UNCLE NE CHAPTER 2 BY NIMCYLUV

 UNCLE NE CHAPTER 2 BY NIMCYLUV


cikin tashin hankali Mummy ta ƙarasa inda yake ƙwancen tare da saurin saka hannu ta jawoshi zuwa jikinta, jijjigashi ta fara yi tare da kiran sunansa “Jalal Jalal” shuru babu magana kuka ta fara sabida daman raguwar zuciya gareta da sauri Mameey ta amshi Nihila a hannunta ita kuma Mummy ta ɗauki Jalal tayi waje dashi da gudu tana kiran sunansa da ƙarfin gaske,tana fara taga strais ɗin benen Alhaji kb na shigowa ganin hannunta ɗauke da bobo ya sashi sauri sakin jakar dake

hannunsa hannu yasa ya amshi Jalal dake hannun Mummy ya ƙarasa dashi wajan duguwar sofa cikin wani irin yanayi yace “mene yasha”?kafin Mummy tayi magana Mameey tace “a ɗaki na aka samesa a ƙwance yaje kaiwa su Irfan chocolate kuma tym ɗin bana part ɗinka ina gyarawa” cikin damuwa ya miƙe tsaye ya nufi part ɗinsa frist acid box ɗinsa ya ɗauka cikin sauri ya fara bin cikar abinda ya sanya shi wannan duguwar sumar da kuma kumfar dake fita a  bakinsa,wajan 30minutes ya ɗauka yana dubawa gaba ɗaya ya haɗa gumi sai zufa yake zubarwa, numfashi ya sauke tare da kai dubansa ga Nihila dake kuka hannun Mameey cikin kulawa yace “kina jinta dai ko?mene yasa baki son bata abincinta ne”cikin son danne kukan da take tace “bana da ƙwanciyar hankali Abbou Jalal kalli bobo a ƙwance ban san ra sashi”jinjina kai yay dan shima ba ƙaramin tashin hankali ya shiga ba musamman daya fahimci abinda Jalal ya sha,kallonsu yay 1 by 1 kafin ta kalli ƴan uku da suka rungome juna suna kuka musamman Aryan domin yafi shaƙuwa da Jalal “wane ya ajjiye maganin feeling a cikinku?” da mamaki suke kallonsa kafin su haɗa baki wajan faɗin “maganin feeling kuma?” da sauri Mameey tace “ayya wallahi na ajjiye saman dressing mirrow i almost forged”girgiza kai kawai yay kafin yace “kin san illarsa ga yara wanda basu da sinadarin sha’awa bare maganin yay aiki a jikinsu,kin san halin da yake sanya su Salmerh innalillahi”kukan Mummy ne ƙaro kafin tace “yanzu wanne hali yake ciki?”goge zufar dake zobu masa yay kafin yace “yana halin Neurological disoders” shuru sukai gaba ɗaya kafin Mummy tace “me kenan?” hannu yasa ya ɗauki Jalal yace “Wasu lokatan Maganin Yakan Tursasa Kwakwalwa take bada Umarni wa Gangar jiki Barkatai sbd aikinta zai karu fiye da yadda takeyi sbd Sinadarin Adrenaline dayake a cikin maganin, haka zaisa shi yaron da bashida feeling sai maganin yanemi ya taba kwakwalwarsa saiyake kamar ana sashi yayi abu, kansa zaiyi masifar ciwo sbd babu Sassan da maganin zaiyi aiki a jikinsa  direct kwakwalwa zai tafi”zubewa tayi wajan tare da faɗin “na shiga uku Ni Jamal wannan wanne irin abune meke shirin faruwa da Jalal ne?hakan na nufin zai dinga abu kamar mara hankali ne ko kuma me ya ilahi wacce irin lukutar masifa ce wannan yaro ƙarami ya fara samun matsala da brain ɗinsa to inaga ya girma basu san abinda hakan zai dinga jawowa ba,basu san mene zai dinga aikatawa ba”da sauri ta miƙe tafi bayan Abbou Jalal tana zuwa ta samesa yana yana ɗaurawa bobo drip a hannu bayan yay masa injection,zuciyarta ce ta buga da ƙarfi sabida gaban Jalal da taga ya tattare waje guda ga fatar wajan ta ya mutse tamkar ba’ai masa kaciya ba,cikin sauri ta ƙara inda yake ƙwancen takai hannunta zuwa saman mararta sa saurin saki tayi tare da fasa ƙara sabida ba tayi tunanin abin har yaje ga haka ba,da sauri Abbou ya jawota jikinsa ya fara rarrashinta cikin sigar lallashi yace “mutum baya tara sani ga Allah Jamal, ƙaddara kutse ta kewa rayuwar ɗan adam ba tare daya shirya amsar ta ba,kamar yadda bamu san yaje ya ɗauki wannan maganin ya sha ba,haka bamu san sanda ƙaddarar zata rabu daga jikin bobo ba,nasan cewa jiya ta huce yau tazo kuma muna jiran ganin gobe to itama ƙaddarar da aƙwai lokacinta,ki ɗauki matsayin wata jarrabawa daga rabbil arshir azeem komai zai zama dai in sha Allah”wasu hawayenne suka ƙara fitowa daga cikin idanunta cikin tausayin halin da Jalal ke ciki ta kalli Abbou tace “amma kalli yadda gabansa ya…” sauri ɗaura labɓansa yay saman nata tare da rungome ta sosai a jikinsa sabida yasan halinta yanzu zata iya birkice masa bayanta ya bubbuga yace “na gani basai kin faɗa ba kiyi masa addu’a kawai”kaita ɗaga masa tace “in sha Allah”sumbatar lips ɗin nata yay yace “that why i always love you babyna” tun ɗazo take tsaye ba tare da tace komai ba sai yanzu da taga zasu tafi wani abun tayi saurin bubbuga ƙofar gaba ɗaya suka juyo suna kallanta idanunta fal hawaye tace “wallahi bada wasa na ajjiye wannan maganin ba,kamar yadda bazan so rayuwarsu Aryan ta lalace ba haka bazan so rayuwar Jalal ta gurɓata ba,domin wata rana shine Garkuwa yarana shine zai zame masu gata dan Allah kada ku zargeni akan wannan abin yadda ban taɓa cutar da Zulfa haka bazan taɓa cutar da jinin ta ba”ambaton sunan Zulfa da tayi yasa Abbou saurin dafe kansa da yaji yana sara masa lokaci guda yaji duniyar na juya masa,ga wata guguwar tsanar Zulfa data ƙara bunƙasa a zuciyarsa,cikin sauri ya shige bathroom ya sakarwa kansa shower gaba ɗaya jikinsa rawa yake idanunsa sun sauya kala a hankali kuma bathroom ɗin ya fara juya masa kafin daga bisani yaji wata iriyar murya kamar ta mage tana faɗin.

“dole ka manta da Zulfa kamar yadda ta gudu ta barka duk da irin soyayyar da kake mata yeeeeeehuuuuuu ka manta da Zulfa a rayuwarka ka manta da ita shine ƙwanciyar hankalinka idan ba haka ba sannu zamu fara….”bai bari an ƙarasa maganar ya fasa ƙara wacce ta karaɗe cikin amma ga mamakinsa shi kaɗai yaji ƙarar domin ko su Mameey dake bedroom ɗinsa basu jita ba, cikin ficewar hayyaci ya tari ruwa a wajan sink ya watsa saman fuskarsa cikin zafin rai da ƙunar zuciya ya buga kansa da bangon bathroom kafin ya samu damar faɗin “na sani daman nasan gujeni kikai kamar yadda ban san waye ni haka kema na manta dake a cikin rayuwata na tsaneki Zulfa na tsaneki” ya ƙare maganar cikin kuka mai tsuma zuciya tamkar ba namiji ba,haka suka ƙare hunin ranar babu farin ciki Jalal shima haka ya huni da wani a zabbban ciwon kai har firgita yake sai dai Abbou ya ƙara ɗaura masa drip da allurar bacci ko abinci ƙin ci yay,haka ƴan uku banda kuka da kiran sunan ahyyyaaa wai yaya babu abinda suke da kƴar sukai rungome juna sukai bacci, Abbou kam bacci gagarar idanunsa yay zuciyarsa fal tausayin bobo saboda shika ɗai yasan matsalar data samu Jalal yaƙi gayawa Mummy ne sabida bai son ta tashi hankalinta,haka shima Jalal har abada bazai taɓa gaya masa wannan tashin hankalin ba,washe gari da safe bobo ya farka jiki da sauƙi cikin nutsuwarsa ya fara tafiya part ɗin Mameey yana zuwa ya nufi bathroom room ɗin kayan cikinsa ya cire tas tare da ƙarewa surar jikinsa kallo, Mameey da gama shirinta kenan zata kaisu makaranta sabida Abbou tun safe ya tafi office hatta huce bathroom ɗin ta sai kuma ta dawo da baya sabida wani nishi da gurnani da taji yana fitowa daga cikin bathroom ɗin a tsorace ta fara buga ƙofar amma sam taƙi buɗewa cikin haka taji wani wani sexcly sound ya fito daga bathroom ɗin ƙara ƙasa kunnu tayi taji an ƙara faɗin “ahhhyashhhh”

Zaro idanu waje tayi cike da mamaki da sauri ta miƙe tsaye tare da zuge wata ƙaramar ƙofa dake jikin door ɗin bathroom ɗin,a hankali ta leƙa a tsaye ta hangesa yana kallon mirrow ba tare da tasan abinda yake ba kasan cewar ya bata baya,cikin ƙwanciyar hankali tace “Jalal..”dadaran idanunsa ya ɗaga wanda sukai jaa sosai ya zubawa mirrow’n idanu, ta mirrow’n kuma yake hangen ƴar Kofar da Mameey ke leƙensa lumshe idanunsa yay tare da sakin murmushi har saida beauty points ɗinsa suka loma,ba tare kuma da yace komai ya ƙarasa wajan ƙofar ya murza key ya fito,ajjiyar zuciya tayi tace “kaban tsoro bobo what did you do inside the bathroom? girgiza kai yyi yana nufar parlour yace “babu fa”  itama ba tace komai ba tabi bayansa har zuwa parlour’n, gaba ɗaya  su Imran suka tawo wajansa da gudu suka rungomesa “ayyya bafiiii ciwooo ko” cewar Irfan, ɗan waro idanu bobo yay tare da shafa kan Irfan yace “shirme kawai naji sauƙi fa”kallon Aryan yyi daya kafesa da idanu yace “ohh hello darling”ya faɗa ya tafa hannunsa kwaɓe fuska Aryan yyi kafin shima ya shige jikin yayan nasa suka haɗe su huɗu waje gudu abin sha’awa “ohhyaa guys Les go” Mameey ta faɗi hakan tana yin gaba, binta sukai a baya ya zamana Jalal shine na ƙarshe yana tafe kamar baya son tafiya hannunsa dafe da mararsa sai lumshe idanu yake,kai tsaye makaranta ta kaisu kafin ta dawo zuwa gida.
da yamma misalin ƙarfe biyar Jalal ya fito compund cikin shigarsa ta farar jallabiya kansa ya sha gyaran da Mummy tayi masa, direct wajan baba Habu ya zauna yana mai sauraran wani news da akeyi a gidan redio a nan yaji mai labaran yana faɗin “hukumar gwamnatin ibadan tana neman yara masu kimanin shekaru biyar zuwa goma domin ɗaukan su zuwa karatu a ƙasar Paris as valunteer,haka kuma duk yaron daya fito da 1st class hukumar zata ɗauke sa ta bashi aikinyi wanda yaga dama” haka yaci gaba da jin labarin a kuma lokacin ya haddace email ɗin da suka bada domin kowa ya tura baya nan sa, baba Habu ne yyi saurin faɗin “wa yaga al’ƙawarin ƴan nepa…, atoo kuyi komai lokaci ne mudai ana watsa mana ƴar yafin shinkafa zamu kaɗa maku ƙuri’a” kallonsa Jalal yay ba tare da yace komai ba, ƙara gyara zama baba Habu yyi yace “sannu boba kai a rasa sunan da za’a saka maka sai na wannan abin zuƙar,ina ruwan ɗan Maraya aida idanuna biyu aljanun suka ɗauki mamanka da gora zan rakasu,ai kaga tun lokacin basu dawo ba,yoo to nima ɗin ai Sheikh ne a ƙauyan mu  kaji siminin da ake karantawa aljanun  ko NASI KO FATIHA ai saba’in ɗin nan na hadda ce ta”miƙewa Jalal yyi tare da gyara zaman farin glass ɗin idanunsa yace “sittin dai”yana faɗin hakan ya shige cikin gida sabida kiran magrib da akai,babu kowa a main parlour sai Imran yana bacci tashinsa yyi yace “time for paryer” da sauri ya kama hannun bobo suka nufi upstrais part ɗin Abbou suna zuwa yana fitowa daga bathroom al’wala suka ɗaura Jalal kuma ya nufi bedroom ɗin Abbou ya fesa parfume kana ya biyosu a baya,dwonstairs a nan suka samu Aryan da Irfan gaba ɗaya suka nufi masjid ɗin dake wajan gidansu.
gaba ɗaya  a zaune suke saman babban daining table suna dinner “mene? hauka ake da za’a bar bobo karatu har zuwa paris babu inda zashi” Mummy ta faɗa lokacin da take kai glass cup bakinta da niyar shan lemon inibin da tayi masu ɗazo, haɗe rar Jalal yyi tamkar babba kuma tsill ya gagara faɗin ko “A” sai juya strawberry ɗin da aka yanka masa ya kasa cin koda ɗaya ne, Abbou ne ya kalli Mummy yace “idan yaro yazo da abu ba’a gwasalesa da a kudu ne iyaye sunwle suke neman shawara wajan yaransu sabida hakan na ƙara buɗa masu ƙwaƙwalwarsu, Ni anawa ganin abarshi yyi abinda ya keso is better” cikin yanayin damuwa Mummy tace “amma tayaya ne zai iya kula da kansa? kai kanka wani lokacin birkici maka yake,yaya kake ganin ace babu wani family nasa..” ta ƙarasa maganar cikin raunin zuciya,domin har zuciyarta bata son tafiyar,girgiza kai kawai Abbou yyi domin daman yasan za’a sha wahala da Mummy “manyan makarantu irin wannan aƙwai kula,domin abinda za’ai wa mutum acan ko gaban iyaye sai haka, addu’a shine kawai ya dace da Jalal” cewar Mameey,ganin da gaske kuka Mummy kesonyi yasa Jalal miƙe ya ƙarasu inda take zaune, murmushi yyi kafin yace “my ambition is ur ambition too zaki farin ciki wata rana”gaba ɗaya kallonsa sukai domin Jalal idan yay magana saika rantse ɗan shekara Ashirin ne bayan ko 6yrs bai rufe ba,yana faɗin hakan ya shige part ɗin Abbou,abinda masu sani ba Jalal ya daɗe da tura baya nansa ta email ɗin da suka bayar.
washegari da misalin 8 aka kira Abbou tare da tambayarsa shine mahaifin Muhammad Jalal? da “eh” ya amsa masu nan sukace ana nemansa shida Jalal yanzu a gidan Gwamnati, murmushi kawai yyi domin ya tabbatarwa kansa Jalal ne,a gurguje yaje islamiyyarsu Jalal Lokacin yana tsaka da bada hadda ya nemi permission wajan malam,ganin babu wata matsala daman saukarsu saura wata guda yasa yace “suje kawai” a parking spaces na gidansa yay parking anan ya tsaya yace Jalal yaje ya sauya kaya, baba Habu na zaune yaji ana buga get da sauri ya ɗauki gorarsa yace “huuu yau naga tsiya iyayenku su nome sannan kuzo aci daku,atoo ina dalili nima dai naje na ɗauko su Iliya a makarantar su daina cin na mutane..” murmushi Abbou yyi yana jinjina abin dryar getman ɗin a haka Jalal ya fito cikin blue black ɗin jallabiya sosai tayi masa ƙyau sabida farar fatarsa,a duniya yana son jallabiya dan duk rabin kayansa sune.
yana zuwa Abbou ya buɗe masa side ɗin kusansa ya zauna,key yaywa motar ya nufi wajan get da ita,a nan baba Habu yace “Allah ya kiyaye,ahaa yama kiyaye ai domin tasss na tofe wannan motar da siminin sama” gaba ɗaya Abbou da Jalal suka saki murmushi lokaci guda,da haka suka bar gidan,sosai sukai cike-cike na takaddu kuma a nan akace nan da wata guda tafiyar,hakan yaywa Abbou daɗi domin har Jalal yay sauka kafin tafiyar,suna kammalawa suka nufi gidan Mama,a parlour suka sameta tana jin motsi tace “naga shegun ƴan wutan da suka yankemin waya” da sallama Abbou ya shiga ganinsa yasa ta washe baki tare da faɗin “lale lale ashe Kabeeru ne da ango na”direct bobo wajanta ya nufa yana zuwa ya haye cinya yace “grandmother badai masifa ba”baki ta saki tare da tafa hannu tace “yau naga tsiya to ubanka Kabeeru shine mafifaffe”sai kuma ta saki dry tana faɗin “hehehe Allah ya jiƙan Laure badan ta mutu ba,tasha jibga Musamman a ruga” zamewa Jalal yyi daga jikinta ya nufi cikin bedroom yana faɗin “kawai kice kinci zali” sai a lokacin Abbou yace “mun sameki lafiya Mama? ya mutsa fuska tayi tace “kadai sameni lafiya, wancan fitsararran ina yake ta lafiyata…,har yanzu ƙafarce ke damuna da ciwo” cikin damuwa Abbou yace “sai hqr ai Mama,kin san shekaru sun fara jaaa”da sauri ta miƙe tsaye tana faɗin “dama na sani to wallahi nida mutuwa munyi hannu riga,yooo nida nake shirin aure zaka jawa masifa jaa ɗanka kuyi gaba” danne dryar dake cinsa yyi yace “ba haka nake nufi ba,amma kiyi hqr”nan ya shaida mata tafiyar Jalal zuwa ƙasar Paris,dryar tayi tace “wlh yaje na sarara ina dalili baka haifa na wani ya addabeka”kafin Abbou yace wani abu bobo ya fito hannunsa ɗauke da fara roba ya cika dambun nama a ciki,sannan ya ƙulle wani a leda yace mata nasu “darling ne”su Aryan kenan “wlh ubanka ka jawa a sara”ta faɗi hakan tana kuntu wata farar sabuwar Naira biyar ta bashi,wannan ƙa’ida ne saita bashi,a haka Abbou ya fito da dubu biyar ya bata kana sukai mata sallama,suka tafi.
Komai aka sawa rana  yana da lokacinsa,sai dai idan ba’a saka ba,a yau Jalal sukayi saukar Alkur’ani mai girma,tare da hadisai,fiqhu,sira, umdatul ahkam,farin ciki wajan Abbou da Mummy harda Mameey ba’a mgn, haka suka dinga walima da ɗaukan photo da allon Jalal ha Kur’ani,har shedar kammalawa, Jalal yasha babbar riga Tamkar babban mutum,a kuma wannan ranar yini yay da a zababban ciwon kai,ta zarar kwana biyar tsakanin jirginsu Jalal ya shilla zuwa Paris, Mummy kuka hadda majina shima a lokacin ji yyi kamar kar yaje,su Irfan daman ba’a zo dasu airport ɗin ba,sabida kukansu akan idanunsu jirgin ɗaliban ya tashi. _(a gurguje)_
after 24yrs
wata ƴar kyakkyawar budurwace mai kimanin shekaru 16 ta fito daga wani part jikinta sanye da wata lafiyayyiyar abaya wacce kalarta kawai zaka gani ka fahimci tsadarta,domin abaya shigar girma da mutunci ce,wanda ya san asalin abaya bazai tuzarta ta ba,wani babban falt ta nufa a wannan flat ɗin wajan side huɗu ne,side ɗin farko ta fara shiga,tun daga ƙaramin parlour’n tasan yana nan bai fita wajan motsa jiki ba,a hankali ta tura kanta cikin bedroom ba tare da tayi sallama ba, idanunta ta shiga juyawa ganin baya bedroom ɗin,ganin komai tsaf yasa tayi murmushi,daka bayanta taji anyi mata cakul cikin sauri ta zabura ganinsa a bayanta yasa ta turo baki tace “naji tsoro” kai ya ɗauke yace “uhm ko..? mene ya kawoki side ɗina bako sallama da ido kamar na mage”kwaɓe fuska Nihila tayi tace “to ba Abbou yace min na gaya maka can yamma za’a je airport ɗauko bobo ba”zaro idanu yyi yace “what!? bobo zai dawo wow”lumshe idanu Nihila tayi tace “Finally zanga kyakkyawan gidan nan yau,zanga bobo na” drya  Irfan yyi yace “to uwar iya fice kiban waje” a can Paris jirgin daya ɗauko su Jalal babu inda ya tsaya sai wani gari mai suna *_Malta_* a  wani yanki da ake kira da *_birnin nufar_* wani yanki na Yahudawa, idan kaga yadda mutanan suke babu musulunci saika rantse tafiyarsu ɗaya da ƙasar *_Israel_* domin yadda shuban garin yake abu babu tausayi saika ɗauka halinsu ɗaya da *_Ben jamn netanyahr_* wato shugaban ƙasar Israel yaransu na Jewish kusan tafiyarsu ɗaya,basa taɓa yadda da Musulmi bare har suyi tunanin haɗa Aure tsakanin banbancin ƙabilun, ban bancin dake tsakanin Birnin nufar da Israel shine Israel ƙasar larabawa ce domin a nan aka haifi Annabi Isa a Kashi a shirin na Annabawa duk a can aka haife su,amma gaba ɗaya mutanan ƙasar basa da tausayi da imani a ransu,kuma baza su taɓa musulunta sai mai rabo,domin sune suka buƙaci a saukar masu da abincin a sama,kuma akai yadda sukace amma hakan bai saka sun miƙa wuya ba,sam basu yadda da Annabi Muhammad ba,amma abin mamakin yadda suka san Kur’ani ko musulmi sai haka,jew (Bayahude) ɗaya yafi profeser ashirin ilimi, (Jewish) shine sunan yaransu ƴan Israel kenan,to suma ƴan birnin nufar haka suke.
a hankali wata lafiyayyiyar mota ke tafiya zuwa hanyar wani yanki dake birnin nufar, wani kyakkyawan farin matashin saurayi ne a bayan motar,kana ganinsa kasan ilimin addini ya ratsa ƙwaƙwalwarsa,farine tas mai faffaɗan jiki musamman ƙirjinsa,yana da ƙyan suru ga haiba da kwarjini,ga wani kyakkyawan saje da yaywa fuskarsa ƙawanya,pouting red lips ɗinsa yay kana ya gyara zaman dark blue ɗin shaddar dake jikinsa,cikin nutsuwa yake operating system ɗin dake saman cinyarsa yana bin cike akan ƙwayar cutar sicler,wani wawan birki drever’n yyi hakan tasa matashin ware labɓansa cikin Muryar nutsuwa yace “meke nan?” a razane drever’n yace “Dr wata yarinya ta tari gaban motarmu fa” zare glass ɗin fuskar wanda aka kira da sunan Dr yyi,a hankali ya ajjiye system ɗin zuwa gefen sa, bai sun su ɓata lokaci a yau yake son isa ƙasar su,  burinsa ya ƙwana gefen Abbou’nsa,juya blue eyes ball ɗinsa yyi ganin da gske yarinyace gabansu sai ɗaga hannun take sama tana ƙunƙuni,sosai Matashin ya karanci yaran kuraman da take masa a kuma lokacin ya fahimci ita ɗin kurmace, fitowa yayi daga motar ya nufi inda take tsaye ganin ya fito yasa tayi saurin ƙarasawa garesa,jaa baya yayi tare da girgiza mata kansa shi su yake yace ta basu hanya sauri suke,a nan itama su take tace masa “ya taimake ta wasu ne suka biyo ta zasu kasheta” da hannu yay mata nuni da suwaye,ganin yadda jikinta ke rawa ga kuma yadda pech lips ɗin ta ke motsawa gaba ɗaya ya jiƙe  da yawo,hakan yasa bai san lokaci data ƙarasu gabansa ba,zaro idanu yay tare da buɗe baki zai magana yaji ta faɗo jikinsa ta ƙanƙame sa,da sauri   Dr Jalal Kabeer bobo ya runtsa idanunsa sbd wani sarawa da kansa yyi..
Hannu yasa ya dafe gefen kansa dake masa wani a zababban ciwon,kafin ya ware idanunsa ya saukesu aƙan yarinyar data maƙale   jikinsa,gaba ɗaya jikinta rawa yake,domin iya tsorata a tsorace take,banda jijjigashi da dukan ƙirjinsa ba abinda take ware manyan idanunsa yyi sabida wani gantallun kaya daya gani a jikinta kamar ƴar kiristan,wani wani czy jeans ne a jikinta iya karshi quiwa,ga kuma wata ƙaramar riga wacce gaba ɗaya bata huce cinya ba,sai dugun gashinta da aka rinashi zuwa 2colour baƙi da blue,ga  wani farce a  jikin yatsun hannunta,saurin zare jikinsa yyi daga nata yana mai ƙarewa surar jikinta kallo gata kyakkyawa ajin farko,sam ba fara bace amma yadda jikinta ke sharning ga skin ɗinta a mulmule,hawayen dake zuba a fuskar ta ne zai tabbatar maka da kuka take,amma a zahiri ko muryarta bata fita sai ƙunƙuni da take, Jalal take tsaye ya lumshe idanunsa a lokacin ɗaya ya gama ƙare mata kallo,ba tare kuma da yace komai ba ya juya abinsa zuwa wajan mota,side ɗin baya ya zauna tare da ɗaukan system ɗinsa yaci gaba da dannawa ba tare da tunanin wani abunba,drever’nsa ne yaywa motar key sai a lokacin Jalal ya ɗaga firgitattun idanunsa zuwa ga murfin motar daya manta bai rufe ba,yana ƙoƙarin rufewa yaji ta shigo cikin motar sai haki take,can kuma yaji Wata hayaniya na tashi daga cikin wata duguwar hanya,rankwafuwa yyi kusanta yyi saurin rufe motar cikin taƙai tacciyyar maganarsa yace “muje airport” da sauri drever’n yywa motar revers ya juya da baya hakan yyi dai-dai da lokacin da wasu matasa kusan su ashirin suka fito daga hanyar hannayensu ɗauke da makamai kala daban-daban, ajjiyar zuwa ta sauke Jalal kam sai a lokacin ya tabbatar da maganarta da tace kasheta za’ai,kai tsaye airport suka ƙarasa suna zuwa aka fara shirin tashi daman shi ake jira sabida wajan wani babban mutum da yace zashi ya saka masa hannu a jikin wani file,yana zuwa aka amshi system nashi  tare da wayoyinsa aka ajjiye waje guda,can baya aka bashi waje ya zauna,kusan 5minutes ya tuna yarinyar bata cikin jirginsa,da sauri ya miƙe tsaye yywa security cikin jirgin magana “jeka kawomin wata a waje” jinjina kai security yyi babu jimawa suka ƙarasu da ita yace “Dr gata”yana daga kishin giɗan ba tare daya kallesu ba yace “to goyata zan?go with her”jin hakan yasa security rufe vip side ɗin sannan ya bata waje daga cikin jerin kujerun jirgin,a haka aka fara sanarwar kowa ya daura blet babu daɗewa jirgin ya fara shawagi a ƙasa kafin ya lula saman gajimare zuwa ƙasar ibadan.
acan birnin nufar gaba ɗaya tawagar mazan da suka biyo yarinyar suka rufawa motarsu Jalal baya,gudun mota dana mutum ba ɗaya ba bisa dole suka tsaya suna mai takaicin rashin samun ta da ba suyi ba,cikin zafin rai Joshua ya fesar da numfashi yana mai girgiza kansa kamar zai kuka haka yake jin zuciyarsa, cikin yaransu yace “nine ta guda,bayan kowa yasan cewa dole ne namiji ya kusanci mace kafin aurensu,domin tabbatar da guzarinta,mene yasa ni taƙi amincewa dani bayan tun tana ƙarama nake kwadayinta,ohhh wow ta girma shine zata gujeni idan har Papa shine kakanta to tabbas zata dawo garin nan,zan nuna mata kalar nawa rashin imani muje zuwa”Joshua ya ƙare maganar yana gyara zaman gudun fanten dake jikinsa,gaba ɗaya jikinsa zanene ga wasu manyan layo,John  dake kusa da Joshua yace “tayaya zaka dawo da ita?bayan baka san inda za taje ba,kuma kasan cewa Papa bazai taba cutar da jikanyarsa ba”a fusace Joshua ya kalli John yace “nasan baka manta uwa SUNDU ba,ita kaɗai ta isa ta dawo min da ita zuwa birnin nufar,kuma ina mai tabbatar maka nama fasa aurenta amma tabbas zan mallaketa matsayin…”kafin ya ƙarasa maganar yaji anyi saurin rufe masa baki cikin jarumta ya hankaɗe hannun John yace “kai bama ita ba,har wanda ya ɗauketa taja masa masifa daga ko yaushe zai fara ganin kalolin bala’in da zan sanya shi”yana faɗin hakan ya juya ya nufi cikin birnin nufar,kai tsaye wajan Papa su kaje nan suka tarar ya shiga cikin gidan domin ganin abinda yake faruwa.
“Papa kayimin rai ka dawomin da yarona,na maka al’ƙawarin zan bashi Joshua matsayin mata (kusan hausar marasa yare,namiji a bashi sunan mace,mace a bata sunan namiji) ƙahon dake kansa ya gyara zamansa tare dayin wani numfashi yace ‘uhmmm..,kai da yaronka bakwai jin mgn,kuna haramta abinda yake al’adarmu,dan haka kiyi kuka da kanki” yana faɗin hakan yyi saurin juyawa zuwa gefen sa sbd kukan da yaji yana tashi,wata ashar ya ƙunduma tare da faɗin “baza ko daina fitomin da wannan abar ma,wlh duk sanda na ƙara arba da ita saina kasheta”ya faɗi hakan yana ficewa waje,da sauri Katarina tayi wajan da Zulfa ke  zaune ta ƙanƙame wani teddy sai kuka take,sanin duk abinda da zatai mata ba zata motsa ba,yasa ta kira Jabir a waya ta shaida masa abinda ke faruwa,yana cikin neman yarin data gudu yyi saurin dawowa cikin babban gidan kai tsaye sashin Katarina ya huce yana zuwa Zulfa ta miƙe da gudu ta faɗa jikinsa dana faɗin “ya rahamanu” duk iya shekarun da tayi babu abinda take faɗe sai haka,haka kuma bata yadda da kowa tun sanda aka kulleta a ɗakin duhu a ranar da Jabir ya kawota birnin,sosai shekarunta suka jaa domin taje wajan shekara 45,amma tana nan lafiyarta lou sai rashin hankalin da take fama dashi,domin idan abun ya tashi haka zatai ta kukan kuraye gaba ɗaya a sauya mata kamani,haka Jabir zatai mata addu’a sabida yanzu ya iya karatu sosai duk da shima shekarunsa sunja,kuma har yanzu bai taɓa aure ba,domin an riga da an cire masa sha’awar mace,koda yace zai auri Zulfa Papa cewa yyi sam bai yarda ba,idan kuma yyi to dashi da Zulfan duk saiya haɗa su da uwa SUNDU, rungome ta yyi tare da faɗin “sorry na barki ko?” Ita dai bata kulasa ba sai ajjiyar zuciya take saki,a haka ya ta zuwa inda take ƙwana ya bata abinci taji sannan ya lallaɓata tai bacci rungome da teddy.
misalin biyar na yamma jirgin ya sauka a filin tashi da saukar jirage dake garin ibadan,a hankali ɗaliban suka fara sakkowa domin sosai suke farin cikin dawowa cikin ahalinsu,kowa yana kewar gida da kuma dangi,sai da kowa ya fita ya barsa zaune saman sofa ya lumshe idanunsa,a wannan lokacin idan ka kallesa saika rantse bacci yake,amma a zahiri tunanin yadda zai da ciwon da yake damunsa yake,wani lokacin har kunyar kansa yake, musamman idan tunaninsa ya juye haka zaita abu ba tare da sanin abinda yake bai dace ba,yana abu irin na wanda hankalinsu da tunaninsu yabar ƙwaƙwalwarsa,babban tashin hankalinsa bai huce yadda mazantakarsa take yawan sauya ba,wani lokacin da zama ƙarama,wani lokacin yyi mmkin girmanta, ajjiyar zuciya ya sauke tare da ware gajiyayyun idanunsa wanda ya kejin sunyi masa nauyin gaske sabida ciwon kan dake fama dashi,ganin Jafar tsaye a kansa ya sashi saurin haɗe rai tare da miƙewa tsaye,ya fara shirin fita,dry Jafar yyi yace “look at ur face my frnd,gaba ɗaya kowa ya sauka sai kai ɗaya,har na fita Abbou yace kana ina,sai a lokacin na fahimci baka fito ba,kai kowa na murnar ganin ƴan uwa kai kana zauna kana banzan tunaninka wanda baya ƙarewa”tunda ya fara magana idon Jalal yake a rufe harya kammala,ware idanun yyi tare da faɗi “uhm” kai tsaye waje ya nufa yana ƙoƙarin ficewa daga jirgi yaji tayi saurin kama hannunsa sai rarraba idanu take, ware idanu yyi tare faɗin “tab” domin gaba ɗaya ya manta da ita,wata sabuwa kenan,zare hannunsa yyi kafin ya ƙara haɗe rai yaci gaba da tafiya tana biye dashi a baya,cikin murna Aryan ya tafi da sauri yana zuwa yyi hugging ɗinsa tare da faɗin “oyoyo brother ur wlcm” murmushin gefen baki Jalal yyi wanda ya ƙara fito da zallar kyansa cikin ƙasa da murya yace “missed u too darling”a tare suka jera zuwa wajan su Abbou tun daga nesa yake ƙarewa Nihila kallo harya ƙarasu inda suke tsaye,yana zuwa Irfan da Imran suka rungome sa suna faɗin “we are happy to see u yaya” kan kowa ya shafa kamar yadda yake masu suna yara cikin mgnarsa wacce babu hausa sosai yace “i’m also so happy to see u darling” dry sukai gaba ɗaya,a hankali ya ƙarasu wajan Abbou yana zuwa ya zame hular kansa tare shigewa jikin Abbou yana sauke wata sabuwar ajjiyar zuciya, rungomesa Abbou yyi tare da shafa kansa yace “Barka da dawowa farin cikina”ƙara shigewa jikin Abbou yyi kafin ya ƙara sauke wata sabuwar ajjiyar zuciya,cikin sanyin murya yace “nai kewarka jigona nayi kewar jikinka”shafa kansa Abbou yyi yace “nima haka yarona ga Mummy can da Mameey da kuma grandmother” lumshe ido Jalal yyi kafin ya sauke kallonsa akan Mummy wacce ta kafesa da ido tana mamakin kyansa tamkar Balarabe,musamman kyakkyawar sumar kansa wacce take ƙwance sai sheƙi take,ganin yana kallonta ta sauke nata idanun tare da ware hannayenta,da sassarfa ya ƙarasa gareta yace “Mummyna”dry tayi tace “eyee bobo ya isa aure masha Allah”kwaɓe fuska yyi yace “i’m still young” haka ya ƙarasa wajan Mameey itama ya rungometa sosai taji daɗin ganinsa,salati yaji an rafka a bayansa tare da faɗin “huuu yau naga taƙadirin  yaro nika tsana kakewa baƙin cikin ganinka”gira ya ɗaga mata tare da faɗin “ashe kina raye”cikin kumfar baki tace “ubanka Kabeeru da Uwarka Jamal su kakewa fatan mutuwa bani ba,yooo ina dalili duniyar nan mai daɗi ka jazamin masifa ina zaune” dry kawai yyi ya rungometa yace “sorry amaryata ykk” dungure kansa tayi tace “ɗan nema kenan ka zama jibgege abinka sai aure”shuru yyi mata,idanun sane ya faɗa kan Nihila wacce ta tsora masa idanu ko kiftawa  ba tayi,juya idanunsa yyi a hankali kuma ya ƙarasa inda take,yana mai ƙare mata kallo,cikin ƙasa da murya yace “don’t tell me Nihila ce wannan wow!!” Aryan yace “gata fa ta zama budurwa” ciki wata murya yace dama za’a bani auranta a firgice Mummy ta ɗago kanta murmushi yyi yace..
Eh Jafar nake son bawa” wata ɓoyayyiyar ajjiyar zuciya Mummy ta sauke,kafin tayi murmushi tace “ai Auta ta kana da iko da ita dan haka na amince”jinjina kai yyi alamar yadda, Mummy na ƙoƙarin faɗin wani abu Mama tayi caraf tace “yau naga sallama,wlh wata biyu na baki kiyi ciki ki haihu,yoo ina dalili haihuwa ɗaya ace wai Auta”Mummy da Mameey sunkuyar da kai sukai sabida wata kunya data kamasu,sam Mama bata iya bakinta ba,musamman yanzu da tsofa ya fara cinta “wai wace wannan take ɓoyewa bayanka ne?”Abbou ya tambaya yana ƙara kallon yarinyar sabida kayan daya gani a jikinta,sosa kai yyi yace “muje gida tukun” kansa ya ɗauke waje guda yace “baby baki missed brother naki ba?”turo baki tayi tace “naga baka kulani ba ai” hannunta ya kama tare da faɗin “uhm” Abbou ya ɗauki Mameey a gaba,sai kuma Mummy da Mama a baya,motar Aryan kuma yarinyar aka saka a gaba sai Jalal da Irfan da Imran sai kuma Nihila a cinyar Jalal tana jaa masa sajensa shi kuma yana danna wayarsa mai ƙirar iphone 12 max pro a haka suka isa gida.
A parking space sukai parking motocin nasu,cikin nutsuwa kowa yake fitowa daga cikin motar,sosai Jalal yyi mmkin gidan sabida gaba ɗaya an sauya masa fasali tamkar a Turai daga nan ya tabbar arziƙin Abbou yafi ƙarfin nada,jin an taɓasa yasa ya juya domin ganin wanene, murmushi yyi ya shafa kan Nihila yace “baby” shagwaɓe fuska tayi tace “bobo ina ka samu wannan age mate ɗin tawa”lumshe idanu yayi tare da jan ma dai-dai cin gemunsa yace “barni da tambaya” yana faɗin haka yyi gaba abinsa zuwa cikin gida daman shine ya rage duk sun shiga,yana tafe tana binsa a baya,jin tafiya a bayansa ya sashi tsayawa cikin haɗe rai yace “ke zo nan”shuru tayi masa ba tare data tan kasa ba,a zafafe ya juya abin mamaki kanta a ƙasa tana kallon fararen ƙafafunsa, hannayensa ya ɗura a waist ɗin sa kamar mace yace “shifa kurma matsala ne dashi”wajanta ya ƙarasu yana zuwa ya sunkuya wajan fuskarta da sauri ya janye jikinsa tare daya mutsa fuska yace “kai rashin addini bai ba,ji yadda kike wari”still bata kallesa ba,ƙafa yasa ya murje ta ta  ƙafar  da sauri ta matsa tana yarfe ƙafarta sabida zafin da taji,a hankali kuma hawaye ya fara zuba daga cikin idanunta,sai a lokacin yasan bai ƙyauta ba domin babu ƙyau ƙyamarsu,ko nuna masu banbanci,a sanyaye yasa lallausan hannunsa ya tallafo haɓarta cikin ƙasa da murya dai-dai kunnanta yace “what is ur name”yyi hakanne domin babu garin da ba’a jin English, ɗago jiƙaƙƙun idanunta tayi kafin ta ɗaga hannunta tare da ware yatsun hanunta ta fara yi masa spelling na sunan da yaran kurmanci,zaro idanu waje yyi da mamakin sunan data faɗa masa yace “what!? Jalilerh fa”shuru tayi tana kallonsa yyinda shima kallon nata yake,ba tare da yace komai ba ya juya ya nufi cikin gidan gaba ɗaya a main parlour ya gansu zaune suna Shira wacce kusan rabinta Mama ce ke zuba abinta,ba tare daya tsaya ba yace “where is my side?”Aryan ne ya miƙe yace “muje na rakaka baƙonmu,ganin hakan yasa Jalilerh saurin ƙarasawa inda yake tsaki yaja kaɗan yace “Mummy a bata ruwa tai wanka ta sauya wannan sheɗanun kayan,sannan taci abincin am coming” Mameey tace “bobo abinci fa? duk sbd kai akayi fa”cije lips ɗinsa yyi yace “zan watsa ruwa”yana faɗin yyi gaba bai tsaya ko ina ba sai babban wani sashe inda yake da side 4 da alama shine na samarin gidan,yana biye da Aryan har side ɗin ƙarshe,key yasa ya buɗe lumshe ido yyi sbd ƙamshin ɗakin,komai sabo fil ga sabbin sofa ga t.v ga fregd,ciki ya shige inda bedroom yake a nan yaga tafkeken royal bed,ga dressing mirrow da kayan shafa kala-kala kuma komai irin wanda ake amfani ne,wajan wardrope ya nufa ware ido yyi sabida sabbin suttura daya gani sama da hamsin,banda jallabiya kusan ashirin a haka wasu na wajan ɗiki,ashe dan  haka suke ta tambayarsa abinda yafi so,zare kayan jikinsa yyi ya rage daga shi sai singlet da boxer,wani side a wajan wardrope ɗin ya saka kayan,kana ya nufi bathroom  shima komai tass yake abin sha’awa sauran kayan ya cire,tare da tsayawa gaban mirrow’n dake bathroom ɗin yana mai ƙara kallon mararsa wacce taya mushe tare da tattarewa waje guda,idanun sane ya kaɗa yyi jaaa sosai, yana mai jin baƙin ciki da kuma takaici hallitar tashi,mekanan? duk wani binkice daya dace yywa kansa a matsayinsa na babban likita yyi amma baya nuna matsalar komai,wazai faɗawa damuwarsa?wazai fahimce sa har yyi sharing damuwarsa dashi, ajjiyar zuciya ya sauke tare sauke hannunsa daga kan mararsa,cikin nutsuwa ya sakarwa kansa shower ruwa ya fara sauka a fresh skin ɗinsa,nauyayyiyar ajjiyar zuciya ya sauke yana jin zuciyarsa babu daɗi kawai daurawa yake,a haka ya ƙarasa wankan,ya fito yana tsane jikinsa,wajan dressing mirrow ya nufa,cikin nutsuwa ya fara shafawa lafiyayyiyar fatarsa wacce tasha hutu lotion,yana gamawa ya juna handrayer ya gyara kansa wanda sumar ta sauka har wuyansa,sai sheƙi take,sassanyan parfume mai sanya nutsuwa ya ɗauka ya fesama jikinsa, pouting lips ɗinsa yyi,tare dasa hannu ya dafe kansa,a hankali ya miƙe ya nufi wajan wardrope wando three gauter ya sanya ba tare daya saka wasu kayan ba,ya koma parlonsa,gudun a.c ya ƙaro kana ya ɗauki remote ya kunna b.b.c news yana nan zaune har aka kira magrib, miƙewa yyi ya ɗaura al’wala tare da zura wata lafiyayyiyar jallabiya maroon wacce ta fito da zallar ƙyansa,farin glass ɗinsa ya ɗauka ya saka kana ya fesa turare waje yyi ya rufe ɗakin,yana fita yaga su Irfan a tsaye da alama jiransa suke, murmushi yyi masu,kana yyi gaba suka bishi a baya suna surutu shi dai shuru kawai yyi yana jinsu,a main parlour suka samu Abbou yana jiransu,gaba ɗaya suka nufi masallaci,haka Nihila tabi Mameey part ɗin ta a can tayi salla,Jalilerh na zaune sai raba idanu take,sanye take cikin riga da wando na fakistan wanda suka amshi jikinta kasan cewar tana da hips da kuma booms,sai a lokacin nake ƙara ganin ƙyanta kyakkyawace ajin farko,tana zaune kan sofa tana kallon Mummy take sallah mamakin fal zuciyata domin bata taɓa ganin irin wannan abun ba,a haka har Mummy ta idar ta fara azkar,duk akan idon Jalilerh “my dear aje ai sallah” shuru tayi mata ba tare data miƙe ba,hannunta Mummy ta kama suka nufi wajan danning area a nan ta samu kowa yazo daman ita ake kira,kujerar kusa da Abbou wacce take hannun damanta ta zauna,sannan ta nuna Jalilerh wata kujera wacce take farcing Jalal.
shuru wajan ya ɗauka kowa yana cin abincin dake gabansa,banda Jalal da yyi shuru tare da sunkuyar da kansa zuwa ƙasa,ganin baicin abincin yasa Abbou faɗin “bobona” a hankali ya ɗago lumshasshun idanunsa ya saukesu a fuskar Abbou ba tare daya amsa kiran sunan nasa da yyi ba “kowa nacin abincin babu kai why?” taune leɓe yyi tare da harɗe hannayensa a ƙirjinsa yana mai kallon Jalilerh,zama Abbou ya gyara yace “who is she?”sai lokacin ya fahimci kallonta yake cikin hikimi yyiwa Abbou bayanin komai har sanda sukabar airport ɗin da ita,gaba ɗaya suka ajjiye bar cin abincin suna kallon Jalilerh kowa mamakin kisan da akace za’ai mata yake “to mene mafita?” cewar Imran lumshe ido yyi tare da fesar da numfashi yace “may be she stay with us” babu wani zaɓi daya huce hakan dole suka amince da abinda Jalal yace,dan idanma sunce a’a ita kanta bata san inda zata zauna ba ajjiye spoon Mummy tayi tace “sam taƙi tayi salla fa” ware manyan idanunsa yyi wanda suke cike da bacci cikin kasalalliyar murya yace “kee tashi kije kiyi” sai lokacin ta kallesa cikin Sa’a suka haɗa ido da sauri ta sauke nata ganin, bakinta ta shiga mutsawa tare da wasa da yatsun hannunta cikin wata ƙaramar murya tace “ban iya ba ai” cikin tashin hankali kowa yake kallonta ko wannansu zuciyarsa cike da mamakin abinda tace, ɓangaren Jalal kuma banyi mamakin hakan ba domin ya gama fahimta wacece itan,babban mamakinsa yadda yaji muryarta ta fita daman tana magana ta nuna masa ita kurmace,tab ɗin lalle ba tasan wanene Jalal ba, miƙewa  yyi bayan yasha coffee wajan Abbou yaje yyi hugging nasa yace “goodnight Abbou” shafa kansa yyi yace “asuba ta gari bobo”hakama yaje wajan Mummy kana wajan Mameey haka wajan Mama “ohh wannan dudane dudanen na baki na mene? wani sabon fitsarar ce?” murmushi yyi yace “wannan matar me take nufi da zamanta a nanne?” “hehehe au ashe ban faɗa maka ba, ɗan baƙin ciki dai ya mutu na dawo nan da zama” shi dai bai kulata ba yyi shigewarsa side ɗinsa domin wani wahalallan bacci ya keji.
kasan cewar gidan kowa da wuri yake bacci haka suka dinga sallama, kowa ya nufi part ɗinsa, Jalilerh kuma Mummy ta jata zuwa ɗakin Nihila,bayan ta bata kayan bacci tare da fesa mata turare tayi masu addu’a tare da kashe masu hasken ɗakin,kai tsaye nata part ɗin ta nufa tayi wanka ta shirya cikin kayan bacci ta nufi sashin mijinta,a ƙwance ta samesa yana tunani tana zuwa ta shige jikinsa tace “me mijina yake tunani ne” kanta ya sumbata yace “the gril” da mamaki tace “which gril are you talking about?” zama yyi kafin ya kalleta yace “takwara bobo i mean Jalilerh,kin fahimci ba musulma bace? nidai bana jin daɗin ganinta hakan ina mata sha’awar musulunci,tana da ƙyau sosai kuma bata da hayaniya komai nata a nutse kamar ba ƙabila ba”jinji kai Mummy tayi alamar gamsuwa kafin tace “ƙilan rabon musulunci ne ya haɗata da bobo kawai muyi mata addu’a, shi addinin musulunci sai mai rabo” a haka ta gama maganar kafin ta juya zuwa wani salon nada ban.
Jalal na zuwa part ɗinsa direct bathroom ya huce ya cire jallabiyar ya ƙara wanka kana yyi al’wala,turare ya fesa,cikin gajiyawa ya ɓalli tablet ya wasa a  bakinsa tare da ɗurawa da ruwa, farin boxer kawai ya saka ya nufi bed ya kwanta,hannunsa ya saka a bed side ya kashe lamp,wani blue light ya maye gurbin hasken, addu’a yyi sosai ya shafa a jikinsa,kana yaja duvet ya rufe naked skin ɗinsa cikin ƙaramin lokaci bacci yyi gaba dashi.
Jalilerh sam ta kasa bacci sai juyi take saman bed ta riƙa ta saba bacci jikin mahaifiyarta shiyasa yanzu ta kasa jurewa,sannu a hankali kuma kewan gidan ya fara ɗaukewa yyinda ciwon mara ya maye gurbinsa,abun kamar da wasa harya nemi zarce tunaninta,gaba ɗaya wata zufa ta kawowa jikinta ziyara,ciwo yyi ciwo harta kai ta kasa jurewa gashi sam bata san wajanwa zata ba dole sai shi,cikin dauriya ta fito daga ɗakin a hankali take tafiya har zuwa sanda ta sakko daga upstrais,a kwance ta samu Mama tana bacci saman duguwar kujera   ta tura cinyar kaza a bakinta ga kuma wata a hannunta,kai tsaye side ɗin da taga yyi ta nufa,sai dai wajan side huɗu ne ko wanne a rufe,cikin Sa’a taga na ƙarshe a buɗe, cikin fitar hayyaci ta shiga kai tsaye bedroom ta nufa,cikin Sa’a ta ganshi ƙwance yana bacci,gabansa taje ta ƙwanta tare da juyawa tana kallon fuskar gaba ɗaya jikinta rawa yake sabida tsananin ciwo da azaba,can cikin baccinsa yaji shassheƙar kukanta,a hankali ya buɗe manyan gajiyayyun idanunsa cikin Sa’a ya saukesu a saman fuskarsa, lumshe ido yyi kana ya ƙare buɗesu, hannu yasa ya zareta daga jikinsa kafin ya juya mata baya gaba ɗaya bacci ne a idanunsa,kuka ta ƙara sakawa tare da ƙanƙame sa,cikin harshen turanci tace “UNCLE cikina ciwo zan mutu” banza yyi mata cikin wani irin hali taja numfashi mai ƙarfi kafin ta ƙara maƙalesa tace “Please help me, Please UNCLE” sai lokacin ya juya ya kalleta sabida kukan da yaji yyi yawa,kallonta ya shiga yi sosai musamman kayan baccin da aka saka mata,cije leɓe yyi kafin yasa hannu ya tallafe haɓarta cikin sanyin murya yace “ina ne?” ya faɗin maganar yana hura mata isakar bakinsa a saman fuskarta sabida zufar take sakko mata,sam a wannan lokacin ba zata iya magana ba,sabida natsananin a zaba da raɗaɗin data keji,cikin wani irin hali ta kama hanunsa tare da cusa shi cikin wandonta a ƙoƙarin ta na son ɗura hannunsa a saman mararta,kansa ne yaji yyi mahaukacin sarawa sabida inda yaji hannunsa ya sauka, ƙara cusa hannun nasa yyi a wajan da sauri ya zare hannunsa sabida ruwan da yaji ya taɓa..¹³,¹⁴

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *