UNCLE NE CHAPTER 5 BY NIMCYLUV
Da yamma Lamir ya sauka gidan president Mubarak Yahya cibo,motoci ne sama da goma sukai parking a parking space,ga wasu securities wajan ashirin duk riƙe da guns,kowa ka gani fuska babu walwala,a haka aka buɗewa President Mubarak Yahya cibo,yana tafe wasu masu tsaronsa suka rufa masa baya,da sassarfa ya shige parlour’n da yake meeting mai muhimmanci wanda ba kowa yasan dashi ba,yana zuwa parlour’n wasu manyan mutane su biyar suka miƙe tsaye alamar
girmamawa,farin ciki fal fuskarsa ya kalli Lamir wanda ya ƙara girma shekarunsa suka jaa,sai dai yana nan fresh bawai ya tsofa bane, zama yyi akan wata lafiyayyiyar kujera a hankali kuma ya ɗauki coffee da aka ajjiyewa ko wannansu ya ɗan kurɓa kaɗan, Lamir ne yace “ur excellency sai naji kira daga sama,naji tsoro sbd tunda ka turani Istanbul domin kula da Company medicine ɗinka baka taɓa kirana ba,shiyasa wannan kiran ya ɗagamin hankali” Gwamna Faisal Lawan yace “ai Lamir abunda ba muyi tunanin zai faru damu ba shine yake shirin faruwa,babu wanda ya taɓa tsayawa takara shugaban ƙasa tun takarar da Khalil ya tsaya shima kafin zaɓe ya mutu,to yanzu an waye gari wani ɗan ƙaramin alhaki na neman tayar mana da hankali, tabbas idan mukai sanya za’a samu matsala” ya ƙare maganar yana kallon president Mubarak, miƙewa tsaye Lamir yyi ya Fara zagaye parlour’n kafin yace “duk wannan ba shine ba,bamu da matsala dashi idan duk sauran gwamnonin da muke dashi basu mara masa baya ba,kaga da zarar anyi zaɓen cikin gida bamu da wata matsala dashi,idan zaɓe yazo a nan zamu tara talakawan gari da matasa mu raba Musa ƴar shinkafa suger da ƴar dubu biyu haka,matasa kuma zamu basu ofer ta aiki amma ta ƙarya,sannan ƴan bangar siyasarmu zamu haɗasu da manyan drugs wacce zata har gitsa masu brain ɗinsu,kaga a nan zasu rage mana wani aikin ranar zaɓe sukaiwa ƴan kungiyar hamaiya farmaki,hakan zai saka magoya bayan jam’iyyar jin tsoro kowa yaƙi fitowa zaɓe sbd yana jin tsoron kada a kashesa ko a yanke sa, shine kawai” murmushi president yyi domin har yaji wani sanyi a ransa, Faisal Lwan shima ya mike tsaye yace “matsalar duk ba’a nan take ba,tashin hankalin da muke ciki a yanzu shine dukkan gwamnonin da muke dasu guda 39 sama da 30 suna bayan sabon ɗan takarar shugaban jam’iyyar D.R.P ɗin” cikin tashin hankali Lamir yace “wai waye wannan sabon ɗan takarar da yake wasa da rayuwarsa data danginsa?” ya ƙare maganar yana fesar da numfashi sai a lokacin President yace “his name is Muhammad Jalal Kabeer bobo” da saurin Lamir yace “what!!!?.
da wajan yamma akai parking da wata sabuwar mota black colour, wasu manyan securities ne majiya karfk sama da 20 suka zagaye motar kafin wani babba yazo ya buɗe murfin motar bayan motar, ajjiye jaridar hannunsa yyi ta daily truts kafin ya ɗauki farin glass ɗinsa ya manna a idanunsa,wayarsa dake gefensa tana ringing ya ɗauka tare da katse kiran ya zuro da fararan ƙafafunsa zuwa waje,cikin a zaba securities ɗin suka zagayeshi,yana sanye da wata light blue ɗin shaddar ɗinkin riga da wando da kuma babbar riga sai zabga ƙamshi yake,fuskarsa ta cika da haiba, kwarjini,annori da kuma cikar zati, wayoyin hannunsa aka amsa wani ya ajjiyesu wajansa,cikin nutsuwa ya fara tafiya har zuwa cikin gidan gonar tasa wacce yake jiyo ihun matasa da kuma ambatan sunansa da suke,yana zuwa aka ja masa kujera ya zauna,yana zama ya lumshe idanunsa kafin a hankali ya buɗesu ya sauke akan dubban matasan da suke wajan,wani daga cikin matasan yace “ALLAH ya taimaki Jalal bobo,ya ɗaukaka in sha Allah mulki kamar kayi ka gama ne, maƙiyan ka sai dai suji kunya,alfarmar Annabi da Kur’ani saika zama shugaban ƙasar ibadan saika kawo mana sauyin da muke fatan samu,sai ka kawo mana ƙarshen matsaloli mu,sai ka ingatan makarantun gwamnati,sai ka tantance mana ingantattun malamai da kuma likitoci,saika magance mana shigo da gurɓatattun magani cikin wannan ƙasar tamu saika magance mana (women trafficking *_Sabon littafi nan da bayan sallah_*) safarar matan da ake zuwa wata ƙasar da niyar aiki kuma sai anje aga ba haka bane,aita lalata mana yaranmu da iyayanmu in sha Allah kai ne garkuwarmu” gaba ɗaya suka haɗa bakin wajan faɗin “Ameen ina sha Allah”
Murmushin sa na gefe wanda yake ƙara masa ƙyau yyi kafin yaja kujerarsa baya kaɗan ya fara kallonsu ɗaya bayan ɗaya yace “Ma sha Allah, Allahamdulillah nagode ƙwarai da soyayyarku kuma ina addu’ar Ubangiji ya bani ikon sauke wannan nauyin da zai hau kaina” ya ƙare maganar yana sauke wani wahalallan numfashi sbd tsayin da maganar tayi masa, Jafar dake gefen sa ne yace.
“Munayi maku barka da zuwa,kuma muna fatan zuwanku ya zame mana alkairi,kuma muna fatan zaku mara mana baya har abada zaku jajirce akan abinda kukeso kada ku juya mana baya,ku zama masu ƙarfin guwwa da kuma tsayawa akan ra’ayinsu,sannan muna buƙatar mutum ɗaya a cikinku wanda zai zame maku jagora wanda kuka amince dashi,sannan munasu ku zaɓi mutane wanda zasu dinga yi mana campaign a social media da kuma muta nan da zasu dinga shiga gidan redio,t.v suna yaɗa manufarmu,dukkan wani taimako daza muyi maku zaku samesa ta hannun mutumin da kuka zaɓa matsayin jagorarku”
da wannan maganar suka gama taron,sannan suka zaɓi shugabansu mai suna Prince Hassan,gaba ɗaya matasan wajan sai murna suke suna ihun daɗi,lokaci guda ƙaunar Jalal bobo ta shiga zuƙatansu, Lamir bayan sun gama nasu meeting suka tsaida maganar da suke ganin za suyi amfani da ita wajan ruguje soyayyar da mutane sukewa Jalal bobo, a main parlour Jafar da Jalal suka samu Abbou da Dasu Mameey zaune sai kuma Lamir wanda yake zaune kusa da Mama an cika masa gabansa da kayan motsa baki, Lamir ne yace “wlcm son,kuma president to be” kallonsa Jalal yyi dan ganin inda maganar tasa ta dusa sai dai babu wata alamar da fuskar Lamir zata nuna baya cikin farin ciki, kansa ya ɗauke yace “wlcm uncle” Lamir yace “thanks sai na kejin abin arziƙi,ai nace zama bai kamani ba shine babu shiri na nemi ticket na dawo domin a fara shirin zaɓe dani” Abbou yace “Lamir amma naga kamar ba jam’iyyar kake ba,domin kowa ya sanka da President Mubarak Yahya cibo,shiyasa nake tunanin abun” murmushi Lamir yyi yace “haba Alhaji Kabeer ai gida yafi waje,tayaya zanyi adawa da jini na,dukkan abinda nake samu wajan President bazai kai alaƙar jini muhimmanci ba,dan haka muna nan zamu fafata” jinjina kai Abbou yyi cike da farin ciki kafin yace “kai abu yyi daɗi Allah ya taimake mu, Allah ya ƙara zumunci “gaba ɗaya suka amsa da “Ameen” murmushi kawai Lamir yake tare dacin abincin dake bagabansa,Jalal bai ƙara magana ba ya shige cikin part ɗinsa bayan yyi wanka ya sauya kaya zuwa na shan iska ya ƙarasa parlour’n ya ɗauki apple da maltina ya dawo saman sofa ya zauna, system yaja ya fara searching akan women trafficking ɗin da suka faɗa masa ɗazo da kuma drugs ɗin da ake shigowa dasu ba tare da Nafdac ta sani ba.
A can Birnin nufar Papa ne zaune gaban uwa sundu yana kirari tare da ɗura hannunsa a sama yana jujjuyawa tare dayin sama da ƙahon kansa,sai da ya shafe awa guda kafin wani abu ya fito daga hannun uwa sundu ya sauka a nasa hannun,da sauri ya duba hannunsa abinda ya gani ba ƙaramin tayar masa da hankali yyi ba, cikin tashin hankali ya kalli jinin sannan ya kalli uwa sundu yace “Me nai maki uwa sundu mene yasa ba zaki amshi addu’a ta ba? ko laifin jikanyata ya shafan? bana da hannu a gudunta sannan bansan inda take ba kamar yadda na faɗa maki,da nasan inda take nida kaina zan kawo maki ita ki yanke mata hukuncin daya dace da ita,domin ita kaɗai ce ta fara bijirewa umarnin ki a wannan birnin mai ciki da iko da kuma tsantsar al’ada” ya faɗa cikin harshansa na Jewish, wata ƙara uwa sundu tayi tare da fiddo da hannunta ta fisciko Papa gabanta kafin ta fara magana cikin wata iriyar murya tace “kayi babban kuskure daka bar wannan matar a cikin birninmu,babban kuskuren da kayi na barin jikanyarka data gudu, kuskure uku akai a wannan birnin wanda bazai taɓa gyaruwa ba,na farkon kai da kanka ka aikatasa,babban tashin hankalin dani uwa sundu na shiga yadda naga wani babban al’amari yana shirin tunkaro mu” zufar data yankowa Papa ce yasa yyi saurin miƙewa tsaye yace “yanzu uwa sundu mene mafita? wacce hanya za’a bi a gano inda jikanyata take sannan mu bada auranta ga Jushoa” wata dryar ta ƙarayi kafin tace “tana cikin wani hasken wanda indai ba barinsa tayi ba,baza mu taɓa samun galaba a kanta ba,duk yadda za’ai mu rabata da wannan hasken sai munyi,domin idan muka barta tabbas zata rushe mana wannan daular tsakanin ita ko hasken dole za muyiwa wani turan aljanu domin su shiga jikinsa su wargatsa masa dukkan wani shirinsa,zai kasance wannan aljanun shune zai taimaka mana wajan ganin ta dawo birnin nufar..
bayan Papa da uwa sundu suka gama tattaunawa ya fice da sauri zuwa can fadarsa inda ake zaman jiransa,yana zuwa ya samu dubban mutanan da sukai na sarar karɓar budurcin wacce tayi masu,wasu kuma sukace gsky bata da daɗin mu’amala,bata da ni’ima sannan tana da raki dan haka zasu jira wata shekarar kafin nan wasu matan sun ƙara tasuwa, Jabir yana zaune ya haɗa kansa da quiwa yana kallon yadda Katarina ke kokawa da Zulfa wacce taƙi zama sai kukan kuraye take tana nunawa Jabir teddy hannunta,bawai yana fahimtar abinda take faɗa bane,amma a tasa fahimtar yana ganin kamar wani abunne ya samu teddyn hannun nata, miƙewa yyi jiki a sanyaye ya ƙarasa inda suke tsaye tare da kallon Katarina yace “matsa gefe muga” kallonsa tayi tace “amma jikin Ummi na ban tsoro kalli abinda take?” hannu yasa ya kama hannun Zulfa da sauri ya janye sbd cizon data sakar masa a hannunsa,wata tsayawa ya daka mata kafin a hankali ya fara tofa mata addu’a yana daga tsaye,idanunta ne suka fara rufewa jikinta ya saki gaba ɗaya sai wani hayaƙi daya fara fita ta hancinsa,ganin tana shirin faɗuwa yyi saurin matsowa ta faɗa jikinsa, rungome ta yyi sosai,yana shafa kanta sai a lokacin wasu hawayen tausayinta suka fara sakko masa daga cikin idanunsa gaba ɗaya jikin nata ya rikice a ƴan kwanakin nan,gashi Papa ya hanashi barin birnin bare yaje wajan malam ya amsar mata maganin.
Jalal na zaune yana operating system turo ƙofar parlour’n sa akai a hankali ya ɗaga idanunsa yaga Mummy ce, murmushi yyi yace “wlcm Mom” shuru tayi kafin tace “me kake yanzu bobo?” ba tare daya kalleta ba yace “ina bincike ne akan wani abu Mom”shuru tayi masa tana kallon sai da yaji shurun yyi yawa yace “ya dai?” numfashi ta sauke tace “Jalilerh babu lfy wajan ƙwana biyu,baka tambayeta ba sannan nima ban gaya maka ba,kuma ita ba fitowa parlour take ba,amma ciwon nata ya tsananta” yana kallon system ɗin yace “to akaita asibiti mana” kafin Mummy tayi magana Nihila ta shigo da gudu tana haki tace “Mummy Ja…Ja.. Jalilerh c…,” bai jira yaji abinda za tace ba ya fice da sauri ya nufi part ɗinsu a hanya sukaci karo da Aryan wanda ya taho da gudu gaba ɗaya sukayi cikin ɗakin..