WA NAKE SO CHAPTER 11
Ganin yayi shiru kuma bata daina kallon sa ba yasa ya daura hannun sa a kaffadar ta ya dan girgiza ta a firgice ta dago tana kallon sa cikin tsoro.
“Me me… Kace Yaa AK?”+
Ta tambaya muryar ta na rawa daga gani a firgice take sosai. Hannun ta ya kama yana murzawa a hankali. Idon sa ya sa a cikin idon ta. Sannan yace
“Aysher! Ki dawo cikin nutsuwar ki, ki saurare ni kiji.”
Kai ta girgiza kawai hannun ta rike da nashi yace
“Aysher i love u. I really love u Aysher please don’t say no!”
Kai ta hau girgizawa tana cire hannun ta daga nashi sannan ta saka a cikin kunnen ta tana karkada su alamar kamar a toshe yake. Sannan ta dago tana kallon sa da manyan idonun ta. Sai yaji ba zai iya jurar kallon idanun nata ba.
Kallon sa take babu ko kiftawa. Menene aibun Ya AK babu a yadda ta sanshi babu sam. Mutum ne mai saukin hali da hakuri ba ruwan sa. Yanzu duk yabo da koda wacce yake so ashe ita ce. Zuciyar ta ce ke bugawa da karfi da karfi wanda bata san ko na menene ba.
Tasha fada masa wacce yake son sa bazata ki shi ba sai da wani dalili shin ita me zata ce masa. Kallon sa ta cigaba dayi ko kiftawa batayi.
Ganin irin kallon da take masa sai yaji jikin sa yai sanyi. Zuciyar sa in banda bugawa shima ba abinda take. Hawaye ne ya fara fitowa a idon ta da sauri ya matsa gaba ta yana fadin
“Kiyi Hakuri Aysher in abinda na fada ya bata miki rai amman ban fada da wata manufa fa dan Allah ki daina kukan nan dan Allah na rokeki. Ba zan taba yafewa kai na ba in har zan saka ki kuka dan Allah ki daina kuka.”
A zahirin gaskiya bata san kukan me take ba amman ni nafi zaton tana kukan wani abun ne dai. Handkerchief 💁 ya zaro a aljihun sa ya mika mata. Bata amsa ba wannan yasa ya fara goge mata da kan sa. Ganin yana gogewa wani na zubowa ne ya durkusa a gaban ta ya tallafe kumatun sa.
“Ki fadan me yasa ki kuka dan na gyara barakar da nayi dan Allah.”
Mikewa tayi ta juya zata shiga gida da sauri ya mike ya kamo hannun ta. Juyowa tayi suna hada ido tai saurin yin kasa da kanta. Sakin ta yayi yace
“Ya zaki tafi ki barni cikin zulumi Aysher ai ko so nane bakya yi kya fadan ba ki tafi ki barni ba kika san halin da zan shiga in kika tafi kika barni baki fadan abinda ke cikin zuciya ki game dani ba.”
“Yaa AK ka daina zaton wani abu negative a tattare dani. Na fada maka ba wata ‘ya mace da zata kika sai da dalili to nima a gaskiya….”
Sai kuka ya kwace mata dan haka da gudu ta bar wajen tai cikin gida.
Da kallo ya bita sai kuma ya koma kan dakalin ya zauna yana zuba tagumi. Hakikanin gaskiya kan sa ya daure ya dau zafi. Zuciyar sa kuwa in banda bugawa ba abinda take.
“Hasbunallahu wani’imal wakil!”
Yake ta nanatawa a cikin zuciyar sa a hankali yaji ya samu nutsuwa jin ana kiran sallah yasa ya mike ya isa tap din dake harabar masallaci. Alwala yayi sannan ya nufi cikin masallacin ya hau jam’i aka tada sallah.
*
Umma dake tsakar gida zaune taga Aisha ta shigo a guje tayi daki tana kuka. Ido ta zaro sai kuma ta mike tabi bayan ta da sauri. Akan katifar ta ta same ta tana kuka kamar ranta zai fita.
STORY CONTINUES BELOW

Zama Umma tayi ta dago ta tana kallon yadda take kukan bil hakki da gaskiya kukan take tana sauke ajiyar zuciya. Janyo ta tayi ta rumgume ta a hankali tana bubbuga bayan ta tana fadin
“Ki na fadin La’ilaha illa anta subhanaka inni kuntu minal zalimin. Sannan kina fadin Hasbunallahu wani’imal wakil!”
Haka Umma ta dinga nanatawa itama a hankali ta amsa tana fada take taji ta samu rangwami akan abunda take ji dan haka a hankali kukan ya tsaya sai ajiyar zuciya da take saukewa.
Jin ana kiran sallah yasa Umma tace
“Tashi kije kiyi alwala kizo kiyi sallah!”
Jiki a mace ta mike ta fita. Umma ta bita da kallon tausayi duk da bata san me yake damun ta ba amman daga yadda take wannan kukan babban abu ne dan Aisha bata taba irin wannan kukan ba.
Mikewa itama tayi ta fita ta dauro alwala sannan ta dawo ta tada sallah. Aisha ma daki ta koma ta tada sallah. Tana idar wa ta hade kai da gwiwa tana cigaba da sauke ajiyar zuciya.
Zuciyar ta ba wanda take kawo mata sai Yaa Muhammad ina ba zata iya amsar soyayyar Yaa AK ba saboda Yaa Muhammad shii ya fara fada mata yana son ta kuma ya cancanci ta soshi. Dole Yaa AK yayi hakuri ba zata iya ba. Amman kuma in tace Yaa AK yayi hakuri shikenan sun daina waya da zumunci abinda bata so kenan bata son ta daina ganin sa.
Sai ta tuna halin da take shiga in yai tafiya kai bama tafiya ba just kwana daya in basu hadu ba ji take kamar sun shekara basu hadu ba.
“Ya Allah!”
Ta fada tana dafe kan ta da yake sara mata saboda yadda tai kukan dan har a lokacin ma hawaye ne ke fitowa daga idanun ta.
Sallamar Umma ta ji dan haka da sauri ta hau goge hawayen nata tana amsa mata. Shigowa tayi ta zauna a gefen katifar ta sannan ta kura mata ido.
“Aisha!”
Umma ta kira sunan ta kasa dagowa tayi ta kalle ta sai dai amsawa da tayi tace
“Na’am!”
“A baya na tambaye ki damuwar ki amman sai kika ce baki da wata damuwa. Sai daga baya kika fada min wanda abin ya tsaya min a rai kullum dashi nake kwana nake tashi Aisha. Ina lura da canji daga gareki da yawa.”
Sai tayi shiru. Can tace
“Ki fada min me yake faruwa kukan me kike yi?”
Shiru Aisha tayi. Umma tace
“Ni ban san meyasa kike boyen abubuwan da ya shafe ki ba amman ban sani ba ko dan bani na haife ki ba. Amman Aisha wallahi duk cikin yaran nan na gidan nan ba wanda nake so da kauna kamar ki. Ke macece dole a so ki kuma a saka miki ido akan duk abinda kike ciki. Dole na shiga tashin hankali dan ban taba ganin ki kina kuka irin haka ba in har kina so hankali na ya kwanta ki daure ki fada min me yake faruwa?”
Shiru tayi sai kuma ta dago tana kallom Umma a hankali ta hau bata labarin Yaa AK da yadda yake koya mata karatu ta boye mata dai a inda suka hadu. Amman daga nan ba abinda ta boye mata na alakar su da abun da yazo mata dashi a yau.
“To ke menene na kukan? Ko bakya son sa ne?”
“Umma Yaa Muhammad kuma ma ni bana son sa.”
Kallom ta Umma take tana mamakin ina wayon Aisha ya tafi. Lallai in abu yazo kan ka wani wayo baka da dabara taka guduwa ma suke yi.
Amman Yadda Umma ta fuskanta Aisha tafi so Yaa AK akan Yaa Muhammad domin a yadda ta fada mata bata boye komai da feeling din da take ji akan sa ba. Tana masa boyayyen so ne da bata san tana masa ba. Zuciyar ta ya kama. son sa ya gama shiga dukkan jikin ta da zuciyar ya wanda ya canja ya koma Kauna.
Ba zata ce bata son Yaa Muhammad ba amman tafi kawo shakuwa su ke dawainiyya da Aisha akan relation din su. Dan haka dole a sannu ta ganar da Aisha kome take ciki dan da matsala in har ta auri Yaa Muhammad dan tasan soyayyar Yaa AK shine a ranta fiye da nashi in kuwa haka ne to akwai matsala dan an cutar da ita an dangarar da ita.
Kamar yadda Abba yake fada ne bazai wa Aisha auren dole ba dan haka a bar ta ta auri wacce take so. Kuma auren wanda kake so shine samun kwanciyyar hankalin ko ma wanene.
STORY CONTINUES BELOW

Aisha ki tsaya ki nutsu ki zabi *Wanda kike so* aure zaki yi bana son kiyi aure kuma daga baya ki gane wani abu daga baya. Muhammad da nane amman in har kika samu wanda kika fi so fiye da Muhammad ba zan miki dole ba. Domin auren *wanda kike so* shi zai baki kwanciyyar hankali da nutsuwa. Dan haka Aisha ki tsaya ki nutsu ki duba kiga soyayyar wa ke cikin zuciyar ki.”
Kai ta girgiza tace
“Umma ni Yaa Muhammad nake ao. Tayaya zan so wani bayan shi.”
“Aisha kenan ki tsaya ki nutsu Kibi komai a hankali sannan kiyi istihara ki gane *Wa kike s?* amman da farko yanzu da kike cewa bakya son shi wannan din kin shirya rabuwa dashi. Kinsan ba zai yiyu kina da aure kina mu’amala da wanda ba muharamin ki ba ko? Kuma ko shi Yayan naki ba zai yadda ba. Kin fada in baki ganshi ba halin da kike shiga shin kina shiga makamancin haka akan Yayan naki? A yanzu shakuwar ku da Wannan har tana son tafi taki da Yayan naki domin shi lokacin da kuka shaku tin kuna yara ne shi kuma wannan da giman ki kuka shaku dashi? Aisha ba zamuyi miki dole ba kuma ki cire tunanin Yayan ku a dan mune ba wanda zamuyi wa dole a cikin ku. Muna son ku samu farin ciki da zabin ranku ne dan haka a wanda zamu ce dole sai ya auri dan uwan sa in yace baya so. Meyasa kike jin abubuwan da yawa akan Yaa AK din bayan a baya akan Yayan ki kike jin sa? Wadan nan tambayoyin ki zauna kiyiwa zuciyar ki kuma ki fada masa halin da kike ciki in da hali ki bashi dama anan zaki gane *wa kike so?* kinga har an fara kiran sallah isha’i ki mika komai ga Allah. Insha Allahu Allah zai iya miki.”
Kan Aisha a ‘kasa ta kasa dagowa ta kalli Umma ma. Mikewa Umma tayi tace
“Bari naje nayi sallah!”
Sannan ta fice. Itama mikewa tayi ta tada sallar tana idar wa ta haye kalifar ta ta kwanta.
“Me maganganun Umma ke nuni akai ne? Umma na son tace ina son Yaa AK ne kome?”
Maganganun Umma ne suka dinga mata yawo aka amman ba wanda yafi tsaya mata sai wanda tace
“Kinsan bai zai yiyu kina da aure kina mu’amala da wanda ba muharamin ki ba ko? Kuma ko shi Yayan naki ba zai yadda ba. Kin fada min in baki ganshi ba halin da kike shiga shin kina shiga makamancin haka akan Yayan naki? Meyasa kike jin abubuwan da yawa akan Yaa AK din bayan a baya akan Yayan ki kike jin sa? “
Tuna wadan nan statement din na Umma yasa taji jikin ta yai sanyi. Tabbas haka ne
“In har ta auri Yaa Muhammad duk wata mu’amala ta tsaya tsakanin ta da Yaa AK shin zata iya hakan kuwa?”
Ido ta runtse tana mamakin yaushe har hakan ya zame mata jiki. Yaushe Yaa AK ya zama haka a rayuwar ta.
“Kwana daya in banga ka ba sai in shiga wani hali ina ga ina gidan miji na shin haka zan tai masa kunci ina tunanin wanin sa.”
Juyi tayi akan katifa tana mai kara tuna kalmar Umma da take cewa
“Meyasa kike jin abubuwan da yawa akan Yaa AK din bayan a baya akan Yayan ki kike jin sa? “
Tabbas haka ne a baya in Yaa Muhammad ya tafi ta dinga kuka kenan da shiga mawuyacin hali wanda a yanzu bata fiya wani damuwa ko kuka da shiga wani haki ba. Sai in Yaa AK yai tafiya. Uhmm ai bama tafiya ba kwana daya aiki ya rike shi bai zo ba na ta damuwa da rasa nutsuwa takenan. Bayan nan ba wanda nake son gani kamar sa. Muryar sa na kwantar mara da hankali kalaman sa na sanyaya mata rai. A da fa duk Yaa Muhamamd take ji wa haka.
“Innalillahi wainna illahir rajiun! Allahu sahala illa ma ja’atahu sala wa anta taja ala iza shita sahala.”
Abinda ta fada kenan tana lumshe idon ta dan yadda taji abubuwa na son cabe mata.
Wayar ta ce ta hau kara wannan yasa ta bude idon ta a hankali ta janyo wayar. Yaa Muhammad ne ke kira dan haka a hankali ta daga tai masa sallama. Amsawa yayi yana fadin
“Me yake damun kanwata?”
“Ba komai!”
“Hmm Aisha kenan amman kinsa daga jin muryar ki ba dai dai kike ba ko?”
“Bacci na fara!”
“Bacci tin yanzu tara ma fa vatai ba.”
“Eh anjima zan tashi nayi karatu ne”
“Ok sai da safe to.”
“Allah bamu alheri.”
Tana kashe wayar ta fashe da kuka. Ta jima tana kuka a kwance ta kasa ko da tashi ne.
Umma ce ta shigo dakin hannun ta dauke da plate na abincin ta.
“Aisha!
Ta kira sunan ta idon ta tai saurin gogewa ta mike zaune.
“Ga abincin ki nan kici.”
Ta ajiye ta fita. Duk da tana jin yunwa amman sai taji a lokacin bata jin wata yunwa. Janyo abuncin tayi tai one spoon sai kuma ta ture shi.
Mikewa tayi ta fita da plate din ta maida kitchen sannan ta shiga bandaki tayi alwala ta fito.
Kayan bacci ta saka ta hau kan katifar ta ta rufa da abin rufar ta.
*
Ana idar da sallah ya zauna a wajen sam ya kasa tashi ya rasa me yake masa dadi. Haka ya zauna ya dinga tufka da warwara har aka kira sallah isha’i aka kara tada jam’i ya mike yai sallah. Bayan ya idar yai shafa’i da wuturi sannan ya zauna yana addu’a Allah kawo masa mafita. Ya jima a masallacin dan sai takwas da rabi ya fita.
A hankali ya dinga tafiya kamar bai son tafiyar har ya karasa gidan sa. Yana shiga mai gadi ya mike yana fadin
“Barka da dawowa!”
“Yauwah!”
Ya fada yana shigewa ciki. A falon sa ya zauna yana dafe kan sa sai kuma can ya mike ya bude firij ya dauki ruwa yana bude murfin ya koma ya zauna yana kafa ruwan a bakin sa vai dire ba sai da ya shanye ta tas sannan ya mike ya saka a dustbin ya wuce bene inda dakin sa yake.
Yana shiga ya cire kayan sa ya nufi bandaki. Wanka yayi da ruwan dumi ya fito ya shirya cikin kayan baccin sa ya feshe jikin sa da turare. Kan gado ya zauna yana tunanin shin me reaction din Aisha yake nufi. Bata son sa ko yaya?
Wayar sa dake kan side duruwa ya mika hannu ya dauko. Kallon screem din wayar ya tsaya yi can ya shiga call log ya fara dialing number ta.
Tana kwance taji wayar ta na kara. Gaban ta taji ya yanke ya fadi tasan ko ba a fada mata ba Yaa AK ne dan ba mai kiran ta daga Yaa Muhammad sai shi. Yaa Muhammad kuma sunyi waya tace masa bacci zatai.
Wayar ta janyo ta tsaya kallon screem din wayar sunan sa ne ke yawo a screem din wayar kasa dauka tayi ta zubawa sunan ido kamar ranar ta fara gano. Zuciyar ta ne ya hau buga da karfi da karfi.
Ido ta lumshe lokacin da kiran ya yanke. Yana yankewa aka kara kira da sauri ta bude idon ta ta dauki wayar amman ta kasa dannan receive hannun ta sai rawa yake.
Kiran ne ya kara yankewa. Ajiyar zuciya ta sauke bata gama samun nutsuwa ba text ya shigo wayar da sauri ta dauki wayar tana bude text din Yaa AK ne dai dan haka cikin hanzari ta bude
_Aysher please pick the call i just want hear your voice. Muryar ki kadai zata sanyaya min zuciya ta dan Allah ki dauka ko na samu nutsuwa._
Ajiya zuciya ta sauke. Wayar ce tai kara daukar kara dan haka ta dannan receive 📞 ta kai kunnen ta hadi da fadin
“Assalamu alaikum!”
Wata ajiyar zuciya ya sauke take yaji ya dan samu relief. Jin bai amsa ba ta kara fadin
“Assalamu Alaikum!”
Ido ya bude yana amsa sallamar da
“Wa’alaikum salam!”
Sai kuma sukai shiru.
Ina fitowa daga bandaki na ga baya office din tsaki kawai na saki na hau kan sallaya na tada sallah. Ina idar wa na mike na hau hada kaya na. Flask din da nazo dashi na fito dashi. Gun mai gadi na nufa na bashi ya juye sannan na koma mota na ajiye kaya na na tada motar na fice a asibitin. A hankali nake tafiya ina tuna dan rainin hankalin nan. Tsaki nayi ganin traffic 🚥 ta tsaida mu. waya ta na dauka ina duba message dan naga nawa ya dauka amma sai naga basuyo min alert ba. Account dina na duba naga ba adau ko kwandala ba. Baki na tabe na ajiye wayar ina kallon titi. A haka aka bamu hannu na tada motar nayi gidan mu da Fu’ad.
A bakin gate nayi parking sannan na shiga. Gidan na nan yadda yake dan ina yawan zuwa na gyara shi. A falo na zauna ina bin dakin da kallo kullum na shigo gidan sai na tuna rayuwar da mukai da Fu’ad.
Ba abinda nake mantawa kamar hadda haka nake ji. Momy taso a kwashe kaya amman na hana. Da tace ko su Hajiyar Fu’ad zasu yi amfani Hajiya ma tace a barmin shi kawai.
Zaga gidan nayi. 6:15pm na fito na rufe na koma mota ta. Gida na nufa kai tsaye kan na karasa har an kira magariba dan haka na kwashe kaya na nayi cikin gida.
Momy bata falo kuma daman ban sa ran ganin ta ba dan haka na shige dakina kawai. Wanka nayi nayo alwala na fito na saka doguwar riga na tada sallah. Har ya zamar min jiki dan in nai sallah magariba sai isha’i nake tashi awajen.
Sai takwas da rabi na fito falo. Momy na sama zaune tana kallo. Zama nayi a gefen ta nace
“Momy ya gida?”
“Alhamdulillah! Yaushe kika dawo.”
“Na dawo ana kiran magariba na shiga nai sallah sai yanzu na fito.”
“Ya aikin?”
“Alhamdulillah.”
“To maza tashi kije kuci abinci dan ba zan yadda da cin kayan flour din nan ba kullum. Ni ramar ki damuna take.”
Mikewa nayi dan nima yunwar nake ji tin kunun da nasha ne a ciki na. Kan dining na isa na bude flask daya naga tuwon semo ne miyar kuka da yaji naman kasuwa. Dayan kuma fried supegette ce da aka yanka hanta a ciki.
Tuwon na saka rabin malmala da aka kulla a leda sannan na zuba miyar na fara ci. Tas na cinye wanda na zuba na mike zan mai da kawon Momy takaraso wajen flask din tuwon Ta bude taga abinda na diba. Fuska ta hade tace
“Me kike ci kenan. Wai ke kam Fateema kina likita baki san illar rashin cin abinci ba.,”
Zama nayi nace
“Momy illar rashin cin kika ce ni kum ina ci ko yaya ne. Matsalar ka zauna baka ci ba shine!”
Tagumi Momy ta zuba tana kallo na nace
“Momy ba kyau fa.”
‘To ya zanyi Fateema ai ke kika saka ni yin tagumin. Ace mutum bashi da abinda ya tsana sai abinci anya kuwa?”
Murmushi na saki nace
“Momy ina ci fa ko a asibiti ina bayar wa a siyon kuma ina sha malt ko fresh yoo!”
“Haka kenan kullum sune abinci. Dan Allah kina cin abinci ko kya yi kumari kalli yadda kike dada karewa sai kace kudin guzuri haba Fateema.”
Kai nayi kasa dashi nace
“Toh!”
Plate din hannu na ta amsa tace
Maza dauki rabin ki cinye. Ji yar mal malar amman ace itama sai an rage ko yaron yaye tai masa kadan bare ke.”
Dauka nayi na saka ina fadin
“In cikina ya fashe ai shikenan!”
STORY CONTINUES BELOW

“Bama zai fashe ba dan wannan dan tuwon to masu ci da yawan ma bai fashe ba bare ke.”
Ci na fara amman jin cikin na nake kamar zai fashe da kyar na karasa turawa na mike na wanke plate din.
A falo na samu Momy na dauki mayafi na yafa nace
“Bari na motsa jiki na ko abincin ya fada daga nan zan siyo chewinggum a wancan super market din dan wallahi ciki na kamar zai fashe.”
“Sai ki dawo!”
Momy ta fada na fita a kafa nake tafi dan cikin ya sauka duk da ba wani nisa ne da shagon ba.
Doguwar riga ce a jiki na ash kala wacce akai mata layi layi da baki bata da shape a tsaye take kawai dan haka dan karamin mayafin ta na yafa wanda shima kalar rigar ne sak. Amman ya haska ni. Fuska ta ta fito ta ciki tai kyau da fresh. Waya ce kadai a hannu na sai ATM card dina.
A haka na karasa super market din. Na shiga na wuce na fara daukar chewing gum da sweet 🍪 chorcholate 🍫 sai wasu biskir din. Duk na zuba a basket.
Mutumin dazu da yake office din ta shine a jikin motar sa a kofar super market din. Sanye yake da ash kalar wando sai bakar riga mai gajeran hannu. Idon sa sanye da glass 👓 baki. Tun da zata shiga yake kallonta har ta shiga. Wannan yasa shima din shiga.
Kan ya karasa har ta gama da gun sweet ta wuce wajen turaruka bin bayan ta yayi, bai magana ba ta fara zabar wadan da take so. Kala kala ta dauka sannan ta dauki irin na Fu’ad. Juya shi ta farayi sannan ta saka a basket din hannun ta. Bayan ta gama ta tafi gun pad, ta duka ta dauki virony manya guda biyu.
“Assalamu alaikum!”
Akayi mata sallama. Jin muryar namiji yasa tai saurin dagowa ido suka hada gabanta yayi mugun faduwa don rass ta ganesa.
Da sauri ta juya ta bar wajen. Da kallo ya bita yana murmushi sai kuma ya bita ya same ta tana daukar soap yace
“Amman dai ai ba kyau ai maka sallama baka amsa ba ko. Ai addu’a nai miki ko ba zaki min ba kya amsa wacce nai miki ko?”
Bata juyo ba kuma bata amsa masa ba yace
“Ya kike ya aikin?”
Still bata kula shi ba. Gaban ta yasha yana murmushi yace
“Kin gane ni kuwa?”
“In na gane ka me zan maka? menene matsalar ka dani ne wai?”
“Haba Hajiya tah baki kala da masu saurin fushi ko fada ba. You are cool i see meyasa kike son canjawa daga yadda kike ehee?”
Juyawa tayi tana kallon wani side din gaban ta na bugawa da karfi.
“Shikenan amman babu fada me zai kawo gaba ehe? Ni dai ayi hakuri in na bata miki rai ne.”
Still tayi a tsaye, bata juyo ba kuma bata ce komai ba. Murmushi yayi kawai ya wuce ya nufi hanyar fita daga mall din.
Baki ta tabe ta dan bishi da kallo ta gefen ido, bayan wasu sakwanni ta bi bayansa, a gun counter ta same shi yana biyan kudin abun da ake masa parkaging a leda wannan yasa ta nufi wajen dayan counter duk da da mutane dan wajen da yake ba kowa sai shi kadai.
Ana xuwa kai na na daura kayan a gun. Yana gama lissafa mata yace
“15500!”
ATM din zan mika sai gani nayi ya mika masu nasa, juyawa nayi ina kallonsa ya saka masu pin dinsa, Hararar sa nayi sannan na fice ba tare da na dauki ledar tawa ba.
Suna cire kudinsu suka mayar masa card dinsa ya dauki ledar tawa ya fito kofar da sauri. Har na bar harabar wajen dan haka da sauri ya biyo ni kan nai aune sai ganin mutum nayi a gabana. ledan kayan nawa ya mikon yana fadin
“Kiyi hakuri in na bata miki dan na biya miki kudin amman ai ba kyau mai da hannun kyauta ba. A ido ba haka kike ba nai miki sallama baki amsa ba na miki ya aiki same sannan yanzu na biya miki kudi amman kin ki amsa dan Allah ba dan ni ba ki amsa nasan kinfi karfin sa amman na biya saboda shishigi irin nawa kiyi hakuri ki amsa ba zan kuma ba insha Allahu.”
STORY CONTINUES BELOW

Tin da ya fara magana kai na a kasa yake in ban da faduwa ba abinda gaba na ke yi. Dagowa nayi a karo na farko naga yana kallo na kai na dauke dai dai lokacin da aka kira sa kenan. wayar ya zaro yana kallon screem din wayar tasa. Murmushi ya saki sannan ya danna receive 📞 ya kai kunnen sa shiru yayi sannan yace
“Am sorry dear gani nan yanzu zan karaso na tsaya siyar miki abinda kika ce kina so ne.”
Ta gefen sa nabi zan shige sai yai saurin kamo hannu na sannan yace
“Ok sai na karaso!”
Hannu na na fincike ina hararar sa nace
“Menene haka?”
Hannu ya daga alamar ban hakuri sannan yace
“Kiyi hakuri gashi!”
Ya mikon ledojin nawa. Kallon kedar nayi yace
“Please!”
Hannu na saka na amsa sannan na juya zan tafi yace
“No thanks!”
Juyowa nayi a zafafe nace
“Ni na sakaka?”
“Ayi hakuri da wasa nake ina nufin ba sallama!”
Kai na dauke na wuce da sauri ya kara shan gaba na yana fadin
“”Toh muje in ajiye ki a gida?”
Da sauri nace
“Bana so!”
Na yi gaba na barshi. bin na yayi da kallo yana murmushi, sai bayan da nayi nisa sannan ya juya ya koma gun motar sa.
*
**
***
****
*****
******
Har asuba daga Aisha har Aliyu ba wanda ya runtsa a cikin su. Gwara Aliyu tin uku ya hau kan sallaya yana sallah yana mika rokan sa ga Allah akan ya shige masa gaba.
Aisha kuwa sai hudu da rabi ta mike ta dauro alwala sannan tazo ta shinfidsa sallaya tai sallah ta zauna tana addu’a da neman mafita. Karfe biyar ta mike ta kawo raka’atanil firij tana idar wa taji an tada sallah dan haka ta mike tayi sallah.
Bata koma ba dan exam suke da ita. Dan haka ta dauki littafin ta sai dai sam ba abinda take ganewa in banda tunanin Yaa AK da take. Littafin ta dire kawai ta zuba tagumi. Har karfe bakwai da rabi tana zaune tana tunanin da ta kasa gane.
Umma ce ta shigo dakin bayan ta gama hada abin kari har tayi wanke wanke. A bakin kofa ta tsaya tana kallon ta dan kuwa sam bata ma san ta shigo dakin ba. A hankali ta karaso ta zauna a gefen ta da sauri Aisha ta dago tana kallon Umma. Sai kuma tace
“Ina kwana?”
“Lafiya Alhamdulillah! Naga baki fito ba har yanzu kuma naga kuna da exam yau ko?”
“Yanzu zan fito karatu nagama ne.”
Ta fada tana dauke littafin dake gefen ta.
“Kinga Aisha ki rufawa kan ki asiri da son sakawa kan ki damuwa. Ki mika komai ga Allah shi zai iya miki. In kika ce zaki sa damuwa zaki lalata abubuwa da yawa a rayuwar ki. Kina ganin jarabawa kike yazu haka zaki je kina yin tunani. Ki sani wannan ita ce damar ki ta karshe in kikai wasa da ita shikenan ki mai da hankali dan shine farin cikin Yayan ki da Yaya AKn naki. Ko kina son ki fadi jarabawar?”
Kai ta girgiza Umma tace
“To ki shiga hankalin ki. Tashi kije ki dibi ruwan kiyi wanka kizo ki shirya ku tafi.”
“Toh Umma!”
Ta fada tana mikewa. Fita Umma tayi ita kuma ta cire kaya ta shiga bandaki. Wanka tayi ta fito ta shirya cikin kayan ta. Tana cikin saka safa Umma ta shigo hannun ta rike da cup din tea 🍵 da plate bread ne da kwai a ciki.
“Maza ki cinye ki fito ki tafi har takwas saura ku da zakuyi jarabawa tara da rabi ai kya je ki nutsu kan lokacin ko?”
Ta ajiye sannan ta fita.
Zama tayi ta fara ci sai kuma ta tsaya kallon waje daya tana tunani. Umma ce ganin Takwas tayi yasa ta fito ta shiga dakin.
“Aisha!”
Umma ta kira sunan ta tana rike haba.
“Haba Aisha yanzu baki sha ba har sai ya huce.”
Dauka tayi ta kafa kai tana sha tana tura bread din da kwai. A haka ta cinye sannan ta mike ta dauki jakar ta tace
“Umma na tafi.”
Kudin makaranta ta bata sannan ta fita. A hankali take tafiya sam bata da kuzari a haka ta karasa makaranta. Ko da take can bayan aji ta karasa ta zauna bata tashi ba sai da aka shigo yin jarabawar. Sit din ta ta isa ta zauna aka basu booklet kowa na rubuta sunan sa da exam number and serial number amman ita ta zubawa papper ido kawai. A haka aka fara passing question paper.
Shima har aka ajiye bata sani ba. Nan fa aka fara jarabawa amman sam Aisha ko biro bata daga ta nufin yin rubutu ba. Tunanin Yaa Muhammad da Yaa AK kawai take duk da na Yaa AK yafi yawa.
Wani lokaci ta tuna da Yaa Muhammad yake fadin
“Buri na a yanzu ki gama makaranta ki fito da sakamako mai kyau. Daga nan sai inda karfi na ya kare na ganin kin cigaba da karatu. Damin yin karatun ki zai taimakawa mutane da yawa ba mu kadai ba har al umma.”
Sai kuma Yaa AK da yake fadin
“Aisha ina son naganki kin zama likitan nan yadda zaki na kin allura in ban da lafiya ko kina duba marasa lafiya. Duk da biyan ki za ai amman zaki samu lada domin kinyi abu mai kyau bare yadda zuciyar ki ke da kyan nan nasan zaki nemi lahirar ki da damar da zaki zamu. Dan haka ban da buri sai na inga yau kin gama jarabawa kin fito da result mai kyau na samar miki makaranta mai kyau. Ya Allah! Wa yaga Aisha ta gama karatun ta ta zama cikakkiyar likita. A duniya ina jin ba wanda zai fini jin dadi da farin ciki. zan ta miki addu’a Allah dafa miki kema kuma sai kin taimaka wajen bada goyan baya kiyi karatu ki kuma hada da addu’a!”
Hawaye ne ya zubo mata a idon ta. Dagowa tayi ta kalli yan ajin kowa ya mai da kai akan aikin sa ana ta rubutu dan haka itama sai ta maida kallon ta kan booklet 📔 dinta da ko A bata rubuta ba. sai kuma ta dauki biron ✒ hannunta ta daura akan paper 📜 📔 din ta. Sunan ta ta rubata with her serial and exam number. Question papper ta dauka tana dubawa. Nan ta fara answering objectives din wanda duk yawanci a cikin karatun da Yaa AK yai mata ne a jiya kan wannan abun ya faru.
Tana cikewa wani abun tana gani kamar a lokacin yai mata bayani dan haka tana fara essay din ta fara bayani kamar yadda yai mata. Sai da ta gama ta daga tana kara dubawa lokacin yan ajin har an fara fita dan haka tana gamawa ta mike tayi submitting sannan ta fita. Can bayan ajijuwan su ta karasa ta zauna tana tagumi.
“I do it just to makes both of u happy.”
Ta fada hawaye na zubo mata.
“Why am i sad, crying, 😢 and disturben why?”
Ta tambayi zuciyar ta.
Zuciyar ta ce ta bata amsa tace
“Saboda kin saka wanda ke son ki cikin damuwa.”
“This shows that am concern with his problem. Why i am Worries with his problem?”
Ta kara tambayar zuciyar ta.
“Is because you love him!”
“I love him!”
Ta mai maita abinda zuciyar ta ya fada mata.
“If i love him what about Yaa Muhammad. How can I loves two person at thesame time!”
Ta girgiza kai. Sannan tace
“Inpossible!”
Ta dafe kai. Sannan tace
“Wannan kenan yanuna bansan *wa nake so?* ba”
Ido ta lumshe sannan ta bude
“How comes…”
Sai kuma ta cije baki. sannan tace
“Tayaya hakan zai faru. Kenan ban san *Wa nake so?* ba. Ya Allahu!”
Ta fada tana rufe fuskar ta da tafin hannun ta. Hawaye ne ya fara zubowa a idon ta sannan ta mike a hankali ta bar wajen dan daman Exam kawai ta kawo su school din.