UNCLE NE CHAPTER 1 BY NIMCYLUV
IBADAN
is the the capital and most populous city of Oyo state in Nigeria.
SANGO AREA
Unguwar Masu kuɗi ce,Unguwa ce da babu wanda ya damu da rayuwar wani,Unguwa ce mai cike da Attajirai,Malamai,haɗi da ƴan boko,Haka kuma Unguwa ce mai cike da ƴan duniya wanda idanunsu suke a buɗe,basa jin wa’azi balle faɗa,haka nan babu wanda ya isa ya tunkaresu da niyyar gaya masu kuskurensu.
Dugun layine wanda yake shimfiɗe da lafiyayyan titi wanda ya ƙara fito da ƙyan unguwar.
Wasu jajaye fitilone sukaiwa titin unguwar ƙawanya,wanda a kullum suke haska unguwar musamman cikin dare,gefe da gefen titin wasu green flowers ne masu ƙyau wanda suke fidda wani daddaɗan ƙamshi.
Can kusan ƙarshen layin wani haɗaɗɗan gidane ginin zamani,tun daga jikin tafkeken get ɗin zaka san tabbas wannan gidan bana ƙana nan mutane bane,ajikin get ɗin anyi rubutu inda aka rubuta hause no 133.
Sosai harabar gidan taƙawatu da kurayan furanni na zamani masu ƙyau da tsari,Compound ɗin gidan cike yake da manyan motoci na zamani irinsu,boggatti,ferari,da sauransu.
Yanayin ginin gidan irin mai sama da ƙasa ɗinanne ma’ana dai ginin bene mai hawa biyu.
Side ɗin parko na gidan wanda ya kasance hawan farko na gidan,babban parlour zaka fara tararwa gefen parlour’n kuma ɗakuna ne masu ɗan yawa kusan bedroom ɗin shida,left hand ɗina nayi domin shine yafi jan hankalina fiye da sauran part ɗin, Tun daga ƙaramin parlour’n dake cikin part ɗin na fara jiyo fitar numfashi mai kama dana zaucewa a hankali na tura kaina cikin bedroom ɗin kasancewar a buɗe yake,saurin tsayawa nayi sabida ganin wata ƙyaƙƙyawar matashiyar mata wacce aƙalla ba zata huce shekara ashirin da biyar ba zuwa shida.
Tana durƙoshe gaban bed ɗin dake ɗakin yayinda hannunta ke riƙe da gadon gaba ɗaya jikinta rawa yake,banda nishi da gurnanin wahala babu abinda ke fita a bakinta,yayinda turtsetsen cikinta ya sauka zuwa mararta banda juyawa da motsi babu abinda “ƊAN‿ cikin nata yake,da alamu shima ya ƙago yazo duniya,karkarwar jikin tane ya tsananta gaba ɗaya ta jigata ta fita haiyacinta banda kiran sunan Allah babu abinda bakinta yake ke faɗi,Can ƙasan zuciyarta kowa maganar data keson furtawa a saman bakinta tane ta kasa,burinta bai huce bakinta ya buɗe ta samu damar faɗin abinda ke damunta cikin rai da kuma zuciyarta,Runtsa idanunta tayi da ƙarfin sabida wani juyi da abin cikinta yay tare da naushin mararta nan take jini ya ɓalle mata ya soma zuba,cikin yanayin na fitar hayyaci tare da zaucewa haɗi da fidda rai ta ɓude baki da ƙyar tace.
“Ya hayyuu ya ƙayyumuu
ya kaliƙu ya zul arshidd majidd,ya fa’alulluma yurid biraha matika astagisuuu”
Takai ƙarshen addu’ar tana sakin wani fitinanan nishi wanda ya kusa ta fiya da numfashinta ya rabbi nan take wani..
Kamar amafarki Mameey dake ƙwance bisa tangamemen royal bed ɗinta ta jiyo sautin numfashin Zulfa cikin kunnuwanta lumshe idanu tayi tana jin kamar a magagin barci take, da sauri ta miƙe zaune daga ƙwancen da take wani irin hantsilawa Mameey tayi daga gadon zuwa ƙasan gadon,a gigice ta fara gyara ɗaurin zaninta dake kuncewa sabida fargaba,tabbas idan bata manta ba yaune E.D.D Zulfa ya cika gaba ɗaya ta manta,cikin tsoro fargaba kiɗima tashin hankali ta fara sakkowa daga stairs ɗin benen.
Tun a babban parlour ta fahimci aƙwai matsala kuma ta ƙara tabbatarwa kanta Zulfa naƙoda take da sassarfa ta ƙarasa shiga cikin part ɗin Zulfa,cikin sauri Mameey ta ƙarasa shiga cikin bedroom ɗin,tana shiga ta samu Zulfa durƙoshe cikin jinin wanda ya ɓata jikinta gaba ɗaya,da sauri ta ƙarasa wajanta tana salati tare da faɗin.
“Zulfa mene zan gani haka?kika zauna cikin ciwo kin san illar duguwar naƙuda kowa?ohhh ni Salamatu yau naga abinda yafi ƙarfina wannan wanne irin jinine haka?mun shiga uku”,
Ta faɗi hakan tana sakin kukan tausayi halin da Zulfan ke ciki,sabida ganin jinin dake zuba ta jikinta ga kuma yadda numfashinta ke sarƙewa jikinta banda rawa babu abinda yake,da hanzari ta ƙarasa matsawa inda take sabida kan babyn da taga yana fitowa,wata jijjiga Zulfa ta fara idanunta na kafewa.
Ganin hakan yasa Mameey sakinta tare da ficewa da gudu tana tafe tana ƙwala kiran sunan Alhaji!! Alhaji!! Alhaji!!!
Alhaji Kabeer na kishin giɗe saman wata lafiyayyiyar sofa,hannunsa dafe da saitin zuciyarsa,yana jin yadda take buga masa da ƙarfi,ga wani raɗaɗi da ɗaci daya keji a cikin maƙoshinsa,gefe guda kuma yana jin tsoro da fargaba haɗi da zullumi wanda bai san kona menene ba.
Ya rasa dalilin daya sanya yake mafalki mara ƙyau akan Zulfansa mace mafi soyuwa a cikin ransa,tabbas bazai jure ganinsa cikin wannan halin mafalkinba,kamar yadda bazai jure ganin Zulfa cikin wani hali ba.
Saurin buɗe idanunsa yay jin muryar uwar gidansa na kiran sunansa,da sauri ya dira daga kan sofar yana fita sukaci karo da Salmerh a birgice ya kalli Salmerh tare da faɗin..
“Salmerh mene ya sami Zulfa?..kada ki sake bakinki ya faɗi babban kalamai dazai sanya zuciyata bugawa..”
Bakinta na rawa tace
“Zulfa haihuwa inajin..”bai bari ta ƙarasa maganar ba ya ƙwasa da gudu zuwa part ɗin Zulfa.
da gudu Mameey ta mara masa baya,suna zuwa tana haihuwa ganin zata danne jaririn ya sanya Alhaji Kabeer saurin isa gareta,yana zuwa ya saka hannu ya gyara mata zama,tare da amsar rezar hannun Mameey ya yanke cibiya,cikin ikon Allah a lkcn mahaifa ta faɗo,yana ganin haka ya saka hannu ya miƙar da ita tsaye cikin murna da farin ciki ya rungometa a jikinsa yana shafa sumar kanta idanunsa fal hawayen farin ciki,bai taɓa tunanin zai samu haihuwa nan kusa ba,sai gashi ubangiji ya azurtashi da ita a lkcn dabai taɓa tunanin samunta ba,tabbas ya yarda da wannan kalmar da ake cewa inda rai da rabo,haka kuma mutum baya fidda rai da samun rahamar ubangiji,domin shine mai bayarwa a lkcn da yaso haka kuma shine mai hanawa a lkcn dayaso,wasu hawayene suka fito daga cikin idanunsa cikin muryar farin ciki yace.
“Thank you soo much my Anuuu,Allah yay maki albarka nagode sosai da ƙyautarki nagode Allah ina sonki Allah ya baki lafiya”
Mameey janye jaririn tayi jin yana tsala kuka a wani zani mai ƙyauta ta ɗaukesa,kana ta zaune bakin bed,catton da zaitun ta fara goge masa jiki da ita,murmushi tayi ganin yadda yake ƙoƙarin sanya hannu a baki da alama da yunwa yazo,sai tsala kuka yake,a cikin ranta take jinjina ƙyan yaron da kuma baiwar da ubangiji yay masa,domin ƙwayar idanunsa ta kasance blue ce,kamarta turawa,ga wani ɗan cindo a gefe yatsanshi.
A sanyaye Zulfa ta rungome mijinta Alhaji Kabeer idanunta na zubar da ƙwalla tace “Yaa rahamanu”murmushi yay tare da sumbatar goshinta,kamar an tsikareta ta sanya hannu ta ture Alhaji Kabeer daga jikinta,a hankali ta fara yin baya ganin hakan ya ƙara matsuwa kusa da ita yana shirin kamata yaji ta fasa wata uwar ƙara,a gigice ya ƙarasa wajanta kafin ya riƙeta tasa hannu ta hankaɗesa tare dayin waje da gudu jinin haihuwa nabin jikinta….
Ƙarar taka birkin motar da kuma ihun da Zulfa tayi shine yaja hankalinsa zuwa gareta,hannu yasa ya dafe saman goshinsa tare da runtsa idanunsa,cikin kuzari haɗi da sassarfa yasa hannu ya buɗe murfin motar,gaba ɗaya ƙafafunsa ya fito dasu waje tare da zuro da sauran jikinsa,lokacin har mutane sun cika a wajan sun yiwa motar ƙawanya,cikin natsuwa ya fara takawa har wajan da Zulfa ke ƙwance cikin jini,da dukkan alamu tayi muguwar buguwa a kanta domin shike tsiyayar da jini,ɗan tsaki yaja ganin tarin mutane amma babu wanda yay ƙoƙarin taimakonta.
Numfashi ya sauke tare da kallon drevernsa mai suna Joseph cikin jarumtar data rage masa yace “ɗauketa zuwa mota mana” yana faɗin hakan ya juya tare da nufar side ɗin baya ya buɗe,ɗan ja da baya ya bawa Joseph waje domin ya sanya ta a mota, bayan an ƙwantar da ita shi kuma ya kuma mazaunin mai zaman banza ya zauna Joseph kuma ya zauna mazaunin drever.
“Yallaɓai ina muka nufa ne?nasan dai babu maganar wani meeting yanzu saboda condition ɗin da wannan matar ke ciki,Nina gama kamar mahaukaciyace”
Tunda ya fara magana har zuwa lokacin da yay shuru mutumin daya kira da sunan YALLAƁAI baiyi magana ba,zuciyarsa ta tafi wani tunani nada ban,lallai mutum da yana sanin ƙaddarar da za ta samesa tabbas da yayi ƙoƙarin kujewa faruwarta,abinda ya kawo shi wannan garin da ban,amma abinda ya samesa da ban,wannan wanne irin abune.
Mene ya fito da ita? ina zata je?wanne jini kebin jikin?wannan sune tarin tambayoyin da suke zuciyarsa amma ya gagara furtasu sabida nauyin da labɓansa sukai masa.
cikin ƙosawa da maganar Joseph yace “muje UNITY MEDICAL CENTRE HOSPITAL dake nan IBADAN”
Cikin sauri Joseph ya joya motar da taimako map suka samu suka isa asibitin kasan cewarsu baƙi ne a garin.
Suna zuwa asibitin kai tsaye emagency aka shigar da ita,likitoci suka rufu a kanta,bin kican farko suka gano haihuwar da tayi da kuma ƙaruwa da tayi wajan haihuwar,hakan tasa suka yi mata ɗinki tare dayi mata allurar haɗi da sanya mata drip,suna gamayin komai suka fito daga cikin room ɗin da aka sanyata ciki,da sauri drever’n ya miƙe tsaye ya fuskanci babban likitan cikin sonjin abinda ke damun matar yace.
“Dr yaya jikin nata?ta samu lafiya dai?”
Jinjina kai likitan yay tare da juya ƙwayar idanunsa zuwa ga mutumin dake can gefe yana leƙa window,sosai yake mamakin mutumin domin ya hangu zallar damuwa da kuma tashin hankalin dake ƙwance a saman fuskarsa,yana ɓoyewa ne kawai sabida jarumtarsa, murmushi likitan yay kana ya kalli Joseph yace.
“Kada ka damu komai zaiyi dai-dai tasha wahala wajan haihuwa ne,ga kuma ƙaruwar da tayi, amma da yardar ALLAH zata samu lafiya amma ina babyn data haifa?kuma yana da ƙyau ace macace a wajan ta ba maza ba”
Sai a lokacin Mutumin ya juyo zuwa gare su tafiya kaɗan yay yace “Kace haihuwa ce ko?amma macen data haihu mai zai fito da ita kan titi? tabbas bayan haihu aƙwai wani ɓoyayyan tuggu a ƙasa..”
“kana nufin kace baka santa ba?kuma baka san asalin wacece ita ba?”
Dr ya tambaya shima cike da tashin hankali domin shima abin ya fara rikitashi “Amma yallaɓai mai zai hana idan ta farka ka tambaye ta sabida gujewar masu haihuwar cikin shege kuma su yadda shi,jinjina kai yay cikin gamsuwa da maganar Dr yace “ok amma sunana JABIR ba yallaɓai ba,zuwa yaushe zamu dawo muganta domin a gobe nakeson komawa birninmu” jin abinda Jabir yace ya sanya Dr yin murmushi yace “babu damuwa Jabir zuwa dare saika dawo ko?”da haka sukai sallama kai tsaye suka nufi Golden tulip hotel ɗin da suka sauka a cikinsa.
To abuba kamar wasa tun Alhaji Kabeer na ganin abun ƙarami harya shallake tunanin sa,duk inda zai bincika akan ɓatan Zulfan yayi amma babu labari,tun a hanyarsa ta zuwa wani gidan redio ya kira gidansu Zulfan ya shaida masu abinda yake faruwa,sai wajan magriba ya ƙarasa gidansa dake unguwar sango.
a babban parlour ya iske Mama wato mahaifiyar Zulfa da kuma Jawad ƙanwar Zulfa sai kuma Lamir yayan Zulfa daman su uku ne wajan Mahaifiyarsu,mahifinsu kuma ya daɗe da rasuwa.
cikin ɓacin rai Lamir ya kalli Alhaji Kabeer sannan yay tsaki tare da faɗin.
“Tabbas munyi kuskuren bawa ɗan kwararo auran tsatsanmu,amma wannan kuskuren na kine Mama da kuka nace a bawa Zulfa shi bayan koda wasa baku taɓa ganin danginsa ba, baku san waye shi ba, kawai kun ɗauki yarinya kun bashi,wama ya sani ko ɗan yan kan kaine,ko kuma masu kidnapping banda haka tayaya zai kalli ƙwayar idanunmu yace mana an rasa Zulfa kamar wata allura kai aƙwai wata a ƙasa.!!”
Lamir ya ƙarasa maganar cikin ɗaga murya haɗi da yiwa Alhaji Kabeer tsawa.
Mama da hanyar yanzu ta kasa cewa komai sai tasbihi take da salatin Annabi a cikin zuciyarta ta ɗago kai ta kalli Lamir tace.
“idan hankali ta gushe nutsuwa ce ke nemushi Lamir amma wannan abinda kake babu abinda zai sauya daga ƙudirar Ubangijin”
“Ohh! yanzu Mama kina nufin muyarda da maganarsa kenan ko?tayaya zai kawo mana zancen da bazai taɓa yiyuwa ba,tabbas wannan abun tuggu ne kawai,amma wallahi saika fito mana da Zulfa”
duk yadda Alhaji Kabeer yaso danne abinda ke ransa kasawa yay,tabbas yana da hakuri da kuma juriya da dukkan wani wulaƙancin da mutum zai nuna masa,amma a wannan karan ya kasa danne abinda ya keji yay,tabbas Lamir baiyi karya ba,shi kansa bai san wanene shi ba,ya wayi gari kawai ya gansa a wannan garin na ibadan,daga ina yake?wanene shi?mene Asalinsa?ina danginsa suke?duk babu abinda ya sani shi dai yasan yana rayuwa farin ciki ne kawai da iyalansa da burin ganin jininsa a duniya, amma wata rana yana tashi da kewa da kuma raɗaɗi a zuciyarsa, ƙwaƙwalwarsa nason tuna masa wani abu daya faru dashi a baya wanda bai san ko menene shi ba.
“Lamir yana da ƙyau kayimin kyakkyawan zato, wallahi ina son Zulfa fiye da kai da kake wannan maganar,ina son Zulfa fiye da yadda na keson nasan wanene ni,dan ALLAH kayi hakuri ka barni da abinda na keji a raina,ka barni da kuncin da kuma kewar farin cikina…”
“Kai malam nika isheni da wannan surutun na banza kawai kace ka tsaface mani ƙanwa …” marin da yaji an sauke masa ne yasa yay saurin dafe fuskarsa tare da haɗiye sauran maganar da bata samu damar fitowa ba,cikin takaici ya kalli Mama yace “Mama akan wannan mutumin kika mareni? ƴar uwata yaje ya saida fa” cikin faɗa faɗa da kuma saurin maganar da take dashi ta fara magana “wallahi Lamir ka fita a idanuna tun kafin na bashi auren Zulfa na yarda da shi,tun kafin akai Zulfa gidansa nayi istihara akansa,na yarda da shi fiye da tunaninka har abada bazan taɓa yarda shine ya salwantarmin da ƴar ba,dan haka ba kinka ya kiyayi aibata mutum domin wata rana zakayi ladama”
baki ya buɗe da niyar yin magana babyn dake bayan Mameey ya fara kuka,cikin sauri ta sakkoshi daga bayanta ganin yana ƙoƙarin sanya yatsansa a baki yasa ta ɗauki dabino da zam zam ɗin data jiƙa masa ɗazo,a hankali ta sanya masa a ƙaramin bakinsa bisa mamakin ta sosai yasha,yana gamawa ta goge masa bakinsa tare da ɗora shi a kafaɗarta har sai da yay gyatsa,luf yay a ƙirjinta yana maida numfashi,Mama data zubawa babyn idanu tana hango zallar kamaninsa da Zulfanta tayi saurin goge hawayen idanunta tace “da wanne suna kayi masa huɗuba?” kansa a sunkuye dan baya so kuwa yasan kuka yake ya saki ajjiyar zuciya yace “MUHAMMAD JALAL” ma sha Allah Ubangijin ya rayasa bisa tafarkin addini,Mameey ce tace “Ameen”
shuru ne ya ziyarci parlour’n kowa da abinda yake saƙawa cikin ransa inda Lamir yake cike da kunci da baƙin cikin marin Mama tayi masa akan Alhaji Kabeer hakan yasa ya ƙara jin tsanarsa fiye da ko yaushe, Mama kam abubuwa da yawa ne sukai mata cunkoshe a zuciya domin rashin Zulfa a rayuwarta babban giɓine tana dannewa ne kawai sabida Lamir domin tasan halinsa,Jamal da tun ɗazo take kukan rashin yayarta ta tace “Mama yanzu shikenan mun rasa adda Zulfa?”shafa kanta Mama tayi tace “kiyi hakuri Auta muci gaba da addu’a Ubangiji ya kaita hannu na gari in sha Allah ba zata wulaƙanta ba”gaba ɗaya suka haɗa baki wajan faɗin “in sha Allah”
Misalin 8 na dare Jabir da Joseph suka ƙarasu hospital ɗin direct office ɗin Dr suka nufa,sallama ɗauke a bakinsa ya shiga ciki da murmushi Dr ya amsa sallamar tare da bashi waje ya zauna,bayan sun gaisa ne Jabir ya kalli Dr yace “yaya jikin nata?”shuru Dr yay kafin ya numfasa yace “aƙwai matsala wallahi”lumshe idanu Jabir yay kafin yaja numfashi yace “tame kenan?”cikin nutsuwa Dr ya zare farin glass ɗin dake manne a idanunsa numfashi ya sauke kafin ya samu damar faɗin “bayan halin da take ciki na haihuwa da kuma jinjigar da yasu kamata Allah bai yi ba,a fahimtar kda nayi mata ɗazo na fahimci aƙwai juyewar tunani a tare da ita,ma’ana dai ta samu taɓin ƙwaƙwalwa,babban tashin hankalin bata magana sannan kuma taƙi yadda kowa ya taɓa ta,da kayar akai mata wanka aka sauya mata kayan jikinta”wani gumi ne ya fara karyowa Jabir gaba ɗaya jikinsa ya ɗauki rawa, cikin Hausar sa da baya fita sosai yace “innalillahi ya subuhanallah meke nan hakan?” Joseph ne ya amshi zan can ta hanyar faɗin “yallaɓai kawai mu sallami Dr muyi tafiyarmu mene za muyi da mahaukaciya wacce bamu san a salinta ba”ɗan tsaki Jabir yaja cikin tashin hankalin da yake ciki yace “Dr mene matsalar daya haukata ta? jinjina kai Dr yay tare da faɗin “shine abinda har yanzu bamu gano ba,duk abinda muka bincika a jikinta yana nuna komai normal only God know what happen to her”
miƙewa Jabir yay kana yay waje abinsa ganin hakan yasa Joseph da Dr suka mara masa baya,kai tsaye room 12 ya nufa inda aka ƙwantar da ita,a sanyaye ya ɗura hannunsa a saman handle ɗin ƙofar tare da ɗan turawa kaɗan tura kansa yay cikin ɗakin haka kawai ya samu kansa da faɗuwar gaba,runtsa idanunsa yay kana ya fara karatu addu’ar da yazo masa,a ƙwance ya sameta ta rufe idanunta gaba ɗaya tulin sumar dake ganta ya baje saman pillow’n da aka ɗura mata kanta “ka ganta ko? tun ɗazo a haka take ko tea taƙi sha” jinjina kai Jabir yay kana yace “tafiya zamuyi” jin haka yasa Joseph zaro idanu cikin halshan turanci yace “tayaya ne zamu shiga BIRNIN NUFAR da MUSULMA bayan kaima kasan ba zaman daɗi kake ba sabida musuluntar da kayi” wata harara Jabir ya watsawa Joseph hakan tasa yay shuru bai ƙara faɗin komai ba “Dr tashe ta”cikin dabara Dr ya fara bubbuga pillow’n da take kai a zabure ta miƙe zaune tare da ƙanƙame pillow’n a ƙirjinta haɗi da jijjigashi,gaba ɗaya zuba mata idanu sukai suna kallon ikon ALLAH,a hankali kuma ta tura hannunta cikin riga ta fara ƙoƙarin fito da Nonon ta da duk alamu a tunaninta wannan pillow’n kallon babynta take masa,ganin hakan yasa Jabir yay saurin faɗin “keee mene haka”duk da irin tsawar da yake mata amma ko a jikinta,ganin da gske fito da nonon take sonyi yasa yay saurin ƙarawa inda take zaune,yana zuwa yasa hannu ya fincikota zuwa gabansa hakan kuma yay dai-dai da fitowar…
Juyi take sosai akan makeken royal bed ɗin ta sai nishi take sama-sama hannunta dafe da mararta,wani zafi da raɗaɗi ta keji a ƙasan mararta,cikin tauyawa halin da take ciki ya samu bed side inda wata sofa ke ajjiye ya ƙwantar da bobo, jiki a sanyaye ya ƙarasa inda take a ƙwancen cikin sanyin murya yace “what is going on dear?”ya tambaya yana miƙa hannu domin taɓa inda take riƙewa,cikin zafin ciwo tace “don’t touch me Abbou Jalal” da mamaki ya kalleta yace “mene yasa? bayan kina halin ciwo” hawayen da take ɓoyewa ne suka shiga fita daga cikin idanunta kafin taja numfashi tace “babu abinda zakai min,duk da nasan ciwo na kaine maganinsa amma a yanzu kai ɗin kamar gidan ashana ne babu ashanar ciki”ɗan waro idanu yay da mamaki a kan fuskarsa kamar bazai magana ba sai kuma yace “yana da ƙyau nasan mene matsalar ki,koda bazan iya yi maki magani ba” kafin yay wani dugun tunani yaji tasa hannu ta jawoshi jikinta tare da ƙoƙarin haɗe bakinsu waje guda da saurin ya juyar da kansa gefe guda tare da faɗin “azumi zanyi alrdy nayi sahur so ki rabo dani” kanta ta sunkuyar gefe guda ba tare da tace komai ba,yasan tabbas yana shiga hakkƙinta amma yaya zai yi,a duk sanda yay sex da ita yana jinsa tamkar a gidan bread yaya take so yay mata, dalilin hakan yake danne abinda ya keji a game da ita sabida bayaso ya nuna mata banbanci a tsakaninta da zulfa,hannu yasa ya ɗago ta zuwa jikinsa cikin sanyin murya yace “look dear kalleni”ɗago kai tayi ta kallesa cikin fahimta ya shafi kanta yace “ba tun yanzo ba nasha gaya maku aƙwai infection jikinki,wanda shine yake ƙara sanya maki ciwon marar, and ina da tabbacin shine yasa har yanzo baki samu dace da haihuwa ba”cikin mamaki take kallonsa kafin tace “wanne irin infection kuma?”murmushi yay yace “nifa doctor ne dear kuma na tabbatar kina dashi domin ina jin haka a tare dake”
infection kashi uku ne.
Ciwon sanyin da ke damun mata kala kala ne. Amma zamu takaita akan guda 3 wanda sune suka fi cutar da mata.
1- Wanda bacteriya ta ke janyowa (Bacterial vaginosis)
2- Wanda fungi ke janyowa (Yeast Infection ko Candidiasis)
3-wanda ake kamuwa ta hanyar jima’i
“yanzu dear bana cikin nutsuwata kema sheda ne” hannunsa ta jawo ta dora5 saman mararta tare da cusa shi,lumshe idanunsa sabida bai son abinda take buƙata a tare dashi “but i need you”hannunsa za zare zare da miƙewa ba tare da yace komai ba ya nufi inda Jalal ke ƙwance yana bacci ɗaukar sa yay tare da dawowa inda take ƙwancen a gaban ta ya anjiyeshi tare da faɗin ” i don’t mean to hurt you please try to understand me ko babu yawa,ko nace zan maki abinda kike buƙata nai ƙarya you alre6 knew Zulfa is missed”shuru kawai tayi masa tana kallon bobo dake bacci harya gama maganarsa ya fice.
A can Golden tuilp jericho hotel fitowar Jabir kenan daga bathroom yana sanye da ƙaramin towel a waist ɗinsa sai kuma dari blue a hannunsa ya goge jikinsa dashi,cikin sauri yake gudanar da komai tym to tym ha kan jaa tsaki kaɗan,gaban dressing mirrow ya ƙarasa tare da tsurawa kansa idanu, ɗan waro idanu yay ganin a wuni guda ya faɗa sam ya bata rabonsa da abinci tun jiya da safe,ya mutsa fuska yay tare da faɗin “look Jabir control ur self komai zai dai-dai everthing will be fine but yaya zanyi da Papa?yanzu nasan suna shirya bikin haɗa samari da ƴan mata domin tantance wanda suka isa aure tabbas naje da waccen yarinyar sai a haɗata da wani shin yaya zanyi ne,ohh God help me”wayarsa ce ta fara ringing alamar kira yazo masa,murmushi ya saki tare da picking call ɗin ya manna a kunnansa yace “Selemu alaika” dry Katarina tayi sabida wata hausa da taji yay mata “hello brother how Are you?” lumshe idanu yay yace “adey fny na and u?” miƙewa tsaye tayi sabida tafiyar da taji a bayanta cikin sauri ta shige cikin bathroom tace ” Papa ya sanya a saka maka idanu indai harya tabbata ka musulunta ko kuma anga kana sallah a tsireka da kibiya i don’t want to lose you dan Allah kada ka dawo”wani murmushi takaici yay yace “all this akan na musulunta ne? dole zan dawo i will back you”cikin Muryar kuka tace “but…”ohh ya rabbi see lrt” yana faɗin hakan yay rejecting call ɗin cikin sauri ya fara shiri yana gamawa Joseph yana zuwa ticket ɗin ya nuna masa harda na Zulfa jinjina kai Jabir yay yace “good job” trolley kayansa ya bawa Joseph kana ya gama shiryawa cikin wasu ƙananun kaya masu ƙyau, direct Joseph wajan motar hotel ɗin ya nufa yana zuwa ya zoba kayan a Boot ya shiga gefen drever ya zauna, Jabir kansa ya tura cikin ɗakin a zaune ya sameta gaba ɗaya ta hargitsa gashin kanta ga kuma pillow data rungome sai cusa masa kyawawan breat ɗin ta a baki sai jijjigashi take tare da shafa saman pillow’n like tana shafa kan babynta(jaririnta) shuru yay mata yana kallon ikon Allah ganin tym na tafiya yasa yace “ohyyya Madam come Les go” da sauri ta ɗago kanta tare da ƙanƙame pillow’n hannunta cikin wata iriyar murya mara daɗi tace “ya rahamanu” ƙarasa shigowa ciki yay tare da zama kusanta yace “bani babyn muga ko”jin abinda yace tayi sauri faɗawa jikinsa gaba ɗaya da sauri ya runtsa idanunsa tare da faɗin “subuhanallah” domin itane kalmar da yafi Zama a bakinsa,hannu yasa ya cireta a jikinta ɗan waro idanu yay sabida ruwan nono da yaga yana zuba cikin sauri ya kawar da kansa yace “mai da ciki riga”Zulfa kam sam bata fahimtar abinda ya kece mata domin ganinsa take tamkar Alhaji kb,hannunsa ta kama ta fara ƙoƙarin ɗurawa a brest ɗin ta baki ya buɗe zai mata tsawa sai kuma yay saurin rufe bakinsa cikin dauri ya saka hannunsa a saman brest ɗin ba tare da wata manufa ya mai dashi cikin riga da idanunta kawai take binsa,ganin bata wani buge buge bare duka yaji daɗin hakan vail ɗin abayar daya siya mata jiya ya ɗaure kai tashi kana yasa hannu ya miƙar da ita tsaye nan fa tace sam bata san wannan ba,haka yay ta fama amma fur taƙi fita koda ya matsa mata saita shiga nuna masa wajan ƙofar fitar, ganin baiga komai yasa yashi sauri ɗaukar ta cak ya nufi waje da ita,abinda bai sani ba,da zarar ya nufi fita da ita sai taga wata ƙatuwar halitta na kusanto inda take tsaye hannunta ɗauke da wasu manyan ƙaho dalilin da yasa taƙi fita kenan,a haka suka ƙarasa mota ta tura ta a back side shima ya shiga,yana shiga ta faɗa jikinsa tare da faɗin “ya rahamanu” kanta ya shafa cikin ƙasa da murya yace “sorry” a haka motar ta nufi airport dasu suna zuwa ana kiran masu tafiya cikin sauri Joseph ya nuna ticket ɗinsu Jabir da Zulfa a vip side Joseph kuma a normal side,lumshe idanu Jabir yay yana jin sabuwar shafin ƙaddararsa na ƙara kusan to shi,bayan yasa wayarsa a airplane mode ya fara duba sabbin message ɗinsa na email,tym to tym yana kallon Zulfa data ƙanƙame sa idanunta na fidda ƙwalla a haka jirgin ya fara tafiya dasu zuwa sararin samaniya to Zulfa a sauka lafiya ki ɗan bamu a ron wasu shekaru kafin muzo gareki.
to abufa kamar wasa gaba ɗaya Alhaji kb baya cikin nutsuwarsa koda yaushe cikin falkin Zulfa yake gefe guda kuma da wani irin yanayi da yake gani cikin falkin wanda har yanzu ya kasa tantance wanne abune,ko ina an baza rahotanni akan ɓatan nata ko ina maganar Zulfan ake,hatta su mama6 da Jamal da Lamir cikin posting picture nata suke a I.G, Twitter, facebook, Whasapp, ga kuma vedio ɗin ta da suke sakawa a tik tok,dukkan Wasu kafafen sadarwa cikin neman Zulfa Zubair amma shuru koda wasa ba’a samun wanda yace yaga mai kama da ita tamkar an kulle bakin jama’a yauta kasance ranar sunday sati biyu ta ɓatan Zulfa Alhaji kb na zaune da bobo a hannunsa yana masa wasa,cikin sauri ya saki bobo daga hannunsa tare da safe saman forehead ɗinsa dake sara masa,da hanzarin Mameey ta tare Jalal kafin yaje kasa “innalillahi sakinaa fa kayi Alhaji yanzu da yaji ciwo fa,koda yake kai babu ruwanka domin ni jama zasu zaga musamman dangin Zulfa”saurin kallonta yay cikin ɓata fuska yace “what!? wanne suna kika ambata?”da mamaki take kallonsa tace “ehhh Zulfa nace kuma nasan kaji”ta faɗa tana jijjiga bobo dake kuka yana ƙoƙarin saka ya tsanshi a hannu, miƙewa yay ya tare da amsar Jalal har yaje wajan strais ya tsaya yace “koda wasa kada ki sake ambatar sunan Zulfa idan ba haka ba…” cikin tashin hankali tace “kamar kada na sake ambatar sunan Zulfa?idan da wanda yafi da cewa yaji sunanta to bayanka yake bi ai kuma Zulfa ai..”da wata gigitacciyar tsawa ya tari nufashinta “my friend shut up i hate this name na tsanani sunan Zulfa na gaya maki” yana faɗin hakan yay saman bene abinsa yana tafe yana jijjiga bobo,washe gari tun da sassafe ya fice da gidan bayan ya kai mata bobo ka san cewar a wajensa yake ƙwana kai tsaye wajan Mama yaje ya nufa yace mata yana son yazo takwashe kayan Zulfa daga gidan,zaro idanu tayi domin bata tsammaci abinda zai faɗa kenan ba, murmushi tayi tace “kamarya ya kenan kb? shuru yay mata sabida bai san abinda zaice mata ba,gyara zama yay yace “hankali na yana tashi idan naga kayanta kullum gani nake kamar zata dawo”tsaki Lamir yay yace “munafiki dai sam baiji daɗin halinsa ba wlh” kwaɓe fuska Jamal tayi tace “ayya bro Lmr babu ƙyau fa”wata harara ya watsa mata yace “kee dalla gafara kema ai munafukar ce sai kace ubanki hala kema yakai jininki an tsaface”Jamal bata ƙara cewa komai ba taja bakinta tayi shuru, “kai Allah ya rabamu da halin gado kai dai Lmr babu inda ka bar kakanka wlh wannan la’antaccen halin ba’a nono na ka tsotsa ba,Kabeeru ina son Jamal ta maye gurbin ƴar uwarta Zulfa ko babu komai Jalal zai tashi hannun ƙanwar Mahaifiyarsa,jinjina kai Alhaji kb yay yana mai danne zafi da raɗaɗin daya keji akan ambatan sunan Zulfa da suke”amma Mama how can that happen?tayaya zan zauna da Jamal bayan ban saki yayarta ba? numfashi ta sauke tace “yanzu waya san inda Zulfa take Kabeeru?baka da tabbacin tana raye dan haka idan ka amince a gobe sai a ɗaura auren ta koma mazaunin yayarta ita ta buƙaci hakan da kanta” miƙewa yay tsaye yace ” shikenan na amince”yana faɗin hakan ya fice daga gidan,a hanya ya biya inda ake samun masu aiki mata yay dace da samun wata matashiyar budurwa,bayan yay parking ya fito baba Habu yace “mai gida wannan abar fa?”zaro manyan idanunta karime tayi tace “wace abar?”washe baki yay shima sai da gatsonsa ya bai yana yace “ke mana wlh ko alahira aka bawa mutum ke yasan bai aika abin arziƙi ba wai ina ruwan duba”haɗe rai tayi tace “wallahi nasan na fika ƙyau jini baki haƙora a waje duk gansa kuka”Alhaji kb danne dryarsa yay yana sauran maganar su,baba Habu ne ya ɗauki goro ya cilla a baki yace “wallahi wannan bakin da kisa ɗaya zan kasheki, Allah sarki innata tasha tsotso ina ruwan Kabilu😂, ganin basu da alamar gamawa yasa Alhaji kb yay shigewarsa cikin gidan.
tofa kamar yadda Mama ta faɗa haka washe gari aka ɗaura auren Alhaji kb da Jamal akan sadaki duba hamsin sosai Lamir yay baƙin cikin faruwar hakan dole yay shuru domin anfi ƙarfin musamman da baba Kamis yay magana yayan Mama kenan.
haka shekaru suka dinga zuwa suna shuɗewa tamkar yadda a kullum nake rubuta page ɗin labari ina tafiya wani page ɗin yanzu muna da kimanin shekaru biyar kenan Jalal ya zama ɗan shekara biyar kyakkyawan yaro fari tas kamar ɗan larabawa ga shegen surutu da wasan tsiya,amma masha Allah aƙwai ilimi musamman na addini baya wasa hakan tasa Alhaji kb yake alfahari dashi,a wannan lokacin Mameey ta haifi yara maza guda uku a lokaci daya ƴan uku kenan Imran,Irfan,Aryan inda Jalal ya basu tazarar Shekara uku kenan a wannan lokacin suna da sheka bibbiyu su kuma, Jamal kuma tana ɗauke da ƙaramar babynta mace mai suna Nihila sosai Jalal yay murna da samun babyn kullum idan ya dawo daga makaranta haka zaita ɗaukanta yana mata wasa,yanzo ma yana zaune yace “Mumy Nihila muna kama ko?” dry tai masa sabida baya gajiya da surutu wani chocolate ta ɗauka tace “maza kaiwa su Aryan”amsa yay da sauri cikin nutsuwa ya nufi part din6 Mameey ganin babu kowa yasa ya shige bedroom ɗin arba yay da wata roba tamkar zuma ce a ciki yana zuwa ya buɗe ya shaye tasss, ganin kusan awa guda bobo bai dawo ba yasa Mummy (Jamal)zuwa part ɗin Mameey a zaune ta samu Mameey ita dasu Irfan suna ganin Mummy suka tashi da gudu suka nufi wajan “eyee ƴan samari an girma ina yayanku? tun ɗazo ya shigo nan babu labarinsa?”Mameey ce ta miƙe tace “nikam ina part ɗin Abbou Jalal su Aryan kuma Yanzu aka kawosu daga school kafin Mummy tai magana Imran yazo da sauri wajan Mummy yace “Mummy ayaa can”ya faɗa yana nuna mata bedroom ɗin Mameey da(7⁸) sauri suka ƙarasa wajansa wata kara6 Mummy tayi sabida ganin Jalal ƙwance a ƙasan carpet kumfa na fita a bakinsa…