sosai yasami aiki awani qualified company dake abuja..bayan dawowarsa ne idanuwansa suka hadu Dana nana hafsat ya’ ga kanin abokin babansa..nande soyayya dakuma shakuwa Ta tsanani tashiga junansu harde abu yafito fili tana kammala secondary school lokacin Tana shekara 18 aka hadasu aure da captain adam..sosai sundace da junansu  Dan nana hafsat karshe ce akyau to shidinma captain Adam kyakkawanne,ashekarar yanema transfer daga Abuja xuwa kano ashekaranne kuma sukai aure suka tare a unguwar sardauna crescent dake badawa kano…shiru shiru nana HAFSAT na xuba Ido amma haihuwa shiru takanyi kuka tasa kanta cikin damuwa amma “captain Adam Yana kwantar mata da hankali tareda fadin da haihuwa da aure da mutuwa duk lokacine arubuce yake.tun yan’uwnsa naganin kamar xata haihu shiru kakeji wai maye yaci shirwa tuni suka fara jefa mata magana.. da lokaci ko ince shekaru suka shude abu seya canxa tuni raini yasake shiga tsakaninsu ganin bata tanka masu kuma da alama wannasu bashida masaniya akai ganin bata fada mai ba besaniba,Se duka kuma da gorin fadin juya ce bata haihuwa sede taci tai kashi takwnta tai barci!!!

Kodah safe bayan Hajia Hafsat ta tashi sosai ta taya haule me aiki gyara gidan Sannan suka hau shirye shiryen kayan breakfast:soyayyen Kosai dayaji hanta da kwai sukai Se plantain da aka soya dakuma doya gefe daya kuma lafiyayyen kwai ne da yaji vegetables Se soup din Kayan ciki dakuma kunun shinkafa dayaji kayan kamshi..sosai suka jereshi a katon dinning table dinsu Wanda xeci babban family of 15.sannan haule tasaka turaren wutan gaf gaf daya hautsine ko’ina da kamshi kamar a company din alharamein ,daki tashiga sannan tawuce bandakin dake cikin dakin Sannan tafaffesa turaren wuta dakuma toilet perfume eu de toilete sosai kamshi yahau tashi..”bude curtains din dakin tayi Sannan tadan daddaki gefen gadon hayatee,hayatee katashi kashiga wanka nahada maka ruwan,gashi har rana tafara fitowa yau kam kasha bacci abinka ka more..

Da salati captain Adam yatashi Yana mika wai my Hafsat Nagode sosai danma Allah yaso natashi nayi asubah a masallaci aida yau bansan mexankira kainaba kaman Wanda tse tse fly yaciza, Hajia Hafsat tai daria to atashi ashiga bathroom nahada Komi inka fito kuma your favourite breakfast na jiranka kan dinning “Capt Adam yai murmushi your wish is my command my Hafsat sena fito Sannan yamike yashiga bathroom Yana yaba kamshin dakuma yadda Hafsat dinsa tagyara ko’ina tsaf dukda kullum haka takeyi amma tsafta irin Tata gaba takeyi abin nata Yana matukar birgeshi sosai yakejin sonta naratsa bargon jikinsa.

Kodah yafito daga wanka ,yadi fari kal a goge yagani kan gado dakuma hula da takalmi a goge shima tayi polishing dinshi agefe ga turaruka da mai samfarin Vaseline na kasar waje shima ajiye agefe ,murmushi yai ganin yadda Hafsat dinsa ke kula da tarairayar sa tun sanda sukai auren saurayi da budurwa gashi yanxu shakera 20 kenan kuma babu abinda yacanxa nadaga kulawar dasuke baiwa junansu haihuwa ce kadai Allah bebasuba kuma har yau basu fitar darai kan hakan ba.cikin shirinsa na dattijantaka yai sauri ya kammala sa kayan nasa Sannan yanufi dinning  area dake parlor din,sosai kamshin aroma din abinci yafara masa sallama bashiri yakarasa cikin dining area din Yana my Hafsat your aroma is calling ,Hajia Hafsat ta durkusa tagaysheshi Sannan ta Kamo hannunsa suka xauna akan kujerun sosai tai serving mijinta cikin plates dakuma mugs atare suka xauna sukaci Komi suna feeding junansu abin gwanin ban sha’awa.

STORY CONTINUES BELOW

BAYAN sati daya ; captain Adam yai shirin xuwa headquarters dinsu dake abuja kamar yadda yasaba duk weekly,sosai Hajia Hafsat taji badadi Dan bakaramin kewar mijinta take ba in yatafi duk koda inyadade acan yai kwana 3 gashi tasan yan uwansa dole suxo su nada mata na jaki kamar yadda suka saba,adaki suke tare dukkansu da safe da alama alokacin xetafi Yana kallon mudubi Yana gyara karin hular Kansa sanann yadora akansa sosai yayi masifar Kyau kaikace saurayi ne dan shekara 30 baxaka taba cewa yawuce shekara 50 ba sosai yabi lungu da sako najikinsa Yana fesa turaruka, itakuma Hajia Hafsat Tana gefen drawer Tana shirya masa kaya cikin trolley dinsa,Yana gama sa links din hannun rigarsa yajuyo yakalleta yadda jikinta yayi sanyi ga idonta ya ciko taf da hawaye ,asanyaye yakara sa kusada ita yajiyo da ita amma taki kallon face dinsa danbatasan yaga damuwar dake face dinta dakuma hawayen dake kokarin zubowa a’idonta ahankali cikin sanyayyar murya yake fadin”my hafsat,Sannan yasa hannu yadago habarta tareda rungumota jikinsa ,”bansan kukanki please my hafsat kiyi hakuri kidanne zucianki karkiyi please idan kuma tafiyan ne bakiso inyi wallahy xaki mamakin kitashi da safe kiganni agarin kano,mexan samo acan abujan dayafi farin cikinki my Hafsat?!please kifadamin mekikeso?!dakyar Hajia hafsat tadedeta muryanta tareda kokarin maida hawayen nata cikin ido “hayatee bakomi,wani abune yadan shigarmin Ido kakka damu Allah yakaimun Kai lapia yadawo dakai lapia of course I’m gonna miss my hayatee but bayan haka bakomi.capt Adam yai murmushi yasa hannu ya gyara gashin kanta Yana Shafa bayanta it’s okay my hafsat insha Allah baxan dadeba xandawo ko ina naje afadin Dunia kisani Ina tare dake,haka suka danyi hiran soyayyarsu Sannan tarakashi parking lodge din dake gidan driver yajashi Se airport xuwa federal capital territory!

Asanyaye tadawo cikin parlor din taxauna tana daily tunanin ta,hawaye ne suketa reto a fuskarta ahankali tashiga yin magana abin tausayi..”Allah kayayemana damuwar dake cikin zukatanmu/zuciyoyinmu!yanxu diyar amina hartakai shekara goma shabiyar,”ya rabbi kayafeni ubangijin Rahama kasa inadaga cikin Wanda xasu dace da kyautar ya’ya hakika ya’ya rahamane,”wannan cin mutunci da kannen mijina sukemin nagaji dashi Sannan tasa tissue Tana goge hawayen fuskarta “naga suma basu sukaba kansuba kuma bawai Allah yafi sansuba,amma sundau kyama sundoramin saboda banida ya’ya ,,”gashide ba inda bamu xaga a dunia ba ance banida Wata matsala hakama hayatee,Toh bayadda xanyi amma basa gani ,”ya rabbi kasakamin kadorani akansu fiye dayadda suka daukeni,Tana cikin maganan ta haule me aiki tashigo ciki ta tsugunna akasa “aunty mexa’a dora da rana?! Hajia hafsat tai shiru kamar menazari Sannan tai ajiyar zuciya “banajin xan iya cin komi haule ,kidafa maku kawai duk abinda kike ra’ayin ci keda hannafi da modu(guardsmen)”haule tai kalar tausayi hakika tasan abinda ke damin auntyn tata dama kuma damuwar bata karuwa harse Capt Adam yakoma wajen aiki,ga fargabar xuwan yan’ uwansa kowanne sati da irin kalar rashin mutuncin dasuke xuwa suyi mata shi.shekara goma kenan da aikin haule agidan kuma duk sati yan’uwnsa  kexuwa  su badawa idonsu kasa a ido su zubamata bolar dasuka kwaso,amma dede da second daya Hajia Hafsat bata taba shedawa megidan nata abunda ke faruwa ba,sosai haule me aiki ke mamakin dama akwai saurin mata irin haka kamar Hajia Hafsat adunia?!to inma akwai su tabbas wasu tsirarine dabasu da yawa,da wannan tunanin da haule takeyi tamike bayan tace “Toh aunty Sannan takoma bakin aikinta a kitchen “yinin ranar haka Hajia Hafsat ta wuni batasa komi cikin taba Se ruwa,sefa aikin amsa kiran da hayatee dinta ke mata,har dare suna manne awaya Sannan bacci barawo yasaceta…washegari Ma abin da yafaru kenan dayake ba gwanar cin abinci bace dakyar haule ta roketa Sannan Hajia Hafsat Ta amince tace haule tamasu faten dankali da bushasshen kifi(smoke fish)! “Washe gari bayan tafiyan Capt Adam da kwana biyu ,Hajia Hafsat ce zaune akan darduma(praying mat)da alama sallah tai ta idar,gefe daya kuma littattafan zikirine da carbi,Se alqur’ani a hannunta Tana karantawa tana Kai aya tarufeshi sannan ta shafa a fuskarta tareda rufewa,Sannan tamaida komi inda yake ,jin kanta Yana ciwo yasa tadan mike akan gado nan take bacci yai awun gaba da ita..

“Addah surayya ce tai sallama tashiga parlor din gidan addah sadeeya dake unguwar Daurawa maiduguri road tarauni…”Tana shiga tadafe haba oh ni surayya,sadeeya kina nufin baki shirya ba wallahi kinfiya shininniki Allah de ya kyauta,..”sadeeya tai Daria Wlhy ni jikina ne yai sanyi karfa muje muga yaya Adam yadawo kinsan Wlhy da kashin mu ya bushe ranar,”surayya tai tsaki kede wannan yarinya da danbanxan tsoro kike kinmanta kwana uku yakeyi ne,kuma Se dare yake dawowa “Dan Allah tashi ki shirya kixo muje ni hannuna kaikayi yake gwara muje mu jibgi banza kinsan Allah nifa bawai danbata haihuwa kadai na tsaneta ba a’a ,”wallahi shegen kyawun datake dashi nakejin tsanarta araina wannan datana da ya’ya musamman ace diya mace wallahy dakinga layin zance agidannan to Se Allah yasan manufar jaki dabeyishi da kaho ba……..

STORY CONTINUES BELOW

                 •✨•

                    3

“Addah sadeeya tai Daria kai safeeya lalle kinfini tsanar matarnan,ni abinda yafi damuna yadda Yaya Adam yadau son dunia yadora wa matarnan yadda kikasan itakadaice mace adunia,”addah  safeeya tai tsaki kyaleshi can daya banzan,”yawwa  nikwa yamaganar magajiyan inno Fanta??kinsan fa lokaci yanadada kurewa inbata aminceba munemo Wata kawai,”addah sadeeya tace ohh about that ?!well munyi maganr da ita takuma amince tace inde har ya aureta to filin kofar na’isa yaxama namu Sannan gidan kajin nan dake lamido terrace shima yaxama namu,addah safeeya tabata hannu suka tafa”tareda doriyar yawwa yar’gari yanxu naji zance Kice muma munada rabon namu arzikin ashe..

“Addah sadeeya tace kwarai kuwa yanxu de gwaggo kawai zamu samu mushawo kanta tayadda Yaya Adam xeyadda ya amince ya auri magajiyan inno,,kinsan dadina da gwaggo saurin daukar zancenmu tai amfani dashi,”addah safeeya tai Daria kwarai kuwa yanxu de isauri kishirya kixo mutafi Dan Allah ..”suna gama shirinsu suka haye Dan sahu se unguwar sardauna crescent dake kano ,”suna xuwa addah sadeeya takalli modu megadi dajikinsa yadau  rawa  danbaxe taba mantawa da marin da ta sharara masa ba.. ranar daya hanasu shiga gidan sanin rashin mutuncin dasuke yiwa matar oga.”ayatsine  tace dashi kai megidan nacikine yadawo daga tafiyan?! Modu murya na karkarwa yake fadin a’a beda…bedawoba,,ko kallon inda yake basu karayiba  suka sa Kai suka shiga ciki .

“Parlor suka shiga inda kamshin faten dankali dayaji kifi yafara dukan hancinsu,adakile addah sadeeya kefadin eh lalle munxo  adede kenan,cikin kitchen din addah sadeeya tashiga tana kallon komi daya bayan daya ga tukunyar Akan gas tanata zabalbalar girki,haule dake rakube da nonstick spoon ahannunta tai tsuru tsuru daga bisani kuma ta tsugunna har kasa ta gaida addah sadeeyan,wadda dakyar ta amsa tana kokarin bude tukunyar sekuma ta fasa Tana kallon haule”ke idan Kingama kixubo manashi duka a foodflask kikawo parlor ,”Sannan Ina wannan juyar take?!haule tace ta..tana daki batada lapia ne..addah sadeeya tai tsaki Allah yakaro Wata akai ta mutu Ma shegiya mayya Uwar taurin rai,sanann ta fice takoma parlor ,”haule tai tagumi oh ya Allah yaukuma da wacce sukaxo haka?!Allah karabamu da mugun hali ameen!

“Haule nagama faten tajuye duka a flask seda tafaki ido taga basanan Sannan ta samu wani madedeci taxuba ciki tarufe taboye cikin kitchen carbinets dan tasan yadda auntyn kesan faten dankali.sannan tanufi parlor takai masu,”addah safeeya tabude foodflask din tana wani baje hanci kamar mayya iceko baki rage kokadan ba ?!dan Wlhy idan nagano kinrage senaci ubanki merabani dake agidannan Se Allah,haule ta sadda Kai kasa a’a duka najuyo maku shi dama badayawa naiba namune nidasu modu,addah sadeeya tace Toh xaki iya tafiya ,seda sukaci sukai nak suka kora da lemon donsimon dake freedge din parlor din Sannan suka mike suka nufi dakin da Hajia Hafsat take..”suna shiga addah safeeya tafara salati eh lalle Yayi Kyau sadeeya kalli yadda sanyin AC ketashi jiyadda juyar nan ta bararraje kan royal bed dinnan shegiya sede taci,tasha,takwanta tai barci.addah sadeeya ta takarkare tadaga hannu sama ta duma mata duka abaya jikake duuuuuum yadda Kasan drum akadaka.bashiri “Hajia Hafsat tamike Tana salati sekuma tasa kuka,addah safeeya tai tsaki Sannan taja kafar Hajia Hafsat basu direta ko’ina ba Se tsakiyar parlor sosai suka gurje mata jiki akasa saboda janta dasukayi..

Sehaki suke kmar Wanda sukai gudun fanfalaki,Hajia Hafsat tadago raunannun idanuwanta dasukai ja saboda azaba ta aza akansu “Dan Allah mena tsare maku?!wannan kiyayya har ina..”addah sadeeya tai tsaki ubanki kikai mana,sosai sukahau dukanta tako’ina tun Hajia Hafsat nabasu hakuri har azaba tasa tadena Se ajiyar zucia datake ,addah safeeya tai wulli da wayar charger datake dukanta da ita akasa sannan taxube akan kujera tana maida numfarfashi,addah sadeeya tahau ruwan cikin Hajia Hafsat taxauna tana Dariar mugunta “gwara mukashe ki mukashe banxa da wofi,haule me aiki dake lekensu tasaki kuka ahankali tareda jingina a drawer din kitchen “wannan wacce irin tsana ce haka?!

•••••

Capt Adam yai murmushi ,”yakalla driver dinsa dake tukinsa daga airport din Aminu kano xuwa gidansa sardauna crescent ,jirgi (yadda suke kiransa kenan Dan ya iya gudu na bala’i)”iceko bakacewa Hajia yau xan dawoba Dan suprise nake san mata,jirgi yakada Kansa “kodaya oga banfada mata kosu modu da hannafi basusan da xuwankaba..Capt adam  yace “Yawwa jirgi nagode kwarai..sosai suke hirarsu har suka Isa kofar gidan ,”Capt adam yace Yawwa basekashiga da motar ba danxan aikeka nan shop rite .yabasa kudin shikuma yasakai yashiga sosai modu da hannafi sunji dadin ganinsa Sannan suka mai sannu daxuwa..modu yakalli hannafi “kan bala’i yau akwai ruguntsumi kenan,”hannafi yai Daria aigwara haka dama hausawa nacewa rana dubu ta barawo rana daya tame kaya!

Capt Adam Se murmushi yake yau xeyi toxali da sanyin idaniyar tasa kwana biyun dabe sata cikin idonsa ba jiyake kaman shekara biyu yai,,”da sallamarsa yashiga parlor din Yana kwala kira my hafsat…my ha..karaf idanuwansa sukai toxali da hafsat dinsa kwance akasa ga kanwarsa safeeya kan ruwan cikinta gefe daya kuma sadeeya ce tsaye da Waya ahannunta..

•✨•✨•✨•✨•✨•

Note;narubuta kanwar Capt Adam da SURAYYA a farkon page,pages na biyu Dana uku..inatasaka SAFEEYA,,wannan yafarune sanadiyar wajen typing Wanda wayata take samun haka..Ayi  hakuri pls,xandawo saka SURAYYA karnai confusing mutane.inafatan xaku gane🙏🏽

                   •✨•

“Karaf idanuwansa sukai tozali da Hafsat dinsa kwance akasa ga kanwarsa surayya zaune daram kan ruwan cikin Hafsat din,gefe daya kuma sadeeya Ce tsaye da wayar charger a hannunta..”bude idanuwansa yai yakara rintsewa shin wannan mafarki yake kokuwa dagaske ne?! Addah surayya  naganinsa tamike tana noke kai sosai saura kadan fitsari yaxubo mata Dan tsabar tsoro ita dinma sadeeya saurin sakin charger dake hannunta tai,suka koma gefe daya suka tsaya zuciyoyinsu Se harbawa suke abinka da marassa gaskia tuni idanuwansu suka firfito waje suna jiran abinda xefaru ..

+
“Capt Adam ya ajiye Kayan hannunsa Sannan ya fice waje bebi takansu sadeeya dasukai tsuru tsuru ba,Yana xuwa yace”modu ku kullemin gidannan da kwado kada kubude harse nabaku izini,Sannan xankiraku xaku amsa min wasu tambayoyi,bejira tacewarsu ba yajuya yasoma tafiya dayake da dan taxara  tsakanin gate din da kuma cikin gidan,”modu yakalla hannafi,yace yaufa xa’ayita kenan agidannan inaga watan sallamarmu ne yai shikenan,jar miya takare Se kuka koriya shar,kuma yau Se kauyen garin dau”hannafi yai shiru Yama kasa magana kwata kwata Se zare Ido yake musanman dayatuno kauyen na garin dau dayadda tuwo ne kullum ba fashi miyar nan koriya ko dandano babu,”yanxu kuwa saboda Allah yasaba cin jarmiya mehade da kaji..

“Kafin Capt Adam ya isa cikin parlor din,addah sadeeya takalla addah surayya dake faman xubar hawaye sekace tsohon famfon dayaki kulluwa.. “kede banxa ce wallahy Banda mukullawa shegia sharri,”addah surayya tasa gefen mayafi Tana share hawayen fuskarta tareda fyace majina”,kyaleni sadeeya wannan duk baxeyiwuba kawai de Se abinda Allah yayi .amma yau me karbarmu a hannun Yaya Adam Se Allah!tana cikin magana “Capt Adam yashigo gurin Hafsat dinsa yanufa ko kallonsu beyiba,sosai yasa hannu ya ciccibi abarsa yakaita daki yabata agajin gaggawa dayake akwai first aid box agidan ..sannu ahankali tafarfado daga suman datayi Sannan yadan sa ruwan dumi  ya gaggasa mata jikinta ,”dakyar take magana hayatee yaushe kadawo ?!”capt Adam yajuya Yana goge hawayen daya xubomai dan bayasan tagani,sosai yau yatabbar da cewar wannan shine dalilin dayasa rannan daxe tafi yaga jikinta yayi sanyi ,kuma tabbas duk tsahon shekarunnan inde yatafi yadawo  yake ganin Hafsat dinsa kullum da sabon tabo da sabon ciwo ..sosai tabashi tausayi dakyar yagyara mata kwanciya bayan yaballi magani yatemaka mata tasha “ahankali yake fadin calm down my hafsat,dama nace maki baxanyi kwana 3 ba if you can recall,yanxu de kiyi bacci akwai abinda xanyi ..”hannu tasa tarike rigarsa pls hayatee kakyalesu ni na yafemasu wallahy Dan Allah banasan abinda xehadani da gwaggo..”Capt Adam yaxaro Ido nakyalesu fa kikace?!axo har gidana agina wannan rashin mutuncin kice baxandau mataki ba,”my Hafsat muna Bawa junanmu shawara nidake muna dauka muyi amfani da’ita..”amma kiyi hakuri da rashin shawararki dayau xansa kafa nashureta,wallahy yau sadeeya da safeeya sesun gane gonar wasuka shigo!beko jira mexata ceba yasakai yafice,”Hafsat tasa kuka Dan batasan tashin hankali,kuma batasan ace itace sanadiyar hada yaya da kanne ,”gashi jikinta kwata kwata ba kuxari balle tace xatabi bayansa haka tahakura tafara yan’adduo’in kwantar da musibar datashigo gidan,harde bacci dadda’da yai awun gaba da ita..

“Capt Adam nakomawa parlor yanemi kujera three sitter yaxauna yaharde kafafuwansa kamar betaba Daria ba,sosai yatsura masu Ido Yana kallon yan’uwan nasa Wanda Sukai masa abinda ko amafarki betaba xatan yan’uwansa najini xasuyi masa shiba,”yai gyaran murya yace surayya kece babba,babbar banza babbar kwabo shashasha mekwakwalwa irinta kifi,wadda kanwarki taxauna Tana juyaki ubangiji Allah yakyauta,”Sannan yakalla sadeeya datai kasa da Ido sekace mumina,yace ke dago idonki karamar munafuka ,dama ke tunda annamimiyace..yanxu kafin Komi yakwana kafin inmuku dukan kawo wuka Wanda xaku gane wannan shine babban kuskuren dakuka tafka a rayuwa..”inasan kufadamin uban meye yake kawoku gidana shekara da shekaru kunacin mutuncin matata?!

STORY CONTINUES BELOW

“Sadeeya tai kasa da Ido Yaya bafa lefin mubane,ita batasan ana zumunci yauma damukaxo takamamu da kokawa kanse munfita daga gidan shi…kafin takarasa Capt Adam yabata wani kyakkywan mari “Yana huci kamar xaki Yana nunata da yatsa you knw me sadeeya I dnt tolerate nonsense ,natambayeku magana kufadamin gaskia xaki sako makircin dakuka saba to kisani nasan matata ciki da bai,,,Capt Adam yace naku wasane Sannan yadaga murya yace “haule xonan parlor yanzu kome kike ki ajiye kixo..a Dari haule tashigo parlor din bayan tayi sallama ta kwashi gaisuwa Sannan takoma gefe taxauna ,”Capt Adam yace Yawwa haule fadamin gaskiar al’amari akan mekika sani gameda wa’ennan kada kiji tsoransu ko suyi maki jan Ido kikasa fada,fadi Komi tun shekara goman dakikai kina aiki a gidannan nasanki da amana,haule tadaga Ido Tana kallonsu,atare suka maka mata harara,sosai haule tahadiye yawun tsorata amma yata iya inde tanasan yan’ cin auntynta Hafsat dole ne tafadi gaskiar lamarin..

“Haule tace abba gaskiar al’amari xanfada tsakanina da Allah daya halicceni,shekara ta goma kenan Ina aiki agidannan,amma bantaba ganin farin cikin Aunty ba harse kana gidannan,inde kayi tafiya to farin cikin Aunty yakare kenan kuma bawani abunne yasaba face addah surayya da addah sadeeya,,sune xasuxo ranar dakai tafiya yawanci da kwana daya ko a rana tabiyun wani lokacin har ranar daka tafi Ma,sukanxo sau biyu duk a yan’kwanakin,”kuma insunxo bawai xuwan mutunci suke ba a’a suna xuwa xasu fara gasa mata bakar maganganu na juya ce bata haihuwa sede taci,ta sha,tai kashi ta kwanta tai bacci,Sannan bayan wannan bakar maganar kuma Se su lakada mata dukan kawo wuka sosai suke jibgarta agidannan wani lokacin idan nazo rabiyar fadan dani suke hadawa suyiwa dukan ,Sannan wancan tafiyar dakai Ina shigowar dakai kaga goshin Aunty ya kumbura ga parlor dinnan yayi kaca_kaca?! “Capt Adam yakada kansa  yaname kallon haule,sosai idanuwansa sunfirfito,hakama jijiyar kansa dukta fito..”haule tacigaba da cewa Yawwa Toh ranar sune sukaxo inda sukai mata duka fitowata daga kitchen kenan naji Kara ashe addah sadeeya ce tahankada aunty  tabige kan tiles,”sannan  wannan satin yau kenan,daxu sukaxo da safe lokacin Aunty tacemin xatasha magani kanta ciwo yake tace namana faten dankali ,Toh nashiga kitchen nadora yakusa dahuwa kenan segasu sunshigo addah tashigo kitchen tace idan yadahu naxuba masu duka a foodflask kada narage ko kadanne,Sannan tacemin Ina wannan juyar take ?!nace mata batada lapia Tana dakinta,bayan nagama nakai masu seda sukaci suka koshi Sannan suka shiga dakin Aunty ,”nide sena koma kitchen danbaxan iya ganin mexasu mata ba,Se yanxu daka kirani..”wannan shine abinda nasani tsakanina da Allah abba..

“Capt Adam sosai yake kuka harda shassheka ,yadedeta muryarsa yace amma haule meyasa baki taba gayamin haka ba??”haule tace Toh gaskia inaso ingaya maka amma Aunty setace karna soma fada babu ruwana batasan tahadaka da yan’uwanka,shisa kawai banfadaba amma wllhy Ina addua Allah yakawo ranar daxaka gani da idonka,Capt Adam yace Toh shikenan haule nagode xaki iya tafiya amma kafinnan kiramin modu da hannafi yanxu kutaho tare,..ba ajimaba modu da hannafi suka shigo duk suka xauna akasa,”Capt Adam yace Yawwa tambayar daxanmku inasan kugayamin gaskiar lamarin,”shin mekuka sani gameda wa’ennan kannen nawa?!modu shekara tafi 18 muna tare dakai kaikuma hannafi shekara 10 kenan kada dayanku yamin karya tunda baci ko sha suke Baku ba inajinku,”modu yace toh gaskia de mude abinda mukasani wa’ennan mata yan’uwankane Sannan kace mana inde yan’uwanka da yan’uwan matarka sukaxo kada mikokarin hanasu shiga,toh akwai Wata rana inaga ranar asabar ce,Hajia tafito xata unguwa ,jirgi harya tada mota ,sega su sunshigo suna xuwa suka janyota daga cikin mota suka fara duka ,dakyar muka rabasu muka fitar dasu daga gidannan,to bayan sati biyu sesuka Kara zuwa nahanasu shiga shine surayya ta mareni tareda  gayamin maganganu marassa dadi,bayan suntafi Se Hajia tafito tabamu hakuri tareda doriyar mukyalesu duk abinda zasuyi Allah Yana sane dakomi Sannan karmu sake mufada maka batason ta hadaka da yan’uwanka wannan shine abinda muka sani.”Capt Adam yai shiru Se ajiyar zuciya yake Yana magana azuciarsa Hafsat wacce irin zuciya ce da ita haka duk irin tozarcin dasuke mata amma bataso afadamai saboda kada tahadasu da yan’uwansa?!dakyar”ya’iya furta shikenan xaku iya tafiya nagode..

STORY CONTINUES BELOW

                  •✨•

                      5

“Muryarsa narawa yake fadin” hakika kun tozartani kun ha’inceni kuma kunnuna baku sona bakwa son abinda nakeso,dan kiyayyar dakukewa my Hafsat Wlhy tallahi ba ita kukewaba ni kukewa,Ina ganin ko Allah yakarba rayuwata inada family din dasuke son matata Ashe duk karyace,”dama hausawa sunce makashinka na *****,to yau na Kara tabbatarwa da hakan,banmasan mexan maku ba saboda duk hukuncin daxan dauka akanku mesaukine,me Hafsat tamaku inbama tanada kyakkyawar zuciya ba ,wacece xaku mata haka tai shiru taki fada shekara da shekaru?!!! Badan Allah yaso nashigo ba shirin kasheta kukeba.,harda zama kan ruwan cikinta,ke kuma yasa hannu Yana nuna sadeeya harda rike charger waya kingama dukanta kenanko??

“Toh da farko de ke sadeeya  Ina gidan kajina dake hannunki Wanda nace kidinga saida kwan kina aikawa  dakudin kaduna,Wanda gwaggo tarufa maki asirine Wlhy bakya kaiwa,Toh kibani mukullin gurina wallahy tallahi nakarba abuna dama bakyauta nabaki ba,”sannan ke surayya tunba yau ba narufa maki asiri shekaru kenan da mijinki yasakeki saki uku narufa maki asiri nabaki gida kike xaman ya’yanki to wallahy tallahi sekin bar gidan nan asatinnan tunda bana ubanki bane,nasan ance hannunka baya rubewa kace xaka yanke ka jefar,to nidai xanyadda nawa hannun tunda yarube wari yakeyi daga yau nayanke…addah surayya taxube akasa tana kuka Dan Allah Yaya Adam kayi hakuri Wlhy banida inda zanzauna Kasan Yaya sameer baxebari nakoma kaduna naxauna ba wurin gwaggo.,.ko kallonta Capt Adam beyi ba sema Danna wayarsa daya keyi ,”sadeeya Ta lallaba tarike kafarsa Yaya kaimin rai Dan Allah kajanye maganar dakai wllhy tanan muke samin abin ci da sha,kasan suhail(mijinta)baya aiki yanxu ankoreshi har kudin makarantar su basmah aciki muke biya..”Capt Adam yajanye kafarsa yai Daria kadanma kuka gani dagake har suhailun,..

“Sannan abu na biyu kada daya daga cikinku,dukkan kuma kada ku Kara takomin kafa kuxo gidana ,babu wannan zumuntar nayanke ta wallahy,addah surayya tasunkuya har kasa Yaya Dan Allah kayi hakuri baxamu sakeba,wani makokon bakin ciki yatsaya amakogaron Capt Adam,dasauri yasa kafa yashureta tafadi kasa tadauje baki Sannan yasa hannu yatsinketa da bahagon mari yaciro belt yahau dukanta,Sannan yakoma kan sadeeya itama yahadata da bango yahau dukanta ,seda yamasu lilis Sannan yajefar da belt din agefe Yana huci,hannu yasa yanuna masu kofa”xoku futa yan’iska marassa mutunci ya’yan Fata,ya’yan Allah bani narokeka,shegu Wanda basuyi halin iyayen suba,Anya Ma ku yan’gidan mune kuwa?!ina tantama inku jinane,bashiri addah surayya da addah sadeeya suka fice kowacce fuskarta tayi suntum,abinka da farare tuni fatarsu tai ja saboda duka..binsu yai abaya yadaga murya”hannafi kubude masu gate su fice yanxunnan,komasu kama dasu kuka sake budewa Gidana abakin aikinku!!!tuni su modu suka aikata hakan,ya yinda su addah surayya suka fice daga gidan,”surayya takalla sadeeya da gefen bakinta yafashe Se jini yake,”yanxu Ina muka nufa?! “Sadeeya tace yanxu abinda yarage Se plan b kuma,yanxu gwaggo xamu samu kawai shine best solution..tuni suka haye Dan sahu yakaisu tashar Kano line inda sukahau motar kaduna ,dama gurin mutum biyu ne kawai yarage,mota tadaga daga kano tadabo tumbin giwa koda mekaxo anfika..xuwa kaduna garin gwamna,garin dabasu da sarki se gwamna..

“Kodah Capt Adam yakoma ciki,kuka yaxauna yanayi shabe shabe sekace karamin yaro,sosai yanayi Yana goge hawayen Yana ci gaba,wannan wacce irin kiyayya ce sekace Wanda suka hada uba daya dasu,shekara kusan 20 suna mata wannan abin?! Amma tace ayi shiru saboda karta shiga tsakanin yan’uwa lalle Hafsat tacika matar kwarai wadda kowa xeso yasamu amatsayin mata uwar ya’ya..yanayi Yana lekawa dakin sosai haryanxu baccinta take peacefully ,yadade Yana kallon kyakkyawar fuskarta Sannan yaja bargo yasake rufe mata jikinta sosai,yarage AC din dake dakin din Sannan yakoma parlor yaxauna,wayarsa yakalla yaga Tana haske seyanxu yatuna Ashe a silent yasakata,7missed calls duk na mutum daya bakowa bane Se abokinsa DR NAUFAAL,tuni yafadada murmushinsa Sannan yakirashi,”aslm  alykm mijin husnah,angon naja’atu,.,

“Dr NAUFAAL yayi Daria bayan ya amsa sallaman “na Hafsat badakanka asare kaje gidah kace ya fadi,Ina miko gaisuwata xuwaga uwar gidah ,sarautar mata..

“Capt Adam yace wannan haka yake,Yaya kadawo daga tafiyan ne?!,

“Dr NAUFAAL yace nadawo daxu shysa nakiraka,naxo da albishir ma,insha Allah gobe da safe xanshigo gidan naka..

“Capt Adam yace kanada kyauta kenan babba,Allah yakaymu goben lafiya..Sannan suka danyi hirarsu sukai sallama..sosai Capt Adam yamatsu yaji albishir dinann Yana kuma Fata Allah yasanya alkhari akoma menene..

“Bayan hour 1 da mintina,Hafsat tatashi daga bacci,sosai Capt Adam yatemaka mata tayi wanka tai sallah,inda haule tai reheating faten dankalin,sosai taci takora da ruwa ,Capt Adam yanata mata hira me dadi,Sarai yaki Gaya mata yadda sukai dasu addah surayya ,,,kalamai masu sanyaya zuciya yake fada mata harde tamanta da duk wani abu da yafaru,wunin ranar Yana gidah Se da akai la’asar Sannan yaje masallaci yadawo inda suka Dora daga inda suka tsaya na hirarsu!!!

“Su addah surayya na Isa kaduna suka xayyanewa gwaggo abinda yafaru amma duk karyace na abinda suka fada,sosai suka badawa idonsu kasa suka karkace suna xuba karya idan surayya tagama seta kalli sadeeya ita kuma tadora datata karyar harde gwaggo tayadda tacika tai fam,tadanna Waya takira Capt Adam “Yana dagawa tace lalle yataho kaduna yanxu kome yakeyi ya ajiye Tana nemnsa,lokacin Capt Adam xaune suke shida Hafsat suna kallon tashar CNN sunajin news din Donald trumph”Yana ajiye wayan yamike Yana gyara hula”my Hafsat Bari naje nan kaduna nadawo wai xankarbo sabo nakawowa Baffa imam(kanin mahaifinsu)sosai yafadi hakan danbayasan yadaga mata hankali,Hafsat tai murmushi tuni tagano abinda yafaru Sarai tasan su addah surayya ne sukaje suka xuga gwaggon abinda take gudu kenan,amma yata iya dole tadanna xuciarta tai kamar bata gane ba”murmushi tai Sannan tamike tana gyara masa hannun rigarsa “Toh hayatee Allah yakayka lapia yadawomin dakai lapia agaidamin dasu gwaggon kafin naxo ,”Capt Adam yace insha Allah my Hafsat xan isarda sakonki ,mekikeso na kaduna?! Hafsat tai daria “ba abinda nakeso Se Allah yadawomin da mijina lafiya,”Capt Adam yai murmushi Sannan yadago habarta tareda bata peck a kai,insha Allah xandawo lapia my Hafsat ,amana addua Sannan yasakai yafice..

“Hafsat takoma kan kujera taxauna bayan tayi addua tashafa na Allah yakai duk Wanda suke kan hanyar tafiya lapia yakuma dawo dasu lapia…Sannan taxauna Tana naxarin abinda ke shirin faruwa yau akaduna Sarai tasan gwaggo intadau xafi akwai yanke hukunci..

“Jirgi driver nagama parking a parking arena din gidansu na kaduna Capt Adam yasaka kafarsa yafuto tare da addua ,Sarai yasan yanxu merabashi da gwaggon nasa Se Allah,Dan haka kannen nasa suke ko abu sukeso agurinsa takan gwaggo sukebi dan sunsan bayai mata musu,bilkisu kanwar suce kawai halinta daban acikinsu shisa basa shiri da ita kwata kwata,da sallamarsa yashiga gidan yana murmushi,ganin bakowa a parlor din dake kasa yabashi damar sanin lalle gwaggon na parlor dinta nasama..

“Nandinma sallamar yai Sannan yasakai yashiga,”zaune dattijuwar matar take sosai Ta manyanta amma dukda haka ,tananan da kyanta jajir fatarta take,Sannan ga gashi nan har gaban goshinta,kamar baxata amsa sallamar ba sekuma Ta amsa,Sannan ta kauda kanta gefe,gefe daya kuma addah surayya ne da sadeeya suma suncika sunyi fam,kotakansu bebi ba yaxauna daf da mahaifiyar tasa ,Kansa akasa yake fadin”gwaggo barka da yamma,nasameku lpy?!gwaggo tai shiru murya adakile take fadin”lpia qalau..ahankali yakara cewa”gwaggo Hafsat tace tana gaisheku kafin tazo,itade gwaggo Shiru tai batace cikan kaba,

+
“Gwaggo tagutsiri goranta,sannan tadaga kai takalli Capt adam,tsugunne kusa da ita kanta akasa,ita kanta tasan dan nata yanada tarbiyya,”Sannan tace ‘dannan,(dayake bata fadar sunansa dukkoda shine nabiyu dashida alhaji sameer dukbata fada shi alhaji sameer tana kiransa da”wannan yaran”kunsan Fulani da kunya,..”Capt Adam yace Na’am gwaggo,

“Gwaggo tace kabani hankalinka nan magana nakeso muyi dakai ,nakira wannan yaron(alhaji sameer)yace mani yanxu xexo shima,amma kafin yaxo inaso kafadamin menene dalilinka nadukan kannenka saboda matarka tanemi tahanasu shiga tana kokawo dasu,kaxo kasamesu ahaka kanemi dalili sunfara fada maka kadakatar,kayi musu dukan kawo wuka,nan sukaxo magana Ma kowacce daga cikinsu dakyar take,saboda azaba,Sannan kadarorin daka basu ka kwace abinka,sanin kanka Kasan ba’a kyauta akarba,shin menene dalilinka nayin hakan?!sarai Kasan ba’a canxa dan uwa har abada amma mata kuwa ana canxa ta,hannunka de baxe lalace kace xaka yarba,amma dukkayi watsi dahakan,tabbas wannan Hafsat nayi danasanin amincewa dakai ka aureta ..”Capt Adam yai saurin dakatar da’ita haba,Haba gwaggo karkice haka Wlhy tlhy bahaka halin Hafsat yakeba,”wa’ennan yaran sunxo sunhada maki zance ne kawai gwaggo.amna Hafsat mutuniyar kirkice wallhy gwaggo tsahon shekaru kusan 20 kenan surayya da sadeeya ketattaro bakaken maganganu sujefa Hafsat dashi ,bama shikenan ba wallahy gwaggo harda duka ,ni bantaba saniba saboda Hafsat tace kada Wanda yagayamun dagacikin yan’aikin gidan,kuma satin da yawuce wallahy har gidah suka xo suka mata duka har goshinta yafashe,Sannan Jia Ma Wlhy surayya nasamu akan ruwan cikinta wannan ninagani da idona wallahy,itakuma sadeeya tasa charger tadaketa,

“Sannan agabansu nakira haule me aikinmu tafadi abinda tasani akai,hakama masu gadina,kuma duk basu musa ba gashi inna masu karya,sannan abubuwana Dana karba wajensu gwaggo dama ni bakyauta nabasu ba,wa’ennan yaran basuda mutunci gwaggo,”caraf gwaggo takarbe tana huci uhm uhm ‘dannan karka sake cemasu haka,kaide kawai ita hafsatun tahadaka da kannenka taji dadi,amma intasan Wata ai batasan wataba ko?! Shide Capt Adam yai shiru sanin halin gwaggo dayai,

“Addah sadeeya dake gefe tai wani shu’umin murmushi ,tana wani karkada kafa,gwaggo Yaya fa baxe yadda da komai ba ingaya maki gaskia ,saboda wannan matar tariga tawanke tabashi yasha,”Capt Adam yace aibase tasha wahala tawanke tabani nasha ba,dakaina nake kafa kai nakesha Sannan yamaka mata harara,”tuni sadeeya tadubibice danbata xaci amsan daxebataba kenan,tuni ta sunkuyar da kanta kasa tana wasa da gashin dake jikin center Carpet din parlorn.

“Gwaggo tace toh Allah ya kyauta tunda haka abin yaxama kuma,”Capt Adam yamarairaice murya ,gwaggo Dan Allah kiyi hakuri nibada wani abin nafada haka ba,wa’innan yaranne gwaggo komai hakurin mutum sesun kaishi makura,suna cikin magana alhaji sameer yashigo kamarsu daya da Capt adam, sede shi becika fari afuska ba,sannan yamanyanta shima amma kyansa yananan,

“Sosai alhaji sameer ya tsugunna har kasa yagayda gwaggonsa,Capt Adam Ma yabashi hannu suka gaysa Sannan yakuma gaysheshi na musamman,su addah surayya ma suka kwasa gaisuwa gun Yaya babba,kamar yadda suke fada mashi ,dan baya wasa ,sharara masu mari agunsa ba abin wahala bane,

STORY CONTINUES BELOW

“Gwaggo tace Yawwa”wannan yaron”(alhaji sameer),kajide duk yadda mukai dakai awaya daxu ko?!,”alhaji sameer yace kwarai gwaggo,”gwaggo tace to Gashinan yamusa xancen kememe yanuna matarshi ce megaskiya,kannensa kuma yace karya suke ,Sannan xancen kayansa tabbas yace yakarba wai aiba basu yaiba,

“Alhaji sameer yace Toh gwaggo xancen gaskia suma sunada lefi,sannan xancen gidah tun jia nace maki gwara daya karba abinsa danni de bansan yarinyar nan mijinta yasaketa har saki 3 ba,shekaru kusan hudu kenan bata tareda shi ,wai kuma Adam yarufa mata asiri yabata gidah aro taxauna ita da ya’yanta,to dan ubanta,kankanuwar ta da ita xata iya renon ya’ya ne itakadai?! hankali Ma bagama isarta yaiba,nide tanan kam adam yabirgeni daya karba gidansa,Toh hardayar marar kunyar ma,gidan kajin dayace taringa aiko maki da kudin kwan,gwaggo Wlhy bata aiko maki,rufa mata asiri kawai kikayi,ni inaganin yadda yaidin shine dede,

“Gwaggo tai tsaki,da Wata akasa kenan ,duk yadda akai,’dannan yakira ka yasheda maka karya da gaskiya dan daxu bahaka mukai dakaiba ‘wannan yaron’,”alhaji sameer yace assha assha gwaggo Wlhy rabona da adam tun da yai tafiya a abuja bamu Kara Waya ba,kawaide nasan halinsu ne gwaggo,bilkisu ce kadai daban acikinsu,amma kiyi hakuri Dan Allah,Sannan “gwaggo xannema alfarma Dan Allah surayya da sadeeya sutashi subar parlorn nan in angama xancen sadawo,

“Gwaggo tace sadeeya kutashi kushiga ciki,Sannan suka mike suka shiga cikin daki suka turo kofa,addah surayya takasa kunne Ta jikin kofa tanajin mexasu ce,

“Gwaggo tace Toh nide nagama magana bakuma xanjanye xancena ba,idan yaga baxe iya yiba,toh natsame hannuna acikin dukkan lamuransa,yakuma je yanema Wata uwar,”nan take “Capt Adam yafara hawaye Yana kallon wansa alhaji sameer,

“Alhaji sameer yace Haba gwaggo meyayi xafi haka?!kifadi komenene insha Allah baxe gagaraba ko Adam?!capt Adam yai nodding Kansa Yana me goge hawayen dake reto a fuskarsa,

“Gwaggo tace Toh nayanke shawarar hada auren ‘dannan(Capt Adam) da zainab yar’ gidan Yaya inno Fanta ,”Alhaji sameer ya ware Ido gwaggo bade magajiya kike nufi ba?! “Gwaggo tace kwarai ita nake nufi tanada wani aibunne daban saniba?!”Alhaji sameer yace a’a Allah yasanya alhairi,”shide Capt Adam kasa magana yai illa sautin kukansa daya karu ,dakyar yace”gwaggo Dan Allah kitemaka kihadani da Wata de ,Sarai kunsan matarnan ba San Hafsat take ba,tunma lokacin magajiyan nada aure,”Alhaji sameer yace Toh nimade abinda nagani kenan,

“Gwaggo tamike tsaye,toh nide nagama magana ,inkaga baxaka dau maganata ba,toh kanemi Wata uwar,sanann’wannan yaron’nagode kwarai daka nuna dan’uwanka yafini matsayi,”Alhaji sameer yace Haba gwaggo wallahy bahaka bane,Dan Allah kiyi hakuri abinda kikace shi xa’ai gwaggo,,

“Itade gwaggo kotakansu batabiba tasa kai tashiga daki abinta,

“Nan alhaji sameer yakoma kan Capt Adam yafara bashi baki,Yana kwantar masa da hankali,yana Kara nuna mashi muhimmancin uwa,sosai yabashi baki harde yaga Capt Adam din yahakura,Sannan yarakashi yabawa gwaggo hakuri kancewar yayarda da auren..

“Adaren Capt Adam yasa jirgi yatukasu lokacin har anyi isha’i,suka taho Kano,zuciarsa Se kuna take,gawani makokan bakin ciki daya tsaya masa awuya,sosai yasan wanann shirinsu surayya ne,amma ya ya iya dole yahakura tunda gwaggo tashiga xancen ,yanxu da wanne Ido xekalli Hafsat yafada mata wannan al’amari?!bayan karyar dayai mata nacewar sako xekarbo na Baffa imam,dafe Kansa yai dake barazanar ciwo Sannan yafara salati,Yana hawaye,shin Hafsat xata yadda makuwa?!

“Haka jirgi yaita sharara gudu sosoi akan titi,Capt Adam yajima Yana kallon daji dakuma yadda bishiyu suke,yadade Yana tunanin Iko da kudira ta ubangiji,lalle Allah mabuwayine gagara misali,basu shigo garin Kano ba se wajen karfe goma nadare,Dede gurin Rahama suya Capt Adam “yace jirgi yafito yasiyo dakwalen kaji guda biyar,Sannan yasiyo masu guda biyu shida su modu da hannafi suma,Sannan suka kama hanyar gidah..

STORY CONTINUES BELOW

“Suna isa,Capt Adam yashiga gidah bayan yakarba ledan kajina gurin jirgi Sannan ya sallameshi,kirjinsa ne yaketa dukan uku uku haka yadanne xuciarsa yashiga cikin gidan dauke da sallamarsa,kwance yasamu Hafsat dinsa akan doguwar sofa din dake parlor tana kallon tv,Tana ganinsa tamike tanufeshi tana murmushi dukkoda tagano tsantsar damuwar dake cikin idonsa,

“Da sauri tai hugging dinsa tana murmushi,”hayatee seda kataho adarennan?!,daka sani ka kwana acan dasafe seka dawo,sannan takwantar da kanta kan kafadarsa tana shakar dadda’dan kamshin turarensa,dukkoda saidatai dage dan Capt Adam dogone sosai,”capt adam yai murmushi”my Hafsat baxan iya kwana nabarki kekadai agidannan ba,kuma Gaskia de I couldn’t sleep without you by my side,”Hafsat tadago face dinta tana admiring kyakkyawar fuskar mijinta da lafuzansa suke ratsa jininta,”ahankali tace nasan dahaka hayatee,kuma Ina adduar Allah yabarmu tare,inakuma fatan sakona ya isa ga gwaggo?!

“Capt Adam yace sosai Ma,tace tana amsawa,,,”Hafsat tace Toh muje ga abinci can a dinning yanxu nayi reheating dinshi,”Capt Adam yabude baki,kadde kice bakici abinci ba seda nadawo xamuci tare ,hannu yasa yataba cikinta ashafe kaman mara,”Hafsat tai daria,hayatee I knw right kaima bakaci abinci ba,kuma kasan baxan iyacin abinci baka kusa daniba and so you,”Capt Adam yace hakane my Hafsat amma pls kidena barmin kanki dayunwa,yanxu de dama nasiyo kaji muje semusa akan abincin muci ko?!”Hafsat tace duk abinda kace shiza’ai,Sannan suka nufi dining sukaci suka koshi,sosai Hafsat take ba Capt Adam kulawa harde yaxamto tayaye masa damuwar dake cikin ransa,

“Washe gari da safe Capt Adam yariga Hajia Hafsat tashi daga bacci,parlor yanufa yaxauna hade da dafe Kansa Yana tuno halin tsaka me wuya dayake ciki “dawanne idon xefadawa Hafsat dinsa abinda yafaru?!,wayarsa ce dake gefe tai ringing ta hanashi tunanin dayake,”adole yasa hannu yadauka wayar Sannan yakara akunnensa ganin dr NAUFAAL ne yakirashi,

“Salam alykm likita bokan turai Ina miko gaisuwata,

“Dr NAUFAAL yaidaria,WA alykm salam,waneni nakai matsayin tuka jirgi aidana more,yanzu de Ina fatan kuntashi Dan ina gab da isowa gidan naku?!!!!!

“Capt Adam yace Toh seka iso Allah yakawo ka lapia,

Yana gama wayan kenan Hafsat dinsa tafito tana murxa Ido,hayatee harka tashi?!'”Capt Adam yamike yanufi inda take “my Hafsat natashi amma bandade da tashi ba,…yanxu nai receiving call din dr NAUFAAL yace yananan isowa nanbada dadewaba,”Hafsat tai murmushi Toh Allah yakawoshi lapia,barinyi sauri indora mana ko noodles ne ,”Capt Adam yai saurin katseta noo kije kishirya Bari haule tadafa yaude kadai,”Hafsat tace  Toh shikenan hayatee,Sannan tashiga daki donyin wanka,

“Sosai tayo wanka tashirya cikin jar atamfa medauke da ratsin baki,bakin mayafi tayafa wadatacce ganin yanxu dr NAUFAAL xe iso,sosai takara gaysawa da megidan nata cikin girmamawa,mintina kadan haule takawo indomie noodles din datasha kwai dakuma vegetables ,sosai sukaci suka kora da cappuccino,harse bayan sunci Sannan dr NAUFAAL ya Iso,sallama yai Sannan Capt Adam yamasa iso yashigo ciki,bayan sungaysa sosai dukkansu sannan Hajia Hafsat takawo masa drinks da snacks ,murmushi fada’de a face dinta tace Doctor Yaya course din dakeje hope everything goes well?!”dr NAUFAAL yashafa cyboc(sajensa)yace Alhamdlh Wlhy ,ai abinda yakawoni Ma kenan,

“Atare Capt Adam da Hajia Hafsat suka hada baki,Toh Allah yasa muji alkhairi’

“Dr NAUFAAL ya nisa Sannan yace ,akan damuwarkune always having a baby,Toh munje inda sosai kusan akan hakan mukai bincike,kuma Alhmdlh ,mungano maganinsa dukda Allah shine maibada haihuwa ,

“Hajia Hafsat tai ajiyar zuciya taname kallon Capt Adam,tuni hawaye suka wanke mata fuska “tace dama inada rabon ganin ya’yan cikina?!”dr NAUFAAL yace Haba,haba Hajia Hafsat ai Allah shine me bayarwa and kudage da addua insha Allahu komai xeyi kamr yadda akeso,yanxu yaushene ovalution period dinki ?!i mean when kika gama period or kindenayi?!”Hajia Hafsat tai kasa da kanta ahankali tace satin dayawuce,”dr NAUFAAL yace toh Alhmdlh dama xuwa yau shine ovalution period din,

STORY CONTINUES BELOW

“Capt Adam yace aiki Se meshi likita bokan turai,””dr NAUFAAL yai Daria Sannan yace barin maka bayani naga madam dintaka kunya takeji dama nasan mrs Adam akwai kunya amma tayau tafi takoyaushe,”Capt Adam yai murmushi kunya adon mace,anyways fadamin komenene,itade Hajia Hafsat tashi tai tabasu waje tana murmushi ,daki tanufa tai alwala Tana sallah Tana me kara Rokan Allah da yacika masu burinsu,

“Bayan dr NAUFAAL yaiwa Capt Adam bayanin komai Sannan yadora da”anasamin haka dama captain,yawanci yanzu situation din da ake fuskanta kenan,and majority of men sesuga Kamn lefin matanne yawanci amfi samun haka

a kauye sekaga ansaki mata an auro wata not knowing the matsla will keep circulating,Wlhy inada Wata aunt wallhy captain seka xubda hawaye ,happy couples fa amma ba ya’ya ,wai mom dinshi husband din baxata iya rayuwa bataga ya’yansaba,ta hura masa wuta kanse yasaki matar ko kuma yakara aure ..”Capt Adam yai Shru Sannan yace Toh meyafaru kuma ?!

“Dr NAUFAAL yai murmushi yace tabbas mijin yakara aure cux yanasan matar yace he can’t divorce her,toh akai auren ingaya maka amaryar natarewa,uwargida my aunt kenan tasamu ciki,yanxu haka ta haihu ba daya ba biyu ba..and you knw what?!”Capt Adam yace seka fada Doctor ,”dr NAUFAAL yace Toh it’s being 7yrs da auren amaryar yanxu ko batan Wata bata taba yiba,itakuma aunt Dina yanxu ya’yanta uku so komai Se Allah yayi,”Capt Adam yace Kai amma namata murna muma Allah yabamu namu ya’yan..”dr NAUFAAL yace I assure you insha Allah Hajia Hafsat xata haihu,tabbas xakaji ana cewa wai juya bata haihuwa,toh Wlhy akwai Wanda suke 40yrs basu haihuwa ba kuma matar xata haihu sede kafin takara haihuwa xa’adade yawanci ya’ya daya xuwa biyu suke,”Capt Adam yai ajiyan xucia Toh Alhamdlh ,nima I’m facing a difficult situation Doctor ,my family ,sisters Dina kenan basusan matata Wlhy tallahi har duka Ashe suke mata bantaba saniba,Se yau nakamasu da idona,Kasan wani abu,sesuka tafi kaduna suka je suka fadawa gwaggo karya da gaskiya ,yanxu haka gwaggo ta tsaida date xatamin auren dole Nida Wata fitsararriyar baxawara magajiya sunanta,abinda yafi batan rai bata shiri da my hafsat,ko abiki taita jefanta da magana kenan tunma lokacin mijinta be saketa ba,Wlhy dr nakasa fadawa my Hafsat abinda ake ciki,

“Dr NAUFAAL yai Shiru Sannan ya girgixa Kansa “Kai amma basu kyautaba nagane ba surayya da ….”Capt Adam yace da sadeeya ,”dr NAUFAAL yace ehh su,amma bakyau haka,amma gwaggo tayanke tsattsauran magana,banji dadiba gaskia amma bayadda xakai biyayya xakai kawai kagama lapia,and gwara Ma kafadawa Hafsat din kafin magana yai nisa taji awani wajen,”Capt Adam yace abinda nakesanyi kenan tunda natashi karfe 3 nakasa komawa bacci ,gaba daya bakaji yadda nakejiba,”dr NAUFAAL yace Haba captain kasan kanada blood pressure ,Dan Allah kabi ahankali kafada mata cikin nutsuwa,nasan xata fahimta saboda Wlhy Hafsat dinka tanada kaifin tunani,”dr NAUFAAL yamike Yana kallon agogonsa,barin wuce captain Allah yashige mana gaba,inada operation a asibiti ,amma pls kafada mata Sannan kagaisheta kace mata natafi senaji good story,

“Capt Adam yamike yabashi hannu Sannan sukai sallama,yadora da insha Allah xataji Sannan xanyi yadda kace,xakiji bayanin komai tawaya ,nagode dr Allah yacika mana burinmu,Sannan akwai tukwici yananan tahowa dukda suprise ne,”dr NAUFAAL yawashe baki ina godia sosai Kasan I do love surprises,har mota Capt Adam yaraka dr NAUFAAL Sannan yadawo ciki,

“Da daddare bayan Habiba Hafsat tamasu tuwon alkama miyan xogale ga soup agefe da sanyayyan xobo ,gefe daya kuma dessert ne,seda sukaci suka koshi sosai captain Adam ya yabi tuwon sosai yaci yakara haka yaitayi,Sannan yai hamdalah,

“Ahankali yace my Hafsat inada magana dake kiban hankalinki pls,”Hajia Hafsat tai murmushi ,”insha Allah hayatee,”Capt Adam yai Shru Sannan yace ko kuma nafasa ,jeki shiga daki Hado mana duk kayan daxamu bukata kixo mukoma wani garin pls kakkice baxaki ba,

“Hajia Hafsat tai murmushi a’a baxa’ai hakaba hayatee,duk nasan mekakeso kafadamin I knw,saboda haka ka kwantar da hankalinka ,yanxu fa aka gama mana albishir din haihuwa,saboda haka babu inda xamu muna nan,inde kishiya ce taxo Ina maraba da ita,nasan dole akai maka,saboda haka insha Allah inde matsla ce baxaka samu daga guri naba,shekaru 20bawasa bace hayatee,nidakai munxama hanta da jini mutu karaba insha Allah,Sannan tai shiru Tana jiran abinda Capt Adam xece…

STORY CONTINUES BELOW

“Shikwa captain he was totally speechless yadda hafsat tai magana ya akai tagano kenan?!

“Dakyar Capt Adam yabude baki yace my hafsat,tabbas abinda kika fada hakan yake,Sannan yasake kaskantar da muryarsa hade da lankwasheta cikin sigar tausayi ta hanyar daxata yadda dashi tayadda Ze sanyaya mata zucia,”anutse yace bayan fitar surayya da sadeeya basu xame ko’ina ba se kaduna,inda suka samu gwaggo sukai mata famfo,sosai suka xaune suka shirya zance sukai mata karya,”wallahy my hafsat kinsan dama yadda gwaggo ke saurin daukar zancen yarannan,atake alokacin tayanke decision Wanda nasan ra’ayinsu surayya ne suka cusamata,tahadani aure da…sekuma yai shiru,

“Hafsat tai murmushi tareda sa hannunta ta dago kansa dayai kasa dashi ,hayatee inajinka fa dawa aka hadaka?!!Nifa nagayama inde nice babu matsala Dan Allah ka kwantar da hankalinka,inkuma kanajin nauyin fadamin sunan Wlhy bakomai aixanga kanwar tawa daga baya,

“Capt Adam yadago raunannun idonsa dasuka kada sukai ja ya axa akan hafsat dinsa,ahankali yakai hannunsa kan kafadarta,,my hafsat gwaggo tayanke min decision din da haryanxu nakejin xuciata tayi nauyi,my hafsat wai Ma….magajiyan inno fanta fa gwaggo tace naje na aura,saboda Allah wannan matar fa,,beside bataganin girmana bataganin mutuncinki,infact bata ganin kan kowa da gashi,she’s very disrespectful wai kuma ita yarannan suka sa gwaggo tahada dani I wonder nawa tasiya bakinsu daxasumin wannan mummunar sakayyar arayuwa …

“Dukda sunan dayafada ya girgixa hafsat kwarai matuka ,Dan sosai tasan halin magajiyan ,sarai hartafi su surayya mugunta da munafunci,hassada da kuma annamimanci,tunkafin mijin magajiyan yarabu da ita take takalar hafsat din da fada sosai take Gaya mata bakaken maganganu masu zafi masu cin rai,bata tashi ci mata mutunci se a taro(biki,suna ,mutuwa),datemakon addu’a hafsat tasamu tadanne xuciarta dukkoda wani bakon al’amari daya xiyarci xuciarta Wanda tasan fargabace hade da kishi,amma Yata iya adole takakaro murmushi Sannan tace”Haba hayatee Dan wannan kakejin zuciar ka wani Iri?!to Dan Allah Ina rokanka hayatee ka kwantar da hankalinka kasawa zuciarka salama(peace),Sannan tai yar’ daria da dan haka kake fadin mucanxa gari?! To wannan ai bawani abun daga hankali bane hayatee,abin kasa goshinka akasane kaiwa Allah godia bisa wannan babbar kyauta da yai maka,samin aure a wannan lokacin ai sa’a ne kuma gashi kasamu kana neman gujemata,

“Kuma de ina adduar Allah yasa tashigo a sa’a,muxauna lapia harmukoma ga ubangijinmu nawa rayuwar take ma ?!,Dan Allah karmu jefa kanmu cikin MATSALAR RAYUWA(littafin Nafee Anka tare dani miss xoxo)wannan ni inaganin WANI HASKE (littafin Ummi_Aisha)ne daga Allah ,karkai wasa dashi,tunda ba’a gujewa maganar iyaye musamman Uwa ,Wanda sau uku ana fadarta,insha Allah babu Wata matsala daxata faru komai xa’ayi cikin lapia agama lapia da yardar Allah,

“Capt Adam yai ajiyar zuciya sosai maganar hafsat taratsa jinin jikinsa,hannunsa yasa yakamo hannunta yasa cikin nasa,”my hafsat Allah yamaki albarka hakikanin gaskia NI DA KE(littafin pherty) HADI DAGA ALLAH(littafin Al’eeman)ne Ina kuma alfahari dake akoyaushe,my hafsat bansan dawanne baki xangode maki ba,tunba yauba kike gayamin kuskurena kuma kike dorani ahanyar gaskia Allah yasaka maki da alkhairi yacika mana burinmu damuke rokansa a kullum amin.

“Hafsat tai murmushi Wanda yake Kara bayyanar da kyakkyawar fuskarta take dimples dinta suka lotsa,”tai fari da idonta,nice da godia hayatee,thanks for everything,”Sannan tai kasa da murya , inasan inje gidah ance murjanatu taxo amma seka yarda fa,”Capt Adam yasa hannu Yana taba dimples dinta Dan suna matukar birgeshi sosai ,Sannan yace Allah yakaymu my hafsat yaushe xakije?!”hafsat tai murmushi nextweek  nakesan xuwa,”Capt Adam yace bakomai my hafsat nabaki dama,kina matukar birgeni yadda kike fadan haka,wallahy Ina alfahari dake,kinsan karar da IMRAN yakawomin kenan wai sajeedah matarsa namatukar bashi matsala,

“Wai bata tanbayrsa unguwa se ranar daxata,shine ingaya maki Wata yar’ Kasan layin nasu kawar tace tana bata shawara kan hakan datake ,haryashigo kwanaki yaji sunayi,you knw wht?!”Hajia hafsat takada kanta a’a seka fada hayatee,”Capt Adam yace hmm yarinyar xe aura upper week daurin auren,

STORY CONTINUES BELOW

“Hafsat tabude baki,kan bala’i amma sajeedah bata kyauta ba,Kasan dama ni bama wani shiri da ita ,kullum taita mita wai Bana xuwa itake yawon xuwa gidannan,”Capt Adam yace gwara haka ae dabakya biye mata ,yanxu gashi ai yawon fitanta yaja mata Karin kishiya,

“Hafsat tai daria Allah de yayi ne ,Toh Allah yahada kansu,”Capt Adam yace Amiin ya rabbi

“Haka sukaita hiransu Sannan suka nufi daki donyin bacci dayake dare yayi sosai,,,,

“Kwana biyu da dawowar Capt Adam daga kaduna suna zaune a center carpet dake parlor din ga kamshin abinci Se tashi yake,foodflask ne kala kala ,abinde ke kan plate din dasuke cin abincin yabani damar sanin,vegetable spaghetti ce dataji hanta,gefe daya kuma sauce ce na minced meat da kuma hadadden salad Se soup din mushroom….se gefe daya kuma lemonade ne dayashe madara karara dashi yasha kankara,,

“Wayar captain Adam ce tafara ringing,kamar baxe daukaba sekuma yasa hannu yadauka ,ganin me Kiran nasa da sauri yadanna okay yasakala a kunnensa,

              

                    •✨•

                       9

“Salam alykm Yaya Yaya barka da rana,Ina yini Ina gajiya?!

“Alhaji sameer yace wa alaykm Salam Adam,lapia qalau Wlhy Yaya jikin hafsat din dafatan tasamu sauki?!

“Capt Adam yace taji sauki Yaya,Alhamdlh ,Yaya su Aunty zainab dasu little Mus’ab??

“Alhaji sameer yace lapia qlau Wlhy ,dama gwaggo ce tabani sako nafada maka nayi nayi da ita kanta fadama da kanta ma taki,saboda gaskia nibansan abinda hafsat xataga kaman da hannuna ciki,

“Capt Adam yai saurin kada Kansa yadda kukasan Alhaji sameer din naganinsa saboda tsabar girmamashi dayake,,aa bakomai Yaya,hafsat tasan ba hannunka ciki duk namata bayani kuma tunkafin nafada mata Ma tafahimta tasan sarai wannan shirin su surayya ne gwaggon Ma ba hannunta ciki,

“Alhaji sameer yace Toh Masha Allahu,kanaji Adam bayan tafiyarka washegari kenan gwaggo tasa gidado driver yabugo invitation cards (katin daurin auren)na bikinka ,jiya takirani tace naraba,na nuna mata nibansan abinda xanshiga ciki saboda kada hafsat taxata hadda hadin kaina,caraf surayya da sadeeya suka karbi xance kansu xasu raba dakansu sunji sunyadda dukkoda nadaurin aurene kawai,

“Nikam bance kala ba nabari suka dauka suka tafi,shine gwaggon tasake mikomin wasu katin wai narabawa mutanena da kuma abokananka na kaduna,harna juya xantafi tace ga wasu katin inbawa danbaxau driver dinta yakawo maka,Toh shaf na sha’afa wallahy danni a mota ma nabarsu seyanxu kaga nashiga gida nafito xanje company ,seganin katina nai a bayan mota a xube yanxu Yaya naturo danbaxau yakawo koxaka xo kakarba tunda naga wannan asabar dinne daurin auren,

“Capt Adam yai Shru Sannan yai ajiyar xucia’babu komai Yaya kabar katinan nan kawai kace ka aikodin,danni gaskia babu Wanda ma xangayyata ni,

“Alhaji sameer yai Daria calm down Adam nasanka da BIYAYYAR IYAYE(littafin ummi_Aisha)saboda haka kada wannan bakon al’amari yasa kai watsi da abinda kadade kana aikatashi ake kuma sa maka albarka kan hakan,bance kabi abokananka duka ka kai masu katina ba kawai de kadauki wasu tsirari daga ciki kabasu ,yaxakai tunda Allah yarubuta hakan?!!komai mukaddarine daga gareshi,kuma de wannan mata da aka hadaku aure yar’uwarkace da mahaifiyarka da tata uwarsu daya ubansu daya,first cousin dinkace kuma JINI DAYA(littafin anee lurv)kadubi girman xumunci katsaida tunanin ka guri daya katsya ai abinnan lapia agama lapia kanaji Adam?!

“Capt Adam yace inajinka Yaya yaxanyi?!tunda haka Allah ya kaddara rayuwata,

“Alhaji sameer yace Yawwa Sannan abu nabiyu kashigo kaduna gobe in Allah yakymu ,semusan yadda xa’ai na kada ahadasu waje daya da hafsat,dan abu baxe Kyau ba,mu roki gwaggo tayadda karaba masu gidah ko ita kabarta Ma nan kaduna gidanka na kawo ko yakace?! “

“Capt Adam yace naji Yaya hakan xa’ai Allah yakaymu goben lapia ,nagode Allah yasaka da alkhairi ameen,

“Alhaji sameer yace Amiin ya rabbi nine da godia,Se Allah yakaymu goben,agaidamin da uwargida Sarauta mata,

“Capt Adam yai Daria xataji insha Allah ,agaidamin dasu Mus’ab kila goben Ma nabiya,,,

   Sannan sukai sallama ,,Capt Adam yacire wayar daga kunnensa ya aje a gefe,

“Sannan yai ajiyar zuciya ahankali yake fadin Allah kashiga tsakanina dasu surayya wannan bala’i dasuka sani ciki Allah kaimin sakayya,

“Hafsat tai shiru ,Sannan tai magana kasa kasa,hayatee kayi hakuri please komai yafaru da Bawa mukaddarine daga Allah saboda haka ka fawwala masa al’amuranka,yan’uwanka ne Ina rokanka da Allah da kada ka rikesu cikin zuciyarka,addua xakai ta masu Allah ya shirye su ,

“Capt Adam yadago idonsa Yana cije lebansa nakasa ‘baxaki ganeba my hafsat wai katin daurin aurene gwaggo hartasa anbugo anfara rabawa kuma nima tabayar abani shine Yaya sameer yace lalle naxo kadunan gobe kanmu shawo kan gwaggo tabari na aje ita magajiyan a gidana na unguwar kawo kaduna,daurin auren ranar asabar ne,ranar daxan koma Abuja kenan ranar dakuma xaki gidah..

“Hafsat tai shiru Sannan tadan dafe Haba,bakomai hayatee aiko guri daya xamu iya xama,”Capt Adam yamike Yana gyara rigarsa ‘aa my hafsat baxeyiwuba Wlhy,hakurin ki yayi yawa,Nina fita wurin dr NAUFAAL senadawo,

“Hafsat tamike Tana Daria tuba nake hayatee na kaina bisa wuya,mexakaci da daddare Toh?!

“Capt Adam yabata peck a kumatu,I have no choice my hafsat ,duk abinda uwargida ran gida tadafa shi xanci,ni aibanda xabi,naxama rakumi da akala seyadda kikai dani,,,Sannan yafice Yana Daria…

“Hafsat tai murmushi tareda daga hannayenta sama ya Allah kabarmun mijina,Adam dina bahadeje daya tamkar da dubu,sanann tashafa a fuskarta ,,,,,

nanahafsat.wordpress.com

SAFIYA TAGARI;

“Washegari da safe Capt Adam yagama shirinsa tsaf cikin manyan kaya kirar bauchi style kalar sararin samaniya(sky blue)kenan,sosai ya mirza Karin hularsa,Sannan yahau fesa turaren Hugo boss Dana shafawa ajiki na company din ulul alharamein ,tuni kamshin yafara gauraye ko’ina nadakin,

“Hafsat ce tashiga dakin dauke da Vaseline a hannunta,cikin shigar doguwar rigar material pink me ratsin blue dinkin Senegalese sosai dinkin yamata  Kyau kamar Wata yar’ budurwa,ahankali takarasa kusa dashi fuskarta dauke da fara’a “hayatee ga Vaseline din kokaga chapette din naka?!

“Capt Adam yajanyota jikinsa bayan yasa hannu acikin Vaseline yalakato kadan yadan Sa a lebensa saboda bushewa,sakala hannunsa yai tacikin waist dinta suna masu kallon kansu ta mudubi,”ahankali yace magana kasa_kasa ‘banganshiba my Hafsat ,amma tunda nasa Vaseline dinma it’s okay,Kinga yadda kikai Kyau kuwa my Hafsat ?!”Hafsat tai murmushi tana kallon dinkin Sannan ta kalleshi ‘hayatee opposite site kake nufi aikaine kaikyau har nake tsoron kada ‘yammatan kaduna su rikemun kai,

+

“Capt adam yai daria,haba haba,me ‘yammatan kadunan suke dashi Wanda baki dashi?ai kece Ma kika fisu tunda har idona yarufe bana ganinsu dakyau seda nai tattaki har Kano sannan naga LIFE PARTNER dina,my Hafsat ke kadaice acikin zuciata karkisa waswasi azuciar ki wallhy xuciata mallakin kice kuma kinsa padlock kinrufe babu Wadda takai matsayin tashiga,(please the ‘YAMMATAN kaduna remark was a joke ,,kaduna ladies wasa nake fa..lol)

“Hafsat tai murmushi sannan tasa hannu tana Shafa cyboc dinsa hayatee I just dunno what to say you take care of me like a little child and appreciate me despite my flaws…..”Capt Adam yasa hannunsa kan lebenta alamar tai shiru ahankali yake girgixa Kansa Sannan yasa hannu yarungumota murya kasa kasa yake radakamata’you have accepted me the way I am and love me every seconds of everyday ,Sannan ya tsugunna har kasa Yana fadin I am one lucky man,I married the best woman on earth.”Hafsat tasa hannu tadagoshi Sannan Tarungumoshi tsam tana hawaye ‘inagodia hayatee kaisauri kutafi kada rana tayi Allah yakaiku lapia yadawo mindaku lapia,”Capt Adam yace ameen Sannan yaisauri yasa hannunsa Yana goge mata hawayen,

  “Dakyar sukai sallama da junansu Sannan Capt Adam yafita jirgi driver yadaga suka tafi,(Allah kabar soyayya,Allah kabarmu damasu sonmu..Ameen ya rabbi!

“Bayan tafiyarsu Capt Adam ko minti 20 ba’aiba kanwar Hajia Hafsat taxo wato murjanatu amma anace mata mjay’ itace karamar kanwarsu adakinsu Batai aure ba kwanannan tadawo daga capetown(South Africa)inda tahado bsc dinta akan karantar dan adam dakuma yadda suke rayuwa acikin doron kasa(Sociology,study of man and the society in general for eg British industrial revolution)kamarsu daya sede ita bakace,

“Da sallamarta mjay tashigo gidan tana murmushi ‘ina Yaya Hafsat din ga mutan capetown sun Iso tunda baki xoba ,ninaci girman naxo,

“Hajia Hafsat tana daki taji kamar magana,fitowatai tana kallon parlor,hango mjay tai,dagudu tanufeta Tana daria Sannan tarungumeta tana murna,mjay Kinga yadda kika Kara Kyau harwani Fresh kika sake wallahy,”mjay tai daria Kai Yaya Hafsat wallahy inanan da bakina,sannan nifa badanke nazo ba Dan Yaya Adam nazo ,Jia ma munyi magana dashi ta whatsapp amma bance mashi xanxoba suprise namashi ,yananan ko yafita cux naji gidan shiru?!

“Hafsat tai murmushi Wlhy kinyi Kyau,sannan yayan naki yaje kaduna yanxunnan kukai ‘sabani,”mjay tace kassh bakomi nasake xuwa ,sannan tasa hannu tarufe baki tareda sunkuyawa kasa bamu gaysa ba ashe “Ina kwana Yaya Hafsat naga sha biyu saura?!ya gida Yakomi ?!

“Hafsat tai murmushi lapia qalau Alhamdulillah mutan capetown ,I heard kinfito da first class ko?!to Allah yasanya alhairi yasa a amfana da abin da’aka karanta ,Allah yasa albarka aciki amin,

“Mjay takoma kan kujera da xauna Sannan tace “amin ya rabbi nagode Yaya Hafsat ,Ina haule ne?!”Hafsat takalli kofar kitchen dayake kofar tana kallon parlor din ,sannan tadan daga murya'”haule,haule,’

STORY CONTINUES BELOW

“A million haule ta iso parlor din da serving spoon a hannunta,”mjay takyalkyala daria a’a haulatu kenan kice naxo a Dede kenan tunda naganki nasan da akwai aroma medadi balle danaga serving spoon dinnan hakan yatabbatarmin dayau akwai dibar beta kenan,Ina kwana haule yagida ya aiki?!

“Haule tawashe baki tana murmushi lapia qalau murjanatu yakaratu ya gidah Yasu Hajia?!tabbas yau xaki kwashi girki,yanxu kika iso ne banji shigowar kiba ?!

“Mjay tai murmushi ehh gaskia bandade daxuwa ba,lapia qalau Alhmdlh su Hajia sunanan qalau …”Sannan tadakko Wata leda agefen jakarta da alama kayane kunce sekuma riga doguwa aleda sabuwa dal,tamika mata ungo haule gashi bayawa arika sawa nikwa Ina wannan bazawarin naki iliyasu?!

“Haule taduka takarba a’a murjanatu kullum da wahala Toh Allah yasaka da alhairi nagode sosai Allah yakara budi, iliyasu yanxu…..

“Hafsat takarbe xancen tana Daria mjay angode sosai,iliyasu yanxu basa tare da haule ai,yanxu yar’gida xamuyi fa,

“Mjay tace kai amma kwa ilyasu akwai kirki Wlhy banso kuka ‘bataba yanxu waye nagidan a ‘kauye ne?!

“Hafsat tace wane kauye Ina haule ta yanxu a birni xata xauna itama’hadin gida xamuyi da modu kinsan shima bara matarsa tarasu dama kuma bata haihu ba,

“Mjay tamike harda ‘yar rawarta dole mukwaso shoki ranar kenan toh Allah yasanya alhairi yasa ayi damu,wallahi kundace dama gashi bafulatani kekuma babarbariya(kanuri)abu yayi kenan,

“Haule tai murmushi Sannan tace Amiin,barin je kitchen kada girkina yakama,Sannan takoma bakin aiki …

“Mjay tace Yaya Hafsat yanaga mood dinki yacanxa tunda naxo nakesan intambayeki?!!!

“Hafsat tai murmushi Bakomi mjay kawai de banjin dadine,

“Mjay ta girgixa kanta Haba Yaya hafsat nasanki fiye da yadda kike xato bahaka kike ba Wlhy,Dan Allah Yaya Hafsat menene nifa kanwarkice atleast idan wani abun ne yake daminki senabaki shawara,

“Hafsat tai murmushi Kai mjay akwai ki dasan jin kwakwaf,bawani abun bane fa,sanann Hafsat takwashe xancen auren tagaya mata tareda doriyar ranar asabar ne daurin auren ma,

“Mjay tabude baki,tohh toh Allah yashiga tsakanin nagari da mugu nifa shysa Bana shiga harkan sisters din Yaya adam,kawai inbanda jealousy ba abinda suka sa agaba,amma babu komai akwai Allah ,gaskia Yaya Hafsat hakurinki yayi yawa upon all this years kice baxaki fada ba,toh Allah ya kyauta ,Allah yasa yadda kikai hakurin nan yabaki abinda kike bukata dunia da lahira…Sannan tadakko Dayan ledan dake Jakarta tamikawa Hafsat din,perfume din ciki na Yaya Adam ne,

“Hafsat tabude ledan taxaro wani kwali jakace maroon aciki da takalminta designer ne kirar company din guess,sosai Hafsat tabude baki tana murna”awww mjay thank you so much,wannan designer nane fa meshegen tsada gashi keda kika je karatu,Nagode sosai mjay Allah yabaki miji nagari,”mjay tai murmushi Amiin ya rabbi,I’m very glad you liked it,”Hafsat tadaga jakan tana kallo I really loved it sunyi Kyau beyond Wlhy…Sannan tadaga kwalin turaren arubuce boldly Elizabeth Aden ,nanma Hafsat taita godia danshima designer na ne,

“Haka sukaita hiransu suna bawa junansu sisterly advice,

KADUNA

“koda su Capt Adam suka Isa kaduna gidan Yaya sameer suka fara xuwa,sosai matansa suka karbeshi hannu biyu,dayake Yaya sameer din matansa biyu tabiyun Ma ‘yar Kano ce,

“Site din alhaji sameer din yanufa inda amaryar Hajia nafeesa ce a duty ,sosai takawo masa lafiyayyen abinci da drinks ,tare sukaci da Yaya sameer dinma ,seda sukai sallah Sannan suka tafi can gidan nasu inda gwaggon take,

STORY CONTINUES BELOW

“Bayan sunje sosai Capt Adam yagaida mahaifiyar tasa seda yai ruwa yai tsaki Sannan gwaggo tasakko daga fushin datake,harde tace masu tama hada Kayan lefe da kudinta tasa dangi sunkai gidansu magajiyan,Sannan sukai hira daga baya kuma,

“Gyaran murya Yaya sameer yai Yana kallon Capt Adam ,Sannan yace gwaggo wurinki mukaxo munasan mudanyi Wata magana dake,

“Gwaggo tace toh,Allah yasa wadda xan iya ji kuma Inyadda da itace,

“Capt Adam yace insha Allah xaki Ma yadda da ita gwaggo ,

“Alhaji sameer yakaikace murya yace ‘gwaggo dama xancen aurennannne,akan inda magajiya xata xauna ne,munyi magana inda ni nashawarci Adam gashi,kan cewar ya ajiye ita magajiya anan gidansa dake kawo,shine muke Neman yardarki gwaggo,

“Gwaggo tadauke kanta kamar baxatai magana ba sekuma tace……

“Gwaggo tadauke kanta kamar baxatai magana ba sekuma tace,’yaxa’ai kabarta anan gidanka dake kawo bayan kaida aiki yamaka yawa baka cika xuwa ba,kuma naga gidan naka dake Kano da girmnsa xeci mata hudu,ballantana biyu..’ita hafsatun ce takitsa maka haka kenan,

“Da sauri Yaya sameer yatari numfashinta’uhm uhm gwaggo Wlhy bahaka bane,Hafsatu ma batasan da wannan zance namu ba,wallhy nine nabawa Adam shawarar hakan saboda zaman lapia,gwaggo tashin tashina batada dadi,abinda za’axo ana dana sani,gwara tun wuri ai maganin lamarinnan,kuma gwaggo kinga gidannan dake kawo kato ne shima harda bangaren baki kusanma ince xedanfi na kanon girma,amma idan har kunfison magajiyan taxauna akano ita hafsatun se’ai mata magana tadawo nan kaduna,

“Capt adam ya sadda Kansa kasa ahankali yace gwaggo kixabar wa magajiyan  inda kikaga yadace ta xauna,ita hafsat batada matsala ma gwaggo,

“Gwaggo ta daure fuska wannan hafsatu tagama dakai,ashe de abinda su surayya ke fadi Se yau nagasgata haka,dama tashirya makircin ta dole tanuna ba matsala mana,Sannan tai ajiyar zuciya ‘nayadda ka aje magajiyan anan garin,Allah yasa hakane yafi alkhairi,ita kuma waccan Allah ya ‘kwatoka daga hannunta ameen,

“Bayadda captain adam ya’iya adole murya adakile yace ameen,Shide yasan Hafsat bataxuwa gurin boka ko Malam,takanyi sallolin darenta ta roki Allah bukatunta,Uwa uba biyayyar datake masa ita tasa ra’ayinsu yaxo daya kuma suke xaune cikin lumana,karamci dakuma dattako..kuma gwaggon tasan da haka ,annamimancin dasu surayya suka haka suka Shuka akanta duk shi ya haifar da abinda take fada yanxu,amma kowa yasan duk cikin surukanta(matan ya’yanta)tafison Hafsat din …

“Alhaji sameer yai murmushi ,ayi hakuri gwaggo insha Allah irin haka baxata sake faruwaba,Sannan Muna godia da yardar dakikayi na xaman magajiyan a nan garin,Allah yahada kansu itada abokiyar xamanta Amiin,

“Shide Capt Adam Kansa akasa yake,gaba daya jikinsa yayi sanyi naganin yadda kirikiri gwaggo tadau karan tsana tadorawa hafsat dinsa,yanzu idan magajiyan tashigo abinda xecigabada faruwa kenan ,lalle dole yakara dagewa da addu’a dan abinda su sadeeya suka aikata ba karami bane,

“Haka yadanne xuciarsa suka cigaba da hira sama sama dasu gwaggo ,dukkoda xuciarsa a kuntace take,Sarai saboda su surayya sunsan abinda suka aikata ko keyarsu beganiba tunda yaxo,’maganar Yaya sameer ce tadawo dashi daga duniar tunanin daya tafi,

“Adam inde yau xaka juya gwara kai haramar tafiya naga garin yau kam Alhamdlh antashi da hazo,

“Capt adam yace kwarai gaskia to barimuyi sallama ,Sannan yaduka kusada gwaggo ,yace gwaggo xamu tafi,”gwaggo tace toh Allah yakayku lapia ,Sannan tace to wannan yaron(Yaya sameer)jamu muyi addua ko?!

“Yaya sameer yace Toh gwaggo ,Sannan yafara jero du’ai,sunayi suma harya karkare da fatiha da salatin annabi Sannan suka Shafa,

“Capt Adam yaciro bandir na 1k guda biyu ya ajiye agefen gwaggo,’gashi gwaggo bayawa ayi hidimar biki,Sannan yadan Sosa keyarsa Yana mikewa daga sunkuyon dayi,naga kinyi lefe ma gwaggo toh Allah yasaka da alkhairi,kila natafi abuja ma gobe,inde tafiyar tayiwu to baxan dawo kaduna ba kuma Se Allah yakaymu ranar asabar din da safe ko jumaa da daddare,

STORY CONTINUES BELOW

“Gwaggo tace toh angode Allah yashi albarka,inde tafiyar bata yiwuba daka ‘kokarta kaxo kunyi magana da magajiyan ko?!yanzu ma badan da hazo ba ai daka biya kun gaysa..

“Shide Capt Adam gaba yai Yana tafiya Yana magana,gwaggo yanxu da haxo gaskia mayi magana da ita ta Waya ba matsala ,

“Da sauri sauri Capt Adam yaiwa Yaya sameer sallama Sannan driver yajashi se kano tadabo tumbin giwa koda mekazo anfika,

KANO;

“Hafsat ce tarako sister dinta mjay xuwa parking space suna magana suna murmushi,

“Hafsat tace toh mjay sekuma yaushe?! koda yake ranar Saturday din xanxo gida insha Allah,

“Mjay tace toh Yaya Hafsat Allah yakawoki,ai ba ranar kikace daurin auren Yaya Adam ba?!

“Hafsat tadafe haba oh ni hafsatu ,mjay karfa kije kina broadcasting wannan zancen agidah Sarai nasan halinki,to wallahi xance yafito waje ba abinda yashafeni,xance bansan magana ba sede in mama(mahaifiyarsu)ce tasani agaba itama kuma Bana fatan tasani,

“Mjay tai daria ,Yaya hafsat to inba afadaba suwaye xasu tsaya sumaki DANNAN ‘KIRJI?!(littafin mrs jh taredani MX)dukkoda nasan ba auren so da shakuwa bane xasuyi,Sannan tabude mota tashiga tana daria,

“Hafsat tasa gefen mayafinta ta kwadawa mjay a fuska da wasa,wato naxama abin tsokana kenan ko?!xakixo kisameni,kigayda su mama kafin inxo,Sannan sukai waving juna,ita takoma ciki,ita kuma taja mota ta tafi gidah..

•••••••

“Karfe biyar saura kwata su Capt Adam suka shigo garin Kano,harsun dau titin sardauna crescent,Capt adam “yace jirgi juya kan motarnan muje zoo road,yasunan shopping center dinnan dakuke yawan xuwa da Hajia ma?!!kaji sunan yabace mun kasan wurin shopping dinne sunyi yawa agarinnan gasunan lungu da sako’

“Jirgi yakada Kansa ayyo sahad stores kake nufi ko?!bare shi ance garuruwa dayawa akwai kantin nasa,,,,”capt Adam yace tabbas sahad stores ne,ai a abuja har biyu ne dashi,”jirgi yace kwarai kuwa oga anan dinma guda biyu ne,,sunata magana har suka isa sahad stores dake titin zoo road Kano ,parking jirgi yayi a parking space din da’aka tanadeshi dan motoci,

“Jirgi na parking Capt Adam yace fito harkai xamu shiga ciki ai,tare suka shiga cikin shopping center din,nan idanuwansa suka kai akwatinan dake jere nasayarwa kusada wurin biyan kudi na maza,tsayawa yai yana admiring kyan wani akwati me set 3 da kit,kirar company din Victoria secret sosai sunyi Kyau gasu kuwa best color din Hafsat dinne wato purple amma da ratsin black Se yabada unique style,

“Kusa dashi wasu dattijan mata ne har biyu suma suna kallon Wanda xasu dauka ,da alama lefe xasu hada dan ga carriage nan na stuffs cikeda kayan kwalliya da aramfofi a hannun daya daga cikinsu,

“Capt adam yadan matsa kusada su Yana kallon dayar dake neman akwatin daxasu dauka,’ahankali akuma nutse yadan gaishesu Sannan yace hajia Dan Allah wannan sets din sunyi Kyau kona dauka wasu?!

“Matar daya cewa hajia tai murmushi “wallahy sunyi Kyau sosai,yanxunnan nake cewa ‘kanwata kinga sets din hannun bawan Allahn can sunyi Kyau sosai da da irin design din damun dauka wa faruk,kaninmune daxeyi aure,

“Capt adam shima murmushin yai,nagode Hajia ,Allah yasanya alkhairi nima lefen nakesan hadawa ayanxunnan,yanayi yanadan sosa kansa,

“Matar tai daria masha Allahu,to bari mutayaka kafin nan ankawo wasu designs din,dama yanxu sukecemana inba sauri mukeba ansauke Kaya yanxu mubari agama shryawa semu xaba Wanda mukeso,to dama faruk dinmuke jira xekawo mana sako ma,

STORY CONTINUES BELOW

“Capt adam yai godia Sannan suka shiga tayashi hada Kayan kamar wasu yan Uwa sosai yasake dasu dayake basuda dauke kai ko wulakanci,toh sudinma haka suka yaba da hankalinsa lokaci daya kuma yashiga cikin ransu,har faruk din yaxo shima yashiga tayasu,suka hadu suka hada komai har shima Capt Adam din yatsaya suka hada na faruk din,har akai sallar magrib,seda sukai sallah suka dawo Sannan suka karasa hada abinda babu aciki,

“Sosai Capt adam yamasu godia kusan rabin kayan dasuka siya shiya biya masu ,Sannan sukai exchanging digits din juna suna cewa sesunxo bikin juna,Shide capt adam daria yai kawai,

“Jirgi driver ya loda kaya a mota Sannan suka tafi gidah suna yaba karamci irin namutanen dasuka hadu dasu,ana kiraye kirayen sallar isha’i suka isa gidah,seda Capt adam yatsaya yai sallah a masallacin dake kofar gidan Sannan yashiga ciki,

“Dadda’dan kamshin turaren wutan da hafsat tasane yafara dukan hancinsa,yawani lumshe ido Sannan yabude har cikin ransa yakejin dadin tsaftar da hafsat keyi,ko’ina nacikin gidan tsaf kai kace duk seconds ake gyarawa,sallama yakarayi akaro nabiyu Sannan hafsat tafuto tana gayra daurin dankwalinta,

“Dagudu ta amsa sallamar sannan tai hugging mijinta tanajin sonsa,”sannu da xuwa hayatee I knw you are tired and exhausted,”Capt adam yai murmushi bayan yadagata cak yamata maxauni akan cinyarsa bayan yaxauna akan kujera,”I’m very tired my Hafsat ,but yanzu I’m okay tunda naga kyakkyawar fuskarki,wai meye sirinne naga Kullum bakya tsufa kaman sanda na auroki?!

“Hafsat tai murmushi hayatee kenan Ina godia ,babu wani sirri Allah ,naga ban tsufa ba kwata kwata nawa nake 38 fa,tanayi tana shagwabe fuska,captain adam yabata peck a kumatu toh nagodewa Allah akullum ganinki nake kamar time din Dana auroki kina 18 lokacin,”Hafsat tai daria,yo kaima aibaka tsufa hayatee,

“Capt adam yamike yana daria fada kike kawai ina,adam ba hadeje aiyakai gangara ,barinje in watsa ruwa my hafsat se inxo inci abinci dan your aroma is calling…”Hafsat tai daria toh seka fito barinyi arranging table kamar Kansa favourite dinka aka dafa,

“Capt adam yace wow,Ina godia dole abaki tukwici my Hafsat,”wanka yashiga yayi Sannan yafito suka ci abinci tai feeding din mijinta sosai,Sannan suka hau hira inda yake fada mata gwaggo tace magajiya xata xauna a kaduna,Sannan yakira jirgi kan yashigo da akwatinan,

“Ana shigo dasu Hajia hafsat tace wow sunyi Kyau Walhy ,yanxu yaushe xa’akai lefen gashi time Yana kurewa?!!!

“Capt Adam yai Daria bayan yasallami jirgi driver yatafi yadago yakalleta,ahankali yataso yadawo inda take Yana kallon kwayar idonta,”my hafsat bakayan lefe bane wannan ,wannan gwaggo tariga tayi har ankai,wannan nakine halak malak hayatee dinki yabaki,

“Hafsat ta ware Ido ,hayatee kana nufin Kayan fadar kishiya ne wannan?!aidabaka wahalar dakankaba,nida ka shawarceni wallahy dabaka siyo ba,seta fara hawaye amma tai sauri tai kasa da kanta danbataso yagani,murya narawa take fadin,duk yawanci sanda kafita kokai tafiya seka kawomin Kaya/sutura/clothings…wallahy sun isa haka hayatee..I do not know what I would do without you,you’hv been there for me thru it all you protect me with everything in you..

“Capt adam yai saurin katseta ssssh my hafsat,I am because of you,not you because of me,I love you pass my mind beyond my soul,,matata Ina matukar sonki,duk abinnan danake maki kadanne nadaga tarin farin cikin dakike sani,tabbas kece FARIN CIKINAH(littafin hafsart Rano)you are indeed my everything ,bar kuka my Hafsat Allah yabarmun ke,yabamu abinda muka dade muna addu’a akai,….

•✨•✨•✨•✨•✨•✨•

“Hafsat tai shiru tana ajiyar zucia,gawani dadi datakeji yana ratsa ‘bargon jikinta nadaga abinda hayatee dinta yake fada, a shagwabance tace’I love you the most of everybody,inakuma alfahari dakai akoda yaushe,Allah yabarmana kai hayatee dina….

STORY CONTINUES BELOW

“Capt adam shima ajiyar zuciar yai ganin tadena kukan datake dan sosai yakejin kukan nata aransa,ahankali yashiga rada mata sanyayyun magana masu sanyaya xucia a acikin kunnenta Wanda Ita kadai tasan meyake nufi dasu,tunda iya su kadai sukasan mesuke cewa,ahankali yaxame ta daga jikinsa Sannan yashiga kiciniyar bude akwatinan,seda yabude su duka Sannan yasakko da’ita daga kan kujeran,oya duba abinda beyiba se’amayar,

“Ware Ido Hafsat tai tanabin kayan da kallo Wanda kowane gida akakai su amatsayin Kayan lefe xasu karbu,sosai suke shake da Kaya ,babu ce kawai babu aciki,hafsat tabi laces da materials din da kallo uwa uba takalma da jakankunan dake ciki designers su suka Kara sata ware Ido,sosai tajima tana kallon Kayan Wanda seta dau shekaru basu kare ba dan sunada yawa,

“Captain adam yai ‘kasa da ido Yana kallon ‘kwayar idonta ahankali yakai hannunsa yadora akan nata ganin yadda tai shiru da alama ta lula duniar tunani,my hafsat you liked it?!idan basuyiba yanxu ma lokaci bekureba semuje acanxo wasu akullum ina gaya maki your happiness matters most,feel free my hafsat….

“Hafsat tai murmushin da dimples dinta suka lotsa Wanda idan tayi Ita kanta tasan tagama da capt adam,”ware ido tai tadora akan nasa fararen idon dasuke mike dagashin ido zara_zara,hayatee wannan kayan ko lefen ‘yar gata se haka,wallahy harcikin xuciata nakejin son kayan nan,shirun danai kuma wallahi mamakin yawon Kayan da kyansu nake,wallahi Kayan nan sunyi matuka kuma nagode wallahy bansan tayaya xannuna maka iyakar godiar nanba,Ina rokon Allah kada yakawo ranar daxan ‘saba maka hayatee insha Allah bana tunanin akwai ranar daxataxo Wanda xaka kawo abu cikin gidannan nace beyiba ko banaso,wani ma baxan masa haka ba ballantana kai dakaikadaine acikin zuciata,ai wannan Kayan sun wuce beyond like,I really loved them..kalla yanda suke daukan ido,what amazes me most was the boxes ,,Hayatee favourite color dina kasamu,wannan de second lefe kamin,nagode Allah yakara daukakamin kai,yabarmu tare har abadan abidina,

“Capt adam ya washe fararen hakoransa Wanda suke jere ras acikin bakinsa,’Alhamdulillah ya rabb I feel beyond blessed,and I’m very glad that you loved them….ai my hafsat komai namaki banfadi ‘kasa ba sede fatan Allah yabarmu tare,batin yawan Kaya kuma karki manta kedin ‘YAR GATA CE(littafin miemee)’yar gatan adam,ko kin manta da wakar da marigayiya(deceased) baba laure ke mana?! “hafsat yar gata ce,’yar gatan adam captain…..

“Hafsat tai daria tana rufe baki,wai tsohon zance Kasan lokacin nan i was 17 fa,baxan manta ba ,,Kai Allah sarki baba laure Allah yajikan Wanda suka rigamu gidan gaskiya da rahama amin,

“Capt adam yace ameen ya rabbi …kai baba laure akwai abin daria sosai…’Sannan yace my hafsat baki tambaye ya akai nahada wannan kayan ba…

“Hafsat tai daria wallahy inataso natambaya kuma namnta I’m all ears hayatee gist me,nasan kila jirgi ne yai haka dan sometimes i wonder yadda jirgi yasan womanly abubuwa haka,’

“Capt adam yadinga daria harda rike cikinsa sedayai kwala”my hafsat kinsawa jirgi ido fa,kimasa excuse kinsan shikadai ne namiji adakinsu acikin su 10,taran duk mata ne shikadai ne Allah yai blessing iyayensa dashi sekuma yaxo yasami mata data maidashi kawarta’kwanaki yanagayamin yana washe baki ,kinaji nakira shi nace yaxo yakaini unguwa seyaxo lokaci a kure,time din kinje gidah,wallahy Ina Gaya maki waidana tambayeshi meyasa haka kinsan meyacemin?!

“Hafsat tadinga daria dakyar tadago kanta tace a’a..

“Capt adam yace hmm secayaimin wai wallahy oga ,me ‘daki nace ana mata ‘kunshi shine tace nakular mata da abinci inyayi nasauke kada nafita ya ‘kone,kinsan me ?!yanayi yana sosa keya yakecemin wallahy oga toh senadan sake dauraye kwanukan gidan ,dayake xamuyi baki kasan takusa sauka(haihuwa)…Capt Adam yakarashe xancen yana magana irinta jirgin… dan haushi my Hafsat ko kallonsa banyi ba nabude murfin mota nashiga,

STORY CONTINUES BELOW

“Hafsat tadinga daria tana ‘kyakyatawa wallahy hayatee ka iya gwada maganar sa kuwa,amma jirgi ya iya abin daria,no wonder yake haka.. gaskia dole na masa excuse kam,amma ya iya zaben kaya dukda nasan hayatee dina shima ya iya daukar favourite choice…amikamin godia metarin yawa ga jirgin,

“Capt adam yace Wlhy kuwa ,amma bafa shikadai muka hada Kayan dashiba,nide nasan I partake in chosen your favourite colors tundaga sets na akwati se kuma jirgi daya temaka da su sets na bangles da necklaces da earrings(awawwaro,sarkoki dakuma dankunnaye)sena ‘hadu dawasu manyan mata dattijai xasu girmeni ashekaru gaskia,wallahy a’dan kankanin lokaci muka saba dasu,suma sunxo hada Kayan brother dinsu wani faruk,sunada kirki beyond Wlhy,infact de sune suka hada maki kayannan karaf senida jirgi damuka tsinto wasu abun Se faruk tunda shi matashi ne auren farko shiya daukar mana latest designs da ake yayi awannan era(zamani)din…

“Hafsat tabaro inda take xaune takoma inda Capt Adam yake,sosai ta rungumeshi tana bashi wasu warming kisses dasuka dinga ratsa ita me sending din sakon dakuma shi dayake receiving din wannan zazzafn kisses,ahankali taxare jikinta daga nashi tana kallon kayan’thank you so much hayatee I love you endlessly ,”Capt adam yace ina godia sosai my Hafsat naji dadi dakike nuna soyayyarki akan duk abinda nabaki…”sannan yadan rage maganarsa ahankali yace dare yayi my hafsat gwara muje mu kwanta dan inaso da safe in Allah yakaymu xanfita munyi xamu hadu da imran,

“Hafsat tace gaskia ne hayatee but tayani zipping akwatunan semu tafi tare,’dukawa sukai atare suna rufe akwatinan suna ajiyewa agefe,harsun mike bayan sungama rufewa sun jera agefe wajan showglass dake cike da turaren wuta,hafsat tahango ledan da mjay takawo masu Kayan tsaraba aciki,

“Sauri tai tarike hannun Capt adam dayai gaba yana fadin my hafsat kinga traffic jam ahanyar kaduna yau?!dakya…

“Bekarasa ba hafsat ta tari numfashinsa”hayatee namnta shaf wallahy daxu mjay taxo Kasan tadawo hartake cemin kunyi magana ta whatsapp amma ta ‘boye maka saboda wai suprise visit takeso tamaka,wallahy shine takawo mana tsarabaa hartaba haule ma dogon riga da kayanta kunce,nikuma kaga,

“Tasa hannu tabude kwalin tace ‘tadaaa'(suprise)”capt Adam yace wow gaskia sunyi Kyau sosai kalla takalmin xema kafarnan taki kyau,”hafsat tai daria sosai ma kuwa akwai shigen design din a wancan Kayan sede shi machel kors ne(mk)Sannan taciro turaren tabashi,”gashi wannan tace abaka,

“Captain adam yace ohh mjay hadda wahala haka,haddani atsaraban?!ware ido yai bayan yaciro kwalin turaren Elizabeth aden fa,”Kai gaskia nagode sosai Wlhy Allah yasaka da alkhairi amin badan dare yayiba dana kirata nayi godia gaskia wannan tsaraba tamin dadi…Allah yabarsu tare da mu’azzam ‘din nata,

“Hafsat tai daria bayan tasaka jakan cikin akwati,ainace mata kagode sosai,Don nasan yanzu mjay taje germany a bacci kasan kamar Wanda Tasha sleeping pills in dare saboda tsabar bacci,”Ina mu’azzam yanxu kam mjay tashure xancensa tace ita gaskia baxata iya da bakinsaba kaji itama kamar ba bakar bace,wai tayi wani acan capetown though masters dinsa yake yanzu ,wani namnta sunansa de wai Ita gaskia yanzu shi takeso saboda fari ne,tafison sudinga haifan ya’ya Fanta and coca cola(fari da baki)…

“Capt adam yai daria Kai mjay akwaita da childish stuff ,xa tadena ne yarinta ce,…

   Haka suka ‘danyi hirarsu Sannan suka nufi ‘daki bawa bacci hakkinsa…

“Koda safe ma haka Capt adam yafita yadawo ,kullum zamansu cikin lumana da mutunta juna,sosai suke xaman lapia ga lokacin aurensa se matsowa yake,hafsat tayi tayi dashi yashirya yaje kaduna yaki yashure xancenta,ko abuja dinma yace yadau absence leave kullum suna tare kaman chewing gum,

“Aikwa ana’i jibi daurin aure ranar alhamis kenan,gwaggo takira Capt adam kan yaxo kaduna yanzu ko me yakeyi ya aje yaxo kaduna,batajira cewarsaba takashe waya,jiki ba karfi yamike yahada ‘yan kayansa tareda temakon hafsat dinsa,sanin Kansa yasan dakyar in gwaggo xata barshi yadawo seta Allah kawai,da kalamai masu dadi hafsat tashrya shi tareda fadin itama ranar asabar xataje gidansu,addua sukai suka Shafa sannan ta rakashi har mota jirgi yaja se kaduna garin gwamna,

“Haka tadawo cikin gida jikinta Yayi sanyi na irin rayuwar daxata shiga idan magajiya taxama matar adam…..

“Da yamma lis jirgi yai parking a parking arena din dake gidansu na kaduna,tunda yataho a mota suke waya da hafsat dinsa,sede in ankirashi yakatse ya amsa Sannan yakira back,dan wayar da suke yi da hafsat din ta temaka matuka wurin rage masa makokon bakin cikin zuciarsa sosai raguwa,dakyar sukai sallama Sannan ya maida wayar cikin aljihunsa,ahankali yataka yashiga cikin gidan yaname addu’a na Allah ya kauda duk wani ‘bacin ran daxe fuskanta acikin gidan nadaga gwaggo dakuma sharrin ‘yan uwa surayya da sadeeya Wanda sanadiyaru ne wannan sabon al’amari yafaru dashi,

“Da sallamarsa yashiga cikin babban parlor din gidan Wanda daka shiga shi kake fara gani,babban parlor ne dake dauke da kujeru har set biyu ,sosai xeci mutane ba kadan ba ,dukkoda ginin da ne amma sosai ankara renovating dinsa Yayi kyau,gidane wadatacce sama da kasa,Kansa tsaye yanufi saman ganin bakowa a parlor din dake kasa,kwakwazon su surayya ne yatabbar masa cewar gwaggon na saman,sarai yagane yanxu sune suka harzuka’ gwaggon tasashi tahowa dole,

“Bakinsa ‘dauke da sallama yashiga cikin parlor din,ayatsine su sadeeya suka amsa sallaman Sannan suka cigaba da hiran da suke,’Capt adam yadauke kansa dan yasan saboda sunga gwaggo agurin ne yasa sukai haka,bebi takansu ba sema haura ‘kafarsa dayai yakarasa wurin gwaggon wadda tacika tai fam kamar wadda xata fashe dan ‘bacin rai,

“Ahankali yakarasa wurin gwaggon tareda xubewa kusada gwiwoyinta ” gwaggo barka da yamma,nasameku lapia?!ayimin afuwa gwaggo abubuwane suka min yawa,wallhy aikine yasani agaba,Allah ya huci zuciarki gwaggo,

“Gwaggo tadauke kanta tana kallon gefe,adakile ta amsa gaisuwar,’dannan(capt adam)yanzu abinda kai yadace kenan?!yanxunnan ina gama kunhadu ahanya da Ita ,magajiya taxo nan tana kuka shabe’ shabe’ da majina cewar gashi daurin aure saura kwana biyu amma bata saka a idonta ba,tace ‘kawayenta da sauran ‘yan uwa sunata tambayar Ina kake ,tace wallhy kunya dukta kamata ,toh kasani ni kaba kunya bawani ba,dan ni nace mata xakaje kuma nace kafin kaje ma xaka kirata awaya kuma haka mukai dakai,da kujerun nan suna magana da sun bada amsa domin sune sheda se wannan yaron (Yaya sameer)…ashe ashe kunnen uwar shegu kai,kai fatali da maganata,ina mamakin sauyawarka lokaci daya ‘dannan..nasanka da BIYAYYAR IYAYE amma yanxu duk karushe wannan tarbiyyar,

“Capt adam yagirgixa Kansa yana hawaye dan dede da second daya bayasan ganin fushin gwaggon nasa,dukkoda yasan har a zyciarta yasan batasan wannan abin datake masa,annamimanci ne da kuma munafurci irin na ‘kannensa Wanda sun saba yimasa shi,har mamaki yake kome yasa oho?!”murya narawa yake fadin gwaggo dan Allah kiyi hakuri wallahy tallahy ba wai da niyya nai hakan ba,

“Naga niba yaro bane Ita ba yarinya ba,mexe sa ma tawani kaini wurin kawayenta su ganni?!,naga ba auren fari bane,amma insha Allah xanje gwaggo xami magana da ita.”Rannan dinma Wlhy akasi aka samu dakuma halin mantuwa irin namu na’yan adam,gwaggo Allah ya huci zuciarki ,nasan nayi kuskure insha Allah baxan sake ba,

“Tsakanin uwa da ‘da se Allah ,kankace me,murmushi har ya fada’da a fuskar gwaggo ,tuni ta yafe masa suka shiga hira na abinda xe wakana a bikin..dama gwaggon ba haka halinta yakeba mata ce me halin dattako da sanin yakamata,”gwaggo tace to lalle bayan magrib yahanzarta yaje su gaisa da magajiyan kada abin yaxama abin magana,

“Bayan sallar magrib kuwa,Capt adam yayo wankansa dukkoda bawai dan magajiyan yaiba,Yayi ne kawai saboda gajiyar tafiya dakuma yanayin hazo nagarin,

“Farin yadi yasa shara shara wanda ake iya hangar kyakkyawar farin shimin (singlet) dake jikinsa me ‘dishi dishin baki,bakar hula yasa tareda takalmi baki se agogon hannunsa silver color na company din swatch,mild perfume yafesa,sosai yayi Kyau kamar wani matashi baxaka taba cewa yakai shekara hamsin ba,kodan yana samin gatane dakuma karatu na alqur’ani dayake akai akai?! Yayi Fresh dashi sosai gashin kansa yakara kwanciya luf, sannan yafita waje wurinsu yace jirgi yakaishi unguwar tudun wada dake kadunan inda nan gidansu magajiyan yake,

“Sosai sunsha wahala kafin su gane gidan ,dan rabansa daxuwa gidan tun mahaifiyar magajiyan na raye wato inno fanta,dede wani madedecin bungalow (gida marar bene/flat)sukai parking kamar yadda aka masu kwatance,

“Capt adam yaja iska ya fezar yana kallon gidan,dakyar yadan kauda kansa gefe murya adakile “yace jirgi samu yaro katura cikin gidan kace magajiya taxo inji adam din gwaggo yanxu,jirgi nafita Capt adam yaja tsaki bumbling idiot kawai ko uwar mexatamin oho,badan kaddara bama wallahil azim mekama da itama baxan kula ba ballanta in aureta,

“Maganar jirgi ce ta katse mai tunani,”jirgi ya leko ta fuskar mudubin mota yana magana’oga ga…ga ta tafito fa,

“Ko kallonsa capt adam beyiba seda yagama ‘fadansa shikadai sannan yaja tsaki yabude kofar motar yafito,

“Bakar fuskar magajiya ce tafara masa sallama ,se washe baki take ,ga gatson bakinta ta sunturo waje,se wangale baki take tana wani rausaya gata shapeless da ita,

+
“Abinda take shi yabawa capt adam daria,se wani  bankaro kirji take tana fari da ido,hamdalah yayi  azuciarsa ganin hafsat dinsa tafita komi,muryartace takatse masa tunanin dayake Jiyai kamar buga drum ake dan sosai yafita sanyin murya,

“Yaya adam ina wuni anxo lapia nayi fushi seyau xakazo?!

“Capt adam yaja tsaki a fili sannan yai  Allah ya isa azuciarsa naganin irin matar dasu surayya suka hadashi da ita,”a fusace yace lpy qalau ,to banda abinki auren nanfa dole akamin sanin kankine inada matata danakeso kuma takeso na,yanxu ma danaxo seki godewa Allah ko,kinje kina neman hadani da uwata ko,to burinki yacika gani nazo…

“Magajiya tai katsa da murya tanawani shagwaba,ni ni yaya adam bawai hadi bane ,’kawayena keta san ganinka shine fa nafadawa gwaggo hakan,

“Capt adam ya murtuke fuska ke dan gidanku nixakiwa shagwaba?!sa’an kineni,kokwa dan ‘kaddarar aure tahadamu shine zaki renani?!sannan yasa yatsa yana nunata ni ba sa’an wasan kibane barganin kin saye bakinsu surayya,sannan inaso inja maki kunne wannan yaxama nafarko kuma nakarshe kada ki kuskura naji maganarnan agun gwaggo wallahy tallahy naji wannan tafito abakin gwaggo to kisani duk hukuncin dana dauka akanki kada kizargi kowa,

“Magajiya tai shiru tana sauraronsa sannan tace Toh seda safe,

“Harta juya tafara tafiya Capt adam yai tsaki nace kitafi ne?!sannan yasa hannu a aljihu yaciro bandir na dubu daya yamika mata ungo kyayi wata hidimar ta biki,

“magajiya tadan tsugunna tasa hannu biyu takarba sekace mutuniyar arziki,kaman gaske…tareda doriyar nagode yaya adam Allah yakara budi’.

“Bebi takanta ba ahankali yace ameen sannan yai tafiyarsa yashiga mota,jirgi yaja suka tafi…

“Suna tafiya magajiya tai Wata bazawar daria tana kallon kudin daya bata’ta yatsine fuska lokaci daya tacanxa yanayinta kamar bata taba fara’a ba,’adam kenan senayi maganinka da so called matar taka dakake ikrarin fadi,sena maidakai tafin hannuna muje zuwa,sannan takoma cikin gidah!

“Tunda Capt adam yazo kaduna gwaggo batabarshi yaje Kano ba,daurewa kawai yake amma Yayi missing Hafsat dinsa kwarai matuka’sede kullum suna manne awaya abinsu,

“Tun ranar juma’a da daddare Capt adam yake kuka sosai kaman ba babban mutum ba ..sosai hafsat take bashi hakuri ta waya,kukan dayai  yafi Wanda yai sanda babansu ya mutu,dukde saboda bakin cikin auren magajiya da zeyi yadda kukasan shine kishiyar daxe xauna da ita,da baki da hafsat take bashi dakuma Wanda yaya sameer a kanwarsa bilkisu suke bashi yasamu salama a zuciarsa,

“Ranar asabar da safe karfe shadaya da rabi aka daura auren Capt adam abdulrasheed da magajiyan inno fanta akan sadaki naira dubu hamsin chif..karfe shabiyu Dede akai reception a farfajiyar gidansu,antaru ba lefi,dukkoda ka’karo murmushi kawai adam yakeyi yana gaisawa da mutane amma cikin zuciarsa tarin bakin cikine wanda baxe misaltuba,

STORY CONTINUES BELOW

“Ana gama hidimar walima capt adam yakoma sashen baki tareda dialing number Hafsat dinsa yana kira,sau uku yana kiranta bata dauka ,hankalinsa yakai matuka atashi,bashiri yaxiri mukullin mota kotakan jirgi driver bebiba yatafi kano,

“Itakwa Hafsat alokacin tana gidansu sunata shan hirarsu wayar tatakuma tana dakin mjay kanwarta sukuma suna parlor,…..

✨•✨•✨•

“Hafsat sunata shewa da yan’gidansu a parlor mama itace mahaifiyar tasu(koda yake mahaifiyarsu hajia amina tadade da rasuwa tinlokacin su hafsat din na kanana,se aka baiwa mahaifin nasu kanwarta ‘Hajja Fareedah’wadda suke cewa mama,sosai take rike dasu kaman ya’yan data haifa,su biyu ne kawai wajen mahafiyarsu daga hafsat din se mjay,inda kanwar maman tasu kedah ya’ya 3 maza biyu wanda yan biyu ne habbab da hanbal,se mace kwara daya ihkhram wadda ke schooling a amsterdam!

“Mjay tadakko wayarta agefen kujeran datake xaune sannan tadago kai tana kallon Hafsat din,”Yaya hafsat anturo RUWAN KASHE GOBARA ki maxa kishiga duniyar makaranta yanzu,’se asannan Hafsat ta tuno tabar wayarta adaki,

“Mikewa tai tana aini shaf namanta wayar ma adakinki,xanso inga dillema din daxe faru tsakanin lamido da ihkas,”mjay tace hmm akwai ruguntsumi nan gaba,Hafsat tai hanyar dakin mjay,tana fadin kede bari ai akwai jan aiki,

“Tana shiga dakin  mjay,tai sauri tai zipping jakarta tadakko wayar tata,Wanda 5 missed calls tagani,3 na

Hayatee dinta se 2 na wata kawarta ‘nafeesat’

“Sauri tai tareda dialing number hayatee din seda ta kusa tsinkewa sannan yadaga,dasauri tai salllama tana fadin hayatee,aimin afuwa pls nabar wayar ne adaki nikuma ina parlor tareda su mama,”capt adam yace bawani abu my hafsat ina driving yanxu I wll call you back,”jiki sanyaye hafsat tace okay hayatee drive safe,sannan takatse wayan,

“Komawatai jikin bed site drawers tajingina ajiki tana tunanin ko Yayi fushi ne da’ita?!to driving din meya keyi yanxu ?!oh okay kila daga wurin daurin auren ne,

“Jiki sanyaye takoma parlor taxauna,mjay tace yanxu nasan andaura auren yaya adam ko?!tanayi tana kallon hafsat din,sekuma tai saurin sa hannu tarufe bakinta dn bakaramar katobara tai ba,

“Mama dake karatun magazine tai saurin ajiyewa agefe tace wane adam dinne xaiyi aure badai mijin hafsat ba?!!

“Itade mjay shiru tai dukta dubibice tai kasa da kanta,hafsat ta kakaro murmushi tana kallon mama, Sanyayyar ajiyar zuciya tai sannan tace “ehh adam ne zekara aure,amma tilasta mashi akai bawai yin kanshi bane,cousin dinsace aka hadashi da ita,kiyi hakuri mama dabamu sanar maki ba,

“Mama tace bakomi hafsat aiba magana me dadi bace dakin gayamin dinma,toh Allah yasa hakane mafi alkhairi ,yabaku xaman lapia yahada kawunanku,Ki saurareni dakyau nasanki da biyayya amma kikara wata akan wadda kikeyi,Sannan babu ruwanki da zazzafan kishi kinajina ,ansan duk macen dabata kishin mijinta batacika mace ba amma atleast kakki nuna kishinki akanta,tukunna ma wacce cousin din nashi aciki?!

“Hafsat tace magajiyan inno fanta wadda auren nan nata ya mutu,

“Mama tace ohh wannan ta kadunan ko,nide ince aiba wasu yammata ragowa inde ba mancewa naiba,akwai wasu addu’oi na tsari na kariya sunanan arubuce insha Allah inxaki tafi xandakko maki Allah yakareki daga sharrin masu sharri ,

“Hafsat tai kasa da kanta Tana fadin amin mama nagode,

“Sosai mama taxauna tana Bawa hafsat motherly advice tana dauka,harzancen kayan daya kawo mata sedata fada mata,mama ta ajiye kunya a gefe tabata shawarwari kan yadda  xata kula da kanta dakuma mijinta,seda suka shafe awa daya da rabi suna magana,”alokacin kuma megadi yaleko yana fadin Capt adam yace amasa iso yana kofar gate,

STORY CONTINUES BELOW

“Hafsat taware Ido tana kallon megadin,”yana  waje kokuma dan aike ya aiko?!

“Kafin yabada amsa mama tace jeka ilu kace gatanan fitowa,sannan tadaga kai takalla hafsat datai shiru kaman me tunani,”jeki yana waje kinsan dasanyi garin kishigo dashi ciki,Hafsat tace toh Sannan tadau mayafinta tayafa tafita wajen ….

                      16

  •✨•✨•✨•✨•✨•✨•

“Da sauri takarasa inda yake tana aika masa da kyakkyawan murmushinta Wanda bakowa takeyiwa ba sefa adam bahadeje,shima sakon murmushin yamar mata Wanda kyakkyawar wushiryarsa ta bayyana,

“Ahankali takarasa inda yake,bayan sungaysa tace hayatee mushiga ciki bansan sanyinnan yatabaka,capt yaware ido yana fadin”inkin ganni lahira kaini akai my hafsat,kinsan nawa mama babban lefi bansan dawanne idon xankalleta ba,

“Hafsat tai murmushi tareda sa hannunta tarike hannunsa suka fara tafiya tana fadin”Bakomi ai hayatee nariga nafada mata duk yadda abin yake kakka damu kanka,

“Atare suka shiga cikin parlor din Wanda mama harta bar gurin..kujera yaxauna yana yan waige waigensa,”Hafsat tasa gefen mayafinta tana daria kasa kasa “hayatee kacika tsoro wallahy calm down mana,bata rufe bakiba mjay tafito daga daki da saurinta ta karaso wajensu tana magana,

“Yaya adam yau agari,sannan tagaysheshi,”capt adam ya amsa cikin fara’a ‘mjay mutan capetown naga turare me dan karan kyau da tsada nagode Allah yasaka da alkhairi,

“Mjay tai daria ‘Yaya kenan naga kamin godia a whatsapp kamin ta waya Sannan yanzuma kasake min godia ,nice xanyi godia hidimomin da kakemana Allah yasaka da alhairi,

“Capt adam yai murmushi kawai ,ina mama?!bamu gaysaba,mjay tamike tace barin kirata…

“Mintina kadan maman tafito sanye da dogon hijabi kamarsu daya da Hafsat din sede itama bakace kamar mjay,gaisawa sukai sosai da adam din cikin kamala da sanin yakamata,

“Murya na rawa capt adam yake bawa maman hakuri kan rashin sanar da ita dayai auren daxeyi,”mama tai murmushi “bawani abu kada kadamu kanka wallahi zance ya wuce,Allah yasanya alhairi yahada kanku,Allah yakauda fitina,

“Capt adam yace ameen,”mama talura a takure yake dan inde tana guri baya sakewa,mikewa tai tanafadin murja kawo masa abinci da drinks a kitchen,”ka gayda mutan gidan,

“Capt adam yatsiri Sosa keya yana dukar da kai,xasuji insha Allahu,

“Seda yaci dadda’dan abincin maman,tsaftaraccen dambun shinkafane dayaji carrots da green beans se yankakken hanta sliced aciki,tareda salad dayasha hadi,gefe daya kuma kunun aya ne dayasha madara se kamshi yake,seda yaci yakoshi dan rabonsa dayaci abinci haka sosai tun yana Kano kafin yaje kaduna,dan duk sanda yatuno magajiya ce xexauna da ita amatsayin matar aure seya ture abincin gefe guda haryadan fada,,sosai yaci yakoshi sannan  yamasu sallama,suka fito shida Hafsat dinsa compound din gidan inda motarsa take,

“My hafsat muje gida ko?!hafsat ta bude idonta tana kallonsa hayatee muyime agidan ?!

“Capt adam yai murmushi tareda daga mata gira daya,yanzu dan miji yacewa da matarsa haka lefine?!

“Hafsat ta girgixa kanta bakai lefi ba hayatee sede naga bekamatabane,

“Capt adam yace ko?!to meyasa bekamataba inajinki?!

“Hafsat tai kasa da idonta danbaxata iya jure kallonsa ba,hayatee kasande yau akai daurin aurenka a kaduna ko,amma kakamo hanya kataho kano yanzu nasan su yayana(Yaya sameer)sunacan suna nemanka tawaya,kaduba kaga zancen nan..Dan Allah kayi hakuri wallahy bada wani abin nafada ba banasan abinda gwaggo xatai fushi dakai hayatee ,

STORY CONTINUES BELOW

“Capt adam yai ajiyar zuciya yana hura iska Yana fezarwa gabadaya mood dinsa yacanxa “da husky voice dinsa yakalleta bayan yabude mota yashiga shikenan my Hafsat nagane uzurinki amma kisani nifa magajiya bandauketa amatsayin matar aure ba,

“Hafsat tai saurin bude gaban mota tashiga’karkace haka hayatee abinnan fa haka Allah yarubuta seya faru saboda haka ka fawwala masa al’amuranka kawai,insha Allah xancigaba da tayaka addua ,”Capt Adam yace nagode Allah dayabani KE amatsayin matata,’Hafsat tai murmushi Sannan ta matsa kusadashi,

“Kiss tamai a kumatu tareda fadin Allah yakaimun Kai lapia hayatee,Capt adam yace uhm uhm my Hafsat ai ba anan kikeminba,Hafsat tai murmushi sannan tamai a inda yakeso Sannan sukai sallama tarufe masa kofa takoma ciki cikeda soyayyar mijinta,

“Hakan take awajen Capt Adam Dan dakyar yaja motar se kaduna ,yanatafe yana tunanin Hafsat dinsa da irin kyawawan kalamanta dasuke shiga jinin jikinsa suke kuma zaga kwakwalwar sa,murmushi yai yanafadin Allah kabarni da Hafsat dita har karshen rayuwarmu!

Seda Capt adam yashiga cikin kaduna sannan yakunna wayansa,dan tunlokacin daya amsa Kiran Hafsat dinsa yakejin alamar waya nashigowa shyasashi yakashe,sosai messages sukai ta shigowa na Allah yasanya alkhairi dakuma na yana ina abokai nata nemansa,bekarasa karanta message din imran abokinsaba dayake tsokanarsa wai ‘mijin hafsat angon amar….kiran Yaya sameer ne yatsaidashi daga karanta messages din dayake,dasauri yadaga tareda sawa a handsfree,

“Slm alykm yaya….bekarasaba ‘Yaya sameer yafara fadin,

“Kana ina haka adam?!yan uwa da abokanan arziki se nemanka suke saboda Allah tunda aka gama reception kaxargawa karenka igiya ina kaje oho,kabar masu daukar hoto da video coverage dukma bawannan ba saboda Allah kasa gwaggo se fada takemin,kana Ina yanzu haka?!

Capt adam yai shiru yana sauraron yayan nasa wanda yasan wannan fadan dayake haka tabbas ransa abace yake,kila gwaggo ce tadora masa lefi,”yaya ina cikin kaduna yanxu xankaraso nadan fitane,

Yaya sameer yai ajiyar zuciya “to kai sauri ka karaso gidah yanxu dan mutan hadeja kai suke jira xasu juya gida yanxu,

Capt adam yai saurin kada Kansa kamar yaya sameer din nawajen dan sosai yake bashi girmansa dukkoda bawani girmansa yai can ba,”ganinan yaya insha Allahu yanzu xan karaso da yardar Allah ,abasu hakuri..Sannan sukai sallama da juna,

Reverse yai yafigi motar aguje yai gidansu malali ,dayake dama yakusa karasawa tafiyar bayawa,musamman dayaba motar wuta…

Yana xuwa yai parking motar yafito,aikwa sauran abokai dabasu tafiba sukayo kansa akafara gaisawa,Sannan daukar hotuna yabiyo baya,dakyar yasaci jiki yashiga cikin gidah,zaune yasamu gwaggo da yan’uwa birjik a parlor din hira akesha ga abinci nan varieties ajere a kasan carpet da drinks ,gwaggo ma tayi Kyau ba lefi cikin atamfar super sheraton Wanda tayi kyanta dede gwrgwado,suma su surayya sunci ado kamar bikinsu ake sosai sukai shiga cikin wani lace blue and silver,

Bilkisu kanwarsa yar autarsu ita tafara ganinsa tataso tana fadin”yaya ,tundaxu naxo bangankaba barkada rana an wuni lapia?!

Capt yai fada’da murmushinsa ganin bilkisu kanwarsa duk cikin kannensa bawanda yakeso kaman ita,batada hayaniya kuma abin dunia beda metaba,”lapia qalau bilkisu  yagida ya ya atiku?!(mijinta)kodayake mungaysa dashi awaje ma,”lapia qlau yaya…

Karasawa yai cikin parlor din inda suka gaysa da yan ‘uwa da abokan arziki,sosai sukaita tsokanarsa shide murmushi kawai yake dan Capt adam bade kunya ba,sosai yaxauna suka sha hira da mutan hadeja inda yamasu goma ta arziki lokacin dasuka tashi tafiya,sosai akaci akasha sannan aka watse ,

Bayan magriba aka kawo amarya magajiya gaysuwa gurin uwar miji wato gwaggo, gwaggo tamata fada irin yadda aka gada daga kaka da kakanni,sannan tabata kudi dakuma turamen atamfofi da turaruka,kai tsaye akai convoy a motoci aka nufi gidan amarya magajiya dake unguwar kawo,gidane tanfatsetsen gaske Wanda ya amsa sunansa ,sama da ‘kasa dakuna birjik da faluka,harda sashen baki..yan uwa se yaba kyawun gidan suke tareda saka albarka dakuma kawo kazantar daki’,

STORY CONTINUES BELOW

Kodah capt adam yaga anwatse sashen baki yanufa nagidan su yashiga yayo wanka tareda daukar Waya yakira hafsat suka sha hirar soyayyarsu yana cikin wayar surayya tashigo ‘kerere ta tsaya akansa,Capt adam yadago kai yakalleta Sannan yacigaba da wayarsa seda aka kusan daukar minti ashirin sannan sukai sallama da hafsat dinsa badan yaso ba yakatse wayan,kotakan ta bebiba yacigaba da harkar gabansa bayan yadakko laptop yana dannawa,surayya tagaji dan kanta sannan tace”kaje gwaggo nanemanka,tajuya tai tafiyarta!

Capt adam yaja tsaki yana karkada kansa,rigarsa daya aje agefe yadauka yazura ajikinsa dan singlet ce jikinsa se dogon wandon rigan tunda yai wanka yake ahaka sunata faman waya da hafsat dinsa,dakin yarufe tareda nufa sashen gwaggo,yana xuwa yai sallama yashiga Ita kadaice a parlor din tanajan tasbaha fuskarnan a murtuke ba’alamar annuri,karasawa yai gabanta yaxauna tareda sunkuyar da Kansa kasa ahankali yake fadin

   “Gwaggo barka da dare,

Gwaggo takauda kanta gefe sedata dau lokaci sannan tace”‘dan’nan mekakeyi haka bayan kasan kaidin yanxu kanada Iyali yanzu anan garin?!sanin kanka ne layin dagidanka yake babu mutane sosai,gashi hardare yaja haka ashe kana sashen baki kome kake oho,maxa maxa yanxunnan katashi katafi kafin raina yaba’ci..

   Capt adam yasake sunkuyar da Kansa yana fadin”shikenan gwaggo bari inje Allah ya huci zuciarki insha Allah haka baxata sake faruwa ba,

Sannan yamike tsaye yana fadin”seda safe gwaggo nina tafi,

“Toh Allah yatashemu lapia,

Fita yai yakoma sashen bakin yai saurin hada kayansa cikin yar karamar trolley din dayaxo da Ita kadunan sannan yahau motarsa yatafi unguwar kawo inda gidan nasa yake,yana tafe yana magana shi kadai harya wuce wani tukubar me nama yai reverse yakoma baya yana fadin”nasan halin kalatacciyar matarnan yanxu inban siya mata namannan ba sarai seta kira gwaggo tafada mata tinda ba kunya ce ta isheta ba ..

Seda yafara biyawa wani dan kiosk yasiyo drinks sannan yatsaya dede wani gurin siyarda nama,zoka  kara suya spot ke rubuce boldly ajikin rumfar me naman,mesaida naman na ganin zungureriyar mota yataso yanufa inda capt adam yai parking tareda saka kansa tacikin glass din motar yana magana”Alhaji nama xaka siyane kaza ko tsire ko balangu ko Kilishi ko…

Bekarasa ba capt adam yakatse shi”gasamin kaji kwara uku,

“Toh alhaji angama yanxu kuwa,sannan yanufi wurin kajin tareda ciro dakwale guda uku yasasu a tukubar   yana kara ‘dumamasu don suyi xafi,sannan yacire su yagyara tareda yankasu yasaka a foiled paper hade da xuba coleslaw agefe da duk wani abinda yadace Sannan ya nannade’ yasaka aleda yakaiwa Capt adam”gashi alhaji angama,

Capt adam yai murmushi “aikinka yayi kyau,dajin kamshinnan ansan naman nan ya amsa sunansa Gaskia dole inxo in Kara kamar yadda nagani arubuce,toh nawa kudinka?!

Mai naman yai daria yana fadin”Dubu uku da dari biyar ne Alhaji,

Capt adam yasa hannu a aljihu yaciro kudin yamika masa Sannan sukai sallama,yafigi mota yai hanyar gidansa,yana xuwa yadanna horn megadi yataso aguje yawangale gate Capt adam yashiga,

Magajiya najin horn din mota tamike tanufi dressing mirror din dakin tafara gwagwada powder da jambaki,sannan takoma kan gado taxauna tareda sa mayafi tarufe fuskar ta wai Ita amarya,

Yana hawa stairs din dakunan yabi yana dubawa kusan duk dakunan biyar din cike suke da Kaya ,Yayi mamaki kwarai naganin yadda aka cike gidan da Kaya Yayi Kyau ba lefi dukkoda yasan gwaggo ce tai ruwa tai tsaki hakan ta faru,dakin karshe dake corridor yashiga nan yahango magajiyan xaune akan gado lullube fuskarta take da mayafi,daria yai naganin yadda tai din kamar wadda bata taba aure ba ,sallama yai sannan yashiga cikin dakin ,

STORY CONTINUES BELOW

Magajiya ta wani rage volume din muryarta tareda lankwasheta sannan ta amsa sallamar,capt adam yanufi gefen gadon ya sunkuya ya ajiye ledan kajin dakuma drinks sannan yamike yana fadin “akwai maganin sauro inxaki fesa acikin separate ledan gefan,Allah yatashemu lapia sannan yasa hannu yakullo mata kofan,

Dakin ‘kasa yasauka ya ajiye kayansa tareda murxa key ,sannan yajanyo wayarsa yashiga kiran layin hafsat,amma kassh beyi sa’a ba wayar tata a kashe take,yasan kuma Sarai tayi hakanne saboda taga andaura masa aure bataso tashiga hakkin magajiyan,siririn tsaki yaja sannan yajanyo system dinsa yana duba sabbin email messages dasuke shigowa,

                   •✨•

                     18

Dedicated this page to my adoring co writer waliyya(walissco)Allah yabarmin ke tawan!

    •✨•✨•✨•✨•✨•

Magajiya na ganin Capt adam yafice tamike tana zagaye dakin,tareda sa hannu akai kamar wadda aka aikowa da sakon mutuwa,

“oh ni magajiya duk uban kayan dana dirkawa cikina da jikina yatashi a tutar babu kenan?!dan wulakanci ko kallo ma ban isheshi ba gaskia baxan yarda ba wallahi.Wannan hafsat ko ‘yar iska tashiga tafita tacireni aransa wallahy sena koya mata hankali xatasan dawa tasaka kafar wando daya” ,

A fusace tajanyo ledojin tana dubawa ,sosai kamshin da’kwalen kajin suka daki hancinta  gakuma sanyayyan yoghurts da lemuka,se katon gwangwanin maganin sauron motein har guda biyu ,tsaki taja sannan tamike tashiga bandaki ta watsa ruwa tareda saka saukakkar rigar bacci sannan tahau cin naman tana korawa da yoghurt din sedataci tai dam ta gyatse sannan tabude dan karamin freedge din dake dakin tasaka leftover na kajin dakuma sauran lemon aciki,seda taci uban mitarta ita kadai tanayi tana tsaki sannan tabi lapiar gado takwanta,agadon ma batabar mitarba kamar wata mahaukaciya tanayi tanajan tsaki dakyar bacci yadauketa cikeda tarin irin mission din daxata hada’wa hafsat din,

Da safe ma haka capt adam yai wankansa sannan yasa jirgi yai ordering abinci anan hamdalah palace,kofar dakinta ya aje mata nata package din sannan yaci nasa Kansa tsaye yai ficewarsa unguwa kotakanta bebiba ,itakwa magajiya bata tashiba se wajen shadaya saura da hamma tamike ko salati babu se asannan tashiga bandaki tadauro alwalar asubah tai sallar da ko karatun sallar batayi ta sallame,sannan tasake komawa bandaki tayo wanka tareda mummulka turaruka dukde nadau kar hankalin Capt adam sannan tashafe rabin awa tana kwalliya harda girar da akeyi yanxu ta concealing.Wani material tasa doguwar riga ‘kirar bubu sannan tai dauri indimi style,tasa hannu tabude dakin karaf idanuwanta suka sauka kan ledar dake ajiye agefen kofar ,

Hannu tasa tadauka tareda budewa ‘lafceciyar wainar kwai ce agefe tareda soyayyan dankali da doya se kuma sauce na kayan ciki ,tsaki taja takoma cikin dakinta tana magana”yanxu bancancanci yashigo yaga yana tashi ba ,bankai kuma yamin magana nadau abincinba sede ya ajiye abakin kofa Allah ya kyauta”,

Koda captain adam yafita gidan Yaya sameer yanufa,Yana xuwa kansa tsaye yanufi sashen yaya sameer din cike yakeda ‘yan gidan Se hira akeyi,Capt adam yai sallama yashiga,bayan sun amsa,yaya sameer yadaga kansa yana duban capt adam din,

“Yanzunnan muke xancenka nida namesake dinka gashinan yanzu yadawo daga school yaketa wai shi nasa driver yakaishi wajenka”,

    Capt adam yai murmushi yana kallon yaron yaya sameer din wanda aka sawa sunanshi amma akece mashi ARFAAN yarone baxe wuce shekara 8 kuma yana yanayi da Capt adam din sosai,

“Zo my boy,my namesake”

yanayi yana mika masa hannu”oya xomu gaysa mana ARFAAN” ,

STORY CONTINUES BELOW

Dagudu ARFAAN din yanufi inda capt adam din yake tareda mika masa hannu”Baffa ina yini?”

“Lapia qlau ARFAAN ya school ya studies hope kana maida kai de ko?!danaxo last week bangankaba akace mamee tasa ankaika boarding school,kayi kokari akwai present babba inka fito da first ,second or third position kaji?”

ARFAAN yai fada’da murmushin dayake jin an ambaci present ,gashi dama keke yaketa San abbanshi yasiya mashi,sosai yasan capt Adam din xe siya mai tinda yasaba yimasu kyauta haka kawai ma,”ehh mamee ce tasa aka kaini turkish boarding sch amma da akwai dadi school din baffa every morning akwai sandwich da milkshake for free da ake bamu,xanyi kokari naxo haka Baffa xaka siyamin keke ko?”

Capt adam yai daria “karka damu ARFAAN insha Allah bayan keke harda wani abun ma xansiya maka,oya gimme a hug”,

Da sauri ARFAAN yasa hannuwa yarungume Capt adam,nan sauran yaranma suka taso aguje suka makalkale Capt adam din suna wasa ajikinsa,

Haka Capt adam yaxauna ya bararraje suna wasa shida yaran gidan suka gama suka hau game din whot aka dawo nintendo,wiii ,sannan sukahau wasan hide and seek ,Shide ransa yanasan yaran dansunada shiga rai uwa uba kuma bashida yara shysa ,amma yaya sameer yayi kan Capt adam din yadau ARFAAN ko MUS’AB amma yace a’a ganin shidinma bawani yaranne dashi dayawa ba dan matan nasa nayawan haihuwa amma sede asamu akasin kobasuxo da rai ba kokuma insun dan girma kadan su mutu,seya kasance ARFAAN dinne babba Wanda aka sawa sunan Capt adam!

Sosai suka sha wasa da yaran Sannan Yaya sameer yai gyaran murya”Toh aje ayi wasan awaje kuma Baffa adam din yagaji haka kwadawo anjima”,

Hira suka shi gayi shi dan uwansa inda yabashi shawarwari kan yarda xe rike matan nasa tsakani da Allah wato magajiya dakuma hafsat,sosai yadade agidan har gabannin sallar la’asar don ananma yaci abincin rana,Sannan yaiwa Yaya sameer din sallama yatafi,

Days passed,bayan kwana bakwai cif captain adam yahada kayansa Sannan yahau saman kamar kullum tana dakinta azaune donshi harmantawa yake da ita ma tunda babu abinda yataba shiga tsakaninsu,da sallamarsa yashiga dakin fuskarsa a’dan sake ,hannu yasa acikin aljihu yaciro bandir na 1k ya ‘aje a gefen magajiyan da batako kallonsa bayan ta amsa sallamar wai Ita irin fushin nan,

“Gashinan koxaki sayi wani abin nixan koma aiki,absence leave din dana dauka yakare”,

Magajiya tawani shagwabe fuska “yanzu my hubby tafiya xakai bayan bakawani da’de ba ninaxata ai sati biyu xakai ko fiye da haka”

Capt adam yaware Ido naganin yadda magajiya ke shagwaba dakuma Jin yadda takirashi wai my hubby,murmushi yai sannan yakadar da xancen yana fadin”idan katin wuta yakare akwai wani acikin locker drawer din jikin tv,nina tafi se Allah yakymu kuma”,

Magajiya tamike tana wani chest out “Allah yakayka lapia my hubby yadawo dakai lapia I will mss you badly Gaskia,barin rakaka”

Tasa hannu xata cire igiyar jakar hannunsa yai saurin dakatar da ita”no thanks base kinfitaba nagode”

Magajiya tabata rai “meyasa my hubby?!”

Capt adam yai shiru yana kwakwalo abinda xe cemata tayadda dan bayaso yajera da ita ,can yakada kansa yace”Kinga akwai maxa yan aiki Wanda ba muharramankiba ko?!”

Magajiya tafara wani blushing taxata har zuci yafadi haka sewani fada take axuciarta yafara kishinta kenan tunda har bayasan maxan waje suganta,murmushi tai tana wani fari da Ido”okay my hubby safe trip”,

Capt adam yafice yana fadin”okay thanks”,

Doguwar ajiyar zuciya yai bayan yafita waje yashiga cikin mota dan dakyar yake iya magana da ita dauriyace kawai,mirza key yai sannan yanufi gidansu dake malali ,yana xuwa yai parking tareda bawa  jirgi driver mukullin.

STORY CONTINUES BELOW

  “Kadan wanke ta kafin naiwa gwaggo sallama yanxu xamu juya Kano dayardar Allah”,

Cikin gidan yashiga dauke da sallamarsa se Murmushi yake duk dan gwaggo karta dakko wata maganar daban,dukkoda tarin bakin cikin dake xuciarsa yafi afadeshi ,sosai yatsani yatashi yaga fuskar magajiya a matsayin matarsa,sallama yai bakowa a parlor din sefa yar dattijuwar dake kula da gwaggon ,gaisawa sukai Sannan tamike tana fadin
“Bari ingayawa gwaggon kazo yanxu itama tashiga daki tadade anan zaune”.

•✨•✨•✨•✨•✨•

Seda gwaggo tadan jima kafin tafito sannan daga baya tafito jikinta sake da babban hijabi har ‘kasa da alama sanyi takeji bayanta kuma me aikintace harira dauke da kaskon wuta cike da garwashi jajir dashi,gwaggo tadan gyaran murya tana fadin”harira sa garwashin acan gefen parlorn yafi turaruwa gaba daya”

Bayan harira tayi yadda gwaggon tace fita tai tabasu wuri,shikuma Capt adam dasaurinsa yabar inda yake yakoma kusada gwaggon,

“Gwaggo barka da safiya antashi lapia?!”

“Lapia qalau ‘dannan,ya magajiyan tananan qalau?!”

“Komai lapia Alhmdlh gwaggo tana gaisheku ma”

Gwaggo tai murmushi jin ya ambaci magajiyan tana gaisheta kenan suna xaman lapia da sauri tafada’da murmushin fuskarta “ina amsawa dakyau”

Capt adam yai ‘kasa da murya yana fadin”gwaggo nixan koma bakin aiki hutun dana dauka yakare dama kwana gomane kwata kwata ,dakyar ma sukabani”

“Toh Allah yakiyaye hanya yakaiku lapia ,gashican bushasshen kifi kadau kwali daya katafi dashi dayan na wannon yaron ne shaf namanta mutan hadejia suka kawoshi”

“Gwaggo godia nake Allah yasaka da alkhairi,ina matukar son kifin nan sosai yake dadi a dafaduka dakuma miyar kuka,nagode kwarai xankirasu nayi godia insha Allah”

Sannan yadan sake dukawa “gwaggo nixan wuce”

Gwaggo tajasu addu’a Sannan suka shafa,sosai sukeyin hakan kullum idan ya’yan xasuyi tafiya ko idan sunaneman wani abun,tunda adduar iyaye dabance,

Sallama yaiwa gwaggon wadda tarakoshi har bakin kofa tana daga hannu sannan jirgi yaja mota Se kano,acikin mota capt adam yakira hafsat dinsa danya shaida mata yanakan hanyar dawowarsa ,ringing na farko tadauka, yasauke nannauyar ajiyar zuciya,da sauri muryarta kamar ana busa sarewa tadaki dodon kunnensa take ya lumshe ido,ahankali takara cewa,

“Slm alykm hayatee kana jina?!”

“Wa alykm salam my hafsat ,gaskia banjikiba kinsan inde ina magana dake i totally lost it”

“Hayatee kenan Allah yabarmin kai,ya kaduna da yan cikin kaduna hope Komi lapia?!”

“Lapia qlau my hafsat,yanzu haka I’m enroute to kano namatsu nai tozali da matata nayi missing dinta beyond words..

“I missed you beyond your expectations hayatee,and I’m so so very happy,Allah yadawomin dakai lapia,mekakeso nadafa maka?!”

“Banda zabi my hafst duk abinda kika dafa zanci,Allah yamaki albarka sena karaso”

“Okay hayatee yanxu kuwa”

   kodah suka gama waya da Capt adam dinta sauri tai tashiga kitchen tafara hada aroma din abinci,cikin lokaci ‘kan’kani tagama tafarfasa kazarta da Kayan kamshi tareda shiryta cikin jar miya dataji tafarnuwa,tuni kitchen din yafara kamshi,Sannan tadora ruwan farar shinkafa data tanadi su carrots agefe da green beans suma duk ciki xata sasu,da sauri taciro catfish cikin freezer tafara shirin gasashi(grilled fish),sedata gama shrya komi sannan tasashi kan grill yafara gasuwa,gefe daya kuma haule ce dake shrya ha’dad’dan salad hardasu dafaffen ‘Kwai agefe…sauri tai tashiga daki tafada bandaki tayo wankan sabulu dana madarar turaren wanka se tashin kamshi take,sakeyin brush tai hade da kuskure bakin da mouthfresh na strawberry ,gaban mudubi tanufa tafara Shafa mai da turaruka da madarar turare,gefe daya kuma kayantane kan kambasa dake turarar kamshi,

STORY CONTINUES BELOW

Kafin captain adam yakaraso har angama jere abincin kan dinning hade da lemonade dayasha madara da ayaba,gidan se tashin kamshin du’aul jannah yake da hafsat tasa,

Karfe 2;00 dede jirgi yai horn aguje hannafi megadi yabude gate din suka shigo da motar ,sosai suka tari ogan nasu suna murnar ganinsa,Kai tsaye yashiga gidah bayan ya sallami jirgi yace shima yaje wajen iyalinsa,

Yana shiga as usual kamshi yafara dukan hancinsa abinda yafara missing kenan Dan magajiya bata taba saka turaren wuta ba kwana goman dayai agidan,bakinsa dauke da sallama yakara cusa Kansa cikin parlor din yana kasaitaccen murmushinsa Wanda yake kara masa Kyau dashiga ran duk Wanda yai toxali dashi,

Da sauri hafsat tafito tana murmushi medauke da fara’a sanye take cikin atamfa yellow and blue riga da skirt dinkin ya amsheta ba kadan ba,tayi dagwas da ita kamar yammata,”afuwan hayatee nadanyi nesa da parlor ne kayi hakuri pls”sannan yasa hannu takarba jakar hannunsa tareda doriyar”barka da dawowa”bayan tayi hugging dinsa tsam ajikinta,

Hugging dinta shima yai sun jima ahaka kafin yadago fuskarta Yana kallo “my Hafsat kin’kara Kyau kullum kara Kyau kike Wlhy”

Hafsat tai daria bayan ta cusa kanta cikin kirjinsa “hayatee kaine ka kara Kyau koda yake kai angone to nima inajin abin ya”….

Bata Karasaba captain adam yai saurin sa hannunsa kan bakinta”sshhh my hafsat talk no more pls kyaleni daxancen aurennan ,tunda natafi wallahy bansamu farin cikiba seda nadawo nagaya maki ni bandauketa amatsayin matata ba sede yar’uwa ta saboda haka kiyi shiru kawai kokinaso raina yaba’ci ?'”

Hafsat tai saurin girgixa kanta”uhm uhm hayatee baxan sake maganarba”

“That’s my Hafsat oya xoki feeding dina da wannan dadda’dan abincin naki pls”

Dinning suka nufa sosai taxage tadinga bashi kamar kullum,har kifin seta tacire ‘kayar sannan ta samashi abakinsa,..,kodah dare ma haka tai special abinci tai feeding dinshi ,ko gurin kwanciya ma Hafsat ta tabbatar ita kadaice azuciar captain adam danyayi missing dinta ba kadan ba toh itadinma hakan yake,

Lokaci yaja watanni sun shu’de amma xaman captain adam da magajiya yananan yadda yake jiya’i yau yana bata kulawa kamar kanwarsa haka yadauketa amma haryau yaki’ karbarta amatsayin matar aure,bayan yataho daga gun magajiyan daga Kaduna danyana kwatanta adalci atsakani dukkoda xuciarsa tafi karkata ga Hafsat dinsa,yanxu kowanne gidah kwana uku uku yakeyi..yakira hafsat yace mata yana hanya,

Da sauri tamike dukkoda tarin gajiya dake jikinta,kwanakin nan gaba daya batajin dadi tasha pain reliever yafi akirga amma jikin meyakwn yai sauki karuwa yake gashi batasan tayarwa da hayatee dinta hankali,

Sassau’kar jollof rice tai da sphagetti dayasha kifi se soup din kaxa kawai datai masa,dakyar tayi donma haule na’dan temaka mata,

Kodah yadawo ma daurewa tai taresa tadanne kanta kamar ba abinda ke damunta danbatasan daga dawowarsa tadaga mashi hankali,sosai tafaranta masa rai,har kwanakin dayai suka kare aranar daxe tafi dasafe yakalleta lokaci daya dukta fita hayyacinta ta rame se fari data kara,nufa inda take yai da sauri yana dubanta

   “My Hafsat bakida lapia ne naga kaman bakijin dadi?!”

“Lapia Lou hayatee kaina ne ke ciwo xedena fa karka damu hayatee”.

“No tashi muje asibiti pls kila malaria ne kwana biyu bakya flirting hala?!”

“Yasss hayatee inaga malaria dan nayi amai ma, xanba haule tasiyo min anti malaria yanzu”

“Tashi pls my hafst muje asibiti barin kira dr NAUFAAL”

Bayadda Hafsat Ta iya adole tamike jikinta yadau xafi rau dashi,hijabi kawao taxura taje parlor taxauna Tana jiransa yafuto,da sauri yafito duk arude yake da Waya ahannunsa yasa a kunne,

“Hello dr NAUFAAL ya kana asibiti ne ko gidah wallahy madam Dina ba lapia?!,,,kana asibitin?!no barshi kawai baseka xoba I can’t wait any longer barimuxo kawai is urgent Kasan yau xankoma kd”

Haka yashiga mota shida Hafsat din,hannu daya Yana tuki daya kuma Yana taba fuskarta datadau xafi,yafadi sorry my Hafsat yafi a kirga,

Mintina kadan suka Isa asibitin dr NAUFAAL,Wanda yamata yan tambayoyinsu na likitoci Sannan yace “Gaskia akwai malaria amma ungo kwalbannan ga bandaki can ciki kikawo urine dinki xamuyi test”

Shiga tai tayi Sannan takawo masa,yakarba yanufi lab dinsu ,mintina kamar 20 yadawo Yana murmushi tareda Bawa captain Adam hannu sukai shaking “congatulations captain you are now a father ,nayi Ma madam dinka test nagano tanada ciki na tsahon sati 14(wata uku da sati biyu kenan)..”

Capt adam yaware Ido tuni hawayen farin ciki suka fara gangara afuskarsa”kana ..kana nufin MY HAFSAT TANADA CIKI?!”

Dr NAUFAAL yai murmushi ‘hade da xaro tissue acikin aljihunsa yasa a idonsa Yana goge hawayen dake zubomai shima nafarin ciki,Dan sosai yasan yadda abokin nasa kesan yara shekara 20 kenan ,danshi har ya ‘aurar da ‘yar sama,Se yanxu Allah yabawa matarsa ciki xata haihu,Allah kenan mabuwayine kuma gagara misali,ahankli yasa hannu Yana daga kafa’dar capt adam din dake kuka,

   “Tabbas matarka nadauke da ciki na tsahon sati goma shahudu(wata uku da sati biyu kenan,semuyiwa Allah godia da wannan babban rabo”

Hafsat dake gefe itama kukan tasa tana me kallon Capt adam,shidinma ita yake kallo,

+
Dr NAUFAAL yakallesu yadda suka shagala suna kallon junansu daria yai sanann yanufi hanyar fita daga consulting room din yana fadin”love birds inkun gama kallon junannaku ni ina scanning room xanmaki scanning muga lafiyan babyn dayadda xa’abaki shawarwari”

     Yana fita captain adam yadawo kusa da Hafsat dinsa ‘hade da janyota jikinsa yasa hannu yana goge mata hawaye ‘hade da gayamata dadda’dan kalamai”my hafsat bar kukannan please ,kinsan bansan naga hawaye yana xuba daga idonki wallahi har cikin zuciata nakejin hakan”

Hafsat tai shiru hade’ da ajiyar zuciya”hayatee nayi shiru kawaide I was beyond happy ne shiyasa,hayatee shekara 20 kenan wai nice da ciki,wallahi harna fitar da rai daga samun haihuwa”

Capt adam yagirgixa mata Kansa hade da dago fuskarta ya sumbaci goshinta”my hafsat nasha gaya maki Allah ne me bayarwa kuma shine me hanawa,shike kashewa kuma shike rayawa,ya axurta Wanda yaso,yakuma talatautar dawanda yaga dama,Komi yanada lokancinsa da aure da mutuwa da haihuwa duk min indillAlh ne saboda haka Allah xamu yiwa godia”

“Hakane hayatee Allah yabamu ya’ya masu yawan albarka amiin”

“Amin my hafsat yanxude xomuyi sujoudish shukruh mugodewa Allah bisa wannan babbar kyauta dayai mana Wanda kudi ko sarauta baxasu taba’ siyan taba kafin muje gidah kuma muyi sallolin godia ga Allah”

Bayan sunyi sujjadar godia ga Allah hade da addua agareshi alhamdulillahil lazi bina’amatihi tatimmussalihat.capt adam yajanyota hade dasa kansa ajikin cikinta wai xeje motsin babyn,hafsat tasa hannu abakinta tana daria kasa_kasa..

   “Hayatee ai baxakaji motsin babyn ba dankaramine fa”

“My hafsat yi shiru I can feel my baby kicking,”

Hafsat tamike tana fadin “to inaga babyn yagane  babanshi”

   Sun’dan jima suna hira kafin sumike sunufi scanning room inda dr NAUFAAL yake,da sallamarsu suka shiga,dr NAUFAAL yadago kai yana kallonsu,

   “To maman baby zoki kwanta barin kira nurse tamaki scanning din”

Itade hafsat murmushi kawai tai tareda kwanciya kan gadon dake gefen scanner din,captain adam kuma yaxauna kusa da ita yana Shafa gashin kanta suna kallon juna suna murmushi,sannu ahankli nurse ke scanning cikin tareda kallon scanner board din,Masha Allah babyn nanan lapia…

   Shawara nurse din tabata kan yadda xata kula da kanta dayadda xata kula da lapiar abinda ke cikinta,sannan dr NAUFAAL yakara danashi shara’do’din daxata bi,atake agurin capt adam yaciro bandir nakudi 1k yabawa nurse din,Sannan yace wa dr NAUFAAL goronsa nanan xuwa nanba da da’dewa ba.

Sallama suka masu Sannan suka hau mota suka gidah ,suna shiga parlor hafsat tamike hanyar kitchen Capt adam yai saurin tsayar da ita”my hafsat bade girki xaki dora bako?!”

“Sphagetti kawai xandora hayatee yanxu xangama Insha Allah”

“Gwarama kidawo kixauna keda girki kuma Se Allah yasaukeki lapia in Allah ykymu”

STORY CONTINUES BELOW

Hafsat tadawo kusa dashi taxauna ahankli a shagwabe’ tana shafa cyboc dinsa daya kwanta luf”hayatee karka maidani raguwa mana kasan inbana aiki wallahy xan sangarce yanxu haka xamu xauna ba lunch kenan?!”

Capt adam yai murmushi”bawani raguwa my hafsat,haule ta iya irin girkin ai,kuma i was planning na ‘karo maki wata yar aikin daxata kula dake sanann inaso nakawo Mjay taxauna kafin nadawo daga kaduna”

“Uhm uhm hayatee haule kadai ta isa base ankaro wata ba,Mjay kuma Allah yasa tayadda taxo kullum wannan chewing gum din yana tare da ita”

    capt adam yai daria “Mjay ai Allah yakarba addu’arta yabata fari dan capetown yamasunanshi my hafsat ?!”

“Sunan yan gayu nedashi ai kamar ita mu’ayyad sunanshi,bayan yamatsa wai shi January dinann yakeso ayi bikin,toh ance mashi de yabari February tunda idan anyi ma capetown din xasu koma daxama”

” Allah yasanya alkhairi yakaimu musha biki,barin je in dakko mjay din mekikeso xanbiya ta eatery nasiyo yanzu kafin haule tadora abincin?!”

“Taliya da wake nakeso”

Capt Adam yabude baki sanin Kansa yasan hafsat Batasan taliya da wake amma yau itace takeso lalle Komi da lokacinsa”shikenan my hafsat take care of your self I will be right back”

Sannan yadurkusa ya sumbaci cikinta my little honey boo boo special,yanzu xanje nadawo…itade hafsat Daria tai tana fadin”Allah yadawomin dakai lapia hayatee”

“My hafsat inaso nafadawa mama karuwar damuka samu amma Gaskia kunya nakeji gwaggo de innaje kaduna xanfada mata”

“Hayatee kakka damu mama xatasani ayanxu kuwa kana xuwa dakko Mjay”

“Kina nufin kafin naje kinbuga kinfada mata?!”

“Habade hayatee a’a kasande xaka dakko parrot and definitely seta fadawa mama ba mama kadai ba I knw right duk wani social ntwrk datake seta rubuta Mjay ce fa”

Capt adam yai daria “aita temakeni kuwa,baride nai sauri naje banasan nashiga kaduna da dare gwaggo tai fada…

•••••••

Capt adam naxuwa gidansu Mjay yai parking Sannan yashiga ciki,xaune Mjay take ita kadai a three sitter bakowa a falon sedanna Waya take tana murmushi ,sau 2 Capt adam yana sallama amma Mjay bataji chatting yatafi da ita,ana ukun ne tai saurin dago Kai sekuma tasaki daria..

“Yayana,wa alaykm Salam I was carried away da wannan chat din Allah de yakyauta min,Ina yini yasu Aunty hafsat?!”

“Komi lapia qalau mrs mu’ayyad”

Mjay tasa hannu tana kare fuskarta alamin kunya “yaya aibanxama ba tukun”

“Xaki xama ai Mjay rai de Allah yakymu,Ina mama?!”

“Mama tana bacci kanta ne ke ciwo”

“Ayyah Allah yabata lapia,dama my hafsat ce ba lapia gashi kuma xantafi kaduna shine nakeso ki’dan xauna da ita kafin nadawo”

Mjay tai saurin ware Ido take fuskarta tadau abin tausayi dantana matukar son yayar tata,”yaya meyafaru da yaya hafsat din?!”

“Kakki damu mjay bawani abin bane alkhairi ne,my hafsat itama Allah ya’azurtata cikin bayinsa Wanda keda rabon ya’…”

Bekarasaba Mjay tasauka Kasan carpet tai sujjada Tana hawaye”Alhmdlh at long last,Allah kaine abin godia”

Batabi takan capt adam ba taihanyar dakin mama,Capt Adam naganin tayi hanyar kofar mama yamike yatafi yashiga mota yaxauna..

STORY CONTINUES BELOW

Sedah Mjay ta tabbatar kowa nagidan yasani kafin tahada kayanta cikin akwati tatafi tashiga motar ,kafin su karasa seda yabiya eatery yasiyo lunch kafin sukarasa har mama takira hafsat din tana mata murna kafin taxo hakama sauran yan’uwa da maman tafada masu don abin ai murna ne aikuma sadaka bisaga wannan babban rabo shekara ashirin ba wasa bace…

…suna xuwa begama parking ba Mjay tafito tashiga cikin gidan tana kwala kira”yaya hafsat”

Hafsat nafitowa daga daki Mjay taje tarungumeta,hakade sukaita murna suna hira sukaci abincin tare,Wanda haule se washe baki take kamar gonar auduga dan hafsat din tafada mata,mintina kadan Capt adam yakara Sannan Hafsat tashiryashi yatafi kaduna tunda kwana ukun daxeyi anan tacika inkuma yasake kwana yashiga hakkin magajiyan!

Kodah dare ma dumama taliyar da wake tasa aka mata taci,Mjay Se kallon cikin yayar tata take tana jin dadi ,kaman anmintsileta tamike tadawo kusa da ita,

“Yaya hafsat yanzu mekikeso ki haifa mace ko namiji?!”

Hafsat tai daria”Mjay kenan ni komai Allah yabani inaso,healthy babies cikon addinin musulunci masu yawon albarka”

“To misali idan namiji ne wane suna xakisa inma mace ce wanne suna xakisa?!”

“Mjay kenan bakya rabo da silly talks Wlhy anyways idan namiji ne inason suna Muhammad_Ahmad”

“Mjay tai murmushi wow nice name to idan kuma mace ce fa?!”

“Idan kuma mace ce to inason sunan dana dade ina adanashi cikin zuciata,shine ‘UMMI_A’ISHA!”

                  •✨•

•✨•✨•✨•✨•✨•

Mjay tai murmushi “Allah yakawomana Wanda yafi albarka macen ko namijin amiin”

“Ameen mjay,masu albarka de amma aimutum bashida choice akan abinda ba kudi ne xe baka ba”

Kiraye kirayen sallar isha’i ne yatsaidasu daga hirar dasukeyi Sannan suka tashi donyin sallah!

                    •KADUNA

Kodah Capt adam yakarasa kaduna tsayawa yai a masallacin dake unguwar tasu ta malali yai sallah Sannan yashiga cikin gidah,bakinsa ‘dauke da sallama yashiga cikin gidan xaune yasamu gwaggon dakuma su surayya da kaskon wuta atsakiyarsu da alama dumin Wutar sukeji don akwai sanyi agarin sosai,

“Wa alaykm salam”surayya ta amsa sallaman Wanda daga gani kan dole tayita,

Se asannan gwaggo ta’dago kai don bataji sallamar tasa ba sefa amsawar da surayyan tayi,amsa sallamar gwaggon tai tana murmushi “dama zakazo ‘din yau?!,ni danaga yamma tayi haka naxata kabar xuwan seda safe nan nace sadeeya takira min kai awaya wallahi anata gwadawa taki’ shiga ba service”

Yabude baki zeyi magana kenan muryoyin su surayya suka katseshi atare suka ce”ina yini yaya?!”

Ko kallonsu beyiba danyasan gwaggon ce tayi masu fada’ dajin yadda suka gaisheshinma kasan bada niyya sukai hakan ba,”lapia qalau”ya amsa ata’kaice” Sannan yajuya hankalinsa ga gwaggon yana fadin”gwaggo barka da dare nasameku lapia?!”

“Lapia qalau ‘dannan ya hanya?!”

“Alhamdulilah gwaggo,dama wani uzirine ya’dan tsaidani na alkhairi amma da tuntuni najima ai anan din”

“Toh Allah yasanya alhairi aciki,iceko awajen aikinne?!”

Captain adam yasa hannu yana sosa ‘keyarsa “gwaggo dama,dama hafsat ce ta tashi da zazzabi shine nakaita asibiti”sekuma yai shiru,

STORY CONTINUES BELOW

“Ina jinka,rashin lapiar ce kuma abin alkhairi?!”

“A’a ba abinda nake nufi ba kenan to bayan munje abokina NAUFAAL shiyai mata test inda aka gano tana ‘dauke da juna biyu”sekuma yai shiru Yana sauraron abinda gwaggon xatace,

Gwaggo taware ido ‘hade da mikewa tsaye,sukwa surayya da sadeeya sandarewa sukai azaune,tuni fuskarsu takoma kalar bakin ciki sosai idonsu yanuna suna hassadar hakan,sekuma kallo yakoma kan gwaggon ganin mexatai,

Hannu gwaggon tadaga sama tana addu’a”Alhmdlh ya Allah ,Allah kaine abin godia ,Tabbas duk abinda hakuri bebakaba rashinsa baxe bakaba…ubangijin rahama kabata lapia ka kuma albarkaci abinda yake cikinta”

Tuni fuskar captain Adam ta fa’da’da da murmushi sosai yaji dadin addu’ar fa gwaggon tayi,”amin gwaggo ,amiin”

Gwaggo takoma taxauna tareda sake fadin”Alhmdlh kunyi sadaka kuwa?!”

“Wallahi bamuyi ba gwaggon shaf namance dakuma saurin danake nataho kar dare yayi”

“Bari yanxu xansa ayi sadaka insha Allahu ai wannan ba abinda yakamata atsaya haka bane,dakasani kuma kabari seda safe yanxu haka kabar hafsatun acan ita kadai’?ita magajiyan aida sena tura sadeeya ko surayya wani yaxauna da ita acikinsu kafin goben in Allah yakymu”

“Nima nayi tunanin hakan gwaggon sede kuma kada nashiga hakkin magajiyan shiyasa kawai nadaure nazo amma na’dakko murjanatu ‘kanwarta taxauna da ita kafin nakoma”

“Murjanatu batana waje karatu ba?!”

“Ta ‘kare tadawo gidah yanxu bautar kasa xatai har ana shirin bikinta ma”

“Ayyo!to hakan aiyafi,Allah yasanya alkhairi amiin”

Hakade gwaggo da capt adam sukaita hirarsu ,sukuma yan bakin ciki su surayya sulalewa sukai suka koma daki dan tinda yafara magana bawadda tai magana cikinsu,shikansa yagane bakin ciki suke amma ko ka’dan benuna masu ba..seda yaci abincin darensa anan wurin gwaggo Sannan yamata sallama yatafi nasa gidan!

Surayya da sadeeya nashiga daki,sadeeya tace”hmm surayya kinajin abinda yaya adam yace?!”

“Naji mana sadeeya nifa wani ma’ko’kon bakin ciki daya tsayamin awuya wallahi haryanxu ya’ki tafiya”

“Kede bari ya akai haka? shekara ashirin fa Kinga wai xata haihu”

“Naso magajiya ce xataita haihuwa wallahy,Gaskia banji dadin wannan lamari ba”

“Inafa da’di wallahi yadda naji bakin cikin abinda yafada da yadda gabana yafadi’ ko mutuwar baaba(mahaifinsu)banji hakan ba”

“Allah yakaimu yatafi muje wajen magajiyan kawai musan yadda xa’a ‘bulloww lamarin”

“Hakan za’ai”

Captain adam na’karasawa gidansa yai horn daknsa Sannan yashiga ciki,dayake barin jirgi yake acan gidan nasu yana kwana dakin baki,yana gama parking yai shigewarsa cikin gidah ,itakwa magajiya hartayi baccinta don duk azatonta captain adam din baxe samu damar zuwa yau ‘din ba.

Kansa tsaye yashiga dakinsa ya ajiye kayansa Sannan yahau saman dakin magajiyan,kwance yasameta se shararar bacci take abinta gakuma minshari datake kai kace ri’kakken zaki ne,

Kulle mata dakin yai yasauka kasa,koda yakoma Kasan wayarsa yadauka yakira Hafsat dinsa amma wannan karan mjay ce ta’dauka wai yaya Hafsat din tayi bacci ,murmushi yai sannnan yakashe wayan yana mamakin baccin hafsat din dawuri haka kodayake cikin ne yasata haka seyanxu yalura tabbas kwanakinnan ashe duk cikinne yake takura mata yawan kasalar datake dakuma kullum yaxo suna tare bashida wata ranar banxa ga fari data ‘kara dakuma kauri dajikinta ya’karayi,fada’wa bandaki yai yadauro alwala yadinga sallolin nafulfuli dakuma godia ga rabbus samawati bisa ga wannan babbar kyauta da ya azurtashi da ita….!

STORY CONTINUES BELOW

Koda safe da magajiyan tatashi tayi mamakin ganin captain adam din hartake ganin ko asubanci yayo yaxo,yasanar mata datin farkon dare yaxo bacci ne yahanata sanin xuwan nasa ,,,a daddafe captain adam yai kwana uku,ana ukun kuwa tunda rana wajen biyu yaiwa magajiya sallama Sannan yatafi gidansu yiwa gwaggon nasu sallama….!

                 •✨•

                   22

…..yana zuwa gidansu yashiga ciki,don ya matsu yagama abinda yake yatafi sosai Yayi missing hafst din tasa kwana ukun dayai kuwa ganin ta yake kamar shekaru uku,as usual gwaggon ce taredasu surayya a parlorn,

Sallama yai yashiga ciki suka gaysa da gwaggon dakuma ‘kannen nasa,gwaggon tace”Yawwa dama kai nake jira yanxu muka gama Waya da hafsatun naji yajikinnata kafin muje,nakuma tambayeta metakeso tace babu seda natakurata tukun tace wake takeso da taliyar hausa,se soybeans na awara..gasucan cikin bacco nasa harira ta’hada komai idan yakare se ayo Waya tunda kana xuwama kaga komai yaxo dasauki,yanxu nasa aka samo taliyar gidanda akeyi can kasan’ unguwar sarki bakagantaba ta murju sarai sarai da ita”

Captain adam yai murmushi “gwaggo harda wahala haka?!to angode Allah yasaka da alkhairi”

Sun’dan taba hira sanann captain adam ya du’ka yanafadin “gwaggo nixan wuce sena sake dawowa kuma”addua akai aka Shafa Sannan captain adam yafita sukadau hanya shida jirgi driver dinsa….!

Yana fita surayya da sadeeya suma suka fita,amma suka sanarwa da gwaggon cewar wai taron shekara shekara da ake na makarntarsu xasu hallarta…,

Suna xuwa megadi yahanasu kanse yasanarwa da magajiyan xuwansu tukunna,tsaye yabarsu ashanye kamar wasu Kayan wanki,tuni sunsaba da haka dan duk sanda sukaxo se hakan tafaru basau daya ba basau biyu ba suke shedawa megadin sufa ‘kannen megidanne seyabasu amsar cewar ai magajiyan ce tace kowaye xexo seta bada izinin shigarsu tukunna,

Sadeeya tace”surayya nifa nagaji da wannan wulakanci haba”

“Kyaleta sadeeya mude aibadan ita mukeba danmusamu abinda muke nema muke”

Haka megadin yawuce yatafi yasa hannu yadanna door bell din shiga gidan wadda ke tahanyar kitchen din daxe sadaka da babban parlor na gidan,

Kwance take tana danna waya,tsaki tasaki naganin irin rage mata Jindadin da xa’ai don taji dadin kwanciyar datayi,murya tadan daga tana fadin”ya akai menene?!”

“Hajia su surayya ne sukaxo sukace aimasu iso”

Ci gabatai da danna wayar hannunta kamar baxatai magana ba ta’dau mintina kafin takara sakin tsaki”sekace su shigo ai,nifa gaskia nagaji wallahi, haba wannan shiga rayuwata dasuke hr ina,Ina dalili kowacce takaso aure suna takurawa tawa rayuwar”

Sallama sukai suka shigo cikin parlor din kowacce atsorace take acikinsu,sewani ‘dari ‘dari sukeyi ,sunsan halin magajiyan kan rashin mutuncinta tayi degree akan fannin duk wani abu dasuke ta’kama dashi”

“Wa alaykm salam”tabasu amsa atakaice taname cigaba da danna wayar hannunta,sedata mula kafin takallesu tana wani yatsine fuska”to dawacce kukazo kuma?!,nifa nagaji da yawan xuwa gidannan dakuke gaskia,kawai ku fa’di metakawo ku kutafi”

Sadeeya takalli surayya,surayya tahadiye yawun bakin ciki murya narawa take fadin”kiyi hakuri magajiya ,bawani abinne yakawomu ba,dama hafsatun yaya adam ce kedah ciki zata haihu”

Shiru magajiya tai takasa magana,gaba daya tanemi muryar maganrta ma tarasa,wani ma’ko’kon tarin bakin ciki yatsaya mata a ma’kogaro,tuni idonta yakawo ruwa hawaye yafara reto afuskarta,”ciki”haka tafurta azuciarta ,

STORY CONTINUES BELOW

Tabude baki xatai magana sekuma tai shiru,tuni hudu’bar makirar ‘kawarta muneera naseer bello(munabi)suka fara mata reto nakarta ‘kara Tofa albarkacin bakinta aduk abinda su surayya xasu fadi ,karta kara sakin jiki ta yarda dasu don itadinma basonta sukeba abin hannunta sukeso,

Ajiyar zuciya tai tareda seseta kanta ta tsaida hawayen datake ,Sannan tadago takallesu “okay naji,xanyi shawara xan nemeku,xaku iya tafiya”

Sosai kalamanta suka basu mamaki,bayadda suka iya jiki a sa’bule suka mike suka tafi gidah ,suna fita surayya kefadin “lalle magajiya amma kalamanta sunban mamaki”

Sadeeya tai daria”mune fa,bade tace xata nememuba munanan dake seta dauka shawararmu ai wallahi munxamar mata ‘karfen ‘kafa”

Haka sukaita surutansu har suka bar cikin gidan,suna fita magajiya tamike tana xagaye parlor din tana surutai ita ka’dai ,wayarta ta’dakko tadanno number ‘munabi’kawarta takira,

“Kawata kixo gida yanzu ba lapia wallahy,ehh yatafi Yawwa sekin ‘karaso…..”

Ko minti ashirin bata ‘karasa ba munabi kawar magajiya ta iso gidan,tana shiga tanufi inda ‘kawar tata take wadda ‘tsabar ‘dimuwa ko sallamar da munabi din keyi magajiyan batajiba,hannu tasa tadafa kafadar magajiyan”kawata lapiar ki kuwa?!tundaxu nake sallama baki amsawa karki janyowa kanki wata damuwar fa”

“Munabi ina cikin damuwa sosai Wlhy Wanda bakiji yadda nakejin ‘kirjina ba”

“Ina jinki mecece matsalarki yanxu?!”

“Hafsatu matar adam mijina itace keda ciki zata haihu”

Munabi tai tsaki “to seme?!danxata haihu shine me?!haba magajiya meye abin damuwa anan kafin ‘dan/’yar suxo dunia xamu iya yin komeye danganin basu xodinba,zakuma mu iya salwantar da rayuwar ita hafsatun gaba daya ma”

“Munabi kenan tayaya xamu iya yin hakan karki manta bamu gari daya fa”

“‘Kawata kenan,me boka yace maki karshen xuwanmu wajensa ana’i jibi daurin auren?!”

“Yace xan haihu da adam din “

“Yawwa ashe baki manta ba,saboda haka yanxu de Ina wa’ennan ‘kannennasa?!Don wannan mission din sedasu ciki”

“Basu dade da barin gidan nanba,abakinsu nakejin hakan,donshi adam din harya ‘karaci kwana ukunsa nan gidan besanarmin hakan ba”

“To abinda nakeso yanxu kinajina ki kira kannen nasa kisan yadda xaki idan takama mubasu kudi ne se abasu din dannaga kajine su seda tsaba”

“Wa’ennan aisu komai seda kudi,ban fahimcekiba ‘kawata mexance suyimin?!”

“Susan yadda xasuyi su kulla makircin dasukasan gwaggo xata yadda kikoma kano gidah daya da hafsatun tanan xamu samu burinmu yacinma ha’ka,nikuma namaki alkawarin xanshiga xanfita xansan yadda xa’ai”

” ‘kawata nida adam fa baxaman ma’auratah mukeba”

“Bangane ba”

“To gaskia baya bani hakkina na auratayya”

“Sekace ba macece ba”

“Nayi iya bakin kokari na wallahy amma duk abanxa”

“To shikenan xanfadawa boka wannan zancen bekamata ai shiru ba”

“Nagode munabi Allah yabar min ke”

“Ameen ameen nifa abuja Ma nakesan xuwa akwai wata harka inkomai yadedetu i will let you knw”

“To ‘kawata Allah ya yarda”

Munabi tamike tana rataya Jakarta a kafada,”sauri nake yanzu xanje suleja xakiji komai bayan nadawo”

STORY CONTINUES BELOW

“Harxaki tafi,to shikenan Allah yadawo dake lapia,kuma kamar nawa zanbayar?!”

Munabi ta harareta da wasa”haba ‘kawata sekace ba ke ba,kinfasan me ake bayarwa ko basenayi dogon turanciba”(Allah karabamu da kauce hanya amiin)

“Xolayarki nake”

Sannan magajiya taraka munabi har parking space ,tashiga motarta kirar marcedez Benz new model!sannan takoma cikin gidah tana shawarar yadda xatai idan takira su surayya…..!

Bayan kwana bakwai ,lokacin captain adam yayi kwana uku a Kano yadawo Yayi uku a kaduna Sannan yakoma Kano da kwana daya kenan,magajiya takirasu surayya kan suzo gida tayanke shewara kmar yadda munabi tace tayi hakan tayi dan bokansu yagama komi kawai komawarta kano shikadai’ yarage,

Tana zaune tana faman kallo a tv film din hausa take kalla na ‘carbin kwai,megadi yadanna door bell tareda fadin”su surayya sunxo”

“Kace su shigo mana”

A tare suka shigo suka xauna a kujera bayan su gaysheta ,magajiya ta mike kamar gaske”sannunku da zuwa”

Freedge tanufa tadakko ruwa roba biyu da lemon kwali babba guda daya Sannan tadakko cups guda biyu ta ajiye”ba’a gama abincin ba nanda yan mintina kadan,ya gwaggo??”

Surayya takalli sadeeya,suka dade suna kallon juna da mamaki don sude basu saba ganin hakan ba agaretaba surayya tai karfin halin fadin”gwaggo nanan qalau,dama kince kinasan ganinmu”

“Ehh nace inason ganinku amma kafinnan,jnabaku hakurin abinda nayi maku rannan rainane a’bace”

Ware Ido sukai danjin abinda Tafada sosai yabasu mamaki,sadeeya tai murmushi “bakomai yawuce”

“Yawwa nagd sosai dama wata alfarma xakumin dan Allah”

Atare suka hada baki

“Allah yasa mu’iya”

“Tunda akai auren nan banso nahada gwaggo da adam ne amma azahirin gaskia hafsatu matarsa tashiga tafita bama….”sekuma ta ‘barke da kukan munafunci…

Surayya tatashi tadawo kusa da ita”magajiya menene meta maki?! dan Allah kidena kukan nan kifada mana mu kuma Insha Allah zamusan abinda xamuyi”

Magajiya tasa hannu tana share kwallar dake zubowa daga idonta”adam baya dauka ta amatsayin matar aurensa ko magana bata shiga tsakaninmu”nanfa taxauna tadinga fadin karya tanayi tana tsara wata karyar tana fesa masu,harse da ta tabbatar sunyadda sunkuma gamsu suncika sunyi fam…

Sannan tabar zancen tareda shiga kitchen tahado masu abinci kala kala takawo masu,dasuka tashi tafiya tahada masu goma shatara da arziki kamar yadda munabi tashirya mata ,kowacce turmin atamfar super holland da dubu 50cif tabasu,

                  •✨•

                    24

….Ana’i gobe captain adam xexo kaduna gwaggo tagama waya dashi,surayya da tai gyaran murya”gwaggo niyaushe xamuje kano ne duba aunty hafsatun?!”

Gwaggo tayi mamaki kwarai matuka amma seta share kawai ganin tamasu fada sosai kila fadan ne yashigesu”Insha Allah karshen watan nan in Allah yakaymu darai da lapia”

Sadeeya takaikace xama kamar gaske “Allah sarki Aunty hafsatu Allah ya yarda,nikuwa senaga yaya adam da yabar xuwa kaduna hakanan yaxauna yakula da ita tunda tana bukatar hutu”

Surayya tai murmushi tana kallon sadeeya”kuma hakane ,saboda sister dinta aure xatayi ba”

Gwaggo tai ajiyar zuciya”Allah de yaxaba abinda yafi alkhairi kawai idan komawar magajiyan Kano ce alhairi toh”

Nanfa dadi yakama surayya da sadeeya naganin abinda sukeso yakusan faruwa,

                             •KANO

Washegari da safe captain adam ne gaban dressing mirror yana gyara collar din rigarsa,hafsat dinsa nagefe tana polishing covered shoe dinsa,ta’kara Fari ga wani Kyau data sakeyi kamar ba ita ba…

    Mikewa tai bayan tagama goge takalmin tanufi inda yake tsaye”hayatee gashi nagama gwara kai sauri katafi kada rana tayi”

Captain adam yajuyo yai facing dinta hade da sarke hannunsu guri guda Yana kallon cikin idonta wani sonta yakeji yana kara shigarsa kamar karya tafi haka yakeji,”my hafsat Allah yamaki albarka”Sannan yadan sunkuya tareda sa hannu yadage rigar ta yana kallon cikinta dayadan fito kadan abin sha’awa hannunsa yasa yana shafa cikin dayake jin sonshi har cikin ransa tunkafin yafito dunia ,kullum haka yake idan xetafi seyayi wa cikin sallama yaudinma hakan yayi yana magana kamar da’dan gaske “honey boo boo special,xantafi kd sena dawo”sannan yai pecking cikin yamike tsaye ,

Sun ‘danyi hirarsu kafin tarakashi mota yatafi ,tadawo gida cike da so dakuma shakuwarsa,gefe daya kuma rashinsa akusada ita ke daminta,shidinma capt din hakan take atare dashi dan gaba daya hankalinsa atashe yake inxe barta yatafi kaduna,har suka isa kaduna tunanin hafsat dinsa yakeyi musanman yanxun daya kamata ace yana tare da ita tunda tana bukatar hakan,

                             •KADUNA

Jirgi na parking ya shiga gidansu kamar yadda yake kullum idan yazo,wannan karan gwaggon ce xaune tareda Yaya sameer ,bayan sungaysa yaya sameer kefadin”yanxu muke xancenka nake cewa kobakazo ba zanje gidan naka gobe in Allah yakymu”

Captain ya’dan duka cike da girmamawa “Toh yaya gani dama isowar mu kenan”

“Ehh dama munyi magana da gwaggo ne yanzu inda tashawarceni amma banyanke hukunci ba muna jiran ka’karaso”

“To yaya inaji”

“Dama gwaggo ce taga kaje kadawo kaje kadawo dakake da wahalar wa kullum kanakan hanya gashi shekaru tafiya suke ,musanman yanzu da Hafsat ke bukatar ka akusa da ita,mexe hana kamayar da magajiyan Kano da xama,har Allah yasauki hafsatun lapia..ko yaya kace?!….”

Captain adam yai shiru seda yadan dau lokaci kafin yace”…..,,.,,.,

•✨•✨•✨•✨•
“Yaya duk abinda kukace shiza’ayi Allah yasa hakanne yafi alkhairi amiin”
Yaya sameer ya ka’da Kansa “Toh shikenan xanyiwa haladu magini magana sesuje idan da akwai gyaran daxa’ai a part din daxata xauna sesuyi”
+
“Ehh baxa’a rasa ba musanman dayake bawani xama ake cikinsaba,nagode Yaya Allah yasaka da alkhairi”
“Babu komai adam Allah yakara hada kawunanku,idan aka gama gyare gyaren seta koma,bayan Allah yasauki hafsat din lapia se kuma asan yadda xa’ai inma takama tadawo nan din duk babu matsala”
Gwaggo taji da’di kwarai dagaske dan bata xaci abinda adam din xece ba kenan,”Allah yamaku albarka ,’dannan
“Ameen,ameen gwaggo nixan karasa can gidan”
“Eh gaskia to shikenan Allah yakaiku lapia ameen!”
Mikewa yai bayan yamasu sallama sannan yatafi gidansa,ransa duk badadi musanman maganar da akai masa yanxu,ahaka yai parking motar yashiga ciki,kamar kullum tana zaune a dogon couch din dake a gefen parlorn tana faman danna waya!
   Mikewa tai bayan yashigo tanufi inda yake tana murmushi”yaya adam,sannu daxuwa” tasa hannu xata rungumeshi yai saurin dakatar da ita “ina zuwa magajiya barinshiga ciki tukun”
Sannan yai wucewarsa daki yabarta nan tsaye,daki yashiga yai banging kofar hade’ dasa hannu yadafe kansa dake barazanar ciwo kamar xe fado,daure zuciyarsa yai yashiga bandaki yadauro alwala yai sallah yana rokon Allah ya shigar masa gaba kan wannan babban lamari daya taso,
Magajiya na ganin yashiga daki tai wani murmushi sannan takoma kan kujera taxauna,”adam kenan xaka dawo tafin hannunane xanyi maganinka”wayar tace dake ringing a gefe ta katse mata maganar datake Ita kadai kamar zaucacciya ,saurin sa hannu tai tadauka ganin Wadda ke kiran tata surayyan gwaggo shine sunan dake rubuce boldly ajikin screen ‘din ,tadanna answer sannan takara akunnenta tatashi tabar wajen taredasawa a handsfree
“Hello magajiya!”shine abinda surayya tace
“Na’am surayya yakike ya gwaggo?!”
“Lapia qlau,yanzu yaya adam yabar gidannan ai”
“Ohh haba nima bejima da shigowa ba”
“Ehh kinsan mun shawo kan gwaggo harma tayiwa yaya sameer magana,yanxu de in ‘kar’kare maki zance yaya adam din ya yadda xaki koma kanon”
‘Karamar ‘kara magajiya tasaki tareda dedeta kanta”Ina godia fa,lalle kunada babban kaso idan nakoma kuwa”
“Tohm Muna godia ,se anjima”
“Nagode sosai”sannan  sukai sallama takashe wayarta takoma parlor tana murna,wayarta tajanyo takira munabi tasheda mata abinda ake ciki…
                •✨•
                  26
Bayan wata daya shirye shirye ake sosai agidansu hafsat na bikin sister dinta mjay,aranar aka kawo set biyu na akwati yan gaske babu abinda babu aciki,komai yayi akasa biki sati biyu masu xuwa inda xa’a kaita South Africa(capetown)!
Alokacinne kuma gwaggo ta tsayar da dawowar magajiyan nanda sati uku ma’ana idan anyi bikin mjay da sati daya kenan,,kulawa ta musanman gwaggon kebawa hafsat din musanman take aika mata da taliyar hausa dakuma waken soya mekyau,
Sosai yanxu cikin hafsat din yafito kamar Wanda yashiga watan haihuwarsa,tayi kyau abinta tana samun kulawa musanman agurin captain adam ‘dinta,sosai takara shiga ransa ko lokacin daya mata magana kan magajiya xata dawo nan da xama bata damuba takuma nuna amincewarta akan hakan ‘dari bisa ‘dari!!!!
STORY CONTINUES BELOW
Sati biyu nazagayowa aka fara bikin mjay kanwarta tundaga kan bridal tea party din gidan yacika hargidan captain adam seda aka sauki baki,washegari aka fara biki ha’dad’dan lunching (kamu)akai a harabar the afficent Kano,se kuma dinner da akai da daddare a golden dragon ,se fulbe day da akai sannan gidan maxa suka ha’da wushe wushe night a meena even center dayake asalinsu kanuri ne amma na’yan chad,ranar asabar da safe aka daura auren mu’ayyad dakuma mjay a masallacin Omar bn khattab,kan sadaki naira dubu hamshin cif tunda albarkar auren akeso bayawan kudin ba!
Masha Allah taro yayi taro mutan kaduna dana hadejia duk sunxo,magajiya ma taxo da munabi kuma anmasu kyakkyawar tarba kowa yatafi da savouniers kala kala ,ranar lahadi da safe iya kawayen amarya da ango sukai barbecue day da daddare kuma aka raka amarya mjay airport suka ‘daga capetown itada angonta mu’ayyad(Allah yabada xaman lapia mrs mu’ayyad),
Sati naxagayowa magajiya ,munabi da ‘yan uwanta su biyu mata (lube,hanne)su suka rakota se surayya da sadeeya,sosai angyara mata nata part din sede ko kusa baxaka hadashi Dana hafst dinba,kwata kwata bama daya bane,dukkoda cikin gidah daya yake,nan wurin hafsat din suka shiga sukai sallah,kamar yadda bokansu yasheda masu kada sutada wata fitina inba hakaba aiki fa baxe ciba,sunbi shawarar tasa dan saboda tsabar kisisina ma magajiya ‘aunty’ take kiran Hafsat din dashi,Itade Hafsat ido kawai take binsu dashi tunda tasan Wanda daga farko yanuna bayasan ka bayayi dakai tofa koya dawo yana sanka munafunci ne,haka suka gama wuninsu sanann mota tajasu se kaduna bayan magajiya da munabi sunshafe sama da awa daya adaki!!!
Washegari da safe ranar takama ranar da hafsat xata koma asibiti amata scanning baby boy ne ko babygirl though de se abinda Allah yasa shiza’a samu,yanzu kowacce Kwana biyu biyu yake a wajenta,da sassafe ya shirya yanufi part din hafsatun sa,itama ashirye take tana karasa shan oats din data dama,”Maman baby”haka yace da Ita,
“Hayatee,aida bakai asubancin tashi ba nacewa jirgi yaxo yakaini”
“Maman baby kema kinsan abinda baxeyiwu bane wannan wasa kike kema”
“To shikenan hayatee”
Light kiss yabata a baki Sannan yasaketa suka fita suka shiga cikin mota ,se asibiti inda nurse tayi scanning sosai baby girl ce keta kicking kafafuwanta abinta,hamdalah sukaiwa Allah dan kowannensu cikin zuciarsa yanasan mace bayama ‘i captain adam din,sannan sukai hoton cikin har guda biyar sekace Wanda xa’abi dangi araba,murna awajen captain adam bakama hannun yaro,haka yadinga washe baki kamar gonar auduga,
Suna xuwa yai parking Sannan yadubeta “maman honeyboo boo tsaya Ina xuwa”
Daria tai Sannan tai kasa da kanta tana kallon cikin nata wanda take matukar Jin sonsa nabin magudanar jininta,jinta gaba daya ahannun captain adam shiya dawo da Ita daga tunanin zucin datake ahankli take dukan kirjinsa da wasa tana magana”hayatee pls ka ajiyeni Baka kojin kunyar masu aikin gidannan?!”
Kotakan zancen datake bebiba seda yadureta da akujera parlor Sannan yakoma yajanyo handle da freedge yaciro fresh milk a ciki yatsiyaya a cup,tabude baki xatai magana yai saurin mika mata cup din “ungo sha ki sanyaya zuciarki my hafsat Dan Allah kidena yunkurin hanani aikin ladan danake maki pls”
Hafsat tai kyakkyawan murmushin ta Wanda inde tasan tayi take gamawa da ba hadejian,ahankli takai cup din bakinsa taname kafeshi da idonta “oya bude bakin mana hayatee,Allah yabarmin Kai”
Captain adam yai Daria “my Hafsat akwai ki akwai wayo fa,Allah yasade honey boo boo tai wayona “
“Ai komaima irin naka xatai Insha Allah”
Janyota yai yadorata kan cinyarsa yana shafa gashinta dayasha kitson shuku,yabude rigantata yana kallon cikin ,bayan wannan shine karo na kusan hudu dayai hakan aranar kawai,cigaba yai da Shafa cikin yanaji kamar yasa hannu yaciro shi dan so,dede nan magajiya tashigo cikin parlor din,
STORY CONTINUES BELOW
Jabayatai tai turus ganin Hafsat din datai ‘dare’dare akan cinyarsa,bayan itako kusadashi baya barin taxauna balle ga hawa cinyarsa ,basumasan tana kansu ba,seganinta sukai akansu ,captain adam yahade rai kamar betaba Daria ba”ke dahankalinki kuwa?!xaki shigo mata parlor baneman izini bakomai Sannan kinshigo buguzum buguzum dake kamar arniya ba sallama meye hakan?!”
“Nayi sallama bakujibane,dama abinci ne karyai sanyi”
Captain adam yai tsaki seyanxu yatuno a part dinta yakema “kije xanxo”
Sedata watsawa hafsat harara kafinta fice tana surutai,Itade Hafsat jikinta yai sanyi ,captain adam yalura da haka sake kankameta yai ajikinsa yana ra’da mata wasu da’da’dan kalamai akunnenta Wanda sukadak sukasan mesuke nufi,
“Hayatee katashi kaje pls”
“Babu ruwanki my hafsat,infact karya ma take ni bawani zancen abinci damukai da ita “
“Hayatee pls katashi kaje bansan abinda Allah xekama ka akai,kabata hakkinta pls hayatee”
“Ohh noo,my hafsat yaushe muka saba musayan yawu dake?!”
“Shikenan hayatee yawuce,ayimin afuwa baxan sake ba”
“Ehhmm yanxu yakamata musa sunan baby ko?!aganinki wani suna xamusa its your choice”
“Hayatee kaine kakeda zabi baniba”
“Nabaki zabi my hafsat,tunyaushe dankwali yaja hula,ainaxama rakumi da akala se yadda kikai dani”
Daria Hafsat tai me isarta Sannan tai murmushi”nikam inason UMMI_A’ISHA”
“Wow,Masha Allah sunan me dadi kuwa,Ummi Aisha yai repeating sunan,Allah yakawo mana UMMI_A’ISHA lapia yarayata akan tirbar musulunci amiin “
Sannan yamike yana fadin”to maman UMMI_A’ISHA,barinje wajen kalatacciyar can kafin takira gwaggo,,,
Gaisuwa maitarin yawa gareku masoyan UMMI A’ISHA Nagode sosai da ‘karfin gwiwar da kukebani inasonku aduk inda kuke akoda yaushe !!!
Cikin hafsat nashiga wata na takwas da sati biyu,captain adam dakansa yatafi dubai yai siyayyar Kayan baby tundaga kan gadon baby har izuwa diapers da wipes dukse da ya siya,akwati 6 yai manya manya 3 na baby UMMI_A’ISHA ne tundaga kan 1month har zuwa 3yrs yasiyo mata ‘dayan sauran akwati biyun kuma na hafsat dinsane kayane nagani na fa’da hadda jakankuna da takalma sauran dayan akwatin kuma na magajiya ne itama babu lefi cike akwatin yake da kaya,yayi hakane saboda fita hakkinta akansa…!
Ranar alhamis ranar da captain adam xedawo da sassafe sadeeya da surayya sukaiwa part din magajiya asubanci ,dukde akan tukwicin datace xata basu,a parlor suka zauna suna jiranta tafito,haka tafito sanye da Kayan bacci kaurara tana wani yatsine fuska hade dayin tsaki ta xauna akujera ..
Atare suka hada baki wajen fadin “Ina kwana magajiya?!”
“Daban kwana ba kwa ganni yanxu ne?!”
Surayya takalli sadeeya tana fadin”tohh meyai zafi??”
“Nide nasan ba xuwan Allah da annabi ne yakawo kuba,inde akan tukwicin danace xanbakune na fasa najanye zancena dangarin nan danawo dinma kusan ince nafi ‘kunsar bakin ciki akan zaman danake a kaduna…gashi kukuma bakwa wa mutum uzuri arayuwa”
Sadeeya taha’de rai “amma de magajiya kinsan mutum baya alkawari de yafa Sa ko?!”
“To anfara yi akaina”Sannan ta mike tana hamma”nikun katse min baccina wallahi,inkun fita kujawomin kofa se anjimanku”haka tashige daki abinta ko takan su batiba….
STORY CONTINUES BELOW
Surayya tai tsaki”shegiya me kama da mayu wallahi dama nasan za’ai haka”
Sadeeya tamike tsaye”kyaleta intasan wata aibatasan wata ba ko?,muje zuwa “
Tashi sukai suka fita sunata gunguni suna mayar da magana,part ‘din hafsat ma ko kallo be ishesuba haka suka fice daga gidan suna mita har akan titi,
Da rana ma hakan take har wajen 2 magajiya na shara rar bacci abinta ,bugowar kofar da akeyi shiyasata daga kan pillow din datake tana huci dan duk azatonta su surayyan ne basu tafi ba”wai waye ne?!”
“Hajia,Aunty muna_b ce taxo”me aikinta ‘dahare tafadi hakan
“Ohh okay ganinan kice mata ina xuwa”
Bandaki tafa’da tai wanka se asannan tai alwala taha’da asubah da azahar tana idarwa tamike tsaye tacire hijabin ta jefar ko zikirn bayan an idar da sallah bataiba tunda bayi’din take ba!!!
Parlor tafuta tana murmushi tana kallon kawar tata muna_b data ‘harde kafafuwanta ta hakimce akan doguwar kujerar parlor din kai kace matar sarki ce “kawata ainayi fushi seyau kika tuno dani?!”
“Kibari kawai ‘kawas kwanannan i wasn’t my self abubuwa was hundred much on me yauma daurewa nai nace barin zo iceko megidan naki bayanan?!”
Magajiya tai tsaki “caxakice min iceko mijin hafsatu bayanan,dan nide ba zaman aure nake ba,Wallahy muna_b bansan wanne irin sihiri hafsat kewa adam ba gaba daya wani irin so yakema ta wanda nide ko a littafi albarka”
Muna_b tai tsaki”bari kawai mu salwantar da rayuwar shegia yar iska”
“Taya ya kenan ?!bayan ko ‘bangaren ta niba zuwa nakeba tunda yahana wai seda izininta nifa har nayanke shawarar karbar takarda ta baxan iya wannan wahalalliyar rayuwar ba”
“Zancen banza kenan ki karba takardar ki akan wani dalilin?!saboda makircin ta tohh wallahi a’a,kinaji ‘kawata yadda zata haihu kema sekin haihu da yardar Allah,Kuma wallahi semun ta tse shi tsaf”
“Kmar kinsan kafin yai tafiyar nan naji yana magana awaya waiya kusa signing resignation letter”
“Yawwa kinga zaki tatsi rabonki abinda boka yafa’di kenan kawata,yanxu mu kauda waccan banxar tukun seki fara tsara taki rayuwar kawata”
“Tayaya kenan kinsan fa takusa haihuwa”
“Bayan ke anhana ‘dahare me aikinki zuwa ‘can dinne?!”
“Nima fa bawai hanani akai ba wai sede na nemi izininta tukun kome yake nufi oho ?!nitunda ga ranar bansake bin hanyar ba ma”
                   •✨•
                     28
___muna_b tai daria hade da xuge zip din Jakarta taciro wani abu a bakar leda tamika mata,”ungo rike wannan shine abinda ze salwantar da rayuwarta dakuma rayuwar abinda ke cikinta”
Magajiya takarba ledar tareda bin ledar da kallo sekuma ta kalli muna_b dake murmushi ita kadai’
“Menene wannan ‘din?!”
“Karkashi ne,Wanda de kika sani mekyau amma fa na nijar ga santsi ga gardi”
“Miya xanyi dashi ko me??”
Muna_b takalli agogo “wai haka lokaci yaja karfe 4 har tayi?!”
Magajiya takalli agogon sekuma takalli muna_b dake zipping jaka tana gyara mayafi zata mike,”kawata bakimin bayanin yadda xanyi miyar dashi ba fa naga Kuma kina shiri wai tafiya xaki?!”
STORY CONTINUES BELOW
“Tafiya xanyi garinmu da nisa kaduna banan kusa bace kawas’,karkashi Kuma babu miyar daxaki dashi kisan yadda zaki kitura ‘dahare me aikinki tazuba a’inda hafsat din zata wuce ,karkashin nijar ne akwaishi da santsi ko ‘kadan akai amfani dashi ballantana duka zakisa ta karkada tazuba,Ina gaya maki sede kikirani kinamin albishir din mutuwar ta itada ‘dan cikin nata”
Sannan ta mike tai hanyar fita”trust me kawas wannan shine ‘kadai solution”
Magajiya tai tagumi “kawata ina tsoron abinda xeje yadawo”
“Toh seki zauna ana takaki ae ‘bawon albasa ma yafiki daraja agidannnan,nina tafi”bata jira cewar magajiyan ba tanufi parking arena din gidan,magajiya tabiyota abaya tana fadin”kawata kya baride mu…..”
‘Karar horn din mota shi yahana ta karasawa,zungureriyar motar captain adam ce tashigo ciki kirar Lincoln lx new model,fitowa yai bayan jirgi yagama parking yanatafe yana waya muna_b tatsaya su gaysa,katse wayar yai suna gaisawa da muna_b,sewani sunkuyar da Kai take kasa kamar mutuniyar arziki tana magana sekace ustaxiya “sannu da dawowa yaya,Nima yanxu nace barin karaso mugaysa naje yiwa kanwata visiting acan shekara boarding school dinsu”hakade suka gaysa Sannan sukai sallama taja mota tatafi,shikuma yanufi site din hafsat dinsa bayan yacewa “magajiya inta gama abinda take taxo takarba sa’ko”
Da wannan zancen dayai magajiya tai murmushi ganin aikinsu yakusa cinma buri ,tana gama abinda take tanufi site din hafsat din kamar yarda yace amma sungama kitsa yadda xasuyi itada ‘daharen dayake Itama ‘daharen duk kanwar ja ce mugayene dukkansu babu Wanda yafi wani mugunta,kar tasan kar ce!
..tana zuwa bayan sun sake gaysawa ya bata akwatin tsarabar ta tanuna farin ciki kmar gaske amma kasan zuciyarta bakin cikine karara musanman ganin akwatunan biyar datai atsakiyar parlor din cike da kaya,”haule,haule”haka hafsat tadinga kiran haulen amma shiru,
Magajiya tai murmushi “ko inkira maki Ita?!”
“A’a Wallahy barinje ainan bakin kitchen ne zani banisa zanyiba naji da’din ‘kafata ma”
Mikewa hafsat din tai tatafi alokacin Kuma captain adam yabar parlor din yana waya dan dayana nanma baze bari hafst din taje takantava sede shi’din yaje,magajiya tai murmushin mugunta azuciarta kwa fadi take”wannan shine karshen tafiyarki adoron dunia”(Allah ka’dora mu Akan ma’kiyan mu ameen)
Wata razananniyar ‘Kara hafsat din tasaki bayan fitarta bawani jimawa,alokacin magajiya tatafi da gudu ha’de dasa moper tai mopping wajen gaba daya yadda kasan wani abu betaba xubewa ba Sannan ta duka santar hafsat din tana dafe kai ha’de da kwalla Kara”Wayyo Allah nashiga uku”Ita Kuma hafsat din idonta arufe yake se hawayen azaba take,
Dagudu captain adam yafito yana ganinta yajefar da wayar dayake beyi wata wata ba yaciccibeta yasa acikin mota,yan aikin gidan duk suka fito harda haule da ‘dahare ashe magajiya ‘dahare tasa tadauke hankalin haulen tahanyar rokonta datai datayimata kitso ko ‘kwara hudu ne,bude mota itama magajiyan tai tashiga se asibiti suna zuwa dr NAUFAAL ya nufi inda suke yana magana “lapia Yaya haka captain?!”
Captain adam dukya fita haiyacinsa”I know nothing Wallahy ,Dan Allah Doctor kace to rayuwar my hafsat”
“Calm down captain Insha Allah I will try my possible best yanxu kanutsu addua xakai mata”
Labor room suka shigar da ita kusan awa biyu ana abu daya but no avail ,kuka shabe’shabe’captain adam yadingayi,magajiya Kuma nagefe kaman tahadiyi zuciya tamutu dan bakin ciki da bakin hali,dr NAUFAAL yafito yanacire handgloves dinsa yawullar agefe yadoshi inda captain adam yake hade da dafashi”captain ya akai matarka tai wannan mummunar faduwar haka?!how on earth ko wani abin yafarune gashi she’s unconcious ma gaba daya sede mu mata operation mu ciro babyn kawai if not akwai matsala Wallahy”
STORY CONTINUES BELOW
Captain adam yashare kukan dayake da tissue “dr bansaniba nima kawai kuyi mata abinda yadace pls dan Allah save my hafsat”
Takarda dr NAUFAAL yabashi yacike Sannan suka dunguma se labor room din,addua,kuka,magana shi kadai haka captain adam yadingayi,Allah me yadda yaso me bayarwa me hanawa me kashewa me rayawa,Allah ya albarkaci hafsat din adam da sunkuto santaleliyar ‘yarta ‘katuwa kyakkyawa Masha Allah exact copy din babanta ce sak wato captain adam sekuma sumar gashin mahaifiyarta data dakko wato hafsat,atake awajen captain adam yai sujjada ya godewa Allah ,amma hafsat haryanxu de she’s unconcious haihuwarma Allah yayine kawai se numfashi take da kyar’ga bleeding datake internally!
Dakyar dr NAUFAAL yashawo kan captain adam yarage kukan dayake,”captain pls kayiwa yarinyarnan duk abinda muslulunci yace ayi,matarka Kuma Insha Allah xamuyi yadda yadace danganin ceto rayuwarta ,Sannan Ina Kayan babyn?!”kamar Statue of Liberty haka captain adam yaxama da aka miko masa yarinyarsa ahankali Kyau de abin har ba’a magana!ko takan abinda dr NAUFAAL ya kecewa bebiba,dr NAUFAAL yaceda wata nurse dake gefensa”nurse dan Allah jeki waje akwai dayar wife dinsa awaje waiting area kice Ina Kayan baby?!”
Da axama nurse din tafita tsaye taga magajiya se zagaye take kafin tayi magana magajiyan tarigata”Yaya tamutu ko?!”
Nurse din taxaro ido”pardon?!mutuwa kuma?!ni Kayan babyn akace natambayeki”
Magajiya tai shiru “kina nufin bata…to babyn fa wai kina nufin…??”
Nurse dintai tsaki tai tafiyarta tana magana Ita kadai”ko mahaukaciya ce ne,Ana xancen baby meye kawo mutuwa Kuma mtscw”
gaba daya magajiya seta nemi tsayuwa tarasa kamar xata fadi,sekace tababbiya taje takawo haka tadinga YI”Kai bade hafsat ba Ita ai yanxu tadade da mutuwa”
Nurse nakomawa labor room din dr NAUFAAL yataho da sauri yana”Ina Kayan?!”
“Dr Wallahy nibanga wadda kake nufi ba,sewata acan din Ita Kuma kamar psycho I don’t think she’s normal”dr NAUFAAL yai tsaki sannan yakira wata nurse awaya kan “lalle takawo Kayan baby na mata yanxu”Sannan yakoma wajen hafsat din suka cigaba da Neman tsayar da internal bleeding din datake,
Captain adam yarike ‘yarsa wadda aka nannade ta a towel pink neatly se tsotsan thumb dinta take da pink lips dinta da alama yunwa takeji,rungumeta yai yana jin sonta akowane sassa najikinta tareda fadin”Allah yai maki albarka’UMMI_A’ISHA”
                     •
Welcome to the world baby UMMI_A’ISHA
       (THE MAGNIFICENT)
Rungumeta yai tsam ajikinsa yana fadin”Allah yamaki albarka UMMI_A’ISHA…muryar dr NAUFAAL ce ta katse masa albarkar dayake sawa tilon ‘diyar tasa,
“Captain mi’ko yarinyar xa’a samata kaya”
Mi’ka masa yarinyar yai yaneme sonta har cikin zuciarsa,,,,nurse hidaya itace tashirya baby UMMI_A’ISHA cikin over roll riga pink me kwalliyan lulu catty black,da hula tayi Kyau ‘das da ita se murmushi take tana ‘bangala ‘dan wawulan bakinta sosai tanada fara’a Kai kace babbace ake mata wasa take hakan,
Da temakon nurse hidaya Hafsat tai feeding baby UMMI_A’ISHA tanasha tai bacci dama yunwa takeji, a’dan karamin gadon babies dake gefe kusada hafst din aka ajiye UMMI_A’ISHA,hafsat tajuyar da kanta da kyar tana kallon ‘yar tata…
Dr NAUFAAL yakalli captain adam da ke gefen hafsat din azaune yana addua yana tofa mata ba bakin magana tunda hafst ‘din bata magana se hawaye kawai datake na azabar ciwo sunyi sunyi su tsaida bleeding din amma ya’ki tsayawa ta galabaita ba ka’dan ba shisa sukai mata allurar bacci don tasamu bedrest din da akeso mai haihuwa tayi”
STORY CONTINUES BELOW
“Captain kakira su gwaggo kuwa da side din Hafsat din?!”
“Wallahi bankiraba amma bari nakira su yanxu”mike wayai bayan yadanna kira yakira gwaggo mintina kalilan yasanar mata da halin da ake ciki,Sannan yakira mama ma yashaida mata,
“Yawwa captain sekuma Kayan sawan Ita Hafsat din seka tura adakko ko daganan Kuma Ina office Dina akwai takardar da danakeso kacike”
Fita captain adam yai zuwa waiting area inda yaga magajiya Ita kadai se safa da marwa take tanaganinsa tanufe shi hankalinta atashe kamar tsohuwar mahaukaciya,”yaya jaririyar?!”don duk axatonta hafsat din ta mutu
“Daga Ita har hafsat din sun samu bacci”murya narawa yake fadin”magajiya kokinsan meyasa hafsat tai wannan muguwar faduwar Xaki’iya recalling?!don tana cikin wani hali”
Hankalin magajiya seya Kara tashi najin tabbacin ai Hafsat din bata mutu ba,gaba daya meyakwan tabashi amsa ma neman guri tai tai maxauni a kujerun waiting area din tafara kuka,
Captain adam duk axatonsa yaxata don yace hafsat din nawani hali yasa take wannan kukan”addua xaki tayata da’ita magajiya kiyi hakuri dan Allah”sannan yamike yafuta daga sashen yana hawaye shima.. Yana fita parking lodge din yahango jirgi driver ‘daga masa hannu yai sanann jirgin yataso yaxo inda yake”oga gani”
“Gidah xakaje gurin haule kace taxo tadakko Kuma akwatin kayan dasuka shirya na haihuwa itada auntyn ta”
“To oga yanxu kuwa,tasauka lapia kenan Toh Allah ya albarkaci abinda aka samu”sanann yashiga mota ya tayar shikuma captain yakoma cikin asibitin…..!yana komawa mama taxo ita da tawagarta da food flask na abinci dakuma katon flask na shayi cikeda kunu,
Gaisawa sukai dasu maman se sunkuyar da Kai yake mama tace “nayi mamaki aini naxata se on 30th tacemin shine expected delivery date din(edd)to Allah me yarda yaso sekuma naji kace tahaihu bacci tasamu kenan”tana kallon hafsat din
“Ehh on 30th ‘din shine ainihin date din tokuma se santsi yakwashe ta,ta zume ta fa’di “
“Garin Yaya kenan?!wannan ai hatsarine inyazo da ‘karar kwana”
“Wallahy nafita ina waya kenan dawowar daxanyi hakan tafaru shima mukai gaggawar kawota asibitin “
“Toh Allah yarufa asiri amma ba cs aka mata ba ko?!”
Captain adam yasosa keyarsa yana sunkuyar da kai “bashi bane dashi din xasuyi mata dansuce tabu gu sosai toh sekuma Allah Yayi ta haihu daknta ma”
“Toh Allah ya albarkaci rayuwar abinda aka samu”Sannan takalli ‘yar tata yar autar su hafsat din (wadda ‘yar mamance da suke uba daya kenan)data dawo daga makarnata da take a amsterdam wato ikhram”ikram ajiye yarinyar nan tasamu tayi bacci tundaxu kike jagwalgwalata kinsan babies skin yadda yake very sensitive Dan Allah ajiyeta ta huta”
Ikhram ta ajiye baby UMMI_A’ISHA badan taso ba,sosai yarinyar tashiga ranta dukkoda bacci take ba idonta biyu ba”mama na ajiye ta babyn ce she’s so cute Kinga pink lips dinta,gata Kuma first niece dina inama Yaya mjay tana nan”
“TubarkAllah”cewar maman tana gyara wa babyn kwanciya,”ai gatanan setaita shan dauka ‘yar mummuna da ita”tana mata wasan kaka da jika,
“Uhm uhm mama wannan ai tafiki Kyau kishi de kike kar baba(mahaifinsu)yafi sonta akanki”
“Kintuno min dakika ce baba”Sannan takalli captain adam dake gefe a xaune”babansu yace yana dawowa daga tafiya shima xexo Kasan yaje General checkup a berlin”
“Ehh munyi waya dashi ‘daxu Allah yabashi lapia ameen”
Sundan jima suna hira da Maman har yan kaduna sukaxo dayake jirgi sukahau Kuma yan mintinan ka’danne,sosai aka shiga hira a nakuma jajantawa hafsat din abinda yafaru hade da murnar sunkuto yar kyakkyawa yarinyar ta datayi kowa yakalleta seya sake kallonta sosai baby UMMI_A’ISHA keda kyau ga farin jini se daukarta ake tunma baga yan Uwa ba har nurses na asibitin bangaren maternity,Banda magajiya dake gefe daka kalleta Kasan bakin ciki take dukkoda tadanne xuciarta ahankanma…!
STORY CONTINUES BELOW
Bayan captain adam yagaisa dasu gwaggo mikewayai yatafi office din dr NAUFAAL kamar yarda ya umarceshi dayaje din,knocking yai Sannan yashiga ciki hade da sallamarsa,dr NAUFAAL ya’ajiye files din dayake cikewa agefe tareda dago Kansa yakalli captain din waba lokaci daya yafita haiyacinsa kamar bashiba”have a sit mana captain”yanayi yana nuna masa kujeran gefe,xama captain adam din yai”gani Doctor Wallahy su mamane sukazo shiyasa seda na’dan tsaya muka gaysa”
“Ohh okay,captain pls kabani hankalinka nan wannan damuwar dakajefa kanka ciki bashi bane kalli kanka this is so not like you,har ka fada kamar Wanda ya wuni yana ciwo,worry not mana matarka Insha Allah xata samu lapia,abinda yasa nace dama kazo nafarko munaso mu’dan mata aiki ma’ana mu wanke mahaifarta kagade wannan faduwan datayi badan darabo ba Wallahy xata iya rasa ranta sosai tabugu ba kadan ba Kuma takasan mararta abin yake gashi Kasan kusan shekara ashirin ne so gurin yaxama very weak jini yana fita taciki Kuma duk internal abu yanada hatsari so xamuyi wankin after then semu dinke gurin dayahuje hakan yafaru ta sanadiyar akan abinda tafadi,seka dan sarara mata for some months.. aikanada wata matar dan dabaka da wata xance kaje Kai aure ma se gurin Yayi healing irin shine inbe warkeba haka ta faru ana samin matsala shine abinda xanfada”
“Tohh shikenan dr,Allah yabata lapia Ita Kuma Allah yarayata amma Ina mamakin yadda hakan tafaru coincidentally hakan tafaru naje waya kenan nadawo natadda da haka”
“Tohh Allah de yabata lapia shine kawai,ayau xamuyi mata komi first thing tomorrow morning kuxan fara sallama se weekly shot(allura)daxa’a dinga mata kawai Banda drugs saboda karyai affecting baby din”
“Shikenan dr,nagode Allah yasaka da alkhairi ameen”
“Ameen,haba captain Dan Allah kadena fadar haka ainine yakamata nadinga maka godia kullum,Banda abin arzikin dakake mana hadda wahalar biyan kudin Umara nida madam na harta dubai kuma gaskia  mungode wanann shine best suprise ever,madam dina Ma anjima xataxo Insha Allah nabarta tadanyi abu me ruwa ruwa takawo wa me jego,yanxu anjima xan rubuta maku abinda yakamata tadinga ci saboda health dinta,Allah yabata lapia “
“To mungode fa”
“Shikenan captain xaka iya komawa nasan a nacan ana nemanka “
“Kamar Kasan sace jikinai na fito,barinje”Sannan yabashi hannu SUKA tafa yafita,
Masha Allah aranar akaiwa Hafsat aiki successfully bawani matsala aka gama,washegari da safe aka sallamesu,akullum tana samun sauki sosai captain Adam yake bata kulawa ta musanman,bayan kwana bakwai aka cika layin da motoci na tents a ko’ina a layin ana raba abincin suna super ganishing dishes aka yi Wanda akai ordering musanman daga wurin meenah center,gidah yacika yai makil da mutane harda yan gayyar sodi ga yan unguwa saboda hafsat din mutuniyar kirki ce kome aka gayyaceta tana zuwa gashi batada wulakanci mutuniyar kirkice,hafsat tayi Kyau ba karya cikin shigar ta dabaxata kirguba tasa tacire tasa Kaya yafi a kirga ga kunshi da yalayalan kitson maiduguri style….
Suna Yayi suna Yayi armashi,Wanda mjay ce kawai bataxo sefata Skype suketa magana da ita tayi kiba tayi Kyau itama hafsat nata tsokanrta kode “itama  tanada unborn baby ne a makale a mararta?!”mjay tai daria tana fadin wai bakomai kawai de ni’mace irinta kasar waje dakuma kulawar mu’ayyad,amma tananan xuwa bada da’dewaba”
Anci ansha masu doubling sunyi,komai awadace tunda asubah da liman yasanar da sunan yarinya UMMI_A’ISHA aka fara sadaqa,se wurin 10 dare sunan ya tsaya Wanda akai a farfajiyar gidan dayake katoto ne xa’a faka mota sama da talatin dayake duk yasai filin kusa da gidan seya shigo dashi ciki, shanu biyu raguna uku aka yanka duk na sunan UMMI_A’ISHA,savouniers kala kala haka adinga bin mutane dashi da rubutu boldly a rabuce’welcome to the world baby ‘UMMI_A’ISHA’……!
__Sosai baby UMMI_A’ISHA ke ‘kara girma ‘bul’bul da ita kamar wadda ake bata wani abun lokacin datakai kwana arba’in kuwa kamar wadda tai wata uku saboda girman jikinta kowa sonta yake yana daukarta ‘yar gwanin sha’awa da ita ,inka cire iyayensa Capt Adam yanxu babu Wanda yafi so duk duniya irin baby UMMI_A’ISHA yanakiranta da(honey boo boo)’daki sosai aka gyara mata komi nacikin ‘dakin pink and purple kamar dakin ‘yar budurwa babu abinda babu aciki an tanadeshi inta girma dayake tanada garin jiki xatai saurin girma…!
STORY CONTINUES BELOW
Tana cika kwana arba’in sukaje kaduna sosai sun zaga dangi har hadejia sukaje suka gayda yan’uwansa na uwa dana uba tunda’yancan ‘dinne dukkansu iyayen nasa,bayan nan suka biyata yola suka yada xango a family house dinsu hafsat din dayake mahaifinsu asalinsa dan yola ne jimeta,aikine yakawo mahaifin nasu alhaji kasheem bn muhammad Kano inda yahadu da mahaifiyar tasu a Kano din marigayiya Hajia ameena,Wanda su yan kano ne yan cikin gari unguwar tudun wuzirci can kusada unguwar gwangwazo,ta rasu lokacin data zo haihuwar mjay inda daga baya aka bashi kanwarta hajia fareedah ya aura..daga yola suka dawo kano nan suka zazzagaya danginta sosai duk inda sukaje se captain adam yamasu abin arziki itama danata kyautar turamen atamfofi da sun’kin sabulai…!
Lokacin da UMMI_A’ISHA tacika wata biyu aka fara kaita gidansu hafsat din ana matso mama a feeder atafinmata dashi,ikhram ce ke yawon xuwa daukarta har hutunta yakare ta tafi,mjay ma taxo da nata ‘dan karamin cikin satinta biyu mu’ayyad yaita kiran awaya adole mama ta matsa mata tatafi…..!
     Ranar wata alhamis da safe lokacin captain adam yatafi abuja kai resignation letter dan yanxu yayanke decision din yai retire awurin aikinsa yabude wajen saida motoci da company sosai kuma yakeda share holders asauran oil and gas holders,zaune take adoguwar couch din dake gefen parlor din nata gefe daya Kuma haule ce zaune da UMMI_A’ISHA ahannunta tanata bu’de wawulan bakinta,
Knocking akai akofar parlor din,haule harta mike xata bude kofar hafsat tadakatar da ita”barshi haule xanbude ke aida yarinya a hannunki”bu’de kofar tai saikuma tai saurin komawa baya tana dafe ha’ba”kode gixo nai,kai banan bane batan kai kikayi”Sannan tasa hannu tana janye kofar kushigo ciki,
Matar da akacewa haka tai murmushi tana “babu wani batan kai ainafiki mutunci ma waye yazo gidannan last?!ni ce”
Hafsat tai daria “kede shigo kawai kinci albarkacin handsome boy ‘dinnan”tafada tana shafa kan ‘dan kyakkyawan yaron dabaxefi shekara 5 zuwa 6 ba,
Drinks da snacks aka kawo masu sannan haule tamike tatafi kitchen don kawo masu abinci,hajia fatee ‘kawar hafsat din tataso tadawo inda hafsat din take tasa hannu takarba UMMI_A’ISHA dake faman wangale mata baki”Masha Allahu tubarkAllah kyakkyawa da ita wallahi Allah yarayata yanzu tayi wata biyar ko?!”
“A’a fah watanta biyu da sati ‘daya”
“TubarkAllah kinsan dakika turomin pic ‘dinta a whatsapp duk axatona xatai 5months wallahy,Allah yarayamana ita”
“Ameen,ashe dagaske kike daki kacemin xakixo naxata iya shegen dakika sabane badan handsome boy dinnan ba aibaxan barki kishigo ba”
“To tuba nakeyi kaina bisa wuya,Wallahy balefina bane tunda mukabar zaman america muka dawo abuja wallahy babansu baya bari inzo garinnan gashide anan ya aureni ya gwanmace idan yara suka samu dogon hutu muxo Kuma bama wuce sati xuwa sati biyu,amma Kuma ninaxo karshe”
Hafsat tai daria”fatee kenan Banda abinki shekara nawa rabonki da nan ‘din?!dan inaga tunkan asan da cikin wannan handsome boy ‘din”
“Gaskia anyi shekaru aide gani nazo,gashinan dan auta”tanayi tana kallon ‘dan nata”zo MUHANNAD kaga kyakkyawar baby,yanasan baby yace mama yaushe xaki bamu baby muma?!”
“Gaskiane gwara ki haifo masa kanwa shima,sunan wa’aka samai ne?!wanann dukyafisu kyauma kode mucanje akai a asibiti?!”ta kyalkyale da daria,
“Haka ake cewa waiyafini Kyau dagani har uban,dama bakisan MUHANNAD ba?!gaskia mundade bamu haduba,sunan baban mahaifinsu akasa mai IBRAHEEM KHALEELULLAH amma se ake cemasa ‘MUHANNAD’ gashinan shekararsa shida fa yana primary one”
Tasowa MUHANNAD ‘din yai yaje inda maman tasa take yasa hannu yana Shafa kan baby UMMI_A’ISHA,”mama yasunanta?!”
“Sunanta UMMI_A’ISHA”
“Mutafi da ita mama”
“Rufamin asiri MUHANNAD,kafin kasa akawo bataliyar ‘yan sanda suka mamu,kana sonta ne mekyau da ita ko?!”
MUHAMNAD yai nodding kansa,
Hafsat tai daria “xataxo maku Insha Allah kafin kutafi batada rigima,kusan kullum agidanmu take wuni”
Haka sukaita hira sukaci abinci Sannan sukai mata sallama xasu tafi,biscuits da sweets da chocolates dayawa Hafsat tabawa MUHANNAD,suma Kuma sunkawo katuwar Leda cikeda kayan jarirai na mata harda turmin atamfa,se bayan isha’i Sannan suka tafi bayan Hafsat tayiwa MUHANNAD alkawarin har gida xata kawo masa UMMI A’ISHA,dakyar yayarda yatafi waishi sesun tafi da ita,
Satin captain adam biyu yadawo dga abuja straight part din Hafsat yanufa dayake haryanxu xaman nasa da magajiya yananan yadda yake se abinda ya’karu ma,yana sallama ya’dauka UMMI_A’ISHA dake kicking ‘kafafuwanta tana tsotsan hannunta,dagatayai sama yana mata wasa “honey boo boo I missed you sosai,se magana yake mata kamar wadda takejinsa kema kinyi missing baffa uhm?!”
Hafsat ce tafito daga daki tana waige waige,ganin UMMI_A’ISHA datai a hannun captain yatabbatar mata shiya ‘dauke ta don taajiyeta kan gadonta se tashiga bandaki tawanko fuskarta tadawo Kuma batagantaba taxatama ko kukatake haule ta dauketa don bandakin can cikin corridor yake a gefen dakin,
Sannu daxuwa ta masa Sannan suka gaysa,sundan jima suna hira Sannan ya bukaci takawo masa abinci”Hayatee a’bangaren magajiya kake fa kada mushiga hakkinta kaga ba da’di”
“My hafsat kiyi abinda nace maki kawai nibaxanci abincin waccan matarba”
Batai musu ba don bata sabayi masa musun ba,takawo masa komi yaci yakoshi,da daddare ma haka yadage anan ze kwana anan seda Hafsat tai masa wa’azi meshiga ciki tareda tsoratarwar irin azabar da Allah xe masa dakuma kalamai masu dadi,haka captain adam yahakura yatashi yatafi don amatse yake sosai,
Haka kuwa akai,komai ya wakana tsakanin captain adam da magajiya ,wadda kamar ansata a aljanna don da’di,da safe hardasu kiran magajiya Sannan tayi farfesun kaji tabayar akaiwa masu gadi sukansu sunyi mamaki kwarai matuka don ‘kwayar shinkafa daya bata taba basuba sefa yau’din,shide captain adam yayine kawai dankada yashiga cikin wani hali tunda yakasance mabu’kaci,
Haka lokaci ya’danja kamar wata ‘daya kenan,sosai yanxu auratayya take shiga tskaninsa da magajiya dukkoda yanayi ne donbabu yadda xeyi ‘din tinda Hafsat din babu dama,muna_b da magajiya sunshigo sunfita tahaka suka fara janyo hankalin captain adam yafara karkata xuwaga magajiya din,abin tunbaya damun Hafsat harya fara damunta dukkoda ko ka’dan soyayyar dayakewa baby UMMI_A’ISHA Dede da kwayar zarra bata raguba,
Da safe Hafsat tashrya xata tafi asibiti tayi mamaki kwarai datacewa captain adam xata asibiti yace jirgi yakaita don hakan bata taba faruwa ba,haka tashrya taje akai mata weekly shot,sannan nurse hidaya tace”Maman UMMI_A’ISHA akwai abinda yake daminkine don naji jikinki zafi?!”
Nan Hafsat tafa’da mata yadda takeji,bp dinta tagwada”Kai,bp dinki Yayi high Maman UMMI_A’ISHA,kirage damuwa gaskia karkijanyowa kanki stroke,Allah ya kiyaye amin….!””Amiin”abinda Hafsat ta iya fa’da kenan,sanann taiwa nurse hidaya sallama tatafi,ba gidah tawuce ba gidansu tawuce yiwa abbansu sallama dayake xasu koma berlin na tsawon shekara biyu don lapiar sa,
Tana zuwa tashiga ciki masu aiki suka fara haba haba da ita kamr yadda suka saba Sannan suka amshi baby UMMI_A’ISHA itade shiga cikin parlor dintai abban nasu da maman xaune suke suna kallon news atashar aljazeerah,bakinta ‘dauke da sallama tashiga ciki,
+
Neman wuri tai taxauna agefensu bayan sun amsa sallamar”abba barkada rana ya ‘karfin jikin?!”
“Alhmdlh Nana”(yadda yake cewa da ita kenan)”jiki da sauki sosai,ya mutan gidan?!”
“Sunanan qalau abba,suna gaisheku ma”
“Masha Allahu”
Juyawatai da kanta ‘bangaren maman”mama barkada safiya,ya me jiki”
“Lapia qlau hafsatu,jiki Alhmdlh,Ina Kuma UMMI_A’ISHA?!”
“Ina shigowa kenan su farila sukakarbeta anan balcony”
“Ayyo nide ince bagida de kika barta ba”
Itade hafsat murmushi kawai tai,
Sun’dan taba hira sanann farila me aiki tadawo da UMMI_A’ISHA wacce ke sunkufe cikin over roll white and orange ga hulan sanyi ga over roll sweater ansa mata tayi kyau abinta ,tuni abba yasa hannu ya karbeta yana mata wasa,bayan yagama yatashi yatafi masallaci Ita Kuma mama takarbeta tacigaba da yi mata rawa,Sannan tabawa Hafsat Ita ta kwantar da ita a kan kujera tinda har bacci yadauketa,Maman taga dukyanayin hafsat ‘din gashinan gashi nan ne”lapiar kikuwa hafsatu?!naga kamar bakya cikin hayyacinki wani abunne yafaru keda abokiyar zaman takine?!!”
“Babu komai mama kaina ke ciwo”haka hafsatun take dede da rana ‘daya bata ta’ba Kai ‘korafi gidah ba shekara ashirin kenan,dama Kuma haka akeso mace takasance bata maida gidansu gurin yaji dakai ‘karar mijintaba,
“Toh shikenan Allah yasawwake,akwai wasu addu’oi da matar sadeeq tabani xandakko makisu inxaki tafi ..kidaure kidinga yi insha Allahu koma menene Allah xekawo karshensa,
“Allah yasa,nagode mama”
Haka sukaita hirarsu har abban nasu yadawo aka sake bude shafin xumunta,sosai shima yashiga yi mata nasihar da jajirtattun iyaye keyiwa ‘ya’yansu,
Sallama tamasu cikeda kewar iyayen nata daxatai natsahon shekaru tinda adaren ranar xasu tafi ‘kasar berlin, takoma gidah jirgi na parking tatafi part ‘dinta….dama captain adam awurinta yake ranar kwana biyu biyun dayake masu taxagayo kanta…
Tuwon semo vita miyar karkashi tayimasa da zo’bo wanda yaji kayan kamshi se fruit salad dakuma soup na kayan ciki,shigatai bandaki tayo wankanta cikin shigar doguwar riga maroon ta material ‘dinkin Senegalese tayi kyau abinta, light makeup tayi shiru ba alamarsa,se wajen tara da rabi yashigo ciki abinda ‘betaba yiba,
Tararsa tayi kamar yadda tasaba,ignoring dinta yai tahanyar karbar baby UMMI_A’ISHA,yana mata wasa jiki sanyaye hafsat takoma baya tana wasa da yatsun hannunta ko kadan beso yake mata hakan ba yarasa meyasa wannan abin yake faruwa dashi tsakaninsa da hafsat ,da addua da komi yasamu yaci abincin data dafa Sannan yashiga ‘daki kafa’darsa dauke da baby UMMI_A’ISHA!
Bandakin dake cikin parlor din tashiga tayo alwala sanann ta ziri hijabi tafara nafulfuli tana mekaiwa Allah kukanta ha’de dayin adduar da Maman tabata,Allah meyadda yaso kafin sati biyu tacika seda hankalin captain adam yadawo jikinsa har kuka yaiwa Hafsat dinsa nadaga abinda yake mata tayafe masa, nuna masa tai aibabu komai ba lefinsa bane tinda bahaka yake ba ba halinsa bane,
STORY CONTINUES BELOW
‘A karshen satinne Kuma magajiya tatashi da matsinancin zazzabi asibiti captain ya sa jirgi yakaita awun farko yanuna tanada ciki positively gashinan arubuce ,tabbas captain adam yaji da’di saboda ‘ya’ya rahamane shida yake nema gashi Allah yabashi yakuma sake bashi,Wayyo zokuga gwalli da gwatsarewa tuni magajiya tadinga tsurfa kala kala dukkoda captain adam din yanayi matane saboda kawai darajr dansa ko ‘yarsa dake cikinta,
Babu wanda besan tanada ciki ba lungu da sa’ko na yan uwa duk sedata fada masu gashi Kuma ba haihuwar fari bace ballanatana ace,tunda ‘Dayan gidan data fito tanada gartsetsen gardin ‘danta baki wuluk kamar ita,,,,abinci se Wanda ta zaba cikin da ko wata daya bekaiba se zuzuta shi take,tuni takira muna_b tasheda mata yadda ake ci,washegari da safe muna_b taiwa gidan asubanci bayan sungaysa sunyi komi muna_b ke fadin”yanxu yaya captain ‘dinnaki da hafsat din?!”
“Oho ‘canta matse mashi,nide tinda nasamu ciki aishikenan dama haka maxan suke?!”
“Haba kawata kmar Wanda kikai auren farko ,barin Gaya maki hadisin maxa,yana daya daga cikin shika shiken maxa,Kinga namiji kamar gurjiya yake se an kasa akansan na kwarai,hmm ‘kawata namiji kamar hankaka yake gabansa fari bayansa ba’ki…nifa Allah natuba bande yi auren ba amma babu namijin daxe ‘boyen halinsa..kede tunda kinyi ciki Alhmdlh sekin cika gidannan da ya’yan ki yanxu Ita banzar tasan kinada shine?!”
“Nasan yafa’da mata mana aibaya boye mata sirrinsa”
“To ai bahaka tabarshiba,kede bari namana wani sabon catch na boka ance aikinsa kamar yankan wu’ka inde kinada farcen susa bakida damuwa,xan jonaki gareshi”
“Yawwa kawas shiyasa Kike da’da shiga raina kullum”
Haka sukaita hira muna_b nabawa magajiya miyagun shawarwari tana ‘dauka,se wajajen ‘karfe hudu na yamma Sannan tai mata sallama tatafi kanzata dawo nanbada da’dewa ba….
Kodah captain adam yasanarwa hafsat magajiya nada ciki tanuna murna kwarai tareda fatan Allah yasauketa lapia,har cikin zuciarsa yaji dadin kalaman da Hafsat din tafada!
‘Kwanci tashi ba wuya awurin Allah UMMI_A’ISHA nada shekara ‘daya da wata daya a duniya magajiya ta haifo ‘yarta ‘Baka Kirin kamar bayan tukunya ko kusa baxakace captain Adam ne mahaifinta ba,ba lefi yan Uwa suntaru sosai ,ranar suna raguna biyu da saniya daya captain Adam ya yanka amma magajiya tai kicin kicin tasa dole yakama mata fabs event center tunda boka yamata abinda kome tatambayeshi seya bata..akai hadadden suna kamar dinner ‘yar gata su kansu su surayya basuji da’din kashin kudin da yayan nasu keyiwa magajiyan ba musanmn yanxu data Juya masu baya kamar basune sukai sanadin auren ba,yarinya taci suna ‘KHADIJA’magajiya ta’dau son duniya ta’dorawa baby KHADIJA,ba lefi captain adam yanasan yarinyar tunda jininsace amma Gaskia yafison UMMI_A’ISHA…!
Baby UMMI_A’ISHA yanxu tana tafiya abinta ko’ina tana ammi wai hafsat dintake kira se bapa(Baffa)yar gwanin sha’awa da ita ga Kyau ga gashi Kuma doguwace kamar tayi shekara uku aduniya tubarkAllah!
UMMI_A’ISHA nada shekara ‘daya da wata uku,hafsat tayayeta dayake tanada saurin girma ga garin jiki,asibiti taje don kwanakin nan batajin da’din jikinta,karo sukaci da magajiya abakin balcony din dake farfajiyar gidan magajiyan tawani yatsine fuska kamar taga kashi hannunta rike da KHADIJA ‘yarta”to kekuma wannan saurin dakike haka Ina xuwa?!nide Nida ‘diyarta kurwarmu kur”Sannan ta tsirtarda yawu akasa ta wuce,
Itade hafsat ko cikanki batace mata ba danyadda takejin jikinta koda dukanta tai baxata mata komi ba,saboda inka raina kasuwa ma ko sautu baxaka bayarba,asibiti tawuce jirgi yakaita tasamu dr NAUFAAL kuwa,gwaje gwajensa yai Sannan ya girgixa Kansa,hafsat damuwa karara a fuskarta take tambayrsa”dr akwai matsalane?!”
“Babu matsala”haka kawai yace da Ita a takaice,waya yakira captain kanlalle yaxo asibiti yanxu ,ba’adau lokaci ba kuwayaxo,inda dr yasheda masa hafsat nadauke da ciki amma yakoma bayan mahaifa yai sauri yasa hannu atakarda donsuyi mata aiki su cire inba hakaba komai xe iya faruwa,gabadaya captain adam a rikice yake se zufa ke ketomai,operation room suka nufa da Ita andau lokaci dr NAUFAAL yafito yana xare safar hannunsa,
STORY CONTINUES BELOW
Captain adam yatafi inda yake”yaya ake ciki dr?!”duk ya ki’dime
Dr NAUFAAL ya girgixa Kansa gaba daya jikinsa Yayi sanyi”captain munyi bakin kokarinmu amma Allah yayiwa……
•✨•✨•✨•✨•✨•
Dr NAUFAAL ya girgixa Kansa captain munyi bakin ‘kokarinmu Allah yayiwa abinda ke cikinta ‘karar kwana dukkoda bekai haihuwarsa ba amma ya’dan girma bayadda  xamuyi mun cire shi”
Captain adam ya girgixa kansa”dr kafa’damin gaskiya saboda daga ganinka nasan hafsat ta rasu” yashiga kuka ba ‘kakkautawa,
Dr NAUFAAL yai murmushi Kawai hade dasa hannu yaja kafa’dar captain adam su shiga cikin office ‘dinsa,harkan kujera ya xaunar dashi Sannan yakoma tasa kujerar yaxauna yaha’de hannuwansa,
“Captain kata’ba ganin anyi wasa da mutuwane?!sannan matan dake cikin operation room sunada yawa Wanda duk nine da temakon nurses mukeyin aikin saboda sauran doc ‘din basanan,ayanxu haka mata masu ciki Wanda xasu haihu ma su uku ne suka rasa rayukansu agaban idona ta ‘karshen data rasu ita jaririyar ta rayu kaji abinda yasa jikina yai sanyi kenan”
Captain ya tsaida kukan dayake Se ajiyar zuciya Kuma”yanxu xan iya ganin my hafst?!”
“Bari agama shryata tukun saboda ta jigata har wankin ciki akai mata nasa nurse ta mata allurar bacci daxan fito harta fara baccin ma itada baby UMMI_A’ISHA”
Captain adam yamike tsaye “kana nufin da UMMI_A’ISHA akai komai kenan?!”
“Abayan nurse hidaya take har aka gama komi,Sannan Hafsat din ta umarceta tabata Ita ta shayar da Ita to hakade sukai baccin tare,nanda awa daya xaka iya shiga bedrest mukeso tasamu dama”
Haka dr NAUFAAL yadinga kwantar mai da hankali harde awar tacika sannan captain adam yamike yashiga ‘dakin da aka Kai hafsat din kwance take idonta biyu da alama ta farka tanawa UMMI_A’ISHA wasa dake kan ruwan cikinta azaune,
Bakinsa ‘dauke da sallama yatura ‘kofar yashiga,sallamar hafsat din ta amsa,UMMI A’ISHA najin maganar baffanta tafara murna tana Neman sakkowa daga kan gadon,da sauri ya’karasa yasa hannu yadauketa Se dadi takeji “‘ammatan baffa yakike?!”itade se murna take tana tafa hannuwanta tana bapa(baffa)seda yagama mata wasa kafin yaxauna kusa da hafsat din yana kallon fuskarta dukta rame kamar ba Ita ba,”ya jiki my hafsat?!”
“Da sauki hayatee”
“Allah yakara sauki mekikeson ci yanxu insiyo maki?!”
“Banajin yunwa bakina ba apatite”
“Dole kici abinci ai my hafsat kalla yadda kika rame”
Itade hafsat shiru tai tana kallon baby UMMI_A’ISHA,
“Ina magana my hafsat”
“Shikenan hayatee asiyo yoghurt ma ya isheni”
Mikewa yai bayan yabata peck akumatu Sannan ya’dau UMMI_A’ISHA “bari muje mudawo xansa jirgi yakawo maki haule”
“Allah yadawo daku lapia ameen”
Futa yai daga ‘dakin itakuma tajuya ta kwanta gaba daya jikinta ba ‘dadi,siririn hawayene yake tsiyayowa daga idonta Wanda tarasa na menene,addua tacigaba dayi acikin zuciyarta har bacci ya’dauketa…
Sallamar da haule tai shiyasata sa hannu tai saurin goge hawayen datake,”Aunty yajikin naki?!”
“Da sauki haule”
“Allah yakara sauki ameen”
“Ameen”
Ba’awani jima ba captain adam yadawo da ledoji fal a hannunsa daya ,dayan Kuma UMMI A’ISHA ce ri’ke akafa’darsa hartayi bacci ,kwantar da ita yayi agefen gadon sannan yaciro wani pack da ‘katuwar robar yoghurt ta L&Z,komawayai ta bangaren da Hafsat din take ya’dagota tareda sa mata pillow ta baya ta jingina,wanko hannunsa yai a bandaki haka yadinga ‘dura mata roasted chicken soup ‘din dakuma yoghurt batai musu ba don bata saba yi masu musun ba harta ‘koshi Sannan ta goce xata kwanta yai saurin dakatar da Ita “my hafsat kakki kwanta yanxu,kibari abincin yai digesting inba hakaba xaki samu stomach upset”
STORY CONTINUES BELOW
Gyara xamanta tai akan gadon bata kwantaba tanata kallon ‘yarta dake bacci peacefully abinta,captain adam ya mi’ke yashiga bandaki yawanko hannunsa sanann yadawo da roba da hand wash ahannunsa yatemakawa hafsat tawanke hannunta sannan yasa yatsansa cikin bakinta ya goge mata ha’koranta ha’de da zaro tissue yagoge mata baki Sannan yakoma bandaki yamayar “my hafsat bari naje wajen dr NAUFAAL”
“Okay hayatee take care”
Fita yai yatafi consulting room ‘din da dr NAUFAAL yake,yaxauna sun’dan ta’ba hira Sannan captain adam yace”nikwa dr meyasa cikin my hafsat yaxube ko domestic issues na gidane yamata yawa?!”
Dr NAUFAAL yai murmushi “no not at all kasan lokacin datai wannan buguwan ta bugu sosai har mahaifan yaxama so weak shiysa data samu cikin seya koma bayan mahaifa Kuma hakan yanada hatsari gashi Kasan da akwai wannan ciwon haryanxu saboda haka Se ahankali don seda muka sake healing dinshi saboda ruwa yake fitarwa”
“To yanxu meya kamata ayi ko waje xanfitar da ita?!”
“dukde abin ‘dayane de Insha Allah xata samu sauki xamu ‘dorata akan magani”
“Allah yasa dr,godia nake”
“Yanzu xan rubuta mata magani,xaku iya tafiya ma tinda jikin nata da sau’ki”
“To shikenan Allah yasaka da alkhairi”
“Yawwa amma Dan Allah KO Yaya taji sauyi ajikinta akawo ta asibiti pls”
“Insha Allah hakan xa’ai”
Sallama sukaiwa juna Sannan captain adam yakoma wajen hafsat ‘dinsa lokacin har baby UMMI_A’ISHA tafarka hafsat din na bata cereal,basu wani da’de ba aka sallamesu suka tafi gidah,
Tunda suka koma gidah tsahon sati biyu kenan hafsat ta warware ga kulawa datake samu na musanman nadaga wajen captain adam ‘dinta ,UMMI_A’ISHA nacika shekara biyu cif aka yayeta ko ince tayaye kanta surutu babu kama hannun yaro ko’ina yawo take acikin gidannan babu sunan Wanda bata ‘kokarin fa’da kaf gidan,Wutar ‘Kinta kuwa kullum ruruwa take a zuciyar magajiya,musanman dataga UMMI A’ISHA din tafi ‘yarta KHADIJA Kyau nesa ba kusa ba,
Kullum magajiya tana tatse captain adam kullum
Bani kaxa bani kaxa bashida bakin yace baxan bayarba tunda ankulle bakin,yanzu dukiyarsa cikin kashi ‘Dari tadawo kashi hamsin,ranar wata lahadi suna xaune a babban parlor ‘din gidan na captain adam ,xaune yake shida hafsat ‘dinsa cinyarsa kuwa UMMI A’ISHA rike da biro se zane take ‘kokarinyi a sketch book ‘dinta,
Magajiya tai sallama tashigo tana zuwa ta’dora KHADIJA a’dayan gefen cinyar Capt adam ‘din,fuskar yarinyar tayi fari ‘kal kamar me bleaching Se ‘kyalli take,Capt adam yabude baki”magajiya meyasamu yarinyar nan kalli yarda fuskarta tai fari ta’dashe ko batada lapia ne?!”
“Lapiar ta kalau lefi ne idan Fuskarta tayi fari bayan babanta farinne?!”
Captain adam yai daria Sannan yasa hannu a fuskar KHADIJAn aikwa ya lakuto foundation powder me ‘maiko,ya ware Ido yana kallon magajiyan”menene wannan kika sa mata?!”
Magajiya tai dubi dubi se xare ido take kamar mujiya tana in’ina”i..inaga bansaniba ta..tasaka”
“Mtscew”captain Adam yaja tsaki tareda mikewa yaba kowacce ‘yarta”‘riketa Kuma kije kigoge mata koma menene kika sa mata,da fari da ‘bakin duk Allah ne yayisu kada kisaka jahilci mana”
Sannan yafice fuuuu,magajiya da borin kunya ta isheta wucewa part ‘dinta kawai tayi don kunya,
A ‘bangaren hafsat captain adam din yake,kamar kullum part ‘din yasha gyara se kamshi turare ke tashi dana abinci,sede dauriya kawai take yau ‘din duk jikinta ba’dadi tarasa meyake mata da’di aduniya,sosai sukaci abincin ranar tare har nadare ma tare sukaci Sannan suka shiga ‘daki kwance suke akan gado suna kallon news da ake rantsar da donald trumph,gaba daya hafsat ‘din hankalinta baya wurinta captain adam yasa hannunsa cikin nata yana murxawa “my hafsat laifi nayine yau ake basar dani?!”
STORY CONTINUES BELOW
Hafsat tai murmushi sanann tajuya da kanta tana facing ‘dinsa tasa hannu daya tana Shafa cyboc ‘dinsa”ko’daya hayatee ni na Isa na basar da rayuwata?!kada Allah yakawo wannan ranar”
“To fada’min meke daminki?!”
Hafsat ta sauke nauyayyiyar ajiyar zuciya tana kallonshi”Hayatee Dan Allah kayafemin abinda namaka dunia da lahira”
Captain adam yasauka kasa down on his kneels yana kallon hafsat dinsa dake hawaye shima hawayen yafara”meya kawo xancen haka my Hafsat ?!sanin kankine Wallahy baki ta’ba min abinda xan ri’ke ki azuciataba kisani idanma kinyi Wallahy bansanshiba bayan Ma bakiyinba dawanda xaki yi nangaba da Wanda kike shirinyi duk nayafe maki dunia da lahira nima kiyafeni”
“Nagode hayatee Allah yabarmin Kai,dan Allah inaso arike min UMMI_A’ISHA tsakani da Allah abata ilimi both islama dana boko”
“Wai my Hafsat meya kawo wannan xancen kamar mebani will ‘dinta”rungumeta yai tsam ajikinsa yana hawaye gaba ‘daya jikinsa Yayi sanyi yarasa meyasa…
Kukan da UMMI A’ISHA take agefe shiya dawo dasu daga abinda sukeyi hafsat tasa hannu tadakko ta tana kallonta,,,”Ammi”abinda UMMI AISHA tace kenan tana kallon mahaifiyar tata,
“Na’am UMMI A’ISHA”
Tashi UMMI A’ISHA tai akan gadon ta ‘karasa inda hafsat ‘din take takwanta akan cinyarta ,hafsat tasa hannu ta rungumeta,,,daren ranar ahaka sukai bacci kowa da abinda yake sa’kawa azuciarsa….
Washegari da safe magajiya ta kira captain adam a waya kan tanaso taje kaduna takai xiyara be mata musu ba yace Allah yadawo lapia tagaishesu,
Da wuri magajiya ta gama shirinta jirgi driver yajata se kaduna hanyar unguwarsu yadosa magajiya dake hakimce a owners corner tai saurin dakatar dashi”bagida xamuyi ba tukun xan karba sa’ko a unguwar locust”
“to hajia”abinda jirgi yace kenan sannan yai reverse ya juya kan mota se locust area unguwarsu muna_b…
Yana zuwa yai parking akofar gidan ita kuma tashiga ciki,gidane flat ya amsa sunansa dan ko unguwarma masu farcen susa ne ke zama cikinta, ita ka’daice aciki dan iyayenta na garin maiduguri karatu ne yakawota kadunan daga nan kuma ta hadu da kawayen bnza suka gurbata mata tarbiyya harde idonta ya bude daga karshede ta ba’dawa idonta kasa taki komawa garin nasu,tabiyewa miyagun kawaye tafara halin banxa kwata kwata ba aure agabanta taguji iyayenta shekara da shekaru sunyi neman harsun godewa Allah. ..
   Tana shiga tai sallama muna_b na kwance tana danna waya”wa alykm salam”tadago kanta ganin magajiya ce yasa tasaki ihun dadi taje ta rungumeta “kawas ashe zakizo? walhy naxata wasa kike”
“habade zanzo mana akwai labari de ko?!”
“mezafi kuwa”
Neman guri magajiya tai taxauna tareda kwantar da KHADIJA agefe dake shararar bacci”inajinki kawas bani nasha”
“da frko de yaya wajen hafsatun akwai wani latest a kasa?!”
“rannan ‘dahare ke bugun cikin haule ai tace wai hafsat din ciki aka cire mata”
Muna-b ta kece da daria “lalle aikinsa yna kyau Kenan”
Magajiya ta ware ido tana kallon muna_b”kawata kina nufin shirinki ne Wannan?”sekuma ta kyalkyale da daria…
“Kwarai kuwa kawas,ai naki jinin kishiyar ki kaman mutuwata”
“kibari kawai aibanki intashi inji ance ba ita a duniyar ba natsani nabude ido naganta a doron duniya shiyasa banasan zaman kanon gaba daya ma”
STORY CONTINUES BELOW
“to albishirinki boka yabada choice ki xabu daya nafarko ko abaki abu kisamata a abinci taci baxata shura ba awajen xata mutu nabiyu kuma ko a haukatar da ita tashiga duniya gaba daya a mata kurciya adenajin ta a duniya gaba daya,wanne kika dauka?baxa’a cika sati ba aiki zeci”
Magajiya tai shiru tana tunani can ta nisa”ina ganin a haukatar da ita tashiga dunia shiyafi don kinga a Iya samin wani yamurje mata kai akan titi ta mutu kinga hakan yafi ai..Amma ta mutu ina wani wahala anan kilama tacika da imani kingakwa bama fatan hakan ta samu koya kikace?”
Muna_b ta kece da daria”wannan zabi naki haka yake barin tashi nadakko maki sakon”
Tashi tai ta tashiga daki tadakko wata leda tadorawa magajiyan akan cinya”gashinan kisan yadda zaki kisa mata ko a abinci,abinsha ko acikin Man kitso dinta ko turaren shafawarta”
“wai Allah yakawo yadda xa’ai amma babu matsala”
“kada ki wasa dashi ki tabbatr kinyi,Allah yabarki dagake se adam dinki”
“Ameen kede bari kawai,to wani hanzari ba gudu ba ita kuma UMMI A’ISHA fa yaxa muyi da ita?!”
“wannan kuma senan gaba semuyi shawarar yadda xa’ayi”
Magajiya Sun da’de suna hira da muna_b kafin tai mata sallama tatafi gidansu,kwananta biyu kullum tana zuwa wajen gwaggo su gaysa a ranr daxata tafi ma da safe tatafi gidansu gwaggo tamata sallama kamar kullum gwaggon na parlour tanajan tasbaha, magajiya tai sallama tashiga bayan sungaysa Sun dan taba hira magajiyan tace”gwaggo zantafi kada nayi dare a hanya”
“to shikenan magajiya Allah yakaiku gida lpia gashinan nono da fura kidau jarka daya kiba hafsatun daya kifinma haka gashinan kusada daddawa anan gefe”gwaggon tafa’da taname nuna mata kayan da hannu
“to shikenan gwaggo Allah yasaka da alkhairi”
Tana fitowa dga gidan gwaggo Suka biya gidan muna-b inda tace mata xata Iya zubawa acikin nonon koda captain din yashama babu abinda xefaru tunda da sunan hafsat din akai komi atake awurin tajuye kullin maganin duka acikin nonon tagirgixa  sallama taiwa muna_b sannan jirgi yaja se kano ta dabo tunbin giwa….
Akwana atashi bawuya wurin Allah kwanan magajiya biyar da komawa kano hafsat taji tana marmarin nono lokacin fitar captain adam kenan daga gidan tatsiyayoshi a cup UMMI AISHA tataho da gudu ta fa’da jikin uwar “ammi dan ta momo”
Hafsat tai murmushi tasa hannu tana shafa kan UMMI AISHA “ba lemo bane UMMI AISHA,kuma da sanyi dana baki jeki wajen haule tana kitchen tabaki”
Haka hafsat ta kafa kai ta shanye nonon tass ta ajiye kofin,sihiri ba karya ba tuni hafsat taxube akan kujera tana dafe kai can ta mike idonta yakada yayi ja tasa hannu xata cire hijabin jikinta takasa wata razananniyar kara tasaki tafice agidan da gudu lokacin su hannafi suna sallah a kofar gidan…
Fitowar haule da UMMI AISHA kenan daga kitchen ba alamar hafsat, haule tashiga dubata amma bata ko’ina gakuma wayarta akan kujera tabarta,bangaren magajiya haulen tanufa bayan tayi sallama tadan tsugunna magajiyan nakwance tana kallo”hajia,aunty muke nema bamu gantaba naxata ko taxo nan”
“bade nanba gaskiya bataxoba kila ba nisa tyi ba”
Jiki sanyaye haule tamike tafita ita kuma magajiya tashiga cikin daki tadinga daria tana kyakyatawa”ohh hafsatu anxama mahaukaciya kenan”waya tajanyo takira muna b tafada mata yadda ake ciki,
Shiru har dare ba alamar hafsat haka UMMI AISHA tagama kukan rashin ganinta tai bacci,koda captain adam yadawo yasamu labarin da ake ciki fitayai nemanta amma shiru kakeji,har radio channels da stations na police duk an fada…..
Washegari ma haka abu har tsahon sati biyu captain adam ya rame yayi baki hakama UMMI AISHA kullum cikin kiran “amminta”take.
Lokuta Sun shude rayuwa taja batan hafsat wata daya kenan captain adam yatattara yakoma kaduna da xama kamar yadda magajiya tabashi shawara kuma yana yawon mafarkin hafsat din da gizo datake yawon yi masa kullum se an sauke mata qur’ani….
     Hakika ba’tan hafsat yagirgixa yan uwa hr izuwa kan yan unguwa,mjay kullum setayi kukn hakan har Kano taxo na sati biyu amma shiru haka ta hakura takoma akarshen shekaranne Allah yayiwa abbansu Hafsat din rasuwa dangi ysake rudewa musanman inka waiga kaga duk an hadu ba hafsat din ..
Mama itace ke ri’kon UMMI AISHA yanzu,bayan shekara biyar lokacin UMMI AISHA nada shekaru bakwai aduniya gwaggo tce lalle captain yadawo da ita nan kaduna wajen yan uwanta,hakan kuwa akai aranar yaje yadakkota da kansa tagirma sosai farace ga tsaho ga gashi,har suka iso kaduna tana bacci yadauketa a kafada yashigar da ita cikin gida magajiya na hakimce akujera se KHADIJA dake kwance kan cinyarta yana shigowa magajiya tabude baki”wacece Wannan din?!”
Be bata amsaba kansa tsaye yashiga wani ‘daki da alama don yaran akatanadeshi gadajene guda biyu aciki pink da purple yakwantar da ita akan purple din ya lulluba mata bargo yafuce daga dakin…komawayai parlor din yadauki remote yana canxa channels yakalli KHADIJA dake faman danna wayar magajiyan”ke tashi kishiga daki ki kwanta gobe monday akwai school ga yar uwarki can gobe xa’ai admitting dinta itama”
Tashi tai tana zumburar baki tatafi daki,tunda ya ambaci yar uwarta magajiya tagane UMMI AISHA yake nufi, itama  din mikewa tai tatafi daki batabi takansaba,tabe bakinsa yai yacigaba da kallon dayake….
Washegari da safe bayan sungama breakfast sunayi magajiya najefa mata harara hakama KHADIJA,captain adam da kansa yakaisu makarantar Wanda dama Khadija anan din take. Uncle bado shine sunan makarantar ,straight Khadija tatafi ajinsu sukuma suka tafi office din principal,successfully tai passing exams dinta akasata a pri 3 ajinsu Khadija dukkoda ita tsallake akai mata hr kofar ajin captain adam yarakata yana in antashi xexo yadaukesu,principal din mesuna uncle David shiya shigar da ita har cikin ajin lokacin English teacher ce a cikin ajin ,ganin UMMI AISHA da Khadija tai duk se ranta ya baci dayake tadakko halin uwarta,sosai principal yai introducing UMMI AISHA yan ajin se sonta sukeyi,sit dinta two sit intevals ne tsakaninsu da Khadija,aunty Helen ta tambayi quetion ajin yai tsit basusan amsa ba dukkoda kunya UMMI AISHA keji hakan be Hanata daga hannunta ba,
     Sosai Aunty Helen taji dadi “silence class, okay UMMI AISHA I’m all ears go ahead”abinda aunty Helen tace da ita kenan……..!
Gaba daya ran KHADIJA ya’baci musanman dayake Ita bata taba answering questions a class ba batada ko’kari,sosai UMMI AISHA tabada amsa ajin akahau tafi,aunty helen taita yabonta,har aka tashi kowane teacher yashigo class din se UMMI AISHA ta amsa questions,gaba daya ran KHADIJA ya ba’ci musanman dataga malaman suna yabon UMMI AISHA agaban captain adam din,suna xuwa gidah ya ajiyesu shikuma ya juya kan mota yafita ,a ‘darare UMMI AISHA tashiga cikin gidan,ganin tundaga bakin kofa KHADIJA tafara kuka tasan makirci xata kulla mata awajen magajiyan…
Ko Yaya labarin hafsat?!!!!
                 •✨•KHADIJA nashiga ta fara wurgi da school bag ‘dinta tana buga kafarta a kasa tana kuka,magijyan ta taho da sauri”menene Khadija wani abin aka maki a school?!”
“ummah ba UMMI AISHA bace take ta ko’Kari a class yau Wannan aunty helen ‘din bakiga yadda take sontaba itada sauran teachers har baffa suka fadawa wai ita tanada kokari”
+
“kan bala’i ina UMMI AISHA din take yanzu?!”
“Tana waje……”bata karasa fadaba magajiya ta mike tana huci tai hanyar waje nan tagano UMMI AISHA arakube ajikin kofar shiga parlour din ta hada gumi da alama atsorace take….
“zonan dan ubanki”abunda magajiya tace kenan tareda sa hannu tajanyota..”shegia dangin mayu dama ainasan angama jikawa anbaki kinsha xakici na jaki kuwa yau agidannan me rabani dake se Allah”
“Dan Allah ummah kiyi hakuri”
“umman uwarki,kar in sake jin kin kirani da ummah niba mahaifiyar ki bace kinajina?!”
“ehhh naji”UMMI AISHA tafa’da a tsorace,
Rankwashi takai mata har sau hudu akanta”shanye kukan nan dan ubanki kika bari hawaye yaxubo sena laka’da maki na jaki”
Bayadda UMMI AISHA ta iya haka tashanye hawayen dake ko’karin zubowa daga idonta,”mtsceew”magajiya taja tsaki tareda jan hannunta bata direta ko’ina ba se dakinta tashiga bude wardrobe dinta tana ciro inner wears dinta da manyan towels”gashinan ki wanke su tass kishiga cikin bandaki kada ki xubar da ruwa akasa wanki uku dauraya uku zakiyi”
“tohmm”abinda UMMI AISHA tace kenan sannan ta debi kayan takai bandaki tadade tana kallon inner wears din wanda suka kunshi tulin braziers,panties,under Wears da towels na wanka Wanda itade Iya saninta aunty ikhram tagani tana sasu sannan ita take wanke abinta da kanta towels din kuma a washing machine taga ake sawa,hasalima bata taba wanki da kanta ba su farila ke mata ..
Tana hawaye sha’be sha’be haka tadinga wankesu sedatai sa’bi uku dauraya uku ta shanya a hanger data gani a bandakin,sannan takoma parlor xaune magajiyan take da Khadija a gefe dakeshan corn flakes..
  “nagama wankin”
Se asannan magajiya ta’dago takalleta a wulakance”kin tabbatar sun wanku kuwa?! dan idan naduba naga basu fitaba sena ci miki mutunci agidannan”
Muryar UMMI AISHA narawa take fadin”Allah sun wanku”
  “shikenan tashi kije”magajiyan tace da ita,jiki asanyaye UMMI AISHA ta mike tatafi daki tana hawaye ga kukan yunwa da cikinta keyi rabonta da abinci tun nasafe don ko a school bataciba ta tsaya tana revising class work din da aka basu,bandaki tashiga tayo alwala kamar yadda akeyi sannan tai sallah baxaka taba cewa yar shekara bakwai ce tanutsu take sallah hakan ba….
        
Bayan ta idar da sallah kenan captain adam baffansu yadawo,duk suna parlor yaga babu ita kuma shiru bata fito ba”magajiya ina UMMI AISHA?! “
                 •✨•
                    35
  “nan muke da ita suna bani labarin school tace yau tayi kokari sosai inaga bandaki tashiga”
“barin kirita baffa”abinda Khadija tace kenan sannan tashiga dakin nasu”ke kizo inji baffa,saura kuma kice ummah tadakeki”
   Itade UMMI AISHA batace komiba illa bin bayanta datai suka fita parlour din…
Capt Adam naganinta yafara washe baki”xo yammatan baffa,yar albarka”
Da sauri UMMI AISHA tanufi inda yake tana murmushi”kinci abinci?! “kafin tabada amsa magajiya tarigata”catai se xuwa anjima”capt adam yawatsa magajiya mugun kallo sannan yasake duban UMMI AISHA akaro na biyu”xakici yanxu?!”
STORY CONTINUES BELOW
“zanci Baffa”
Haka Capt adam yaxuba masu shida ita spoon by spoon tadinga ci seda takusan tashi da rabin abincin sannan tadawo ci ahankali seda yaga takoshi sannan yabata ruwa tasha yadauraye mata bakinta, wasu hawayene ke neman zubomai yai saurin maidasu musanman dayaga tafara juyewa kama da Hafsat dinsa, dakyar yadaure yajawo leda agefansa yaciro school uniform set biyu da school bag da Socks guda biyu da takalmi guda biyu da textbooks dakuma notebooks da sauran abubuwa su pen da mathset yamikawa UMMI AISHA”gashi jeki ajiye adaki seki fara amfani dasu gobe in Allah yakymu”
   “to baffa nagode”sannan ta mike tatafi daki ta ajiye..
Magajiya tacika tai fam kamar ta fashe”baffa nimatextbook dina na ugo c ugo ya bata”
“bade wanda nasiyo maki shi shekaran jia ba?!”
“Allah Baffa sacewa akai a ajinmu”
Capt adam yagigrixa kansa yana Kallon magajiya”wannan duk lefin kine,saboda allah yarinyar nan kullum batada adani littafinnan nasiya mata yafi akirga,kwata kwata batada adani,yau littafinta ya bata gobe mathset dinta ya bata kullum kuma yan ajinsu ke sacewa saboda ita kadai suka tsana kenan?!safa kuwa kullum semun tsaya a shago ansiya sannan tasaka tashiga cikin makaranta,haka zata tashi ba adani kenan?!tun yanxu awannen shekarun idan baki koya mata tattali ba wallahy haka zata tashi”
“to yaya kakeson ayi kenan?!yarinyar nan tace ansace aibaxatai karya ba ko?!ansace ‘dinne”
“okay hka zakice?!to shikenan wallahi baxan siya ba”mikewa yai yatashi yashiga cikin dakinsa be tsaya jin mexata ce ba,
Sa hannu tai ta rungumo yar tata meyakwan tamata Fada batayinba sema hakuri datake bata”yi hakuri yar gatan ummanta,kyale baffa nixan siya maki kinji?!”
   Shiyasa khadijan tatashi asangarce ga rashin kunya da tsiwa….
                     •KATSINA
___dattijawan matane su biyu zaune suke akujerun da suka amsa sunan royal chairs,kayan alatu ne cike agabansu acikn wani tray hira suke abinsu hankali kwance dayar daga ciki wadda da alama itace taxiyarci dayar tace “hajia barira nikwa ina yar aikin nan naki take me kirki?!”
“ohh firdausi kike nufi tana kitchen sarkin aiki”
“nace ki aramin ita na sati biyu takoya wasu amal girki kinki”
“bahaka bane inajin dadin xamanta agidannanne amma xataxo maki insha Allah”
“to ko xa’asa momin wata kamar ita dn Allah”
“naga yamaki itama labrinta yanada tsaho,kinsan gidan yaya Yakumbo tai aiki harna tsahon shekaru biyu daxata koma jos shine tabarmin ita”
“okay haka itace wadda kikace kamar an gusar mata da hankali ko?!”
“kwarai kuwa ko sunan da ake kiranta dashi firdausi  yaya Yakumbo ce tasaka mata”
“tamanta komai nata kenan?!”
“kwarai kuwa,bari ma inkirata ku gaysa”sannan tadan daga murya tana fadin”firdausi”
                    •✨•
•✨•✨•✨•✨•✨•
Da sauri ta’karaso wajen ta tsugunna tagaisheda da aminiyar aunty bariran wato hajia hajja,murmushi fa’da’de a fuskar hajia hajja ta amsa mata gaisuwar tareda doriyar”inata cigiyarki ai”
“ina kitchen ne hajia”
“ohh ayyah,to shikenan ki koma aiba yanxu xan tafi ba”
“to hajia”sannan ta mike ta koma bakin aikinta a kitchen…
STORY CONTINUES BELOW
Hajia hajja ta cire tagumin data zabga”mutum yaji tsoron duniya,dan Allah me Wannan baiwar Allahn tayi xa’ai mata Wannan mummunar sakayyar?!”
“kibar mutum kawai,ai wasu mutanen Sun dauka babu hisabi,wallahy hajia hajja nikaina seda nazubar wa da baiwar Allahn nan hawaye”
“shekaru kusan uku ko?!”
“hudu de,kinga labarin nata me tsawo ne fa,farko ai kawu haruna ne yakadeta a mota can hanyar katsina yace kawai tafiya take bata kallon gabanta yanata mata horn duk abanza gashi yakasa tsayar da motar,nande yakadeta though bataji wani rauniba yakaita asibiti aka bata magani,bata magana bata komi shine seyatafi da ita gidansa dake funtua akaita yi mata magani da sauka inda wani malami yace ai kurciya akai mata tashiga dunia tareda sihirin gusar da hankalinta”
“wayyo Wannan mata tashiga halin tsaka me wuya”hajia hajja tafadi hakan tareda girgiza kanta alamar tausayi ..
“wallahi ina gaya maki akaita mata magani wallahi,yadikko gaji matar Kawu harunan tace bayan kamar wata daya da hakan da safe setaji tanace mata ina kwana?!,tace setace mata yasunanki?!wallahi yadikko tace setace min wallahy bansaniba  atakaice duk tambayar dasukai mata bata saniba tamance komai nata”
“Allah sarki baiwar Allah”
“wallahi shine suka gayawa wanda yake mata rokon Allahn yace ai agodewa Allah ma da abu yazo da sauki,don mugun sihiri akai mata tashiga dunia takuma zamto Me gusar hankali abin kyama cikin mutane,saboda haka se ahnkali tunaninta ze dawo jikinta komin daren da dewa,shekararta daya agidan kawun bayan rasuwar kawun se rikonta yadawo hannun yaya Yakumbo dake funtua inda take kiranta da firdausi shekararsu biyu tare ita kuma kinsan mijinta aikin Bank yakeyi kullum cikin chanza garuruwa Sukeyi ashekara biyun ne akai posting mijinta jos shine fa tabarmin ita haryau de muna adduar tunanin ta yadawo don mumai da ita gida shekaru biyar kenan nasan yan uwanta sunacan suna nemanta baiwar Allah, Allah de yakawo karshen koma menene amiin”
Hajia hajja tagoge hawayen dayake tsiyaya daga idonta”Allah yasakawa baiwar Allahn nan,kowaye yai mata Wannan abu bekyau taba, ubangiji Allah yaimana katangar karfe da makiyanmu amiin”
“Ameen ya rabbi,makiyinka babu
Abinda baxeyiba dan ganin yayaye maka farin cikin rayuwarka,rayuwar yanzu se du’ai kullum nai sujjada sena mata addua Allah ya karya sihirinnan yahada baiwar Allahn nan da yan uwanta nasan sunacan sunyi neman sungaji wasuma sun fitar da rai”
“insha Allah nima zan tayata”
_______koda hafsat(firdausi kamar yadda ake kiranta yanzu)takoma kitchen neman waje tai tazauna akan kujera hade da tabe habarta tana hawayen dabata san na menene ba,
‘kaurin kamawar tuwon data keyi shiyadawo da ita daga tunanin datake wanda batasan na menene ba,sauri tai takashe gas din takwashe taxuba a foodflask taware nasu na yan aiki sannan tadebi nata tatafi daki,bayan taci takoshi lokacin hajia hajja ta leko sukai sallama har gate hafsan tarakata sannan tadawo daki takwanta dayake dare yayi, karfe daya da rabi tafarka tafara nafilfilinta kamar yadda tasaba ……!
                  •KADUNA
              •✨•
               37
Da sassafe UMMI_A’ISHA tatashi tashiga bandaki tai wanka tayo alwala tafito tai sallar asubah raka’a biyu,gefen gadon Khadija taje dake shararar bacci tadan daddaki gefen pillow dinta”khadija kitashi karmuyi late a school”
Meyakwan Khadija tatashi sema gyara kwanciya datai tacigaba da baccinta haka UMMI AISHA tacigabada da tashinta amma duk a banxa hakura tayi tasa uniform dinta da socks dinta sannan ta rataya school bag dinta tafita parlor taxauna,dede lokacin da magajiya tafito daga daki tana hamma ware ido tai tana kallon UMMI AISHA datai kyau cikin uniform dinta ga kitson shuku biyu yayi dass kamar zanashi akai dukse bakin ciki yatararwa magajiyan tahade rai tana jefa mata harara kotakan gaisuwar datake mata bata biba musanman data duba parlor din babu Khadija babu alamarta”ke ina Khadija?!”
STORY CONTINUES BELOW
“inata tashinta taki tashi”abinda UMMI AISHA tafada kenan muryarta se rawa take. .
“karya kike,muguwa wato ke kin shrya ita kuma bata shrya ba in baffanku yafito yayi mata fada kenan ko?!to zoki koma cikin dakin seta gama shryawa tukun ‘karamar yarinyarki dake se mugun hali”‘kwas takai mata rankwashi akai”shige muje”tana nuna mata daki”kuma kika kuskura hawaye yazubo wallahy senamaki lilis agidannan”
Dakin suka shiga tare,itade UMMI AISHA neman waje tai taxauna akan stool, magajiya tasha fama kafin tatashi Khadija dake faman bacci har abandaki sekace wadda xa’a sake mata dare….dakyar tashiryata kayan uniform dinma kowanne dakyar aka hadashi hijab akan gado,skirt akan mudubi rigar da tie kuwa cikin drawer suke hade da kayan wanki masu datti dama safa ba’a maganarta kullum sabuwa ake siya,
Parlor suka fito lokacin har captain adam yafito daga daki yana parlor din yanashan Coffee,gaysheshi sukayi ya amsa cikin fara’a”ya akai kukaso kuyi latti yau?”
Caraf Khadija ta Cafe”baffa ba UMMI AISHA bace tundaxu nake jiranta tashrya se bacci takeyi dakyar ummah tatasheta”
UMMI AISHA tai shiru tana tunanin karyar da Khadija tayi mata kamar ba itace ke jiranta tun daxun ba,muryar bafface tasa tadena mamakin datake”shikenan yawuce kuxo Kuci abinci nai dropping dinku school”
Abincin sukaci sannan suka tafi school,koda suka dawo da aka basu assgnnt Khadija bata iya ba UMMI AISHA tace taxo takoya mata taki,tagwan mace aunty Helen tai purnishing kota kwafi na frnds dinta ….
Kwanci taci bawuya awurin Allah,su UMMI AISHA sungama primary school dinsu inda duk wani awards seda taci kuma ita taci best student of the year akabata scholarship a one of the best school a kaduna wato ‘danbo’
Khadija bataci komiba dan da ana bada award akan wadda tafi kowa dakikanci to xa’abawa khadijan magajiya,haka magajiya ta kafa kahon zuka da naci da magiya da sihiri dakomi magajiya tashawo kan Capt adam yayarda yabiyawa Khadijan danbo din itama,
Alokacin UMMI AISHA nada shekaru goma ita kuma Khadija nada tara,kyau,ilimi,tarbiyya,biyayya,ibada awajen UMMI AISHA ba’a magana,aranar baffansu yakarbo masu uniform wanda ita UMMI AISHA kyautane har books da komi duk under scholarship ne ita kuma Khadija duk seda aka siya mata …..
Shekara uku kenan da komawar UMMI AISHA kaduna amma bata tab’a fadawa capt adam tsangwamar da muguntar da magajiya keyi mata ba,ranar monday suka fara xuwa school din aranr UMMI AISHA tai kawa wata me hankali kuwa sunanta WALIYYA,bayan antashi daga school suka koma gida da wata mota a fake jeep jikin Khadija se rawa yake dama gata da son maxa me aikinsu delu itace ke wanke wanke a gefen babban kitchen din dake waje Khadija tamatsa kusa da ita tana Bin motar da kallo”delu suwaye sukazo?! “
“ya’yan baffa sameer ne”
“ARFAAN KO MUS’AB?!”
“ARFA…”delu bata karasa fada ba Khadija tashige cikin gidan da gudu don ba karamin sonsa takeba kankanuwar ta da ita,shi abinma daria yake bashi dukkoda shidinma yaro ne baxe wuce shekara goma sha bakwai aduniya ba..
UMMI AISHA dake gefe sanda Khadija tafadi haka tai murmushi kawai itama tashiga cikin gidan,tasa hannu kenan xata bude kofar taji muryar ARFAAN ‘din yana fadin “to ina kuma UMMI AISHA?!!!!”
‘Karasa tura kofar tai tashiga ciki, ARFAAN yajuyar da kansa dan ganin waye,magajiya harda murmushinta kamar gaske”ai gata ma wadda ake nema,ARFAAN ke tambayanki maza zokici abinci kicire uniform kije ki wanka sekuma islamiyya,baki bude UMMI AISHA ke kallon magajiyan da tsananin mamaki atattare da ita. 
Basarwa kawai itama tayi sannan ta karasa kusada ARFAAN din dake aika mata da sakon murmushi har kasa ta tsugunna tana gaisheshi “yaya ARFAAN ina yini?!”
STORY CONTINUES BELOW
“Lapia qalau UMMI AISHA ya studies!!”
“Lapia qalau”
“Masha Allah,kuje kuci abincin ya fada yana kallon khadija data maida hankali kan game din datake a wayarsa”sannan yasa hannu yakarba wayar tasa……
Magajiya dake gefe tace”nikwa ARFAAN next yr xakaje university ko?!”.
ARFAAN yai daria”aunty nashiga  level one hundred fa anan umyuk”
“Habade?!lalle girman dan mutum ba wuya to mus’ab ne xeshiga nxtyr kenan?!”
“Ehh shise nextyr da nima se next yr din Greece suka bani admission,to kumade se baffa yace kawai naje umyuk din tunda dama nayi jamb kuma naci point dina yakai,shine se naje can umyuk din ina studying mechanical engineering”
“Ai gwara hakan dakai ta zama,toh Allah yatemaka ameen”
“Ameen”
ARFAAN yadan da’de anan din harse bayan isha’i sannan ya masu sallama yatafi yaso ganin UMMI AISHA kafin yatafi amma babu dama saboda tana gama homework dinta tai bacci…
•KATSINA
Hafsat tareda sauran masu aiki suketa aiki a kitchen din da alama ba’ki zasuyi….Hajia barira matar gidan ita tashigo cikin kitchen din tana ‘dan duba abin da xa’a kara da Wanda xa’arage sannan ta karasa kusada hafsat dake faman soya snacks da hada coleslow…
“Firdausi sannu kinji kitashi kije ki huta se innar wasila tacan jeki”bayan tasa hannu takarba robar da coleslaw din ke cike aciki….
Hafsat ta mike tana karkade zaninta”to aunty barinje,amma aiba wani aiki bne Wannan yanxu xan karasa”
“Kide je kihuta firdausi inde su ASHRAF ne sekin gaji da tsurfarsu”
Hafsat batai musu ba ta mike tatafi dakinsu da aka tanadar masu..
Bayan sun kammala komi suka koma daki suna hutawa dama su uku ne dattijawan masu aiki hafsat da jummai me wanke wanke se inna me ‘ya wasila haka ‘yar karama baxata wuce shekara uku a duniya ba shine akece da ita innar wasila…
Kamar kullum suna xaune a farfajiyar dakinsu,wasila diyar inna dake kwance akan gado tafara kuka tatashi daga bacci
Da axama hafsat tasa hannu tadauketa don tana matukar son yarinyar har magudanar jininta take sonta innar wasilan dake gefe tai murmushi”firdausi kidena daukar katuwar yarinyar nan kina dorata akan cinyarki”
Hafsat tai murmushi kawai tana shafa kan wasilan tana mata wasa”xakici abinci?!”
“Andima danci”tafada ahausarsu ta yarinta….
               •✨•
                39
 
Ita de hafsat tana son yrinyar sosai inkuma tadauketa setaji kamar diyarta,kwakwalwarta tafara charge tafara tunanin da kanta yafara ciwo”menene firdausi?!”abinda innar wasila tace da ita kenan….
“Babu komai inna kawaide narasa meyake damuna ne kwanakin nan sena dingajin wani iri,kuma kullum sena dinga mafarkai wasu iri”
“Kamar yaya kenan banganeba?!”
“Kamar muna zaune tareda wasu da bansan suba kuma muna hira,inaji ajikina kamar jini nanesu,amma bansaniba ko sharrin mafarkine tunda nide nasan banida kowa se Allah seku”
Innar wasila tai shiru sekuma tai ajiyar zuciya tanemewa Allah godia acikin zuciarta tunda tasan abinda yasamu da abokiyar aikin tata wadda ko satin daya wuce malamin dake was hafsat din rokon Allah seda yace da yardar Allah tunaninta xedawo ahankali……
STORY CONTINUES BELOW
“Ba sharrin mafarki bane firdausi kede kici gabada addua kawai”
“Banganeba innar wasila”
  
   ____muryar jummai abokiyar aikinsu ita takatse musu maganar dasukeyi”Hajia tace kuzo su ASHRAF sun karaso”
“Toh gamunan” suka fada atare ,maganar da basu’kara saba kenan suka tashi suka tafi parlor inda Hajia bariran take da wasu kyawawan yara guda biyu mace da namiji…..
“Yawwa”abinda hajia bariran tace kenan tana kallon yaran nata oya kutsugunna ku gaishesu dama kunsan inna da hajia jummai Wannan kuma tasa hannu tana nuna Hafsat”sunanta aunty firdausi”
Hafsat tai murmushi tana kallon yaran data kejin sonsu,da gudu yarinyar tatafi ta rungume hafsat din tana ta’ba jelar gashin hafsat din data fito ta bayan dankwali tana tabawa tana kallon maman nata”mama kinga gashinta kamar na barbie doll”
Hafsat tai daria”yaya sunanki?!”
“Sunana ayush,ga yaya nacan sunanshi ASHRAF”tafada tana nuna ASHRAF din dake zaune yanata durawa cikinsa chocolate….
“Ohh ni barira”Hajia bariran tafada tana dafe ha’ba”Ayush yaushe zaki dena shirmene?! Bari abbanku yazo ummah ta shagwaba ku dayawa”
Hafsat tabi yadda suka ‘bata parlor din da kayan ledar chocolates da sauran tarkace duk sun zubar,…
   Sun danyi hira sannan Hajia bariran tasallamesu suka koma dakinsu bayan sunyi sallah ne su jummai da inna suna maganar marassa ji sunzo aiki xeyi doubling hafsat tai shiru tana mamakin to ya’yan waye?!
“Nikwa inna su ASHRAF dinnan ya’yan waye?!,ni nakasa ganewa”
“Ya’yan hajian ne to abokiyar zamanta bata haihuwa shine farko seta fara bata ASHRAF lokacin yana shekara biyar to bayannan seta kara haihuwar ayush itama bayan ta yayeta seta barwa kishiyar,tunda kinga ita bata taba haihuwa ba ita kuma hajian ya’yanta takwas mata uku sunyi aure harda ya’yansu aikin sansuma se maza uku biyu sunyi aure dayan kuma bana xa’ai nasa shima se laila dake karo karatu a turai,se su ASHRAF din”
“Amma ta kyauta kam,kuma anan katsinan take itama?!”
“A’a ita tana kano,a can suke ita dinma tana zuwa nandin tai Hutu lokaci lokaci itama hajian tana zuwa,suna zaman lapia da mutunta juna yaranne de basaji ko miskala zarratan ansha canxa mashi aji a makaranta”
“Tabbas naga yadda sukai kaca kaca da parlor ma dazu”
“Haka suke wallaby,barin ASHRAF din miskili ne sosai shi magana fa inba wani sabawa kukaiba ko cikin yan uwansa bayi yakeba,gashi duk yafisu kyau kamarsa daban”
“Sosai kuwa tubarkALLAH,Allah yarayasu amiin”
   Haka sukaita hirarsu har dare yaja sannan sukai addua suka kwanta……
#teamARFAAN
#teamASHRAF
#teamMUHANNAD….
••
___WANENE ALHAJI KABEERU KAMILU KANKIYA?!
Alhaji kabeeru kamilu kankiya babban dan kasuwane agarin nakatsina sanannene sosai yana da company din motoci nasiyarwa dakuma oil and gas shares ba’anan yatsaya kadai ba babban ‘kusa ne a gwamnati inda shine director general na depence, shine babba agidansu basuda yan uba mahaifiyarsu ita kadaice wajen mahaifinsu shine namiji babba se kannensa mata su uku kawai…….
Alhaji kabeeru yanada mata biyu,matarsa ta farko Hajia barira wadda Allah ya albarkacesu da ya’ya har takwas,inda biyu daga ciki mace daya namiji daya tabarwa kishiyar tata hajia aishatu wadda sunanta ne akasawa ayush autar hajia bariran,ita hajia ayshatun bata haihuwa…ita a kano takeda zama daga daya daga cikin gidajen alhaji kabeerun dake unguwar Lamido crescent,tana zaune tareda ya’yan kishiyar data rikesu kmn nata wato ayush dakuma ASHRAF…….zamane sukeyinsa cikin karamci da mutunta juna,suna ziyartar mahaifiyar tasu duk sanda suka damu dogon Hutu!!!!!!
STORY CONTINUES BELOW
  Haka rayuwa taja lokuta suka shu’de,bangaren hafsat tana samin sauki sosai ba laifi,tunda hartana tuno tanada diya mace UMMI_A’ISHA dakuma mijinta captain abinda ta’iya tunanowa kenan sefa kanwarta datake yawon anbata wato mjay dakuma mahaifinsu Wanda bata iya fadin sunanshi,tabbas cikin kashi ‘Dari na sihirin da ake mata kaso saba’in babushi ciki abin se godiar Allah Kuma Hajia barira da Ma maigidanta sunji dadi kwarai dagaske Kuma sunyi alkawarin inde takara samin lapia xasu nemi duk inda danginta suke adoron duniya sukaita…,
Bangaren UMMI A’ISHA Ma abin ba sauki,samari tun tana jss classes suke binta ballantana yanxu datake ss2,Masha Allahu ta Kara Kyau,fara ce farinta mekyau ne me daukar ido,Sannan tanada tsahonta Dede misali,jikinta ma moderate ne tanada yalwataccen gashin gira da Kuma sumar gashi harta zubo tagefen fuskarta taxama kamar saje,ga ido dara dara,Masha Allahu UMMI A’ISHA batada wata makusa wai ance dan adam Tara yake becika goma ba to itade UMMI A’ISHA tacika taranta cif,
Tun farkon shigarsu ss2 da suka samu wani dogon Hutu bayan sunje gidan gwaggo wadda yanxu ta manyanta sunyi mata hutu sunje gidan Yaya sameer shima sunyi masa hutu,sekuma sukaje hadejia danginsu captain sameer nanma sukayi hutu,bayan sundawo ne captain adam yake cemata yakamata suje zaria danginsu magajiyan na uba suwunar masu suma tunda basu taba xuwa ba,
Shiri sukayi nazuwa kaduna,KHADIJA wadda yanzu sunanta yakoma BABY KAY,babu Wanda besantaba a school dinsu inde harkar ya’yan masu kudi ce to tana ciki,duk wata latest waya data fito to se magajiya tasaya mata,tana daya daga cikin Wanda aka sani a kaduna Wanda sukai forming Union wato ‘richest babes of kaduna’babu Wanda be san baby kay ba,’yar karya ce ta ajin karshe…sun shirya cikin manyan Kaya ko wannen su,magajiya tayi shiga cikin tsadadden lace din French lace Ita Kuma baby kay tasaka atamfar super holland dinkin ya amshi jikinta dukkoda bawani kyan jikine da ita ba seta yafa yalolan mayafi kalar kayan shidinma tasa Kane saboda baffansu karyai mata fada,saka mayafi babu shi acikin agenda dinta,UMMI A’ISHA tasa atamfarta mekyau itama super holland purple da torches black setasaka wadataccen mayafinta baki tai rolling dashi…
Zungureriyar mota kirar sienna Ita tajasu zuwa garin na Zaria,tunda asalin magajiyan dama ba zazzagiya ce,se daure fuska take tamau Ita adole kar a renata,dakyar sukai parking a layin daya sha jar kasa kaikace karkarace kodayake a zarian ma a outskirt dinta suke,dede wani gida ginin kasa suka tsaya Wanda seda sukai tambaya dakyar suka samu gidan dayake magajiyan ba zumunci ne da su ba,Iri dayane gidajen amma kowa da kofarsa,
Kawunsu ta hango wato kawu tanimu se faman asuwakhi yake da hakoransa da suka rine suka koma ja saboda cin goro,baby Kay se buya take a bayan uwar kamar wadda xa’a saceta,captain adam ya bude kofa yafito yasamu waje akan tabarmar dayaga kawun yake dashida wasu matasa da alama yaran sane,ya samu waje yaxauna ya mika masu hannu suka gaisa daya daga cikin yaran Kawu tanimu yace”kamar magajiyan kawun birni ce ko da mijinta ?!”yaname nuna magajiya da hannu data dora fuska tamau kmar bata taba daria ba!!!
Captain Adam yai murmushi”ehh mune”
Yakalli magajiyan dake yatsina fuska ga baby Kay a gefe datake masu kallon banxa se UMMI AISHA dake rakube ajikin dakalin kofar gidan”tohh saiku shiga daga ciki gurin matan ko”
Ran magajiya be so ba haka suka shiga cikin gidan ta tsaya a tsakar gidan tai jim tarasa wacce kofar zasu shiga domin ita babu wadda xata iya ganewa ciki duk kuwa da cewa sunje bikinta ammafa sunga wulaknci wajen yan uwanta da muna_b don duk wani aiki sede kaji ana akira mutan zaria gashi kuma babu wani kyakkyawan magana tsakaninsu ko gurin kwana ma dakin me aiki suke kwana duk kuwa dacewa dangin ubanta ne amma sundau kesu a wulakance,sunmanta cewa ko cikin rashi anasamin damar samu Wanda Allah keda ikon hakan….
Suna nan tsaye UMMI AISHA tanemi gefen wani bokiti daya tsage tazauna don baxata iya tsaiwarba,Banda baby Kay data makale kunnuwanta dana’uwar nan wato ear piece se kida ketashi,magajiya tai shiru tana naxarin tawanne kofa xasu shiga ciki tunda duk kawunnannata ciki suke Kuma gashi babu Wanda xata iya ganewa acikin gidan koda sukaje bikinta Ma basu samu ganinta ba saidai su hango ta daga nesa,
STORY CONTINUES BELOW
                     •✨•
                       41
“Ummah nifa I’m damn sick of this place,haba mana ummah ga wani gutter atsakar gidan Kuma kinsan ni I’m allergic to all sort of this”baby kay ce tafadi hakan tana mewa magajiyan nuni da kwatar dake tsakiyar gidan cike da kayan gwa’bi gwa’bi
Magajiya tabude baki xatai magana taji motsin yara sun shigo da gudu cikin gidan ganinsu yasa yaran suka tsaya suna kallonsu wani yaro me dan tsaho daga cikinsu yasa hannu yana nuna UMMI AISHA”Laaa ga India taxo gidanmu”
Sauran yaran dabasu gantaba hancinsu fal cikeda tasono da majina suka zuro kai suna zungurin yaran dayaga UMMI AISHA”habu tana ina indian,!”suka fadi hakan suname kokawar ganin UMMI AISHA dake aika masu da sa’kon murmushinta me dauke hankalin duk Wanda yai tozali da ita,baby kay ta juyar da fuskarta tana me toshe hancinta tana kallon magajiyan”ewwwww ummah I can’t stand th….”bata karasaba ji kake tumbul kwata a watse waje sai fuskar baby Kay,kwatar Ita ta raba hanyar shiga gidan lokacin data zo tsallakewa kenan wai tana kyaman kwatar har tana mamakin ta Yaya mutum xaici abinci agidan nan ai itakam amai xatayi segashi shegun yaran nan ya’yan talakawa sun watsa mata kwatar a fuskarta batasan lokacin data xube a wajen tafara kuka ba takaici goma da ashirin dama Ita ba san xuwannan takeba,gashi nan ai abinda ummanta tajanyo mata,yaran kuwa mai zasuyi inbanda ihu,
“Ta Kamo kifi,soyayye,ni da su’din kwano soyayye,ni da siyo manja”da karfi sukeyi har saida Maman daya daga ciki ta jiyo hayaniyar tayi yawa ta fito ta leka me yake faruwa?!sai taga magajiya da diyarta dakuma wata balarabiyar yarinya,da alama diyar kishiyartace..sekuma diyar magajiyan jikinta duk kwata yara suna mata ihu da saurinta matar ta iso gurinsu ta kori yaran sannan ta kama hannun baby Kay dake tuttujewa tana zunduma ihu kamar wadda akaiwa rasuwa,matar wadda da alama tana daya daga cikin matan kawunnen magajiyan tashiga dasu bangarenta tana”lale da xuwanku sekuma kannenki suka watsa maki kwata Kiyi hakuri kinsan yaranmu na kauye yanzu haka garin kallonkune kunsan basu saba ganin yan gayu ba shyasa”
Itade baby Kay aranta catake wadannan kalaman yaran Wallhy ba kannenta bane,hanci fal majina kayansu ayage kaman almajirai itakam gaskiya ba kannenta bane…dakyar baby Kay tayadda ta tsaya atsakar gidan ta wanke jikinta ,matar tayi tayi takai mata ruwa bayan gida ta wanke jikinta taki,haka ta damalmala kayanta koma ta xauna se kumbura take Kamn funkaso,
Fitsari ne ya matsi magajiya ba shiri ta mi’ke tana xare ido”akwai bandaki mekyau fitsari nakeji”
“Ehh bari akai maki ruwa yanxu aka deboshi na dam ne”
Magajiya ta rataye mayafinta a kofar dakin Sannan tashiga cikin bandakin dake tsakr gidan,ware Ido tayi ganin shaddar a bude ga kashi nan yana mata Sannu da zuwa dake shaddar a bude take,amai yataho mata cikinta ya kulle taje xata tsugunna agefen shaddar dataga yadanfi kyau kawai seganin wani wandon yara tayi cike da kashi fal aciki,dukkoda warin daya cika hancinta haka ta takarkare ta daki Kara,bashiri baby Kay,UMMI AISHA da matar suka kwaso aguje sukai hanyar bandakin,ca’ba ca’ba suka sameta cikin kashi tana kuka,matar taso tayi daria seta daure de kawai,
Ta tayata ta tashi taje ta dakko mata zani da ruwa abokiti ta ajiye mata da sabulu irin yankan na wanki dashi suke wanka,magajiya tana kyankyami tana komi haka ta wanke jikinta tafito,matar ta bata kayanta sabo fil atamfa,bayan ta gama tafito UMMI AISHA tadaure tace”Sannu umm…”bata karasaba magajiya ta wurga mata harara”se intashi namaki dukan kawo wu’ka Wallahy,duk ba lefin Ki bane yar kan uba dangin mahaukata”
UMMI AISHA tai shiru inda Sabo ai ta saba,matar tai shiru tana naxarin wannan BAKON LAMARI,dakyar ta iya fadin”diyar mijin kice itama?!”
“Ehh itace ‘yar kishiyata mahaukaciyar nan hafsatu ba,dangin mahaukata ba”
Itade matar bata Kara maganaba,ba acika minti 30 ba dakin ya cika da matan kawunansu,sunfi mintina talatin ana gaisawa bayan an malala taburma cikeda Kayan abincin kauye ,dukkoda bawanda ya ishisu magajiya,”ke ‘yar balarabiya baxakiciba”acewar wata mata dake tambayar UMMI AISHA”wallahi a’koshe nake,amma barinsa albarka”bayan tadan gutsiri biskin gero tasa a bakinta….baby Kay kuwa ko hannunta bata yarda tasa kan abincin nan ba,
Ana cikin haka captain ya shigo cikin gidan,gaggaisawa sukai da matan Sannan ya masu sallama yabasu wrapper dubu hamsin yace matan su raba,bayan can waje Kuma yaba kawunnannata dubu Dari yace su raba,haka magajiya sukai sallama da yan uwanta ko kwabonta bai shiga hannunsu ba saima murnar barin garin daxasuyi takeyi….
Akan hanyar su ta komawa captain adam ke kallon magajiya ganin ba kayanta bane jikinta”ya akayi na ganki da wasu Kayan davan?!”
Takwashe labarin komi tabashi harda ‘kari,captain Adam ya girgixa Kansa”amma abu beyi dadi ba Ina Kayan naki to?!”
“Ga sucan cikin boot ko cikin gidah baxasu shiga ba se laundry”
“Amma magajiya kinban mamaki kinaso kice min wa’encan da bawani hali ne dasu ba su fiki wadatar zuci kenan tunda har suka barki kika taho da kaynsu amma kika kasa bar masu naki tir da halinki Wallahy”
“Akan wannan yamutsattsiyar atamfar kake gayamin magana?!lace Dina Kasan nawa ne kuwa xan bar masu?!”
“Nasani mana tinda dukta je tadawo nina siyo shi Kuma ko nawane lace dinki ai dattako ko Ma Abu ne mai Kyau,Sannan ko nawa suka siya atamfar idan Ma naira Dari ne Wallahy sunfiki sau dari tinda sun barki kin taho masu dashi,Kuma ko bakyaso sena gaya maki gaskiya abinda kikai har ga Allah baki kyauta ba,gashi nan abinda suka bamu cikin boot Kuma dukke xakiji dadin amfani dasu,kije Kiyi tayi”
Magajiya tacika tai fam,har suka Isa kaduna Batai magana ba,maigadi yatayasu shiga da Kayan kauyen da aka basu cikin gidan,,,bayan dawowarsu daga Zaria da sati daya UMMI AISHA ta shirya kamar yadda baffanta Yayi niyya taje tayi sati daya akano kafin moc exams dinsu,har Kano driver yakaita gidansu mama kakarta wannan karan Aunty mjay tananan da ya’yanta guda biyu ‘yusra da haneef’se shrye shryemu bikin su habbab da hanbal ake Wanda a satin ne akayi bikin,kwananta bakwai cif tadawo kaduna cikeda kewar yan’uwanta,,,bayan tadawo washegari taje islamia a hanyar dawowa wani matashi a Benz yake binta ta mota yana tuki da hannu daya ya xuro da kansa ta window”malama dan Allah minti daya”
UMMI AISHA tai biris dashi taci gabada tafiyarta,shikuma yana binta ta baya har sukaje kofar gidan se magiya yake mata”Dan Allah fa nace gaki Kuma daga Islamiyya kika dawo daga ganinki anga ustaxiya”hakan daya fada bakaramin Daria yabata ba bayadda ta iya haka taja ta tsaya ganin ya hadata da Allah”Yawwa ko kefa”yace da ita yana futowa daga cikin motar..hakan daya faru karaf a idon baby Kay bayan ta fito daga wani shopping complex dake kallon gidan nasu,fuu tashige cikin gidan kamar iska taxubarda ledar data siyo Kayan kwalliyan a kasa tana bubbuga kafa,magajiya ta mi’ke daga xaunen datake tana nifar inda baby Kay din take”lapia babyn ummah?!”
“Ummah,Kinga zungureriyar jeep na Benz new model dataxo wajen UMMI AISHA?!ummah bakiganshi ba Wallahy”tafadi hakan tane lekensu UMMI AISHA dake balcony din gate din gidan dayake ana gani ta cikin window,
“Kan bala’i”magajiyan tace taname sake bude curtains din tana kallon zankadeden yaron da yazo wajen UMMI AISHA”Sannan tajuya tafara sauka daga stairs tana huci kamar tsohuwar zakanya…..!

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *