UWAR GIDAN BAHAUSHE CHAPTER 18 BY SHATU

UWAR GIDAN BAHAUSHE CHAPTER 18 BY SHATU

Www.bankinhausanovels.com.ng 

Karfe takwas malamin dake zuwa yimin karatun islamiyya yazo, an riga anyi min wanka nan ma se da akai rigima Dani Dan seda Abbu yazo yace yayimin alkawarin ranar birthday Dina ranar Zan fara wanka da kaina, I was super happy na yadda Nanny tayimin , ta shiryani cikin riga da skirt na lace, tea ta bani Nasha sannan ta rakoni parlor na zauna bayan na Gama gaida malamin, gaba daya karatun na one hour ne sannan ya tafi na cire hijab na dawo daki na tafi gurin Abbu. Na samu ya Gama shiryawa for breakfast so a dakin shi muka ci abinci. Bayan mun Gama yace na dakko home work Dina se muyi tare dashi, na wuce dakina na kawo backpack Dita da dayan littafin, Yana dauka yace

” Princess wannan ba littafin ki bane ai”

Na karba littafin daga hannun shi trying to confirm, dama ban iya spelling Ringim ba amma nasan six letters Suka hada ringim, ni Kuma gashi Naga four letters, sauran sunan irin nawa ne. Nayi shiru se can nace

” Abbu canjawa mukai da Amina da Zan Sha ruwa”

Ya dafe kanshi sannan Bai ce komai ba ya Ciro waya ya Kira class teacher din mu, ita ce ta fada Masa address din gidan su Amina, yasa Nanny ta canja min casual wears din jikina zuwa wata English gown, aka saka min hula da takalmi, tayimin packing chocolate kamar yadda Abbu yace a bani nakai wa Amina. A garki suke nan muka je, Abbu yayiwa security din bayani, Babu jimawa Sega wani mutum ya fito, Yana zuwa ya gaida Abbu yace mu shigo, Yana fada Masa su Basu ma gane cewar Amina ba book dinta ta kawo ba. Ciki mukaje tana ta Wasa da siblings dinta, seda ta ganni sannan ta taho hade da Jan hannuna nayi Wasa, Dole Abbu ya tafi ya barni a gida se yamma ya dawo ya tafi Dani, that’s how Maman Amina ta Zama a figure a cikin rayuwata.

Duk Sunday Abbu zai kaini salon, zaa wanke kaina sannan a yanke min farce, ayimin kitso, idan na zauna Baku labarin yadda Abbu ya kula Dani Zan karar da duk wani karfina kafin na shiga gundarin labarin. Abbuna ya min duk wani Abu da uba da uwa zasu min, akwai abubuwan da kake rasawa kake samun makamancin su Amma nikam har na koma ga Allah nasan bazan samu madadin Abbu ba. Rooks cousin dita ce, mahaifiyar ta ita ce Mummy Maryam, kanwa wajen Abbu. Mijinta Dan sarkin Ringim ne Daddy. Tun da ta haifi Rooks ya samu aiki a NY se ya tafi dasu can dama field din daya karanta was international relations. Ban Santa ba se lokacin da nayi birthday Dina na shekara takwas Abbu yace zai kaini Newyork gurin Aunt dina. Banyi wani murna ba saboda ni nafi son kawai na zauna a gida Ina gannin Abbuna. Ya Mana Visa komai dasu passport ya zama ready mukaje Ringim nayi ma Hajiya sallama, se muka biya Kano wajen Uncle Tijjani Abbu ya kaini Naga Basma da Bata wuce 40 days ba. Tunda Naga yarinyar nayi tama Abbu shagwaba Nima se ya siyo min Baby, se da Anty Salma tace min naje idan na dawo zata hada Mata Kaya se na tafi da ita gidan mu. Bamu Kara kwana uku a Nigeria ba muka wuce NY, Mummy tazo airport ta dauke mu, Rooks na makaranta, inata kallon gidan, da dakin Rooks din komai na fulla ne yayi kyau sosae. Na dinga kalla with so admiration a idanuna Ina fatan inama nawa dakin haka yake. Mummy ta shigo tana min murmushi tace

” So daughter.”

Na matso inda take na zauna ta shafa kaina tana ta murmushi tace

” Feel at home, Rooks ba zata Jima ba zata dawo. Yaya yaje ya huta zai dawo kinji”

Na gyada kaina Ina rarraba idanuna na rashin sabo, abinci ta kirani naci a parlor, Ina fara ci se ga Daddy da Rooks sun dawo, da gudu ta shigo hannunta dauke da backpack dinta, ta rungume ta tana shafa kanta tace Mata

” Afiyya tazo”

Ta juyo ta kalleni sannan ta kalli mamanta, se Kuma ta wuce dakin ta. Abbu yazo da daddare har lokacin bamu magana da Rooks ba kamar she’s not happy nazo gidan su, Abbu washegari ya tafi ya barni shima seda aka fita Dani Dan da ya dawo kuka nayi tayi Bai zo ba. Kwana biyu na sake jiki itama Rooks ta saki jikinta Dani, seda nayi sati uku anan kafin na koma gida,shi ne mafarin sabon da mukai da Rooks.

Rayuwa ta cigaba da tafiya, Junaidu har ya Kai matakin shiga karamar secondary, Babu Kuma abinda ya sani haka dai kawai akai gaba dashi ya bar makarantar ko Allah zaisa su huta. Babu jimawa karatu ya kankama nanma ya bude sabon babin iskancin shi, baya zuwa makaranta ko Kuma yazo a makare Kuma kafin a tashi ya sallami kanshi, anan ma ya fara hada gang na bad boys Yana koya musu duk abinda ya iya. Ana haka ya shiga aji biyu daf da karshen term akai fada a gidan su. Ya dawo da yamma ya cake da abubuwan da yake zuka, Yana shigowa gidan Ashe Fatima ta bawa yarta zainab ta siyo Mata kayan Miya, yarinyar wani ya karbe kudin a hanya tana zuwa gida tace ai Junaidu ya karbe kudin. Tunda taji zance tace ai wallahi ko kasa da sama zata hade se an biya ta kudinta ta gaji da dibar albarkar da yake musu a gidannan, jiya ya daki yayanta kawai darajar zaman tare yasa ba tayi magana ba, yau Kuma gashi ya kwace kudi a hannun yarinya, me ake da haihuwar irin su, da kamar Dan Allah bani, inama da akazo haifar shi barin shi akai… Maganganu marasa Dadi Hajja Huwaila na gefe tana bakace ko dago kanta batayi ba balle ta maida martani, a ranta fada take Dan kuka me jawo uwarshi jifa, Hasiya ta fito ta kalla Fatima da har lokacin Bata bar mita ba tace

” Ke kuwa kin tabbatar shi Junaidu ya karbe kudin, kinsan yarannan sun iya karya”

” To idan bashi ba waye, shi din bako ne a gidannan da ita zainab zata kasa gane fuskar shi?”

” Ba bako bane Fatima Amma maganganun da kike fada sunyi nauyi da yawa mahaifiyar shi fa ta nan, ai da kunya”

Ta tabe baki yace

” Wannan ku ya Dana, tunda ta Haifa se ta bada tarbiyya tunda ta gagara bayar wa se ta bude kunnuwa ta saurari me zamu fada kudina se an biya ni”

Kafin Hasiya tayi magana se Suka ji maganar Junaidu a zaure yana fadin

” Zan babballa kashin ki wallahi shegiya me Kama da mayu, kin tashi ko Sena hada Miki jini a fuska”

Da gudu salama ta shigo, tayi Bayan Fatima wadda ke tsaye tana jiran taga da wa yake, shigowa yayi a lokacin kana kallon shi kasan yasha wani abun, gaba daya idanun shi sunyi jawur tafiyar shi ma Babu nutsuwa, dakin Hajja ya nufa Fatima da ganganci se ta rike Masa riga,

” Allah ya Toni asirinka, se ka fito min da kudina kafin na mare ka a gidannan”

Ya kalleta sannan ya kalli hannun ta da ta Kama rigar shi ta rike gam yace

” Ke dallah sakeni, wanne kudi kike magana anan?”

Ya fada Yana kicinayar kwacewa, ta Kara rikewa tana fadin

” To meye Dan kace min dallah Naga uwar data haifeka baka gaishe ta, ka Zama Dan shayeshaye meye Dan ka zageni, kudi se ka fiton dashi”

Hannun shi yasa ya doke nata yayi gaba abinshi, Amma Bata hakura ba tabi shi ta Kara Kama shi, a zuciye ya juyo Yana juyowa ya hambare ta, aikuwa se gata a zube a kasa, har mamakin karfin Junaidu nake, yayanta sukai kanta, Hajja Huwaila ta mike itada Hasiya suka
i kanta, bakinta da hancin ta se jini suke saboda makewar da yayi Mata. Dake salama tafi wayo tana ihu ta tafi ta Kira Malam dake dakin shi, aikuwa ya fito lokacin an maida Fatima daki se kuka take wallahi ba zata yarda ba, Malam ya shigo ya tsaya yayi Shiru ya rasa me zaice saboda yadda zuciyar shi take kamar zata fito ta bakin shi. Hajja Huwaila daki ta koma ta sameshi yayi daidai ya ware fanka Yana bacci, ta daka Masa duka, ya bude idanun shi yayi tsaki ganin ita ce, ya juya Dan gyara kwanciyar shi ta fara fadin

” Tashi ka fitar min daki na, kaidao Allah ya wadaran halinka, bakai halin arziki ba San”

Dake ba fada ne da ita ba,shi kanshi a sanyaye take fadar hakan. Ya Mike ya nufi tsakar gida zai fita sega Yan sanda sunzo Kama shi Wai Fatima yayanta Ashe DPO ne anan division din Kazaure.

DPO ya turo yaran shi akan suzo su tafi da Junaidu, kunsan yadda Yan sanda suke na Nigeria kamar haushi dama suke ji balle Kuma an tabo kanwar DPO Kuma kunsan se inda man su ya Kare, suna zuwa sukai handcuffing din shi Suka tafi dash, mutane suka taru a kofar gidan Dan ganin kwakwaf, malam Yana ciki ya tasa Fatima a gaba ya zuba Mata idanu, ita Kuma ta bawa banza ajiyar shi. Da ya tabbatar ba zatai magana ba se yace Mata+

” Nayi tunanin hakurin da na baki zakiyi hakuri kiga hukuncin da Zan yanke, Amma kin nuna min kinada Dan uwa”

” To Malam Naga kaima dai Junaidu a gidannan ya gagare ka, kana kallon dukan da yayi min da da karar kwana sede a Kira ka ace maka na mutu”

Bai ce Mata komai ba ya fito daga dakin nata, Kan shi har juyawa take saboda yadda ran shi yake a bace, dakin Hajja Huwaila ya nufa ya sameta tana kuka Hasiya na gefen ta

” Hasiya ni nasan Junaidu Bata jin magana Amma nasan bazai karba kudi daga hannun zainab ba, idan sata ya fara daga dakina zai fara…”

Hasiya tace

” Yanzun duk wannan ba wani amfani, kizo muje mu samu Malam ayi bailing shi”

Ta girgiza Kai tace

” A’a gwara a barshi su daka yadda itama Fatima zata ga an Rama Mata, ni abinda ya Bata min Rai Sharron Sara, wallahi Dana haifi barawo gwara ace kaf garinnan yafi kowa shaye shaye”

Anan Malam yayi gyaran murya yayi sallama ya shigo, Hasiya ta Masa sannu sannan ta fara kokarin fita ya dakatar da ita, seda ya zauna sannan yace da Hajja

” Kukan me kikeyi? Addua Zaki Masa Allah ya shirya ki Amma kukan ki kamar karar shi kike wa Allah”

Ta goge hawayen ta amma Bata ce komai ba, ya dubi Hasiya yace ta Masa bayanin abinda ya faru, tiryan tiryan ta fada Masa, ya Gama ji sannan ya fito ya kwallawa zainab Kira, tana dakin Babarta ta fito, yace ta biyo shi daki. Idanunta sunyi raurau ta bi Bayan shi zuwa parlon shi. Seda ya zauna sannan ya fara takbayarta cikin lallami Wanda ya karbe kudin a hannunta, se tace Masa kudin ne Suka Fadi ita Kuma tasan mamanta zata dake ta shiyasa tace Junaidu ne ya kwace. Ya Mata fada sosae akan karya da Kuma husumar data hada a gidan sannan yace ta tafi.

Bayan mun dawo daga NY da sati daya na koma makaranta, Abbu ya maida min dakina na Barbie kamar yadda mummy tace mishi, dama naje makaranta ne Ina dawowa Naga har wallpapers duka an canja min, na dinga ihun murna Ina dariyar farin ciki, Nanny na zaune sede tayi murmushi kawai tana kallona. Da ya dawo na rungume shi nace

” Abbu kaga dakina yayi kyau, ya koma na Barbie!”

Yace min haba dai? Na jashi inata nuna mishi se yace shi ya saka aka gyara min, na Kara rike hannun shi nace

” Abbu thank you!”

Ya shafa kaina yace idan nayi addua na dinga cewa Allah ya jikan Mama ya Mata Rahma, ban taba manta wannan maganar ba Kuma duk abinda zanyi se na Yi Mata wannan adduar. Da sati ya Kama ne ranar Saturday Bayan islamiyya classes Dina nayi home work, mukai Baki, ban taba ganin su ba so banma sansu ba. Har parlor Abbu ya kawo su Ina zaune kan sofa Ina kallon cartoon din Bob the builder a MBC 3. Suna Zama na gaishe su, daya daga ciki ya dubi Abbu yace

” Ta girma Babyn, Allah ya jikan Halima”

Abbu yayi murmushi Yana shafa kaina dake gefena ya zauna yace

” Lokaci gudu yake Yi ne, gashi ta kusa Gama primary na”

Suka gyada kansu in agreement da abinda Abbu yace Suka fara hirar mutuwa, nidai anan nayi bacci jikin shi.

” Nasan ba lallai sakon da muka zo maka dashi yayi maka dadi ba, Amma Babu yadda zamuyi muma Yan aike ne”

Abbu ya gyara Zama Yana sauraran kawu na, kanin Mama ne

” Munyi shawara last week se muka ga ya kamata ace min karbi Afiyya daga gurin ka, she needs a mother’s care”

Abbu yayi murmushi yace Yana kallona

” Afiyya Bata bukatar wannan, nasan ko na amince ku tafi da ita ba zata zauna ba balle ma Nima bazan bada ita ba gaskiya saboda lokacin da nake tunanin zaku karbe ta Babu Wanda yace zai karba, yanzun Kuma ita kadai nake gani na cigaba da rayuwa. Kuyi hakuri Zan dai dinga kawo ta Dan ta Saba daku, Kuma se ku dinga zuwa yadda zata gane ku”

” I knew bamu kyauta ba, a lokacin idan mu karbe ta gani muke it will break you more, shiyasa muka bar maka ita, to yanzun ta fara girma she needs a mother ba komai zaka iya Mata ba”

Ya girgiza Kai yace

” Afiyya needs only me, akanta tasan batada uwa ni ne ubanta ni ne uwarta, bana son na dagula Mata lissafi Kuma. Beside Kun riga kun  Yi missing chance din ku na rike ta”

Duk yadda sukai Akan Abbu ya Basu ni yaki, they threatened him Amma dukda haka yaki amincewa haka suka tafi ko abincin da aka hada musu Basu ci ba. Wannan shi ne abinda ya fara hada gaba tsakanin dangin mamata da Abbu, su a ganin su duk lokacin da suke so suna da right su karbe ni shi Kuma ya nuna musu akasin haka. Daga wannan se suka shafe batuna cikin rayuwar su Suka manta cewar suna da ya a wani gurin. Shima Abbu se ya tattara su ya kyale su kawai ya zuba musu idanu. Rayuwa ta cigaba da tafiya har na Gama primary school dina. A wañnan hutun Abbu ya dakko Hajiya dani da kawu Sa’idu da Nanny muka tafi saudiyya aikin hajji, acan muka samu Uncle Babawo yazo daga Central Lancashire inda yake msc acan. Tunda yazo kullum zamu tafi harami gurin shi nake zuwa ya rike ni, har Hajiya na cewa Uncle Babawo ya kwace wa Abbu na ni, ni Kuma Kama take min sosae da Abbu, though bani kadai na fada ba, kamar su day Abbu ta baci shiyasa nake son shi, Sabida I see my father in him. Da muka Gama aikin hajji se ni da Abbu muka tafi Paris saboda yayi min alkawarin zai Kai no Naga Eiffel tower. Harda Uncle Babawo muka tafi sauran Suka juya Nigeria. Kwana nan mu uku muka koma Nigeria muma. Nigerian Turkish college nan na samu admission nayi joining Js1 din, har lokacin tare muke da Amina tunda babanta ya tambayi Abbu se yace Masa ai Turkish college zai kaini shima se ya nemawa Amina can muka tafi tare. Baa boarding muke ba day mukeyi, so Abbu se yasa driver kawai yake daukar mu ya kaimu, har gida muke zuwa daukanta mu maida ta, ita Kuma duk ranar Friday Mom dinta zata zo ta dauke mu muje gidan su na wuni. A kwana a tashi kullum rayuwa tafiya take, ni ina Kara girma kamannina suna Kara fitowa da mamana, idan ka ganni sak uwata, komai nata irin nawa ne. Tamkar tayi kaki ta tofar haka nake da ita.Rayuwa ba komai bace musamman idan ba kada komai, idan kana dashi zaa dama dakai Amma daga ranar da bakada shi to kaima ka Zama Dan kallo. Duniya abace me ban tsoro, dare daya zata dauke ka ta nunawa duniya kamar Kaine kafi kowa, idan ta aje ka se kowa ya manta da cewar you have ever existed.  Idan mukaje Ringim ni da Abbuna dake mostly duk gurin da zaije tare dashi nake zuwa, ko fada zaije to tare dani zaije, idan muka fito daga fada zuwa nan ausar ba wani nisa bane, mutanen da zamu dinga haduwa dasu Kan Hanya kowa se yayi kkakrin yimin alkhairi, hannuna cikeda k
udi Zan koma gidan Hajiya, idan aka kirga se na tashi da abinda yafi 7000. Idan dare yayi da suka fahimci idan munzo Abbu na siya min kifi, Kar kuso kuga kifin da ake kawowa. Daga gidan Kawu Sa’idu kullum su Siyama na hanyan zuwa gurina dukda ni bana zuwa gidan su saboda yadda umman su ke hantara ta, ni Kuma bansaba ba duk gurin da na tashi Sona ake, Babu abinda ke zuciyata se soyayya I don’t believe any other thing exist Bayan soyayya.+

Sede ba komai ke daurewa ba, kamar yadda aka Mana alkawarin wuya ba zata daure ba hakan Dadi shima baya daurewa, in one way or the other Allah zai jarabceka, mafiya yawan bayin da ake jarabtar su Allah na sansu ne. Sede wani lokacin idan na zauna I kept wondering Anya akwai Wanda akai wa jarabawa irin tawa? Wani lokacin se naji kamar me nayi Dana cancanci hakan, nakan Yi istigfar , a yanzun ma da nake fada muku Allah ya yafe min! Shekarata Sha biyu na Gama js2 Ina Shirin tafiya js3. Bayan na Gama munyi hutu na takura Abbu Alan lallai se ya kaini Ringim nayi hutu saboda Rooks ma sunzo daga NY. Shi Kuma ya rasa yadda zaiyi Dani dan shi Central Lancashire yake son zuwa UK gurin uncle Babawo.

” Princess ki Bari muje UK mu dawo I promise you Muna dawowa Ringim zamu wuce”

Na Dan Bata rai nace

” Ni Abbu Hajiya nake son naje na gani, Kuma Rooks fa tazo”

Ya Dan marairaice fuska yace

” Princess ban sanki da rigima ba fa, kinsan menene gurin Babawo zanje”

Idanuna na bude da kyau nace

” Abbu da gaske, lemme park my clothes straight away”

Yayi dariya Yana zame hannun shi daga cikin nawa, tuni na tafi dakin Nanny Dan nace Mata ta hada min kayana, na bar Abbu zaune ya tsaurawa katon hoton shi da ni da mamana idanu, lokacin Dana fito na same shi a tsaye Yana shafa hoton, I can see the pains in his eyes.

” Abbuna!”

Na fada Ina Kama hannunshi, juyowa yayi ya sakar min murmushi Nima nayi Masa murmushi nace

” Kullum ban manta ba inayi Mata addua fa”

Yayi murmushi yace

” Allah yayi Miki albarka, Allah ya Kare min ke Aminatu”

I can say wannan ranar ne farkon da na fara jin shi ya Kira sunana Aminatu, he always refer me princess, Dan hakan se naji jikina yayi sanyi sosae, na zauna a kusa dashi dukda kankantar shekaru na Amma Abbuna kowanne Hali ya Shiga Ina iya ganewa tunda kuwa dashi na sani, shi na tashi na rayu dashi. Wannan kwanakain bansani ba ko ya akai ya fahimci wani Abu Amma se yake kadaice Kan shi shi kadai a daki,idan naje se yace min na tafi daki na jira shi,ba zai zo ba se nayi bacci so a tunani na he was busy seda na Kara girma nayi hankali sannan na fahimci he was fighting the toughest and silent battle of his life. Sede mukai sati Yana min hakan, duk nabi na damu fuskata walwalar da kullum zaka gani akai ta bace se de na zauna nayi shiru,  a Daren da zamu tafi yazo daki Ina zaune akan sofa kafana da socks hannuna dauke da wani pineapple juice Ina Sha naji sallamar shi, nayi saurin juya bayana, Wai no nayi fushi, jin Bai shigo ba Babu Kuma motsin shi yasa na turo bakina na juyo, Yana tsaya ya Kara tsufa he looks drained, bana tunanin Zan manta tausayin Dana hango nawa a idanun shi.

STORY CONTINUES BELOW

” Abbu fushi nakeyi ni”

Yayi murmushi ya karaso ciki yace

” Princess ai Bata fushi da Abbun ta,ko so take ayi Mana dariya”

Na girgiza Kai inajin sanyi a raina, ya matso ya zauna na nufi Kan shi Zan hau ya girgiza Kai yace

” Yanzun princess ta girma, kada ta Kara Hawa Kan wani namijin,kada princess ta Kara rike hannun wani namijin kinji?”

Na gyada kaina Ina pouting yayi murmushi yace

” That’s my girl, muje yau a waje zamuyi dinner”

Ya fita ya barni Ina Neman abinda Zan saka, a waje mukai dinner washegari very early jirgin mu ya tashi zuwa Lancashire, though munyi trans in a Singapore na wajen 12hours Nan ma seda Abbu ya fita Dani Wai Naga gari , munyi yawon wajen awanni uku kafin muka koma muka huta. Bayan mun huta jirgin mu ya Lula se UK, a Oxford mukai kwana uku ya nuna min famous and prestigious University yace nan zai kawo ni nayi degree dina. Nayi dariya Ina admiring yadda makarantar take no wonder ta samu gurbin Zama one of the leading universities in the globe. Bayan nan se Manchester a kalla munje states tafi bakwai kafin mukaje can inda Uncle Babawo yake, se Naga kamar ma wani aikin ya kawo shi gurin shi, Dan tunda mukazo suna tare ni Kuma ya saka wani Yana zagayawa Dani inda ya kamata a cikin garin, satin mu daya sannan muka dawo Nigeria. Bamu kwana a Abuja ba muka wuce Ringim, tun a jirgi ya dakko wani karamin diary ya bani, a jiki akwai buttons da zaka Danna 4 number passcode kafin kayi accessing din shi, na kalleshi yace

” Passcode din year of birth din ki ne, keep it safe with you, whenever you Miss me akwai abubuwan da zai dauke Miki kewa a ciki. Aminatu ki sani rayuwa Abu ce me ban tsoro, Babu abinda ke daurewa walau Dadi ko akasin haka, for these years nasan na Miki tarbiyyar da Zaki iya Zama da mutane, kiyi hakuri da duk yadda rayuwa zata zo Miki kinji?’

Na gyada kaina Ina jujjuya diary a hannuna, ya shafa kaina ganin face Dina ya Zama grumpy yace

” Princess!”

Na dago na kalleshi ya sakar min Murmushin da har yanzun idan na tuna Murmushin Abbu it kept me going. Se naji karfin gwiwa a hakan muka Isa Ringim muka samu Hajiya batada lafiya, Amma jikin da sauki. Kwanan mu biyu inata sharafi na ni da Rooks, yawo Kam munsha har inda ban taba zuwa ba, duk inda mukaje se ace Rooks ta fini kirki, it doesn’t matter to me as far as Abbuna is happy with me mutane ba a gabana suke ba. Washegari ranar jumaa Rana ce da bazan taba manta ta ba a rayuwa ta, Rana ce data bude min wani shafi cikin rayuwata Wanda ban taba tunanin akwai wani mahuluki da ya taba tsintar Kan shi a ciki ba. Nayi tunanin duniya waje ne na soyayya farin ciki da karbar mutane a duk yadda suke, Ashe hassada ce da mugunta a zuciyar mutane, kowa jira yake Wanda kake dashi ya Kai suyi embarking a abinda suke kullawa. Abbu ya fito cikin Shirin shi na zuwa masallaci, na Mike da tab dita na Masa hoto, farar shadda ce Kal a jikin shi se daukar idanu take, kanshi sanye da hula baka yayi kyau, Yana murmushi ya shigo parlon ya tadda fura ana damawa an Bari half way, ya gaida Hajiya, da annuri a fuskarta ta amsa tanata Masa addua kamar kullum, ya dubeni da murmushi ganin yadda na dage Ina dama fura kwakwa, yace

” Princess furar waye?”

Na aje ludayin hannuna nace

” Taka ce Mana Abbu, kayi sauri ka dawo daga masallaci Kar ta huce”

Ya shafa kaina ya kalli Hajiya ya Mata sallama ta amsa tana cemin Wai iyayi ne Dani, Ina gamawa nasa a fridge nayi wanka Nanny na maiduguri taje wajen family ta so komai da kaina nake yi. Na shirya sannan na dawo na zauna Ina duba Tab Dita Ina ganin moments din mu da Abbu a kasashe da dama.  Se naji hawaye ya zubo min a idanuna, Allah kadai yasan yadda nake son shi, sallamar shi tasa na tashi Ina Masa oyoyo, shi da Kawu Sa’idu ne da Kuma Baba da Yaya yayanshi, kawai bansan me yasa ba bana son kawu Sa’idu kullum a idanun shi greed kawai nake gani, da haushi, hatta kallon da yake min na tsana ne da hassada a ciki. Cup na dakko na cika ma Abbu da fura na tura Masa gaban shi, na gaishe dasu, Yaya ya dawo munata Hira Bayan Suma na San musu furar. Babu jimawa suka tafi se Abbu yace

” Princess kaina na ciwo Bari na Dan kwanta”

Nace

” To Abbu sleep well!”

Shikenan se ya tafi daki na bishi da kallo Ina jin jikina yayi sanyi, se na dawo na zauna nasa kallo inayi, can aka Kira laasar na nufi dakin nashi Dan na tashe shi Amma se Bai tashi ba, na dawo nace

” Hajiya Abbu yayi nauyin bacci Bai tashi ba”

Tayi shiru se ta Mike a hankali ta tafi dakin, Nima nabi bayanta, muna Shiga se naji tsoro nake ji, I’ve never
felt so scared a rayuwata kamar wannan tsoron da naji ba, Hajiya ta Dade a kanshi kawai se naji salatin ta, na shiag da sauri, MY FATHER,  MY WORLD MY EVERYTHING IS LYING DEAD!!!

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *