UMMI CHAPTER 7
MK SODANGI RESIDENCE ASOKORO+ Tsaye suke a bakin qofar main falon gidan yayinda take riqe da jakar Macbook dinshi gam ta qi saki. Kusan minti goma kenan da MK ya shirya zai tafi office amma Ummi ta tare hanya ta hana shi tafiya. Ji nayi yace “please Ummi let me go..” Girgiza kai tayi tace “ni kam kayi mun magana da yaren da nake ji…” Murmushi yayi yace “nace don Allah ki bari in tafi..” Kai tsaye tace “ka je ina wai?? Hamma babu inda zaka je yau… ka kuwa san irin damuwar da na shiga jiya a dalilinka??”3 Yace “sai kin fada… wanne irin damuwa kika shiga??” Tace “wallahi ji nayi kamar zan mutu lokacin da kanka ya tsananta maka da ciwo… Zuciyata sai zafi take yi. Gaba daya rayuwar nan ta daina yi mun dadi… da akwai yadda zan yi in cire ciwon kan in mayar a kaina da nayi. Hamma don Allah kar ka qara tayar mun da hankali har haka…”11 Shiru yayi yana murmushi yayinda yake kallonta. Kafin yayi magana ne wayar shi tayi ringing ya fiddo daga aljihun shi yace “kin ga an fara kira na ko???” yayinda yayi answering. Kafin ya kai wayar kunnen shi ne Ummi ta qwace wayar sannan ta kai kunnenta tace “don Allah ku qyale shi ya huta idan ba so kuke ku kashe shi ba…” Fahad wanda ya cika da mamaki yace “toh fa.. Ummi lafiya??” Ummi dai ta gane muryar Fahad don haka ne tace “Hamma wallahi jiya kanshi ya dinga ciwo cikin dare… da qyar ya samu sassauci. ka ga ai bai dace ya fita ba ko??” Shi dai MK sossai yake mamakin yarinyar da yadda take dictating mishi abu wanda yake kasa tsallakewa. Gaba daya ta sa yayi laushi yayinda ya ji lallai kawai fasa fitar zai yi. Fahad yana kwasar dariya yace “Lallai Ummi akwai ki da wayau.. tunda kin hana Hamma fita shikenan mun haqura. Sai kiyi qoqari ki kula da shi” Tana murmushi tace “Yauwa Hamma nagode” Ta miqa ma MK wayar yayinda ta sa mishi idanuwa. Ko da ya kai wayar kunnen shi ji yayi Fahad yace “ya kan naka ya sassauta??” Yana kallon Ummi yace “yes my friend.. her hands did the magic. I really am grateful for having her close to me” Fahad yana dariya yace “hmmm.. yanzu dai mun barka ka huta for today amma fa kar ka manta da tafiyar mu zuwa Lagos gobe da yamma.. our meeting is next tomorrow” Gani nayi ya dan shafa kan shi sannan yace “Okay my friend, thankyou. Incase akwai wani abinda zai buqaci attention dina just let me know..” Fahad yace “okay Sir, ka huta lafiya” Bayan sunyi sallama ne ya kashe wayar yayinda yake kallonta yace “toh yanzu da kika hana ni fita me zaki bani??” Tana murmushi tace “duk abinda kake so Hamma” A haka dai Ummi ta hana MK fita. A falon shi suka zauna inda ya sa ta dinga karanto mishi karatun Al-qur’ani yayinda yake ta jin dadin sauraron muryar ta. Kamar kullum tana yi yana gyara mata. Saboda dadin muryarta kuwa bai san lokacin da bacci ya kwashe shi ba. Da ta ankara kuwa murmushi tayi yayinda ta dauki wayarta ta fara buga game. Haka suka yini tare a yau. Sossai sukayi enjoying company din juna dukda ba wata hira suke yi ba. STORY CONTINUES BELOW Kusan rabin zaman nasu ma shi yana kallon TV ita kuma tana buga Game a wayarta. Lokaci-lokaci kuma sukan hada idanuwa suyi ma juna murmushi. One funny thing about them is idan dai suna kusa da juna ko kuma suna ganin juna basu damu da suyi ma juna magana ba.. they are okay. ************* Washegari!! A yau ne MK zaiyi tafiya zuwa Lagos tare da Fahad. Asali dai wani meeting zasuyi a Lagos din wanda manyan software engineers zasu halarta. Wuraren qarfe goma sha daya da rabi na safe MK yana tsaye yana hada kayan shi a cikin jakar tafiya yayinda jikin shi yake a sanyaye. Ya so zuwa ofis amma sam ya kasa. Ko da suka yi waya da Fahad sunyi akan zai biyo mishi su wuce airport tunda dai dama Fahad din ya gama shirya komai nasu na tafiyar kuma dama da private jet din MK zasu je they don’t need to make reservation na flight. Shi kam Allah ya sani baya son tafiyar domin kuwa baya so yayi nisa da yarinyar. Gani yake yi kamar idan baya kusa da ita wani mummunan abu yana iya faruwa da ita… Bai taba son zama kusa da wani abu a rayuwar shi ba kamar yadda yake son zama kusa da yarinyar. Bai taba son protecting wani abu nashi ba kamar yadda yake son protecting yarinyar.. Gani nayi ya rufe wadrobe dinshi yayinda ya shafa kanshi da hannu biyu yace “Ya salaam… wanne irin abu ne wannan??? meyasa kika shigo rayuwa ta Ummi?? me kike so??”2 Ajiyar zuciyar ya saki sannan ya dauko jakar ya fito daga closet din. Gani nayi ya ajiye ta a kan gadon shi sannan ya juya ya fita. Duqe take a tsakiyar falon yayinda take goge centre table. MK wanda ya fito daga dakin shi gani nayi ya jingina da bango yayinda ya sa mata idanuwa. Ba da son ranshi yarinyar take yin ayyukan da take yi ba toh amma it’s the reason why she is here.. Idan ya hana ta a matsayin me zata cigaba da zama a gidan??? Ummi wadda take aikinta ta sani sarai MK yana cikin falon amma ta qi juyowa domin kuwa gaba daya jikinta yayi sanyi tun da ta tashi daga bacci a yau. Gani nayi ta kwashe kayan aikinta ta miqe jiki a sanyaye zata bar falon. Bata ankara ba tayi tuntube wanda har sai da ta kusa faduwa. Da sauri yace “hey careful..” Ya qaraso wurinta da sauri ya karbi kayan aikin daga hannunta yace “me ke damun ki?” Kanta a duqe tana kallon yatsun qafafuwan shi kawai ta fashe mishi da kuka. Runtse idanuwa yayi ya bude sannan yace “don Allah ki daina kuka” Hannunta ya riqo ya ja ta ya zaunar da ita a kan kujera yayinda ya tsugunna a gaban ta yana kallonta. A yanzu itama shi take kallo yayinda take ta rusa kuka.. Farar fuskarta tayi Ja.1 MK wanda kukan yarinyar ke qona ranshi ne yace “Ummi don Allah ki daina kuka… tell me, me ke damun ki??” Cikin kuka tace “Hamma ji nake yi kamar wani abu zai faru” Muryar shi qasa-qasa yace “wani abu kamar me??” Tace “Ji nake yi kamar za’a raba ni da kai.. kamar bazan qara ganin ka ba…”8 Qara fashewa tayi da kuka tace “Hamma bana so a raba mu…” MK wanda yake sauraronta dai kamar yadda yarinyar take ji shima haka yake ji.. gaba daya jikin shi yayi sanyi a yanzu. Da sauri yace “sssshhhhh…” STORY CONTINUES BELOW Gani nayi ya kamo hannunta ya dunqule a cikin nashi yayinda yake bubbugawa alamar lallashi. Numfashi ya saki sannan yace “Ummi” Tace “na’am Hamma” Yace “kukan ki yana qona mun rai… ki daina kin ji?” Girgiza kai tayi yayinda ta koma sakin ajiyar zuciya. Ji tayi yace “tafiya zanyi anjima amma…” Da sauri ta miqe yayinda ta fashe da sabon kuka tana fadin “na shiga uku Hamma… ashe dama shiyasa nake ji a jikina…” Yana nan a tsugunne ne yace “Ummi dawo ki zauna ki saurare ni..” Maimakon ta zauna a kan kujerar sai ta zame ta zauna a qasa. Handkerchief ya fiddo daga aljihun shi yayi stretching hannun shi ya goge mata hawayen fuskarta yayinda ya zauna a gefenta yace “jibi da safe zan dawo…” Da sauri tace “don Allah Hamma ka dawo gobe” Kai tsaye yace “idan hakan zai sa hankalin ki ya kwanta toh kar ki damu, zan dawo gobe… amma fa idan har bazaki cigaba da kuka ba” Gani yayi ta karbi handkerchief din hannun shi sannan ta share hawayen ta. Ji tayi yace “kar ki damu zan dinga kiran ki a waya sannan duk abinda kike so ki fadi mun zan sa a kawo miki” Tana wasa da yatsun hannun ta ne tace “Hamma idan zaka kira ni ka kira ni irin wanda zan gan ka…” Yana murmushi yace “Video call??” Tace “yauwa video call” Girgiza kai yayi yana murmushi yayinda yace “an gama Babyn Hamma… Jira ni ina zuwa” Tana nan zaune ya tashi ya nufi hanyar dakin shi. Bayan dan lokaci sai ga shi ya dawo riqe da kudi bundle na 100k har guda uku ya zauna a gefenta yace “ga wannan” Miqewa tayi da sauri harda matsawa nesa da shi tace “Hamma na waye???” Yace “naki ne kuma sai kin karba..” Muryarta tana rawa tace “don Allah kayi haquri wallahi babu abinda zanyi da su” Miqewa yayi ya matsa kusa da ita yace “eh na ji.. karba ki ajiye. you might need it” Qara matsawa baya tayi tace “don Allah Hamma…” Kafin ta qarasa magana kuwa ya murtuke fuska yace “kina so rai na ya baci ne???” Da sauri ta karbi bundle daya tace “Kayi haquri Hamma.. sai dai in cire daidai yadda nake so don wallahi sunyi yawa” Murmushi yayi yace “toh cire yadda kike so” Gani yayi ta qirga 5000 naira ta cire sannan ta miqa mishi sauran” Qin karba yayi yace “ban gane ba.. dubu biyar fa…” Tace “wallahi Hamma wannan din ma babu abinda zan yi da shi.. zan ajiye maka idan ka dawo in baka kayanka. Ni kawai bana so ranka ya baci ne..” Fashewa yayi da dariya tare da mamakin halinta. Ya kula ma kamar kudi suna bata tsoro. Ji nayi yace “shikenan Ummi.. idan dai kina buqatar ko ma meye ki kira ni a waya zan sa a kawo miki kin ji??” Tace “toh Hamma nagode” ***************** Ko da Fahad ya zo daukar MK har wurin mota Ummi ta raka shi. Kana ganin fuskarta kuwa zaka hango damuwa sossai. A lokacin da zasu tafi kuwa sai gani yayi ta fara kuka. Ai kuwa sossai hankalin shi ya tashi yayinda Fahad yake mamaki. Shi kam ya sani sarai wata gagarumar soyayya ce a tsakanin abokin nashi da Ummi toh amma meyasa shi bai gane hakan ba???6 STORY CONTINUES BELOW Haka MK ya dinga lallashinta amma kamar ma qara ziga ta yake yi. Shi kuwa Fahad sai kallon su yake yi yana ta kwasar dariya. Dabara ce ta fado ma MK yana kallonta yace “ina wayarki??” Cikin kuka tace “tana falo a kan kujera..” Yace “toh je ki dauko ta.. zan kira ki video call.. don haka tun yanzu zamu fara hirar kin ji” Gani nayi ta dan yi shiru yayinda take ta goge hawayenta. Cikin rashin yarda tace “Hamma wayau zaka yi mun??” Ya fara dialing number dinta sannan ya nuna mata yace “see??” Murmushi tayi tace “toh Allah ya kiyaye hanya kuma ya baku sa’a akan abinda zaku je yi” Yace “ameen Babyn Hamma..thank you so much” Tace “Hamma kar ka kashe fa…” Yana murmushi yace “Go ahead Ummi..” Gani sukayi ta ruga a guje ta shige gidan yayinda Fahad yace “abokina what the hell have you done to this girl??” Girgiza kai yayi yace “the same thing she has done to me..” Fahad wanda ya tada mota ne yace “toh me kake jira ne??” Kafin ya amsa shi ne suka ji muryar ta a lokacin da ta amsa wayar. Daga nan fa suka shiga hira. Wasa wasa dai har suka yi boarding jet din MK na waya da Ummi yayinda Fahad yake ta mamaki. MK dai ya sha tambayoyi a wurin Ummi domin kuwa duk abinda ta hango a kusa da shi sai ta tambaye shi kamar wata ‘yar jarida. Da qyar ta haqura ta qyale shi suka yi sallama wanda kuwa ta dinga zabga mishi addu’o’i. ************* Washegari!! Zaune take a qasan kicin din da safe riqe da wayarta a hannunta yayinda take ta jiran kiran shi kamar yadda yayi mata alqawari. Ummi dai sossai tayi missing din MK.. Tunowa tayi a irin wannan lokacin da yana nan ta hada mishi cappucino wanda lokutta da dama idan ya shanye baya neman breakfast yake tafiya ofis. Gani nayi ta dora kanta a bisa gwiwarta yayinda na ji yace “Allah ya dawo da kai lafiya Hamma..” Wayarta ce tayi ringing yayinda tayi saurin answering. Gani nayi ta kafa ma screen din ido yayinda take neman inda zata ganshi. MK dai positioning wayar yayi yayinda yake qarasa shirin fita zuwa meeting din. Cikin ‘yar qaramar muryarta da yake so ce ya ji tace “Hamma kana ina?” Matsawa yayi kusa da wayar yace “Sorry Babyn Hamma… gani nan” Murmushi tayi yayinda tace “ina kwana..” Yace “kin tashi lafiya??” Tace “lafiya lau Hamma.. kana azumi yau??” A lokacin yana daura agogo a hannun shi ne yace “yes ina yi… ke fa??” Tace “Ina yi Hamma….” Yace “good girl… kiyi mun addu’a kin ji??” Tace “insha Allah” Murmushi yayi yayinda ya girgiza kai yace “Allah ya sani nayi kewar ki Babyn Hamma..” Ita dai sossai take so idan yana kiranta da wannan sunan- Babyn Hamma Tana murmushi tace “Hamma ina so idan kana kira na wannan sunan”2 STORY CONTINUES BELOW MK wanda yake fesa turare a lokacin yana murmushi yace “sunan ya dace da ke ai.. yarinya kyakyawa, fara sol mai halin kirki, mai addini, mai hankali da natsuwa wadda take ji da Hamman ta….”6 Fashewa tayi da dariya tace “Hamma duk ni kadai? nagode sossai” Yace “ni ne da godiya Babyn Hamma.. kinyi mun abubuwa dayawa wadanda har in mutu bazan manta ba.. Nagode sossai” Tace “yau zaka dawo??” Yace “Ba kin ce in dawo yau ba??” Ta girgiza kai alamar eh. Yace “yau zan dawo insha Allah.. duk abinda kike so shi zanyi Babyn Hamma” Sossai ta ji dadin kalaman shi yayinda tace “nagode sossai Hamma… Allah ya baku sa’a kuma ya dawo da ku lafiya” Yace “Ameen” Fahad ta hango a bayan MK wanda ya shigo dakin yayi mishi magana cikin harshen turanci. Tunda dai bata ji, bata san me yace ba. Gani tayi MK ya juya yayi mishi magana cikin harshen turancin shima sannan ya juyo yace “Ga Hamma Fahad ku gaisa” Ko da Fahad ya karbi wayar bata jira sun gaisa bane tace “Hamma don Allah kar ku bar shi yayi aiki dayawa saboda kar ciwon kan shi ya tashi… yana shan wahala fa dagaske” Fahad dai fashewa yayi da dariya sannan ya kalli MK yace “I swear she is crazy about you..” Ya juyo ya kalle ta yace “kar ki damu Babyn Hamma.. bazan bari kanshi yayi ciwo ba” MK ya karbi wayar yace “kema bana so ki ba kanki wahala da aiki tunda kina azumi.. ki je ki kwanta ki huta kin ji. idan na gama meeting din zan kira ki” Tana murmushi tace “toh Hamma nagode” Yace “in kashe??” Tace “dan tsaya..” Yace “what??” Tana kallon shi tace “kayi kyau” Fashewa yayi da dariya yace “nagode Babyn Hamma.. in kashe??” Tace “dan tsaya Hamma..” Yana murmushi yace “what again Ummi..” Shiru tayi tana kallon shi na dan lokaci sannan kuma tace “shikenan Hamma… kashe” Yana dariya yace “Okay Baby sai na kira anjima.. take care. Bye!!”1 Bayan sunyi sallama ne ta kashe wayar. Dago kan da zata yi ne zuciyarta tayi wani irin mugun bugawa a dalilin fuskar wadda ta gani. Maleeka!!15 Gani nayi ta yunqura zata miqe yayinda muryarta take rawa tace “Adda sannu…” Bata qarasa ba ta ji saukar wani mugun mari wanda ya sanya ta duqe qasa tare da sakin wayar hannun ta.2 Tuni ta fashe da kuka. Maleeka dai jiya da daddare ta dawo. Ko da ta nemi MK bata gan shi ba hakan ya tabbatar mata da yayi tafiya ne. A yanzu da safen nan ta fito ne don gani ko chefs sun gama breakfast.. ganin babu komai a dinning ne ta nufi kicin din. Tun tana daf da shiga kicin din ne take ta jin maganar yarinyar… A yadda ta ji kalaman da yarinyar take yi babu tantama da saurayinta ne. Abinda ya fara bata mamaki shine ina ta samu wayar?? ko kafin ta gama wannan tunanin kuwa ta jiyo muryar mijinta.. MK?? Cike da tsananin bacin rai Maleeka tace “Miji na??” Ummi wadda take kuka ta dago kai tace “Adda don Allah…” Maleeka ta qara kwashe ta da wani marin da ya fi na farko sannan tace “ashe dama karuwa ce ke ban sani ba? miji na??” Ta shaqo wuyan Ummi sannan ta hada ta da bango tace “Dan ubanki ki fadi mun abinda kike yi mishi da har yake kiran ki Baby sannan yake fadin bazai taba mantawa ba a rayuwar shi” Ummi wadda fuskarta tayi jajawur hawaye suna bin fuskar yayinda take ta kakarin amai ce tace “wallahi ban san me yake nufi ba Adda.. kawai..”2 Wani marin ta qara kwasa mata yayinda tace “Qarya kike yi munafuka… karuwar banza. look at you.. ‘yar qauye da ke.. illiterate without class, you dont have a single dime to your name, useless and worthless whore. Dan ubanki dama iyayen ki sun turo ki birni yawon karuwanci ne ko?? toh wallahi mai raba ni da ke yau sai Allah.. idan na kashe ki kuma na kashe banza.. shegiya munafuka kawai…Yau ko asiri kika yi mishi wallahi zan karya shi… ke da ganin shi kuma har duniya ta nade don barin gidan nan zaki yi..”3 Ummi dai bata ankara ba ta ji Maleeka ta fara dukanta ta ko ina yayinda take ta masifa tana fadin “Honey nawa ne ni kadai… babu wata macen da ta ta isa ta kusance shi bayan ni..” Sossai ta haukace kamar sabuwar mahaukaciya. Muciya ta hango ta ruga a guje ta daukota ta dinga dukan Ummi da shi. Wayar Ummi ma da ta gani a qasa kuwa sai gani nayi ta sa muciya tana ta buga ta yayinda ta tarwatse tayi kaca-kaca. Sossai Ummi ta sha duka a hannun Maleeka… Kuka kuwa tayi shi har ta gode ma Allah. Jikinta duk yayi ja ya kumbura a dalilin dukan da ta sha… Ga fuskarta da tayi ja.. bakinta da hancinta sai Jini suke yi. Haka Maleeka ta ja ta har zuwa dakinta yayinda tace “maza tattara kayanki ki bar mun gida..” Ummi dai ko gani bata yi sossai haka ta fara tattara kayanta yayinda take ta rusa kuka na fitan hankali.. tun tana ba Maleeka haquri har ta daina” Ummi dai ko kayan nata bata gama hadawa ba ta zuge zip din Ghana must go dinta domin kuwa sossai take cikin tashin hankali… Ga azabar radadi da jikinta yake yi. Maleeka kuwa har wajen gate din gidan ta ja Ummi da kayanta ta watsar da ita. Gaba daya ma’aikatan gidan suka zo suna ta bata haquri a dalilin ganin mummunar halin da Ummi take ciki amma Maleeka ta taka musu birki. Babu shiri suka natsu yayinda suke ta tausaya ma halin da yarinyar ta shiga. Mamaki suke yi akan wane irin laifi tayi mata da har ta shirga mata irin wannan dukan?? Ji nayi Maleeka tace “ki je inda ya dace da ke… brothel” Daga nan ta juya tayi tafiyarta. ♧♧♧♧♧♧♧♧♧ who saw this coming??😭😭 Lallai an zo wurin…MK SODANGI RESIDENCE ASOKORO+ Wuraren qarfe goma na dare ne security ya bude gate din gidan yayinda motar Fahad ta shigo. Security din ya duqa har qasa alamar yana gaida su… MK wanda yake riqe da wayar shi cike da tsananin damuwa bai ma kalle shi ba. Dayake glass din motar a dage suke horn kawai Fahad yayi mishi. A lokacin da suka kai porch din gidan ne MK ya bude qofa zai fita. Fahad ne yayi saurin riqo hannun shi yace “abokina ko in jira ka duba ta ne???” MK yace “kar ka damu… just go home and rest. incase of anything I will call you” Fahad yace “okay, take care” Ko da MK ya fito qofar baya ya bude ya cire jakar shi. Ma’aikatan gidan ne suke ta yi mishi barka da dawowa wanda gaba dayan su babu wanda ya kalla balle ya amsa. Daya daga cikin su ma da zai karbi jakar hannushi dakatar da shi yayi sannan ya shige cikin gidan. Fahad wanda yake kallon shi har ya shige cikin gida ne na ga ya girgiza kai sannan ya tada motarshi yace “it’s time you realise cewar son yarinyar nan kake yi abokina.. wannan damuwar da ka shiga is not normal” MK dai basu gama meeting dinsu ba sai gab da magrib.. bayan sun gama meeting din yayi ta kiran Ummi a waya amma a kashe. Hankalinshi yayi masifar tashi domin kuwa bai taba neman wayarta ya ji ta a kashe ba. lokutta da dama sai dai ya kira har ta gama ringing bata amsa ba wanda kuwa hakan yana nuna cewar bata kusa ne… but switched off?? why?? Aikuwa nan da nan suka shirya dawowa Abuja. Dayake dama da private jet din shi sukayi tafiyar babu wani bata lokaci suka kamo hanya. Daga airport zuwa gida ne ma suka bata lokaci saboda ‘yar tazara da keda akwai tsakanin airport din da gida. MK dai duk gudun da Fahad yake yi da motar Sam bai gani ba… gani yake yi kamar ma rarrafe yake yi. Sossai yake cikin damuwa. Sai addu’o’i yake yi akan Allah yasa Ummi tana nan lafiya.2 *************** Tsaye take a kusa da window na dakinta riqe da wayarta a kunnen ta yayinda ta hango shigowar su MK. STORY CONTINUES BELOW Maleeka dai bayan ta kori Ummi daga gidan komawa tayi ta kira Jameela a waya ta sanar da ita abinda ya faru yayinda take ta rusa mata kuka.. Jameela dai ba wani mamaki tayi ba da jin maganar because ta sani cewar with what is happening between them dole MK zai fara tunanin qarin aure.. abinda ma ya dan bata mamaki shine why the small girl?? Jameela dai calming dinta down tayi a lokacin yayinda ta gwada mata laifin ta a dukkanin abubuwan da suka faru sannan ta bata shawara akan ta jira ya dawo tayi confronting dinshi da maganar ta ji me zai ce. Aikuwa yinin ranar banda kuka babu abinda take yi.. Gaba daya ta zabga cikin yini guda saboda masifar kishi.5 A yanzu ma kukan take yi yayinda na ji tana magana da Jameela a waya tana fadin “Wallahi Jay bazan bari yayi mun kishiya ba… bai isa ba..”3 A dayan bangaren Jameela tace “calm down Leek… ba dai ya dawo ba?? toh please go and talk to him kuma I beg you banda girman kai.. ki bi shi ahankali don wallahi duk ke kika janyo abinda ya faru..” ************ MK dai ko da ya shiga gidan gani nayi ya jefar da jakar shi sannan ya nufi sashen da Ummi take zama. Hannun shi yana rawa ya qwanqwasa qofar dakin yayinda zuciyar shi take bugawa. Ko da ya ji shiru ne ya murda qofar ya shiga. Gani nayi ya tsaya cak yayinda zuciyar shi ta buga. Gaba daya dakin a hargitse yake.. da alama dai wani abu ya faru.. dukda kuwa ya ga wasu kayan ta a nan amma da gani yasan lallai ta bar gidan. Kan shi ne yayi mugun nauyi yayinda qafafuwan shi suka yi sanyi. Ji nayi yace “Inna lillahi wa’inna ilaihir raji’un… where is she??” Muryarta ya jiyo daga bayan shi tana fadin “kana neman wani abu ne??” Da sauri ya juyo yana kallon Maleeka wadda da ganin ta yasan ba daidai take ba domin kuwa duk tayi buzu-buzu. fuskarta tayi jajawur, ta ci kuka har ta gaji. Idanuwanta sunyi jajawur.. Kai tsaye yace “Ummi…” Bata bari ya qarasa bane wasu zafafan hawaye suka fara gangarowa daga idanuwanta yayinda ta dago hannu ta nuna shi da yatsa yace “wallahi baka isa ba..”4 Shi kam MK gaba daya ma hankalin shi baya tare da shi.. a yanzu haka da bai ga Ummi ba ji yake yi kamar zai mutu. Gani nayi zai ratsa ta gefenta ya fita wanda tayi saurin tare shi tace “babu inda zaka je sai ka gaya mun abinda kuke yi da yarinyar nan da har kake fadin bazaka manta da ita ba a rayuwarka.. ” Ta qara fashewa da kuka tace “…and you even call another girl Baby?? Honey why???” MK wanda ran shi yake a bace ne yana kallonta yace “matsa ki bani wuri..” Cike da masifa tana kuka tace “bazan matsa ba.. yanzu Honey duk soyayyar da ka nuna mun tun muna yara ta qarya ce?? ka rasa wadda zaka ci amana ta da ita sai ‘yar aiki?? qaramar yarinya??? ‘yar qauye wadda ko karatu bata yi ba?? what does she have da har zata yi takara da ni?? toh albishirinka… nayi mata dukan banza kuma na kore ta kuma bazaka qara ganinta ba.. Ni Maleeka ni kadai ce matar ka a duniyan nan kuma bazan taba bari ka auri wata mace ba bayan ni”9 MK wanda ya runtse idanuwan shi ne ya bude cike da tsananin tashin hankali ya ratsa ta gefen ta ya fito daga dakin. Bayada lokacin Maleeka a yanzu.. the only one person on his mind is the girl- UMMI!!3 Ganin yayi watsi da ita ne ta bi bayan shi sannan ta shiga gaban shi tana kuka tace “idan na qara ganin karuwar yarinyar nan sai na kashe ta… I promise you”4 STORY CONTINUES BELOW Ban ankara ba na ga ya shaqo wuyanta ya hada ta da bango.5 Maleeka kuwa kuka ta cigaba da yi yayinda ta riqe hannun shi tana ta kakarin amai. Nan da nan fuskarta tayi jajawur a dalilin mugun shaqar da yayi mata. Da idanuwan shi wadanda suka qanqance suka yi jajawur yake kallonta cikin ido yace “idan kika qara zagin Ummi sai na wulaqanta ki… just leave me alone” Ya sake ta yayinda ya juya ya bar wurin… Sossai Maleeka ta tsorata da yanayin da ta ga MK a yanzu.. Tun da ta taso a rayuwarta bata taba ganin shi a irin wannan yanayin ba. Zubewa tayi a qasa riqe da wuyanta wanda yake yi mata mugun zafi ta cigaba da rusa kuka kamar zata mutu yayinda ta dinga zabga tari.3 Cike da mamaki tana kuka na ji tace “zai wulaqanta ni a dalilin ‘yar aiki?? kenan ya fi sonta akan ni Maleeka?? wallahi baka isa ba.. ni kadai ce macen da ta dace da kai…”7 Miqewa tayi kamar mahaukaciya ta nufi dakinta da gudu ta dauko dan qaramin gyale da makullin mota ta fito.2 Haka ta wuce ta fita tana ta rusa kuka. Ni kuwa nace ina zata je???3 ♧♧♧♧♧♧♧♧♧♧ MUHAMMAD SODANGI RESIDENCE MAITAMA Mamy ce zaune a falonta tare da Hafsah suna kallon TV sannan suna hira. A wannan lokacin kuwa kusan qarfe Goma sha daya na dare domin kuwa sun ma fara haramar zuwa dakunansu su kwanta. Ganin Maleeka sukayi ta fado musu a birkice yayinda take ta rusa kuka kamar zata mutu. Cike da tsananin mamaki Mamy tace “Subhanalillah Maleeka me ya faru??? ya akayi kika fito cikin wannan daren??? MK din bai dawo bane??” Maleeka dai fadawa tayi jikin Mamy yayinda sautin kukan ta ya qaru. Hafsah wadda ta koma kusa da su hankalinta a tashe tace “Ya Maleeka wani abu ya samu Ya MK ne??” Ganin tana ta rusa kuka ba tare da tayi responding bane Hafsah ta janyo wayarta tayi dialing number din MK amma har ta gama ringing bai amsa ba. Kallon Mamy tayi tace “baya picking” Mamy wadda take shafa kan Maleeka ce tace “yi shiru ki daina kuka… tell me, me ke faruwa???” Cikin kuka ne Maleeka tace “Yana cin amanar auren mu da mai aiki na…” Mamy tace “Subhanalillah..” Yayinda Hafsah tace “what??” Mamy ce tace “da mai aiki?? ban gane ba.. Yaushe aka yi auren naku da hakan zai fara faruwa? Me ya samu MK a qwalwa da zai yi hakan? maza yi mun bayani in ji” Daga nan fa Maleeka ta basu labarin abinda ya faru da safe da yadda tayi ma Ummi duka ta kore ta amma fa bata fadi musu ita laifin da tayi mishi ba before this…1 Mamy dai tunda ta fara bada labarin take salati. Ita kuwa Hafsah shiru tayi tana tunani. Tabbas ta san cewar Ummi holds a special place a zuciyar yayanta. idan ma an ce sonta yake yi bazata musa ba domin kuwa abinda ta gani da idanuwanta ya tabbatar mata da lallai akwai connection mai qarfi a tsakanin su. Ji suka yi Maleeka tana fadin “Mamy mutuwa zanyi idan yayi mun kishiya…” Mamy ce ta rufe bakinta yayinda tace “yi shirun ki Maleeka… yanzu abinda nake so da ke shine kiyi haquri mu bari zuwa gobe da safe zan kira shi ya zo muyi maganar.. ina so in ji daga bakin shi. Idan banda shirme duka auren naku wata nawa da har za’a fara samun matsala irin wannan? bari zai zo ya same ni ai” STORY CONTINUES BELOW Ta kalli Hafsah tace “tashi ki kai ta daki ta kwanta ta huta..” Hafsah ta miqe yayinda ta janye Maleeka suka yi ma Mamy sai da safe suka nufi sashenta. Haka suka tafi suka bar Mamy tana ta masifa yayinda na ji tana fadin “kayi sa’a Abban ku baya nan da abinda zai biyo baya ya fi haka amma dukda haka bazan qyale ka ba… Ka wulaqanta ‘yar uwar ka a kan mai aiki.. Allah ya kai mu gobe lafiya…..” ♧♧♧♧♧♧♧♧♧♧♧♧♧ MK SODANGI RESIDENCE ASOKORO Zaune yake a qasan dakin shi yayinda ya jingina da ottoman din gadon shi ya dora kanshi a bisa gwiwar shi. Kusan minti talatin yana nan zaune a wannan position din. Magana na ji ya fara yi wanda na kasa jiyowa. Ko da na matsa ji nayi yace “Inna lillahi wa’inna ilaihir raji’un… Ummi why will you leave me at a time like this one?? ya zanyi da rayuwata idan babu ke?? meyasa kika tafi baki jira ni ba??”2 Gani nayi ya zabura ya miqe yayinda ya fita daga dakin. Bai tsaya ko ina ba sai study dinshi inda control na CCTV cameras din gidan suke. Gani nayi ya zauna ya kunna yayinda ya dinga duba cameras din gidan. Hankalin shi ne yayi matuqar tashi ganin lokacin da Maleeka ta ga yarinyar tana waya da shi a kicin da dukkanin maganar da suka yi zuwa yadda tayi mata dukan tsiya. Zuciyar shi ce ta dinga zafi ganin yadda Maleeka ta dinga dukan ta da muciya wanda take ta kuka… Ji yake yi kamar a jikin shi dukan yake sauka. Gani nayi ya dafe kanshi yayinda idanuwan shi suka yi jajawur. Wata camera ce ta hasko mishi lokacin da Ummi ta fito daga daki riqe da Jakarta yayinda Maleeka ta dinga ball da ita har tsakar gida… Kan cameras din da suke haska waken gidan ya koma inda ya ga Ummi a lokacin da Maleeka ta jefa ta waje… Duqawa tayi a wurin da ta fadi yayinda take ta kuka. Ta dade a wurin tana rusa kuka wanda daga baya ta miqe ta dauki Jakarta sannan ta kalli hagunta da dama… da alama she is confused akan ta inda zata bi. Finally ta bi dama wanda daga nan bai qara ganinta ba… ji yayi kamar ya riqo hannun ta ya hana ta tafiya amma inaaa…. Gani nayi ya miqe dafe da kan shi ya fito daga Study din ya shige dakin shi. Fadawa yayi bisa gado yayinda ya dinga jero addu’o’i kala kala domin kuwa zuciyar shi ta daina zafi a yanzu.. Quna take yi!! Gani nayi ya dafe zuciyar shi wadda ta cigaba da quna… Kan shi kuwa tamkar zai fashe saboda tsananin ciwo. Ji nayi yace “Meyasa na tafi na barki ke kadai??? me yasa ban tafi da ke ba?? I need you very close to me??? I just cant continue without you.. wa zai kula dani idan babu ke Ummi? you have become an important part of my life.. baki sani cewar babu abinda zan iya yi a rayuwar nan idan babu ke a kusa da ni ba Ummi?? meyasa baki jira ni ba?…” Haka dai ya dinga surutai iri-iri yayinda ya shiga wani hali… Gaba daya ya birkice. Sossai na tausaya mishi domin kuwa lallai na tabbatar Ummi itace rayuwar MK a yanzu. toh wai tana ina ne??? ************* Washegari!!! Wuraren qarfe takwas na safe ne motar Mamy qirar Mercedes Benz Formatic SUV GLE- 350 ta shigo gidan. Hafsah ce take tuqawa yayinda Maleeka take gefe sai Mamy wadda take zaune a owners corner a baya. Masu aikin gidan ne suka rufe motar yayinda suke ta kawo musu gaisuwa. Mamy da Hafsah dukda suna cikin damuwa sun saki fuska sun amsa cikin fara’a. ita kuwa gimbiyar ko kallo basu ishe ta ba dukda dai dama cikin tashin hankali take. Daga jiya zuwa yau duk ta bi ta lalace.. fuskarta ta kumbura saboda kuka ga rashin bacci. Kai tsaye suka shiga cikin gidan.. Sashen MK suka nufa domin kuwa sossai Mamy take buqatar yin magana da shi tun kafin maganar ta kai kunnen Abba. Mamy da Hafsah sunyi zaune a babban falon MK yayinda Maleeka ta nufi dakin shi don kiran shi. Tana bude qofar dakin nashi ne na ga tayi freezing a tsaye. Wani irin ihu ta saki wanda ya sanya Mamy da Hafsah suka nufi dakin da sauri don ganin abinda ya faru… Me ya faru???3 ♧♧♧♧♧♧♧♧♧ MK SODANGI RESIDENCE ASOKORO+ Kwance yake a kan gadon dakin shi yayinda yake bacci. Cannula ce maqale a hannun shi yayinda na’urar EKG take kafe tana aikinta na monitoring heartbeat dinshi. Yinin yau dai MK yana kwance bai san inda kan shi yake ba.6 Gaba daya hankulan su Mamy a tashe yake. Dr. Davis wanda ya kammala wasu rubuce-rubucen shi ne ya miqa ma nurse file din sannan ya juyo ya kalle su. Ko kafin yayi magana ne Daddy yace “Doctor how is he?? is it related to his migraine??” Dr. Davis ya gyara glasses din idanuwan shi yayinda ya girgiza kai yace “it’s not his migraine Alhaji.. this is a bit related to his heart. he is having a serious high blood pressure right now.. A normal blood pressure should be reading 120/80mmHg but presently his blood pressure is reading 140/90mmHg which is bad” Mamy wadda ta cika da tsananin damuwa tace “how bad Doctor??” Yace “Hajiya right now we need to do everything possible to make sure his blood pressure doesn’t rise above the present reading because it could result to hypertension and further resulting to hypertensive crises…” Jin haka kuwa ya sanya su suka fara zabga salati . Fahad wanda yake tsaye yana sauraron likitan sossai hankalin shi ya tashi. Ya sani sarai koma menene yake damun abokin shi is related to Ummi… Jiya bayan ya koma gida yayi ta kiran wayar shi har ta gama ringing baiyi picking ba. there and then ya gane akwai matsala wanda ganin dare yayi sossai ne ya haqura ya bari sai yau da safe ya zo gidan don ganin abinda yake faruwa. Gyaran murya yayi yace “uhm doctor, what do you think is the reason behind the high blood pressure??” Dr. Davis ne yace “well, we all know that Mr. Muhammad Kabir is a workaholic.. it could be stress..”2 Maleeka wadda tayi saurin dagowa ta kalli Mamy ce tace “Mamy dagaske babu wani stress.. wallahi a dalilin wannan karuwar yarinyar ce..” Mummy da Daddy ne suka ce “what??” Fahad wanda ya ji kalaman Maleeka kuwa a yanzu yayi decoding komai… Gani nayi ya runtse idanuwa ya bude yayinda ya ji Maleeka tana basu labarin abinda ya faru da yadda ta kori Ummi daga gidan har zuwa threatening dinta da MK yayi akan zai wulaqanta ta idan ta qara zagin Ummin. Daddy da Mummy dai sun cika da tsananin mamaki. Dukda Maleeka diyar su ce ko kadan basu yarda da zancen ta ba domin kuwa sun san halinta sarai sannan sun san halin MK, ko da akwai qamshin gaskiya a zancen ta sun tabbatar there is more to the story. Ji nayi Daddy yace “Maleeka listen to me.. tunda kin kori yarinyar shikenan. I dont want to hear about this anymore… Kin ji ni ko??” Tace “amma Daddy…” Yace “shut up Maleeka… nace zancen ya wuce and its final. come up with the issue again and I will deal with you” Mummy cikin fada tace “yanzu don ma baki da tausayi ya zakiyi ma ‘yar yarinyar duka?? me ya hana ki kira ni? ai da na aiko an tafi mun da ita tunda ni na dauke ta aiki.. yanzu duk ranar da Rakiya ta dawo neman ta me zan ce mata? gashi ban san garin su ba..” STORY CONTINUES BELOW Cikin kuka Maleeka tace “toh Mummy ni me ya ruwa na da ita??? wallahi duk wata macen da ta kusanci Honey sai na lahanta ta..” Mummy ta dago hannu zata zabga mata mari yayinda Mamy tayi saurin kareta tace “yi haquri Mummy.. ni kaina wannan abu ya daure mun kai.. duka duka wata nawa da yin auren su har an fara samun matsala irin wannan? Banda don Daddy yace a manta da zancen ai da sai nayi confronting dinshi…” Haka dai suka cigaba da tattaunawa akan zancen yayinda Hafsah da Fahad suke ta sauraron su. Su kam ai sun sani cewar akwai wani abu a tsakanin MK da Ummi dukda shi din ya qi acknowledging. thank God ma da Daddy yayi dismissing case din domin kuwa Maleeka is no doubt saying the truth. Maleeka dai sossai ta ji haushin hukuncin da Daddy ya yanke… dukda hakan kuwa ta qudurta a ranta cewar it’s not over.4 A yanzu haka she has made up her mind akan zata yi watsi da shi.. idan ya samu lafiya zai dawo ya bata haquri sannan su cigaba da zaman auren nasu..12 Kun ji Maleeka fa!!2 Dr. Davis wanda ya gama dudduba MK ne ya juya yayi ma nurse din wani bayani sannan ya kalli su Mamy yace “please he shouldn’t be pressurised or stressed with anything until he recovers fully… I will leave my nurse here to keep monitoring him and I will drop by later to check on him” Bayan sunyi mishi godiya ne ya tafi. Daddy ne ya kira Abba a waya ya sanar da shi halin da MK yake ciki… Ya buqaci a cigaba da updating dinshi before he returns tomorrow. ♧♧♧♧♧♧♧♧♧ Wuraren qarfe Goma saura na dare ne ya bude idanuwan shi. Hafsah da Fahad ne kawai a dakin. Sai nurse wadda take ta monitoring dinshi. Mummy da Mamy dai suna falo.. Maleeka kuwa tana sashen ta tana wanka.2 Daddy kuwa ya tafi gida wanda yake ta kiran waya akai-akai don jin update. Muryar shi qasa-qasa yace “Ummi where are you..” A wannan lokacin kuwa tuni nurse din ta tashi tana dudduba yanayin jikin shi. Hafsah da Fahad ne suka kalli juna yayinda Fahad din yayi saurin matsawa daf da shi yace “abokina please relax… ka daina kiran sunan Ummi akwai tension yanzu haka.. let’s talk about it later”3 Gani nayi MK ya runtse idanuwan shi yayinda ya dafa kan shi. Hafsah ce ta kalli Nurse din tace “how is he doing??” Nurse din wadda take ta dudduba shi ce tace “I am not sure ma’am, let me call Dr. Davis” Hafsah ta fita yayinda ta sanar da su Mamy cewar MK ya farfado. Aikuwa da sauri suka shigo dakin yayinda suke ta gode ma Allah. Gaba dayan su sun zagaye shi yayinda ake ta yi mishi sannu. Idanuwan shi a rufe yake amsawa. Shi kam babu abinda yake so irin ya bude idanuwa ya ga Ummi. babu abinda yake son ji irin muryar ta mai dadin gaske.. Zuciyar shi ce take ta zafi yayinda yake ta faman tunanin halin da take ciki a yanzu. Shin ta koma gidan su ne?? ta kai azumi da take yi kokuwa wahala ta sa ta karya shi??? ciwon da Maleeka ta ji mata yana zafi?? ta samu tayi treating??? shin ina zai ganta ya dawo da ita cikin rayuwar shi???10 Bai ankara bane ya ji muryar Maleeka tana fadin “Ya farfado??”2 A wannan lokacin kuwa ji yayi kamar ya rama dukan ta tayi ma Ummin shi. Gaba daya ma ji yayi baya so ta matso kusa da shi saboda mugun haushinta yake ji. STORY CONTINUES BELOW Maleeka why??? Yana Jinta ta haye bisa gadon yayinda suke wasu hirar da bai sani ba.3 **************** Bayan Dr. Davis ya dawo ya qara duba jikin nashi dai ya tabbatar musu cewar zai samu lafiya amma kar a matsa mishi da hayaniya saboda yana buqatar hutu sossai.2 Bayan likitan ya tafi ne Fahad ma yayi musu sallama. Kamar kullum dai Maleeka ko kallon shi bata yi ba domin kuwa ta sani sarai harda hadin bakin shi ake yi mata abinda ake yi tunda dai dama ta san baya sonta kamar yadda itama bata son shi.. Fahad dai ko da ya tafi ya sani sarai abokin nashi ba bacci yake yi ba.. a dalilin jin Maleeka zaune kusa da shi ne yayi kamar yana bacci domin kuwa a yadda ya san halinshi da abubuwan da suka faru ya tabbatar Maleeka has pushed him to the wall wanda ya san sai ta lallaba shi sannan ya sauko… Hakan kuwa abu ne mai wuya considering her nature na Gadara.8 Mummy da Mamy ma komawa gida suka yi ganin jikin nashi babu laifi dukda dai baya magana yayinda suka bar Hafsah tare da Maleeka. ♧♧♧♧♧♧♧♧♧♧ A yau kwana biyu kenan da MK ya kwanta. Har yanzu dai baya wani maganar kirki.. a koda yaushe zaka gan shi da idanuwa a rufe kamar mai bacci amma sam ba bacci yake yi ba… tunaninta kawai yake yi. Abba ya dawo ya duba jikin nashi.. Ya so a fitar da shi turai a duba shi amma Dr. Davis ya gwada musu babu wani matsala… by the time da zuciyar shi ta samu hutu sossai he will be fine. Shi kuwa Fahad tun ranar da wannan al’amari ya faru yake so yayi having private conversation da abokin nashi amma babu chance. It’s either Maleeka tana nan ko kuma su Mummy wadanda baya iya ce musu suyi excusing dinshi. *********** Kwance yake a dakinshi da idanuwan shi a rufe kamar kullum. Hafsah ce take zaune a gefen shi riqe da wayarta yayinda take ta chatting da Sadiq saurayinta kuma wanda zata aura domin kuwa har an sa bikin su nan da wata biyar masu zuwa. Fahad ne ya qwanqwaso qofar sannan ya shigo cikin sallama. Hafsah ta dago kai ta amsa sallamar yayinda suka gaisa. Fahad ne yace “ya jikin nashi??” Tace “Alhamdulillah..” Fahad wanda ya samu opportunity na yayi magana da MK ne yace “uhm.. Hafsah can you please give us a moment? ina so inyi magana da shi” Hafsah ta kalli MK tace “bacci yake yi ai…” Murmushi yayi yace “please Hafsah..” Tace “okay” Har ta miqe zata fita ne yace “Maleeka fa??” Tace “yanzu aka kira ta daga boutique dinta ana son ganinta and its urgent..” Ji nayi yace “perfect”2 a ranshi kuwa yace “which foolish woman leaves her sick husband to attend to some stupid business???”5 Nikuwa nace sai Maleeka… Tsaki yayi sannan ya nufi wurin MK ya zauna gefen shi a kan gadon. Aikuwa Hafsah tana rufe qofa ne na ga MK ya tashi zaune da sauri ya riqe hannun Fahad yace “abokina I need her back in my life… don Allah ka taya ni neman ta” Fahad wanda ya matse hannun MK a nashi ne yake mamakin yadda abokin shi ya rame a cikin qanqanin lokaci… because of the girl??2 Ji nayi yace “calm down my friend… it’s the reason why I am here. I have been looking for a chance da zamu yi magana but babe dinka da su Mamy are always present… Yanzu abinda za’ayi kawai ka bani details dinta..” MK ya shafa kanshi da hannuwan shi biyu cike da tsananin damuwa yace “wallahi bani da details din..” Kafin ya rufe bakin shi ne Fahad yace “what?? ban gane ba… kana nufin baka san daga ina ta zo ba??” Ya gyara zama cike da mamaki yace “wait amma dai ka san full sunan ta ko???” MK dai runtse idanuwan shi yayi ya bude yayinda ya dafa kanshi wanda ya fara yi mishi ciwo a yanzu. Shi kam he just realised cewar he is in a serious trouble.. like he doesn’t know anything about the girl… toh ya aka yi haka??!! Fahad dai ji yayi yace “abokina wallahi ban sani ba… UMMI kawai na sani…”1 nace what??? Fahad ya girgiza kai yace “haba MK.. Ummi ai ba suna bane… she must have a name ai. duk ba wannan ba ma, ya akayi baka taba sanin komai akanta ba??? I thought she shared her story with you.. kana nufin duk zaman da kuka yi da ita baka taba tambayarta labarinta ba??”6 Muryar shi qasa-qasa yace “I swear nima ban san ya akayi haka ba.. Abokina wallahi with Ummi close to me, I tend to forget every other thing a rayuwar nan.. being with her made me think she is part of me.. like everything about her is about me… I see her like a reflection of me.. I just.. I just…”4 Ya runtse idanuwan shi sannan ya bude yace “right now babu abinda zan iya yi idan yarinyar nan bata dawo kusa da ni ba. please I beg you.. help me find her”2 Babban magana… Fahad yana kallon abokin shi ya dan yi shiru yana tunani sannan yace “abokina gaskiya without her details zai yi wuya a gano Ummi.. Nigeria has a population of over 200million people.. sannan there are thousands of Ummi dispersed across the states in the country… it would have been very easy da ace turai ne tunda suna da accurate database but Nigeria?? ta ina zamu fara???” Kai tsaye MK yace “I don’t care Fahad.. just send out people- Secret service agents, the police, the military if possible.. duk wani search team da ka sani a qasan nan please engage them… su je su nemo mun Ummi. Use as much Human and Financial Resources as you need… the only thing da nake so shine a nemo ta, I want her back in my life ASAP” Fahad dai a yanzu al’amarin MK ya ma daina bashi mamaki domin kuwa ya tabbatar idan ba’a gano mishi Ummi ba akwai babban matsala. Ajiyar zuciya ya saki sannan yace “I will see what I can do abokina… amma ina da tambaya” MK yace “go ahead” Yace “idan aka gano ta me zaka yi?? auren ta zaka yi??? ka dai san zaman ta a gidan nan a matsayin ‘yar aiki bazai yiwu ba ko???”2 Gani nayi ya shafa kanshi da hannuwan shi biyu cike da tsananin confusion yayinda ya kasa ba abokin nashi amsa…4 Habawa.. ♧♧♧♧♧♧♧♧♧