UNCLE NE CHAPTER 6 BY NIMCYLUV
Gaba ɗaya parlour’n suka zabura tsaye sbd jin abinda Jalilerh ke faɗa,wani gumine ya yankowa Aryan kafin ya juya ya kalli Jalal dake jingine jikin bango idanunsa lumshe, ajjiyar zcya ya sauke kafin ya fice daga cikin gidan, Jalilerh dake jikin t.v ta ɗura da faɗin i hate him I don’t want see him in my life ever,he betraying me” ta ƙare mgnar tana sakin kuka, Abbou zubewa yyi akan kujera hannunsa
dafe da kansa dake kuya masa, Mummy kuka ta sanya tana faɗin “wlh wannan maƙiyya ne wanda basa ƙaunar ci gaban ka,nasan baza ka taɓa aikata wannan sauƙon Ubangiji ba, dukkan wanda yake neman ka da sharri da izinin Allah sai dai ya gani a kansa,daman abinda nake jiye maka kenan,wlh bana ƙaunar wannan siyasar taka,yanzu duniya da kuma mutanan gari wanne irin kallo za suyi maka? Allah dukkan wanda yace tukunyar wani ba zata ta fasa tasa ko zafi ba zatai ba,duk sharrin mutum sai dai ya gani a kansa amma alfarma Annabi da Kur’ani babu abinda zai sameka” ta faɗa tana zubewa ƙasa tare sakin wani sabon kukan, Mameey dake tsaye kamar butum butumi ta share hawayen dake cikin idanunta tace “yaya akai Jalilerh ta fita shine Abin tunani tabbas aƙwai wani abu a ƙasa,dukkan wani zai ɗauki Jalilerh sai wanda ya san kan gidan kuma…,” Kafin ta ƙarasa Lamir ya shigo da sauri tare da kallon bobo yace “yanzu ina cikin driving zani gida nake jin wata magana a redio,ban tabbatar ba sai da aka kirani nace ban yarda ba,daga ƙarshe na kunna data naga abun nata yawo a media hadda photon Jalal a ciki,innalillahi wa’inna ilaihir raji’un wacce irin masifa ce wannan” Mama dake gefe tayi sauri faɗin “kul ka ƙara faɗin masifa a nan,duk wanda yyi haka sai wanda bakin uwa ke binsa,ohhhh wannan duniya za maninmu babu ruwan wani da wani amma yanzu wlh ko kashi kake ka ga mutum zauna akan abinda,yanzu za kaji ana wacce tayi kashi mai tauri,huuuuu ai sai da nace kayi aure kaƙi da duk hakan bai faro ba,ahhh to babu ruwana ba dai ina faɗin abu kuna ganin kamar banda hankali ba” kallonta Mummy tayi tace “haba Mama wannan duk ba abin Suratu bane,neman mafita shine abinyi” tace “sannu uwata ahhh nace sannu Zulai,jika na ne dukkan abinda ya samesa ya saman yooo mai fimini komai a kanki ba” Lamir yace “yanzu mu fara tunanin inda yarinyar dake kafin wani abu ya biyo baya” kallonsa kawai Jalal yayi kafin ya juya yyi shigewarsa part ɗinsa.
Shuru parlour’n ya ɗauka aka rasa mai faɗin wani abu kowa da abinda ke damunsa a zcy, Jalal na shiga parlour’n sa ya fara zirga zirga yaje ya dawo tamkar wani zautacce,a haka Jafar ya turo ƙofa ya samesa,kallonsa yayi cike da tausayin halin da yake ciki,a zahiri idan ka kalli Jalal zaka ɗauka babu damuwa a tare dashi,zaka ɗauka dukkan abinda ake tamkar ba akansa ake ba,dan ko ajikinsa ko fuskarsa taƙi nuna damuwar da yake ciki,amma cikin zcyarsa wani zafi da ƙona ya keji yana jin duniyar na sara masa,gaba ɗaya wani duhu-duhu yake gani a cikin idanunsa ga yadda ƙirjinsa ke bugawa da ƙarfi tamkar zcyarsa zata fasa ƙirjin ta fito,maƙogaransa wani ɗaci yane ya gauraye cikinsa,abinda yake tunani wane yyi masa haka? Wane yyi masa muguwar tsanar da harya zaɓi ya tuzar tashi,tuzarzi mai muni irin haka,mene aka zaɓi ayi amfani da rauninsa wajan cutar da rayuwarsa?,mene yasa magautansa suka zaɓi wannan hanyar akan su ɗauki wata? Ko da wasa ko a mafarki mai taɓa tunanin rayuwar aure ba,bare kuma har yayi tunanin aikata wata aba wai zina,runtsa idanunsa yyi da ƙarfi kafin ya fesar da wata iska mai zafi ta cikin bakinsa, mene yasa zai aikata haka gare ta,yarinyar da take masa kallon uba ko wani jigo nata,tayayama zai aikata hakan bayan yasan tarin ayoyi da hadisan da sukai bayani akan wanda ya akaita zina da auren ko bashi dashi,me yasa suke tunanin wannan abinda sukai zai tauyesa,ko kuma zai sanya tsoro cikin zcyarsa har ya janye abinda yake mafarkinsa tabbas sunyi kuskure, kuskure mai girman gaske domin basu san wanene Muhammad Jalal bobo duk yadda suke tunanin daƙoshe bai taɓa damunsa ba,yana sane da dukkan abinda yake faruwa a harkar siyyasar,amma dole ya sauya damunsa dole yasan wanda ya ɗauke Jalilerh.
Jafar ne ya kallesa kafin yace “Jalal wannan shurun naka a yanzu mazai tasiri ba,nasan kana da hankali tunani ilimi addini kowa yasan kana da wannan,domin ni a karan kaina nasa gane da iliminka na addini dana bature wanne yafi a wajanka,nayi imani da Allah dukkan wanda yasan ka bazai taɓa yarda da wannan ƙazafin da akai maka ba,kada ka damu kanta domin nasan yadda kai shurun nan Allah kaɗai yasan abinda ka keji a cikin zcyarta domin duk yadda wani yakai yaji baƙin ciki ba kamar kai ba, You have to control ur self,wannan selfishness da mai yyi kama” ya faɗa yana dailing wata number a wayarsa.
Tunda ya fara magana Jalal bai ɗago kansa ba,ya hasali ma shi kaɗai yake surutansa,dan “a” na cikin maganar Jafar babu wacce yaji bare ya fahimci abinda yake faɗa, abubuwan da zcyarsa suke faɗa masa daban da wanda yake son aikatawa,me zaibi a yanzu kansa zaibi ko son zcyarsa,ina kuma zai nemu Jalery shine abinda yafi tsaya masa a rai,ina take?wanne hali take ciki? Me suka aikata mata da har ta faɗi wannan maganar lallai sunyi pursing nata ne,duk da yasan ba komai take ganewa ba bare harta fahimta,amma dole zata fahimci wanna kalmar ta rape data ambata,fesar numfashi ya karayi kafin ya sanya hannu cikin tulin sumar kansa ya fara hargitsa ta,a hankali kuma yaja cikinsa zuwa wajan fridge ya ɗauki bottle water ya ɓalle murfinta tare da kafawa a bakinsa sai da ya shanye tass kana ya yar da emty robar a ɗan zafafe ya fara tafiya harya shige cikin bedroom ɗinsa ya saka key ya kulle kansa.
Da idanu kawai Jafar ya bisa,kafin idanunsa ya sauka akan wayarsa da yake amfani da ita a gida,kamar yyi tunani hakan ta kasance,da sauri ya shiga xender ya tura photonan Jalal da Jalilerh wanda sukai a tare,wasu ita ta ɗauka wasu kuma tana zaune aka ɗauke su,wasu kuma shi ya ɗauka idan abun nata ya mutsa tana rigima,wanda sukafi kyau ya tura kafin ya miƙe tsaye tare da ficewa daga cikin part ɗin.
A parlour ya samu Abbou da Alhaji Kamal da Mummy da Mameey Mama nacan rakuɓe zai baza idanu take,jin wajan yyi shuru yasa ya kalli Abbou yace “Abbou Aryan, Imran, Irfan suna ina?” Abbou kasa cewa komai yyi sai Mameey da tace “Aryan tun ɗazo ya cewa har yanzu bai dawo ba, Imran Irfan kuma suma basu jima da fita ba” kai ya jinjina yace “ok tom Allah dai ya kiyaye gaba” sai lokacin Mummy tace “Jalal fa?’
Cikin sigar tausayi yace “Mummy Jalal tunda na fara magana babu abinda ya cemin da alama ba kamar baya fahimtar abinda nake faɗa masa,yanzu haka ya shige bedroom ya kulle kasa ciki” kuka Mummy tasa tace “kaga abinda nake tsoro ba,wannan shurun na bobo cutarsa dashi zaiyi,nasan bai iya ɓacin rai ba tun yana ƙarami yanzu Allah kaɗai yasan abinda zaiwa kansa,zan iya jure komai amma ba zan cure ganinsa a haka ba,bazan jure wani abu ya samesa ba” kallonta suke kawai cike da tausayi domin yadda ta keson Jalal ko Nihila bata samu wannan ƙaunar ba, Jafar ne yace “Abbou zan je in sha Allah komai zanyi dai-dai” yana faɗin hakan ya fice daga cikin gidan ga baki ɗaya.
Yana fita Alhaji Kamal yace “yanzu haka maganar da nake maka Nusaibat banda kuka babu abinda take,bansan me zan mata ba,na sani ko wajan Muhammad tazo ba zata zamu abinda take nema wajansa ba,sai yanzu nake far gaɓar abinda mukai” juyawa Abbou yyi ganin har yanzu Mummy kuka take Mameey kuma na zaune ta zabga tagumi, Allah ya sani yadda ta ɗauki Jalal da muhimmanci haka ta ɗauki rayanta,kawai tana ɗauke kai ne sbd Jamal ta fita ƙarfi a wajan Jalal,ita jikinsa ce dole take kallon wani abun da ido yace “kuje ciki” miƙewa sukai Mameey tayi part ɗinta Mummy kuma ta nufi part ɗin Jalal yace “ki barsa kada kije wajansa yanzu” jin hakan yasa ta nufi part ɗinta, Mama ma da bin bango ta shige nata part ɗin, kallon Alhaji Kamala yyi yace “inaga wannan maganar ba wacce zamuyi yanzu bace, kaje ka rarrashi Nusaibat komai zai yi daidai in sha Allah” da Ameen Alhaji Kamala ya amsa kafin ya miƙe ya nufi fita waje,shima abbou part ɗin Mummy ya nufa yana zuwa ya sameta zaune tana kuka,tana ganinsa ta miƙe da saurin ta nufi wajansa tare da faɗawa jikinsa ta saki sabon kuka,bayan ya bubbuga kafin ya jata zuwa saman sofar parlour’nta yace “babu wanda zai ce kullum zaiji daɗin rayuwa babu lokacin da baza’a jarabcesa ba,munsan dole Jalal ya samu magauta da kuma maƙiya,amma abin tunanin yadda aka rasa dawa za’ai amfani wajan cutar dashi sai da Jalilerh yarinyar daba komai take fahimta bare ta gane,kuma a wannan rayuwar ba maƙiyi ne abin tsoro ba..,” kallonsa Mummy kafin yace “eh tabbas masoyin da zai nuna maka zallar ƙauna bayan a zcyrsa ba haka bane,duk abinda ya samu da Jalal zamu barshi matsayin ƙaddara wacce a kullum tana iya samun ɗan adam,abin farin ciki itama ƙaddarar tana da nata lokacin hawai dauwama dake a tare da mutum ba,kenan kinga akwai ranar da zamu bada labarin ita wannan ƙaddarar ranar data zama tarihi garemu baki ɗaya” da wannan na sihar ya rarrashi Mummy kafin ya ɗauki key din motarsa shima habar gidan.
Jalal na shiga part ɗinsa ya nufi bathroom ya sakarwa kansa shower lumshe idanunsa tare saka hannunsa a saitin zcyarsa dake breathing vrt fast,a hankali kuma gargasar jikinsa ta fara mimmiƙe wa,kafin jijiyoyin kansa suyi faɗa raɗa a saman goshinsa,a hankali yanayin jikinsa ya fara sauyawa jikinsa ya ɗauki rawa idanunsa sukai jaaa har wani ruwa-ruwa suke,ga yadda ya hargitsa gashin kansa,a hankali maganar ta ta ƙara dawo masa “he raped me I hate him” wani ihu yyi wanda ya cika gida baki ɗaya tare dasa hannunsa ya daki madubin mirror’n dake cikin bathroom ɗin nan take ya farfashe jini ya fara bin hannunsa.
Da sauri Mummy da Mameey suka fito daga part ɗinsu tare da nufar part Jalal da gudu,kai tsaye bathroom ɗin sa suka nufa,tsaye sukai bakin bathroom ɗin aka rasa wanda zai magana, Mummy da haryanzu kukanta bai tsaya ba tace “idan kace cutar da kanka zakai tabbas kamar ka cutar dani ce,abinda zakaiwa kanka zafi baƙan tamin akan abinda akai maka a yanzu,dan Allah Jalal ka fito kada ka cutar da ranka abinda kai ka san cewa ba gsky bane” Mameey ta ɗura da faɗin “duk abinda za kaji a cikin zcyarka muma munajin makamancin sa domin bazance munajin kamar naka ba,amma komai a hankali ake binsa,yadda ka ɗauki abu a haka zai zo maka,amma da ciwo yarinyar daka riƙe ta a maka sharri da ita,a yanzu halin da Jalilerh take ciki shine abin tunani,kasan cewa a yanzu daman fushin naka suke buƙata shi ya sanya sukai maka haka,kayi faɗa da zcyarka ka fito ka yaƙi maƙiyanka yanzu lokacin ka ne,damar kace tayi abinda kake so domin duk wannan abinda ake hukumar zaɓe inec bata duba wannan ba,yanzu aka sanar an tabbatar da kai a ɗan takarar governor IBADAN.