UWAR GIDAN BAHAUSHE CHAPTER 16 BY SHATU

UWAR GIDAN BAHAUSHE CHAPTER 16 BY SHATU

To meye matsalar ki da abinda ta Haifa, you can’t just be angry saboda ta haihu. Kema haihuwar nan ai kin uita ko?”+

Farida ta fada ma Kubra Bayan zuwa da tayi ta sameta ba yadda take, fadila tayi tsaki tace

” Namiji fa ta Haifa!..”

” Se meye Dan ta haifi namiji, Yaya gaba daya daya suke, me albarka kawai kake nema, maza nawa ake Haifa Suka kasa jin Kan iyayensu? Se Mata din. Allah Yaya kada ki bari haka ya shiga kanki, meye a haihuwar namijin me”

Ita dai Kubra kuka kawai takeyi, ba haihuwar namijin kadai ke Bata Mata Rai ba, a’a fact that Yan uwanshi idan ta haihu wasu se suyi kwana biyu Basu zo ba Amma Ina haihuwa dukka sun tattaro sunzo a ranar a Kuma nan Suka wuni, Mama Bata taba zuwa Dan ta haihu ba sede su bita Kano da babyn Amma karewa sati daya zuwa haihuwata tazo. Tunda na dawo a asibiti da tazo ta gaida mu Bata ma dauki babyn ba seda Adda Nanah tace Mata Bata dauka babyn ba sannan ta dawo ta dauka.

Dangin miji suna canjawa tabbas, Amma kada mu manta dukkan mu dangin miji ne, ba kowanne lokaci suke rashin gaskiya ba, shi mutum Yana kula Wanda yake Yi dashi ne. Nima kaina inada cikin dangin miji Amma yadda Suka karbeni se na watsar da makamai na na rungume su Nima, ni bazan hada Kai dasu mu cuci wata ba hakan Dan wata bazan fasa musu abinda ya kamata nayi ba.

A ranar aka sallame mu, da daddare Sega Baffa da Mama sunzo, Ina zaune a parlor hannuna rike da baby Mama na fama Dani akan feeding din shi, ita ta kasa gane kunyar ta nakeji shiyasa naki sakin jiki na bashi ya Sha sosae, se Anty yusra ce ta Mata signal se tayi murmushi ta shiga daki nan na ware na bashi. Albi ya fara shigowa da Mama yace min Baffa zai shigo, Mama muka gaisa da ita ta karbe shi tana ta Masa baa Khadija na Rama Masa ni Kuma Ina ta dariya. Ni na Kira Mama tazo suka gaisa da juna sannan Baffa ya shigo, sun kusa second talatin shida Maman Kano suna kallon kallo kafin tace masa ya zauna, ya zauna Yana ce Mata kwana da yawa, suka gaisa sannan nazo na tsugunna na gaishe shi ya karba Babyn Yana min sannu, Afaf dake zaune nace taje ta Kira Maman ta. Bata Jima ba tazo ta gaida Baffa sannan Mama ta fice. Kwanaki suka ja yaro yaci sunan Baffa Aminu nace ace Masa Abhi kawai tunda ni duk sunan da aka fada a familyn mu Muna da daya ko biyu. Mama ta kula Dani yadda bakwa zato, ko uwata data haifeni karshe abinda zatamin kenan. Rayha dasu Anisah da Anty Safara’u tun ana gobe suna suka zo, Sosae aka zo  ranar suna har Wanda banyi expecting ba, su Hanifa su Ramla, in fact a gidan su Baba Ummaah ce kawai Bata zo ba anan nake jin Wai ta zame daga bene ta fado anma tafi da ita Germany shekaran jiya, yadda Hanifa ke fada min kamar spine dinta ya samu matsala, na runtse idanuna Ina ayyana yadda kowa karshen shi ke zuwa, ya kamata mu lura duniya ba matabbata bace. Haka dangin Ammi ma sun Mata Kara sosae.

Kwana goma inata zuba Ido naga Ammi Amma shiru ranar na shiga daki nasha kuka na, Albi ya shigo ya sameni zaune akan stool na kifa kaina akan dressing mirror Ina kuka, Abhi na bayana a goye Dan Mama tace na dinga Goya shi yadda zai Saba da goyo. Dago kaina yayi da damuwa a fuskar shi yace

” What’s it? Me ya faru?”

Na share hawayena Ina jijjiga Abhi dake mutsu mutsu a bayana nace

” Kuma Ammi har yanzun bata xo ba fa”

Ya sauke ajiyar zuciya ya zauna tareda riko hannuna yace

” Is that the reason for this tears? Zan kirata nace Mata tazo kinji?”

Na gyada Kai, yayimin murmushi Nima na mayar masa, yasa na wanke fuskata. Washegari Sega Ammi da Baba, wannan ne Karan ta na farko data zuwa, kamar bakina zai fita saboda murna. Ta dauki Abhi tace

” Kama yake dake ai”

Usman dake gefe yace a

” Ai kamar Baba ya haifeshi”

Kuma hakane da Baba yake Kama sosae. Seda nayi kwana talatin sannan na tafi Gumel nayi sati biyu nayi sati daya a kano na dawo.

A Germany, Ummaah an karbe ta sede duk yadda suka so taimaka Mata already an samu matsala da spine dinta, ba zata Kara iya tafiya ba zata karasa rayuwar ta akan wheel  chair haka Kuma sede ta dawamma da robar fitsari a jikin ta, Abu na karshe ba zata Kara controlling yadda Bayan gida zai fita daga jikinta ba, sede kawai ya fita da kanshi. Ismail ya Jima a zaune ya kasa mikewa saboda yadda yake jin kanshi na Sara masa tamkar zai fita, Wambai ya dafa kafadar shi yace

” Kayi hakuri! Tashi muje”

Mikewa yayi Amma ko uffan Bai ce ba Suka nufi dakin da aka kwantar da Ummaah bayan an fito daga aikin. Tana kwance har lokacin Bata farfado ba,hannunta Ismail ya kamo tareda daura fuskar shi kan hannun Sega hawaye ya fara disa. Wambai ya runtse idanun shi ya dafa Ismail Yana patting bayan shi alamun rarrashi. Zuciyar Shi ta karye Bai kawo hakan ba dukda dama sun ce musu chances din ayi recovering spine dinta 10% ne. To Bai kawo after aikin ma haka ce zata kasance ba.

Ummaah Bata farfado ba se washegari, Ramla na zaune gefen ta se Ismail a gefe shi Kuma Wambai da babbar yarta Yaya Asiya sunje gurin doctor. Muryar ta a hankali ta Kira sunan Ismail, Ramla tayi saurin dubanta tace

” Yaya Ummaah ta tashi!”

Cikin sauri Ismail ya taso yazo ya rike hannun Ummaah Yana jera Mata sannu. Dukkansu Suka taru kanta suna kuka Bayan an sanar da ita halin da zata karasa rayuwar ta a ciki.Hannuna na tsame daga cikin kayan Dana wanke ma Abhi jin Kiran da Albi ke min. Parlon na shigo ta kitchen na sameshi zaune fuskar shi a murtuke. Na zauna daga Dan nesa dashi yanayina ya canja, zaman da nayi ma tamkar Ina tsoron Zama haka na Dan dosana jikina nace+

” Albi lafiya?”

” Wai ni dake waye babba a gidannan?”

Cikin rashin fahimta nace

” Kamar yaya, wacce irin magana ce Albi kake Yi”

Runtse idanun shi yayi sannan ya daka min tsawa

” Just shut up! Gidana was peaceful kafin kizo Amma tunda Kika zo na kasa samun nustiwa, kullum Kuna cikin fada…”2

Mmamaki kamar zai dauke ni a gurin da nake zaune, na kalle shi to be sure cewar daga bakin shi maganganun Suka fito.

” Na gaji da wannan abubuwan, kullum Rana Ina cikin raba fada kamar ni daya nake da Mata biyu a duniya. Look, I’m not tolerating this kece karama you have to compromise!”

A hankali na Mike bance Masa komai ba na koma kitchen na fita baya na karasa shanya sannan na dawo kitchen na tsaya jikin island din Ina shafa gurin, gaba daya kaina ya kulle na kasa tantance me yake faruwa. Nidai nasan Muna Wasa da dariya ya fita, nace zanyi wanki but what happened precisely shi ne abinda na kasa ayyanawa. Na furzar da iska Ina jin yadda Raina yake Kara baci with each passing second,ni nasan banyi ma Kubra komai ba, itama Kuma haka, Dan tunda na dawo daga Kano na koma aiki Abhi yanzun watan shi hudu, kamar yadda bana fita tunda haka yanzun ma bana fita, but what happened shi ne abinda na kasa sani. Kukan Abhi yasa na fita a kitchen din na sameshi ya tashi Kuma ya kasa Zama saboda tugging dinsa da nayi, dauki shi nayi Ina kallon shi muka hada Ido ya bangale Baki ya fara min dariya, se kawai naji zuciyata tayi sa
nyi na samu na zaunar dadhi inata Masa Wasa se yadan dauke min hankali, tabbas da Rahma ne and I feel I’ve a reason to continue living.

Bai Kara dawowa ba se yamma Bayan laasar Ina zaune a parlor hannuna dauke da wayata Ina chatting da Rayha tana fada min bikin Naeeyla da ya taho. Seda na amsa sallamar sannan ya shigo, na kalleshi briefly for like 30seconds sannan na dauke kaina tareda aje wayar, na Mike zuwa kitchen. Har lokacin muryar shi da ihun da ya dinga min echo suke min cikin kunnuwa na, Ian jin tamkar a lokacin yake fada min cewar ni ce silar lalacewar gidn shi. Na bude bkina Ina hura iska hawayen da yake kokarin taruwa ya koma, na dauka tray din Dana jera Masa abinci na nufi parlor, Yana zaune yayi shiru deep in thought, Abhi na aje cikin seater din shi nasa Masa lullaby yana swinging din shi, yayi shiru like the good boy he always is, da sucker bakin shi. Table na janyo na aje tray din sannan na dubeshi nace

” Yanzun zaka ci abincin?”

Kanshi ya gyada min nayi serving dinsa sannan na wuce daki. Na shiga toilet na saki kuka a hankali, I’ve hold on too much, wani lokacin Ina jin inama hannun agogo zai juya may be I wouldn’t have chosen Usman, may be Dana Kira wani yazo na aureshi,Kai na na girgiza Ina jera istigfar ganin Ina Neman kauce Hanya, na sani aure Yana da dadi, mutane na ganin shi kamar is an imprisonment, to me it’s a total freedom, Amma a cikin shi akwai abubuwan Dana riska Dani baa fada min hakan suke ba. Komai na tafiya yadda ya kamata Amma lokaci daya Usman zai birkice ko Abu nace ayi bazai Yi ba se har idan bukatar tayi daidai da Kubra shi ne zai hada yamana, I remembered telling him bulb din toilet ya dauke, na corridor toilet idan na kunna se yana spark ta socket. Dole se de na kashe, tun kafin na dawo daga arbain din Abhi nake Masa complain Amma har na dawo baa gyara ba, se kawai na kyale shi. Naje aiki na dawo da daddare ya shigo Yana fada min surprise Baby, ya kunna bulbs din duka Suka kawo, naji dadi sosae nace Masa nagode se yace ai jiya bulb din Kubra na kitchen yayi bindiga shi ne yau tayi complain ya hada Dani da nayi wata da watanni Ina haska fitila idan zanyi amfani da toilet, Kuma wannan ba shi ne Karo na farko ba, ko Kuma se na saya Abu na Masa kwalliyya se yace ga kudi a siya ma Kubra. Wannan abin ya Bata min Rai yadda bakwa tunani I felt kamar na fasa kwan haka naji. Ban mishi magana ba kullum Ina bashi lokaci zai canja but abinda yayi min yau ya kaini bango.

Abin mamaki Bai Kara zancen ba se ya dauki fushi kamar yadda Nima na dauka, har ya bar dakina ya koma nata yayi kwana biyu da safe zai leko ya ga yadda muke bazai Kara shigowa ba se dare da pyjamas dinaa ta bacci, saboda tunani se na rame ga yadda Abhi ke sucking Dole na Masa introducing solids ya fara saboda yadda yake zukeni se Rama nake. Ranar da zai dawo dakina na gyara ko Ina kamar yadda na Saba, na Masa egusi da pounded yam. Nayi kunun aya aikuwa na gaji likis. Ina zaune se na fara tuna possible abinda Kubra zata fada Masa nayi Mata yasa ya Zama flustered haka. Ranar Khadija tazo da saurayin ta Wanda aka saka musu Rana yazo min barka saboda Baya lokacin Bai Jima da dawowa ba. Nayi order snacks na tarbar shi har Albi nace min wai shi tunda yake zuwa zance ban taba eh snacks ba, na dinga dariya nace da sau nawa ne ya taba zuwa zancen. Se yace abar maganar. Kafin suzo ya fita, ya kawo kayan barka sannan zasu tafi nace su leka part dinta. Basu Jima ba Naga Khadija ta fito ranta a bace, ban tambayeta me ya faru ba hakan itama Bata fada min ba mukai sallama suka tafi.

What happened then? Na dakko wayata nayi dialing number dinta ta dauka tana min kirarin data saba, nayi dariya na e

” Amarya ranar da Kika zo da kukaje part din Maman Afaf what happened there?”

Tayi tsaki tace

” Na manta ban fada Miki ba fa, kawai Muna Shiga ta dinga Bata Rai Wai ai tun dazun ta San munxo mukaii zuwa inda take, nace Mata dama ba gurinta muka zo ba ai, gurinki muka zo. Shikenan fa se tace wai dake damu ba zamu cireta matsayin matar Hamma ba, duk abinmu. A gaban shi fa Amaryar Hamma take fadar hakan, se ya fita ni Kuma bakina bazai shiru ba na gaggaya Mata magana na fitowa ta. Bata da Kai wallahi”

Na gyada Kai kilan tace Masa ni nasa Khadija tayi hakan. Na Bata hakuri mukai sallama, na dafe kaina nayi shiru. Tun karfe shida ya shigo Amma ko inda nake Bai leko ba se ya tafi can, har bayan sallar Isha Yana can wajen Tara na Gama kunsar bakin ciki saboda ya riga ya nuna Mata we’re in bad times dashi, na Gama Shirin bacci nayi rocking Dana har yayi bacci. Na kulle kofar parlon na bar key jiki yadda nasan shima bazai iya shigowa ba, Ashe kofr Baya a bude take. Wajen 10pm se naji motsin shi a gefe na, har lokacin banyi bacci ba in fact ji nayke kamar na fito da zuciyata na wullar ko Zan huta da zafin da take min.

Wutar dakin ya kunna ya tsaya Yana karemin kallo na wani lokaci kafin ya hayo gadon ya kwanta Bayan ya kashe Kwan. Hannunshi yasa ya zagayo kuguna dashi, dayan Kuma yasa cikin rigata, ya sani it’s something that weakens my soul and body, ya riga yasan Lago ne, ganin zai fara min wasu abubuwa yasa nasa hannuna na buge nashi. Cak ya tsaya tareda fadin+

” Bakiyi bacci ba?”

Ya tambaya da mamaki a muryar shi, Wata zuciyar na fada min nayi hakuri kar nayi magana na nusa Masa bacci nake  Amma na kasa hakan saboda Gani nake zuciyata bugawa zatayi na mutu kafin safe, Abhi is what will make me live, na tashi na zauna tareda daukar wayata na kunna fitilar Dan ya ganni na ganshi ayi wadda zaayi.

” What happened to your face? You cried?”

Ya tambaya saboda yadda idona ya kumbura fuskata tayi ja, haka fuskata take ko tashin hankali kwakwara ba shiga se tayi ja.  hannunshi ya Kai Yana kokarin caressing fuskar na dauke kaina se hannunya sauka a kasa. Kawai se na fara kuka nace

” Na Bata maka gidan ka, tunda nazo ka rasa zaman lafiya! Amma Ina son ka tuna ni bani na dinga binka ka aureni ba, Kai ka dinga Bina kana son ka aureni…”

Hannun shi yasa a bakina Dan nayi shiru saboda muryata ta fara sama alamar Raina yakai kololuwar baci, cizon hannun nayi yayi saurin daukewa Yana yarfe hannun, alamar na ciza da yawa. Na cigaba da fadin

” Na fada maka matar daka aura shekara dari da wadda ka aura kwana daya hakkinsu daya, me kake nufi dani, zaka nunawa kishiyata bamu zaman lafiya, whatever you will do muyi shi ni dakai stop involving her, lemme tell you this duk abinda kake min Allah Yana kallonka and at this rate nayi Dana sanin aurenka!Kuma idan Kun hada Kai Kun zalunce ni Allah ya Isa tsakanina da ku.”

Ina Gama fadar hakan na dira a gadon na dauki Dana da wayata na barshi a zaune tamkar mutum mutumi, he always says I’m stubborn I’m sure Bai taba tunanin haka ba Dan ko ni ban taba tunanin zai iya min hakan ba. Ina kwantar da Abhi ana dauke wuta, gashi dakin shi ne kawai Babu sauro a part Dina. Nayi shiru Ina tuna fadan da aka min da zaa kawoni, cewar no matter what kada mu raba daki, kada Naga daki uku gareji, Amma yau bazan iya ba, bazan iya kwana dashi ba balle har ya taba ni. Nayi kamar na koma dakin saboda tsiron kada sauro ya ciza Abhi Amma na hakura, Hawaye wani na bin wani na nufi dakina na dakko net dinsa na Masa shimfida nasa shi ciki ni Kuma na zauna tareda saka kaina cikin gwiwata na dinga kuka, saboda inajin shi kadai zai saka zuciyata ta warke daga radadin  da take. A hankali naji ya rungume ni ta baya Yana buga bayana, I needed wani ya lallashe ni a lokacin to tell me everything will be ok, Amma ba daga gurin shi nake bukatar hakan ba, hakan yasa na ture shi da duk karfina na tashi tsaye na nufi Abhi Dan na dauke shi, se yayi saurin rikeni muryar shi a hankali yace

” Safiyya you can’t sleep here, akwai sauro da yawa. Idan Baki son mu kwana tare ni Zan bar Miki dakin. I’m very sorry”

Nai Masa banza na cigaba da goge hawayen dake fita, wannan sorry da yace kara Bata min Rai take. ya gaji da tsayuwa yaga na ma kwantta kan dandanin carpet, yasan Rai
na ya Gama baci kenan, Dan ko baccin Rana zanyi nafi son najini in comfy of my bed. Ya janye jikin shi ya koma can Kan kujera zai kwanta se Kuma ya fasa ya tafi dakina Dan yasan na hanashi kwanciya akan kujera saboda saurin lalacewa, lokacin idan na fada Masa haka se yace gori nake masa. Na sauke ajiyar zuciya wadda tunda kukan ya dauke nake sauke ta akai akai, a hankali na fara tunani how much I don’t know life, I’m not so much exposed into this world, nayi tunanin Amarya ke cutar uwargida, nayi tunanin duk namiji Yana tarewa wajen amaryar shi ya takurawa UWARGIDAN shi kenan abin ba haka yake ba, a kowanne rank kike Zaki iya cutar abokiyar zaman ki. Naki auren Usman saboda kada daukina yasa ya cuce ta se gashi uta take cuta. Ni a gurina Babu zancen nayi hakuri, wannan idan na cigaba da dauka ba hakuri nake ba hauka nake Dan haka tun kafin Abu yayi nisa Zan nema ma kaina mafita. Alwala na tashi nayi Lokacin da dare ya tsala na shimfida sallayya na fara sallah mostly idan na fara addua se na fara kuka, haka se da nayi asuba sannan wani bacci me karfin gaske ya tafi Dani wata duniyar. Wajen Tara na Mike a gigice saboda kukan Abhi, nasa hannuna na Ciro shi Ina rarrashin shi na fara feeding dinsa Ina dudduba ko sauro ya cije shi kamar yadda ya cije ni, I felt relief da naji Bai cije shi ba. Kamar yasan jiya Babar shi na cikin masifa ko farkawa baiyi ba I’m very grateful for that. Cikin sauri na mishi wanka Nima nayi, nasan ya Dade da fita Dan naji tada motar shi Amma kuma kafin ya fita har pecking Dina yayi a goshina sannan ya lulluba min quilt ya fita. Ina Gama shiryawa na sakko da trolley na bude wardrobe na loda Kaya a ciki na Goya Dana na jawo kofar na fita ban dauke ko quilt din da na lulluba dashi ba balle shara ko kintsa gurin.

STORY CONTINUES BELOW

Karfe biyu na Rana ya Gama duk abinda zaiyi a office ya dakko back pack din shi ya fito, secretary din shi ta mike tana fadin

” Sir badai fita zakai ba?’

Yau dinnan a hargitse yake Dan haka ya tsaya yace

” So se na nemi permission din ki kafin na fita kenan?”

Tayi saurin girgiza Kai tace

” Not at all sir, Naga akwai board meeting anjima shiyasa”

” Postpone it, kice inada patient a gida!”

Daga haka Bai Kara magana ba balle ya amsa sakon dubiyar da take ya bi lift zuwa ground floor ya Shiga motar shi. Ya Jima Bai yada motar ba, Yana tuna Daren jiya. Se yanzun yake tambayar kanshi me yasa Bai bincika abinda Kubra ta fada Masa ba, he knows Safiyya for sure ba zata Yi fada akan abinda Babu ruwanta a ciki ba. But what happened? Khadija ya ayyana hakan yasa ya fara dialing number dinta, tana dauka ko amsa gaisuwar ta baiyi ba ya tambayeta abinda ya hadata da Kubra, batada tsoro ta fada Masa komai

” That’s disrespectful of you, Kubra Mata tace she’s like an elder sister to you! Kada ki Kara. Me yasa kikai dragging Safiyya ciki?”

” Wai Mom Abhi? Kai Hamma Bata sani ba ma fa, se jiya ta kirani ta tambayeni na fada Mata. Wallahi Bata San komai ba”

Wani huci ya furzar Yana ayyana abinda Baffa ya taba fada Masa, true halayen mace baya fita se ranar daka Kara aure. Kenan Kubra has been instigating duk abubuwan nan. Ya ja motar zuwa gida Yana jin tsananin kunyar hada idanu dani. Bai masan bana gidan ba. Wani store yaje ya siyo min novels da suka fito Babu jimawa ya hado da bouquet of flowers saboda yasan Ina son wannan kyautar.

Yana shigowa gaban shi ya Fadi saboda ganin Babu motata. Me gadi ya tambaya yace Masa tun safe na fita da akwati. Da sauri ya bar gurin ya nufi kofata ya bude ya Shiga komai a hargitse, dakina yaje yaga wardrobe Dina a bude banma rufe ba. Parlon komai yadda ya Bari haka yake, Abu ne da Bai taba gani ba, ko lokacin da nake tsakiyar laulayi Ina kokarin gyara gidan.  Idanun shi ya lumshe ya ciccibi akwatin ya mayar min saman wardrobe sannan ya fara tunanin possible inda zanje, banida kawa yasan ko naje Kano ko Gumel. Cikin sauri ya Kira Anisah yadda ta amsa shi yasan bana nan. Ya Kira Rayha itace ma tayi sensing matsala Amma yace Mata Babu komai. To Ina naje ya Jima Yana pacing dakin sannan ya fita Yana Kirana se yaji ringing dinta akan coffee table din parlon. Kanshi ya dafe hankalin shi ya Kara tashi.

Ina fita na wuce gidan Adda Asiya kamar yadda muka tsara zamuyi lunch tare. Dukkansu sunzo me aikin ta ta karba Abhi da akwatina ta Shiga dashi ciki, suna zaune kowacce shigar ta kana kallo kasan masu kudi ne. Adda maimuna ta karba Abhi tana fadin

” Oyoyo Father!”

Na zauna muka gaisa Adda Asiya tace

” Adda Sofy ya fuskarki haka?”

Na danyi kalar tausayi Dan tuntuni na tsara abinda zance musu nace

” Abhi baiyi bacci ba shiyasa Nima na Zama haka”

Ta gyada kanta, Anty yusra tace

” Wannan akwatin kamar kinyi yaji”

Nayi dariya nace

” Adda Nanah kayan gyaran ne fa”

Sukai dariya Wai seda gaban su ya Fadi, Nima nayi haka ne Dan na tsiratar da Dan uwansu. Tare muka yini mukai Hira sosae very educative Hira, se wajen time din lunch Khadija tayi joining dinmu. Har duhu ya fara Shiga sannan muka fito kowa an Masa packaging dinner dinshi. Nace musu next ni zanyi hosting. Da ace inada inda zanje bazan koma gidan ba but ban Isa ba nasan yanzun ya dawo ya tarar da sako na. Na dauki hanya zuwa gida lokacin Dana iso an Shiga sallar Isha, na wuce parlon na kwantar da Abhi na fara gyara, dake ba datti bane kawai kayane a zazzaune se na Dan Jima ban Gama ba. Ina gamawa Yana shigowa, muna hada idanu ya saki ajiyar zuciya ya shigo ciki Yana fadin

” You scared me. Ina kikaje Baki fada min ba”

Ba tareda na kalleshi ba nace

” Ai na fada maka cewar zanje gidan Adda Asiya may be ka manta ne”

Se yayi shiru yana tuna na fada Masa Amma tun farkon week Dole zai manta.

” Ance kin fita da akwati, let’s talk I’m sorry!”

Na kwace hannuna nace

” Kayi tunanin nayi yaji ne? I’m not a Coward, na Kai gyara ne and mind you bana bukatar hakurin ka ka rike ka Kara akan Wanda kakeyi akaina”

Daga haka na wuce dakina dama shi nayi fleeting, wanka nayi na shirya cikin riga iya cinya ta se short nasa a ciki iyakar rigar, kaina na daure da band Anty yusra ta min kitso dazun, nasan Yana son kitso so I know he’ll like it as such I’m gonna torture him. Yana zaune da system gaban shi n kawo Masa abinci na zauna can gefe Ina cin nawa, ajewa yayi ya dawo inda nake zaune Ina bawa Abhi mashed potatoes yace

” I’m sorry, bansan me ya hau kaina ba na Miki ihu akai, bansan Baki ma San me ya faru ba. Your silence is killing me, talk to me, shout at me and hit me indai zaisa ki huce. I can’t afford your silence”

Na kalleshi cikin idanu he looks pitiful nace

” Ai ni ba kamar Kai nake ba, why will I shout at you?…”

“Kiyi hakuri nasan nayi kuskure, I shouldn’t…”

Na daga Masa hannu nace

” Bacci nakeji”Ya shafa kanshi yana girgiza Kai sannan ya dauka Abhi ya bini dashi, ya sameni Ina zaune na kashe wutar dakin Amma baby phone Dina na kunna touch dinta Ina rubutu jikin wani littafi. Zaunar da Abhi yayi a gefena, yaron ya rarrafo se Dole ya karbe pen din, haka na tattara na aje gefe Ina fadin to taho naji menene.+

” Safiyya I said I’m sorry, why are you doing this for crying out loud”

Bance komai ba, se ya kyaleni Naga kamar ranshi ya baci ne ya fita a dakin. Ban Jima ba bacci yayi gaba damu, but cikin bacci naji yadda ake kokarin daga min hankali with those palms of his, kafin nayi retaliating yayi dominating, I can’t resist Dole na bada Kai bori ya hau. Washegari ya Gama kwanan shi Dan haka ya koma wajen gimbiya sarautar Mata. Da safe na gaishe shi dukda inata hade Rai shi kuwa ko a jikin shi se wani murmushi yake, kamar na shake kaina haka nakeji na biye Masa da nayi. Yayi breakfast ya fita office.
Na zauna na fara lissafin yadda Zan daidaita gidana, shi yanzun nasan bazai Kara abinda yayi min ba tunda kwana biyunnan ya amshi gashi yadda ya kamata, ita Kuma Kubra na riga na Gama da ita tunda yanzun duk abinda zata fada a matsayin makaryaciya wadda Bata son zaman lafiya take a gurin shi, I’ve gained his trust hakan kadai ya isheni. Ba kowanne lokaci fada yake ci ba, ba kowanne lokaci zaka dinga mita ba, mutane masu Miya they’re boring, simple Abu zakiyi indai kece me gaskiya magana ta kare. Ya kamata mu fito mu gyara rayuwar mu, dukkan mu dangin miji ne, idan mun Hana wata zaman lafiya muma zaa hanamu. Me yasa maza basuda matsala kullum semu.

” Aiki zata fara zuwa Kuma? Ai bamuyi haka da Kai ba. Ka barta tana tuka mota tana daga min hanci ni banida ita, nace ka siya min kace bakai ka siya Mata ba yanzun Kuma kace zataje aiki ni Kuma na Zama me muku gadi kenan”

Ya gyara zaman shi Bayan ya Gama sauraron duk abinda Kubra ta Gama fada yace

” Na farko Zan Kara maimaita Miki, mota ganinta nayi da abar ta, mahaifinta ya siya Mata banida right da zance ba zata tuka mota ba, ni sauki nane ma ta Kai kanta inda take so. Na fada Miki bazan siya Miki mota ba saboda banida wannan halin yanzun. Duk inda kike son zuwa Zan kaiki ko nasa a kaiki. Na biyu Lokacin da na aureta ta Gama karatu, tayi karatu babanta ya dauki nauyin karatun ta ya Samar Mata aiki ban Isa nace a’a ba, ban Mata wahalar komai ba Dan haka akan wannan bazan tauye su ba. Da na aureki secondary kawai Kika Gama, banmiki zancen makaranta ba, kema Kika nuna Baki damu ba, to kin gani ba yadda zakiyi sede kiyi hakuri”

Ta Bata Rai tace

” Haka ma zakace? Ni fa sede na koma makaranta”

Yayi dariya Yana kallonta yace

” Allah ya bada saa”

Kamar Wasa ta Kade ssce dinta ta fara neman admission a GSU, ni banma San me suke ciki ba na riga na fara aikina Kuma na jona masters dina, seda akazo jamb sanann ta gane kanta ya kwanta bataia making ba Dan haka ta fara neman college of education Allah ya taimaka ta samu ta fara karatu, gaba dayan mu se muka Zama very busy into our lives kowa na neman na kanshi bamu da lokacin Zama muyi fada, mussaman ni idan bana gurin aiki Ina gurin research work Dina. A hakan lokacin yayen Abhi yazo na aika shi wajen Mama ta yaye shi daga haka ta rike shi.

” Seda nace kikai shi gurin Ammi Amma Kika nace ke gurin Mama, yanzun gashi Taki bada shi”

Nayi murmushi nace

” To meye abin fadan Kuma, I wanted space dama yazo ya hanani na maka abubuwa da yawa”

Yayi dariya yace

” Sharri Zaki Masa! Yaron da Babu ruwanshi”

Nima nayi dariya Ina Kara rike wayar a kunnena nace

STORY CONTINUES BELOW

” Yanzun karfe nawa zaka dawo gida”

” Mhm..kafin maghrib haka. Anything for me?”

Nayi murmushi Ina shafa cikina nace

” Many things await your arrival”

Se yace min zai gudo Dan yasan it’s must be important ya sani, nidai dariya kawai nayi mukai sallama, ajiyar zuciya na sauke Ina murmushi, gashi dai auren mu Wasa Wasa min Kai shekara uku Babu Yan watanni, abubuwa da dama suna faruwa suna wucewa, dukda Babu improvement a zamana da Kubra Amma shi Kam ba karamin fahimtar juna mukai ba, duk wani Abu da zaiyi zai nema shawara ta, idan Kubra ya Masa complain akaina zai Kira ni a gabana ta maimaita, zaiyi sulhu wannan yasa abubuwan suka Dan ragu itama ta hakura da Kai Kara tunda yawancin Babu riba. Wayata na dauka nayi dialing number Yaya Ismail kamar yadda nake lokaci zuwa lokaci naji jikin Ummaah, dukda idan na shiga Kano Ina zuwa na dubata Amma Babu Wanda yake Shan wahalar rashin lafiyar ta kamar shi da Ramla. Daga wayar da yayi ya katse min tunani da nake

” Yaya Ina wuni?”

” Lafiya Lau Sofiyya, Ina baby boy da Baban shi”

Na amsa Abhi na Kano , Alby yaje office, se yace zasuje shi da Hanifa su ganshi ai Basu San Yana Kano ba, nace ai yafi three months kuwa.

” Jikin Ummaah da sauki Sofy, thank you very much for your concern”

Nayi murmushi nace Babu komai. Mukai sallama har na kashe ya sake Kirana, Ina dauka yace

” Ina ta San na roke ki wani Abu, kunya nakeji. Dan Allah zaku iya yafewa Ummaah, she’s suffering, idan kuka yafe Mata nasan ko ta rasu Allah zai gafarta Mata shima”

Yadda yayi maganar kamar Wanda yake Shirin Sanya kuka, cikin sanyi nace

” Yaya ni na yafe Mata, gaba dayan mu ma Allah ya Bata lafiya yasa kaffara ne”

Ya amsa da Amin sannan yayi min godiya. Na dafe kaina Ina tuna Ummaah da mulki da izza yadda take abubuwan ta cikin gadara tamkar she owns the world, duk abinda Ummaah ta tsana se tayi destroying dinsa kamar yadda ta tarwatsa gidan mu, ta lalata Mana jin dadinmu. Amma ya wuce har Raina na yafe Mata hakan Rayha balle Ammi da idan ta tuna ta se tayi kukan tausayin ta, ni ta wani gurin ta taimake mu tasa Ammi tayi realising potentials dinta. Rayha na Kira dake fama da tsohon ciki ko yau ko gobe. Muka gaisa tace min

” Se yaushe Zaki zo ?”

Nace

” Ke ki barni da kanon nan, a Gombe nake fa”

Tayi dariya tace

” So nake muyi Hira sosae”

Na kawar da wannan zancen na fara fada Mata yadda mukai da Yaya Ismail taji tausayin su sannan ta fara fada min halin da Amira take ciki an kaita rehab home saboda yadda shaye shaye ya Mata illa. Se lokacin abin yayi clicking kaina tabbas Hanifa ta fada min lokacin ana Kan case din, Amma Ashe abin yayi nisa haka

” Banso ace abin akan Amira yayi befalling ba naso ace Anty jidda da take ganin taci banza ita abin ya hau kanta”.

Nayi Murmushin takaici nace

” Baki gane ba, ai ita Anty jidda a tashin hankali take kinsan drug addiction kuwa. Allah ya Bata lafiya kowa yaji bakin cikin da muka ji”

Mun Jima muna Hira sannan mukai sallama na fara Shirin tarbar Alby, Bai dawo ba se bayan laasar nayi wanka nayi kyau cikin lace Baki da sea green a jiki. Dinkin yayi kyau sosae ya kamani ya fito da dukkan curves Dina. Yana shigowa na rungume shi shima ya maida gesture din Yana fadin

” Allah ya Miki albarka my love”

Ni idan muna tare mantawa nake Wai next door kishiyata ce, Yana nunamin kamar nice best thing a rayuwar shi, Yana sawa Ina mantawa da har kaina ma saboda yadda yake nuna min tsananin soyayya. Toilet na jashi bayan nasa ya kulle idanun shi na Mika masa strip din, ya karba sannan ya bude idanun shi, ya Jima Yana kallon strip din kafin ya fahimci abinda nake nufi, ciki ne dani. Ya kankame ni Yana murmushi tareda shimin albarka!!!!

Tammat Bihamdulillah! Godiya ta mussaman ga dukkan mutane na Wattpad,shatuuus’ kingdom, Takoris’forum, Maman moon novel, Mrs BB novel group, zeenert novel group. Group din sister Aisha shafiee da bana ciki sakon ku ya iso gareni. Nagode se Kun jini.

I hope sakon da nake son isarwa ya tafi, mu so kanmu, muyi accepting Kan mu a kowanne lokaci, matsalolin mu bazasu Kare ba Amma I’m sure idan muka Zama Yan uwan juna matsalolin zasu ragu. Nagode da goyon Bayan ku a kullum. A yau Ina sanar daku sabon novel da zai zo muku nan bada jimawa ba, sede shi din is a paid novel, ka biya ka karanta. Thank you so much!

        💔 AFIYYA 💔

” Auren Dole AFIYYA? you mean Kawu zai maki aure da wanda Baki sani ba? Baki taba haduwa dashi ba?  come on AFIYYA this is freaking 21st cent not lokacin da, rayuwa ta canja Afeey!”

Nayi shiru Ina tunanin me zance ma Rooks dake bambami cikin wayar, abinda take bazai canja fact that aure kawu zai min ba, banida Wanda zai taimaka min. Da gaske na fahimci a wañnan lokacin zumunci ya Kare, idan har dangin babana zasu min hakan, su Kuma dangin mamana da Basu taba t
akowa sun gani ba saboda fushi da suke da babana, Basu San wanne irin Hali nake ciki ba.

” come on Rooks, maganar nan ta tsaya tsakanin mu, bana son kowa ya sani saboda Kawu Sa’idu ya fadawa kowa ni nake son mijin. do this for me sister please”

Tayi shiru se can tace

” But know that I’ll always be there for you?”

nayi murmushi daya fitar da dimples Dina Wanda ko magana nake lotsawa suke, I remembered Ummaah na yawan cewa Yunwa CE tasa nake da dimple ba kyau ba.

Auren ma nayi tunanin zaa hadani da Wanda Zan kalla naji dadi Amma da aka tashi se aka Nemo Wanda ko a lahira bana zata Masa Shiga aljanna, Kar kuga laifina Manson Allah SAW yace Wanda yabi iyayenshi kamar ya bini ne, idan ka Saba musu ni ka sabawa! Shi yayi fatali da wannan maganar.

                                                       

***

” Wannan menene yake hayaki daga dakin Junaidu? kada dai gobara ce”

Hajja Huwaila ta nufi dakin da kafarta da take limping, ga age ga jiki da take dashi. tana zuwa ta ganshi a zaune Yana gaban katon kasko cikeda garwashi Yana watsa Abu se wuta tayi sama, ga kauri ga zafi Amma ko a jikin shi

” Junaidu me kake Yi haka ne?”

Yana dagowa yace

” ke kuma wa yasa  dake, na tsani shishiggi a lamurana. Mtss!”

ya ja tsaki, sokoko hajja Huwaila tayi tana jin radadin abinda Dan data Haifa a cikin ta yake Mata, ta juya ta koma cikin gida tana jin Fuzaima kishiyar ta tana dariya tana fadin,  Da haihuwar wasu gwara barin su!

Kullum mu kanyi labari ne Akan mace, Akan matsalolin da Mata suke fuskanta akan soyayya da Kuma zamantakewa. Wannan labarin zai karkata akalar shi akan mutane biyu. Labarin Afiyya yarinyar top business tycoon, wadda gata da wadata Suka lullubeta, sede ba ko yaushe rayuwa ke tafiya yadda ta dakko hanya ba,. Kamar yadda lokaci daya mutuwa ta yanke Mata wannan jin dadin ta maida ta wata aba daban. Ta maida rikon ta hannun Wanda Basu San cewar da da dukiya baka musu mugunta ba, Sabida baka son waye zai Mora ba.

Lokuta da dama mukan dauke kanmu daga abinda mutane suke fada akan mu, mun manta ya kamata ka duba kaga mutane me Suka dauke ka saboda da shaidar su zaayi amfani wajen maka hisabi. Ba kowanne lokaci bane suke fadar son zuciyar su lokuta da dama akwai kamshin gaskiya a zancen su

Labarin Junaidu Wanda ya kasance me matukar kokarin ganin ya boye ainahin kanshi da shi din waye, Amma mutane sun riga sunsan shi din waye. Kuma kullum suna kokarin Kara binciko halayen shi. Kaddara ta kan saka ka rashin dace a farkon rayuwar ka ko Kuma a karshe. Let’s go people

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *