UNCLE NE CHAPTER 3 BY NIMCYLUV

 UNCLE NE CHAPTER 3 BY NIMCYLUV

Jini ya gani ƙwance a saman yatsun hannunsa,cikin takaici da kuma ƙyanƙyami haɗi tashin zuciya ya sanya hannun a jikinta ya goge jinin,ita dai sam bata fahimtar sa banda nishi da riƙe mararta babu abinda take,shuru yyi yana kallon yadda take jijjiga kanta,sam bai san mene zai manta,bai san ta ina zai fara ba,bai san wanne taimako zai mata ba,gaba ɗaya kansa ya kulle,ganin ciwon na neman kasheta ya saka ta miƙe zaune tare da ƙanƙame jikinta ta saka masa kuka,wani mugun haushi take basa amma babu yadda zaiyi dole ya taimaka mata domin shi ɗaya ta sani a gidan, miƙewa yyi tare da saka hannu a bed side ya danne wani abu nan take haske ya gauraye ɗakin,cikin nutsuwa da kamalar data gama ratsa jikinsa ya fara tafiya zuwa parlour kai tsaye wajan fregd ya nufa ya ɗauko bottle water mai sanyi kana ya dawo cikin bedroom ɗin,inda yake ajjiye tablet ɗinsa ya nufa ya ɗauki diflopenic kana ya dawo inda take ƙwace,zama yyi gefe yana tunanin yadda zai mata, Allah ya sani tana bashi wahala babu wata mace data taɓa raɓar jikinsa sai ita,taɓe baki yyi cikin ransa yace “abinka da mara addini”
da wannan tunanin ya saka hannunsa ya ɗago ta zuwa gefen kafaɗarsa,tablet ya ɓalli guda biyu tare kallonta yace “haa” da kƴar da buɗe bakinta hannunta ɗaya ta sakale wuyansa,saka mata maganin yyi a hankali kuma ya ɗura mata gorar ruwan,da sauri tasha sabida wani ɗaci daya game bakinta,tana shan ta langaɓe sai kiran sunan “jesus” take haɗe rai yyi cikin zafin rai ya zameta daga jikinsa yace “nasan ko a littafinku aƙwai sunnan ALLAH so idan ba zaki faɗin sunan ALLAH kimin shuru da baki,babu wanda ya isa ya baki sauƙi sai ALLAH da kuma alfarmar Annabi Muhammad (s.w.a)”shuru tayi duk da ciwon data keji hakan bai hanata nazartar maganarsa ba,wajan 5minutes ta kallesa tare da kwaɓe fuska cikin sigar shagwaɓa tace “Uncle wani abu nabin jikina” miƙewa yyi tsaye tare da nufar bathroom yana tafe yana jan gemunsa wanda yasha gyara kamar ba zai tankata ba sai kuma yace “baki taɓa ganinsa bane?” cikin shassheƙar kuka tace “eh! tsoro na keji” tsayawa yyi yace “uhm! aure kikeso tunda kin fara ganin al’adarki” yana faɗin hakan ya shige cikin bathroom ɗin.
gaba ɗaya tsoro ya gama cika zuciyar Jalilerh,sai a lokacin abinda Joshua yay mata ya fara dawowa cikin tunaninta,hakan na nufin abinda zai sameta kenan idan tayi auren? tayaya zata yadda wani yyi mata hakan, Allah yaga zuciyarta bata taɓa sha’awa ba kamar yadda ba zata taɓa amincewa da buƙatar Joshua ba,kamar yadda ba zata taɓa amincewa da aurensa ba,saurin zabura tayi sabida wani abu daya ƙara fitowa ta cikin jikinsa,kuka tasa sabida sam ba zata iya jure zubuwarsa ba.
JALAL na shiga bathroom ya cire boxer’n dake cikinsa ya sakarwa kansa shower,babu jimawa ya gama tare dayin brush ya ɗaura al’wala,bathrope ya saka a jikinsa tare da tsane kansa da towel,yana gamawa ya fito ya ƙarasa wajan wardrope ya ɗauki wata ash ɗin jallabiya mara nauyi ya saka,bayan yyi komai ya fesa turare ya ɗauki paryer mat ya nufi waje parlour,da sauri tace “Uncle yaya zanyi?” ficewarsa yyi baiko tsaya ba bare ya tankata,a haka ya ƙarasa parlour ya shimfiɗa daddumar ya tada sallar lafila,sai da yyi raka’a huɗu ya lumshe idanunsa cike da tunani kala kala a ransa kafin ya fesar da wani numfashi mai zafi,ciki  daddaɗar muryarsa mai amo da kuma sauti haɗi da sanyi,ya fara karanta suratul الكهف yadda yake karatun a nutse da kuma yadda yake fidda makarijin huruf da tajweed zaka fahimci ba ƙaramin ilimin addini garesa ba,sosai yake karantu yadda bazai damu wani ba,  kuma yadda bazai takura kansa ba, ma’ana bai ɗaga murya ba haka kuma  bai ƙasa da murya ba.
Lamo Jalilerh tayi tana sauraran muryasa dake fita a taushashe kuma cike da kuzari,haka nan taji ciwon nata ya lafa ga kuma daɗin karatun data samu kanta ciki,tun tana sauraran daddaɗar muryarsa har bacci ya ɗauke ta.
Jalal bai tashi a wajan ba,sai da aka kira sallar asuba yana zaune har akai assalatu, miƙewa yyi ya nufi cikin bedroom ƙwace ya ganta ta cure waje guda ga jinin gaba ɗaya ya ɓata jikinta da kuma bedsheet, taɓe baki yyi ya ƙara ɗaura sabuwar al’wala tare da ɗaukan hula tashi kafiya naci,irin hular nan da larabawa da suke sakawa,sosai ya fito tamkar balaraben gske,a haka ya fito zuwa part ɗin su Abbou, a babban parlour ya samu Abbou zaune da casbawa a hannu,can gefen kuma Irfan ne zaune shima cikin farar jallabiya,da alama Imran da Aryan suke jira,babu jimawa suka fito a tare,gaba ɗaya suka nufi masjid,suna shiga su kaga kowa a zaune ga lokacin sallah yayi, Abbou ne ya kalli maƙocinsa yace “Alhaji Naseer lafiya ina malam muktar ɗin?” “wlh baya da lfy shine aka rasa mai tada sallah” kafin Abbou yyi mgn yaji saukar Muryar Muhammad Jalal bobo a kunnansa na faɗi “sahuu iƙamun sallat” jin haka yasa kowa ya hau sahu,tare da dai-dai ta ƙafafuwa cikin sassanyar muryarsa ya fara tada kabbarar harama kafin a hankali kuma ya fara karanta fatiha kana sura ta biyo baya, sosai kowa ya nutsu har sukai raka’a biyu,bayan anyi sallama tare da addu’a masu tafiya suka fara tafiya wasu kuma suka watse, Jalal ko mutsawa bai yi sai Kur’ani daya jawo ya fara karantawa,kafin ya idar ya fara azkar.
ƙarfe 6 dai-dai ya dawo cikin gidan a main parlour ya samu Aryan na shirin fita motsa jiki,ganin Jalal yasa yayi saurin tsugunawa yace “Barka da asuba yaya” lumshe ido yyi cikin gajiyawa yace “yawwa barister” murmushi Aryan yyi yace “nina tafi motsa jiki sai na dawo” uhm kawai Jalal yace kai tsaye upstrais ya nufa inda Mummy ta koma,yana zuwa yyi knkg tana ciki tana tunanin waza ta gayawa ba taga Jalilerh gaba ɗaya hankalinta ya gama tashi tunda taje data Nihila tayi sallah taga bata cikin ɗakin ta kuma tabbatar wa kanta ba zata fita ba, gyara tsaiwa tayi tace “come in” jin haka yasa ya tura ƙofar bakinsa ɗauke da sallama ya shiga,ganinta tsaye ya sashi durkosawa yace “Mrng Mummy” kansa ta shafa tace “mrng too boo yaka tashi da kuma kwanan baƙunta” cije lips yace “Allahamdulillah” miƙewa yyi tare da juyawa sai kuma ya tsaya cikin tarin baccin dake a idanunsa yace “Mummy yarinyar can na side ɗina” da mamaki tace “a can ta ƙwana? shiyasa naga babu ita duk hankalina ya tashi” ɗauke kai yyi sam ya fara gajiya da yawan surutun nan haka nan,kamar zai kuka yace “wai mararta ke ciwo,i think period ne” murmushi tayi kafin tace “ok bari nazo jeka ƙwanta naga sai yanzu ka shigo” fita yyi ya nufi side ɗin nasa a parlour ya tsaya tare da zare jallabiyar jikinsa ya ajjiye gefen sofa sannan yay ƙwanciyarsa babu jimawa bacci ya ɗauke sa.
yana fita Mummy taje wardrope nata ta ɗauki pat da pan,bayan ta ɗauka taje ɗakin Nihila tana ƙwance sai bacci take tamkar kasa,duguwar riga ta atamfa mai ɗinkin stone,tana da faɗin wuya ga kuma shaf,ita Mummy ta ɗaukar mata,bayan ta ɗauka ta nufi side ɗin Jalal kai tsaye ta shiga bakinta ɗauke da sallama, tsayawa tayi sabida ganinsa da tayi ƙwance a saman sofa sai haɗa zufa yake,ga yadda jijiyoyin kansa da suka firfito,ko ba’a gaya mata tasan kan nasa ne ya mutsa,jitai babu daɗi a ranta domin har zuciyarta bata sha’awar taga wani abun yana damunsa, remote ta ɗauka ta ƙaro masa gudun a.c kafin tasa hannu ta miƙar masa ta ƙafarsa data langwashe,saman forehead ɗinsa ta taɓa taji wani zafi mai ratsa jikin mutum da sauri ta janye hannunta,tasan baccin kawai yana yin sane bawai dan daɗi ba,cikin zallar tausayinsa tace “sorry Bobona laifi nane” cikin bedroom ɗin ta huce a nan ta samu Jalilerh ra kuɓe sai shassheƙar kuka take cikin damuwa Mummy tace “sorry dear tashi muje bedroom” miƙewa tayi sai a lokacin Mummy taga irin jinin data zubar warm water ta haɗa mata a cikin jakuzzie tace ta shiga,batai gardama ba ta shiga ciki,runtsa idanunta tayi sabida zafin ruwan da taji,bayan ruwan ya gama ratsa ta, aka ƙara sauya mata wani kana Mummy ta wanke mata kan tas,har sai da rinin da tayiwa kanta ya fara fita,bayan ta gamayi mata komai tace “kinga yadda nai maki wanka jiya ko” kaita gyaɗa mata alamar “eh” murmushi Mummy tayi tace “good gril nasan you are a shy baki bari yanzu nai maki,maza kiyi ki wanke ko ina na jikinki lungu da saƙo i’m coming” tana faɗin hakan ta fice daga cikin bathroom ɗin, bedsheet ɗin ta cire ta naɗe waje guda,kana ta fita dashi zuwa washing machine,cikin bedroom ta ƙara komawa ta sauya wani bedsheet ɗin ta share ɗakin tayi mopping,ta fesa airfreshiner tare da kunna turaren huta,haka ma parlour ta gyara komai har t.v sai da ta goge bayan ta gama komai ta koma cikin bathroom ɗin tsaye ta sameta ɗaura da towel a jikinsa,ta juna handrayer tana busar da kanta, murmushi tayi tace “yawwa my dear kinsa pat ɗin yadda na nuna maki?”cikin jin kunya Jalilerh ta ɗaga kanta alamar “eh” handrayer ta amsa taci gaba da busar mata da kan tare da faɗin “ki daina kunya im ur mother ba kiga Jalal Mummy yake faɗi ba,so kema ni mummynki ne,duk abinda kikeso ki sanar dani kinji” murmushi tayi tare da sunkuyar da kai ƙasa cikin siririyar muryarta tace “Thank You Mummy” jinjina kai tayi tace “never mind you are my daughter” tana faɗin hakan ta jata zuwa bedroom ta bada underwear ta saka kana ta bata duguwar rigar tasa hannu ta haɗe waje guda alamar 👌🏻tace ” wow! what a beautiful girl” sosai rigar ta amsheta ga yadda hips ɗinta ya zauna dass a jiki ka san cewar atamfar mai orange ce sai ta haska chocolate skin ɗinta,sam batai ƙoƙarin ɗaura mata vail a kanta ba sabida tasan ba hurumin ta bane,direct ficewa sukai daga bedroom ɗin tare da jawo masa ƙofar har yanzu yana ƙwance yana bacci, taso tashinsa ya koma cikin bedroom amma bata son katse masa baccinsa, hasken parlour’n ta rage masa nan ma ta jawo ƙofar suka fice daga ɓangaren samarin gidan.
a babban parlour suka samu Mama gabanta cike da kayan ciye-ciye plat ɗin farfesun kayan ciki daban,ga plat ɗin soyayyan dankalin turawa wanda yasha ƙwai daban,ga kuma wani cup ta cika tea dashi ga ƙaton biredi sai rarakar cikinsa take,dryar dake cin ran mummyce ta subace ai kafin tace wani abu tace “yau naji masifa,mutum yaƙi ci a tsiri kai sa asibiti,naci kuma abun ya zama abin magana,ita dai lfy abin tattalawace ina dalili ga kaya tili guda a gidan amma sai anyimin surutun jalala” shuru Mummy tayi kafin tace “ayya ba haka nake nufi ba,naga gaba ɗaya yanzu 8 tayi shiyasa,amma kiyi hqr ban ƙarawa” ƙarasa tura naman bakinta tayi har yawo na tsiyaya kafin ta haɗiye da kƴar tace “yanzu wannan ahlil kitab ɗin anan zata zauna salon da janye min hankalin jikata,ohhh ni yau naga ta kai na wannan zaƙo-zaƙon abin a hannu fa” ta ƙare maganar tana riƙe haɓa wacce take nuni da ba ƙaramin mamakin abin Mama ta keyi ba, ƙasa da murya  Mummy tayi cikin damuwa da zan can da Mama tayi tace “haba Mama babu ƙyau fa,muda muke fatan ace sanadinmu ta samu rabauta da musulunci,amma mene yasa ke zaki faɗi hakan dan Allah” taɓe baki Mama tayi tace “yanzu kina saka ran wata rana wannan zata musulunta,ehh to kuma abun a hannu Allah yake” murmushi Mama tayi tana haurawa upstrais tace “ah to nufi ne na Ubangiji ai,my dear follow me” ta faɗi maganar tana shigewa ɗakin Nihila tana shiga Nihila na fitowa cikin sauri domin tayi late a school,tana ganin Mummy taje tai hugging ɗinta tace “good mrng Mummy”  shafa kanta tayi tace “mrng baby how are you” cire jikinta tayi tace “Allahamdulillah bye sai na dawo” girgiza kai tayi domin tasan ba zata zauna yin brekfast ba,a haka Nihila ta fita zuwa compund tana fita drever ya jata zuwa N.S University of ibadan (kirkirarriyar makaranta ce) kwanciya Jalilerh tayi tana tunanin maganar Mama,abinda yake damunta shine mene banbancin nasu addini da kuma musulunci,taga kowa da kalan nasa addini kuma kowa aƙwai abinda yafi so game da addininsa,amma mene yasa Mummy keyi fatan ta musulunta? haka tai ta tunani a ranta ba tare data fahimci komai ba,sannan ta kasa gane banbancin nata addinin da kuma na Musulunci da suke faɗa.
misalin 11 na safe kowa ya haɗu a wajan danning, Mummy, Mameey, Mama, Abbou, Imran,Irfan tun 7 yabar gida sabida aikin bank yake, Aryan shima yana da Shari’a yau,tun 7 yabar gida, JALAL kuma har yanzu bai fito ba,bayan sun kammala breakfast ɗin ne, Abbou ya miƙe yace “nizan tafi ina da meeting by 10:30 i will be back soon” gaba ɗaya sukai masa sai ya dawo,kasan cewar a ɗakin Mameey yake har jikin mota ta rakashi, Mama kam main parlour ta koma ta kunna t.v ta fara kallon cartton,turo ƙofar ɗakin Mummy tayi a hankali Jalilerh ta ɗago kanta tare dayin murmushi fararan haƙoranta sukai bai yana,cikin nutsuwa ta miƙe daga zaunan har Mummy ta ƙarasu inda take tsaye tace “my dear ke ɗaya a ɗaki ko” murmushi kawai tayi ba tare da tace komai ba,kama hannunta Mummy tayi tace “ban son shurun nan naki yana takurani Jalilerh” kallon Mummyn tayi tace “babu yare sosai a baki” dry ce ta ƙwacewa Mummy sai da tayi mai isarta tace “ehee haka kikaji hausa ashe” kafin ta ɗura da faɗin “haka za kice babu hausa a bakina sosai” turo baki tayi tare da shagwaɓe fuska kamar zatai kuka tace “that’s what i mean” “okey dear muje ki kiramin bobo” tana faɗin haka suka nufi downstrias a parlour suka samu Mameey da Mama na zaune, Mameey na kitsewa Mama kanta,tanayi amma Mama na bata basifar babu abinda ta iya,dry kawai Mummy tayi tare neman wajan zama ta zauna,ganin har yanzu Jalilerh na tsaye bata je inda ta aiketa ba,ya sata faɗin “maza jeki kiransa mana” da “okey” kawai ta amsa ta nufi part ɗin nasu kai tsaye side ɗinsa ta nufa,a hankali ta ɗura hannunta a saman handle ɗin tare da tura kanta cikin kyakkyawan parlour’n nasa,ganin  babu kowa sai ƙarar a.c da kuma ƙamshin airfreshner, rarraba idanunta ta fara yi kamar mara gsky,sam bata son shiga cikin bedroom ɗin,amma idan ta koma mene zata cema Mummy? sanin bata da abin faɗa yasa ta ƙarasa baƙin ƙofar shiga bedroom ɗin cikin tsoro daya kamata ta tura kanta ciki,wata nauyayyiyar ajjiyar zuciya ta sauke ganin babu shi a bedroom ɗin, ƙarar watsa ruwa da taji ya tabbatar mata yana cikin bathroom,a hankali ta ƙarasa wajan dressing mirrow tare da saka hannu ta ɗauki parfume ɗinsa wanda yafi so,ta shiga fesawa a jikinta,nan da nan ƙamshin ya shiga cikin bedroom ɗin,ya haɗu da ƙamshin airfreshner da kuma sanyin a.c ya bada wani kalan ƙamshin mai daɗin gaske, ƙarar buɗe ƙofa da taji yasa tayi saurin  juyawa a tsaye ta gansa ya juya mata baya hannunsa riƙe da ƙaramin pech ɗin towel yana goge ruwan dake sauka daga sumar kansa zuwa fresh skin ɗinsa,tana tsaye harya ƙarasu wajan dressing mirrow’n ya fara ƙoƙarin juna handrayer,duk abinda take yana kallonta sai dai sam ba ita ya bawa attention nasa ba,juyawa tayi zata bar ɗakin yyi saurin saka hannu ya jawota zuwa gabansa, kallonta yyi sama da ƙasa kafin ya lumshe idanunsa tare da sanya tafin hannunsa a saman wuyanta, ƙara matsuwa yyi sosai kusa da ita har numfashinsu na haɗuwa waje ɗaya cikin wata kasalalliyar murya wace take ɗauke da manufofi kala-kala yace.
“kin iya gulma ko?” ya faɗi hakan yana zare hannunsa daga wuyanta daman yyi hakanne domin yaji zafin jikin nata kuma thanks God she is fine ba kamar jiya ba,baya yaja kaɗan tare da jan stool ya zauna ya fara  busar da sumar kansa wacce take a jiƙe,bayan ya gama ya ɗauki wani lotion mai daɗin ƙamshin da kuma sauƙin zafi a jiki,har zai zare towel ɗin jikinsa sai kuma ya fasa,ba tare daya kalli inda take ba bare yasan ina take kallo yace .
“get out”
lumshe ido tayi sabida yadda muryarsa ta daki kunnanta,yatsun hannunta ta fara wasa dashi,a haka ta samu damar ware ƙaramin bakinta wanda yake ɗauke da jajayen laɓɓa tace.
“Mummy ne yace kazo”
shuru yyi mata kamar yadda bai motsa ba,haka itama bata fita ba kamar yadda yace,a ransa yake mmkin rashin kunyarta, anata ɓangaren kuma jira take taji amsarsa shiyasa bata fita ba,abinda bata sani ba indai Jalal ne ƙala bazai ƙara cewa da ita ba.
bayan ya gama shafa lotion ɗin a ƙirjinsa zuwa cikinsa ya fara zare towel ɗin dake  ɗaure a waist ɗin sa,da sauri ta juya masa baya and she closed her eyes,hannu tasa ta dafe ƙirjinta dake bugawa sabida bata taɓa ganin kyakkyawar sura mai ɗaukan hankali kamar tasa ba,a hakanma Allah ya taimake ta ba taga tsarai cinsa ba,sai kwantacciyar sumar data gani ƙwance on his lap abin ya bata mmki,domin bata taɓa ganin suma a cinya ba sai a kansa.
Jalal duk miskilancinsa sai da ya kusa yin dry sabida yadda yaga ta tsorata abin ba ƙaramin dry ya basa ba,amma taurin zuciya da mislikanci irin nasa ko murmushi bai yi ba,sai ci gaba da shafa lotion ɗin yake a saman farar fatarsa,tsaki yaja kaɗan a zuciyarsa yace.
“tayaya zan bar wata taga jikina,wannan al’ƙawari ne daga zuciyata zuwa zuciyar dana aminta taga tsarai cina,amma ba wata middle class  like Jalilerh ba”
duk wannan maganar a zuciya yake yinta, Jalilerh data tabbatar bazai magana ta sauke ajjiyar zuciya tare dajan ƙafafunta tayi waje ta barsa da mislikanci sa,tana fita yana gama shafa lotion ɗin body spray ya fesa a saman fatarsa,kana ya shafa wani mai a saman sumar sa,tare  dasa cump ya ƙara ƙwantar da sumar ta sauka har wuyansa,wajan wardrope ya ƙarasa ya ɗauki farar singlet da kuma farin boxer ya saka a jikinsa,bayan ya gama ya ɗauki wata ɗan yar shadda getzner lemon colour,ya saka a jikinsa, a gogan adidas ya maƙala a hannunsa tare da saƙala farin bluetooth a kunansa, ohud mood ya fesa a jikinsa kana ya ɗauki farin glass ɗinsa ya manna a idanunsa, yana gama shiryawa ya kwashi wayoyinsa yyi waje.
A zaune Jalilerh ta samu Mummy ita da Mameey suna shira sai Abbou da dawowarsa kenan, ya zauna tare da fara kallon labarai b.b.c news, cikin sanyin jiki da kuma na muryar tace.
“Hello”
gaba ɗaya suka kalleta a tare kafin Mameey tace “ya naga ke ɗaya where is he?” ta tambaya tana leƙa bayan Jalilerh,ganin babu kowa kuma Jalilerh batai magana ba yasa Mummy faɗin.
“how is he? hope ba jikin nasa bane,dan ɗazo na samesa baya jin daɗi”
“bobo ne babu lfy? kuma shine baki gayan ba,bayan kinfi kowa sanin halin da yake shiga idan jikin nasa ya mutsa wannan ai sakaci ne dear,yanzu yana ina?”
kafin su ƙara magana yyi sallama cikin daddaɗar muryarsa mai cike da kamala, miƙewa Abbou yyi ya ƙarasu inda yake tsaye yace.
“bobona yaya jikin when ka kasance babu lfy?”
ya jera masa tambayoyi lokaci ɗaya, lumshe ido yyi tare da ware su a saman fuskar Abbou kamar yaro haka ya kwaɓe fuska sai kuma yyi hugging Abbou yace.
“i’m fine Abbou na,bana jin ciwo”
sumar kansa ya shafa tare da ɗan bubbuga bayansa cikin nuna jin daɗi yace “ma sha Allah, Allah ya ƙara sauƙi bobona” da “Ameen” ya amsa kafin ya ƙarasa kusan Mummy ya zauna yace “Barka da hutawa Mummyna”
hanci ta lakuce masa tace “naƙi na amsa,tun safe nake jimaminka sbd na sameka kana fama da ciwon kai yanzu kuma kace a’a”
murmushi yyi kaɗan wanda iya kacinsa saman labɓansa yace.
“eh Allahamdulillah sai yunwa”
cikin nasa ta shafa tace “ai dole kaji yunwa,rabonka da aminci tunda jiya da daddare shima kuma coffee da indomie,bobo tayaya rayuwa zata yiwo kanama kanka huran yunwa?”
langwaɓar da kai yyi gefe ba tare da yace komai ba,sabida yasan dukkan abinda zai faɗa baza ta taɓa ganewa ba,a duk sanda yaci abinci mai nauyi ranar baya ƙwana da lfy,shi kaɗai yasan abinda ke damunsa,babu wanda zai iya gayawa sirrinsa,babu wanda zai yadda ya bashi damar da zai fahimci rauninsa,yasan komai mai hucewa ne,daman haka rayuwar take,zai ci gama da zama da lalurar dake damunsa,idan yana da rabon samun lfy  babu shakka shima zai zama mutum mai kuzari da kuma cikakkiyar lfy,zai zama na miji mai taƙama da kansa,amma yanzu bashi da wannan ikon shi ɗin kamar fankon asha na ne wanda bashi da wani amfani,idan lalurarsa bata warkewa bace zaici gama da zama a haka daga nan har lokacin da zai koma ga ubangijinka, ajjiyar zuciya ya sauke Lokaci da Mummy tace.
“mene kake tunani tun ɗazo ina magana shuru ko aƙwai matsala ne?”
Kafin yyi magana Mama tayi saurin cafe zan can ta hanyar faɗin.
“yooo wacce matsala wacce ta huce nunƙufarci,mutum yyi ta zama da basir yana kumburasa kamar ana jiƙa yissa ana bashi,nikam sam bani kayo ba,nawa basir ɗin lafiya yake ƙarawa,idanma zaka daina cin wannan taliyar yaran gwamma ka daina ahhh to shawara nake baka ba basir ba”
ta ƙare zan can tana zama a ƙasan carpet ta ƙara da faɗin “ohhh wannan ƙafar Allah dai yyi mki Albarka,amma kina bani matsala walle”
sai a lokacin Jalal ya ware manyan idanunsa da suke a lumshe kamar bai son mgn yace.
“Ga Dr kusa ai”
ya faɗi hakan yana jawo ƙaramin table ɗin da Mummy ta jera masa abincin a kai,wata uwar harara Mama ta watsa masa kafin ta kalli Abbou tace.
“wlh Kabeeru ka rabani da ɗanka tun yanzu,to ko Zulfa ce a gabana ƙarewar kai babu wanda ya isa ya tsiramin wannan shegiyar abar”
ajijjye spoon ɗin hannunsa yyi bayan ya sanya dafaffiyar hanta a bakinsa,sai da ya gama taunawa a bakinsa ya haɗiye kana ya kalli Mama yace.
“wace kuma Zulfa?”
ya tambaya yana ƙara saka wata hantar a  bakinsa, Mummy ƙirjinta ne ya  buga da ƙarfi domin bata taɓa tunanin zai tambaya ba,ta ɗauka zai mata shuru kamar yadda share surutan ta na baya, Abbou ma tsayawa yyi da kallo sabida kansa daya sara masa,haka nan yaji ransa ya ɓaci ba tare da san dalili ba, Mummy ce ta  kalli Abbou taga ya sunkuyar da kansa ƙasa kamar mai nazarin wani abun.
jin shuru yyi yawa yasa ya ɗaga kansa ya fara kallonsu ɗaya bayan ɗaya har yazo kan Mummy wacce idanunta ya sauya, ajjiye spoon ɗin yyi kana ya ɗauki gorar ruwa mai sanyi ya shaye tass ya ajjiye  emty bottle ɗin,cikin nutsuwa ya miƙe tsaye yana mai kallon Jalilerh wacce bacci ya ɗauketa a ƙasan carpet.
“but bobo ai baka ci komai ba?”
ɗan haɗe rai yyi kana ya kalli agogon hannunsa 1 saura,part ɗinsa ya nufa yana tafe yace “how can i ate? bayan kun tsora min ido kamar marasa gsky” yana faɗin hakan ya kalli Abbou yace “it’s time for paryer Abbou” yana faɗa ya shige part ɗinsa domin ɗaura al’wala.
gaba ɗaya kasa tanka masa sukai hatta Mama da take sarkin karaɗi,kowa da tunanin da yake a cikin ransa, Mummy tunanin yadda al’amarin ya kutsu kai ba tare da tayi tunanin zuwansa ba,sam bata taɓa tunanin aƙwai ranar da za’a ambaci sunan Zulfa a cikin gidan ba,duba da yadda babu wanda ya santa a yaran, dukkan wani sing da zai nuna ita wacece a gidan an guje masa,fatan ta ɗaya wannan ranar ta zama ta ƙarshe, addu’ar ta ɗaya ALLAH yasa Mama ba zata ƙara mai-mai ta wannan kuskuren ba,domin su take ta nunawa Jalal itace mahaifiyarsa,ita ta kawowa duniya,tana son ta bashi gata kamar yadda ko wacce uwa take bawa yaranta.
Mama tayi hakanne sabida zallar kamanin da suke a fuskar Jalal,sai take ganinsa tamkar Zulfanta babu abinda ya ban ban ta su sai banbancin jinsi,ganinsa a yanzu yasa taji kewa da kuma rashin uwar tasa ya faɗo mata a zuciyarta,ta ambaci sunan tane sabida bata son a manta da ita a cikin gidan.
Mummy itama a gareta kusan hakanne,bata sha’awar ko kuma fata ace yau Jalal ya fahimci ba Jamal bace ta kawosa duniya ba, addu’ar ta ɗaya yaci gaba da kwallon Jamal as his mother,shine fatan ta.
sallamar Aryan dake shigowa yasa ko wannansu ya dawo cikin hankalinsa, ƙarasa shigowa cikin parlour’n yyi kai tsaye ya nufi inda Jalilerh take a ƙwance yace “Mummy kalli bacci take a ƙasa,ai sai jikinta yyi mata ciwo” ya faɗi hakan yana saka hannunsa ya ɗago ta zuwa jikinsa hakan yyi dai-dai da fitowar Jalal daga part ɗinsa, taɓe baki yyi a zuciyar yana mai faɗin “fuck You Aryan”
ƙwantar da ita yyi akan duguwar sofa kana ya zauna a gefen kanta yace “bar kanku da hutawa ya zaman gida”
miƙewa Mameey tayi tace “to aku sarkin surutu ya shari’ar?” dry yyi yace “Mummy kin jita ko? so take nayi shuru kamar yaya Jalal” dry Mummy tayi tace “rabu da ita yarona fatan kayi nasara dai?”
miƙewa yyi yace “Allahamdulillah wlh Finally yau naga ƙarshen shari’ar,kuma at the end nayi nasara”
ma sha Allah cewar Abbou ya faɗa yana mai sakkowa daga saman bene, cikin jin daɗi Mummy tace “i knew ai duk yarana babu ragun ɗaka Allah ya taimake ku baki ɗaya”
tsaki Jalal yyi kana ya kalli Abbou a gajarce yace “muje lokaci fa” yana faɗin hakan yyi ficewarsa sam Aryan bai damu ba,domin yasan Jalal tun ba yanzu ba, lokacin da yake Paris idan suna chart sai ya ɗauki sama da awa uku ba tare daya masa replay ba,kuma yana online,idan ya kirasa vedio call tsakaninsa dashi uhm to a’a,ko kuma yace a kira masa Nihila su gaisa,a hakanma sunfi shaƙuwa dashi akansu Irfan,zama ya gyara yana mai ƙarewa Jalilerh kallo wacce take bacci cike da ƙwanciyar hankali,haka nan yaji wani abu ya ɗarsu a ransa game da ita,sosai ƙyanta ya ruɗesa haka nan ya samu kansa da kallon fuskarta.
Jalal kai tsaye masjid ya nufa yana zuwa mutane duk suka miƙe alamar daman shi suke jira,wajan liman yaje ya tsaya tare da tada kabbarar harama,ya buɗe baki zai fara karatu kenan yaji kansa ya sara da ƙarfi har sai da..
Buhainat: Da mmki Education secretary ɗin yake kallon Jalal kafin yace “uhm muda muka  ɗauke ka karatu zuwa Paris as valunteer,duk ba kaga wannan ba, har kai ne kake da bakin cewa zaka bamu aiki,mene kake dashi? dame kake taƙama da zaka bamu aikinsa…!,?” ya ƙare mgnar yana ɗan ɗaga muryarsa,kallonsa Jalal yyi da lumshasshun idanunsa kafin yyi pouting lips ɗinsa cikin jan numfashi yace.
 “ai sauƙi na nema maku,daman kuma da ra’ayin hakan naje karatun,bawai dole nake maka ba amma dai na faɗa maka nike da aikin da zan baku”jinjina kai Education secretary ɗin yyi kafin yace “mene aikin?” hand back ɗinsa da yazo da ita ya ɗauka tare da zuge zip ɗinta ya fara ciro wasu takardun,bayan ya gama ya tura gaban mutum yace “dukkan baya nan da zai nuna shaidar ni haifaffan garin ibadan ne aƙwai shi a nan…,” ajjiyar zuciya ya sauke tare dajan sajen fuskarsa ya ƙara da faɗin “takaddun primary,secondry, University duk aƙwai su  nan,dukkan shaidar da zata nuna ingancin ILIMINA,da kuma nagarta ta, aƙwai ciki” yana faɗin haka yaja bakinsa yyi shuru yana sauraran abinda Education secretary ɗin zai faɗa, murmushi yyi ya fara duba file ɗin nasa tare da faɗin “what the you want,all this na mene Jalal?”miƙewa Jalal yyi tare da mayar da farin glass ɗinsa yace “i want be a president”cikin ɗaga murya haɗi da mmki yace “what..!?president,meye haɗin ka da zama shugaban ƙasa kai da kake babban likita mai zaman kansa,na ɗauka ma za kace asibiti ka keso a buɗe maka,gsky Jalal kayi tunani zaka saka kanka a haɗari domin haɗa ta kara da President Mubarak Yahya cibo,ba ƙaramin haɗari bane,kai ne baka san shi ba,amma ni nayi masa farin sani” mai maƙon jikin Jalal yyi sanyi saima ƙara jan kujera da yyi,tare da juya kujerar ya ɗan fesar da numfashi few seconds ya kalli mutumin yace “meye naka ciki? iya kaci ka kai maganata ga shugaban jam’iyya,dukkan abinda yace kana da number na” yana faɗin haka ya miƙe tsaye,tare da miƙawa Education secretary ɗin hannu sukai musabawa kana yyi ficewarsa daga office ɗin,zama Mustapha yyi yana tunanin maganar Jalal, tabbas yana da nagartar da za’a bashi dukkan abinda ya keso,amma bai taɓa tunanin abinda zai nema ba kenan,ganin  bashi da wata mafita dole ya miƙa maganar Jalal ga shugaban jam’iyya,da wannan tunanin ya miƙe ya fara haɗa kayansa da kuma file ɗin da Jalal ya bashi kai tsaye shima ya bar office,tare da bawa p.a ɗinsa saƙon dukkan wanda yazo nemansa ace ya jira zuwa gobe,domin yau bazai samu zama ba…,da “okey sir” ta amsa shi kuma ya nufi harabar waje inda yake ajjiye motarsa, Jalal na fita ya daɗe cikin motarsa kafin ya fesar da wani numfashi mai zafi kana yyiwa motar key yabar wajan gaba ɗaya,a parking space yyi parking motar yana gamawa,ya ɗaga kansa ya kalli Moll ɗin,gaba ɗaya bai son hayaniya da kuma tarin jama’a amma dole ya shiga dan bai son ɓata ran Mummynsa,a hankali ya buɗe murfin motar ya fito,yana fitowa yaja gajiyayyun idanunsa ya rufe sabida wata daddaɗar iska daya buge fuskarsa,agogan hannunsa ya kalla yaga 11:30 sai a lokacin ya tuna ko coffee da yake sha yau bai sha ba,cikin takonsa na taƙama,ya shige cikin moll yana shiga ma’aikatan wajan sukai masa barka da zuwa,ganin ya shafe 30 second a tsaye ya sanya wata ma’aikaciya ƙarasuwa wajansa tace “sir what the you want?” ba tare daya kalleta ba yaci gaba da latsa wayarsa yana faɗin “ki haɗamin kaya na mace, komai da komai” cikin mutuntawa tace “ok sir shekaru fa? taɓe baki yyi tare da manna wayar a kunansa kana yace “16 to 17 yrs” da sauri ta juya ta fara haɗa masa dukkan wasu kaya na sawa da mace zata buƙata,abaya irin marasa nauyin nan, fakistan,seket da riga na ƴan kanti,dugun wando jeans,vest, underwears,dasu pat, yana daga tsaye yake kallon abinda take haɗawa komai ta ɗauka sai yaga ya dace da ita,sauke idanunsa yyi yaci gaba da faɗin “Jafar i want see You,but bana gida yanzu zuwa dare ina free” daga can bangaren Jafar yaja tsaki cikin takaicin halin Jalal ɗin yace “kana da matsala wlh mutum yyita nunƙufarci shi ɗaya wannan ba rayuwa bace” lumshe ido Jalal yyi yace some few seconds yace “Thank God tunda bada wani nai ba,bye i will back you lrt”wayar ya katse tare da kallon matar, da hannu yyi mata nuni takai masa mota,yana daga cikin ya danna key ɗin motar Boot ɗin ya  buɗe, a.t.m ya bayar suka ciri kuɗinsu,cikin mota ya koma yyi mata key kana yabar cikin moll,a hanya ya tsaya a wani super market ya siyi apple, strawberry, inibi, chocolate,yougurt, ice cream, shurt bread,da duk wasu takarkacan zaƙi,kana yasa aka kawo masa gashasshen kifi ana gama haɗa masa,ya nufi gida yana zuwa yyi parking ya fito, cikin Sa’a yaga Murtala mai gyaran shuka da hannu ya kirasa yana zuwa ya durkosawa yace “yallaɓai barka da dawowa” lumshe ido yyi ya bude hakan alamace ta ya amsa masa, Boot ya buɗe yace “kai ciki” gaba ɗaya Murtala ya fara kwasar kayan yana shigewa dasu cikin gidan,bayan an kwashe komai ya rufe Boot ɗin,shi kuma ya juya zuwa masjid,bayan an idar da sallah ya fito daga masjid,yana ƙoƙarin shiga gida Nusaibat na fitowa,da idanu ta kafesa har ta ƙarasu inda yake tsaye, shikam kota kanta baimi ba ya tura kansa cikin compund ɗin gidan,yana shiga shima Abbou ya fito daga masjid ɗin,kallon Nusaibat yyi yace “a’a daughter har kin fito kenan” kaita ɗaga masa tare da faɗin “eh Abbou” murmushi yyi mata yace “kuma sai yanzu bobo ya shigo gidan,aida kin tsaye kun gaisa,ba kya yi zaman banza ba” kanta a ƙasa tace “a’a naga ya gaji zan dawo ne ai” jinjina kai yyi yace “ok sai kinzo” da haka ta shige gida a tare suka jera ita da Alhaji Mubarak mahaifinta zuwa cikin gidan….,lokacin daya shiga gidan babu kowa a main parlour sai Mama ta tisa gashasshen kifin da yazo dashi tana ci hannu baka hannu ƙwarya,fito da ido waje yyi tare da faɗin “yau naga kama ɓera” washe baki tayi tace “a’a Muhammadu lale ai nace tun da naga kifin nan nace nawa ne ka siyo min, sabida kam cikin yaran nan babu mai tunanin siyomin wani abu sai kai, ahhh to ka dama Imran yaji labari,kaiii Allah dai ya ƙyauta mana ai ban taɓa ganin marowacin yaro kamarsa ba kuma…” dry Imran yyi yace “wato matar nan baki da al’ƙibila,yanzo fa kika gama faɗin yaya Jalal bashi da kirki mislikanci yyi masa yawa,baki taɓa ganin Mutum mai taurin zuciya irinsa ba,gashi ƙato kamar basa mude dukkan matar da zata auresa ba ƙaramin jahadi zatai ba…kai ni wani abunma bakina bazai iya faɗin sa ba domin yyi muni” salati Mama ta zabga tare da sauri haɗiye kifin data saka a bakinta tace “yau naji haɗin faɗa Allah Nagode maka ina da sheda ina yarinyar nan mai irin sunanka dan Allah faɗa masa gsky…” ta ƙare maganar tana kallon Jalilerh wacce take ƙwance tana kallon Jalal da duk maganar da ake idanunsa a rufe yake,shima sai lokacin ya buɗe idanunsa ya sauke a cikin nata idon,sauke idanunta tayi,kayan jikinta yabi da kallo ganin wando three gauter a jikinta sai ƙaramar riga wacce ta fito da surar jikinta ga yadda gashinta yyi ƙwance a gefen fuskar, ɗan ƙwana biyon da tayi a gidan gaba ɗaya ta sauya kamar ba ita ba, Aryan dake tsaye tun ɗazo a bakin ƙofa yace “beb ke kifaɗi gsky mana tunda a gabanki akai” ya faɗi maganar yana shigowa cikin parlour’n,turo baki tayi gaba cikin ƙaramar muryarta tace “ban iya mai-mai tawa aƙwai tsayi maganar” salati Mama ta kuma rafkawa tace “daman da ganin yarinyar nan muguwace babu Allah a ranta,amma akan idanunki na faɗi komai kice wai baki sani ba,ehhh ai ba abun mmki bane tunda ahlil kitab ce ke” miƙewa Jalal yyi tare da faɗin “uhm wannan kifin dai na barbaɗa giya ciki” da sauri ta furzar dana bakinta tace “ahhha kai dai Muhammad aƙwai mugun mutum,ashee dai nayi gsky banda mugunta babu abinda ka iya,kabarni naita turawa a cikina..,haba shiyasa naji na fara juyawa idanuna yana janyewa wlh ka sani nai maye ban yafe ba” Imran ne yyi dry yace “da kuwa kinyi ƙyau da mayen” miƙewa tayi ta fara kumfar baki tare da faɗin “wlh gidanku zan bar maku,sbd kunga ina zaman cin arziƙi ko? nima da Lamir yana nan bako isa ku ganni a wannan shegen gidan naku ba,gidan kamar za’a sai da mutum lungo da saƙo,jiya na leƙa wani waje na ɗauka irin ruwanan ne dake taruwa ashe naku na mugunta ne banda wannan yaron Murtala nake faɗa maku da tuni nayi iyooo a ciki” duk miskilancinsa sai da yyi murmushi, Abbou da Mummy dake sakkowa daga saman bene Abbou yace “gidanku bobo me kai mata ne” waro ido Jalal yyi tare da juyawa idanunsa yace “kawai gigin tsofa ne” kallon Abbou tayi tace “Nagode Allah daya nuna maka abinda Muhammadu kemin,haka jiyama sabida na shiga ɗakin sa neman wannan abun na roba wanda ake lakata da cokali ya koroni” girgiza kai bobo yyi jin abin hadda sharri kallo Irfan yyi wanda shigowarsa kenan daga makaranta sabida lecture ne yace “kai min kayan nan side ɗina” yana faɗin haka  ya shige cikin part ɗinsa, Abbou da kƴar ya lallaɓa Mama tayi shuru, Jalal bayan yyi wanka ya sauya kayansa ya zauna daga shi sai three gauter ko singlet ɗin dake sakawa yau bai saka ba,yana zaune yana watching t.v yaji an turo ƙofar kai ya ɗaga dan ganin wake shigowa,kamar yadda yyi zato itace h riƙe da tray a hannunta sai kuma dugun jug da ƙanan glass cup guda biyu, miƙewa yyi ya nufi wajan t.v ya ɗauki remote,tana ajjiye tray ɗin a saman table ta juya da sauri zata bar parlour’n tako biyu yyi ya sanya hannu ya damƙo ta, hannu yasa a saman lips ɗinta ya kama ya murɗa da ƙarfi zafin data jine yasa ta kifa kanta a ƙirjinsa ta saki kuka tana yarfe hannu,ganin yadda take kukan yasa shi zagaya hannunsa ya rungometa a jikinsa tare da ɗura laɓɓansa a saman kunanta ya ɗan busa mata iskar bakinsa yace..
Buhainat: Ya saka hannunsa ya dafe saman kansa,a zuciyarsa yana mai karantu sunayen Allah guda 99,har kan ya lafa masa,kana ya fara karatun cikin nutsuwa da  kuma kamala,a haka suka idar da sallah zuhur ɗin, bayan an sallame anyi azkar wasu suka buƙaci Jalal da yayi masu ƙarin karatu haka ya fara karatun nan kowa ya zauna yana sauraran sautin daddaɗar muryarsa,kowa yaja Kur’ani gabansa yana kalla amma shi idanunsa lumshe yake yana karatun cikin ƙwarewa.
    bayan sun kammala sukai masa gdy shima miƙewa yyi tare da ficewa daga masjid ɗin, ƙofar get ɗin gidansu ya samu Abbou tsaye shida Alhaji muktar suna tattaunawa,suna ganinsa sukai shuru,kallon Abbou yyi kana ya kalli abokin Abbou yace “barkan ku da hutawa” cikin nuna kulawa Alhaji muktar yace “yawwa Muhammad Jalal yaya karatun” lumshe ido yyi tare da pouting lips ɗinsa yace “Allahamdulillah” yana faɗin hakan ya kalli Abbou cikin ƙasa da murya yace “Abbou ban key ɗin motarka zani duba motar dana saka a kawomin sbd gobe aƙwai inda zani mai muhimmanci” hannu Abbou yasa a aljihunsa yace “to! aikam na bar key ɗin a main parlour bari na kira Aryan ya kawo maka” girgiza kai Jalal yyi tare dayin hanyar ƙaramin get yana tafe yana faɗin “no bari naje” ya ƙarasa maganar yana shigewa cikin gidan.
   Bayan shigewarsa Alhaji Kabeeru ya kalli Abbou cikin damuwa da maganar da suke yace “anya Jalal lfy yake? naga ya faɗa ko kuma a haka yake ne,kasan rabona dashi tun yana ƙarami” numfashi Abbou ya sauke cikin damuwar shima yace “Ni kaina lamarinsa yana bani mamaki,amma tun ranar daya dawo gida nasan baya cikin nutsuwarsa kuma lfy bata ishe sa ba,lamarin Jalal yana damuna shiyasa ma yanke shawarar abinda naga ya dace banda kai da liman babu wanda ya san da wannan lamarin hatta shi Jalal ɗin banso ya sani, nasan wata rana zaiyi alfahari da abinda nayi masa”
murmushi Alhaji muktar yyi domin ya fahimci manufar abokin nasa,da kuma babban dalilinsa akan wannan lamari,kuma shima yana tare dashi “yanzu yaushe za’ai kenan?” 
“dole mu jira sanda liman zai dawo masjid sabida ina son komai ya tafi yadda mukeso” da wannan maganar Alhaji muktar yace “shikenan Allah ya taimaka yyi jagora” sallama sukai kowa ya shige cikin gidansa.
  tura ƙaramin get Abbou yyi ya shiga cikin gidan nasa,yana shiga ya samu baba habu da Laure suna cece kucan nasu da suka saba, girgiza kai kawai yayi ya nufi cikin gidansa.
     yana shiga cikin gidan ya samu Aryan da Jalilerh suna magana wacce ta shinta kenan daga bacci, duk irin baccin da tayi akan idanunsa,sabida ko cikin part ɗinsa baije ba,zama yyi akan sofa yana mai kallon Jalilerh wacce itama shi take kallo kansa ya ɗauke yace “dear naji Mummy tana kema  ba kiji daɗi ba, Allah ya baki lfy ya jikin yanzu?” cikin jin daɗin kulawar daya bata tace “naji daɗi yanzu Abbou” dry Aryan ya fara yi sabida Hausar da yaji tayi Turo baki tayi tare da shagwaɓe fuska cikin Muryar shagwaɓa tace “Abbou ka ganta ko” shima Abbou danne dryar dake shirin ƙwace masa yyi yace da ɗan haɗe rai yace “rabo dashi kinji, Jalilerh shima ai bai iya magana ba” yana faɗi hakan yana juyawa bayansa sabida takun da yaji a bayansa,shima Aryan juyawar yyi, Jalilerh kuma saurin sunkuyar da kai ƙasa tayi sabida tun kafin ya ƙarasu daddaɗan turarensa yyi mata sallama, miƙewa Aryan yyi yace “Abbou zan raka yaya” da sauri Jalilerh ta riƙe hannun Aryan tace “zani” wani banzan kallo Jalal ya watsa ba wanda ya sanya tayi saurin zame hannunta daga jikin Aryan,shi kuma Aryan san bai kula da hakan ba,hannunta ya riƙe tare da sunkuyawa kaɗan yace “yanzu yaya zan raka,ki bari week end yazo sai mu fita tare da Nihila kinji beb” kanta ta gyaɗa masa alamar yadda,wani tsakin Jalal ya kuma yi ba tare kuma da yace komai ba yyi ficewarsa daga cikin gidan,yana fita ya ƙarasa jikin motar Aryan ya sanya ke ya buɗe kai tsaye mazaunin drever ya zauna,hannu yasa yaja murfin motar yyiwa motar key,da sauri Aryan ya ƙarasu yace “am sorry na tsayar dakai” lumshe ido Jalal yyi tare da fesar da wani zazzafan numfashi ta cikin bakinsa kafin yyiwa motar revers yace “no na fasa fitar dakai,naga kana abu mai muhimmanci” yana faɗin hakan yaja motar da gudu daman tuni baba Habu ya buɗe masa get,kai tsaye ya fice daga cikin gidan.
    baki sake Aryan yabi motar da kallo harya fice daga cikin gidan,juyawa yyi ya koma yana shiga Jalilerh ta miƙe tsaye tare da ƙarasuwa wajan ta faɗa jikinsa tace “oyoyo” kanta ya shafa tare da janyeta a jikinsa yace “beb na fasa fitar ai tunda baki so” murmushi tayi har saida dimples ɗinta suka loma cikin jin daɗi ta ƙara shiga jikinsa tace “Thank You brother” hannunta ya kama yace “zauna kiyi kallo zan watsa ruwa na huta kafin ai la’asar” sakinsa tayi kafin ta tace “mene la’asar?” suit ɗin jikinsa ya cire tare da riƙeta a hannu yace ” nasan a garinku kuna zuwa Church ko?to muma a nan muna zuwa masjid muyi ibadan mukaiwa Allah kukanmu tare da gaya masa buƙatun mu,kuma sai kiga alfarmar Annabi Muhammad (s.w.a) ya biya mana dukkan abinda muke nema wajansa” shuru Jalilerh tayi tana sauraran abinda yake faɗa mata,kafin tayi saurin faɗin “amma mene yasa bakwai roƙan jesus?” murmushi yayi mata tare da bata dukkan nutsuwarsa yace “jesus shine Annabi Isa Alaihissalam,kuma ɗa ga Maryam,shima Allah subhanahu wata’ala shine ya hallicesa kamar yadda ya halicci Annabi Muhammad,kuma babu wanda muke da ikon bauta wa sai Allah,sannan kuma muyi Annabi Muhammad mubaya’a domin shine Annabi gsky,kuma shine mai cetanmu ranar lahira” Mameey dake sakkowa daga upstrais ta ɗura da faɗin “kuma dukkan wanda ya yarda da Allah ya zama dole ya yarda da Annabi Muhammad (s.w.a)ko a Bible bayan an ambaci Annabi Isa,sai aka ambaci Annabi Muhammad wanda hakan na nufin babu wani Annabi bayan shi” ta ƙare maganar tana sakkowa daga saman bene nan.
     waje ta samu ta zauna gefen da Jalilerh ke zaune tace “my dear babu wanda zai maki dole,amma dai addinin musulunci shine addinin gsky dole zaki hqr da zamanmu a tare dake sabida zaki dinga ganin abubuwan da maki san dasu ba,ina fatan Jalilerh ta gane nufi na” ita sam ta kasa gane maganarsu amma tana ɗaukan ta amatsayin gsky,domin ta samu zuciyarta da kwadayin jin labarin addinin Musulunci,gefe guda kuma idan ta tuna birnin nufar da kuma Papa,da uwa SUNDU sai taji bata ƙaunar jin abinda suke faɗa,sabida ba zata iya da azabar da za’a gana mata domin tasan hukuncin da akewa dukkan wanda ya musulunta a birnin nasu,hawayen da take ƙoƙarin mayarwa ne suka samu damar sakkowa ta cikin idanunta,da sauri Aryan ya tsuguna a gabanta yace “ohhh beb why Are you cry? ki daina kinji ban son ganin hawayen” ya ƙare maganar yana share mata hawayen tare da miƙewa yace “Mameey yunwa na keji fa,bari na fito amma” dry tayi masa tace “babu abinda ka iya sai raki kamar kai kaɗai ne mai ciki,kasan dole sai kowa ya dawo gida sannan za’a ci abinci” dry yyi mata yana shigewa part ɗinsu yana faɗin “i knew” bayan shigewarsa Nihila tayi sallama Mameey ce kawai da amsa mata banda Jalilerh wacce bata san muhimmancin amsa sallamar ba,zama tayi tsakaninsu tace “washh Mameeyna na gaji rana yunwa,kai Mameey karatu aƙwai wahala wlh” ta ƙare maganar tana kama hannun Jalilerh tace “sister muje ciki ko” miƙewa Nihila tayi tace “Mameey ya gidan shuru wai?ina bobo,yaya Ara
yan,yaya,Irfan,yaya imran duk suna ina?”  miƙewa Mameey tayi ta nufi kitchen tana tafe tana faɗin “baby duk masa gidan fa” tana faɗin haka ta ƙarasa ciki ta samu Laure harta kammala girki,ta zuba komai cikin cular,itama part ɗinta ta koma domin yin wanka ta shirya kafin la’asar.
  Nihila na shiga ta kalli Jalilerh tace “ina fatan ki sauya pat ɗin jikinki,kuma kinyi wanka kin sauya kaya?” girgiza kai Jalilerh tayi alamar “a’a” da sauri Nihila tace “kan uba,wlh wari za kina yi idan baki gyara jikinki,baki san najasa bace?” turo baki Jalilerh tayi domin sai maganar Jalal ta faɗo mata inda yake cewa wari take,ita kuma ta ɗauki al’ƙawari bashi mamaki sai yasan ita ya gayawa,cikin shagwaɓa tace “to yaya zanyi?” ta ƙare maganar hawaye na sauka daga cikin idanunta,cikin bathroom Nihila ta shiga ta haɗa mata ruwa mai zafi tare da saka mata turaren wanka da kuma wani magani wanda Mummy ta bata,tana gamawa ta fito tace “ga ruwa can kije kiyi wanka kamar yadda na gaya maki,idan kin gama kiyi brush ki busar da wannan tulin sumar,da alama ke ko damunki ba tayi” ita dai bata ce mata komai ba ta shige cikin bathroom ɗin.
    A hankali yake dreving motar cikin ƙwarewa,duk da ya daɗe rabonsa da dreving amma hakan bai sa ya manta yadda ake ba,yadda yake murza kan motar a zafafe zaka tabbatar yana cikin damuwa,banda sakin numfashi da ajjiyar zuciya babu abinda yake,yaci ace yaje inda zashi amma ko rabin zuwa baiyi ba,sabida yadda yake tafiyar kamar bai son tafiyar,a haka ya samu ya ƙarasa inda ake saida manyan motoci Masu ƙyau da tsari, parking yyi tare da kifa kansa a kan abin dreving ɗin,so yake yaji sauƙin abinda ya keji a ransa da zuciyarsa,amma abin ƙara yawa yake tun yana jurewa har rauninsa so yake ya bai yana,banda ƙarfin addu’a,da tuni ƙwaƙwalwarsa ta jima da daina aiki,da tuni mutane sun daina ganin girmansa,da tuni mutane sun fara gudunsa,amma duk da hakan zuciyarsa na sashi son ya aikata abinda sam bai dace ba,a gefe ɗaya kuma babu abinda yake sha’awa ko kuma fata ace ya  cimma sai burin daya tasu dashi tun yana Shekara biyar,burine wanda yake ganin bashi daya kawo abin ba hatta mutanen da abin bai shafa ba zasu ji daɗin sa kuma za suyi alfahari dashi, tabbas dole ya aiwarta dashi koda zai zama tawaya a nasa bangaren,baka da wani sauran dama wannan itace damarka Jalal,lalurar dake damunsa ba zata hanashi ai watar da abinda yyi niya ba,a hankali ya ɗago firgitattun idanunsa da suka janye kaɗan sukai jaaa sabida zallar damuwar dake a ransa, lumshe idanunsa yyi kafin a hankali ya ɗauki gorar dake kusa dashi,ya ɓalle murfin gorar sai da ya shanye tass kana ya ajjiye gorar a gefe guda,a hankali yaji zuciyarsa nayi masa sanyi nutsuwa ta fara saukar masa,cikin ransa yake ƙara jaddada sunayen Allah a haka harya samu damuwar dake ransa a kaso 100,80 ta tafi,fitowa yyi daga motar tare da sanya hannayensa duk biyun a cikin aljihun rigarsa,cikin jarumta kuzari nutsuwa yake taka ƙafafunsa tamkar ba shine yake cikin damuwa ba,sosai haiba da kamala da ƙwarjini ya sauka a saman fuskarsa,a haka ya ƙarasa shiga wajan motocin ganin ƴan mata a wajan yasa ya haɗe ransa tamau,da sauri ma’aikatan wajan suka ƙarasu inda yake tsaye ya bashi kujera tare da tambayarsa wacce kalan mota ya keso,hannu yasa ya shafi sajen fuskarsa cikin wata daddaɗar murya mai daɗi yace “alrdy na zaɓa,nama tura kuɗin,kawai ina son a kawomin ita gida yau” ya ƙare maganar yana sauke ajjiyar zuciya sabida tsayin da maganar tayi masa,cikin girmamawa mutumin yace “ok are you Muhammad Jalal Kabeer bobo ko?” miƙewa tsaye yyi tare dayin gaba sabida ƴan matan da yaga sunyo wajan yana tafe yace “Yes i am”
   yana shigewa motar ƴan matan ma zuwa wajan, tsaki Hibba tayi tace “wlh Ikram kin cuceni,tun ɗazo nake son nazo wajan wannan guy ɗin amma kika ƙi rakoni yanzu kalli a sarar da kika jamin?” ta ƙare maganar kamar zatai kuka,cikin dryar mugunta Ikram tace “kee mene ya hanaki zuwa wajansa? dole sai na rakaki wai?” cikin damuwa Hibba tace “wlh ƙwarjini yyimin ko idanunsa na kasa kalla,wlh ina sonsa?” zare ido Ikram tayi cikin mmki tace “so kuma Hibba? kina cikin hankalinki kowa? daga ganin mutum sai faɗin kalmar so wlh wannan haukan ba da Ikram ba” hannun Ikram ta kama tace “wlh Ikram ina son shi,ha salima ban taɓa ganin mutum da yyimin kamarsa ba,yana da ƙyau sosai,yana da ilimi uwa uba kuɗi,jin kansa ya ƙara ruɗanu” zuwa yanzu kallon baki da hankali Ikram ta fara yiwa Hibba kafin tace wani abu Hibba ta kalli manager’n wajan tace “dan Allah ka taimakamin da address ɗin mutumin nan ko kuma number waya” har ya zura hannu a aljihunsa sai kuma ya ciro hannun yace “hajia bana da ko ɗaya daga cikin abinda kika tambaya” gdy tayi masa tare da jan hannun Ikram suka shiga Mota suka bar wajan,a ranta kuma tayi al’ƙawari dukkan inda ya shiga saita nemo sa in dai ya raye.
  3:30 dai-dai yyi parking a parking space,yana fitowa ko cikin gidan  bai shiga ba,ya nufi masjid kasan cewar yana da al’wala shiyasa bai ma tsaya yin wata al’walar ba,a masallacin ya samu Abbou da Aryan da Irfan da Imran,da kuma abokinsa Jafar,salla ya jasu ana idarwa yyiwa masu jiransa karatu tare dayin azkar, bayan ya fito kai tsaye ya shiga cikin gidan a danning table ya gansu zaune har da Jafar ba tare daya ƙara kallon su ba,ya juya zuwa part ɗinsu,jinjina kai Jafar yyi a ransa yana mamakin mislikanci Jalal, haka Jafar ya zauna a gidan har dare tsakaninsa da Jalal ya gansa a masallaci.
  washegari tun asuba bai koma bacci sabida a yau ya keson yaje neman abinda ya sanya ya fita ƙasar Paris karatu, 7 na safe ya shirya cikin wani farin boyal mai manyan zane,mara nauyi da kuma duhu,domin hatta singlet ɗin jikinsa ana gani,wata Black ɗin hula mai taushi ya ɗauka ya saka,sannan ya ɗauki Black half covert shoe ya saka,yana gamawa ya fesa turare,kana ya fito cikin nutsuwa tare da rufe side ɗinsa,a babban parlour ya samu Nihila ta fito da shirin makaranta, wajansa ta ƙarasa tace “good mrng bobo” kansa ya ɗaga aikam cikin Sa’a idanunsa ya faɗa cikin na Jalilerh wacce tayi tsaye tana kallonsa ta saman  bene,daman jikinsa ya basa kallonsa ake,kansa ya ɗauke yace “mrng too baby so ya school ɗin kina karatu dai ko?” washe baki tayi ta fara zuba masa surutu da sauri yasa lallausan tafin hannunsa ya rufe mata  baki a hankali kuma yace “talkative” a haka suka ƙarasa gaban dalleliyar motarsa wacce ake yyi yanzu,wacce ta kasance blue black, sosai Nihila ta fara santin motar domin tana bacci jiya aka kawo masa ita, mazaunin drever ya shiga yace ta shigo ya kaita,sosai taji daɗi yau ɗaya yayan nata zai fita da ita,har makarantar ya kaita kana ya juya ya nufi gidan Gwamnati,yana zuwa ana tashi daga zaman MAJALISTA, kai tsaye office da zai sa dashi da shugaban ilimi na ƙasar ibadan ga nufa,yana zuwa kai tsaye aka bashi damar shiga,kujera yaja ya zauna bayan ya zauna,yace “mrng sir” murmushi Mustapha yyi tare da faɗin “Muhammad Jalal Kabeeru bobo ɗalibai da yawa su amshi ofer ta aikinsu wasu ma a ranar da kuka dawo,kai kuma shuru daba ina da niyar kiranka domin kazo ka faɗi aikin da kakeso,kasan cewa kaine ɗalibin da yafi kowa samun result mai ƙyau,dan haka yanzu ka faɗi aikin da kakeso” murmushi gefen baki yyi a ransa yana mmkin mutanan  da idan suka fara mgn basa tsayawa, lumshe ido yyi kafin yaja numfashi cikin wata murya mai ƙwarjini yace “bana son aikinku,nine dai na keson baku nawa aikin…²¹,²²

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *