UMMI CHAPTER 1

UMMI CHAPTER 1

ALIYU SODANGI RESIDENCE MAITAMA, ABUJA+ Security ne ya bude gate din gidan yayinda wata hadaddiyar Baqar Audi Q3 sabuwa dal ta danno kai cikin gidan.2 A yadda motar ta shigo gidan zaka tabbatar akwai matsala domin kuwa on normal basis mamallakin motar ya kan tsaya ya amsa gaisuwar ma’aikatan gidan amma a yau ko kallon su bai yi ba. Daga inda nake tsaye na hango wani dogo, kyakyawa, mai kyan tsari ya fito daga motar. Muhammad Kabir Sodangi wanda aka fi sani da MK shine ya fito hankalin shi a tashe. Gani nayi ya jefa ma Ya’u driver key yayinda ya nufi cikin gidan da sauri. Ya’u ya shiga motar ya gyara mishi parking. *********** Mummy ce zaune a falonta tare da qawarta Hajiya Aisha suna ta hira. MK ya shigo falon cikin sallama yayinda ya qarasa ya duqa har qasa ya gaishe su. Bayan sun amsa ne Mummy tace “MK lafiya na ga kamar kana cikin damuwa?? aren’t you supposed to be at work?? what happened??” Sosa kai ya dan yi yace “Mummy everything is fine. uhm… tana ina??” Murmushi tayi tace “kar kace ita ta sa ka baro office at this time… how many times do I have to tell you ka daina biye ma Maleeka…” Kafin ta qarasa maganar ne yace “Mummy kiyi haquri.. this is a bit serious ne shiyasa..” Mummy ta girgiza kai tace “hmm.. Allah ya shirye ku da kai da ita. she should be in her room…” Da sauri ya miqe yace “bari in duba ta” Bayan MK ya wuce sashen Maleeka ne Hajiya Aisha ta kalli Mummy tace “gaskiya soyayyar yaran nan tana birge ni. Na tabbatar auren su zai qara danqon zumunci a tsakanin ku. Shin yanzu auren saura wata biyu ko??” Mummy tana murmushi tace “eh wallahi… ai gwara ayi mu huta.. yanzu dai ki duba ki gani yaron nan yana wurin aikin shi ta taso shi kuma na tabbatar ba wani abu bane banda ya zo su je siyan chocolate…” Hajiya Aisha tana dariya tace “Maleeka hoo…” ************** Kwance take a kan makeken gadon dakinta wanda ya qawatu da kayan jin dadi na zamani na gani na fada tana kuka. Qwanqwaso qofar dakin yayi sannan ya shigo. Hankalinshi a tashe ya qaraso wurinta ya zauna a gefen gadon yace “Babes..” Cikin shagwaba tace “leave me alone” Ji tayi yace “don Allah kiyi haquri, wallahi I was in a serious meeting ne kamar yadda na fadi miki… yanzu haka I had to pause the meeting for you…” Bai qarasa maganar shi ba ya ga ta tashi zaune tana kallon shi. MK wanda yake kallonta a ranshi ne yace “Ya Salam.. she manage to look beautiful even when she is all messed up… how I love you my babe” Bai ankara ba ya ji ta dora kanta a bisa kafadar shi yayinda ta riqe hannun shi cikin shagwaba tace “Honey I am sorry too, kawai I was bored ne shiyasa..” MK wanda ya zare kanta daga kan kafadar shi ne yace “hey.. ba na fadi miki ki daina hada jikin ki da nawa ba??..” Turo baki tayi tace “toh wai mu ba ‘yan uwa bane?? again it’s just two months to our wedding fa” STORY CONTINUES BELOW Girgiza kai yayi yace “still… it’s not right kin ji??” Tashi yayi tare da fadin “oya sauko mu je toh” Da sauri ta sauka daga kan gadon. Sanye take cikin wata lilac jumpsuit wadda ta bala’in yi mata kyau. MK yana tsaye yana kallonta ne ya ga ta nufi gaban Vanity mirror dinta ta gyara fuskar ta sannan ta shiga closet dinta ta fito riqe da wani qaramin veil ta yafa a kanta yayinda ta juyo ta kalle shi tace “na yi kyau??” Girgiza kai yayi alamar a’a. Bata rai tayi cikin shagwaba tace “Honey this is from one of my latest collection fa.. wai meyasa baka appreciating brand dina?? are you even…” Ji tayi yace “sssshhhh… babe ba haka bane.. on the contrary I love your brand alot.. you are doing an amazing job. the thing is irin wadannan kayan ba wadanda yakamata ki dinga fita da su bane… some of them are a bit tight and revealing.. zan fi so ki dinga sa su only at home..” Cikin shagwaba tace “but…” Yace “but nothing my babe..” Gani tayi ya shiga closet dinta ya dauko wata atamfa ya fito. Tana ganin shi riqe da atamfar ta bata rai amma kuma babu yadda zata yi. Duk duniya MK ne kadai yake tanqwara Maleeka. Shi kadai yake sa ta yin abubuwa against her wish.. Yanzu haka tana ta turo baki ta karbi atamfar daga hannun shi. Ji tayi yace “zan jira ki a falon Mummy..” Bayan ya fita ne ta shiga closet din don shiryawa. ************ A lokacin da MK ya dawo falon Mummy ya tarar Hajiya Aisha ta tafi. Ko da ya zauna Mummy tana murmushi tace “har kun daidaita kenan” murmushi yayi yace “eh Mummy, dama akwai inda zan kai ta ne…” Girgiza kai tayi tace “siyan chocolate din ne dole sai kai ne zaka zo ka kai ta?? Yanzu kullum haka zaka dinga biye mata?? ni dai ina gaya maka wallahi ka dinga tsawata mata.. you shouldn’t always give in to her demands” Yana murmushi yace “Mummy I love her alot.. bana so in bata mata rai besides yanzu zamu je mu dawo..”3 Mummy tana murmushi tace “toh ai shikenan, Allah yayi albarka” yace “ameen” Wayar intercom Mummy ta dauka ta kira ta sanar da masu aiki su kawo ma MK kayan motsa baki. Bayan ta ajiye wayar ne suka shiga hira. MK yana cikin hira da Mummy ne ya ji wata murya ‘yar qarama mai dadin gaske wadda take dauke da accent na fulani tayi sallama. Zuciyar shi ce ta buga da jin wannan muryar.1 why??? Da sauri ya amsa sallamar yayinda ya juya don ganin mai dauke da wannan muryar.5 A wannan lokacin kuwa tuni ta ajiye tray din a kan side stool. Shi dai MK bai samu damar ganin fuskarta ba sai dai kawai ya ga qaramar mace sanye cikin hijabi. Har qasa ta duqa tace “ina wuni” wanda a daidai wannan lokacin ne Maleeka ta shigo falon. Ji nayi yace “lafiya” yayinda hankalin shi ya tafi ga kallon Maleeka wadda ta shigo falon sanye cikin atamfar da ya zabar mata. Dinkin fitted gown ce wadda ta bala’in yi mata kyau. MK wanda ya sa mata idanuwa yayi regretting zabar mata kayan domin kuwa rigar ta kama jikinta yayinda gaba daya curves dinta suka fito. Runtse idanuwa yayi sannan ya kauda kanshi. A lokacin kuwa tuni mai aikin ta fita daga falon. STORY CONTINUES BELOW Maleeka wadda ta zauna a kan hannun kujerar da MK yake zaune ne tace “Honey na shirya mu je..” Mummy ta harare ta tare da fadin “saura ki je kiyi ta bata mishi lokaci.. kin dai san he needs to get back to work” Cikin shagwaba tace “I swear zanyi releasing dinshi as fast as possible Mummy.. ni kawai I just want to spend some time with him ne..” MK yayi murmushi yace “I love you my babe” Itama tana murmushi ta kashe mishi ido daya tace “I love you too my dearest cousin”2 Mummy ta girgiza kai yayinda tace “toh marassa kunya sai ku tashi ku bani wuri..” MK yana dariya yace “yi haquri Mummyn mu” Ya kalli Maleeka yace “tashi mu je babe” Haka suka fita yayinda Mummy take cike da farin ciki. ************ Ko da suka fito Ya’u ya miqa mishi key. Maleeka ta kalli motar MK ta zaro idanuwa tare da fadin “honey.. like seriously?? when did this arrive??” Murmushi yayi yace “Shekaran jiya…you like it???” Tace “sossai ma..” Kafin ta rufe bakinta kuwa yace “mu je toh idan mun gama sai ki sauke ni a ofis ki dawo da ita… it’s all yours” Ihu ta sa yayinda tayi hugging dinshi tare da fadin “oh My God… are you being serious??” Da sauri ya banbare ta daga jikin shi ya tura ta baya tare da murtuke fuska. Kafin yayi magana ne tace “I am sorry for that… sai munyi aure ko??” Murmushi kawai yayi yayinda ya ji ta cigaba da fadin “…thank you so much Honey. I love you so much” Nan da nan kuma ta bata rai tace “amma fa Daddy zai yi fada… ka ga this is like the 5th car da ka bani kyauta” Murmushi yayi yace “dont worry I will explain to him… besides it’s just 2 months until you come to my house and I give you as many as you want my babe” Lumshe idanuwa tayi tace “Allah ya bar mun kai my Love” Yana murmushi ya miqa mata key din motar yace “oya mu je… remember ana jira na a ofis” *********** Haka Maleeka ta ja shi suka je Shoprite suka siyo Chocolates sannan ta sauke shi a office dinshi ta tafi. ♧♧♧♧♧♧♧ MK-TECH SOFTWARE COMPANY Tsaye yake jikin window na office dinshi yayinda ya hango su lokacin da ta sauke shi ta tafi. Gani nayi ya girgiza kai sannan ya juya ya fita daga office din. A lokacin da MK ya fito daga elevator ne ya gan shi a tsaye yana kallon shi yayinda hannuwan shi suke cikin aljihun shi. Ko kafin Fahad yayi magana ne MK yace “hey look I am sorry, wallahi I needed to go ne” Fahad yace “suna ta jiran ka a conference room..let’s go and finish up” MK ya shige gaba yayinda Fahad ya rufa mishi baya. Ko da suka shiga dakin taron sun tarar da su suna ta tattaunawa. MK ya basu haqurin bata musu lokaci da yayi yayinda suka cigaba da meeting din. Bayan kusan awa biyu ne suka gama meeting din inda kowa ya kwashi files dinshi suka koma bakin aikin su. Baqin da suka zo kuma suka cigaba da tattaunawa da su MK din for extra 30minutes sannan suka tafi. STORY CONTINUES BELOW *********** An hour later… Zaune yake a kan executive chair na office dinshi wanda ya qawatu da kayan zamani yana duba wasu reports a Macbook dinshi. Fahad ne ya qwanqwaso qofar ya shigo yayinda ya daga kai ya kalle shi yace “hey buddy..” Fahad wanda ya zauna ne yace “I cant believe you kept us waiting again.. she could’ve waited for you to…” MK ne ya katse shi tare da fadin “Fahad don Allah kayi haquri.. Maleeka is not just my cousin, she is my love and my life” Ya nuna office din gaba daya yace “I can give up all these for her..” Fahad ya girgiza kai tace “I know my friend and i hope yadda ka damu da ita haka ta damu da kai”1 Murmushi yayi yace “its evident she does… nasan ka shaida hakan. the feeling is mutual buddy, I really cant wait to have her in 2 months time” Fahad yana murmushi yace “Allah ya kaimu abokina” Ya miqe sannan yace “let me go and prepare for our trip to Hong Kong… when I am done sai kayi reviewing” Yace “thanks my friend… I appreciate” ************ MUHAMMAD SODANGI RESIDENCE Zaune suke a dinning yayinda suke dinner. MK dai a kullum gidan iyayen shi yake cin abinci. Qanwar shi Hafsah da Mamy dai white rice da liver sauce suke ci yayinda MK da Abba suke cin tuwo miyan kuka da pepper soup. Hafsah ce ta kalli MK tace “Ya MK na rasa me ya hada ka da tuwo miyan kuka… of all the foods ka rasa wanda kake so sai wannan” ta kalli Abba tace “gwara Abba shi dama dattijo ne.. ” Gabadayan su suka fashe da dariya yayinda MK yace “akwai dadi ne Hafsy, besides babu wahala wurin ci” Tace “toh yanzu idan kayi aure wa zai dinga tuqa maka?? yakamata babe dinka ta koyi tuqa tuwo tunda kana so”3 Murmushi yayi yace “the last time da muka yi maganar she told me cewar zata koya but ban sani ba ko ta koya din” Hafsah tana dariya tace “wallahi in dai Ya Maleeka ce babu wani tuwon da zata koya, ni fa ban taba ganinta a kicin ba… kawai abincin chefs zaku dinga ci” Haka suka dinga dariya yayinda Mamy tace “wai ya maganar shirye shiryen bikin?? hope komai na tafiya da kyau??” Yace “everything is going well Mamy, na riga na bata kudin komai da komai.. she is taking care of everything” Hafsah tace “hmmm… Na tabbatar bikin ku will be the best da aka taba yi cikin garin nan.. Ya Maleeka will surely have a fairytale wedding just as she wants” Abba ne ya kalli MK yace “yakamata idan kayi auren nan ka dauki hutu mai tsawo saboda ka samu hutu sossai.. bana jin dadin yadda kake yin aiki babu hutu especially because of your health”1 MK yayi murmushi yace “Insha Allah Abba.. ” Wayar Abba ce tayi ringing yayinda ya miqe tare da fadin “excuse me please” Hafsah ce tace “Go ahead Abba…” Gaba dayan su suka fashe da dariya harda Abba wanda ya riga ya san halin Hafsah. idan dai ana zaune tare da ita ta dinga sa su dariya da shirmen ta kala kala. Bayan ya bar Dinning din ne Mamy tace “imagine him telling someone to reduce the rate at which he stresses himself with work when he himself is a workaholic” MK da Hafsah suka fashe da dariya yayinda Hafsah tace “wallahi Mamy kinyi qoqari zama da Abba.. shi fa kullum he is busy with his business trips… Yanzu haka idan nace muku gobe zaiyi tafiya kar kuyi mamaki” Ta kalli MK tace “Ya Maleeka ma zata yi haquri da kai bro.. don wallahi baku da wani bambanci da Abba… don ma dai Ya Maleeka tayi sa’a she also has her business to take care of” Mamy da MK suna dariya yayinda yace “I will always have time for Maleeka no matter what.. she comes first because she is the love of my life” Hafsah tace “awwwnnnn” Mamy wadda take murmushi tace “Allah ya sanya albarka a auren ku” Gaba daya suka amsa da “ameen” ♧♧♧♧♧♧♧ THE BODY BOOTH AND SPA MAITAMA, ABUJA+ Kwance suke akan wani portable spa bed yayinda ake yi musu back massage. Jameela ce tace “yanzu Leek dagaske kawai sai ya baki motar kyauta?? as in the latest Audi Q3??” Maleeka wadda take murmushi tace “yes Jay, kin ga it’s the fifth one da ya bani kenan.. I swear I love the guy” Jameela tana murmushi tace “gaskiya soyayyar ku tana birge ni.. ga ku cousins sannan ga soyayya mai qarfi” Maleeka ta lumshe idanuwa tace “I can’t believe my dream came true.. I have always wanted a handsome guy, classy guy, extremely rich guy, one who is famous and above all one who will love me like crazy.. Honey is just the best Jay”3 Jameela tace “gaskiya the guy has given you everything, ina Roqon ki kema kiyi qoqari ki mayar da shi top priority dinki a rayuwar nan.. try as much as possible to reciprocate each and every kindness and love he has shown you. kin san samun irin Ya MK a zamanin nan abu ne mai wuya” Maleeka tana dariya tace “I will do just that Jay, I swear” Bayan an gama yi musu massage din ne suka koma section din gyaran gashi yayinda suka cigaba da hira. Wayar Maleeka ce tayi ringing. Ko da ta duba ta ga sunan shi murmushi tayi sannan tayi answering. Cikin muryar ta mai kashe mishi jiki tace “hello Honey” A dayan bangaren MK yace “hey babe, how are you?” tace “I am fine” Yace “har yanzu kina spa din ne??” tace “yes honey, ana gyara mun gashi na ne yanzu” Yace “Okay that’s good” Ya saki ajiyar zuciya sannan ya cigaba da fadin “Babe I am starting to miss you tun ban tafi ba..” Lumshe idanuwa tayi cikin shagwaba tace “toh ka fasa tafiyar mana” Yace “if not because my attention is needed there da na fasa.. amma kuma ko na fasa ai kema tafiya zakiyi ki bar ni.” tana murmushi tace “toh ai ni sai next week zanyi tafiyar” Yace “you are still leaving me behind babes..” Turo baki tayi kamar yana ganinta tace “anjima zaka zo??” Yace “yes, me zaki bani idan na zo??” Tace “duk abinda kake so..” Kai tsaye yace “tuwo nake so” Zaro idanuwa tayi tace “what?? don Allah kayi haquri.. na manta ma ban fadi maka ba I swear bazan iya koyon yin tuwon nan ba.. akwai wahala fa”5 Ji tayi yace “relax, ni bana son ki da wahala… idan baki iya ba dole in haqura” Cike da jin dadin maganar shi tace “Honey you know I love you ko??” Yace “yes babe and I love you so much more….” Haka dai suka cigaba da hirar soyayyar su har sai da aka nemi attention dinshi wurin aikin nashi sannan suka yi sallama. Bayan sunyi sallama ne Jameela ta kalli Maleeka tace “meye na ji kina maganar koyon tuqa tuwo akwai wahala??” Maleeka tace “akwai wahala dagaske…” Jameela tace “ki rantse da Allah kin taba gwadawa kin ga wahalar shi… Leek like seriously?? duk abinda gayen nan yake yi miki ace bazaki iya jurewa kiyi mishi this little thing ba?? what is wrong with you??” STORY CONTINUES BELOW Maleeka ta turo baki tace “Jay please..” Jameela wadda ranta ya baci ce tace “please what?? I swear son jikin nan naki zai kai ki ya baro… Allah ya so ki Cousin dinki ne kuma da alama son da yake yi miki ya fi wanda kike yi mishi.. but dukda haka try and change because you dont know what the future holds” Haka dai Jameela ta dinga gaya ma qawar ta gaskiya yayinda ita kuma ta dinga turo baki tana fushi. ♧♧♧♧♧♧♧♧ ALIYU SODANGI RESIDENCE Wuraren qarfe takwas da rabi na dare ya iso gidan. Sai da ya shiga sashen Daddy suka dan taba hira sannan ya wuce qaramin falon gidan don jiran fitowar gimbiyar tashi. MK yayi kusan minti ashirin yana zaman jiranta ne ta shigo. Sanye take cikin wata Mint green lace-chiffon long dress wadda tayi mata bala’in kyau. Kanta babu dankwali yayinda gashinta Wanda ya sha gyara ya kwanta a kafadunta da gadon bayanta. MK dai tunda ya daga kai ya kalle ta na ga ya mayar da idanuwan shi kan wayar shi. Maleeka wadda ta kula da hakan ta sani sarai dressing din da tayi ne bai yi mishi ba wanda kuwa ita a tunanin ta yakamata ya yaba domin kuwa it’s one of her best dresses na latest collection dinta. Bai ankara ba ya ji ta qwace wayar hannun shi yayinda ta tsaya mishi a kai tace “Honey kace kawai ban yi kyau ba instead…” Murmushi yayi yace “hey babe…” Kafin ya qarasa maganar shi ne zuciyar shi ta buga a dalilin jiyo muryarta cikin sallama.1 The second time that this particular voice does some weird stuff to his heart??? why????6 Da sauri ya amsa sallamar yayinda yake qoqarin ganin ko wacece amma ya kasa a dalilin gimbiyar tashi da tayi mishi tsaye a kai. Mai aikin ce ta ajiye tray na kayan ciye-ciye yayinda ta duqa tace “ina wuni” the sweet voice, the fulani accent…6 MK wanda har yanzu bai samu damar ganin fuskarta bane yace “lafiya” yayinda ta tashi tayi tafiyarta. Daga kai yayi ya kalli Maleeka wadda take tsaye yace “babe kin zama soja ne ban sani ba??” Hararar shi tayi tare da turo baki. Girgiza kai yayi tare da yin murmushi yace “kin dai san you are the most beautiful girl on earth ko?? the dress is beautiful and it looks super great on you” Lumshe idanuwa tayi yayinda ta saki murmushin jin dadi tace “thank you honey” Shi kam MK he only said that saboda baya so ya bata mata rai but deep down he hated the dress. Rigar deep neck gareta wadda ta bayyana cleavage dinta.. ga gashin kanta a bude. Dukda shi din dan uwanta ne he feels she shouldn’t have come out like that. Muryarta ya ji tana fadin “Honey ka ga kayan nan da na sa?? it’s another one of my latest collection.. I pray it’s going to sell well…” Murmushi yayi yace “I bet it will my Babe.. kwana nawa zakiyi a France din??” Tace “sati daya afterwards zamu je Dubai mu hado kayan lefen tare da Jay” Yace “ok, idan kudin basu isa ba please let me know” Tana murmushi tace “haba dai.. kudaden da ka bani sunyi yawa ma ai Honey” MK ne ya janyo Five alive drink ya zuba a cup yayinda ya ji Maleeka tana fadin “na manta ban fadi maka ba.. I think I will go for gidan nan na Asokoro because its classy compared to na nan Maitama” STORY CONTINUES BELOW Murmushi yayi yace “it’s okay babe” Tana kallon shi tace “but wait, ya zaka yi da dayan gidan?? hope you are not planning on taking up another wife after me??” MK ya fashe da dariya yayinda yake kallon fuskar ta yana mamaki. Cup din hannun shi ya ajiye sannan ya juyo yana kallonta yace “babe, meyasa kike tunanin zan qaro aure when I already have you?? bana sha’awar auren mata fiye da daya.. kin fi kowa sanin bana son hayaniya considering my health.. dealing with my company alone ya ishe ni” Lumshe idanuwa tayi tana murmushi yayinda tace “hmmm… Honey ai bazan ma bari ka qaro wata ba… kasan yadda na tsani kishiya kuwa??” Yana dariya yace “ke dai fadi gaskiya.. tsoron ta kike ji” Ta turo baki tare da fadin “Nah… there is no girl that can compete with me akan ka.. I have all it takes to defeat kowace irin mace…” Shi kam MK gyara zama yayi yana kallonta yayinda yace “interesting” Ji yayi ta cigaba da fadin “…na tabbatar bazaka samu macen da ta kai ni kyau ba, bazaka Sami mai zurfi ilimi na at this age ba, I have become a successful business woman within a short period of time and I doubt you will get someone that has achieved more than I have at this age…” MK wanda yake kallonta yace “Babe relax.. I am not even looking for anyone. ke kadai kin ishe ni. As for the other house we can always go there if we need a change of environment within Abuja… so no big deal” Murmushi tayi sannan tace “thank you so much my dearest Cousin, I love you sooo much” Yana dariya yace “I love you more my Babe” Daga nan kuwa suka cigaba da hirar su ta soyayya yayinda take ta bashi labarin abubuwan da take tsarawa na bikin su da yadda take so bikin su ya zama grandest amongst duk wadanda aka taba yi. MK bai bar gidan ba sai kusan qarfe sha daya na dare wanda kuwa da qyar ta sallame shi. Dayake the next day sai da yamma ne tafiyar shi zuwa Hong Kong tayi mishi alqawarin zata je office din shi suyi sallama. ♧♧♧♧♧♧♧♧ Washegari… MK-TECH SOFTWARE COMPANY Wuraren qarfe Goma sha biyu ta shigo Company din cikin danqararrar motar ta qirar Mercedes Benz AMG CLS 63 fara sol. A daidai entrance din company din ta tsaya yayinda ta fito ta jefa ma security key din don ya gyara parking. Tunda ta fito kuwa ma’aikata suke ta gaishe ta domin kuwa sun sani cewar ‘yar uwar Oga ce sannan his wife-to-be. Sanye take cikin wata Burgundy long sleeve maxi dress yayinda ta yafa wani dan qaramin black veil a kanta, kusan ma rabin kanta a bude yake. Make up dinta on point. Idanuwanta sanye cikin wani designer Gucci sunglasses. Sai baza qamshi take yi. Babu qarya Maleeka tayi kyau domin kuwa first class babe ce, kyakyawa ta qarshe. Tunda ta fito daga motar kuwa take magana a waya, haka ta shige ciki ba tare da ta bi ta kan ma’aikatan da suke gaishe ta ba. Ko dama on normal basis bata wani ansa gaisuwar tasu. **************** Zaune yake a kan kujerar office dinshi yayinda Nayla take duqe a gefen shi tana nuna mishi wasu reports a laptop dinta. Maleeka ce ta shigo ofis din yayinda zuciyarta ta buga a dalilin ganin yadda Nayla din take daf da shi. Ko da suka dago kai suka kalle ta gani nayi yayi murmushi yayinda yace “hey Babe..” Maleeka kuwa fuskarta a murtuke ta qarasa wurin su yayinda ta dauke Nayla da wani mugun Mari… Gaba dayan su sun zama shocked. MK ya miqe da sauri yace “Maleeka meye haka??” Nayla wadda take dafe da kumatunta kuwa tuni ta fashe da kuka yayinda Maleeka ta turo baki tace “Honey me take yi very close to you?? who is she?? ni fa wallahi…”9 Daga nan ta fashe da kuka itama yayinda ta juya zata bar ofis din. Da sauri yace “Babe please wait… dawo mana” Ya kalli Nayla wadda take ta zubar da hawaye yace “uhm Nayla I sincerely apologize on her behalf… you know how jealous you ladies can get sometimes” Tana share hawayenta tace “it’s okay Sir, I understand” Yace “can we finish this later??” ta girgiza kai tace “as you say Sir..” Nayla ta dauko laptop dinta sannan ta bi ta gefen Maleeka ta fita a ranta tana fadin “stupid spoilt brat..”3 Maleeka tana tsaye tana ta rusa mishi kuka ne ta ji muryar shi a bayanta yana fadin “Babe I am sorry.. Please ki daina kuka.. kukan ki breaks my heart”1 Juyowa tayi tace “Honey meyasa kake yi mun haka???” Hannunta ya janyo suka zauna a kan sofa yayinda yace “look babe, Nayla is an employee in this company, she was only here to show me a report. You shouldn’t have done that to her.. it’s very wrong.. please kar ki sake kin ji??” Turo baki tayi yayinda ta girgiza kai alamar ‘toh’ Ya saki ajiyar zuciya tare da fadin “You are my queen and I love you soo much… MK naki ne har abada my dearest Leek.. bazan taba rabuwa da ke ba insha Allah” Gani yayi ta kalle shi yayinda tayi murmushi tace “promise??” Yace “you know I dont..” Da sauri tace “i know i know.. you dont make promises but only give your word” Hannunta ta miqa mishi yayinda ya zaro handkerchief daga aljihun shi ya dora mata a hannun yana murmushi. Gani nayi ta share hawayen fuskarta sannan ta harare shi tace “kawai ka sa makeup dina ya lalace” Kashe mata ido daya yayi sannan yace “you look soo beautiful even without makeup my Babe..” A haka kuwa ya cigaba da lallashin ta tare da kashe mata jiki da kalaman soyayya har ta saki ranta sossai suka cigaba da hirar soyayyar su kamar kullum. Gaba daya appointments dinshi yayi cancelling yayinda ya tura masu requiring urgent attention dinshi zuwa office din Fahad. Shi dai Fahad tunda ya ga haka ya tabbatar gimbiyar tashi tana building din. Sossai yake mamakin irin bala’in son da abokin nashi yake yi ma Maleeka da yadda yake bala’in girmama al’amuran ta. ♧♧♧♧♧♧♧ ASALIN LABARI+ Alhaji Muhammad Sodangi da Alhaji Aliyu Sodangi sun kasance ‘yan uwan juna. Iyayen su sun rasu shekarun baya. Wadannan mutane dai Asalin su ‘yan Katsina ne gaba da baya.4 Wadannan mutanen biyu sun tashi cikin gata na iyaye domin kuwa mahaifin su ya kasance shahararren Dan kasuwa Wanda ya tara dukiya mai yawan gaske. Sun Sami ilimi na boko da Islamiyya mai zurfin gaske don haka ne basu samu matsala ba a cikin zaman rayuwar su. Alhaji Muhammad Sodangi wanda shine babba yayi fice a kasuwancin shige da fitar da mai. Shine mamallakin Oil and Gas Company dinnan mai suna Sodangi Oil and Gas Nigeria limited. Alhaji Muhammad Sodangi yana daya daga cikin manyan masu arzikin qasar mu. Babu state din da bazaka ga gidajen man shi ba. Alhaji Muhammad Sodangi yana da Matar shi daya mai suna Hajiya Sameera wadda ake Kira Mamy. Yaran su guda biyu ne. Muhammad Kabir shine babba sai Hafsah wadda take bin shi.1 Hafsah dai dukda ta taso cikin gata sossai take da discipline. Shekarun ta Ashirin da daya a duniya. Hafsah dai gaba daya karatunta a Abuja tayi dukda kuwa iyayenta sun bata damar zabar duk qasar da take so tayi karatu amma ta qi. Ita dai Hafsah Momma’s pet ce, bata so tayi nisa da Mamyn ta domin kuwa bala’in sonta take. A yanzu haka tana yin karatun Masters dinta ne a nan University of Abuja. *********** Alhaji Aliyu Sodangi ya kasance daya daga cikin Ambassadors na qasar mu wanda ya wakilci qasar mu a Ingila tsawon shekaru sannan ya dawo Nigeria. Hajiya Lubna wadda ake Kira Mummy itace matar shi. Asalin Mummy ‘yar qasar Somalia ce. ‘yar su daya tak Maleeka, daga ita kuwa Allah bai qara basu haihuwa ba. ♧♧♧♧♧♧♧ MUHAMMAD KABIR SODANGI?? Muhammad Kabir Sodangi wanda aka fi sani da MK ya kasance kyakyawa, dogo, fari amma ba sol ba. Yana da yalwatacen gashi a kan shi da fuskar shi wanda ya qara mishi kyau. MK is the kinda guy da zaka kira one in town. He is perfect in every aspect. Don dai Ance dan Adam tara yake bai cika goma ba amma da sai in ce shi kam ya cika Goma. MK dai tunda ya taso baya da hayaniya ko alama. Ba mai yawan magana bane sannan baya da zafin rai. A taqaice MK ruwan sanyi ne, idan dai ka ga yayi fushi toh kuwa ba qaramin qure shi kayi ba. Idan ma yayi fushi da zarar ka bashi haquri tare da admitting kayi laifi shikenan ya wuce wurin. MK dai dukda tarin dukiyar da Allah yayi ma mahaifin shi baya da Gadara da girman kai sannan baya da qyamar talaka. Yana da yawan son kyautata ma marassa qarfi. MK hafizi ne sannan yana da son karance-karancen litattafan addini. Sossai ya mayar da hankali akan sanin addinin shi wanda hakan yake masifar birge iyayen shi. MK tun yana yaro ya kasance mai qoqarin gaske a boko. Tunda ya fara makaranta shine yake topping a class dinsu. Tun yana yaro yake son research, wannan ne yasa a koda yaushe zaka ganshi gaban computer, yana duba wayar shi ko I-pad, wasu lokutta har newspapers yana bi sannan yana bala’in kallon business news. STORY CONTINUES BELOW Tunda ya gama Primary dinshi a cikin garin Abuja ne Dad dinshi ya tura shi Ingila ya cigaba da karatun shi. Dayake kawun shi yana can sai yayi zaman shi a gidan. A lokacin da ya kammala high school ne yayi joining college inda ya karanci software engineering. Bai tsaya ba har sai da yayi Masters dinshi sannan yayi wasu professional courses. A yanzu haka shekarun MK talatin a duniya. Shine CEO na shahararren kamfanin nan wato MK-TECH software company. A yanzu haka MK-TECH is the biggest software company in Nigeria and he has become one of the richest young guys in Nigeria. Yayi achieving wannan on his own without the influence of his Dad, MK ya sanya alot of dedication, passion, extra hardwork to get to where he is today. A dalilin sleepless nights da kuma mugun aikin da yake yi ne Migraine yayi mishi mugun kamu. Har Germany ya je ganin likitoci yayinda suka dora shi akan treatment tare da bashi shawarwari akan yadda zai rage ma kanshi stress. Akan dole ya rage stressing kanshi dukda dai ciwon ya kan tashi lokaci-lokaci amma dai baya tsananta mishi kamar da. The only entertainment da MK yake zama ya kalla with passion shine WWE (wrestling). MK dai babu wrestling din da yake wuce shi: Pay-per-views, Monday night Raw, Wednesday NXT, Friday night Smackdown. Ya kan samu time ya je kallo idan har ya je business trips dinshi a America. Abincin da yake bala’in so a rayuwar shi Tuwo miyan kuka. Sossai Maleeka da Hafsah suke mamakin yadda Classy guy kamar shi yake son tuwo. Maleeka kuwa kullum sai tayi qorafi har tana fadin abincin qauyawa ne. shi kuwa to him it’s a great dish kuma yana so. MK is a fan of the famous Italian Cappuccino Coffee. He starts his day with it and ends the day with it. A duk ranar litinin da alhamis kuwa zaka ga MK yana azumi.. haka duk sauran azumin nafila basu taba wuce shi. Fahad Usman ya kasance best friend din MK Wanda tare suka yi karatu dukda shi Fahad din ya samu zuwa Ingila ne through scholarship a wannan lokacin. Iyayen Fahad ba masu arziki bane, MK yayi supporting din shi financially during their stay a Ingila for which he is forever grateful. Ko da suka dawo Nigeria tare suka yi building kamfanin MK din Wanda har ya kai matakin da yake a yau. Fahad shine next in command a kamfanin Wanda kuwa MK yana jin dadin aiki da shi domin kuwa ya riqe gaskiya da amana. Fahad has become a brother he never had. Babu sirrin juna da basu sani ba.. they are so close. A yanzu haka wata biyar da suka wuce ne Fahad yayi aure wanda abokin nashi ya taka rawar gani a bikin sossai. MALEEKA ALIYU SODANGI??? Yarinya kyakyawa, ajin farko, fara sol. Maleeka doguwa ce, slim with a beautiful body, Tana da dogon gashi irin na mahaifiyarta.. In all she is a super gorgeous lady. Maleeka dai ta taso cikin soyayyar iyaye da dan uwan ta MK, ‘yar gata ce gaba da baya domin kuwa she is the only child a wurin iyayenta. Maleeka dai a qasar Ingila aka haife ta, anan tayi karatun ta har ta kai matakin masters. Maleeka dai classy babe ce ta qarshe, komai ka gani a wurinta toh fa designer ne. Maleeka akwai ta da ji-ji da kai da girman kai.. sossai take alfahari da kyan da Allah yayi Mata da kuma matsayin da take da shi. STORY CONTINUES BELOW Maleeka bata qaunar low-class mutane… gaba daya friends dinta yaran masu kudi ne. Dukda tana da qawaye dayawa her only one true and best friend is Jameela Mukhtar wadda itama iyayenta suka zauna a Ingila kafin suka dawo Nigeria. Mahaifin Jameela shima Ambassador ne Wanda suka yi aiki tare da Daddyn Maleeka. Jameela dai halinsu ya bambanta da na Maleeka ta kowanne sabga. Jameela batada girman kai ko alama… a very down to earth human being unlike qawarta. It still remains a mystery how they are able to stay as best of friends over the years. Maleeka dai tun tana yarinya take bala’in son Fashion. burinta bai wuce idan ta girma tayi owning brand dinta ba. Da farko iyayen ta were against it because a cewar su harkar yahudawa ce amma ganin ta kafe ne suka barta. A yanzu haka Maleeka owns the famous clothing Brand dinnan mai suna ‘Leek’ Wanda ya zagaye qasashe da dama. MK shine yake sponsoring gaba daya business din nata from the onset har zuwa yanzu. A america ake producing mata designs dinta sannan take marketing dinsu a website dinta. Maleeka tana da wani qaton Boutique a cikin garin Abuja.. wannan boutique din kuwa dauke yake da kaya kala-kala. Sossai manyan yaran Abuja suke patronizing kayan domin kuwa clothing line dinta is unique and classy. Har fashion shows din da ake yi a qasashe Maleeka tana attending inda models suke showcasing designs dinta a kan runway. Shekarun Maleeka ashirin da uku a duniya and she has become a successful business woman at a very young age. Burin Maleeka a rayuwa shine ta auri namiji kyakyawa, mai class, mai ilimi, mai kudi sannan Wanda yake bala’in sonta. She found all these in her dearest Cousin MK. ♧♧♧♧♧♧♧♧ Soyayyar Maleeka da MK ta samo asali ne tun suna yara. Zamu iya cewa tunda aka haifi Maleeka MK yake bala’in sonta. Sossai ya shagwaba ta. Hakan yasa take bala’in sonshi itama. MK ne kadai yake sanya ta yin abu against her wish. Akan tilastawar MK ne Maleeka ta dan zauna ta koyi karatun addini shima ba wani mai zurfi ba. Shine kadai yake tilasta mata sanya kayan mu na hausawa dukda kuwa dinkunan duk matsatsu ne. MK ya hana ta fita babu mayafi a kanta.. tun tana bata rai don ya janye har ta gaji akan dole ta fara sakawa dukda kuwa yawanci zaka ga mayafin dan qarami ne wanda baya qarasa rufe gashin nata. Maleeka dai dayake a Ingila ta tashi ta riga ta saba da al’adun su na mace tayi hugging namiji anyhow sossai ta samu matsala da MK. A da yana zaune ma saidai kawai ya ji ta fado mishi a jiki. Ko da yayi mata bayanin hakan ba daidai bane qin amincewa tayi har tana fadin tunda su ‘yan uwa ne ai babu wani abu. MK dai sai da ya buda mata wuta sannan ta daina. Har yanzu idan ta manta takan rungume shi wanda kuma idan ta ankara sai ta bashi haquri. Da farko iyayensu sunyi tunanin soyayyar ‘yan uwantaka suke yi ma juna amma daga baya suka fahimci gagarumar soyayya ce. Sossai hakan ya faranta musu rai domin kuwa a cewar su it will make their relationship stronger. Maleeka kuwa bata taba yin wani saurayi ba a rayuwarta sai MK haka shima MK bai taba yin budurwa ba sai Maleeka. Maleeka tana da bala’in kishi a rayuwarta. Bata son sharing komai nata da wani. Sossai ake samun matsala da ita idan ta ga mace a kusa da MK. Sanin haka ne ya sa MK yake qoqarin kiyaye duk wani abinda zai hada shi da mace domin kuwa baya so ranta ya baci. Sossai MK yake kashe ma Maleeka kudi. Duk abinda ta nema a wurinshi yana bata even more than abinda ta nema din. A yanzu haka manyan motocin da ya bata kyauta sun kai biyar. Su Daddy sunyi fada har sun gaji. Hidimar Maleeka itace priority din MK a koda yaushe. duk abinda yake yi idan har Maleeka ta nemi attention dinshi koda kuwa trivial abu ne toh fa bari yake yi yayi attending to hidimar ta. Fahad yakan yi mamakin yadda ana zaune ana meeting sai yayi pausing just for her. Shi kam asali Fahad baya son Maleeka. he feels abokin shi deserves a better woman than her domin kuwa a yadda yake gani son da Maleeka take yi ma abokin nashi bai kai yadda yake sonta ba. According to him she doesn’t even care about him. Shin dagaske ne??5 Maleeka on the other hand itama bata son Fahad domin ta kula baya sonta. Ko maganar shi bata son ji.1 MK ya sani sarai basu son juna. Yayi iya qoqarin shi wurin clearing misunderstanding din da sukayi ma juna amma Sam abin ya qi. Akan dole ya haqura ya qyale su. The one thing da Maleeka take bragging akai shine MK bazai taba samun macen da zata yi substituting dinta a zuciyar shi ba. A cewarta he can never get a better lady wadda tayi achieving abinda tayi achieving ba a rayuwa.4 She is 100% sure cewar a zuciyar shi she is irreplaceable.7 Is it true???2 A yanzu haka bikin MK da Maleeka saura wata biyu Wanda gaba daya hidimar bikin yana hannunta. MK dai ya bata millions of naira Wanda zata yi amfani da su wurin hidimar bikin. Tun daga kayan lefenta har zuwa events da every other thing da take so. Maleeka kuwa sossai take planning bikin da ba’a taba yi ba a garin Abuja- her dream wedding. Shi kam MK dukda baya son events din da take lissafo mishi he had no choice.. as it is Maleeka is his life and he can never say no to her when it comes to fulfilling her dreams.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *