UMMI CHAPTER 9

UMMI CHAPTER 9

Bello (Baffa) da Ibrahim (Hardo) sun kasance ‘yan uwan juna.. uwar su daya sannan uban su daya.+ Asalin su fulani ne na qauyen Rugange a cikin qaramar hukumar Yola ta Kudu (Yola South). Wadannan mutane sun kasance suna da qanwa mai suna Aminatu (Goggo) wadda uban su daya amma Uwar ta daban. Asali dai mahaifiyar Aminatu ta rasu tun lokacin tana ‘yar shekara Goma don haka ne ta girma a wurin mahaifiyar su Bello. Mahaifin su ya kasance yana da rufin asirin shi daidai gwargwado a lokacin da yake raye domin kuwa yana da gida harda gona. Bello yayi aure tun lokacin iyayen su suna raye. Ya auri Saratu (Daada) wadda itama a nan qauyen Rugange ta girma. Da farko dai iyayen shi basu so ya auri Saratu ba domin kuwa babu wanda bai san halin mahaifiyarta ba.. Sossai take bin malamai… Mahaifin Saratu ya zama tamkar hoto a gidan domin kuwa juya shi take yi tamkar yadda ake juya waina a tanda. Dayake dai an riqe Bello da asiri tun kafin auren sossai ya kafe akan lallai shi Saratu zai aura. Sai da aka kai ruwa rana sannan dai iyayen nashi suka amince ba don sun so ba. Saratu dai irin matan nan ne masu tijara. Tun sirikan ta suna raye suke kuka da halinta. Saratu bata da kirki ko alama sannan bata girmama na gaba da ita. Saratu tana zaune tana kallon sirikar ta tana aikace-aikacen gida amma bata taba taimaka mata. Kullum sai jefa qananan maganganu marassa kan gado. Shi kan shi mijinta Bello ta raina shi sossai.. duk abinda tace shi yake yi. Gaba dayan su gidan babu wanda take kallo da idon mutunci. Anyi bikin Bello ba da dadewa bane Allah ya dauki ran mahaifin su Bello a sanadiyyar kwanciya jinya da yayi. Sossai Iyalin shi suka ji rasuwar shi amma kuma ya zasu yi?? dole su rungumi qaddara su cigaba da yi mishi addu’a kamar yadda suke yi ma Mahaifiyar Aminatu da daukacin Musulmin da suka riga mu gidan gaskiya. Bayan shekara daya da rasuwar mahaifin su Bello ne Aminatu ta samu miji itama tayi aurenta yayinda ta zauna a gidan mijinta wanda akwai ‘yar tazara da gidan su. Asali mijin da ta aura kuwa sunan shi Musa dan gidan mai Unguwa.. babu laifi yana da rufin asirin shi daidai gwargwado domin kuwa a lokacin gidan Musa yana cikin gidajen da suka fi kyau a qauyen.. gida ne gini na siminti ba na qasa ba. Bello dai sana’ar trader yake yi a kasuwa. shi kuwa ibrahim tunda ya girma yake bin manyan motoci suna kai kaya garuruwa don haka ma shi ba mai yawan zama a gida bane. A duk lokacin da ya dawo kuwa yana fuskantar matsaloli da dama daga wurin Matar yayan nashi. Baya jin dadin ganin yadda take yi wa mahaifiyar shi wulaqanci iri-iri. Ko da ya zaunar da Bello yayi mishi magana sai Bello ya hau shi da fada akan an sa ma matar shi ido.. Ya buda wuta akan duk wanda ya kafa ma matar shi tsana zasu sa qafar wando daya da shi. Mahaifiyar su ce ta tausa Ibrahim ya manta da zancen. A haka dai aka cigaba da zama dukda dai zaman babu dadi domin kuwa rigimar Saratu ta safe daban sannan ta yamma daban. Ana cikin haka ne Saratu ta samu cikinta har ya girma ta haifi yaro namiji wanda ya ci sunan mahaifin su Bello wato Abdullahi. Bayan shekaru Uku da haihuwar Abdullahi kuwa Mahaifiyar su Bello itama Allah yayi mata rasuwa. STORY CONTINUES BELOW Sossai Bello da Ibrahim suka ji mutuwar mahaifiyar su musamman Ibrahim wanda ya shaqu da ita sossai. Akan dole suka haqura suka cigaba da yi ma iyayen su addu’a. Shekara daya da rasuwar Mahaifiyar su ne Ibrahim ya zo ma yayan shi Bello da zancen ya samu matar da yake so ya aura. Ibrahim dai ya hadu da Shatu a qasar Cameroon a wani zuwa da suka yi kai kaya ta border. A wannan tafiyar ne ya ganta wanda kuwa basu samu suka fahimci juna ba sai da ya dawo sannan ya koma da shiri. Bello kuwa ya ji dadin jin cewar qanin shi ya samu matar da zai aura. Anan dai aka gabatar da juna akayi abubuwan da suka dace.. a dalilin an fahimci juna kuwa aka sa rana. Saratu dai jin cewar Shatu ‘yar Cameroon ce duk ta bi ta tsane ta tun kafin auren.. dama kuma shi kanshi Ibrahim din bata son shi a dalilin gani da tayi ya fi mijinta Bello samu tunda shi Bello trader yake yi a kasuwan nan qauyen Rugange. Aikuwa dai ko da aka yi auren ta ga Shatu sai ta haukace gaba daya domin kuwa Shatu kyakyawa ce ajin farko… Fara ce sol kamar tsada, ga dogon gashi wanda ya sauka bayan ta sossai. Shatu dai tana da shape irin wanda ake kira hour glass sannan gata da hankali, tsabta, addini tare da girmama na gaba da ita.1 Tunda Shatu ta zo gidan kuwa Saratu ta sa mata ido ta hana ta sakewa ko alama gashi dama ita Shatun bata iya rigima ba. Zaman nasu sai ya kasance kamar kishiyoyi. Gaba daya aikin gidan kuwa Shatu ce take yin shi… Shatu dai har abincin gidan ma ita take yi. Sossai ta iya girki.. A kullum ana ci ana santi amma fa banda Saratu wadda yau tace yaji yayi yawa sai gobe tace gishiri yayi yawa jibi kuwa sai tace abincin yana warin quna. Dayake Shatu tana da addini sossai duk dare tana tashi tayi sallolin nafila tayi ma mijinta addu’a sannan tayi ma kanta na neman tsari daga sharrin maqiya da mahassada. A dalilin duk dare takan fito tayi alwala don gabato da sallolinta ne ya sanya Saratu ta sa mata idanuwa tare da yi mata sharrin wai mayya ce. Wai a kullum sai kowa ya kwanta bacci take fitowa tana qaryar alwala nan kuwa maita take yi. Sharri dai kala-kala amma sam daidai da rana daya Shatu bata taba kula ta ba. Ibrahim dai dayake yana samun kudi a sana’ar shi a duk dawowa yakan zo da tsaraba kala-kala wanda kuwa har Aminatu yana aika mata da nata ta sanya albarka itama. A duk lokacin da za’a ba Saratu nata ta dinga qorafi kenan akan an ba Shatu kaya masu kyau an bata na banza (kamar mijin ta ya siya)2 A shekarar da Shatu ta zo gidan ne ta samu ciki, a lokacin kuwa itama Saratu tana da ciki wata hudu. Haka dai suka cigaba da rainon cikin su yayinda suke zaune kamar kishiyoyi. A lokacin da Saratu ta haihu ne ta samu mace mai kama da ita sak. Yarinya dai baqa ce sannan mummuna. Ta ci sunan Mahaifiyar su Bello wato Fatima amma ana kiranta Binto. Bayan watanni kuwa itama Shatu ta haifo Babyn ta ‘yar mace kyakyawar gaske mai kama da ita sak. Yarinya dai fara ce sol kamar uwarta sannan ko a matsayinta na jaririya da gani zaka san lallai zata yi gashi… gashin har gaban goshinta. Aikuwa tun da Saratu ta ga jaririyar sai ta hau baqin ciki. Sossai yarinyar ta tsole mata idanuwa. Gashi tunda ‘yan qauyen suka ji labarin an haifi jaririya kyakyawar gaske ne aka dinga zuwa gidan barka yayinda ake ta sanya mata albarka. Hakan kuwa ya dinga qona ma Saratu rai domin kuwa lokacin da ta haifi Binto ko 20% din wadanda suka zo barkan wannan yarinyar bata gani ba. Ranar suna kuwa ta ci sunan Mahaifiyar Shatu wato Umm Aimaan amma ana kiranta Ummi. Aikuwa mutane sun halarci sunan sannan yarinyar da mahaifiyarta sun kwashi kayan suna. STORY CONTINUES BELOW Yarinya dai farin jini gareta sossai. Saratu kuwa kamar zata mutu don baqin ciki. ********** Haka dai suka cigaba da rayuwa.. Daada (Saratu) tana nan da tijarar ta. Baffa (Bello) dai yana nan sai abinda tace yayi shi yake yi. Sossai ta riqe shi da asiri. Tunda Ummi ta taso ne take bala’in son kifi a rayuwarta. A kullum idan Abbanta zai dawo sai ya kawo tsarabar kifi a dalilin Ummi. Haka Ummanta take zama tana cire mata qaya tana bata wanda kuwa yau da gobe ta koya itama har ta koma cirewa da kanta. Babu laifi Ummi ta taso cikin gata na iyaye domin kuwa duk abinda take so wanda bai fi qarfin su ba suna yi mata a dalilin bala’in sonta da suke yi. A lokacin da su Ummi suka kai shekara shidda ne aka fara zancen sanya su makarantar boko da Islamiyya. A wannan lokacin kuwa kamarnin Ummi da mahaifiyarta ya fito sossai. Ga gashinta dogon gaske har yayi mata yawa.. Farin ta kuwa kamar na turawa. A dalilinta ne ake kiran gidan su gidan turawa. A wannan lokacin kuwa sossai Ummi take ta murnar za’a sa su a makaranta. tana bala’in son ta ganta sanye cikin uniform da kuma littatafai a hannunta tana rubutu kamar yadda take ganin yaran qauyen masu zuwa makaranta suna yi. Ana cikin wannan shirin ne wata magana ta fito a qauyen. Surayya ‘yar gidan Malam Rabi’u, yarinya ‘yar shekara Goma sha hudu tayi ciki.. ko da aka yi bincike sai aka gano Dauda dan gidan Malam Yahaya maqwabtan su shine yayi mata cikin a makaranta. Dama dai kullum idan aka tashi sai su qi tafiya gida sai kowa ya tafi sai su samu empty class su shige abinsu. Ai kuwa wannan ya sanya iyayen yara suka cire ‘ya’yan su daga makarantar boko, masu shirin saka nasu yaran kuwa suka fasa. A cikin su harda Baffa da Hardo. Shi dai Abdullahi dayake namiji ne sai aka qyale shi ya cigaba da zuwa dukda shima a shirme yake domin kuwa ba kullum yake zuwa ba… asali ma idan an tura shi makarantar zamewa yake yi ya bi yaran qauye su shige daji suna farauta ko kuma su tafi bakin rafi suyi wanka. Ummi dai ko da ta ji ance bazasu je makaranta ba sossai ta dinga kuka.. Haka dai da qyar Ummanta ta dinga lallashinta har ta haqura. Dayake dama Malam Lawali maqwabcin su yana koyar da yara karatun addini a nan zauren gidan shi sai kawai aka sanya su Ummi. Sossai Ummi ta mayar da hankali wurin karatun amma ita Binto sam ta qi. Lokutta da dama ma kwanciya take yi ta qi zuwa. Baffa kuwa idan yana nan sai yayi ta fada yayinda Daada take kare mata tace batada lafiya don haka a barta ta zauna gida. Ummi dai har qagara take yi lokacin karatun yayi ta tafi… sossai take daukar karatu a kanta. Tunda ta faro karatunta kuwa hadda take yi. Idan ta dawo gida kuwa Umman ta tana koya mata itama wadanda ta iya. Ummi dai dayake ta taso ta ga mahaifiyarta tana yawan yin azumi ranar litinin da alhamis haka itama tun bata kai yin azumi ba take hadawa da yin rabi rabi. A dalilin mugun farin jini da Ummi take da shi a qauyen ne ya sanya Umman ta bata so tana yawan fita musamman akan abinda ya faru da Surayya. Wannan ne ya sa bata zuwa ko ina idan ba tare da Umman ta ba. Hatta gidan Goggo idan ba tare da Umman ta ba bata zuwa ita kadai saboda akwai ‘yar tazara a tsakanin gidan su. A cikin gidan kuwa duk wani aiki Umma da Ummi sune suke yin shi. Daada da Binto kuwa sai dai su nade qafafuwa a cikin daji ko tsakar gida. Ummi takan tambayi Umman ta dalilin da ya sanya kullum suke cikin aiki alhalin su Daada basu yin komai.. Umma sai tace mata aikin taimako aikin lada ne don haka zata ga riba a gaba. Ita dai Ummi bata ga yadda mutum zai ci riba da wahala ba. STORY CONTINUES BELOW Tun Ummi tana ‘yar qaramar ta take kallon Umman ta idan tana yin girki wanda a haka ta dinga koya. Sossai Daada take jin haushin Ummi saboda yadda ta fi diyarta farin jini, ganin idanuwan iyayenta ne ya sanya take raga mata amma banda haka da ba qaramin wahalar da ita zata yi ba. Ana cikin haka ne Malam Musa mijin Goggo (Aminatu) ya rasu. Ya rasu ya barta ita kadai babu da babu ‘ya… Goggo dai Allah bai bata haihuwa ba tsawon zaman aurenta da Malam Musa. Akwai wani yaro mai suna Lado wanda Malam Musa ya riqe lokacin yana raye. Lado dai yaron wani abokin shi ne wanda iyayen shi suka rasu a sanadiyyar hatsarin mota tun yana da shekara uku. Ko da Malam Musa ya rasu Goggo ta cigaba da riqe Lado tamkar dan da ta haifa. Malam Musa ya rasu ya bar Gonaki dayawa. ko da aka sayar aka raba gado aka ba Goggo nata kason sai ta bude babban shago a kasuwan qauyen wanda ake sayar mata da hatsi sannan ake bata kudinta don haka da ita da Lado basu samu matsala ba a rayuwa. ♧♧♧♧♧♧♧♧♧♧ A lokacin da su Ummi sukayi shekara bakwai kuwa Umma ta samu ciki. Tunda ta samu wannan cikin take fama da laulayi. Da qyar take yin aikace-aikacen gida. wasu abubuwan ma bata iya yi sai Ummi ce take yi mata. Ganin halin da take ciki ne Baffa ya dan rage tafiye-tafiyen da yake yi. Sossai Umma take jin jiki domin kuwa har ta kai bata iya yin komai. Kullum sai Malam Lawali ya aiko mata da rubutu ta sha. Goggo takan zo gidan ta zauna da ita har ta taimaka mata da wasu aikace-aikace na gidan… A lokacin da cikin Umma ya kai wata takwas ne tafiya ta kama Hardo. Tafiyar kuwa akwai samu a cikin ta. Shi kam bai so yin wannan tafiyar ba domin kuwa baya so ya bar Umma a halin da take ciki. Umma kuwa ganin tafiya ce mai samu dayawa a cikin ta sai ta qarfafa mishi qwarin gwiwa tare da nuna mishi tunda akwai su Baffa da makwabta sannan kuma ga Goggo kar ya damu. Shi kam Hardo ya sani sarai Daada ba wani kula mishi da iyali zata yi ba… shima Baffan tunda dai an sani sarai sai abinda Daada tace sai bai bada qarfi akan zai yi wani abu ba don haka ne ko kafin ya tafi yayi ma Malam Lawali magana akan lallai ya kular mishi da iyalin shi. Haka yayi ma Goggo magana itama dukda nata gidan akwai nisa amma tayi alqawarin zata dinga zuwa kullum tana duba su. A ranar da zai tafi kuwa Ummi ta maqale a jikinshi ta dinga rusa kuka.. dukda kullum haka take yi idan zai tafi a wannan karon kukan nata yayi yawa. Da qyar aka banbare ta daga jikin shi sannan ya samu yayi musu sallama ya tafi. Tafiyar Hardo da kwana uku ne da safe Umma ta tashi da matsainacin ciwon ciki. Tun da safen kuwa Baffa ya tafi kasuwa, Abdullahi kuma ya tafi makaranta yayinda Binto take gidan kakanin ta. Malam Lawali kuwa sun tafi garin matar shi wadda mahaifiyarta ta rasu. Daada ce kawai take gida.. tana kwance a dakinta tana ta jin Umma wadda take ta fama da ciwo amma ta qi leqowa. Ummi kuwa gaba daya ta bi ta rude. tana riqe da Umma tana ta kuka yayinda take ta yi mata sannu. Ganin ciwon na ta gaba ne Ummi ta fita a guje ta sallama qofar Daada sannan ta shiga tana kuka ta sanar da ita abinda yake faruwa amma sai Daada ta kore ta yayinda ta dinga masifa tana zagin su. Ummi dai haka ta koma wurin Umma wadda ta fara fita daga hayyacinta. A guje ta nufi wurinta ta tsugunna a gaban ta tare da rungume ta tana kuka tace mata zata je ta Kira Goggo. Ko da ta miqe zata tafi kuwa sai Umma ta riqo hannunta ta qara rungume ta ba tare da tace komai ba.. Banda kuka babu abinda suke yi. Sossai jikin Ummi yayi sanyi a wannan lokacin. Da qyar ta sake ta sannan ta fice a guje. Har tayi nisa sai kuma ta dawo ta tsaya jikin labulen dakin Umman ta tana ta kallon ta. Daga nan kuma ta juya ta fita a guje. Haka Ummi ta dinga zabga gudu tana kuka yayinda mutane suke ta kallonta. wasu ma har tambayar ta suka dinga yi me ke damunta amma a dalilin ja mata kunne da iyayen ta suka yi akan ta daina yi ma mutane magana a hanya kwata kwata bata kalle su ba. Haka har ta isa gidan Goggo. Goggo kuwa ganinta ne hankalinta ya tashi matuqa. tun kafin ta fara yi Mata bayani kuwa ta San Umma ce babu lafiya. Mayafinta ta janyo suka fice tare cikin gudu-gudu, sauri-sauri yayinda Ummi take ta bata labarin abinda ke faruwa tana kuka. A lokacin da suka shiga gidan ne suka tarar da Daada ta fito daga dakin Umma wanda kuwa ganin su ya sanya ta sha jinin jikin ta. Ko gaisawa basu yi ba ta shige dakinta da sauri. Goggo da Ummi kuwa suna shiga dakin Umma suka tsaya turus ganin abinda ke gaban su. Umma ce kwance cikin jini sannan ga jarirai kyakyawa ‘yan qanana guda biyu a gefen ta amma basu motsi.. Da hanzari suka qarasa wurin ta yayinda take ta kakarin amai.. SARATU… Abinda suka ji tace kenan.. daga nan kawai sai suka ji tana salati yayinda Allah ya dauki ranta. Hankalin Goggo ya tashi matuqa.. Salati kawai ta dinga yi tana kuka. Ummi kuwa dukda yarintarta ta san mutuwa. Zama tayi a gefen Ummanta da ‘yan biyun tana kallon su itama tana ta rusa kuka. Daada kuwa tun kafin mutane su taru a gidan ta dauki mayafinta ta bar gidan. Ummi tana zaune aka yi ma mahaifiyarta wanka tare da ‘yan biyun (qannen ta) aka fito da su. Babu abinda take yi banda kuka. Dayake Hardo yana da waya sai Baffa ya sa a kira shi amma wayar ta qi shiga. A haka har aka yi ma su Umma sallah aka tafi da su gidan gaskiya. Saratu kuwa bata dawo gidan ba har sai da aka tafi da gawar su Umma Maqabarta. Ko da ta dawo sai ta dinga koke-koke harda birgima. Da yamma ana zaune ana ta juyayi ne wani tashin hankalin ya bayyana. Wata mota ce ambulance ta zo dauke da gawar Hardo wanda suka samu hatsari a hanyar su ta dawowa…3 Anan kuwa hankula suka tashi. Goggo, Baffa da Ummi sun zama abun tausayi a wannan lokacin.. Gaba daya sun birkice. Haka shima aka shirya shi aka kai shi gidan shi na gaskiya. Ummi ‘yar qaramar yarinya ta rasa iyayenta da qannen ta a rana daya… ta zama marainiyar Allah.. Allah ya jiqan su. Tun bayan rasuwar iyayenta Ummi take matsa ma Goggo akan yakamata a kashe Daada saboda ita ta kashe Ummanta da qannen ta.+ Goggo kuwa sossai hankalinta yake tashi idan ta ji Ummi tana wannan maganar. Goggo ta sani cewar Daada tana da hannu a mutuwar Umma amma kuma tunda basu da qwaqwarar shaida ko sun fadi ba sauraron su za’ayi ba sannan hakan yana iya janyo ma Ummi matsala musamman idan akayi la’akari da halin Daada na qulla asiri iri-iri. Ba qaramin aikin Daada bane ta bata ma Ummi rayuwa don haka ne Daada ta dinga tausa Ummi tare da fadi mata Allah ne ya dauki ran mahaifiyarta saboda ya fi su sonta. Ita dai Ummi ta san ance Allah ne yake daukar rayukan mutane amma kuma ita abinda ta sani shine Daada ta dauke na uwarta da na qannen ta. Da qyar dai Goggo ta shawo kanta ta haqura ta daina yin maganar amma fa har duniya ta nade bazata taba manta abinda Daada tayi ma Ummanta ba. Bayan kwana uku da rasuwar Su Hardo ne kamfanin da Hardo yayi ma aiki suka bashi kudade masu yawa as compensation. Babu laifi a wannan lokacin kudi ne masu yawa. Goggo ce ta bada shawarar ayi amfani da su a siya ma Ummi shanu ayi ta mata kiwo ko kuma a siya mata fili ayi ta noma ana tara mata kudin. Baffa dai daga farko ya amince da hakan tunda dai gadonta ne. Daga baya kuwa Daada ta qeqashe tace sam baza’a yi haka ba. Tunda dai su zasu cigaba da riqon ta dole ne suyi amfani da kudaden wurin ciyar da ita da sauran hidima. Shi kuwa Baffa dayake mijin-tace ne babu musu ya amince da shawarar Daada. Ran Goggo ya baci matuqa…. Har rigima suka yi da Baffa akan hakan. Daga baya ma ce musu tayi su bata Ummi ta tafi da ita tunda dama ita Allah bai bata haihuwa ba… zata dauki nauyin hidimar ta gaba daya amma ayi qoqari a siya mata property da kudin gadonta. Daada kuwa ta hana.. dama dai neman hanyar da zata gallaza ma yarinyar take yi a dalilin haushin yarinyar da iyayenta da take yi. Idan har ta bari Goggo ta tafi da ita babu halin cutar da ita kenan don haka ta ziga Baffa akan lallai kar ya amince da zancen Goggo. Babu wanda ya cancanta ya riqe Ummi idan ba shi ba tunda dai shine ainihin wan mahifinta wanda suke uwa daya uba daya. Goggo dai tana ji tana gani ta haqura ta bar musu Ummi. Ummi kuwa ko da ta ga Goggo tana tattara kayanta zata koma gida bayan sadakar bakwai sai ta sa kuka akan zata bi ta domin kuwa ta sani sarai Daada zata ci qaniyar ta tunda ba son ta take yi ba. Haka Goggo ta dinga lallashinta tare da fadi mata zata dinga zuwa tana duba ta. Da qyar dai Ummi ta haqura.. tana kallo Goggo ta koma gida. ************* Tunda iyayen Ummi suka rasu ta shiga wahala a duniya. Sossai Daada take gallaza ma yarinyar. Ummi dai gaba daya aikin gidan ita take yi dukda qarancin shekarun ta. Idan kuwa tayi ba daidai ba ta sha duka na fitar hankali. Ga Binto ‘yarta bata komai.. sai dai ta zauna tayi ta ma Ummi dariya idan ana jibgan ta. Tun da asuba da bulala Daada take tada ta daga bacci ta fito ta fara aikin gida. Haka Ummi tana kuka tana yin aiki wanda a shekarunta sunyi mata yawa. Abincin kirki ba’a bata.. watarana ma haka take yini ba’a bata shi ba. Goggo takan zo ta duba ta sannan tana kawo mata abubuwan ci kala-kala. A duk lokacin da Goggo ta zo kuwa sai tayi ta kuka tana bata labarin abubuwan da ake yi mata yayinda take yawan roqonta akan ta tafi da ita amma sai Goggo tayi ta bata haquri.1 STORY CONTINUES BELOW Cikin ‘yan tsakakanin lokacin kuwa sossai yarinyar ta rame sannan ta yi duhu saboda wahala. Goggo ta zaunar da Baffa tayi mishi bayanin abinda yake faruwa tunda dai yawanci baya nan ake azabtar da yarinyar amma maimakon ya tsawata ma matar shi sai yace wai itama Ummin bata jin magana ne. ♧♧♧♧♧♧♧♧ A lokacin da Ummi ta kai shekara Goma sha daya kuwa Daada ta fara dora mata tallar nono. Daada dai dukda ba garken shanu garesu ba haka take sa ana saro mata nono tana dora ma Ummi don dai kawai ta gallaza mata. Gashi wani ikon Allah tunda Ummi ta taso bata son qarnin Nono kamar ba bafillatana ba.. Daada ta sani sarai amma don mugunta sai ta hada yarinyar da shi. Haka take fita da shi tana kuka yayinda take rasa yadda zata yi da shi. Dayake yawancin ‘yan matan da ake dora musu tallar nono sukan yi layi a bakin kasuwa itama can din take zuwa ta zauna. Sossai ake tausaya mata domin kuwa babu wanda bai san Ummi ba (yarinyar da aka yi ma gidan su laqani da gidan turawa a dalilin ta). Akwai wata yarinya mai suna Murjanatu wadda itama tana zuwa bakin kasuwar sayar da nono tare suke zama kullum. Ummi tana rusa kuka yayinda ita take sayar musu da nonon. A dalilin farin jinin Ummi mutane sun fi taruwa a wurin su wanda nan da nan ake saye nasu gaba daya. Idan Murjanatu ta gama sayarwa sai ta ba Ummi kudin nata sannan ta raka ta har gida sai ita kuma ta tafi nasu gidan. Tun Ummi tana kuka har ta daina. Tuni sun qulla qawance da Ummi. Ita dai Murjanatu sossai take jin dadin kasancewar su qawaye domin kuwa tana son Ummi. Binto kuwa saidai idan yamma tayi ta ci kwalliya ta fice yawo abun ta. Yarinya ‘yar shekara goma sha daya tuni idanuwan ta sun bude. samari gareta kala-kala.. Abdullahi kuma babu abinda ya sa a gaba banda shaye shaye… sai ya kwana biyar ma baya gidan. Tun Baffa yana fada har ya gaji ya zuba mishi ido. *************** Akwai ranar da Ummi ta fito da qwaryar Nono a kanta ne Goggo ta hango ta. Sossai hankalinta ya tashi.. Janye Ummi tayi suka tafi gidan ta wanda kuwa daga ranar bata qara zuwa tallan nono ba. Asali dai a kullum idan Ummi ta fito da qwaryar nonon gidan Goggo take zuwa da shi. ita kuwa Goggo sai ta kira Lado idan ya dawo daga makaranta ta miqa Mishi qwaryar ya tafi da ita kasuwa wurin su Murjanatu.. haka yake zagayen nema mata customers har a saye na Ummin a saye nata itama. Dayake dai dama an saba da sayan na Murjanatun a dalilin Ummi sossai aka cigaba da siya a wurinta din dukda Ummin bata zuwa. Idan Murjanatu ta sayar kuwa sai ta ba Lado kudin na Ummi shi kuma ya kai ma Goggo. Ita kuwa Ummi kwanciyarta take yi a wurin Goggonta, ta ci ta sha sannan tayi baccin da bata samu tayi a gida a dalilin azababben aikin da ake sa ta dare ta rana. Idan Lado ya dawo mata da kudin tallar sai ta tafi ma Daada da shi. Da yamma kuwa tana zuwa gidan Malam Lawali don daukar karatu. Ummi dai sossai ta mayar da hankali wurin karatu. Har a wannan lokacin hadda take yi wanda kuwa tayi nisa sossai. Wannan shine mafarin sassauci da Ummi ta samu a rayuwarta. A kullum kuwa zaka ga Ummi sanye cikin Hijabi.. bata yawo ba tare da ta sanya Hijab ba sannan kuma tuni ta fara kai azumi complete.. duk litinin da alhamis tana yin azumi Wanda a kullum sai tayi ma iyayen ta addu’a. STORY CONTINUES BELOW Sossai Ummi take son tuwo da miyan kuka don haka kullum idan tana gidan Goggo sai ta tuqa mata shi. musamman take aikawa kasuwa a siyo mata kifi tayi mata farfesu ta ci kayanta. Ita dai Goggo sossai take tausaya ma yarinyar don haka duk wani abu da tasan Ummi tana so tana yi mata shi daidai gwargwado. A haka dai shekaru sukayi ta tafiya. Tuni Ummi ta dawo da hasken ta sannan babu alamun yunwa a tare da ita. A lokacin da take shekara goma sha hudu ne ta fara al’ada. Inda Allah ya taimaka kuwa ranar tana gidan Goggonta. Sossai ta birkice tana ta rusa ma Goggo kuka.. a tunaninta wani ciwo ne ya kama ta wanda zai zama ajalin ta. Goggo kuwa ta dinga yi mata dariya. A haka dai Goggo ta zaunar da ita ta fahimtar da ita komai yayinda ta koya mata yadda zata gyara kanta da kuma yadda zata tsarkake kanta idan ta gama kamar dai yadda addinin mu ya tsara. Ummi kuwa a duk wata idan al’adarta zata zo sai tayi fama da ciwon ciki. Haka zata yi ta rusa kuka tayi ta murqususu. A gidan Goggo kam tana samun kulawa amma a gida saidai ta gama kukanta ta natsu dan kanta. ♧♧♧♧♧♧♧♧ A lokacin da Ummi ta kai shekara Goma sha biyar ne wani babban al’amari ya faru. An wayi gari an ga Binto da ciki har na tsawon wata biyu. Aikuwa Hankalin Baffa ya tashi matuqa.. sossai ya dinga yi ma Daada bala’i. sossai suka hau sama a lokacin amma dayake an riga an asirce shi, kasa daukar mataki yayi akan ta. Aikuwa tuni ‘yan qauyen aka dauki zancen cikin Binto ana ta yadawa yayinda ake tir da tarbiyar da aka bata. Babu shiri kuwa Daada ta dinga jiqe-jiqen tarkace tana dura mata har dai cikin ya zube. Hakan kuwa bai hana Binto canza dabi’arta ba.. ganin ma idan anyi cikin ana iya zubarwa sai bata damu ba idan ta qara yin wani… tuni ta cigaba da iskancinta a cikin qauyen. Babu dan iskan qauyen da bai kwanta da ita ba. Ummi kuwa samari masu ji da kan su a qauyen suke bibiyar ta amma sam bata kula kowa. Asali ma abinda ya faru da Surayya da Binto yake matuqar bata tsoro don haka ne ma bata bada fuska. Akwai wani dan kyakyawan saurayi mai hankali da natsuwa mai suna Jauro da yake bala’in son Ummi amma sam ta qi kallon shi ma balle ta yi mishi magana. Shikuwa ya dage akan lallai yana sonta kuma ya sa a ranshi baya da mata sai Ummi. Jauro dai dan gidan hakimi ne kuma yana zuwa makaranta domin kuwa yana jin turanci sossai. Da ka gan shi zaka ga yana da bambanci da sauran yaran qauyen domin kuwa shi ya waye. ‘yan mata dayawa suna son Jauro amma sam ya qi kallon kowacce mace sai Ummi.. Ana nan kuwa aka sa ranar bikin Murjanatu wadda zata auri wani dan makwabcin su mai suna Muntari. A ranar bikin kuwa Jauro ya dinga bibiyar Ummi amma ta dinga kaucewa.. A dalilin nace mata da yayi ne ta gudu gida. Har aka gama bikin kuwa bata qara komawa ba. Sai bayan da aka kai Murjanatu dakin mijinta sannan ta leqa. Ta sha qorafi a wurin qawarta amma ta dinga bata haquri tare da yi mata bayanin ainihin dalilinta na guduwa. Ita dai Murjanatu tana ta mamakin yadda Ummi bata son kyakyawa mai aji kamar Jauro.. ita kuwa sai ta gwada ma qawarta ita auren ne bata so kwata-kwata. ****************** Da shekara ta zagayo ne Murjanatu ta haifi ‘yarta mace wadda aka sanya ma suna Zainab. Sossai yarinyar ta shiga ran Ummi.. A dalilin yarinyar take zuwa gidan Murjanatu duk bayan kwana biyu suyi ta wasa. Idan tana ganin yarinyar sai ta dinga tuno qannen ta guda biyu wadanda suka rasu a ranar da suka fado duniya. takan yi tunanin irin abubuwan da zasu yi tare da suna raye. Idan ta tuno da innocent faces dinsu tare da na Umman ta a lokacin da suke kwance babu rai kuwa sai tayi ta rusa kuka. STORY CONTINUES BELOW Sossai take missing iyayenta. ♧♧♧♧♧♧♧♧ Ummi tana daf da shiga shekara goma sha bakwai ne wata rana ta dawo gida riqe da qwaryar nonon da Lado ya sayar mata (tunda Murjanatu tayi aure sai ya koma ajiyewa a wurin wata Zulaihatu wadda ya cigaba da samo musu customer ita kuma tana sayarwa) A lokacin da ta shiga gidan ta tarar Daada tayi wata baquwa wadda ake kira Rakiya mai ‘yan mata. Cikin sallama ta shiga gidan yayinda ta qarasa wurin su ta gaishe su. Aikuwa Rakiya tana ta kallon Ummi har ta miqa ma Daada kudin Nonon sannan ta miqe zata shiga dakinta. Bata qarasa shiga bane ta ji Rakiya tana fadin “ke kuwa Saratu kina da irin wannan yarinyar a cikin gidan nan kike kukan talauci??” Ummi dai zuciyarta ce ta buga yayinda ta shige dakinta ta maqale jikin qofa tana sauraren su. Daada tace “ban gane abinda kike nufi ba Rakiya” Rakiya ta gyara zamanta tace “ai irin wannan yarinyar da zaki bani ita ina zuwa da ita birni za’a dauke ta aiki.. kin san suma ‘yan birni suna son kyakyawa masu haske..” Daada ta fashe da dariya tare da tafa hannu tace “kai amma na ji dadin wannan shawarar.. kin ga dama fa ina so mu aurar da Binto kwanan nan kuma gashi kudin basu shigowa.. kin ga idan na tura yarinyar birni ai na tabbatar cikin wata shidda ma zata hado mana kudin.. aikuwa zan baki ita.. yaushe zaki koma??” Rakiya tana murmushi tace “gobe da sassafe zan tafi saboda na riga na samu yara har guda shidda.. kin ga sai in hada da ta hannun ki su zama bakwai” Ita dai Rakiya ta tafi tare da yi ma Daada alqawarin washegari tun da asuba zata zo daukan Ummi. Bayan ta tafi ne Ummi ta fito a guje tana kuka ta qaraso wurin Daada ta durqusa har qasa tace “don Allah Daada kada ki tura ni wani wuri.. idan baki so in zauna anan don Allah ki mayar da ni gidan Goggo..” Aikuwa anan take Daada ta kwashe ta da mari tace “dan ubanki idan kika zauna a gidan Goggon ina zan samu kudin da zan aurar da Binto ‘yar uwarki??…” Haka ta dinga zabga masifa yayinda Ummi ta dinga kuka tana roqon ta amma sam. Ummi kuwa a ranar ta so ta gudu ta tafi gidan Goggo amma Daada ta rufe ta a daki. Hatta Karatun ma ta hana ta zuwa. Baffa yana dawowa kuwa ta kanannade shi da zancen wanda da farko ya so ya qi amincewa amma daga baya kuwa sai ya amince a dalilin shima kasuwancin nashi ba tafiya yake yi ba sannan yana so ya aurar da Binto a dalilin lalacewa da ta yi. A ranar kuwa Ummi ta kwana bata yi bacci ba. Banda kuka babu abinda take yi.. matsalarta a wannan lokacin wane irin aiki zata je yi da har zata samu kudin da za’a yi ma Binto aure? Cikin dare kuwa ta dinga salloli tana kai kukan ta zuwa ga Allah.. Kafin asuba kuwa zazzabi ya rufe ta sossai. Tun da asuba Daada ta bude qofar dakin nata ta tarar da ita kwance tana kyarmar sanyi. Cikin fada tace “Dan ubanki kin hada kayan naki ko kuwa??” Ummi da qyar take magana, tace “don Allah kiyi haqu…” Kafin ta qarasa kuwa Daada ta fizgota ta jefa ta waje sannan ta dauki jakar Ghana must go ta zuba kayanta ta fito. Rakiya tana tsaye tana ta ba Ummi haquri yayinda take yi mata bayanin cewar zata ji dadin inda za’a kai ta. Haka Rakiya ta tafi da Ummi yayinda Baffa yake zaune cikin daki cike da tsananin damuwa.. ya kasa ko leqowa ya ganta. Deep down within him ya san abinda aka yi wa yarinyar ba’a kyauta ba, ya rasa dalilin da ya sanya ya kasa hana tafiyar yarinyar (an riga an asirce shi) STORY CONTINUES BELOW Goggo dai ganin Ummi shiru bata je gidanta ba ne ta tafi gidan don ganin ko lafiya. A wannan lokacin ne ta tarar da mummunar labari wai Ummi ta tafi aiki birni. Wannan abu ya baqanta ma Goggo rai matuqa.. sossai ta dinga bala’i.. har kuka tayi saboda baqin ciki amma kuma ya zata yi??? Aikin gama ya gama!! ♧♧♧♧♧♧♧♧ ABUJA Ummi dai wannan shine farkon shigarta birni, farkon barin qauyen su tunda aka haife ta. Gaba daya a firgice take… banda kuka babu abinda take yi. ‘yan matan da aka kawo su tare sai murna suke yi sun zo birni sabanin Ummi wadda take ji kamar an raba ta da rayuwarta ne. Ummi tana fama da zazzabi suka iso Abuja. Allah ya taimake ta Rakiya ta hado mata magunguna ta sha.. A dalilin kwanciya jinya ne har aka kwashe sauran ‘yan matan bata ma sani ba. Ita kadai ta rage. A ranar da Rakiya tace mata ta dauki jakarta ta fito kuwa hankalinta yayi matuqar tashi yayinda ta dinga rusa kuka. Ganin hakan ne ya sanya Rakiya ta kwantar mata da hankali tare da sanar da ita aikin ‘aikatau’ zata yi ba yawon iskanci ba. Da wannan ne ta dan saki ranta. Gidan Alhaji Aliyu Sodangi (gidan su Maleeka) aka kai Ummi wanda kuwa Mummy ta dauke ta a matsayin ‘yar aiki wadda zata cigaba da taimaka ma Inno a dalilin ayyuka da suka yi mata yawa. Sunyi da Rakiya akan zata dinga zuwa duk wata ta karbi kudin aikin Ummin ta aika ma iyayenta gida. Da farko dai Ummi ta qi sakin jiki amma dayake Inno tana da kirki sai ta dinga tausa ta har ta rungumi qaddararta yayinda suka cigaba da aiki tare dukda dai ba wata hira mai yawa suke yi ba domin kuwa Ummi tunda ta taso ba mai sakin jiki bace da mutane anyhow. Inno ta gwada mata yadda ake amfani da abubuwa a gidan tunda dai Ummi bata san komai ba. Dayake tana da qwalwa nan da nan ta fahimci yadda komai na gidan yake aiki. Mummy dai ta kyautata ma Ummi sossai domin kuwa har sabbin kaya ta dinka mata sannan ganin ma’abociya sanya hijabi ce ta sa aka dinka mata su. A dalilin tsabta da natsuwar Ummi ne ya sanya Maleeka ta aminta da ita don haka ne ta riqe ta a matsayin personal maid dinta. Bayan wata daya da fara aikin Ummi a gidan ne Rakiya ta zo ta karbi kudin aikinta na watan farkon. A lokacin da wata ya zagayo kuwa sai Mummy ta ji shiru… wayarta kuma bata shiga. Haka har aka cinye wata na uku ma babu Rakiya babu dalilinta…. Da wannan ne Mummy ta cigaba da ajiye ma yarinyar kudin aikin nata yadda duk ranar da Rakiya ta zo sai a bata ko kuma idan yarinyar zata tafi gida sai a bata. Rakiya kuwa guduwa tayi a dalilin ‘yan Human Right da suka kama wasu abokanen sana’ar ta da laifin dauko yara daga qauye suna kai su birni suna aikatau.. Tunda Allah ya bata iko ta kufce kuwa ba’a sake jin labarin ba. Wannan kenan!!! ************** ☆☆☆☆☆ ……A lokacin da Maleeka ta kori Ummi daga gidanta bayan tayi mata dukan tsiya hankalin ta a tashe ta bi hanya ba tare da ta san inda zata je ba. Haka tayi ta tafiya kan hanya tana kuka yayinda jikinta yake ta radadi. Ga unguwa GRA babu kowa a kan hanya. Sai da tayi tafiyar kusan awa daya sannan ta isa busy road inda ta samu taxi ta shiga aka kai ta tashar mota… Mai Taxi din kuwa ganin yanayin da Ummi take ciki ma ko sisin ta bai karba ba. Naira dubu biyar din da ta cira a bundle din da MK ya bata da su ta biya kudin mota ta dawo garinsu.. Adamawa! shima da qyar masu motar suka amince a dalilin ganin halin da take ciki domin kuwa kudin motar ya wuce hakan….. ************* Ummi dai ko da ta dawo Rugange straight gidan Goggonta ta tafi domin kuwa ta sani sarai idan ta nufi gidan Baffanta sai Daada ta kashe ta. Hankalin Goggo dai ya tashi matuqa ganin yanayin Ummi a wannan lokacin. Banda kuka babu abinda ta dinga rusawa.. Ko da Goggo ta tambaye ta abinda ya faru sai tayi mata qaryar Barayi ne suka shiga gidan da take aiki suka yi ma kowa dukan tsiya yayinda suka tafi da Alhajin gidan… daga nan ne ta gudu!! Babu shiri Goggo ta kai ta chemist aka duba lafiyarta sannan aka yi treating din ciwon da Maleeka ta ji mata suka dawo gida. Tunda Ummi ta dawo kuwa take cikin tsananin tashin hankali.. Dare da rana tana kwance a dakin Goggo tana tunanin MK. Idan ta tuna shi har kuka take yi yayinda zuciyarta take zafi sossai. Ummi tayi missing din MK domin kuwa har mafarkin shi take yi. Ta tabbatar har ta mutu bazata manta da shi ba sannan rayuwarta bazata taba komawa daidai ba. Bayan sati daya ne Daada ta ji labarin dawowar Ummi… aikuwa tana sanar da Baffa ta ziga shi akan lallai ya je gidan Goggo ya dauko ta. Goggo kuwa tana ji tana gani Baffa ya tafi da Ummi tana ta kuka. Daada kuwa sai da tayi mata shegen duka saboda ta dawo babu ko sisi sannan ta hana ta fita ko qofa tunda dai sun sani sarai idan ta fita gidan Goggo zata je. Goggo dai har wurin sarki ta kai qara amma akayi overruling case dinta tunda dai Baffa shine yayan mahaifin Ummi sannan shi ya cancanci ya riqe ta. Hakan ya ba Goggo haushi musamman yadda ba’ayi la’akari da halin da yarinyar take ciki a gidan ba… babu yadda ta iya dole ta haqura. Ana cikin haka ne Alhaji Buba ya ji labarin dawowar Ummi a gari sai ya nemi Baffa da ya bashi aurenta. Da farko Daada ta so ta hana ganin cewar Alhaji Buba yana cikin masu kudin qauyen ita kuma Bata so Ummi ta je inda zata huta amma daga baya da ta tuna cewar Alhaji Buban dan iska ne na qarshe sai ta amince. Ga kudade, shanu da gona da yayi alqawarin zai basu idan dai za’a bashi Ummi. Aikuwa nan da nan aka sanya ranar bikin su sati daya wanda da aka sanar da Ummi har suma ta dinga yi saboda tsananin tashin hankali da ta shiga. Goggo kuwa tayi baqin cikin wannan abu. Musamman ta je gidan ta roqi Baffa akan kar ya aura mata Alhaji Buba amma sam Baffa ya qi ji. Da qyar ma Daada ta bari Goggo ta kai ta chemist aka duba ta. Haka akayi ta mata allurai wanda da dambe ake yi don bata qaunar allura a rayuwarta yayinda aka bata magunguna. Goggo dai haka ta dinga tausa Ummi tare da yi mata nasiha akan rungumar qaddara a duk yadda ta zo mata… A haka ne har ranar auren ya zo wanda MK ya je qauyen ya biya Alhaji Buba kudaden shi da ya kashe akan Ummi sannan ya aure ta. Wannan shine labarin Ummi!! Bayan sallar azahar Goggo tana zaune a kan tabarma tana dama fura da nono.+ Cikin sallama MK ya shigo gidan yayinda ya qarasa wurinta ya tsugunna har qasa ya gaishe ta. Cikin fara’a ta amsa sannan ta nuna mishi tabarma a gefen ta tace “Ga wuri ka zauna Kabiru.. Ya kuka koma jiya??” ●●●● MK dai a jiya ko da Goggo ta gama bashi labarin Ummi sossai ya tausaya ma yarinyar.. Sossai ya ji haushin Baffa da Daada.. Ya so dauko ‘yan Human right su bi ma Ummi hakkin ta musamman a wurin Daada wadda ta nemi ta wulaqanta mata rayuwarta amma Goggo tace ya bar su kawai tunda dai abinda suka yi ma yarinyar bai tsinana musu komai ba.. Yayi ma Goggo alqawarin zai kula da Ummi matuqar yana raye kuma bazai taba barin mummunan abu ya same ta ba haka kuma bazai taba bari ta wulaqanta ba. MK ya sanar da Goggo cewar washegari zai zo ya tafi da Ummi saboda aikinshi da ya baro a Abuja… Sun tattauna akan abubuwa da dama sannan ya tafi… abubuwan da zaku jiyo daga baya don haka ku bi ni bashi..!!!2 ●●●● MK yace “lafiya lau Goggo..” Tace “bisimillah ga fura.. dukda na tabbatar da Ummi tana kusa da ta hana ka sha tunda bata so..” Shi kam jin tace Ummi bata son Fura da Nono sai ya ji shima har ga Allah baya so.4 Kai tsaye yace “Alhamdulillah Goggo” Tace “au.. kai ma baka sha kenan” Murmushi yayi ba tare da yace komai ba. Tana ta dama furar ta ne tace “ai dazu da safe Bashir ya kawo likita ta duba ta… sannan Kabiru wadannan kaya da ka aiko ai sunyi yawa.. wa ya fadi maka mu ‘yan qauye muna ciye-ciye haka?” MK dai dariya yayi yace “kiyi haquri Goggo, me likitar tace?? na manta ban kirata ba… dayake akwai wasu ‘yan abubuwa da na tsaya yi” Tace “eh toh babu wani matsala.. kawai ciwon da yake bisa goshinta ne wanda shima tace zai warke” Kai tsaye yace “bata yi mata allura ba dai ko??” Goggo tana dariya tace “ai ta fadi mun wai kace kar ayi mata allura.. Ummi kam ai bata son allura ko alama… da dambe fa aka dinga yi mata alluran da nake kai ta chemist…” MK yana dariya yayinda ta cigaba da fadin “…Likitar dai ta bata magunguna, ka ga lokacin shan na ranan ma yayi bata sha ba.. bata yi sallah ba sannan abincin nata yana nan ajiye a dakin bata ci ba” Kai tsaye yace “tana ina ne??” Tace “tana cikin daki tana bacci tun dazu..” Gani nayi ya miqe yace “bari in duba ta..” Goggo ta miqe ta dauki furar ta tace “dama kuwa zan duba Mairo a nan makwabta ta haihu ban je barka ba.. Yau din zaku tafi ko??” yayinda ta nufi wurin tsohon qaramin fridge dinta ta sanya shi a ciki. MK yace “Insha Allah Goggo” Tace “toh madallah.. ni sai na dawo” ****************** STORY CONTINUES BELOW Kwance take a kan katifar dakin yayinda take bacci. Gaba daya ta dunqule a cikin hijabinta kamar wadda take tsoro..2 MK wanda ya shiga dakin zama yayi a gefen katifar yayinda ya sanya mata idanuwa. He still cant believe he got married.. abinda bai taba ko da mafarkin yi ba- qara aure!! Ummi wadda take bacci ce ta dan motsa a dalilin qamshin turaren shi da ya cika ta. A tunaninta mafarki take yi amma tana bude idanuwan ta sai ta gan shi zaune yana kallon ta. Da sauri ta juya mishi baya yayinda ta qara dunqulewa cikin hijabin ta. Zuciyarta ce take ta bugawa yayinda jikinta yayi mugun sanyi. Girgiza kai yayi yana murmushi yace “yau kuma Babyn Hamma bata son ganin Hamma ne??” Ita dai Allah ya sani tana son muryar MK.. kai komai ma nashi birge ta yake yi.. A yanzu haka tana jin muryar shi wani sanyi ta ji har cikin ranta.. Shiru tayi yayinda ta qi amsa shi. Ummi dai har yanzu mamakin abinda ya faru take yi.. gani take yi kamar mafarki take yi wanda idan har hakan ne toh fa bata so ta farka..5 Wai yau ita Umm Aimaan tana matsayin matar shi?? MK?? Hamman ta?? Ji tayi yace “ki tashi ki ci abinci ki sha magani sannan kiyi sallah” A yanzu ma shiru tayi bata ce komai ba. Har yanzu kuwa zuciyarta tana ta bugawa. Matsawa yayi daf da ita wanda tsakanin su bai wuce inch daya ba yace “Baby idan baki tashi ba zan dauke ki… kin dai san yanzu ni ba Hamma bane… ni mijinki ne” Da sauri ta matsa tare da tashi zaune. Yana murmushi yace “ya jikin ki??” Kanta a duqe tace “Alhamdulillah” Yace “toh da me zaki fara?? abincin ko sallah” Miqewa tayi tace “sallah” yayinda ta wuce da sauri ta fita daga dakin don yin alwala. Shi kuwa bin ta yayi da idanuwa yana murmushi. Yana nan zaune yana latsa wayar shi ne ta shigo dakin. Ko da suka hada idanuwa murmushi yayi mata yayinda tayi saurin kauda kanta. Yana ta kallonta yayinda take sallah cikin natsuwa har ta idar. Ta dade zaune tana addu’a sannan ta miqe. Tana cikin ninke Dadduma ne ta ji yace “Kin roqi Allah ya bamu zaman lafiya ko??” Da sauri ta juyo ta kalle shi, muryarta kamar zata yi kuka tace “don Allah Hamma ka sa a raba auren nan… wallahi Adda zata kashe ni.. dagaske fa lokacin da…” Katse ta yayi tare da fadin “sssssshhhhh.. babu wanda ya isa ya taba mun ke as far as ina nan Baby… kiyi haquri tunda haka Allah ya tsara”6 Daga nan bata qara cewa komai ba sannan bata zauna ba. Ji tayi yace “zo ki zauna ki ci abinci..” Babu musu ta qarasa wurin tuwon da Goggo ta ajiye mata ta zuba. Yana kallonta ta zauna dan nesa da shi sannan ta fara ci. MK wanda yake kallonta ne yace “haba Babyn Hamma.. shine ko tayi babu??” Tana kallon kwanon tuwon tace “yi haquri Hamma ban san zaka ci…” Ko kafin ta qarasa maganarta sai ya matso kusa da ita yace “zan ci amma fa ke zaki bani da kanki..” A firgice ta kalle shi yayinda duk ta bi ta rude. Muryarta tana rawa tace “ya za’a yi in baka Hamma?” STORY CONTINUES BELOW Yana kallonta yace “saboda ke Mata ta ce a yanzu Ummi…” Da sauri ta duqar da kanta yayinda zuciyar ta take ta bugawa. Ji tayi ya cigaba da fadin “…kin dai san Allah yana fushi da matar da mijinta ya sa tayi abu ta qi ko?” A rude ta kalle shi tace “don Allah kayi haquri Hamma..” Yace “ni babu ruwana ai… Allah ne yace..” Bai qarasa magana bane ya ga ta gutsiro tuwon ta sa a miya sannan ta kai hannunta saitin bakin shi.1 Shi dai MK da wasa yayi mata don kawai yana so suyi hira ganin yadda ta qi sakin jiki da shi kamar da toh amma a yanzu tunda ya ga ta zata dagaske yake yi sai yayi seizing opportunity din kawai…. Hannun nata kuwa sai rawa yake yi don haka ne ya riqe hannun sannan ya kai bakin shi. Ita dai Ummi kallon shi kawai take yi yayinda take ta mamakin halin shi.. ya ma za’ayi tace bata gode ma Allah ba da ya bata shi a matsayin miji? mutumin da duk kudin shi, duk matsayin shi bai taba nuna qyama a gareta ba.. mutumin da ya biyo ta har qauyen su ya tausaya mata ya aure ta don kawai ya cece ta daga fadawa hannun mutumin banza Alhaji Buba… Muryar shi ce ta dawo da ita daga duniyar tunani inda ta ji yace “Baby ina jira fa..” . Wayancewa tayi yayinda ta mayar da hannunta cikin kwanon. Wannan karon da ta debo qin bude baki yayi yayinda yayi mata nuni da ta ci. A haka dai suka cinye tuwon wanda idan ta bashi sai itama ta ci. Tun tana jin kunya kuwa har ta daina..8 Ledar maganin ta ya janyo ya balle ya miqa mata ta sha. Bayan ta kwashe dishes din ne ta fita da su sannan ta dawo ta zauna bisa katifar yayinda take wasa da yatsun hannunta. Yana kallonta ne yace “Goggo ta fadi miki yau zamu tafi ko???” Gaban ta ne yayi mummunar faduwa da jin maganar shi. Tabbas Goggo ta fadi mata tun da safe amma Allah ya sani bata so ta bi shi. Dago kai da sauri ta kalle shi sannan tace “Hamma don Allah ka tafi ka bar ni anan..” Zaro idanuwa yayi yace “what?? bazai yiwu ba. Kin san akwai aiki yana jira na a Abuja ko?? sannan kuma kin san babu yadda za’ayi in bar nan ba tare da ke ba don haka kawai kiyi haquri..” Ji yayi ta rushe da kuka yayinda duk ya bi ya rude. Cikin kukan ne tace “toh kayi haquri sai gobe” Shi fa ya sani sarai ba wai shi ne bata so ta bi ba… Maleeka ce bata son gani. Tabbas shi kanshi yana fargabar tafiya da ita din.. me zai ce ma su Abba??? Yace “Baby don Allah ki daina kuka.. Yanzu gaya mun meyasa sai gobe??” Da ta rasa abinda zata ce ne kawai tace “ban yi sallama da qawa ta ba…” Yace “tashi mu je muyi mata sallama toh” Da sauri tace “ni ba sai mun je tare ba” Yana murmushi yace “aikuwa tare zamu je sai dai idan bazaki je ba..” Sallamar Goggo suka ji ta dawo.. MK ne ya amsa sallamar yayinda ya miqe ya kalli Ummi yace “ina jiran ki a waje” Ummi tana nan zaune ta ji MK yana fadi ma Goggo cewar zasu je yi ma Murjanatu sallama… *************** Tsaye yake a jikin motar shi yayinda yake ta latsa wayar shi yana jiranta. Haka mutane suke ta wucewa suna kallon shi yayinda ake ta mamakin yadda Allah ya sauya ma Ummi rayuwa cikin qanqanin lokaci.. STORY CONTINUES BELOW Ummi ce ta fito sanye cikin Hijabinta kamar kullum yayinda kanta yake a duqe. Tunda ta fito ya sanya mata idanuwa. Yarinyar dai dukda ta rame sossai tayi mishi kyau.. gani yayi ma kamar ta qara kyau.. Wani irin jin ta yake yi a ran shi fiye da lokacin da take gidan shi… is it because she is now his wife??4 Ji yayi tace “Hamma mu je..” yayinda ta fara tafiya. Da sauri yace “tsaya mana Baby.. ban gane ba. A qafa zamu je?” Tace “eh.. ai nan baya ne babu nisa” Shafa kan shi yayi yace “yi haquri ki zo mu je a mota.. ke da baki da lafiya ma” Ta dan kalle shi tace “Hamma nan nan ne fa..” Matsawa yayi kusa da ita ya kamo hannunta yace “mu je a mota please…” Haka ya ja ta zuwa motar. Yana shirin budewa ne ya ga tayi pause yayinda ya ga tana kallon wani direction. MK dai da sauri ya bi direction din da take kallo ya ga wani yaro wanda shima yake kallon ta. Haka kawai sai ya ji zuciyar shi tana tafasa yayinda ran shi ya baci. “Waye shi???” abinda ta ji ya tambayeta kenan. Da sauri ta juyo ta kalli fuskar shi wadda ta canza lokaci daya. Hakan kuwa ya bata tsoro yayinda tayi saurin shiga motar ta zauna. Ganin bai rufe qofa bane ta san lallai yana son jin amsa ne. Muryarta tana rawa tace “Hamma ka shiga mota.. zan fadi maka” Ba tare da yace komai ba ya rufe qofar ta sannan ya zagaya shima ya shiga. “Hamma don Allah kayi haquri.. Sunan shi Jauro.. shine wanda ya nace akan shi lallai so na yake yi da aure tun a baya.. amma ni wallahi bana son shi” hahahaha… Ajiyar zuciya ya saki sannan yayi murmushi yace “toh yanzu da ya gan ki tare da ni shine yake ta harara ta?? toh me nayi mishi??”2 Cike da mamaki tace “Hamma bai harare ka ba fa” Ya tada mota sannan yace “baki dai gani bane… ni kam bari inyi sauri in dauke ki daga qauyen nan naku kafin ayi mun dukan tsiya.. gashi kuma banda qarfi..” Ji yayi ta fashe da dariya yayinda tace “bazan bari kowa ya taba ka ba Hamma… in dai ina raye bazan taba bari wani mummunan abu ya same ka ba” A yadda ta fada kuwa it came directly from the bottom of her heart. Murmushin jin dadi yayi sannan yace “Allah na gode maka da ka bani mata wadda ta damu da ni sossai…”5 Murmushi tayi yayinda ta ji kunyar yadda yayi addressing dinta- MATAR SHI!! Ummi dai yau ita ce rana ta farko da ta fara shiga mota tare da MK. Sossai motar ta birge ta.. qamshin turaren shi da ya gauraye da sanyin AC ne yake ta ratsa jikinta yayinda take jin ta a wani yanayi mai dadin gaske. Ita dai Allah ya sani da MK da duk wani abu nashi bala’in birge ta suke yi. Tabbas duk duniyan nan babu mutanen da take so sama da MK da Goggon ta. A haka dai ta dinga kwatanta mishi har suka iso gidan su Murjanatu. Bayan yayi parking ne yace “yanzu wai dama kina nufin a qafa zamuyi wannan tafiyar? ai akwai nisa..” Ummi tayi murmushi tace “wallahi babu nisa Hamma… kai dai kawai baka saba tafiya bane shiyasa… bari in je in zo” STORY CONTINUES BELOW Yana kallonta ta shiga gidan yayinda na ga ya bi ta da kallo yana ta murmushi… ****************** MK yana nan zaune a cikin motar shi ne ya ga Ummi ta fito riqe da Zainab a hannunta. Yana kallon su ya ga Murjanatu ta zaro idanuwa da baki yayinda take kallon motar shi tana yi ma Ummi magana wadda ta juyo ta kalli motar ta dan yi murmushi. Daga nan kuma sai ya ga Ummi tayi mata magana sannan suka fara approaching. Bude qofar motar yayi yayinda ya sauko da qafar shi daya waje.. Da sauri Murjanatu ta duqa har qasa tace “Hamma ina wuni” Ya miqa hannu zai karbi Zainab ne yace “lafiya lau, tashi don Allah ya gida??” Murjanatu ta miqe yayinda tace “lafiya lau” Ji suka yi yace “Cutie zo mana… ya sunan ki?” Ummi ta miqa mishi ita yayinda tace “Zainab..” Murjanatu ce tayi saurin fadin “kar ta bata maka kaya duk tayi wasa da qasa” Yana murmushi yace “ba matsala ai..” Gani suka yi ya zaunar da ita akan cinyar shi yayinda ya dinga yi mata wasa har suna hira. Ummi dai sossai MK yake birge ta.. shi kam he is a simple and down to earth human being. Ana fadin ‘yan birni suna da qyamar talaka dan kauye ita kam ta sani cewar banda MK. Murjanatu ce ta ja hannun ta suka matsa gefe yayinda tace “ke Ummi wallahi kinyi sa’a a rayuwar ki… kalle shi fa..” Ummi tana murmushi tace “na sani cewar nayi sa’a qawata toh amma matar shi fa bata so na??” Murjanatu tayi tsaki tace “toh me ya ruwanki da ita.. ai ba ita kike aure ba don haka wallahi ki riqe mijin ki da hannu biyu ku sha soyayyar ku.. Gashi fa da alama yana son yara. na tabbatar kuwa zaku haifi kyakyawa don kuwa ke mai kyau shima mai kyau”10 Zaro idanuwa Ummi tayi cike da mamaki hade da tsoro tace “yara??? mu fa ba zamuyi abinda ake yi a haifi yara ba.. a matsayin Hamma na zan cigaba da zama da shi”8 Murjanatu ta girgiza kai tace “tab.. aikuwa a yau na tabbatar ke din baki san komai ba.. toh ki je ki zauna tare da shi a matsayin Hamma mu gani…” Ta dafa kafadar Ummi cike da tsokana sannan ta cigaba da fadin “Wallahi na tabbatar babu abinda bazaku yi ba..”6 Kafin Ummi tayi magana ne Zainab ta rugo a guje riqe da wata qatuwar envelope ta miqa ma Murjanatu tace “Umma.. an bani” Ko da Murjanatu ta karba ta duba sai gani nayi ta zaro idanuwa tace “innalillahi wa’inna ilaihir raji’un…” Da sauri ta miqa ma Ummi wadda itama hankalin ta yake a tashe ta duba ta ga kudi bundle na 100k guda uku. Da sauri ta juyo ta kalli MK wanda yake riqe da waya a kunne yana magana.. Ji tayi Murjanatu tace “Ummi wadannan kudaden na waye?” Ummi wadda take dariya tace “naku ne qawata.. mu je kiyi mishi godiya” Murjanatu wadda qafafuwanta suka yi sanyi da qyar ta bi Ummi suka qaraso wurin MK wanda har sai da suka jira ya gama wayar sannan ta duqa har qasa tace “Hamma na ga kudi ka ba Zainab… sunyi yawa ai” Yana murmushi yace “babu yawa..” Tace “Allah ya saka da alkhairi.. Allah kuma ya bar zumunci.. mun gode qwarai” Yace “its okay” Ya kalli Ummi wadda take ta kallon shi yace “Baby kun gama sallamar mu tafi??” STORY CONTINUES BELOW Ta kalli Murjanatu tace “mun gama” Daga nan sai gani yayi sun rungume juna yayinda suka qi breaking hug din. Ji suka yi yace “zamu dinga kawo ziyara insha Allah kuma muna sa ran kema zaki zo wata rana..” Da sauri Ummi tayi breaking hug din ta kalle shi sannan tace “dagaske Hamma zamu dinga zuwa?” Yana murmushi yace “Insha Allah… duk lokacin da kike so..” Sossai ta cika da murna. A haka dai suka yi sallama da Murjanatu suka tafi yayinda Murjanatu ta dinga mamakin irin arzikin da MK yake da shi da har ya basu kyautar kudi har yawan haka… Nikuwa nace 300k ne fa🤣… Allah sarki qauye dayake cost of living is very low compared to birni…7 ♧♧♧♧♧♧♧♧♧ Da suka dawo an kusa kiran sallar La’asar don haka ne ko da Ummi ta shiga gida shi MK ya tafi masallacin da yake nan kusa da gidan Goggo tare da Lado don yin sallah. Bayan an idar ne mutanen da suka yi sallah tare suka dinga gaishe shi tare da yi mishi godiya na ceton Ummi da yayi daga zaluncin su Daada. MK dai a siyasance ya ja Limamin masallacin har wurin motar shi ya danqa mishi kudade masu yawa a cikin envelope yace a gyara masallaci.. sadaka fisabillillah. Haka Limamin ya dinga godiya. ♧♧♧♧♧♧♧♧♧ A lokacin da MK ya dawo gidan Goggo ya tarar da Ummi kwance a kan cinyar Goggon tana ta rusa kuka yayinda take sauraron nasihar Googgo… Ko da MK ya zauna ji yayi tana fadin “….kiyi zaman haquri da abokiyar zaman ki.. na san ki da haquri Ummi, ki dora akan wanda kike da shi. Banda neman tashin hankali. Sannan mijinki.. Ki tabbatar kin kula da al’amuran shi, ki zamanto mai kiyaye duk wani dokoki da zai baki.. Aljannar ki tana qarqashin qafar shi don haka duk abinda ya sa kiyi mishi ki tabbatar kinyi matuqar bazai saba ma addinin mu ba. Allah yayi miki albarka.. Allah ya jiqan iyayen ki kuma Allah ya baku zaman lafiya” Kukan dai take yi har yanzu amma marar sauti. Goggo ta kalli MK tace “toh Kabiru, ga Ummi nan na baka ita amana.. Ka dinga dubi da matsayinta na marainiya ka dinga kyautata mata.. ka zamanto mai kare ta daga abinda zai cutar da ita domin kuwa batada kowa sai Allah sai kuma kai.. Allah yayi albarka” MK yace “insha Allah zan kula da Ummi… Kar ki samu damuwa Goggo” Goggo ta dafa Ummi tace “tashi ku tafi Ummi… Allah ya tsare” Ummi tana kuka ta tashi yayinda Goggo tace “bari in dauko miki kayan ki…” Da sauri MK yace “bar kayan nan Goggo… za’a siya wasu” Goggo tace “toh ai dukda haka ko kala biyu…” Yana murmushi yace “ki bar su dai Goggo..” Tace “toh shikenan… Allah ya saka maka da alkhairi Kabiru” Yace “Ameen” Har wurin mota Goggo da Lado suka rako su. Bayan ya bude ma Ummi ta shiga ne ta kifa kanta a gwiwa ta cigaba da kuka yayinda Goggo da Lado suke ta lallashinta. MK kuwa ko da ya zagayo ya bude qofar baya wata jaka na ga ya bude ya fiddo wani qaton envelope da kudade a ciki ya miqa ma Goggo yace “ga wannan Goggo… Zan aiko su Bashir da saqo sannan don Allah akan maganar da muka yi…” Wacce magana???🤔6 Murmushi Goggo tayi tace “kai Kabiru… kai kuwa wane irin mutum ne.. don Allah mu bar maganan nan…” Shima yana murmushi yace “kar ki damu Goggo.. hakan zai fi ai” Gani nayi ya sake dauko wani envelope din ya miqa ma Lado yace “Dan uwa kaima ga naka..” Lado ya duqa har qasa ya karba tare da fadin “Allah ya saka da alkhairi Hamma… nagode qwarai” Ya qara miqa ma Lado wata envelope din yace “wannan ka kai ma malamin da ya koyar da Baby karatu..” Lado yace “Malam Lawali kenan ko??” MK yace “yes shi..” Goggo ta girgiza kai tare da fadin “kai amma an gode Kabiru.. wannan dawainiya haka. Ubangiji Allah ya saka maka da alkhairi” Yace “ameen Goggo” A haka dai suka yi sallama suka tafi yayinda Ummi take ta kuka.3 ♧♧♧♧♧♧♧♧ A cikin mota kuwa Ummi sai rusa mishi kuka take yi yayinda yake ta faman lallashin ta tare da gaya mata maganganu masu sanyaya rai. Da qyar ta haqura ta daina kukan amma fa da ganin fuskarta ka san akwai damuwa. Wayar shi ce ya miqa mata tare da fadin “ko baby zata buga game ne..” Gani yayi ta sa hannu ta karba yayinda ta shiga game ta fara bugawa. Sossai hankalin ta yayi nisa a buga game din wanda da alama ya mantar da ita damuwar da take ciki. MK dai yana tuqi yana kallonta. A ranshi ne yace “Alhamdulliah.. finally, I got her back..”1 .

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *