WA NAKE SO CHAPTER 1
A kishingide yake kan wata lallausar dadduma irin ta manyan masu sarauta ta. Ba ajin komai a dakin sai karar AC. Dakin ya gama haduwa da kayan alatu kai ba kace a cikin duniya kake ba. Ga wani haske da ya mamaye dakin mai kara mantar da mutum a Inda yake, Yana sanye cikin shiga ta alfarma.
Daga kallo zaka san wannan mutumin ya hada mulki da kudi da mukami. Dan daga yanayin shigar sa da dakin da yake da yanayin walwalar fuskar sa ma abin kallo ne.
Sallama aka yi daga bakin kofa. Da kyar ya iya amsawa. Bayan ya dauki fin minti uku da jin sallamar Wani bawa ne ya shigo cikin shigar ja da blue din uniform din su na fada.
Zubewa yayi akasa yana fadi,
“Allah kara maka lafiya da nisan kwana.”
Yana daga kishingide da yake bai ko da motsa ba. Sai Hannu kadai da ya daga masa ba tare da ya kalle shi ba.
“Yallabai, Hajiya ce ke son shigowa.”
Dagowa yayi a hankali ya aika masa da wani kallo wanda yasa bawan nan shiga cikin hankalin sa. sannan ya kara daure fuska. Ya ce,
“Waya fada mata na shigo gidan?”
Cikin rawar jiki da tsoro da fargabar ya fara magana jiki na rawa ya ce,
“Allah taimake ka. Ban sani ba. Tazo dai ta ce, kai take son gani kuma na fada mata dokar da ka bayar amman tace nazo na fada make….”
Dagowa yayi ya watsa masa kallo kafin ya ce,
“Ya isa haka, amman kasan nace, bana son ganin kowa yanzu. Yanzu lokacin hutu nane,”
Tsaki ya saki.
Sannan ya ce,
“Kace mata bacci nake.”
Ba faden cikin rawar jikin abin bai kai da nisa ba ya amsa da
“To ranka ya dade.”
ya mike da sauri ya fita.
Tsaki ya sake saki. Dan a rayuwar sa ba abinda ya tsana kamar takura. Yana son hutu da nutsuwa. Dole ya bar garin nan. in ba sa’a yaci ba yanzu sai a kara zuwa ace yayi baki. Kai kenan bawa kullum cikin hayaniya da damuwar jama’a.
Ido ya lumshe, kamshin turaren ta ne ya doki hancin sa. Tsaki yayi ya bude ido.
Wata matashiyar yarinya ce tsaye a gaban sa. Fara ce amman bata da hanci haka nan idon ta kananu ne, sai dai Tana da kiba kuma bata da tsayi sosai.
Kai ya dauke ita kuwa ta zuba masa ido kamar taga wani abu. Tsaki yaja ya ce,
“Waya baki damar shigowa.”
Waje ta sama ta zauna ta ce,
“Ni kam har sai an ban damar shigowa wajen wanda nake sa ran zama miji na.”
Shiru yai mata. Ta ce,
“Wai kai me yasa sam baka bani wannan matsayin ne.”
Shiru ya kara. Ta ce,
“A gaskiya ya kamata muyi auren nan ko na samu na canja maka wannan halin naka.”
STORY CONTINUES BELOW
“Keeee!”
Ya daka mata wata tsawa wacce bata san sanda ta fado daga kan kujerar da take zaune ba.
Idon sa jajir saboda surutun ta har ya saukar masa da ciwon kai. Kofa ya nuna mata. Ya ce,
“Kika kara shigowa nan sai kinyi dana sani. Get out.”
Jiki na bari ido na zubar da kwalla ta mike ta fice. A ranta kuwa jin son sa da kaunar sa taji yana kara ratsa ta.
Shi kuwa tsaki ya saka yana dafe kan sa dan wani sara masa da yaji yayi. Kuma ba komai ya kawo hakan ba maganar ta da tazo ta cika masa kunne da hayaniya.
Mikewa yayi cikin tafiyar kasaita ya nufi wata kofa dake a cikin dakin.
Wani falo ne, madaidaici wanda yaji kujeru irin na gidan sarauta ta farare ne tas (royal chairs) sai kayan kallo da labulaye hadi da center carpet duk farare ne amman kai ba kace ana zama a gun ba dan yadda suke tas dasu sai daukar ido da suke yi gwanin ban sha’awa. Dakin sai tashin kamshi yake da sanyi AC da ta cika dakin.
Wata kofa ya kara dosa. Wacce ta sada shi da wani katon bedroom. Kayan gadon irin kayan falo ne sai dai Bed room din kan sa abin kalla ne. Dan shima an zuba masa kaya masu kyau ga kamshin sa na daban ne. Komai dai na bangaren nan da ka kalla kasan kudi bakaramin kuka sukai ba.
Babbar rigar jikin sa ya cire, ya rataye yana bin rigar da kallon tsana. Ya ce a ransa,
‘Shikenan mutun in yana gida kullum cikin saka wannan kayan. Tsaki yayi ya fara cire kayan jikin sa.
Farar fatar sa ta bayyana. Dan jikin sa yaji hutu sai kwanji da yake a mike dan duk jikin sa a murde yake ko dan training da ya sabar masa. Duk jikin sa gashi ne kwance luf luf bama saman kirjin sa. ban daki ya fada yayo wanka. Yana fitowa yaji wayar sa na kara. Kasancewa yasan ringing din ko waye yasa ya mika hannu cikin kasala ya jawo wayar.
Cikin daurewar fuska ya kara wayar a kunnen sa. Magana ake ta dayan bangaren wannan yasa yai shiru yana sauraro. Sai da aka gama sannan ya ce,
“Mamah na fada miki in ina hutawa bana son damu, Mamah yarinyar nan daga zuwan ta ta samin ciwon kai. Mamah shikenan ni ba zan samu hutu ba in nazo gida na huta. Haba Mamah in kuma ban zo ba ku damu dan Allah Mamah kuna bari na ina hutawa a gun aiki ba hutu anan ma in nazo na hutu baza ku bar ni ba.”
Ya gama fadi yana dafe kansa dan ko maganar da yayi ba karamin gajiyar dashi tayi.
Mamah ta can gefen ta cika da mamakin yadda Baban nata yau yai magana haka mai tsayi. Lallai an kai shi bango dan ko ita mahaifiyar sa ta san in za ta shekara tana son suyi hira bai fiye biye mata ba daga eh sai a’ah suke nan.
Hakuri ta bashi. Tana fadin.
“Kayi hakuri Baba nah ai ban san hutawa kake ba kuma ni da ta tambayen zata gun ka bama zan bar ta ba amman kayi hakuri kaji.”
Ajiyar zuciya ya sauke sannan ya ce,
“Gobe zan koma ma.”
Da sauri ta tari numfashin sa ta ce,
“A’ah ka bari ka karasa sati biyun da kace zakayi man.”
Kai ya girgiza ya ce,
“Mamah bazan iya ba. Daga wannan sai wacan ji fa Mamah, yanzu anjima kadan zakiji Abbah ya aiki naje fada. Mamah ni bana son irin wannan rayuwar ta ku wallahi duk takura mutum yake.”
Ya karasa maganar da kyar kamar zai yi kuka. Mamah ta ce,
“Ka dai bari zuwa weekend ka tafi.”
Bai son musu da doguwar magana wannan yasa ya amsa mata da Toh Kawai.
Yana gama wayar ya dafe kai har harbawa kan sa yake, ido ya lumshe can ya bude ssu.
A ransa ya ce,
‘In har na tafi sai kun neme ni zaku ganni. Daga wannan yarinyar sai mutane.’
Tsaki yayi ya haye gadon sai kuma ya saki dan gajeran murmushi wanda in ba jin sa yayi a mood din da yake so ba baya taba yin sa.
Wanda murmushi shi kan sa ba wani yalwatate bane. Amman ba karamin kyau ya karawa fuskar sa ba geen kumatin sa ya lotsa fuskar ta cika da yalear rahamar dan murmushi rahama ne.
Mood din kuwa bai wuce ya ganshi zaune shi kadai ba a gu mai shiru da ni’ima to anan zaka ga dan murmushin sa shima ba wani murmushi bane kawai dai zaka ga fuskar sa a dan sake.
STORY CONTINUES BELOW
Mamah kuwa bayan sun gama wayar ta sauke ajiyar zuciya. A ranta tana mai jin son dan ta na kara shigar ta. Duk da wannan halin nasa tafi son sa a cikin ya’yan ta gaba daya. Haka ma mai martabba yafi son sa. Ko yan uwan sa suna masifar son sa. Sai dai shi fa ba fuska bare har ka nuna masa.
Ko mahaifiyar sa daga gaisuwa yake dinke bakin sa yayi shiru sai dai in ta tambaye shi abu shima daga uhm sai A’ah ko Eh ko a daga kai ko a girgiza.
Tana mamakin sa shi wannan mulkin yai masa yawa. Da kyar ta fahimci halin sa. Wannan yasa ta kyale shi take bi da shi ta yadda yaso. Sai dai addu’a da fatan samun nasara da cigaba a rayuwa.
Ita Mamah tana zaton in har yai aure matar sa zata gyara masa wannan halin nasa. To amman sshi bai kawo maganar mata ba. Ita kanta tasan a irin wannan halin sa ba ko wacce mace ce zata iya tinkarar sa ba saboda tsare gidan sa.
Kuma a ssanin halin sa ma tasan shima bazai tsaya kula mata ba duk da tasan mace dai a bar ta.
Sam Kuwa mace bata gaban sa, bata ma a lissafin sa. Shi fa a rayuwar sa in ba Mamah da kanwar sa ba yakan manta da mace, mutum ne wanda bai da jin mace, wato feeling kuma Allah bai yi shi mai sha’awa ba.
Ko da yake akwai ibada dan azumi kullum cikin yin sa yake. ban da addu’a ta sa da ta iyaye da yan uwa akan Allah ya tsare shi da imanin sa. Ya sanya tsoron Allah a zuciyar sa. Mata na son sa amman ko tinkarar sa basa yi.
Bacci yayi dan sai karfe uku da ashirin ya tashi. Wanka ya kuma yi yai alwala ya shirya cikin wata sky blue din shadda dinkin riga da wando tazarce wacce tai masifar yi masa kyau.
Ko da yake shi me kyau ne daman can. Turare yai wanka da shi, ya hau kan sallaya ya fi minti talatin yana sallah sannan ya sallame ya zauna yai azzkar sannan yai addu’a akalla sai da ya dau awa guda yana ganawa da ubangijin sa da kai masa bukatun sa sannan ya mike ya fito karamin falon sa inda dining din sa yake.
Wajen shake yake da kayan abinci na gargajiya da na zamani. Zama yayi ya bubude fulas din, al kubus ya gani da miyar agushi shi yai sha’awa dan in ba yana gida ba yana manta menene alkubus ma bare ya ganshi ya ci.
Shi kadai yaci ya kora da lemon zobo da Mamah tayi masa da kanta dan tasan yana son sa.
Sai da ya gama yai hamdala sannan ya mike ya koma babban falon sa. Bai jima da zama ba akai kwada sallama. Daman yasan hakan zai faru.
Da kyar ya bude baki ya amsa. Wani ba fade ne, ya zube a gaban sa. Yana kwasar gaisuwa. Hannu ya daga masa kadai.
“Ranka shi dade. Mai martaba na son ganin ka wai kayi baki sun zo maka barka da zuwa.”
Kamar bazai magana ba ya dago ya kalle shi ya ce,
“Kaje kace ina zuwa.”
“Angama ran ka shi dade.”
Ya mike ya fita.
Mikewa yayi cikin tafiyar sa ta kasaita da mulki ta kofar baya ya fara yin cikin gida.
Bashi da tazara da Mamah dan daga part dinta ssai na shi. Dan da duk part din ta ne ma ta sa aka fitar masa da shi dan yadda take son ssa.
Ta cikin lambu da ya raba tsakanin part din Mamah da nasa ne ya shigo ta kofar da ba kowa kebi ba daga shi ssai Mamah ko kuwa kanwar sa da mai martaba.
Lambun kan sa abin kalla ne an kawata shi da bishiyu da flowers kala kala in ka kalli wajen kai ka zata a wata kasar kake ban da gun shakatawa da wajen swimming dake gefe sai grasscarpet da ta kawata wajen gun abin sha’awa da ka shiga gun wani sanyi mai dadi da ni’ima zai ziyarce ka.
Ko da kana cikin bacin rai ni’ima da kyan waje. zai sanyaya maka rai. Bare kuma ka zauna kana ganin tsuntsaye da shakar kamshi da sanyin wajen.
Bangare ne guda wanda yake katon gaske an kawata shi da ado da kayan gidan sarauta haka anan yaji kayan alatu da more rayuwa masu tsada.
STORY CONTINUES BELOW
Yana shiga kamshi da sanyin dakin ya doke shi. Ido ya lumshe sannan ya bude, karamin falo ne wanda aka zuba masa komai ja da baki.
Tafiya ya cigaba har ya wuce ta faloli guda uku masu kyau da tsari da kayan more rayuwa.
A can babban falon ta inda ta saba zama da yamma ya same ta.
Wata datijuwar farar buzuwar mata ce, wacce ta ci ado da kaya masu kyau da tsada. tana zaune bayin ta na baje suna tai mata hidima. Suna ganin sa suka hau barin wajen bayan sun mika masa gaisuwa. Da hannu yake amsa har suka gama suka gama suka fice.
Kansa a duke ya ce,
“Mamah barka da hutawa.”
Cikin fara’a da jin dadi ta amsa da
“Yauwah Baba nah. Ka fito kenan.”
Kai ya gyada mata kawai. Ya nemi gefen ta ya zauna.
“Kaci dai abincin ko?”
Nan ma kai ya gyada mata.
“To ba abinda kkake bukata.”
“Babu!”
Ya fada a takaice. Kallon sa tayi ta saki murmushi ta ce,
“Ya kamata ka fin ka tafi kaje kaga yayun ka a gida ko?”
“Toh!”
Shiru sukai gane ta gama fadar abinda zata fada yasa ya dukar da kai ya ce,
“Zani gun Abbah!”
“Allah kiyaye. Kayi addu’a ka karanta hasbunallahi wani’imal wakil, da lahaula wala kuwata illa billayil aliyul azim kafin ka fita daga nan haka nan kan k shiga cikin fada. Allah ya tsre ya kiyaye min kai.”
Kai ya gyada yana fadin,
“Nagode Mamah.”
“Allah maka albarka.”
“Ameen!”
Mikewa yayi a hankali ya karasa bakin kofa sai da ya tsaya yayi duk abinda mamah ta fada sannan ya. fita. Tin daga fitar sa aake gaida shi baya amsawa sai dai zai daga hannu kawai. dan zikirin da Mamah tasa yayi shi yake tayi. Inda samo ya saba kullum Mamah cikin bashi wadan nan zikiran take yi wanda shi kan sa yana jin dadin su. Suna dada masa kwarjini da kariya a jikin sa.
A haka har ya karasa fadar da mai martabba yake zama da yamma.
Fadar cike take da jama’a, yana zuwa aka fara zube masa, ana masa kirari, wanda shi ciwon kai ya haifar masa ma.
A hankali yake tafiya har ya karasa kofar fadar, yana tafiya yana karanto addu’oi a cikin ran sa. nan ma gaisuwa aka farai masa ana kirari.
Shiga yayi yayi gun mahaifin nasa.
A kasa ya zauna ya dukar da kansa. Mahaifinsa ya dafa sa,
“Barka da Yamma Abbah!”
“Bar ka dai ‘dana, ya gajiya.”
“Babu.”
“Tin dazu kai baki amman aka ce kana bacci.”
Kai ya gyada masa.
“Mun basu masauki kai kawai suke jira!”
“Nagode Abbah.”
“Tashi kaje suna can suna jiran ka.”
Yana mikewa fadawa suka nufo shi suna masa kirari da yabo. Zasu raka shi ya daga musu hannu alamar baya so kenan.
In da sabo sun saba dan kullum suna tare da shi amman kullum in suka nufo shi sai ya dakatar dasu, abinda yake sawa yake fita ta kofar Mamah kenan da ya gujewa haduwa dashi su taso shi a gaba kamar wani yaro ko wanda ake nema yayi laifi.
Tin iyayen na fada har suka gaji suka zuba masa ido sai dai addu’a Allah ya tsarr shi.
A hankali ya shiga dakin da akace yana da baki. Bai yi mamakin irin manyan mutanen da ya gani ba dan ba yau ya saba ba. Sai dai a ciki ba yace wannan wane bane waccan wane bane, a fuska dai ya san su dan sun saba kawo masa wannan ziyarar in dai yazo garin nasu.
Abokan mahaifin sa ne, amman da yake mahaifin nasa mai mulki ne, wai su da kansu suke zuwa gaishe sa.
Zama yayi suna gaigaisawa har suka tafi. Sannan aka fara shigo da jama’a daya bayan daya ana masa sannu da zuwa.
Can sai kuma fadawa suma suka shigo,
“Ranka ya dade Allah ya kara girma Allah yasa a gama lafiya Allah tsare ka daga sharrin makiya. Dan sarki jikan sarki, takawar ka lafiya gaba salamun baya salamun. Allah ya cika buri.”
“Ameen!”
ya fada cikin kasaita.
Sai mangariba ya samu kansa. Suna yin sallah ya bacewa mai martaba dan yasan da ya ganshi ba zai bar shi shiga ciki ba. Dan haka suna idar wa yayi cikin gida. Wanka yayi ya saka three quarter wando na kakin sojoji da farar riga mara nauyi.
Zama yai a falon sa yana kallon new yana shan fruit. Har akai isha’i ya mike yai sallah ya dawo ya zauna. Sai tara ya mike ya shige daki.
Wanka yayi ya fito ya tsaya gaban madubi yana feshe fashe da shafe shafe. Sai da ya gama sannan ya hau kan gadon sa.
Al kur’ani ne a kan site dorowar sa, dauka yayi ya fara karantawa azuciyar sa. Har karfe goma sannan ya ajiye ya mike yayo alwala ya hau kan gado. Ya jima yana addu’a samnan ya tofe ko ina ya kashe fitila ya kwanta.
Karfe uku ya mike, bandaki ya fada yayo wanka yai alwala wata jallabiyya ya saka milk kala, ya feshe jikin sa da turare, ya saka wata brown hula tashi ka fiya naci sosai yayi kyau da shi. kai ka rantse balarabe ne. kan sallaya ya hau, sallah raka’a biyu yayi wacce ta dauke shi awa daya sannan ya zauna ya fara lazimi. Ba shi ya mike ba sai da yaji ana kiraye kirayen sallah a waje.
Massalaci ya tafi. Acan suka hadu da mai martabba. Sai da aka idar da sallah sannan suka gaisa. Daga nan xama ya cigaba da yi a massalacin sai da yayi karatun alkur’ani ya kai izifi uku sannan yai aazkar ya jima yana addu’a, Bashi ya baro massalaci ba sai karfe bakwai.
Ya fito yana tafiyar sa ta kasaita mai ban sha’awa a haka ya shiga bangaren sa. Yana shiga ya doshi wani daki dake cikin bedroom din sa. Kayan training ne kala kala a ciki. Rigar jikin sa ya cire ya rage daga shi sai threequater wandon sa. Training ya fara yi. Ba shi ya gama ba sai karfe tara da rabi.
Yana gamawa ya sha ruwa sannan yai wanka ya shirya cikin manyan kaya milk din shadda da brown din hula. Half cover takalmi brown ya saka sai brown agogo. Wanka yayi da turare ya nufi dining.
Yau ma dining din cike yake da kayan abinci kala kala. Na gargajiya da na zamani. Zama yayi ya dibi kunun gyada da yaji madara. Sai masa da miyar taushe da yaci.
Sai da ya ji ya koshi sannan ya mike ya fita. Tafiya yake cikin kasaita fuskar nan tasa a hade har ya karasa bangaren mahaifiyar ta sa.