UWAR GIDAN BAHAUSHE CHAPTER 19 BY SHATU
Bayan Malam ya Gama sauraron duk bayanan zainab se ya sakata a gaba Suka tafi police station Dan ita kadai ce zata saka ayi bailing Junaidu. Tunda dama it’s din ta hada husumar so seta Zama wadda zata warware ta. Lokacinda Suka Isa gaba daya Junaidu ya canja kammanni saboda dukan da ya Sha, tunda Suka shiga DPO yace a lallasa masa shi har se ya gane baa dukan mace. Ga Junaidu da bakar zuciya haka yaki Basu hakuri se amsar dukan yake. Malam na Isa yayi ma officers din dake tsaye a reception bayani, daya daga ciki yace Masa+
” Malam kawai ka tafi Dan bansan ranar belin wannan gaggararren Dan naka ba”
Malam ya gyara tsayuwan shi yace
” Idan ba zaku damu ba Ina son magana da DPO din ku”
Daya daga ciki yace
” DPO baya gari yaje headquarter acan Dutse”
Malam ya gyada Kai yace
” Idan ba zaka damu ba ko Zan samu num…”
” Baya cikin aiki, kaga Malam Muna ganin girmanka a gurinnan, tunda munce ka wuce kawai ka tafi”
Malam ya Kama hannun zainab Suka fita a station din, haihuwa kenan sanadin ta Babu abinda bazai same ka ba walau sharri walau khairi, shi Bai taba zuwa police station ba Amma dalilin Junaidu yau shi ake cewa ya fita duk girman shi da darajar shi.
” Ai da ka sani ka tatse shi wallahi, malaman nan kudi be dasu, yaran Yan siyasa ne fa”
Dayan yace
” A’a gwara dai a kyaleshi saboda wannan Yana da connection da manyan mutane kada mu jawa aikin mu”
Yana zuwa gidan ya tarar da fada ya barke tsakanin Fatima da Hasiya, Hajja nata kokarin raba su Amma sunki, sede suka hi sallamar shi sannan cacar bakin da suke ta lafa, Bai ce musu komai ba ya nufi dakin shi, Amma kowacce Tasha jinin jikinta, Hajja ta bi Bayan shi ta sameshi zaune ya kurawa guri daya idanu, he looks disturbed. Zama tayi tana fadin
” Malam kayi hakuri kada ka Bari abin Junaidu ya dameka, adduar shiriya ita ce zata rabamu dashi”
Ya gyada Kai Amma Bai ce komai ba hakan ya tabbatar Mata ba zaiyi magana ba, se ta tashi ta fito dukda tana son taji yadda aka Kare a station din Amma Bata son damun shi, Kuma alamu sun nuna baayi nasara ba, tunda ya shigo babu Junaidu. A tsakar gida taji zainab na fadawa Hasiya yadda sukai a station da officers din, hankalinta ya Kara tashi to Amma ya zatayi? Sai dai ta zubawa sarautar Allah idanu. Wasawasa magana se ta Zama babba tun Malam yana zuwa wajen police din suna Masa yawo da hankali har ya kyalle su, Fatima Kuma sunyi magana da DPO akan se Malam ya Bata hakuri sannan zai sake Junaidu. Ko fahimtar abinda take nufi yayi se ya kyaleta Bai ce da ita komai ba Amma se ya kaurace Mata, kwana biyu da tayi a dakin shi magana ta fatar Baki Bata hada su ba, hankalin ta yayi mummunan tashi, washegari wajen azahar se ga Junaidu an sako Shi, fuskar shi ta kumbura saboda duka, ga jikin shi da duk shatin bulala a jiki. Hajja Huwaila ta daura ruwan zafi tasa yayi wanka, ta gasa Masa jiki sannan ta shafa Masa man zafin da Hasiya ta kawo Mata. Yaci abinci ya kwanta a ranshi Yana saka next abinda zaiyi!
Na karasa gaban gadon tareda jijjiga Abbu, Amma a hakan nan dai yake kwance lifeless, Babu digon numfashi dake jikin shi, gaba daya jikin yayi sanyi, kwayar idanun shi a rufe tamkar me bacci, hakan ya tabbatar min daga baccin aka zare Masa Rai. Naja baya da sauri tareda rufe bakina da hannuna Ina jin ilahirin jikina Yana rawa kamar ana kada min mazari. Hajiya na kuka ta fita yayinda ni banyi kukan ba sede Ina tsaye a gaban shi Ina fatan Nanny ta buga min gefen gado na ta tashe ni tace min na tashi zanje makaranta, Amma ba mafarki nake ba, idanuna biyu it’s happening in reality Abbu is no more. Nayi shiru ban masan me zuciyata ke sakawa ba a wañnan lokacin, bazan iya Baku labarin yanayin da na shiga ba nasan dai I was more than shattered. Babu wata kalma da Zan muku amfani da ita ta nuna bayyana muku halin da na shiga, Wanda kadai ya rasa iyaye shi zai fahimci me nake nufi. Ina nan a tsaye na fara jin koke koken mutane, Ina tsaye na tsira Masa idanu, Kawu Sa’idu da wasu daga cikin Yayan sarki Suka shigo, duka Ina tsaye aka fara kokarin shiray shi, nasan an ja hannuna an fita Dani, but bazan iya cewa waye ba, kowa kallon shi kawai nake na Zama tamkar statue. Gidan kafin wani lokaci ya cika dam da mutane, se kuka suke Amma gani nake duk yadda suke ji ba zai Kai yadda nakeji ba. Mummy Maryam da Rooks Naga sun shigo, ta rike hannun Mummy dake wani irin kuka tamkar ranta zai fita Amma Ina nikam nawa idanu ne. Seda aka fito dashi cikin makara sannan na Mike tsaye, Kawu Tijjani yazo ya rike hannun na idanun shi se hawaye ke fita yace
STORY CONTINUES BELOW

” So ki Masa addua”
Haka na bi bayan shi na zauna gaban gawar, my Father,my love, Abbuna, abokina, uwata da ubana? Shi ne a cikin makara ya tafi, ya mutu Kuma bazai dawo ba. Se na kankame shi na saki wani kuka me daci Ina fadin
” Abbu why will you leave me? Bansan kowa ba, you’re my everything Abbu ya zanyi rayuwa yanzun…”
Na kasa karasawa saboda gaba daya na shide, ban Kara farkawa ba se Bayan awoyi goma da wasu abubuwa sannan na farka a firgice Ina Kiran sunan Abbu, Nanny dake gefena tayi saurin rungume ni a jikinta tana kuka, tana rungume ni nasan ita ce Dan haka na saki jikina na fara kuka bance komai ba Amma radadin da nakeji a cikin zuciyata ya wuce gaban na rubuta muku. Allah sarki Abbu ya tafi ya barni se nake jin inama Nima na mutu na huta, Babu abinda ke tsoratar Dani shi ne na tuna Wai Dole Zan rayu Kuma Babu Abbu.
A cikin gida an kaishi makabarta a wañnan yammacin, itama Hajiya tunda aka dawo da abinda aka lullube shi ta mike se kuwa ta yanke jiki ta Fadi, Babu shiri aka dauke ta se Kano asibiti, kafin suje ta rasu itama, Dan hakan mutuwar se ta hade Mana, ga ta Abbu ga ta Hajiya, kowa ka kalla kasan ba karamin blow sakon ya bashi ba, a lokaci guda Allah ya nufi tafiyar su! Rayuwa kenan. Kwana uku gida ya watse Nima aka sallamoni a asibiti , na dawo gidan kowa ya kalleni yadda na rame na lalalce lokaci daya se hawaye ya fita a idanun shi, fada min rasuwar Hajiya ta Kara daga min hankali Amma ban nuna ba Dan ko magana banayi, bana kuka se idan Babu kowa na zauna nayi kuka na share hawayena, a Rana ta biyar Yan maiduguri suka zo, suka Mana gaisuwa, Mummy da Nanny ke kaina wajen tabbatar da naci abinci Kuma Ina nan, wani lokacin ji nake kamar na gudu na fada ruwa Nima ace na mutu da wannan kuncin da nakeji a cikin Raina. Da zasu tafi sukace suna so su tafi Dani nan Mummy ta nuna musu ita zata tafi dani Dan hakan se suka Mana sallama suka tafi, wani lokacin Ina jin inama na bisu may be da duk haka Bai faru ba, to Amma idan na kara wani tunanin se Naga duk abinda ya faru Dani dama is already written in my book, Dole ne ya faru Dani. Ranar sadakar bakwai aka watse ranar nayi kuka Dan Ina zaune kowa ya dinga bajewa sede su shafa kaina su ce min nayi hakuri, nayi kuka na rashin gata, na rashin madafa na rashin
sanin yadda rayuwa zata zo min. Abinda kadai ya rage min shi ne Nanny da Rooks. Nanny ta zauna gefena tace
” Ki ci abinci kinji, ko so kike kiyi rashin lafiya?”
Ina kuka nace
” Meye amfanin naci abincin, Abbuna ne ya mutu fa Nanny, banida kowa Nanny”
Ta rungumeni tana shafa min baya hawaye itama na bin fuskarta, tausayi na na dawainiya da ita, shigowar Mummy da Uncle Babawo yasa na Mike na nufe shi, ya rike hannuna Yana lallashina, se akai saa nayi shiru har Nasha tea. Fita sukai Shi da Mummy tace
” Ina ganin Zan tafi da ita kawai, kallonta is breaking my heart”
Ya shafa kanshi Yace
” Ita ce abin tausayi Kam, da nayi aure ni Zan dauke ta Amma Zan bar Miki kawai”
Washegari Suka zauan meeting akan fate Dina, Mummy ta dubi kawu Sa’idu da mamaki tace
” Yaya Sa’idu ni Zan tafi da Afiyya tunda kaga dama ta Saba da Rooks”
Ya dago idanu ya kalleta yace
” A’a ba zata je gidan wani ta zauna ba watarana ayi Mata Gori ni Zan rike ta”
Kawu Tijjani yace
” Eh da wannan dukda nasan Daddyn Rooks bazai taba haka ba, dama mafi Dadi ace mu mazan muka riketa. Sede Yaya ka Bari na tafi da ita kawai”
Ya Kara Bata fuska yace
” Ni Zan rike ta anan Ringim, magana ta kare”
Mummy ta hade Rai tace
” Yaya Sa’idu in har bazan dauki Afiyya ba to kaima ba zaka dauketa ba, Allah ya gani sede Tijjani ya tafi da ita, ya zaayi yarinya ta tashi a Abuja a dawo da ita Ringim”
” Ke wawiya ce Maryam, ke baa Ringim din aka haife ki ba? Mutuwa kikai da Kika girma anan. Kunji maganar banza”
Haka dai sukai ta musu aka tashi Babu dadi, Mummy tace musu Dole suyi fighting din Kawu Sa’idu ita Bata yadda dashi ba, washegari da suka je aka raba gadon Abbu, sannan aka raba na Hajiya nan ma yace se de a bashi nawa anan ne Uncle Babawo ya fito da will din Abbu kan dukiya ta ya damka ta a hannun Uncle Babawo haka kawu Sa’idu ya hakura. Bansan me ya faru ba kawai se dawowa sukai sukace Wai a gidan Kawu Sa’idu Zan zauna, Nanny ta bi Mummy dake ta kuka ganin Ina kuka Dan taji me yasa bazan zauna hannun daya daga cikin su ba, Mummy tace itama ba yadda zatayi she can’t fight him. Ina ji Ina gani aka tattara kayana duka aka maidani gidan Kawu Sa’idu Kuma yace Nanny ta tafi maiduguri!
a Mino dake zaune gefena,