WA NAKE SO CHAPTER 10
Tin daga lokacin kuma Momy ke kula dani sosai dan bata bari na na zauna ni kadai kullum cikin min abinda zai dauken kewa suke ita da Yaa Kamal dan Suraiyya ta shiga busy rabon invitation card.
Samun kulawa a gun Momy sai ya kwantar min da hankali sosai dan ban fiya sa tunani ba sai dai in naje bacci da kyar nake yi saboda tunanin Fu’ad ga zuciya ta dake ta min zafi da radadi wanda na rasa saboda me duk maganin da nake sha a banza.+
Wani lokacin sai na sha maganin bacci nake samun da kyar baccin ya dauke ni sam bani da kwanciyyar hankali na rame sosai. Son Fu’ad ke dawainiyya dani. Ga kewar sa. Muryar sa kadai nake son naji amman ba hali duk na shiga tashin hankali.
Yau tin da na tashi da wata kewar sa na tashi wanda ji nake in banga Fu’ad ba ba zan iya kaiwa ba. Sosai hankali na ya tashi fa da gaske ji nake kawai ni shi din nake son gani ko ta halin ka’ka.
Tunani na fara shin ni a ina zan ga Fu’ad bayan kullum sai na kira wayar sa sau ba adadi amman a kashe. hajiyar sa na kira mu gaisa bata taba ce min sunyi waya da Fu’ad ba.
Waya ta na dauko na fara dailing number Hajiyar sa bayan ta dauka nace
“Ina yini?”
“Lafiya lou Fateema ya jikin?”
“Alhamdulilh!”
“To Allah kara sauki “
“Amin nagode.”
Shiru nayi na rasa me zance can nace
“To sai anjima.”
“Tace ki gaida Hajiyar.”
Nace
“Toh!”
Na katse wayar. Komawa nayi na kwanta ina dafe zuciya ta dake min zafi tana buga min da sauri da sauri.
Mikewa nayi na fita Falo. Momy na sama zaune ita kadai dan Suraiyya ta tafi lalle dan anjima ma za ai kamun ta. Kallo Momy ta bini dashi. Zama nayi nai kasa da kai ina wasa da zoben hannu na nace
“Momy daman Abu zanje na dauko a can gidan.”
“Waye zai kaiki?”
“Driver ne.”
“Ok kada kije ki zauna. Zanyiwa Hajiyar tasa magana ma akan za a kwashe kaya dan gwara a kwashe kawai.”
Da sauri na dago nace
“Saboda me?”
“To me za a bar su suyi a can ehee?”
Kai nayi kasa dashi na mike na shiga daki. Ni da za abi tatawa abar min kayan ina zuwa ina ganin gidan shima zai ragen wani abu. Hijab na saka na fito kafata sanye da flat shoe.
Momy na zaune nace
“Na tafi.”
“Sai kin dawo.”
Ta fada na fice. Drivern mu na zaune tare da me gadi na karasa wajen sa. Bayan na gaishe su nace
“Zaka kaini gida ne zan dauko abu.”
Da sauri ya mike ya dauko mota na shiga muka tafi. A bakin gate yai parking na fito na kalle shi nace
“Kaje zan kira ka in na gama.”
“To ranki yadade.”
Ya fada ya tada motar ya tafi. Bakin gate din na nufa na saka key na bude Babban gate din na shiga cikin. Compound din na dinga kallo sannan nayi entrance din gidan Change over na kunna sannan na karasa wajen kofar na saka Key na bude.
Dakin na nan a yadda yake bai komai ba sai dan kura da yayi. Hijab na cire nayi bedroom dina. Gyara dakin na hau yi na gama na share nayi mopping na shiga na wanke bandaki sannan na nufi dakin Fu’ad.
STORY CONTINUES BELOW
Ina shiga kamshin sa yai min sallama. Ido na lumshe nace
“I miss u. I miss ur Fragrance!”
Na dauki jallabiyar sa ina shinshinawa. Na jima a haka sannan na share dakin na wanke masa bandakin sa. Na fito main Falo na hau gyara shi na share nayi mopping na saka turaren wuta gidan ya dau kamshi. Tsayawa nayi a falon ina kare masa kallo.
Hawaye ne ya zubon a ido na naji nayi kewar gidan kawai. Ji nayi ina son moment din da nayi spending a gidan da su dawo. Kan kujera na fada ina sakin kuka
“Why Fu’ad? Why? Why?”
Na fada ina fashewa da wani kukan
“I love u. Wallahi i really love u.”
Na fada ina mai cigaba da kukan. Na jima a gun na mike na koma dakin Fu’ad. Kan gadon na hau na ja filo na kwanta ina rumgume da jallabiyyar sa kamar za a kwace min ita. Ina kwance ban san lokacin da bacci ya dauke ni ba sai jin kiran salah magariba nayi. Da sauri na mike ina kallon inda nake.
Jiki a sanyaye na shiga bandakin na dauro alwala na fito na tada sallah sai da na idar nai addu’a sannan na mike na fita wayata na dauka naga missed call din Momy da Suraiyya har da Yaa Kamal.
Momy na kira tace
“Kina ina ne tin dazu nake kiran ki zanje wajen kamu kin koma gidan ne?”
“A’ah yanzu zan koma!”
“A ina kika tsaya?”
“Ina gidan!”
Shiru Momy tayi can tace
“To maza ki kamo hanya ki taho dare yayi ko da yake bari na turo Kamal ya dauke ki.”
“Toh!”
Na fada na kashe wayar. Dakin mu na shiga dan dauko album din bikin mu sai dai me ba ko daya. Wannan yasa na hau duba amman ban gansu ba koma agun na ajiye. Ina tsaka da dubawa Yaa Kamal ya kira yace
“Ina jiran ki a waje.”
“Gani nan!”
Na fada ina mikewa ganin ban gansu ba. Fita nayi na rufe kofar sannan na kashe wutar gidan na fita compound din ina jin kamar kar na tafi ko anjima Fu’ad zai dawo. Duk da a raina na na saka sai na dawo duba Album din nan.
Ina fita na rufe gate din sannan na nufi wajen motar Yaa Kamal da yai parking a kofar gidan. Gidan gaba na bude na shiga ina fadin
“Ango barka da dare.”
“Yauwah kanwata. Me kika zo yi nan ne?”
Ya tambaya yana tada motar muka dau hanya.
“Abu nazo dauka kuma ina cikin dubawa kazo ban ma ganshi ba.”
“Amman tin yamma fa kika taho.”
“Na gyara gidan ne.”
Na fada ina kallon titi. Kallo na yake cike da mamaki sannan yace
“Gyara gidan kuma bayan Momy tace kayan ma za a zo a kwashe.”
Da sauri na dago ina zaro ido nace
“Saboda me?”
“Saboda me?”
Ya dawon da tambayar sai kuma ya girgiza kai kawai yace
“Ke kin fiso a bar kayan su lalace a haka ne?”
“But ka sani ko ya dawo..”
“In ya dawo me zai miki Fateema?”
Yaa Kamal ya tambaya yana kallo na. Ido na ya kawo ruwa kai ya girgiza yace
“Kada ki manta yanzu ba aure a tsakanin ku ko ya dawo to menene na jiran nasa Fateema ya kamata ki fuskanci rayuwa yanzu dai aikin ki nake so ki fara gudanar wa a asibitin ki.”
Kai na na jingina a jikin kujera ido na na zubar da hawaye. Kallo na yayi ya dauke kai yace
“Kukan nan ba wata mafita bace. Addu’a zaki rika sannan ki samawa kanki mafita shiyasa nake son ki fara aikin zai debe miki kewa sosai.”
Ban kara magana ba shi ya dinga kidan sa yana rawa na lallashi na. Amman ni ban da kuka ba abinda nake. Dan sam na manta wai saki uku ne tsakanin mu da Fu’ad.
Yanzu iya tarihin soyayyar tamu kenan. Yanzu wannan shine son da Fu’ad ke min. Hakika Fu’ad yai min gurguwar fahimta domin nafi son sa akan Yaa Fauwaz nafi son farin cikin sa akan na Yaa Fauwaz. Saboda me yai min haka?
STORY CONTINUES BELOW
Ido na runtse dan har zuciya ta ta fara min zafi da radadi. Dai dai lokacin da muka shiga gida yai parking kenan. Jin an tsaida Mota yasa na bude ido na ganin mu a gida na bude motar na fita.
Da kallo ya bini yana girgiza kai. Ina shiga na wuce daki na. Kan gado na fada ina sakin kuka mai taba zuciya. Domin na rasa me yake min dadi komai ba dadi zuciya ta ta min zafi ga radadi da take min kai na ya hau sara min wannan yasa na mike na balli magani na sha sannan na koma na shige bargo na kwanta. Ina duba hutunan Fu’ad na cikin wayata jin son sa da kaunar sa nake tana kara shiga min cikin zuciya ta.
Saboda magungunan da na sha nan da nan bacci ya dauke ni cike da tunanin Fu’ad. Wanda har da mafarkansa.
Karfe tara Momy ta dawo daki na ta shigo ta tadda ni ciki bargo karasowa tayi ta zauna a gefe na sannan ta dan yaye bargon. Kallo na ta tsaya tana kallon yadda nake sauke ajiyar zuciya alamar nayi kuka kenan. Tin daga yadda taga ido na ya dan tasa tasan nayi kuka.
Ta jima zaune tana kallo na tausayi na da kaunata na shigar ta. Da kyar ta mike ta fita dan ta watsa ruwa itama ta kwanta.
*
**
***
****
*****
******
Tsakanin Aisha da Aliyu kuwa shakuwa ce ta kuma nisa sosa. Dan in daya bai ga daya ba ya ta shiga tashin hankali da damuwa kenan. Dan ma yanzu da waya sai abun ya ragu dan ko gida ya koma bayan sun rabu sai sunyi waya. Haka da safe kan ta tafi makaranta da ta dawo kan ta tafi isilamiyya sannan da ta dawo daga isilamiyya yake zuwa.
Wannan ya kara sawa suka shaku fiya da tunanin mai karatu wanda basu da buri da bege sai na kasancewa da junan su sam basa gajiya da junan su a haka kuma Aliyu ke kara tusa son sa cikin zuciyar Aisha.
Dan in yai mata wasu sakonin sai su daure mata kai wanda irin sakonin kuma in ta karanta sai taji dadin su.
09:00pm
Kwance take cikin bargon akan katifar ta. Da yake damuna ce an sha ruwa tin wajen karfe biyu ake ruwa har akai magariba garin yai sanyi dan haka tana cikin bargo kewar sa na damun ta domin kuwa yau bai zo ba saboda ruwan da aka sha.
Idon ta a lumshe yake ba abinda take sai tunanin sa. Ta kan rasa dalilin da yasa baya barin cikin tunanin ta dan sai dai bata kadaita ba kai ko bata kadaitan bama sai yana fado mata dan kusan yanzu in ta zauna sai dai ta ji an taba ta dan ana ta magana ma bata ji ba.
Yanzun ma hakan ce ke faruwa domin kuwa har ya kira wayar ta sau biyu bata dauka ba sai da ta gyara kwanciyya fuskar ta ta fuskanci wayar sannan ta ga wayar na haske wannan yasa cikin kasala ta mika hannu ta dauki wayar tana kallon allon wayar *Yaa AK* ta gani rubuce ajiki wannan yasa ta dannan ok ta kai kunnen ta.
“Assalamu alaikum!”
Muryar sa mai dadin sauraro tai mata sallama sam bata san ta lumshe ido saboda yadda muryar ta shige ta ba. A hankali ta bude idon sannan ta amsa masa sallamar da
“Wa’alaikum salam!”
Itama cikin sanyin murya.
Wanda yasa tsigar jikin Aliyu mikewa. Duk da yana kwance shima a kan katon gadon sa wanda ya rufa da bargon sa iya kan sa ake iya hangowa kawai yace
“Ya kike yan mata na?”
Baki ya dan turo ta shagwabe tace
“Lafiya kai fa?”
“Alhamdulillah amman me yake damun ki? Ko bacci kika fara ne naga na kira har sau biyu baki dauka ba.”
“Hmmm Ba komai. Kuma kasan wayar na kusa dani amman banji ba sai da na gyara kwanciyya na gani.”
“Why?”
“Nima ban sani ba “
“Uhm uhm Aysherr fada min gaskiya ko dai tunanin saurayin naki kike?”
“Nifa ban da wani saurayi da zan tsaya tunanin sa.”
“Har ni?”
Shiru tayi. Yai murmushin sa mai kyau da sauti yace
“Kina ji na?”
“Uhmm!”
Ta fada yace
“Nace har ni?”
“Ai kai ba saurayi na bane”
“Au haka ne fa. To in nace a ban matsayin saurayin naki fa kanwata?”
“Ai kana da matsayin da ya wuce na Saurayi na.”
“Haba?”
“Sure!”
“Kenan in nace ina son wancan matsayin zan iya samu?”
Murmushi kawai tayi tace
“Wai kai ina iyalan ka ko ba a garin nan suke bane?”
“Me kika gani?”
“Kawai dai!”
“Suna garin nan Aisha. Ina da mata daya.”
Shiru tayi dan sai taji gaba daya bata ji dadin yadda yace mata yana da mata daya ba.
“Are u there?”
Ya tambaya jin tayi shiru. Wanda shi ya dawo da ita daga tunanin da ta fara tace
“Yes!”
“Why silent?”
“Nothing!”
“Kin tabbata?”
“Eh!”
Sukai shiru sai can tace
“Ya’yan ka nawa?”
Dan murmushi yayi domin a gaskiya Aliyu yana son yaga by now shima ya fara tara iyali dan kannen sa ma suna da ya’ya bare shi. Yana son yara sosai dan haka tambayar da Aisha tayi masa kamar fami ne akan abinda ke damun sa. Cikin sanyin murya yace
“Bani da yara!”
“Allah kawo masu albaka!”
“Ameen dear.”
Sai suka kara shiru. Mikewa yayi zaune yace
“In tambaye ki mana?”
Kai ta gyada itama ta mike zaune tana jan bargon da ta rufa zuwa saman cinyar ta. Sanye take da kayan bacci ash kala. Rigar mai dogon hannu da wando. Ido ta lusmhe sannan tace
“Eh!”
“Zaki iya auren me mata?”
Jin tambayar tayi har tsakar kan ta wanda hakan yasa ta zame ta kwanta batai niyya ba.
A hankali tace
“Meyasa kai min wannan tambayar?”
“Aysher ina son muyi magana ta fahimtar juna ni dake. dan haka ki ban hankalin ki kuma dan Allah kada ki boye min komai kinji?”
Kai ta gyada kamar yana gaban ta tace
“Insha Allahu ba zan boye maka komai ba.”
“Gud Girl. Answer my question first to.”
Shiru tayi can tace
“Menene da auren mai mata Yaa AK? Ni ba da matar zan zauna ba tinda ba xaman ta nake ba zaman miji na zanyi dan haka a tunani na ba ruwa na da harkar ta my business is with my husband shine in kula dashi da masa biyayya.”
“Gud. A tsarin rayuwar ki ya kike ganin yanayin kishin ki?”
Shiru tayi tana tina a da in Yaa Muhammad yana bata labarin yan matan sa ta dinga gwasale shi tana kushe su da hata rai. Har wata rana yace
“Kai Aisha amman kishin ki yai yawa.”
Duk da a lokacin tana da karancin shekaru. Sai ta fara tunani ace tana son mutum kamar ta mutu shin ya zata ji in taga wata a tare dashi tana son sa ko makamancin haka.
Ido ta runtse dan har zuciyar taji ta baci wannan yasa tace
“Duk macen da bata da kishi ai ba mace bace kuma ina jin sai dai in bata son abu shine ba zatai kishin sa ba. Amman inda so dole akwai kishi.”
Murmushi yayi domin Aisha akwai hikima ba zata fito ta fada masa actual abinda yake son yaji ba sai ta bashi a bai bai to ba komai hakan ba.
“Gaskiya ne! Kinga kenan kada kiga laifin wanda yayi kishin ki akan wani abu ko?”
Murmushi tayi tai shiru kawai.
“Ki fada min kina da saurayi?”
Gaban ta taji ya fadi duk da ba yau ya farai mata wannan tambayar ba amman meyasa take ce masa bata dashi. Ko dan ta dauki Yaa Muhammad a dan uwan ta ne bata fiya kallon sa a saurayin ta ba.
“Aysher!”
Ya kira sunan ta a hankali. Wanda shi ya dawo da ita daga tunanin da ta fara yi.
“Na’am!”
Ta amsa masa a hankali itama dan gaba daya jikin ta ya fara sanyi da wannan tambayoyin nasa.
“Nace kina da saurayi ne?”
Shiru ta kara yace
“Hmmm to menene a ciki feel free and tell me Kinji?”
Kai ta gyada tace
“A tarihin rayuwa ta na fada maka komai ai. Abu daya ne ban fada maka ba shine Yaa Muhammad zan aura!”
Damm! Kirjin sa ya buga da karfi. Amman ya dan dake yace
“Did u love him?”
Duburburcewa tayi ta rasa me zata ce masa.
“Aysher ki ban amsa mana. Kin min alkawarin fadan gaskiya ta duk tambayar da zan miki right?”
“Sure!”
“Uhmm kina son sa?”
“Yaa Muhammad ai dole na so shi. Ya min abinda ko Mamah na batai min shi ya kula dani har a yanzu ma yana kan kula dani tayaya ne xan kasa son wannan bawan. Gaskiya i feel i can do everything to makes him happy domin nima yana min duk abinda zai sakani a farin ciki.”
Take mood din Aliyu ya canja ya yaye ragowar bargon da ya dan lulluba dashi dan take yaji ya daina jin sanyin duk kuwa da sanyin da ake zubawa.
Jin shirun nasa yai yawa tace
“Are u there Yaa AK?”
“Uhm!”
Kawai ya fada
“Naji kayi shiru!”
“Ina tunani”
“Thinking of what?”
“Aysher!”
Ya kira sunan ta a hankali kamar bai son ya kira. Tsigar jikin ta ce ta tashi ta kara jan bargon jikin ta, ta rufa sannan murya na rawa ta amsa da
“Na’am!”
Ido ya lumshe sannan ya bude a hankali yace
“Me kike ji game dani?”
Ido ta zaro dan ji tayi kirjin ta yai mata wani irin nauyi da tambayar sa. Take ta ji jikin ta ya fara rawa cikin rawar murya tace
“Uhmm m… Me ka kace?”
Murmushi yayi wanda iya kar sa baki yace
“Eh nace me kike ji game dani?”
Ido ta dan kara zarowa dan kan ta ya riga da ya kulle ta kasa gane tambayar tashi. Wani sanyi taji yana shigar ta kanar bata rufa ba.
“Ni ban gane tambayar ba!”
Ta fada tana dunkulewa waje daya domin kuwa sanyin da take ji kara daduwa yake yi ga yadda jikin ta ke rawa ta rasa na menene.
“Kin gane Aysher ki daure ki ban amsa ta please!
Ya fada a hankali kamar bai son maganar. Kirjin ta dake dukan goma goma ta dafe tace
” Ni ban sani ba amman ina jin abu mai kyau game dakai wanda ban san ya yake ba. Yaa AK kai fa?”
Murmushi yayi yace
“Zan baki amsa but in na gamai miki nawa ko?”
Kai ta gyada tace
“Toh!”
Shiru sukai na kusan minti biyu sannan yace
“Aysher!”
Zuciyar ta ce ta buga domin yadda yake ambatar sunan ta ma kadai daban ne wanda har tsigar jikin take tashi. A hankali ta amsa da
“Na’am!”
“In nace ina son ki how will u feel?”
A razane ta mike wanda yasa wayar hannun ta, ta subuce ta fadi da sauri jiki na rawa ta dauko. Ji tayi dama wayar ta mutu ta huta.
STORY CONTINUES BELOW
A kunne ta saka ta a hankali tace
“Me kace?”
“Uhmm nace innace ina son ki ya zakiji”
“Bangane ba?”
“Kingane Aysher ki daure ki ban amsa dan Allah.”
Wani fitsari taji ya taho mata wanda ta mike tsaye da sauri. Kan tai magana taji wayar ta katse da sauri ta nufi kofa ta fita ta shiga bandaki dan kama ruwan.
Wayar sa ce tayi shutdown dan ba charge wannan yasa cikin hanzari ya jona ta a charge. Jikin sa na rawa dan ya fiso a yau suyi ta ta kare kawai ya fallasawa Aisha sirrin zuciyar sa ya huta.
Tana gamawa ta shigo daki ta hau katifar ta taja bargon tana rufe har kan ta. Tunani ta fara wacce amsa zata bawa Yaa AK. Shiru tayi tana sake sake can dai ta lalluba Wayar ta dake gefe ta dauka ta hau dubawa taga text din Yaa Muhammad da ya turo mata. Budewa tayi tana karantwa kamar haka
_Assalamu Alaikum Kanwata ya kike ya na barki lafiya? Na kira naji ya kike? Sai naji linebusy dawa kike waya ne?_
Ido ta zaro ta rasa me zata ce masa. Kin tura masa reply tayi dan taga tin 09:30 ya turo text din gashi kuma yanzu 11:23 zai ce me take batai bacci ba kuma ita bata san me zata ce masa ba.
Wayar na yin 5% ya kunna ta a ransa yana addu’a Allah yasa batai bacci ba. Number tata ya fara dailing yaji ta shiga. Shiru yayi yana son yaji ta dauka.
Tana tsaka da wannan tunanin taji wayar na vibration wannan yasa ta dauko ganin Yaa AK yasa taji gaban ta ya fadi a hankali ta dauki wayar ta kai kunnen ta tana fadin
“Assalamu Alaikum!”
“Wa’aialaikum salam! Kinji wayar ya katse ko?”
Ya amsa cikin zumudi da batai bacci ba.
A hankali ta amsa da
“Eh!”
Domin jikin ta yai masifar jin sanyi ga yadda kirjin ta ke bugawa kamar wata mara gaskiya.
Numfashi yaja yace
“Ashe charge ne ya kare.”
Kai ta gyada a hankali tace
“Ayyah!”
Yai murmushi a hankali yace
“Muna magana ko?”
Tsigar jikin ta taji ta tashi tace
“Eh!”
Ya dan shafa sumar kansa sannan yace
“Ina sauraron ki.”
Shiru tayi sai kuma tace
“Ni ban san me zance maka ba.”
Murmushi yayi mai sauti yace
“Kamar ya? In nace ina son ki zaki amshi ni muyi soyayya?”
“Yaa AK ai sai kaga mutumin ya maka ko?”
Ta fada tana toshe bakin ta dan bata san maganar ta fito ba.
Ya gyada kai yace
“Haka ne. Kin tinon da abu to ni na miki?”
Ido ta zaro hannun ta har lokacin akan bakin ta takasa yin magana. Wani murmushin ya kuma yace
“Ok shikenan fadan irin mijin da kike son ki aura.”
Shima shiru tayi wayar ya dauke a kunnen sa yana kallon allon wayar sa ya ga tana kan connecting dan haka yace
“Aysher!”
Kasa amsawa tayi. Ya kara kiran suna da
“Aysher!!”
A hankali kanar kar tayi magana tace
“Na’am!”
“Ko kin fara bacci ne?”
Kai ta girgiza sai kuma tace
“A:ah!”
“Amman kikai shiru! Fada min mana yar kanwata!”
“Uhmm to!”
“Ina sauraron ki…”
Ido ta runtse sannan ta fara fadin
“Ina son mutum ma’abocin addini, gaskiya, rikon amana, fara’a da hakuri sannan mai sanyin hali da so na.”
Shiru yayi tin da ta fara maganar yake murmushi yana shafa kan sa.
“A tsarin hallitta fa Aysher?”
Fuskar ta kamar zatai kuka ta runtse ido ba wanda ta fara gani sai Yaa AK hakika halittar sa da kyan sa yayi mata duk da cewa Yaa Muhammad ma ba baya ba amman Yaa AK fari ne irin farin nan na fulani da ya hade da mahaifiyar sa buzuwa.
STORY CONTINUES BELOW
Kyakyawa ne na karshe domin kuwa yana da manyan idanu wadan da ko da yaushe suke a lumshe kamar mai jin bacci. Ga gashi wanda suke gazar gazar a mike da yawa da cike a idon nasa. Girar sa a cike take taf da gashi amman kuma a gyare take ka rantse da Allah shaping nata yayi. Hancin sa dogo ne dan siriri dashi bakin sa madaidaici mai dauke da dan gashin baki sidik.
Dogo ne, yana da fadin kirji jikin sa a murde yake ko dan yadda yake training din sa ne. Yanayin dabiun sa da ta sani ta lura shi miskili ne magana bata fiya damun da ba amman a yanzu yana dan sakewa da ita. Sam bashi da yanayi yana da sanyi da hakuri.
Ajiyar zuciya ta sauke tana fadin
“Duk wanda na sama zanyi godiya ga Allah Yaa AK!”
“Sure?”
Kai ta gyada sannan tace
“Eh!”.
“Me kika fi tsana to?”.
“Like?”
Ta tambaya tana gyara kwanciyar ta.
“Dan gane da wanda kike so ko wani abu.”
“Na tsani karya, cin amana da zalunci “
“Gud girl!”
Murmushi tayi. Jin an fara kiraye kirayen sallah yasa ya dubi agogon dake kafe a dakin sa. Hudu saura. Abinda Aisha ma taji kenan ta zaro idon ta tana fadin
“Kaji me naji Yaa AK?”
“Uhmm mun kwana idon mu biyu. Yanzu mu tashi muje muyi alwala muyi sallah kan a kira sallah asuba ko?”
“Insha Allahu.”
“Ok bye!”
“Aha bye!”
Ta kashe wayar ta zuba tagumi. Tunani take yadda ta kai wannan lokacin idon ta biyu. Kuma ba tare da taji bacci ko kundura ba.
Sam bata gajiya da kasancewa da Yaa AK ko me hakan yake nufi? Ido ta lumshe tana mai sakin murmushi sai kuma kwanta rigingine hannun ta akan kirjin ta. Ta jima a kwance dan jin ana kiran sallah yasa ta bude ido.
Karfe hudu har da rabi wannan yasa ta mike da sauri ta nufi bandaki ta kama ruwa sannan ta fito ta daura alwala. Kan sallaya ta hau tai sallah sannan ta zauna tana tasbihi. Karfe hudu da hamsin ta tashi tayi raka’atanil fijir sannan ta mike ta tada sallar asuba. Tana idar wa tayi azkhar din ta sannan ta kwanta agun tana cigaba da jan carbin ta.
Aliyu ma yana kashe wayar ya dan lumshe ido yana dan cije leben sa. Bandaki ya nufa wanka yayi ya dauro alwala Shiryawa yayi cikin wata sky blue din jallabiyya ya saka hular sa tashi ka fiya naci wacce ya zama tamkar balarabe. Turaren sa masu dadin kamshi ya feshe jikin sa dasu sannan ya nufi kan sallaya. sallah ya tayar ya jima a zaune yana addu’a akan Allah ya mallaka masa Aisha domin a yanzu ya gama yadda da aminta da irin son da yake mata. Yana jin ana kiran sallah ya mike da hanzari yai raka’atanil fijir sannan ya wuce masallaci yana can carbi.
Acan masallacin ana idar wa ya zauna ya dauki alkur’ani ya fara karantawa. Bai fito a masallacin ba sai karfe bakwai dai daii.
Yana fitowa yayo gida a compound ya tsaya suka gaisa da Mai gadi da wasu masu aikin dake ta aikin gyara gidan.
Falon sa ma har an gyara sai kamshi yake dan haka ya nufi dakin baccin sa. Da kan sa ya gyara kamar yadda ya saba dan masu aikin sa sam basa shigar masa dakin baccin su. Iyakar su Main Falon sai ko falon sa na zama
Yana gamawa ya nufi bandaki yayi wanka ya fito ya shirya cikin blue black din suit wacce tai masa kyau sosai sai tashin kamshi yake sai kace wanda yai barin turare. Kafar sa sanya da sau ciki baki sai sheki yake. Briefcase dinsa ce a hannun sa ya nufi dining yana jin sa cike da nishadi.
Zama yayi a dining ya dauki wayar sa yana mai fara dailing number Aisha. Har bacci ya fara daukar ta ta jiyo karar wayar tata. a hankali ta mike ta nufi katifar tata. Zama tayi sannan ta dauki wayar tana duba mai kira. Hamma tayi ta rufe bakin ta tana salatin annabi sannan ta dauki wayar ta kai kunnen ta.
Cikin kasala tayi sallama a hankali
“Assalamu alaikum!”
“Wa’alaikum salam!”
Ya amsa cikin muryar sa a dake kamar Wanda ya tashi a bacci ya koshi sam bai kama da wanda za ace ya kwana yana waya ba.
“Bacci kike yi?”
Ya tambaya. Kawar da tambayar tayi tace
“Ina kwana?”
“Mun kwana tare ai. Ya kike bacci kike na tashe ki ko?”
“Lafiya!”
“Sorry kinji. Zan fita ne nace bari na kira naji ya kike kema ki tashi ki shirya ki tafi makaranta ko?”
“Uhmm yanzu zan shirya.”
“To ayi karatu da yawa Kanwata Miss u!”
Murmushi tayi tace
“Insha Allah. Miss u too. Amman yau zaka zo ko?”
“Kina so nazo ne?”
Kai ta gyada tace
“Eh mana!”
“Da gaskiya?”
Yai maganar yana daukar cup din coffee ☕ dake ajiye akan dining din. Bismillah yayi ya kai bakin sa ya dan kurba.
A hankali tace
“Eh! Allah ya ara mana garin yau zan zo insha Allahu!”
“Ni dai ko anyi ruwa kazo!”
Tayi maganar cikin shagwaba. Kai ya gyada yace
“To ranki ya dade!”
Tai murmushi tace
“Ok Allah kiyaye ya tsare Yayanah. ayi aiki da kyau. Aci halak!”
“Insha Allahu Swt Baby nah. Bye!”
“Aha bye!”
Ta kashe wayar ta mike ta fara gyara dakin nata ta gama ta share sannan ta fita ta dau tsinsiya ta fara sharar tsakar gidan.
Umma ta sama tana tafasa ruwan tea. Durkusawa tayi tace
“Ina kwana Umma?”
“Lafiya kin tashi lafiya?”
“Lafiya lou!”
Ta fada ta karasa sharar ta fara hada wanke wanke.
Umma tace
“Ai fa yau kin makara kije ki wanka kawai yanzu nazo nayi wanke wanke.”
“To Umma!”
Ta fada tana shiga daki. Kayan baccin ta ta cire ta dauro zani ta saka hijab a sama sannan ta dibi ruwan zafinta sirka zata shiga bandaki Yaa Umar kanin Yaa Muhammad ya fito cikin shiri xai fita.
“Ina kwana Yaa Umar?”
Ta fada tana shirin shiga bandakin.
“Lafiya lou yau me kika tsaya baki tafi makaranta ba har yanzu?”
“Makara nayi!”
“Ok! Ga kudin makaranta.”
Amsa tayi tace
“Nagide a dawo lafiya.”
Yayi wajen Umma yana fadin
“Allah yasa.”
Kudin ta ajiye a daki sannan ta wuce tayi wanka tana fitowa ta shirya ta fito cikin sauri rataye da jakar ta. Umma ta kalla tace
“Umma na fito zan tafi.”
Kallan ta Umma tayi tace
“Ba kici komai ba fa.”
“Umma na makara fa.”
“Ai kam zauna ko ruwan tea ne ki sha.”
Kamar zatai kuka ta zauna ta amshi tea tana kurba. Kadan ta sha ta mike ta ce
“Na tafi.”
“Ga kudin makarantar!”
“A’ah Umma ki barshi Yaa Umar ya bani dazu.”
“Ke da baki karya ba zai ishe ki?”
“Eh!”
“To a dawo lafiya Allah tsare ya bada sa’a.”
“Amin!”
Ta fada tana fita.
A gajiye ta dawo ta fada saman katifar ta tana zare farar safar ta. Bayan ta cire ta zare hijab din ta ta cite uniform din ta. Ta daura zani dan wanka take son tayi. Hijab ta saka ta mike ta dauki uniform din ta dan kullum sai tayi wanki duk da ba kala daya bane da ita amman bata bari su tarar mata. Har ta kai bakin kofa sai ta zube kayan ta dawo ta zauna ta dauki wayar ta.
Missed call din Yaa Muhammad ta gani sai text din Yaa AK da yai mata budewa tayi ta tsaya kallon screem din wayar tata.
_Yan mata na ya kike ya ckul din kin dawo lafiya? I really miss u Aysher nah._
Murmushi tayi tace
“Na dawo lafiya Yaya nah! Ya aiki? Miss u more Yayanah. Kayi aiki lafiya bye!”
Tura masa tayi ta fara dailing nunber Yaa Muhammad har ta gama bai dauka ba. Tana shirin ajiyewa taji wayar ta dau kara tana dubawa taga Yaa AK ne. Dauka tayi tai sallama a hankali
“Assalamu Alaikum!”
Ido ya lunshe dan muryar Aisha har amsa kuwa take masa a kunne wani lokacin shi kadai sai yaji kamar muryar ta na masa magana. Tana da dadi da sanyin murya ga zaki.
Ji ahiru ta dauke wayar tana kallon screem din. It’s connected ta gani dan haka ta kara fadin
“Assalamu Alaikum!
Da sauri ya dawo daga duniyar da ya tafi ta shauki ya ce
” Wa’alaikun salam!”
Yadda taji muryar sa sai hakan ya mata wani iri dan muryar sa ta canja tace
“Are u ok?”
“Eh! Me kika ji?”
“Naji muryar ka ba dai dai ba.”
“Haba?”
Ya fada yana shafa kansa.
Kai ta gyada tace
“Eh ko aikin ne?”
“No i thinking is all what am.feeling ne!”
“What are u feeling Yaya na?”
Murmushi yayi yace
“Ya makarantar?”
“Alhamdulillah nace me kake ji?”
“Love!”
Ya fada kai tsaye.
“Love?”
Ta maida masa abinda ya fada cikin salon tambaya.
“Yes Aysher!”
Shiru tayi can tace
“As in how?”
Ido ya lumshe ya bude kirgin sa na bugawa. Meyasa kullum in zai fada nata yana son ta sai ya kasa meyasa haka? Ya rasa dalili.
“Kar kace min aure zaka kara dai?”
Ta katse masa tunanin sa. Kai ya gyada yace
“In aure zan dada akwai matsala ne?”
“Amman kana zaune lafiya da yar matar ka!”
“Ni na fada miki haka?”
“Me?”
“Muna zaune lafiya!”
Murmushi tayi tace
“A’ah!”
“Aysher a gaskiya ina son na kara aure amman wacce nake son ce na kasa fada mata ina son ta ki ban shawara mana.”
Murmushi tayi duk da a kasan zuciyar ta taji wani abu dan har sai da kirjin ta ya buga da karfi sannan tace
“Kai Yaa AK da gaske?”
“Eh ina sauraron ki!”
“To ni waye zai kika Yayanah baka da aibu gaskiya ka fada maka nasan ba zata taba kin ka ba sai dai in da wani dalili amman nasan ba na kana da aibu ba.”
STORY CONTINUES BELOW
“Ko?”
“Eh man!”
Murmushi yayi yace
“Nagode!”
“Haba menene na godiya.”
“Kinci abinci?”
“A’ah kai fa?”
“Nima van ci ba ina jin ma sai na dawo gida anjima zanci.”
Ido ta zaro tace
“Har anjima. Wai matar ka tana garin nan?”
“Eh! Menene?”
Ya tambaya.
“Nothing naga yadda kake zuwa kake yi ne in ka dawo daga aiki ka taho nan ita kuma fa.”
Murmushi yayi yace
“Kin ga kije kici abinci kan time din isilamiyya yayi anjima ai zan zo ko?”
“Haka ne. Kai ma please ka samu wani abu kaci kaji!”
“I will insha Allah!”
“Ok thanks bye!”
Ta kashe wayar. Tana duba screem din wayar taga missed call din Yaa Muhamma sam tana waya bata ji shigowar sa ba. Kira tahi sai dai taki ta shiga dan haka ta duba agogo karfe biyu saura yasa ta mike da sauri dan tana son tayi wanki tayi wanka sannan ta tafi isilamiyya.
Tana fuita ta hau wankin bata jima ba dan basuyi datti ba ta wanke da kayan baccin ta sannan ta shiga tai wanka. Ta fito ta shirya cikin uniform din ta sallah tayi sannan ta fito ta zuba abincin da akai shinkafa da miya ne da salad. Kadan ta zuba taci sannan ta mike ta dauko hinab da jakar tta.
Dakin Umma ta leka ta ganta a kwance tana dan gyangyadi dan haka ta ce
“Umma ni na tafi makaranta.”
Bude ido Umma tayi tace
“To a dawo lafiya Allah bada sa’a!”
“Amin!”
Ta fice ta tafi.
*
*
*
5:40pm
Tafe take ita da Salima kawar ta sun taso daga makarantar kofar gidan su Salima aka zo sai suka dan tsaya kallon Salima tayi tace
“To sai gobe!”
“Allah ya kaimu ki gaida Umma.”
“Zata ji.”
Salima ta shige gida ita kuma ta cigaba da tafiya dan karasawa gida.
“Yan mata ji mana!”
Ya fada yana biyo bayan ta. Duk da taso ta dau muryar duk da an makale ta amman hakan bai sa ta juyo ba.
“Haba Yan Mata nah just two minute!”
Nan ma bata juyo ba. Murmushi yayi yace
“Yan mata nah!”
Da muryar sa yai maganar wannan yasa ta juyo da sauri. Kallon sa ta tsaya yana sanye da bakin wando da farar riga mai dogon hannu.
Yar hararar wasa ta jefa masa sannan ta dauke kai tace
“Daman kai ne?”
Murmushin sa me kyau ya saki. Tace
“Ba ruwa na da kai!”
Hannun sa biyu ya hade yana fadin
“Haba Gimbiyya ta ayi min afuwa ba zan sake ba.”
Yadda yake yi sai ya bata dariya dan murmushi ta saki ta fara tafiya. Biyo ta ya fara yi a baya yana fadin
“Au ba zaki hakura ba.”
Yai maganar kamar zai kuka. Da sauri ta juyo sai taga ya dan turo bakin sa. Abun yai masa kyau. Kai ta dauke tace
“Ya aiki?”
“Alhamdulillah! Ya school!”
“Same!”
“Good!”
Ya fada yana kallon ta ita kuma sam taki ta yadda ta kalle shi bare ta dago ya kalli idanun ta.
“U didn’t miss me ko?”
Dagowa tai da sauri ai kam karaf suka hada ido nan da na ta dauke kanta tana fadin
“Kana son nai ta mai maita maka kenan ko? Just yasterday but ….”
Sai kuma tai shiru. Gira ya dage yace
“But what? Please say it out!”
Murnushi kawai tayi dai dai lokacin da tazo kofar gida ta kalle shi tace
“Ina zuwa!”
“A fito lafiya!”
Tayi ciki ya bita da kallo yana mai lumshe ido hadi da shafa sumar kan sa.
Tana shiga ta tadda Umma a gaban murhu tana kwashe tuwo bayan ta amsa sallamar ta tace
“Umma sannu da gida!”
STORY CONTINUES BELOW
“Yauwah ya makarantar?”
“Alhamdulilah!”
Tayi cikin daki kayan ra ta canja ta saka bakin siket da riga top fara. Sai da ta saka tai murmushi tace
“Munyi anko!”
Humra ta shafa. Hijab ta dauka fari ta saka sannan ta fito rike da wani littafi a hannun ta. Umma da ta gama kwasar tuwo ta kalle ta. Aisha tace
“Yaa AK yazo ne!”
“Ok Allah bada sa’a!”
“Ameen!”
Ta fice yana zaune akan dakalin gidan ya juyawa kofar gidan baya.
Littafin ta saka ta dan tsakuli wuyan sa. A hankali ya juyo suna hada ido suka sakar wa junan su murmushi.
Zama tayi a gefen sa tana fadin
“Tunanin me kake?”
“Wacce nake so!”
Ya fada yana kallon ta. Murmushi ta dan saki tace
“Gaskiya ta caba.”
“Saboda me kika ce haka?”
Ya tambaya. Kallon da yake mata yasa tai saurin dauke kanta tana fadin
“Naga yadda kake ji da ita har tunanin ta kake a ko ina.”
“Haka ne amman kuma bata san ina yi ba.”
Ido ta dan zaro tace
“Ina mamaki me yasa ka kasa fada mata?”
Kai ya dauke daga kallon ta yace
“Na fada miki ina jin tsoron kar tace bata so na. “
Yar dariya tayi tace
“Nima na fada maka ba wacce zata ‘ki ka haka kawai sai dai in tana da dalili.”
“To in ta’kini ya zanyi. Hakuri da dangana Allah xai shiga lamarin ka.”
“Haba?”
Kai ta gyada tace
“Sure!”
Yai murmushi yace
“Nagode da kika ban kwarin gwiwa.”
Murmushi tai masa kawai.
*
**
***
****
*****
Washe garin ranar da naje gidan na akai Bridal shower anan falon gidan mu akai ranar amarya tai kyau cikin blue din material dinkin doguwar riga an mata makeup. Kawayen ta kuma suka shirya cikin wani farin material.
Wata bakar doguwar riga na saka yar dubai wacce duk jikin ta stone ne golding kala. Fuska ta ba kwalliyya ko daya sai mayafin da na yafa na rufe kai na dashi.
Anan akai hutuna da yan raye raye sannan aka waste aka bar mu da Amarya da wasu daga cikin yan uwan mu sa’anin mu.
Washe gari kuma dinner akai wacce nace ba inda zani duk yadda Suraiyya tayi dani kin yadda nayi. Yaa Kamal yace a kyale ni tinda nace ba zani ba. Dan haka gidan ya rage daga ni sai Baba Uwani sai wata kanwar kakan mu da tazo ta sauka a gidan mu.
Su suna can dakin Baba Uwani ni kuma ina daki komai ya tsaya min. Ko tunani rasa wanne zanyi nake yi. Na gama ramewa dan daga kallo daya in kai min zaka gane lallai ina cikin damuwa mai tsanani na zama so weak in ka ganni sai kaga kamar na cire rai da rayuwar duniyar ma.
Ina kwance wajen sha daya da rabi na fara jin hayaniyar yan mata suna dawowa da sauri na mike na bar dakin dan a yadda nake jin mood din na sam bana son ko wacce irin hayaniya.
Dakin Dady na shiga anan falo na kwanta akan three sitter carbi na gani akai na dauka ina tasbihi wanda ban san lokacin da bacci ya dauke ni ba.
Da safe ma ban fita ba anan nai sallah na zauna akan sallah yana ta addu’oina. Har karfe goma sha daya Suraiyya na nema na ga waya ta a kashe gidan ta fara dubawa anan ta same ni a dakin Dady. Shigowa tayi tace
“Nan kika kwana ne?”
Kai na gyada tace
“Me zan kawo miki kici?”
“Nifa bana jin yunwa.”
“Ai kuwa daurewa zakiyi kici ki sha magani. Dan Allah Fateema ki daina saka damuwa a ranki har yaushe zaki dauka a irin wannan yanayi. Da kinji wannan yanayin ki dauki alkur’ani ki karanta insha Allah zaki samu saukin duk abibda ke damun ki. Damuwar ba abinda zata haifa miki sai ‘da mara ido.”
Shiru nayi hawaye na zubo min.
Fara gogen hawayen tayi tace
“Bari na kawo miki ko tea ne kisha sai kisha maganin ko?”
Kai na gyada ta mike ta fita bata jima ba ta dawo da cup da plate sai ledar magunguna nan. Tana zama Yaa Kamal ya shigo kallon sa tayi tace
“Yauwah zo ka taimaka min. Inje gun ba’kin can.”
“Anki nima kizo ki ciyar dani.”
Murmushi tayi tace
“Bata in na dawo na baka.”
Yai murnushi yace
“Ina jiran ki fa.”
Kai ta gyada ta kallen tace
“Ina zuwa.”
Yaa Kamal shi ya sani dole na sha tea naci dankalin sannan ya ballar min magani na sha. Muna zaune Momy ta shigo. Kallon mu tayi tace
“Au ashe kuna nan.”
“Ina kwana?”
Na fada a sanyaye kai na akasa.
“Lafiya ya jikin?”
“Da sauki.”
“Allah kara sauki. Kamal in ka gama ina jiran ka kazo ka amshi sakon.”
Ta fada tana juyawa ta fita. Yaa Kamal ya amsa mata da
“Toh Momy!”
*
A ranar sister day akayi shima banje ko ina ba. A haka aka gama bikin suraiyya ina daki dan ko ranar yini da akai a compound din gidan mu ban fita ko ina ba. Saboda tun lokacin da naje gida na sai komai ya dawon sabo zuciya ta ta karye na kasa yadda da cewar Fu’ad ya sake ni.
Duk da ina son na koma amman ganin yadda gidan muke a cike kuma Momy na busy na bakin dake gidan mu ya sa ban tayar da maganar ba.
A ranar su Hajiyar Fu’ad suka zo. Kowa yana compound din gidan mu inda akai decoration aka saka kujeru. Anan Momy ta amshe su. Suna zama ta kawo musu ruwa da lemo sannan suka fara gaisawa. Hajiya tace
“Ina Fateema ne?”
Momy tace
“Tana ciki ta’ki fitowa.”
“Allah sarki. Bari muje mu gaisa.”
“Haba dai bari na kira muku ita.”
“A’ah mu bari muje.”
Dole Momy ta hakura tai musu jagora har dakin na.
Ina kwance a kan three sitter hannu na rike da waya ta ina kallon pictures din Fu’ad naji sallamar su Momy mikewa nayi zauna ina amsawa. Ina ganin Hajiyar Fu’ad nai kasa da kai na na sauka akan kujerar. Zama sukai Momy ta juya ta fita.
Kai na a kasa na gaishe dasu suka amsa suna fadin
“Ya taro?”
Nace
“Alhamdulillah.”
Nan Hajiyar Fu’ad taga yadda na kara ramewa ga damuwa da tai min yawa dan haka tace
“Fateema komai fa na duniya hakuri ake dashi. Ki tayin hakuri kinji kuma ki ta addu’a amman ajiye damuwa ba abinda zatai miki sai kara miki lallura. Dan Allah ki daina ko kin fiso ki ta ganin Momyn taki a cikin tashin hankali tana ramewa ita ma. Kalli fa duk yadda kika lalace dan Allah ki daina damuwa kinji.”
“To Hajiya Nagode!”
“Allah miki albarka.”
A hankali na amsa da
“Amin!”
Sun jima a dakin sannan suka fita suka bawa Momy gudunmawa suka ce zasu tafi. Takeaway Momy ta basu da gift suka tafi kowa na godiya da dan uwan sa.
Ranar lahadi aka kai Suraiyya gidan angon ta Yaa Kamal. A ranar ni kai na nayi kyka dan a zama na a gida tabbas su suke debe min kewar sosai yau kuma an wayi gari suna gidan su.
Zuciya ta tai min wani irin nauyi yanayin da nake ciki kuwa sam ba zan iya fasalta shi ba dan ni kaina ba gane a wane halin nake ba. Ganin ina neman fita a haiyaci na yasa na dauko alkur’ani ina karantawa. Sannu a hankali abinda nake ji ya dannen zuciya ta ya fara sauka a hankali naji duk yanayin da nake ciki yana yaye min.
Kan wani lokacin naji ni kamar an cire min duk abinda yake damu nah. Alkur’anin na rumgume hawaye na zubo mun a ido na ba kukan komai bane sai na saukin da naji na samu lokaci daya. Lallai na yadda alkur’ani maganin ne da waraka da komai dake damin dan adam.
Lokacin karfe biyu na daren ranar littinin wannan yasa na mike na shiga na dauro alwala. Sallah nayi raka’a biyu sannan nayi addu’a na jima akan sallaya na koma na kwanta. Ban jima ba kuwa bacci mai nauyi ya dauke ni.
Washe gari da safe bayan nayi wanka na shirya cikin wata doguwar riga ta atamfa. Dakin na gyara sannan na fita falo. Momy na sama na gaishe ta, ta amsa tana tambaya ta jiki nace da sauki.
“Kije ki karya kizo kisha maganin ki.”
Ta fada. Mikewa nayi na isa dining din. Kunun da akayi kadai nasha na zo falo na sha magani na anan falon na kwanta.
Ina kwance sai ga sallamar Yaa Kamal nan da sauri na mike ina fadin
“Ango Ango!”
Ya dan hararen yana nuna min Momy. Murmushi nayi nace
“Ina yar uwa ta?”
“Tana gida ita tace nazo na dauke ki.”
Ido na zaro nace
“Lallai ai kam ba inda zani.”
Yai murmushi yace
“Amman ba amana.”
“Kasan dai yanzu bai dace ina yawan fita ba ko?”
“Na sani amman ai kai ki zanyi na dawo dake. Ai kin iya zuwa gidan ki ko?”
Fuska na rufe da hannaye na.
Momy ya kalla yace
“Ina kwana?”
“Lafiya lou ya Suraiyyan?”
“Alhamdulillah! Momy Fateema nazo daukar mata.”
Kallo na tayi tace
“Ai gaka nan gata “
Ya kallen yace
“Jeki dauko Hijab din ki ko?”
Ba musu na mike na dauko Hijab dina. Baya falo dan haka nace
“Momy mun tafi.”
“Allah tsare ki gaishe ta.”
Na amsa da
“Amin zata ji.”
Sannan na fita. a cikin mota na same shi na shiga ya tada muka tafi. Kai gidan Yaa Kamal yai kyau duk da ba wani babba bane flat ne mai kyau an tsara shi sosai. Abba ma ya cika dakunan da kaya masu kyau da tsada.
Ina shiga tazo ta rumgume ni tana fadin
“Oyoyo Sister!”
Na saki murmushi na zauna nace
“Amarya kinsha kamshi.”
Tace
“Sosai kuwa wallahi.”
Ido na zaro nace
“Wato bakya jin kunya ta ko?”
Murmushi tayi tace
“Ke ai ba sirika ta bace ko Momy ba zanyi sirikantaka da ita ba bare ke.”
Murmushi nayi nace
“Oh ko?”
Tayi fari da ido tace
“Sis ashe haka aure yake?”
Dan hararar ta nayi nace
“Ke ni bar ni da maganar nan. Me zan samu?”
“Ki shiga kitchen ki duba. Ai fushi ma nake wallahi ace kwana na nawa baki zo ba amman ai ni washe garin kai ki sai da nazo kuma na kara zuwa.”
“Haba Sis kiyi hakuri kinsan bai kamata ina yawan fita ba dai ko?”
“Uhmm daman haka zakice amman menene in driver ya kawo ki ya maidake.”
“Gashi nan dai yau nazo ai ko?”
“Da nasa a dauko ki ba.”
Nai murmushi na nufi kitchen. Firij na bude na ga lemuka kala kala. Rufaida na gani ita na dauko na dawo falo ina sha
Ina zaune Yaa Kamal ya fito ya kalli Suraiyya yace
“Ni zan fita sai na dawo.”
Allah ya kiyaye.”
Ya amsa da amin. Ya kallen yace
“Sai na dawo.”
“A dawo lafiya.”
Na fada ya yi hanyar kofa na kalli Suraiyya nace
“Malama kije ki rakashi mana.”
Murmushi tayi ta mike tabi bayan sa. Sai da ya fita ta koma ciki. Nan na dinga mata mita akan tana kula da mijin ta. Suraiyya na murmushi tace
“Ah ah kaga manya fa.”
STORY CONTINUES BELOW
Tare mukai girki rana sai yamma Yaa Kamal ya dawo shima ya kara fita bai dawo ba sai bayan isha’i nace zan tafi amman yace sam bai san zancen.
“Ina ba inda zaki kwana zakiyi .”
“Amman kasan ban fadawa Momy ba ko?”
“Zan kira na fada mata.”
Ba yadda nayi haka na kwana a gidan dan ko Momyn ma bai kira ba dan yasan in ya kira ma da kyar ta yadda na kwana.
Washe gari kuwa muna gama break na ce ni dai gida zan tafi. Dole ya tashi ya mai dani gida. Momy muka sama a falo ta bimu da kallo tace
“Kun kyauta.”
Ni dai daki nayi bayan na gaishe ta. Sai Yaa Kamal ne ya zauna yana bata hakuri. Ban san yadda suka kaya ba.
Akan gado na zauna na zuba tagumi can na bude ido. Tabbas gidan mu nake son zuwa to tayaya Mony zata bar ni naje. Shiru bayi ina tunani can na miki na fita.
A kitchen na same ta tana girki wannan yasa na amsa ina taya ta. Sai da muka gama na kalle ta nai kasa da kai nace
“Momy daman gida nake son naje na dauko wasu abubuwan nawa.”
“Ai kayan ma za aje a debo.”
“Saboda me?”
“Saboda gidan ku!”
Momy ta ban amsa. Kai nayi kasa dashi nace
“Inje?
Tana dagowa sai na bata tausayi dan haka tace
” saura in kinje ki kwana!”
“Haba dai.”
Na fita da murna jaka ta na dauka na dauki keyn gidan na fita. Driver mu ya dauko mota muka tafi. Muna zuwa na sallame ahi nace bayan magariba ya dawo.
Ciki na shiga na rufe kofa. sai da na kunna wutar gidan sannan na shiga. Dakin yana nan tsaf dashi dan ko sati banyi da gyara wa ba amman hakan na tashi na kara gyara dakun nan ko gajiya ban ba na gama sannan na zauna duba inda na ajiye album amman sama ko kasa baya daki na.
Dan haka natafi dakin Fu’ad can ma na duba amman sam babu zama nayi ina tunanin inda sukai sai naji kiran sallah la’asar wannan yasa na shiga nan bandakin Fu’ad nai alwala na fito na tada sallah.
Ina idar wa na haye kan gadon da ina shakar kamshin turaren sa. Ido na lumshe ina tina moment din da muka kasance a tare a baya. Ban san lokacin da bacci ya dauke ni ba sai kiran sallah magariba kawai naji.
Da sauri na mike ina kallon dakin da nake. ajiyar zuciya na sauke sannan na wuce na dauro alwala. Sallah na zo nayi na jima ina addu’a sannan na shafa.
Ina mamakin yadda nake bacci sosai in ina gidan nan bama dakin Fu’ad a gida kan nayi bacci ina jimawa tunane tunane amman in nazo gidan nan sai naji nutsuwa hankali na ya kwanta.
Hakika nasan nayi rashi wanda ba zan taba mai dashi ba. Dana sani akace keya ce lallai na yadda da haka
Ina zaune sai ji nayi ana horn ko ban duba ba nasan drivern gidan mune dan haka na mike na rufe ko ina na debi abinda nake bukata sannan na fito na rufe kofar na kuma kashe wutar gidan.
Gate na rufe sannan na nufi mota na shiga muka tafi gida. Yana parking na fito ina fadin
“Nagode!”
Ban jira amsar sa ba nayi cikin gida. A falo na samu Momy nai saurin yin kasa da kai na. Da ido kawai ta bini tana girgiza kai. Ina shiga na cire kaya na, na wuce bathroom. Wanka nayi na fito na saka kayan bacci na tada sallah isha’i. Ina idar wa nayi shafa’i da wutiri sannan na dauki alkur’ani ina karantawa.
Ina zaune a gun ina karatu na dan yadda nake jin nutsuwa na shiga ta yasa ko karatun ban san dainawa dan da na shigo gidan ni kadai nasan a wane hali nake ciki amman tin da nai sallah na fara karatun naji komai na tafiya a hankali wanda a yanzu naji zuciya ta tayi sakat da ita. Wannan yasa ban gaji ba dan bana son na daina kuma in fada tunanin da zai kara karya min zuciya ta.
STORY CONTINUES BELOW
*
*
*
*
9:45pm
Yasmeen ta shigo dakin da nake gani na ina karatu yasa ta juya. Bata jima ba sai ga Momy nan ta shigo dakin hannun ta dauke da cup dayan kuma ruwan jarka.
Zama tayi a gefen gadon sannan ta ajiye min cup din. Kankana ce aka markada ta aka saka madara a ciki.
“Dauki ki sha ki sha maganin ki.”
Ba musu na dauka na fara sha. Sai da na shanye sannan ta mikon magungunan nawa. Amsa nayi na sha sannan ta mike ta fita.
Ina zaune har sha biyu da rabi ina karatu sannan a hankali na tashi na koma kan gado. Nayi addu’ar bacci ina mai lumshe ido na tare da addu’a Allah yasa bacci ya dauke ni ba sai na tsaya tunane tunane nan ba.
*
*
*
*
Wasa wasa sai zuwa gidan mu ya zamar min jiki dan da Momy ta duba bata ganni ba tasan ina can tin tana fada har ta dawo nasiha amman sam ba ji nake ba.
Momy bata san in naje can nutsuwa da kwanciyyar hankali nake samu ba dan ko ban baccin dare ba da naje can na shige dakin Fu’ad bacci ke dauke ni. abinda yasa nake zuwa kenan.
Lokacin na gama idda ta amman duk da haka bana cire rai da dawowar Fu’ad lokacin na rame sosai. Wanna yasa Momy ta fara magana da Yaa Kamal kan na koma bakin aiki ko na samu nutsuwa in ina samun abun da zai debe min kewa.
Haka kuwa akayi dan ban san komai ba sai katin gayyatar bude asibiti na na gani. Wannan abun ba karamin dadi yai min ba dan nima ina son abinda zai na dauken hankali na daga yawan tunanin da nake.
Ana gobe bude asibitin da yamma muna zaune muna ta shirye shirye dan ko a hakar budewar na na zama busy. Zaune nake ina ta lissafe lissafe a daki na.
Momy na falo tana zaune suka jiyo sallama amsawa sukai Hajiyar Fu’ad ce ta shigo. Momy ta mike ta fara akan fuskar ta tace
“Sannu da Zuwa Hajiya.”
Nan ta zauna suka gaisa cikin girma da mutunci kowa fuskar su dauke da fara’a.
“Ina Fateema kuwa?”
Momy tace
“Tana ciki kinsan Fateema ta zama ta daka ta daka.”
“Wai har yanzu bata sake ba?”
“To gata nan ne dai in abu yai sauki sai kiga ya dawo daga haka sai kiga jikin ma ya rikirkice.”
“Ya salam! Amman Hajiya ai da an hada mata da taimako ko?”
“Haka ne!”
“Zanyi wa Kawun su Fu’ad magana a taimaka mata. Amman ai ba ace haka mutum zai zauna kullum a damuwa ba.”
“Haka ne dan wallahi kusan kullum tana can gidan nace za a kwashe kaya nan ta zauna tana tai min kuka a bar kayan.”
“Allah sarki Fateema Allah ya bata hakuri da juriyar rashin Fu’ad Allah yasa haka shine mafi alheri.”
“Amin! Bari na kira ta.”
Momy ta mike ta shiga dakin. Ina kan aikina ta shigo a bakin kofa ta tsaya tace
“Hajiyar kuce tazo ki fito ku gaisa.”
Da sauri na mike nabi bayan Momy. A kasa wajen kafar ta na zauna kai na a kasa nace
“Ina yini?”
“Lafiya lou ya kike ya gidan?”
“Alhamdulillah!”
“Allah yayi albarka kinji ki tayin hakuri Fateema Allah kuma yasa haka shine mafi alheri.”
Ta fada tana dafa kai na. Kai kadai na gyada mata.
Nan tace zata tafi ni da Momy muka mike muka rakata iya kaci na bakin kofar falo na koma na barta da Momy da suke kara dan taba hira sama sama. Anan Momy take fada mata bude asibiti a gobe tai mana addu’a da fatan nasara sannan ta tafi akan duk yadda ake ciki zata yo waya.
Daga nan wajen Uncle din Fu’ad taje tai masa bayanin komai nan yai rubutu ya bata gida ta koma sannan ta aika jikan ta har gidan mu ya kawo min na kwana bakwai. Ranar na fara amfani dashi.
Katon asibiti ne mai bangarori daban daban sai a lokacin na ga lallai Dady ba karamin aiki yayi a asibitin ba dan ba abinda ba a zuba ba. Ni kai na katon office ne dani guda wanda tsaruwar sa ma kadai abar kalla ce.
Ko ginin asibitin ka kalla da irin abubuwan da aka zuba masu kyau da tsada ne dan haka ba abinda zan yiwa Dady sai addu’a Allah ya jikan sa yai masa rahama. Amman Dady yai mana gata a rayuwar mu.
Washe gari muka bude asibitin wanda na saka masa sunan Dady *Umar Specilist Clinic* wanda ya samu hallartar manyan mutane ne. Likitocin da muka dauka kwararru daga ko wanne bangare dan haka a washe gari littinin aiki aka fara kawai.
Ranar litinin da naje ba abinda nayi sai sauran tsare tsaren da na gama ina gamawa kuma na fito a mota na bar asibitin. Gida na na nufa a bakin gate nai parking sannan na shiga.
Tin rana sai magariba sannan na koma gida Momy ko ba a fada mata ba tasan na biya ta gida. Ina shiga daki nai wanka sannan ya fito dan neman abinda zanci.
Rubutu na Momy ta ban na sha sannan naci abinci. Tin daga lokacin kullum na tashi a aiki sai na biya ta gida na. Momy dai shiru kawai tayi ta zuba min ido tana mai min addu’a.
*
A asibiti kuwa aiki muke tukuru Wanda muka tsara abin cikin rangwami dan duk wanda yazo ana cire wani parcentage kyau ta ne. Haka nan kudin katin mu ba mai tsada ba kuma in folder zaka bude ma a saukake. Kudin ganin likita shima duk bamu tsawalla ba. Wasu test din ma kuma kyauta muka dinga yin su. Dan haka nan da nan asibitin ya daukaka kowa sai dai kaji yana fadin *US Clinic* zai je.
Alhamdulillah Allah ya saka mana albarka sosai a aikin wanda duk wandan yazo wajen mu sai ya samu waraka cikin ikon Allah asibitin mu yai suna a lokaci kan kani da bude shi.Cikin hukuncin Allah yadda Momy da Hajiyar Fu’ad suka dage akai na da addu’a da neman taimako sai komai ya fara saki na duk da dai son Fu’ad na zuciya ta a dangare dan kamar kara min ake amman na yi dangana dan ko gidan na daina zuwa duk kaya na na sakawa na kwaso na dawo dasu gida.+
Ba abinda na saka a gaba a yanzu sai aiki na, in taimakawa marasa lafiya. Dan haka yanzu am busy a asibiti aiki in na dawo gida ma bincike nake dan zaka ganni rike da computer ina aiyuka na da daukar wasu darasin ta ciki dan haka sam ba zaka ce ga abinda ke damu na ba ni kadai nasan abinda yake damu na.
Abu daya ne Momy ta kara lura dashi shine tin daga lokacin da muka rabu da Fu’ad na kara zama so silent ga shi nai sanyi ba kamar da yadda nake da kazar kazar ba.
*
*
*
*
Tin asuba in na tashi a bacci bana komawa dan zanyi sallah na zauna yai tsabihi ga Allah sannan inyi karatun alkur’ani bana tashi daga kan sallaya sai karfe bakwai sannan na gyara dakin. In wanke bandaki sai na shiga nai wanka da nayi wanka.
Toh yau ma hakan ce ta faru dani ina fitowa na tsaya a gaban mirror ina tsane ruwan jikina sannan na shafa mai. Sam bana kwalliya in kaga abu a fuskata daga hoda sai kwalli da man lebe. To ni a zan wa kwalliya wanda zan wa ma baya nan.
Yanzun ma hoda ce kadai a fuska ta sai kwalli da na saka da man lebe. Amman in ka kalli fuska ta zaka zata wata kwalliya nayi. Dan gira ta ba me son yin jagira bace in ka kalla ma sai ka zata na gyara ta ne na dada mata jagira. Haka nan baki na da yake pink kala in ba sani kayi ba sai kace jan baki na saka dan haka in ka kallen sai ka zata wata kwalliya nayi.
Gun durowa ta na nufa na dauki wata brown kalar doguwar riga wacce take mai fadi sai hannaye kawai amman gaban ta an mata ado da wasu manya da kananun stones silver. Gashin kai na na gyara sannan na dauki farar hula na saka wacce keyar ta tashi kamar nayi acuci maza. Mayafin rigar na yafa akai na. Turaruka na na hau fesawa sai da na gama sannan na dauki irin wanda Fu’ad ke amfani dashi na shinshina. Ido na lumshe domin kamshin kadai naji yana tino min da Fu’ad wanda dan haka na siya nake amfani dashi lokaci zuwa lokaci. Duk da ban fiya shafa shi ba amman zan dauka in shinshina sannan in ajiye dan nafi amfani dashi ma in zan kwanta. Sai da na shafa sannan na dauki farin sandal dina na mai dan tudu na saka sannan na dauki farar jaka ina zura wayata a ciki.
System dina dake kan side durowa na dauka na fito da ita a hannu na. Karfe takwas na fito falo ba kowa a falon dan har Yasmeen ta karya ta tafi makaranta. Akan kujera na ajiye sannan na nufi dakin Baba Uwani.
Suna zaune ita da Momy dan haka na karasa har kasa na durkusa na gaishe da Baba Uwani bayan ta amsa na gaishe da Momy. Itama ta amsa.
Mikewa nayi ina daura agogo a hannu na nace
“Momy ni zan tafi sai na dawo.”
“Kinci abinci ne?”
“A’ah zan dauki fresh Yo a firij.”
“Wai Fateema Fresh Yo abinci ne?”
Shiru nayi ina kallon agogon da na saka a hannu na kalar rigar jiki na nace
“Momy na makara kuma akwai aikin da zamuyi by 9am yana da kyau inje kan time din.”
STORY CONTINUES BELOW
“Ai shikenan fadan dai nawa ne bakya so ko? Allah ya bada sa’a yasa ayi a sa’a!”
Ta fada. Baba uwani mantai min addu’a sannan na fice.
Jaka ta na dauka da system dina sannan na fice da sauri dan har takwas da kwata tayi. A sit din gefe na ajiye jakar da system dina sannan na shiga mazaunin driver nayi addu’a na tada motar a hankali na danna horn.
Mai gadin mu dake daki ya fito ya buden gate na karasa wajen sa na gaishe dashi ya amsa yana min addu’ar Allah kiyaye hanya.
8:40am na karasa bakin gate din asibitin. Mai gadin na gani na ya bude gate din ina zuwa inda yake na tsaya muka gaisa yai min addu’a na shige ciki. Inda nake parking nai parking sannan na fito da jaka ta da system dina.
Malam Auwal mai gyara shukuki ne ya karaso da sauri zai amshi jakar system din na dan na riga na rataya jaka ta. Na saki murmushi ina fadin
“Malam Auwal barka da safiya!”
“Yauwah Hajiya da fatan an tashi lafiya?”
“Alhamdulillah ya aikin?”
“Alhamdulillah!”
“Madallah.”
Ganin yana mikon hannu nace
“A’ah ka barshi zan karasa dashi na gode.”
A haka na karasa duk inda na bi gaishe ni ake yi cikin girmamawa duk masu aiki ne a wajen daga nurses sai likitici da masu kananun aiki. Duk cikin sakin fuska da girmama su nake amsa gaisuwar tasu har na shiga office dina.
Kamshin turaren da nafi kauna wato turaren Fu’ad shi ya daken na lumshe ido na, na shiga ina sakin fara’a. System na ajiye akan desk dina sannan na duba agogon hannu na har 08:55am a wajen gaishe gaishe na bata lokacin nan. Nan da nan na ajiye jaka ta na dauki lab coat dina na rike a hannu na fita ta wata kofa da zata sadani da main cikin asibitin.
Ina shiga komai an shirya shi dan haka dakin nima na cire zubona na da agogo na na saka labcoat dina. Dakin muka shiga bayan an shiga da wacce zamuyiwa operation din.
Awa daya da rabi muka dauka muka ciro mata Baby Girl kan akai Maman Babyn daki har an gama gyara babyn an kai ta gun yan uwar mahaifiyar itama ma aka mai da ta daki.
Alhamdulillah tin daga lokacin muka ga aiki yai kyau dan haka hamdala na dinga yi ga ubangiji na. Daga nan office dina na isa kai tsaye. Alwala na shiga nayi na fito nayi sallah walha dan lokacin har sha daya tayi.
Ba jima akan sallaya ina addu’a akan Allah ya shiga lamari na sannan na shafa na mike na bude firij din dake office din fresh Yoo na dauko na bude na fara sha ina lumshe ido na rabi na sha na ajiye sannan na fara attending mara sa lafiya dan ba kowa nake gani a ranar talata ba sai wanda yai booking ko nake ganin sa akan wata cutar ta daban.
Har karfe biyu na kai ina duba su duk da ban gama ba na mike nayi sallah sanna na dawo na ckgaba da duba su. Sai uku da rabi na gama nan kuma na hau round din wanda suke under my control suma na gansu duk da akwai likitocin dake kula dasu sannan na koma lokacin ana kiran sallah la’asar. Sallah nayi sannan na zaina aiki a cikin system dina.
Sai 5:30pm na gama da komai na fito a matukar gajiye dan duk ranar talata haka nake ina gajiya dan aiki na hadar min sosai saboda wanda sai ranar kawai nake ganin su.
Ina fita Sister Jamila ta karaso ta amshi jaka ta ai kuwa da sauri na mika mata dan nima na gaji sosai. A hanya ma haka na dinga amsar gaisuwa da adawo lafiya har muka karasa fita na saka abubuwan nai wa Sister Jamila godiua sannan na tada motar na tafi. Bayan munyi sallama da mai gadi. Shida da minti biyar na karasa gida saboda dan cinkoson yamma.
Ina shiga na tadda Momy a falo kan kujera na fada ina fadin
“Momy sannu da gida!”
“Yauwah sannu ya aikin?”
“Alhamdulillah!”
“Allah taimaka.”
“Amin!”
Mikewa nayi na shiga daki na akan gado na ajiye jaka ta na cire kayan jiki na, na shanya sannan na shiga wanka nayi na dauro alwala. Ina fitowa ana kiran sallah nagariba dan haka na saka riga kawai na tada sallah. Ina idar wa na zauna lazimi ban tashi a gun ba har sai da nayi isha’i nayi shafa’i da wuturi sannan na mike a hankali.
STORY CONTINUES BELOW
Yunwa nake ji dan yau ba abinda naci a hankali na fita falo jin hayaniya nayi tai yawa nace
“Yau kuma wanne bakin muka yi?”
Ina fita naga ashe Yaa Kamal ne da Suraiyya da cikin ta ya fito. Murmushi na saka ina fadin
“Maman biyu ya baby nah?”
Harara ta tayi tana kallon Momy nace
“Ina yini Ya Kamal?”
“Lafiya ya aiki?*
” Alhamdulillah! “
Dining na isa ina fadin
“Ni dai yunwa nake ji ku taso muci abinci.”
Suraiyya ce kadai ta mike tayo gun dining din tana fadin
“Me aka yi ne?”
Flask na fara budewa nace
“Nima ban sani ba dan ban jima da dawowa ba. Aikin Momy ne.”
Fried rice ce da pepper chicken sai caslow na zuba na kalle ta nace
“In zuba miki?”
Kai ta girgiza tace
“Caslow din kadai zanci.”
Ta diba a wani bowl ta fara ci. Muna gamawa muka koma falo muna ta hirar mu. Sai goma suka tafi bayan na rakasu ina dawowa na shige daki.
Abinda ya zame. Min jiki wato karatun alkur’ani shi na fara…
*
**
***
****
*****
******
Lokacin har anyi qualified wanda yaci an dauke masa daga waec har neco gwamnati ce zata biya wanda bai ci ba kuma za a biya masa neco a gida a dauki nauyin waec. Wannan ba karamin taimako ya kawo ga harkar karatun daliban ba. Duk da Waec ya dauki nauyi da kudin gwamnati amman neco da kudin sa ya dauki nauyin masu yi. Haka nan Jamb yasa a zabo masu kokari a makaranti a raba musu.
Duk Aisha taci dan haka bata da matsala exam kadai za a fara kuma cikin hukuncin unbangiji har da ita aka zaba a wadan da AK Foundation zata biyawa kudin Jamb. Aisha tayi murnar da bata taba yin irin ta ba.
Sunyi waya da Yaa Muhammad ta bashi labari ya taya ta murna sosai yace kuma ta dage da karatu da addu’a shima zai tayata da addu’a a inda yake.
Lokacin da taje bawa Yaa AK labari wani sanyi yaji yana ratsa sa dan yadda take farin ciki kadai ke sanyaya masa zuciyar sa. Yana son farin cikin Aisha.
Haka yake zuwa suna karatu dan tare suke karatun jarabbawar duk abinda ya shige mata duhu ya koya mata.
Wannan ya kara sa musu shakuwa dan kullum suna tare da dare kan ta kwanta suyi waya haka nan da safe da text din sa take tashi ka kuma ya kira da ta dawo daga boko zata tadda text din sa bayan yasan ta gama hutawa ya kara kiran ta.
Sosai yake debe mata kewa dan kan ta kira Yaa Muhammad shi ya kira ta su sha hirar su. In Yaa Muhammad yace ya kira busy sai dai tai shiru kawai shima sai ya basar.
A haka har suka gama weac suka fara neco komai na zuwar mata yadda take so. A lokaci kuma Aisha ta kara zama yan mata kyan ta ya kara fitowa sosai. Bata da damuwar komai sai ta saka karatun ta a gaba. Tana da masoya masu son ta da bata kwarin gwiwa haka nan a gida komai bata da matsalar sa. Dan shago da Aliyu ya bawa Abba Allah ya saka masa albarka sosai suna samun rufin asiri sosai.
Ga yayyen ta Yaa Umar level 3 da Shu’aibu yana level 2 da Ibrahim level 1 duk suna karatun su. Yaa Mustapha ne gwamna ya fitar dashi waje dan daman shi irin gifted din nan ne dan haka suna daga cikin wadan da aka fitar waje.
Sai Yaa Muhammad dake karantar Agriculture wanda yana final year shekara ta biyar amman dan yayi diploma sannan ya juya shiyasa time din yaja haka.
*
*
*
*
A haka sukai nisa a jarabawar tasu wacce sauran kadan su gama dukkan jarabawar. Yadda Aliyu yake damun ta da wacce yake son nan har abin ya fara damun ta dan har in zai farai mata maganar sai ta basar ta dauko wata maganar a zuciyar kishin ta take amman a fili sai ta zata ko dan tana wahalar dashi ne.
Ya gama damun tada wacce yake so. Kullu cikin fadar kyawawan dabi’un ta yake abinda ke sa take jin sam bata son yarinyar amman in za a kashe ta bata san dalili ba tana danganta hakan da wani dalili nata. Gani take ita kamar wahalar dashi take.
Yanzu ma suna zaune a kofar gidan su Aisha da yake ranar friday ne yana sanye da golding yellow shadda wacce take ta kyalli da maiko. Yayi kyau har ya gaji da kyau kafar sa sanye da sandal baki wanda ya haska farar kafar sa. Tayi lumi lumi da ita. kan sa ba hula sai gashin kan sa da ya kwanta abin sha’awa. Da yake garin damina ne yamma kuma tayi sai garin yayi lumlumi dashi. Aisha na gefen sa sanye da atamfa purple and milk kala dinkin three quarter akai mata da zani sai hijab da ta saka milk kala. Tayi kyau fuskar ta ba kwalliya amman tayi fresh da ita gashin girar ta a kwance bakin ta pink kala kallon sa take da dara daran idanun ta da yaji kwalli ya kara haske da girma. Yana fadin
” Yaushe zaki rakani wajen wacce nake so ne?”
Fuska ta bata ta dauke kai tace
“A’ah ni ba zani ba.”
“Saboda me?”
Ya tambaya yana kallon ta. Shiru tayi sai kuma tace
“Uhmm bayan bata san me ke zuciyar ka ba.”
“Kuma fa haka ne na kasa wallahi Aisha.”
Kallon sa ta juyo tana yi ido cikin idon tace
“Haba Yaa AK kai fa namiji ne ka zama mai kwarin gwiwar tunkarar komai in dai kasan mai kyau ne. Tayaya zaka bamu kwarin gwiwa ka kana haka. Ka fada mata kawai kada kayi nauyin baki azo a samu matsala.”
Kallon juna suka tsaya yi sam ya kasa daina kallon ta. yana son Aisha har bai san adadin son da yake mata ba. Zuciyar sa ta gama mutuwa a so da kaunar Aisha bai taba soyayya ba amman yadda yake jin sa cikin so da kaunar Aisha abin har mamaki yake basa.
Yan mata wanda suka amsa suna yan mata manya sun sha masa tallan kansu amman ko kallo basa isar sa haka nan ya’yan gwamnoni da shugaba kasa duk na son sa amman bai taba jin digon son ko daya a cikin su ba. Sai yar baiwa Aisha yarinya karama ta sace masa zuciyar sa. Zuciyar sa fada masa take kawai ya fada mata abinda ke zuciyar sa.
“Aysher ke nake so!”
Daram taji zuciyar ta ta buga.
“Kin dade da shigar min ciki zuciya kin yi kane kane a cikin ta. Na rasa taya zan fada miki tsoro da fargabar fada miki nake kada kice bakya so na. Na jima ina fada miki kece hasken rayuwa ta farin cikin rai na ina sonki Aysher ban taba soyayya ba sai akan ki ban san menene so ba sai a kanki kin canja rayuwa ta, kin canjan tunani na kin kawo haske mai yawa cikin rayuwa ta Aysher ba da wasa nake miki ba ke ce wacce nake so ke nake kauna.”
Ido kawai ta zaro dan ko motsi ta kasa saboda yadda ta shiga shock najin kalaman nasa. Ji take anya ba mafarki take ba. In har haka ne me zatayi. Zuciyar ta ce ta dinga bugawa da sauri da sauri ta kuma kasa dauke ido daga kallon sa shima kuma kallom nata yake yana fada mata sirrin zuciyar sa.
Har yai shiru sam abubuwan da ya fada wasu bama ji take ba dan ta tafi duniyar tunani akan abinda ya fada da farko wai ita yake so.
Ganin yayi shiru kuma bata daina kallon sa ba yasa ya daura hannun sa a kaffadar ta ya dan girgiza ta a firgice ta dago tana kallon sa cikin tsoro.
“Me me… Kace Yaa AK?”
Ta tambaya muryar ta na rawa daga gani a firgice take sosai. Hannun ta ya kama yana murzawa a hankali. Idon sa ya sa a cikin idon ta. Sannan yace
“Aysher! Ki dawo cikin nutsuwar ki, ki saurare ni kiji.”
Kai ta girgiza kawai hannun ta rike da nashi yace
“Aysher i love u. I really love u Aysher please don’t say no please!”
Kai ta hau girgizawa tana cire hannun ta daga nashi sannan ta……..
*To fah me kuke tunani shin Aisha zata amshi soyayyar Aliyu AK ko kuwa? Akafta!*