WA NAKE SO CHAPTER 12

 WA NAKE SO CHAPTER 12

Aisha ce zaune ta yi zugum tana tunanin rayuwa, ba wanda take tsananin so da bukatar gani sai Yaa AK. Tin jiya da ta bacewa Yaa Muhammad bai kara ganin ta ba. Dan daki ta shige tana jin sa kuma ta kwanta kamar mai bacci wannan yasa bai tashe ta ba.+

Tana son kasancewa da kowa a cikin su ta kasa gane wanda tafi son kasancewa da. Tasan tana son Yaa Muhammad amman meyasa zuciyar ta take kawo mata tunanin Yaa AK wanda har bata da abun yi sai shi kuma shi ke debe mata kewa. Yaa Muhammad ne ya shigo dakin ta, tana ganinsa ta yi saurin bude littafi kamar mai karatu.

Zama yayi a gaban ta ya ce, ‘

“Aisha tawa ana ta karatun ne?”

Murmushi kawai tayi tai kasa da kanta. Dan satar kallon sa tayi taga ya zura mata ido hakan ya sa ta yi saurin kau da kai. Yana kallon ta yace

“Ya karatun to ba wata matsala ko?”

“Yaa A…..”

Sai tai shiru kuma. Kallon ta yayi yace,

“Mutumin nan yana da matsayi mai yawa a gun ki Aisha,  wanda har kina mantawa kina  kiran sunan sa,  ko duk dan ya tafin ne ko kuma meyasa ma kika damu haka?”

‘’Yaa Muhammad kawai dai ya taimaka min ne a rayuwa. Ban taba haduwa da mutum irin sa ba komai nasa daban ne ba ruwan sa a nutse yake ga hakuri sanyin hali da kamala. Sai yadda yake koyan karatu kullum fa muna tare amman yau kwana shida ban gansa ba. Ji nake duk ba dadi gaskiya ina kewar sa,  ina son na gansa mun jima bamu yi kwana ki haka ban ganshi ba.”

Ta karasa maganar cike da damuwa akan fuskar ta.

Take yaji ziciyar sa ta tabu wacce yake mutuwar so ita ke jin wannan feeling din aka wani ‘da namiji. Kallon sa tayi sai ya dauke kai yace

“Ba tin yau ba hankalina ya fara tashi akan halakar ki da wannan mutumin.ina tsoron kada ya kwace min ke Aisha saboda na lura kin damu dashi sosai Aisha. Na lura kina son kasancewa dashi baki da abu sai na labarin sa. A gaskiya ina kishin ki Aisha.”

Murmushin yake ta saki dan itama a yanzu ta fara gaskata cewar tana son Yaa AK amman dai tana kin yadda ne da kwabar zuciyar ta. Dan haka ne ma yasa ta saki murnushi dan bawa Yaa Muhammad kwarin gwiwa tace

“Just fa taimakon da yake min ne kuma na saba tare muka fara kararun exam tin waec har farkon neco da yanzu da baya nan. Ba wani abu in ba mutunci sai taimako da yake min ba. Mutumin dake da mata haba Yaya na,  meyasa za kai kishin sa ba fa sona yake ba kawai na dauke shi a matsayin Yaya na ne, ai kai kadai nake so kamar yadda kake sona’’

Murmushin jin dadi yayi wanda ya nuna mata komai ya wuce ya kuma  gamsu da bayaninta. Dan haka Ya ce, ‘’Aisha za ki aure ni ?’’

Dagowa tayi ta dan kalle sa sai kuma tai kasa da kai tace

‘’In ban auri Yaya na ba wa zan aura? Kai kadai kafi cancanca dani dan haka kai zan aura nasan ban da damuwa domin kai ne rayuwa ta. Majinginata ma hadib rayuwa ta in Allah ya yadda.”

Idon tane ya kawo ruwa wanda bata san ya digo kan littafin ta ba sao shine ya lura dan ya zuba mata ido jin kalaman ta da suka sanyaya masa rai. Yana ganin hawayen kuma ya matso ya dago fuskar ta. Kuka kuwa takeyi. Tagumi ya zuba yana fadin

“Me kuma ya faru dan Allah ki rufab asiri ki fadan menene kinji. Daina kukan muyi magana kinji Kanwata.”

STORY CONTINUES BELOW

Hawayen ta hau gogewa. Yaa Muhammad yace

“Fada min menene?”

“Ina son ganin Mama!”

Ta fada duk da ba hakan bane a ranta bata san me yasa ta kukan ba. Kallon ta ya tsaya yi tai saurin dauke kan ta dan tasan yanzu zai gano ta  dan haka ta kakalo murmushi tace

“Ni ban son kallon nan.”

Shima murmushin yayi yace

“Saboda baki da gaskiya ko?”

“Kai Yaya na ni din?”

Ta fada tana nuna kanta. Yace

“In ba haka ba ki kallen mana.”

“Nifa karatu nake kazo ka hanani gobe naje na rubuta hirar mu a jarabawa.”

Littafin gaban ta ya dauka ya bude ya duba sannan yace

“Bari nai miki bayani sosai.”

Kai ta gyada. Nan ya farai mata bayani tiryan tiryan tun tana ganewa har bata san lokacin da tunani yai mata karfi akan ta ba ta daina jin mema yake ji. Jin shirun ta ya dago yaga ta kura masa ido amman ko kiftawa babu wannan yasa yace

“Aisha!”

Amman shiru. Hannun sa ya tafa a fuskar ta wannan yasa ta zabura. Sai kuma ta kalle shi tai saurin dauke kan ta ganin yadda ta zuba mata ido.

“Tunanin me kike?”

Kai ta dan sosai ta fara kame kamen me kuma zatace can tace

“Jarabawa!”

“Jarabawa kamar ya?”

“Tunani na ace yau na gama jarabawa sakamako ya fito yai kyau.”

Ta lunshe ido tana murmushi. Shima.murmushin yayi yace

“To sai ki rage tunanin ki maida hankali akan karatun in an gama karatun kyayi tunanin karatun kinji?”

Kai ta gyada tana mai hamdala da ya yadda da ita dan kuwa ba abinda take tunani sai a wane hali Yaa AK yake

*

**

***

****

*****

******

Tafiya nake ina tsaki dan ba karamin batan rai wannan mutumin yai ba. Gida na karasa na tadda Momy zaune a falo. Zama nayi akan kujera ina zube kayan da na siyo. Kallon kayan tayi tace

“Uhmm aikin dai!”

Murmushi nayi nace

“Bismillah!”

“Nagode!”

Ta fada kwashewa nayi na mike na shiga daki. Agogo na duba naga har tara da rabi. Ruwa na shiga na watsa sannan na fito na saka kayan bacci.

Zama nayi a gefen gado na dauki wayata whatsapp na shiga ina dan dube dube na. Ina tsaka da chat Kira ya shigo min wayata. Kallon number na tsaya yi. Ban san ta ba. Kin dauka nayi ina kallon wayar call din ya kara shigowa wayar tawa.

Dagawa nayi a hankali na kai kunnena, Sallama aka yi daga daya bangaren cikin cool voice, Shiru nayi da farko, can kuma nace

“Waye ne?”

Murmushi naji yayi sai kuma yace

“Baki amsa sallama ne ke?”

Fuska na bata nace

“Ai ba dole ne in amsa a fili, who are you please?”

Murmushi ya kuma yi sannan yace

“Ohk first , how are you?”

Dan tsaki na saki nace

“But I asked who are you first?”

Yace

“Tsoro kike ji ne? Ai ba a satar mutum a waya ko?””

“Uhmm sure. Sorry I think it’s a wrong call bye…”

Zata dauke wayar yai saurin cewa

“Meyasa kike haka Doctor? Why are you doing so please?”

Nace

“Saboda naga ba ka shirya wayar bane. Dana tambayi waye sai kace wane ne shikenan. Saboda me zan na waya da wanda ban sani ba?”

“Am sorry zaki sanni but not now just call to say gud nyt sleep tight!”

Yana fada ya katse wayar. Da kallo ta bi wayar sai kuma ta saki tsaki.

Kan gadon ta haye tana gyara Kwanciyya. Tsaki ta saki sam a rayuwar ta ta tsani mu’amala da namiji in ba ta aiki ba. Duk maza yanzu basa gaban ta kawai ita aikin ta shiyasa sam bata basu fuska amman wasu sun fiya naci shiyasa ma take musu irin haka dan bata son suna shige mata.

Tsaki tayi tana fadin

“Da wancan dan rainin hankalin da wannan sun raina ni.”

Ido ta rufe tana addu’ar bacci.

*

**

***

Yana gama wayar ya zauna yana murmushi hannu ya saka yana shafa gashin kansa da ya kwanta. Ido ya lumshe. Matar sa Aisya ce ta fito,  kyakyawa ce son kowa kin wanda ya rasa. Sanye take cikin wasu kayan bacci masu kyau da tsada. Tana fitowa ta tsaya kallon sa can kuma sai ta matso tana fadin

“Ya dai Honey?”

Ta fada tana zama akan cinyar sa. Ido ya bude yace

“I miss u Baby!”

Hancin sa taja tace

“After all ai yanzu muna tare ko?”

Ido ya kanne mata yana murmushi. Kallon sa ta tsaya dan a duniya ba wanda take so da kauna kamar mijin ta. Idon ta ya hure yana fadin

“What?”

“I love u Sweetheart!”

“I love u more Honey!”

Rumgume shi tayi ya mike ya dauke ta cak kamar baby sukai dakin su.

*

Washe gari friday na shirya cikin doguwar riga ta shadda golding yellow 💛 wacce akai wa aiki a gaban rigar da coffe kalar zare wanda yake tin daga wuya ya biyo har tsakiyar rigar zuwa kasa. Hannun rigar ma haka sannan an bi aikin da yake mai circle ne stone fari. Dauri nayi mai kyau na saka dan kunnen gold sai agogo da abin hannu. Turare nai wanka dasu sannan na dauki mayafi na coffe kala da takalmi shima coffe kala sai jaka.

A falo na samu Momy. Tana ganina ta tsaya kallo na. Murmushi na saki nace

“Ina kwana?”

“Lafiya lou. Amman kinyi kyau!”

“Nagode!”

Na mike nace

“Zan tafi sai na dawo.”

“Zo nan!”

Momy ta fada. Kallon ta nayi ta kalli dining tace

“Maza je ki karya!”

Ba wasa a fuskar ta dan haka na wuce kawai. Tea na hada na sha ina cikin sha tazo ta bude flask. Dankali ta zuban mai uban yawa da kwai sannan ta tura min tace

“Ki maza ki cinye kuma.”

Haka na tura kamar zanyi amai na mike nace

“Na gama na tafi.”

“Allah ya bada sa’a!”

Na fita. Mota na dauka na bar gidan. Ina shiga asibiti na wuce office dina. Jaka ta na ajiye kawai na fita round. Sai karfe sha biyu na dawo na zauna. Wayata na dauko na sako kamar haka

_Morning My moonlight da fatan kin tashi lafiya. I just saw u. You look gergous da zan samu wata alfarma a min hoto a turo min._

Wani tsaki ta saki sannan ta goge text din. Aiki ta tayi na duba marasa lafiya. Na karshen da zata duba lokacin karfe uku ne ya shigo.

Dagowa tayi jin kamshin turaren sa. Ai kuwa suka hada ido shima yana sanye cikin kalar shaddar ta. Wacce yayi kyau a cikin ta kansa ba hula sai gashin da ya kwanta yai kyau yana sheki. Hannun sa daure da agogon azurfa. Kafar sa sanye da sau ciki baki. Yai kyau har ya gaji da yin kyau. Wani murmushi ya saki sannan ya karaso ya zauna kujerar gaban ta yana fadin

“Ina kwana Doctor?”

Fuska ta hade ta mike tana son barin wajen……Dagowa nayi jin kamshin turaren sa. Ai kuwa muka hada ido shima yana sanye cikin kalar shaddar ta. Wacce yayi kyau a cikin ta kansa ba hula sai gashin da ya kwanta yai kyau yana sheki. Hannun sa daure da agogon azurfa. Kafar sa sanye da sau ciki baki. Yai kyau har ya gaji da yin kyau. Wani murmushi ya saki sannan ya karaso ya zauna kujerar gaban na yana fadin

“Ina kwana Doctor?”+

Fuska ta hade ta mike tana son barin wajen

“Nifa ba wani abu ya kawo ni ba bani da lafiya ne kuma haka kike treating pateint din naki?”

Dan hararar sa nayi ta gefen ido sannan na koma na zauna nace

“Uhmm ina jin ka me yake damun ka?”

Hannu ya saka ya shafi sumar kansa idon sa akan ta yace

“Ciwon so ke damu na!”

Dagowa nayi da sauri nace

“As how? Ko da yake ni ba likitar wannan bangaren bace. Sai dai kaje ka nemi wani ya baka maganin sa.”

“I know but to me u re the only medicine to my Ache!”

Mikewa nayi ina hada kayan dake wajen. Ina gamawa na dauki handbag din ta nazo zan wuce sa.

Hannun na ya riko da sauri na juyo na fincike hannun nawa. Zan magana ya tare numfashina. Yana fadin

“Da ceton rai aka san likitoci Doctor.”

Kai na dauke na kuma kasa gaba kuma. ya dawo gabana yana fadin

“Ki taimakan da magani Doctor wallahi ina cikin zafin sa, sai dawainiyya yake dani. Tinda ita wacce nakewa taki saurara ta ki taimaka ki ban maganin please.”

“Wane magani kake tunanin zan iya baka. Bayan ban san ina yake maka ciwo ba.”

Na fada kai na a kasa saboda yadda naga yana bina da wani irin kallo.

“A cikin nan nake jin ciwon!”

Ya nuna kirjin sa. Dagowa nayi na dan kalle shi sannan nace

“Kamar yaya?”

“Ni dai kawai bana jin dadin sa. Yana damuna da tunanin ta da hasaso min ita a ko da yaushe sam bai bari na nayi aiki daga kwana biyu da na ganta bacci bana iyawa haka nan abinci ma bana iya ci ki taimaka ki bani magani.”

Agogon hannuna na kalla nace

“My time is off now. Kuma ina da program da zanje nayi a gidan radio dan haka kayi hakuri kaje ka samu Dr Auwal ko Dr Ahmad nasan zasu baka magani with good advice on how to treate ur ache.”

Ina gama fada nayi gaba da sauri.

“Fateema!”

Naji ya kira sunana. Juyowa nayi ina kallon. Wani murmushi ya sakar min yana fadin

“Ba mai iya ban maganin what am feeling sai ke.”

Kallon sa na tsaya. Ya matso kusa dani yace

“Yes ke kadai ce maganin ciwo na Fateema. Na fada miki ina son ki”

Yana fadar haka ya nufi kofa yana zuwa bakin kofa ya juyo yana fadin

“Sai wata rana.”

Sannan ya fice kan kujera na fada na zauna na zuba tagumi zuciya ta na bugawa da karfi da karfi.

Wayar ta dake cikin jaka naji tana kara da sauri na dauka na kai kunnen na

“Am sorry am on my way!”

Na fada na mike da sauri ina duba agogon waya ta wanda hakan yasa sam ban kallon gaba na dan haka naji nayi tuntube nayi gaba zan fadi kenan naji an taroni. Wata ajiyar zuciya na sauke sannan na fara kokarin mikewa ina dagowa naga wannan mutumin dai a gaba na. Baya nayi da sauri murmushi yayi yace

“Ki tafi a hankali.”

STORY CONTINUES BELOW

Ya juya. Kallo na bisa dashi sai kuma a hankali nace

“Thanks you!”

Ban san ma zai ji ba sai gani nayi ya juyo yana min murmushi sai kuma yace

“U re always welcome.”

Yai gaba. Da kallo na bishi har ya karasa parking space ya dauki motar sa ya fice. Nima da sauri na isa tawa motar na shiga na tafi gidan radion da nake da program acan.

Kan naje har anci minti biyar dan haka ina zuwa kawai fara answering call mukai ina bada amsa akan tambayoyin su da shawarwari.

Yana shiga gidan da yai parking motar sa. Kai ya jinginar a jikin kujera yana mai sakin murmushi sai kuma kamar an tabo shi ya dago ya kunna radio cikin motar. Searching stations ya dinga yi yana kanna wa na biyu yaji murya ta cikin sanyi da nutsuwa tana bawa wata mata shawara da tace zatai planing wane hanya zata bi.

Wanda take bata shawarar kamar haka

“A gaskiya kije asibiti tukkuna zasu gwada ki suga wanne ya dace da jikin ki. In kika je zakiyi kai tsaye zai iya kawo miki illa amman kika je asibiti aka duba ki za a ga a kan wanne za’a daura ki bayan an duba lafiyar ki sosai. Dan haka kada kiyi komai ki tafi asibiti kawai.”

Wata ce ta kara kiran wayar tai tambaya kamar haka.

“Doctor ina da ciki ne wata bakwai to amman in na tashi sai naji kamar mai nakuda dan kafafu na suna rike min kuma mara ta tai tamin ciwo. A shekarar baya nayi kusan irin haka wanda shima cikin yana wata bakwai ma na haifi yaron ba rai. Shine nake tambaya ko akwai matsala ne?”

Cikin nutsuwa yaji muryar tata tana fadin,

“Batun wancan karon kin haihu ba rai wata bakwai ya kamata kije a duba ki. Amman yanxu da kike cewa marar ki na ciwo kafar ki na ciwo wannan duk ba matsala, dan me ciki musamman cikin da yai nisa har wata bakwai. Nasha yin magana akan wannan musamman in ciki yai nisa yaro yana kokarin turmusa kan sa ne a kungun maman sa to wannan kokarin da yake na son turmutsa kan sa sannan kuma ga nauyin da yayi shi yake zama ya durrutse jijiyoyin kafa. Su wannan jijiyoyin sune suke taimaka mana wajen sarrafa kafafuwan mu. Saboda jijiyoyin da suke taimakwa ko mace ko namiji sune tun daga kugun mune. wannan yasa in tazo tashi zataji kafar kamar ba a jikin ta yake ba. Ko kuma taji in ta tashi kamar ba zaki iya daga ta ba. Wannan yake jawo ciwon kafa nauyin kuma da kike ji a marar ki saboda dan da yayo kasa ne. To koma dai yaya ne ya kamata by now ace ai kina zuwa awo dan haka in kinje kiyi bayani wanda in kinje za a kara bincikawa a gane ba wata matsala bace. In matsala ce za a magace miki.

Abun da zan kara bayani akan sa na ciwon marar nan ki tabbatar in kinje yin fitsari bakya jin ciwo in kuwa kina jin ciwo wannan na nuna akwai matsala kila kwayoyin cuta sun shiga dan haka in har haka ne ya kamata ki maza kije asibiti ko da ba ranar awon ki ba.”

Shiru nayi wacce take gabatar da shirin ta fara karanto wani sako da aka turo kamar haka

“Aslm Doctor ina da juna biyu wane lokacin zan fara zuwa awo?”

Kai na gyara nace

“Wannan kila haihuwar fari ce. To a gaskiya anan gida nigeria bamu da takaimaimai lokacin fara awo. A turai dai su tin kan ka samu ciki ma akwai awon da zakaje anan za afada maka sign na ciki in ka sama ka sani. Sannan akwai stage na wanda za akoya maka yadda zakai in kana laulayi sashe ne da ke koya yadda zakai rainon ciki at first stage da yake karami sannan akwai wanda ake yi daga wata uku shima. Amman mu anan abinda yasa ba zamu ce ayi bayan wata uku ba saboda akwai wadan da su kuma nasu cikin yana bukatar in so samu ne su fara awo kan wata uku. Misali wanda suke da bakin mahaifar su yake a sake in sun samu ciki da ya fara nauyi sai ya bare su wadan nan ana bukatar tun kan wata uku su fara awo wanda anan za ai duk shirye shiryen da za ai na bata kariya wanda in ma za a kulle bakin mahaifar dan kar cikin ya bare.

To kinga anan idan kai tsaye nace miki sai wata uku in kina cikin wannan jerin da matsala kenan dan yanzu kije asibiti. Amman in kuma kalau kake ya kamata da yai wata uku a fara awo.

Amman ace wacce zata fara haihuwa ne gaskiya da ta samu ciki a shawaran ce taje a duba ta agano menene matsalar.”

STORY CONTINUES BELOW

Shiru nayi sannan mai gabatar war ta dauki waya kamar haka

“Ina wa Dr fatan alheri.”

“Ina godiya!”

Na fada. Sannan tace

“Dr Ina da ciki wata takwas ina zuwa awo sai aka ce min wai yaron ba dai dai kwanciyyar sa take ba. Ina shan ruwa ina shan ruwa kuma har yanzu banji ya canja ba kuma gashi lokacin haihuwa na gabatowa.”

“Wannan ciki na nawa ne?”

Na tambaya. Tace

“Na farko ne.”

Nace

“Gaskiya ne idan kwanciyyar yaro ba dai dai bace gaskiya da matsala. Lafiyayyar kwanciyya na yaro shine kan sa na kasa kafar sa na sama idan ya kasan ce a zaune yake da akwai matsala. Kuma idan haka ne dole ai miki aiki gaskiya. Yaro zaki ga wani a giciye wani akai kai ce. Amman batun kisha ruwa gaskiya bansan inda aka samo wannan ba dan ban san inda aka ce in an sha ruwa zai sa kwanciyyar yaro ya canja ba. Ina jin a tunanin su in an sha ruwa suna zaton ko ruwan zai sa ruwan da yaron yake ciki ya karo kuma wannan ba haka bane a likitance. Amman dai gaskiya ya kamata a yanzu a fara tunanin yaya zaki haihuwa. Sannan zan baki shawara ko da wasa kada ki bari ki haihu ke kadai kuma a gida. Dan in kwanciyyar sa ba dai dai bane kika gwada haihuwa a gida daga ke yar dan kuna cikin hatsari. Saboda haka in ma a karamin asibiti kike awo ki koma babba a kula dake sannan a fara tunanin yadda zaki haihu. Bayan haka kuma wani cikin yana iya kai wa har wata tara bai juya ba to in hakan ne har yanzu kina iya sa ran da watakila ya juya din amman zai fi kyau tin yanzu a fara shiri ya za ai ta haihu.”

Watace ta kara kira tace

“Assamu alaikum Dr ina yini ya aiki?”

“Alhamdulillah!”

Na fada a hankali.

Tace

“Doctor ni ina yawan samun ciki sai ina yin bari. To da akwai matsala kenan?”

“Gaskiya da akwai dan matsala ke kawo yin bari ko ya kasance shigar kwayoyin cuta ta hanayar fitsari wani kuma zakiga ko da yaushe a cikin cuta na maleria da ya samu ciki sai tai bari. Ko kuma da ta samu ciki in zatai fitsari tana jin ciwo ko debetics da hawan jini. Ko masu bakin mahaifa a sake dan da ciki yai nauyi zai bari. Wasu kuma garkuwar jikin suce kan yaki d’a in an samu ciki. Abubuwan dai na da yawa amman zuwa asibiti zai sa ayi bincike a gano irin wanda kike da ta yadda za’a taimaka miki.”

Wata wayar ce ta kara shigowa. Shiru nayi ina sauraron ta tace

“Doctot Allah saka miki da alheri.”

“Amin nagode!”

Na fada.

“Dr nayi bari a watan 1 sai akai min wankin ciki sai na samu ciki a watan 2 to a watan 4 kuma sai cikin ya lalace aka karai min wankin ciki to tin lokacin ban kara samun ciki ba wanda nake ciki wani yanayi.”

“Wanne irin yanayi?”

Yana tambaya.

“Da in zanyi al’ada yana min kwana biyar yanzu to kwana uku yake min!”

“To da farko dai ina son ki fahimci cewa barin ki na biyu yana iya zama yana da alaka da barin ki na farko munsha fada a nan cewa in mace tai bari mafi karancin lokacin da zata kara bari ta dauki ciki to tabbata a kalla ya kai wata shida. To kinga kinyi bari a wata 1 kuma daga wannan bayan an miki wankin ciki a watan 2 kika kara samun ciki to kinga abinda ya biyo baya yana da matsala da na biyu. A yanzu dai ciki ba naki bane in son samu ne. Tinda kince kinyi bari a watan 4 to yanzu a kalla sai nan da watan 10 kafin ma ki fara tunanin kara samu ciki. Lokacin kin huta.

Dalilin wannan shine na farko kinga dai sanda kika samu ciki nan kin fara samun sauyi a jikin ki wanda akwai bukatar wannan yanayin ya juya ya koma kamar yadda kike kafin ki sake samun ciki wannan zai taimaka sosai wajen zaman cikin. Sannan ke akan ki nutsuwar da daidaituwar ki da samun kwanciyyar hankalin ki kasancewa yanzu nan kikai barin nan kina kara samun wani cikin kullum a cikin fargaba kike wanda wannan ma yana da tasiri wajen zubewar cikin ki. Sannan kuma abinda ya sanadin zubewar ciki na farko xai iya kasancewa bai bar ki ba. In ma har an gano. Kuma kila bama a kai ga gano wa ba gashi kinzo kin samu ciki na biyu to abinda ya lallata cikin farko zai iya lallata ciki na biyu yanzu shawarar da zan baki kiyi a kalla wata 6 kan ki kara samun ciki.”

Text aka turo kamar haka

“Dr ni na saka Emplain na wata uku amman bana sati biyu banyi ciwo ba ulcer tata tashi to shine naje aka cire min sai suka bani magani pills. Na yellow da ja amman yellow kadai nake sha saboda an ce in bana shan red din ban zan period ba to yanzu nasha jan jiya daga minti biyu sai na shiga nake jina wani iri.”

Kai na girgiza nace

“To da farko dai ina son naja hankalin ta kan cewar ba lallai dan an saka mata emplan kawai ke kawo mata matsala ba wai ta dinga ciwo ko ulcer ta tashi ba. Da waya tayi muka ji me take ji sosai watakila. Zai fi kyau dai da ta fadan me take ji dai muji yana daga cikin abubuwan da muka fada cewar idan mace tana kan tsarin planing din zai iya ja mata.

Na biyu batun zancen cewar ance kada kisha red din saboda kada kiyi al’ada a gaskiya ba dai dai bane dan kina kan maganin planing ki dinga cewa ke bakya son kiyi al’ada gaskiya bai kamata ba indai ba wani dalili da likita ya bayar ba, dalilin da yasa in kika ce haka zakiyi to kamar kina tayin irin abin nan ne da masu lallurar nan da mukai bayani wanda basa fidda kwai (marasa haihuwa) wanda muka ce fatar jikin mahaifar su zatai ta ginuwa tai ta kauri sai lokacin lokacin da suka tashi yin al ada sai siyo ta mai yawa muka ce tana zuwa da wani irin burtaci burtaci to kwatan kwacin haka kike kwatan tawa. Ma’ana fatar jikin mahaifar tana ta kauri kuma kin hana jinin ya zuba to saboda haka abinda zai biyo baya randa duk kika sha ja.

Shi ainahin wannan jan ba wai magani ne da zai jawo al alada ba shi magani ne na karin jini. Amman dan kar ace tsallake sati daya mace kuma ta manta ta kwana goma ko ta kwana fiye da haka bata sha ba to sai akayi wanda zai taimaka mata wajen karin jini. Shan jan ba wai lokacin da kika sha zai zo ba kila ma sai kinyi kwana daya zuwa biyu sai kiga yaxo. Shi ba magani ne da zai jawo matsala ba shi magani ne dake kara kawo karin jini.

Akwai wasu sabida yanayin da suke shiga in sun zubda jini to akan ce wani lokacin a barsu sukai wasu watanni kan suyi al’ada.

Ko kuma misalin da na bayar na masu zuwa aikin hajji suce bari in yi kaza wanda wannan din shima ina gargadi akan a daina yin sa kai tsaye ba tare da shawara masana kiwon lafiya ba. Domin shin sa shi kadai yana kawo matsala dan sai kinje acan wajen aikin hajji abu ya baci ki fara al’ada. Amman kika bi shawarar masana komai zai zo miki da sauki.

Anan abinda zance miki shine kada ki kara kin shan jan gaskiya.

Ina baku shawara akan cewa duk lokacin da zakuyi planing kuje asibiti kada kuyi kai tsaya.”

Anan muka tsaya akai concluding din program din dan lokaci ya riga ya cika.

Anan mukai sallama da ma’aikaciyar gidan radion sannan na fito dan na tafi.

Yana cikin motar sa tinda ya jingina kan sa a jikin kujerar bai dago ba yana sauraron muryar ta. Matar sa da taji shigowar sa kuma taji shiru yasa ta fito.

Taci kwalliya cikin wani dakareren leshi kai ka zata gasar kyawawa ko kwalliyya za ayi da ita. Wajen motar ta nufo tana zuwa ta tsaya tana kallon sa. Tafi minti biyu sannan yaji kamshin turaren ta shi ya dawo dashi daga tunanin ya tafi ya dago kansa a hankali ya sauke akan ta.

Murmushi ya sakar mata yana fadin

“Sweetheart!”

“Me yake damun ka?”

“Me kika gani?”

“Tin dazu ka dawo fa amman baka shigo ba.”

“Wani program naji mu shiga ciki muyi magana.”

Ya fita ya zagaya ya kama hannun ta sukai cikin gida.

A falo ya zauna ta kalle shi tace

“Honey ba zakai wanka ba.”

“Bar wankan nan.”

“To abinci fa.”

Kallon ta ya tsaya yi. Ta marairaice fuska tace

“Please mana.”

Mikewa yayi suka karasa dining nan tai serving nasa kadan yaci ya koshi. Falo suka koma ta zauna akan cinyar sa ta sakalo hannun ta ta wuyan sa tace

“Fada min menene ?”

“Wani program naji da wata likita wanda ya ja hankali na akan muje mukai matsalar mu ko Allah zai sa a dace.”

“Kana ganin hakan ba matsala.”

“Sure!”

“But wane asibitin ne?”

“US Clinici!”

Ido ta zaro tace

“Ranan kawata ke bani labarin sa. Domin itama taje kuma tace suna aiki sosai.”

“Ok shikenan zan amsar mana appointment dan haka sai ki shirya ko?”

“Insha Allah. Allah yasa mu dace!”

“Amin Honey!”

Fuskar sa ta shafa tana murmushi tace

“I love u honey!”

“Love u more Baby nah.”

Yai peck nata a kumatu.

Daga gidan radio gida na nufa kai tsaye. Biyar da rabi na shiga cikin gidan. Parking nayi na fito hannu na rike da jaka ta na gaji sosai. Dan haka a hankali nake tafiya har na shiga falon mu.+

A falo na samu Momy na waya dan haka na zauna akan kuujera ina fadin

“Yaa Allah!”

Jingina nayi da jikin kujerar ina mai lumshe ido na. Ina jin Momy ta gama wayar na bude ido na a hankali. Kallon ta nayi na ce

“Sannu da gida Momy!”

“Yauwan. Ya aikin?”

“Alhamdulillah!”

“Yanzu ai nagama jin program din ki na ‘A tambayi likita!’ “

Murmushi na saki na mike zaune nace

“Bari nai wanka na fito.”

“Ok amman yaushe zaki gidan Hajiyar Fu’ad ne?”

Ido na zaro nace

“Kai wallahi na manta ai.”

“In kin shiga ki shiryo kawai.”

“To Momy!”

Na fada nayi d’akina. Ina shiga na fara cire kayan jiki na ratayesu. Towel na daura sannan na shige ban daki. Ina fitowa na shafa mai na saka doguwar riga pink mai blue stone. Banyi kwalliya ba sai tashin kamshi nake. Wardrobe na isa na dibi kaya kala hudu sannan na dauki na bacci da under wears dina da turare mai da mayafai da hijab. A karamin akwati na saka dukka abubuwan da zan diba har da toothbrushe dina. Wayata na dauka da system dina na fice falo.

Akan kujera na zauna nace

“Na fito.”

“To me zaki kai mata?”

“Me kike ganin zan kai mata?”

“Ki siya mata sabulun wanka da wanki da lemuka da wasu abubuwan.”

“To Momy!”

Na mike rike da jaka ta nace

“Na tafi.”

“Allah kiyaye hanya.”

Na fita. A cikin mota na saka kayan na zauna sannan na tada motar na fice. Sulermarket na shiga na dibar wa Hajiya kaya masu yawa sannan na biya na koma mota ta.

Minti ashirin  ne ya kai ni gidan. Nai horn mai gadin su ya bude min. Parking nayi sannan na  fito da kaya da nazo dasu. Yaran da ke musu aiki na ganina suka taho da sauri suka dauki kayan sukai ciki dasu. Motar na rufa nabi bayan su.

A falo na tadda su suna fadawa Hajiya nice nazo. Ina shiga ta mike ta kamoni tana fadin

“Ashe dai zaki zo!”

“Wallahi Mama Aiki ne ma ya rike ni.”

“Ai ban jima da gama jin program din ki ba Allah yayi Albarka ya kara basira.”

“Amin Mama! Ina yini?”

Na durkusa ina gaishe ta. Dago ni tayi a zaunar akan kujera tana fadin

“Lafiya lou yasu Momyn taki?”

“Tana lafiya tace in gaishe ki.”

“Ina amsawa.”

“Ga kaya nan Mama ba yawa!”

“Oh Fateema bakya gajiya haka ko?”

Murmushi nayi nai kasa da kai nace

“Ai ba yawa.”

Tace

“Mai yawan kenan. Allah yayi albarka.”

“Amin!”

Na fada kaina a kasa.

“Jamila! Jamila!!”

Ta kira mai aikin ta. Da sauri zo. Tana gani na tai murmushi ta gaishe ni cikin girmamawa nima na amsa cikin sakin fuska. sannan Hajiyar Fu’ad tace

“Dauki kayan ta ki kai daki na.  Sannan ki turo min Hanne ta dauke kayan nan.”

STORY CONTINUES BELOW

“To Hajiya.”

Ta mike ta dauki jaka ta, ta tafi. Hanne ta turo sannan ta tafi kai jakar. Hajiya ta sauka tana duba kayan. Sai Hanne tazo gaishe ni tayi. Na amsa mata. Hajiya ta raba gida biyu duk abinda na kawo tace

“Dauki kayan nan ki kaiwa Hajiyar cikin gida kice mata Fateema ce ta kawo.”

“Toh!”

Ta dauka ta fita. Kiran sallah mukaji ana yi ta Magariba wannan yasa Hajiya ta mike tace

“Muje muyi sallah!”

Dakin ta muka shiga nai alwala na zauna anan kan sallaya. Itama tana kan tata daga ni har Hajiya ba wanda ya tashi a inda muke har akai sallah isha’i.

Sai da aka idar sannan Hajiya ta fita bata jima ba ta aiko Hanne tazo ta kira ni. Mikewa nayi na fita. A falo na same ta tana zaune. Nan Hajiyar Fu’ad ta saka yan aikin ta suka cika min gaba da kayan abinci kala kala.

“Zauna kici Fateema!”

Na zauna na dibi shinkafa da miya. Kallon abinci Hajiya tayi tace

“Haba Fateema ki sake kici abinci. Bari na tashi in kunya ta kike ji.”

Da sauri nace

“A’ah wallahi Mama zan iya ci ki zaman ki ba wata yunwa nake ji ba hakan ya ishe ni.”

“To ki zuba pepper soup din kici dan Allah ki koshi.”

Na zuba ina ci a hankali. Ita tuwo taci bayan na gama na mike zan kwashe kayan amman sam Hajiya ta hanani dole na koma na zauna. Yan aiki tasa suka kwashe.

Kallon Hajiya nayi nace

“Zan shiga na gaishe Hajiyar cikin gida.”

“To shikenan.”

Na mike na fita.

Cikin gidan na nufa acan na samu hajiyar cikin gida zaune ita da wasu jikokin ta da ya’yan yan uwan ta. Mata ne su hudu. Ina shiga ta saki murmushi tana fadin

“Aah fateema yau kece a gidan namu?”

Kaina a kasa nace

“Wallahi Hajiya ina yini?”

“Lafiya Alhamdulilah yasu Hajiyar taki da aiki?”

“Lafiya Alhamdulillah!”

Yan matan Hajiyar ciki gida ta kalla tace

“Baku gane ta bane?”

Daya a ciki ta ya mutsa fuska tace

“Ba Matar Uncle Fu’ad bace ta da?”

Dayar ta zungure ta tace

“Ina yini Anty Fateema?”

Murmushi nayi nace

“Ya kike?”

Itama murmushin tayi tace

“Ya aiki. Wallahi ina jin program din ki sosai kuma muna karuwa Allah bada lada ya kara daukaka.”

Murmushi kawai nayi nai kasa da kai na.

“Mtszzz!”

Naji anyi tsaki an fara tafiya. Dagowa nayi naga wata budurwa ce ta wuce ciki. Kai na dawo dashi kasa. Dayar dake dannan waya tace

“Ina yini?”

“Lafiya lou!”

Nima na bata amsa a takaice. Wacce muka gaisa tace

“A ina address din asibitin ki yake ne?”

Nan ba bata address tace

“Insha Allahu wata rana zaki ganni.”

Nai murmushi nace

“Ina zuba ido.”

“Nusaiba kawo mata abinci!”

Hajiya ta fada. Wacce muke magana ce ta mike nai saurin fadin

“Wallahi Hajiya na koshi yanzu na gama cin abinci.”

“Kai Fateema?”

“Wallahi Hajiya na koshi kuma dare ya mayi tara ta wuce bana kara cin abu sai safiya.”

“Kaga likitoci manya. Allah taimaka.”

Kai na a kasa muka amsa ni da Nusaiba. Da

“Amin!”

Haka ta dinga jana da hira da yan tambayoyi akan kiwon lafiya sosai nai nata bayani kuma ta gane. Dan har me dane danen waya ta mike zaune tana kallo na bata dai yi magana ba amman da alamu na burge ta ne dan sai kallo na take tana gyada kai hadi da murmushi.

Karfe tara da rabi nace

“Hajiya zan je na kwanta sai da safe!”

“Lah ba zaki kwana a gun yan uwan ki ba.”

Shiru nayi. Nusaiba tace

“Hajiyar cikin gida nima binta zanyi a wajen Hajiya zan kwana.”

“To shikenan. Sai da safe.”

Muka mike muka fita muna tafiya tana karai min wasu tambayoyin a haka muka karasa Bangaren Hajiya. Tana falo muka same ta dan haka ta kalli Nusaiba tace

“Me kuma Kika zo min bayan guduwa kikai kika barni.”

“Kai Hajiya ai gun yan uwana naje kuma yanzu da na samu wata yar uwar ai gashi na dawo.”

Haba Hajiya ta rike tace

“To koma inda kika fito.”

“Kai Hajiya  in na tafi fa ba zaki kara gani na ba sai kinyi kuka.”

“Allah kiyaye me kike min zan neme ki ji ni kam!”

“Kaji Hajiya ai zaki zo ne kice nazo.”

“A’ah ni dai kar kisa min hajiya magana da daren nan a barta ta huta.”

Na fada ina murmushi.

Hajiya ma tai murmushi tace

“Yauwah ‘ya ta fada mata ta barni na huta ehee!”

Mukai murmushi. Hajiya ta mike tace

“Daman ke nake jira in rufe kofa naje na kwanta “

Ta mike zata rufe kofa da saurii na mike na rufe kofar tace

“Allah yayi albarka.”

Nace

“Ameen!”

Hanyar dakin ta ta nufa tana fadin

“Sai da safe to.”

“Allah tashe mu lafiya “

Muka fada ni da Nusaiba.

Kallo muka zauna muna yi muna dan taba hirar film din mune har sha biyu idon mu biyu dan haka muka mike na kashe kayan wutar mukai dakin da ke kusa da na hajiya.

Wanka nayi na sa kayan bacci na hau kan gadon. Nusaiba ma na fitowa a wankan ta biafiyar gado

*

**

***

****

*****

******

*******

Zaune take tayi nisa a tunani ta dan ta zuba tagumi hannu bibbiyu. Bata san yana kan ta ba sai ji tayi kawai yana goge mata hawayen dake bin kumatun ta da sauri ta dago tana ganin shine ta saka hannunta karasa goge hawayen idon nata.

Ido ya kura mata ba ko kiftawa. Kanta tayi sauri tai kasa dashi. Zama yayi yana mai cigaba da kallon ta yace

“”Aisha me ke damun ki? Me kike yawan tunani? da na zaci girma ne ya canja ki amma yanzu na lura akwai wani abu. Na yi zaton ba kya boye min abu ko ma meye ni ne mutum na farko da zai sani, amma naga alama kin canja wannan damuwar taki boye min kike. Ba tin wannan zuwan na gane kina da damuwa ba tin wancan amman kika ce ba komai sai dai ta wannan naga tafi ta wancan dan wannan ramar da kike kila har da damuwar da kike ciki ne dan ina lura dake bakya bacci dadin abun ma naga gaban Allah kike kwana mika masa bukatar ki gashi bakya cin abinci shin rayuwa zata tafi a haka. Na gane wannan damuwar taki mai girma ce tin da har kika kasa fada min to yanzu na tambaya. Ki fada min menene damuwar ki?”

Kai ta hau girgizawa a sanyaye tace

“Nifa ba komai!”

Kallon ta ya tsaya yace

“Aisha  ko ba kya so na ne? Kin daina s……”

Sai a lokacin ta dago kan ta da sauri ta kalle shi tunda ya fara Magana ta yi saurin katse shi, tana fadin

‘’Kar ka fadi haka Yaya na,  kada ka kara fadin haka, ina sonka, kai ne mutumin da nake son yin rayuwata tare da shi, kaine komai nawa Yaa  Muhammad. Kai ma ka san ina son ka Yaya na, kar ka sake fadin haka dan Allah’’

Jikin sa ta fada  tana fadin

“Me zai kawo maka kwanciyyar hankali Yayana auren mune kadai zai kawo maka kuma ya tabbatar maka da ina son ka. Na yadda ko a yanzu Baba ya daura mana aure.”

Yaushe rabon da yaji Aisha a jikin sa tin da ta fara girma ta gane shi ba muharamin ta bane wanda a isilamiyya aka fada musu tin lokacin dan haka wani abu yaji ya ratsa masa tin daga kan sa har tafin kafar sa.

Yana son Aisha yana tausayin Aisha fiye da tunanin me karatu. Ta tashi ba uwa ba uba duk da su Umma da Baba sun tsaya mata ba me cewa bata ba su suka haife ta ba.

Sheshekar kukan ta yaji dan haka ya saka hannu ya zagaye ta yana bubbuga bayan ta a hankali. Cikin kuka take fadin

“Ban san me ya shiga kai na ba ya canja min rayuwa da buri na da nafarki na. Amman na baka dama Yaya na ka canja min rayuwa ta. Nafi gane kai na a waccan rayuwar *wannan rayuwar* tana hargitsan lissafi na. In ka aure ni, ne kadai nake tunanin zan fita a *wannan rayuwar* da nake ciki. Nasan zaka dawo min kamar yadda muke da kai min wanki ka tayani shara muyi girki tare na kwana a wajen ka ka goya ni ka tsefen kai ka taje min kai min kwalliyya Yaya na. Ina son wadan nan abubuwan su dawo ko naji komai nawa na baya ya dawo yanzu sun gudu sun tafi sun barni. Zaman mu in mun koma kamar da shi zai dawo min da abubuwan da suka tafi suke son komawa wani wajen.

Yanzu yaushe rabon mu zauna ni da kai na fada maka abinda nake so, in fada maka burina da abinda da nake so in zama a rayuwa, kai kuma ka dinga taimaka min kana sa ni a hanya kana nuna min yadda burina zai cika. Yaushe rabo,  wannan yasa na bawa wani wannan damar. Abun na damu na tayaya haka ya faru….”

Ta fashe da kuka, tace

“Yaya na ka dawo dani Aishan da ba wannan ba ka canjo ni yanzu ban san in zauna waje daya haka in yi shiru,  na kasa tunanin komai na kasa yin komai, ba na iya aikata komai, na zama kamar ban da amfani, ina ganin rayuwata na tafiya ba tare da na yi komai ba. Ya Muhammad ban san *wannan rayuwa,* ka taimaka min in koma kamar Aisha da nake da’’+

Kallon ta yake kamar talabijin, ya lura ba ta hayacinta ma bai taba ganin ta a cikin irin wannan makammancin halin ba sai yau. Hankalin sa ya mummunan tashi,

“Tabbas ba zan yafe wa kaina ba tuntuni na kasa tambayar Aisha meye matsalarta, duk da a tunanina za ta iya fada min da kanta ba sai na matsa mata da tambaya ba, na manta cewa yanzu lokaci ya canja, haka komai ma ya canja.”

Maganganun da yake fadi kenan a cikin zuciyar sa.

Ya ji kamar ya fashe da kuka, kan sa ya kulle ya kasa gane ina ta dosa duk da ya halakan ta haka da bata haiyacin tane amma wasu abubuwa na masa yawo a ka yana so ya gano su yana son ya tambaye ta amman me? Yadda take kuka kamar ranta xai fita dan har numfashin ta sama sama yake shiyasa ya janyo ta jikin sa ya rumgume ta sosai kamar zai maida ta cikin jikin sa ya dinga bubbuga bayan ta a hamkali yana fadin

“Ki kwantar da hankalinki, saurare ni ban san me ya kawo canji rayuwarki ba, ban san me ya sa komai ya canja a tare da ke ba, tunaninki, yanayinki da komai ya canja. Ina son ki mai da al’amarinki ga Ubangiji shi ya fi sanin me ke boye, ya fi mu sanin abinda bamu sani ba.

Sannan na biyu Aisha komai lokaci ne, Aisha in lokaci yayi za mu yi aure, ina miki so na hakika, haka zan taimaka miki in ga kin yi abin da kika yi niyya, zan taimaka miki ta kowace fuska in ga burinki ya cika. Sannan Yayan ki ya miki alkawari muddin yana raye zan miki komai, ba zai barki ki kuka ko ki shiga wani hali makamancin wannan ba. Zan zama makari katanga gare ki in share miki duk wani abu da zai bata miki rai ba abinda zai saki hawaye sai farin ciki wanda shima bana so.”

   

Ya dan shafa kanta yace

“Ki kwantar da hankalin ki da naso sai na gama service nayi settling sai muyi aure amman tin da haka ne zan karai wa su Baba magana ai mana auren mu kawai mu ko anan gidan ma zauna sai a hade dakin ki da nawa ya ishe mu kan nan na gama service in ya so aiki da gidan su zo daga baya. In dai ina rayen dukkan abinda Aisha na ke so shi za a mata, don haka share hawayenki ki yi dariya, komai zai warware burin ki zai cika zaki farin ciki insha Allahu. Domin ina nan zan miki dukkan maganin matsalolinki, zan share miki dukkan hawayenki’’

Ya dago kanta yana goge mata hawaye. Murmushi ya sakar mata itama ta mai da masa tana fadin

” Nagode Yaya na. Allah ya kare min kai ya biya maka bukatun ka na alheri. Allah ya dafa maka ya barmu tare.”

“Ameen Aisha nah!”

Ya fada yana jan hancin ta. Kai tai kasa dashi.

Daga haka kuma suka fara hira duk dan ya rage mata tension ya debe mata kewa. sosai ta sake har da su kyalkyala dariya ahaka kuma har bacci ya kwashe ta, ya zaune a gun yana kallon ta yana jin kaunar ta a ransa. Son ta mai tsananin ya dinga bijiro masa. Mikewa yayi ya gyara mata kwanciyya ya rufe ta da abun rufa sannan yai mata addu’a ya tofa mata ya fita.

Yana shiga daki ya kwanta kasa bacci yai kwata kwata dan yana tunanin kalaman Aisha wanda yana son ya gano inda suka dosa me yake faruwa me ya canja ta haka sam bai bacci ba tunani yake kawai wanda ya kasa gano komai.

   

Aisha kuwa yaushe rabon ta da bacci dan haka tinda ta kwanta take baccin sosai dan ba karamin bashin sa taci ba na kwana ki dan haka ba ita ta farka ba sai asuba. Sosai tai mamaki baccin da tayi.

STORY CONTINUES BELOW

Sallah tayi ta zauna akan sallaya tana addu’a. Bayan ta idar ta koma kan katifar ta. Ba abinda take tunani sai abun da ya faru jiya.

Dan jiya kadai da ta fadi wani abu dake zuciyar ta taji dadi kuma taji saukin abun sosai a ranta. Mikewa tayi tana fadin

“Allah sarki Yaya na mutumin kirki, mutum mai adalci, na ji an ce SO daya ne tak, haka mutum ba zai so abu biyu lokaci guda ba, musamman mace namiji daya za ta so. To amma ni me ya sa zuciyata take yaudarata ? me ye sa take min karya? me ya sa zuciyata ta kasu biyu ? tabbas na san daya karya ne daya gaskiya ne. Wanda Yaya na shi ne gaskiyar rayuwata.”

Shiru tayi sai kuma tace

“Amma me ya sa tun rashin sa yasa na kasa samun sukuni? me ya sa nake ji kamar bazan iya rayuwa ba shi ba? me ya sa zuciyata take ta maimaita min cewa na yi ba daidai ba na kin  fada  masa ina son sa,  amman kuma ni ga hakane dai dai Me ya sa nake jin ba zan iya rabuwa dashi ba. Meyasa bai zo ba kuma bai kirani ba?”

Abin ya dame ni, ya tsaya min arai na kasa sukuni. me ya sa nake jin rasa shi kamar rasa wani babban abu ne a rayuwa ta? Dan me ka tafi ka barni baka kara nema na ba kasan a wane hali nake shin wannan ce soyayyar da kake min kana ina Yaa AK. Kwana nake tunani da tsamanin zuwan ka ko kiran ka.”

Koma wa tayi ta zauna tana fadin

“Meyasa ban fadawa Yaya na wannan abubuwan? me ya sa ma nake fargabar fada masa wannan abubuwan? Me ya sa ba na so ya san komai game da Yaa AK? bayan ba sirri ko ‘yar boye-boye a tsaninmu.”

Ta fashe da kuka,

“Wayyo Allah Yaa AK ya zanyi ya zanyi? Ya Allah ka kawon dauki cikin rayuwa ta. Ka kular min da Yaa AK kasa baya cikin wani hali ka kare min shi yaa Allah.”

Kwanciyya tayi tana kuka wanda bata san lokacin da bacci ya dauke ta ba dan kuwa taci bashin sa dole a yanzu ta rama shi. Ko ta shirya ko bata shirya ba.

Washegari basu da jarrabawa  don haka ba ta ma tashi ba,  Sai   Wajen karfe sha daya ta tashi tayi wanka ta shirya, sannan ta nufi gun Umma a kicin bayan ta gaishe ta, ta ce, ‘’Umma me ya sa baki tashe ni ba? kin ga yau ba aikin da na miki’ ina ta bacci.”

“Aisha na lura dake sam bakya bacci kwana biyu dan tin asuba ma kike gama aikin gida da dare a kan sallaya kike kwana to ni kuwa dan me zan tada ki yau kin samu kina ramuwar sa. Ai ni dadi naji wanda hakan ya nuna kin samu sassauci ko kin gane wani abu. Wanda hakan ya kawo miki relief a rayuwar ki. Dan Allah ki daina saka abu a ranki ki mikawa Allah komai kinji.”

Kai ta gyada tace

“Nagode Umma.”

“Maza ga abincinki can kije ki karya.”

“Ina Yaya na?”

“Ya fita. Ya leka ai ya tadda kina bacci.”

Fulas ta dauko tw hada tea sannan na fara cin bread da awara da kwai da aka soya. Kadan taci ta mai da kayan ta dawo ta zauna a kusa da Umma.

“Kwana biyu Yayan ki ba ya zuwa ina dai ba korar sa kikai ba?”

Idon ta ne ya kawo ruwa tace

“Wallahi Umma ban koreshi ba nima bansan meyasa ba.”

Sai ta saka kuka. Shiru Umma tayi tana kallon ta can tace

“To ya isa menene na kukan Allah yasa lafiya dai.”

“Amin!”

Sai kuma ta mike tayi daki. Da kallo Umma ta bita.

*

Bata fito ba sai da akai kiran sallah tayi alwala ta koma daki sallah tayi tai addu’a sannan ta dauko littafi dan ta duba gobe suna da jarabawa.

Karfe hudu da rabi ya shigo gidan dakin ta ya shiga ya same ta zaune akan katifa rike da littafin ta. Zama yayi yai mata murmushi yace

“Sarkin karatu!”

Murmushi tayi tace

“Yaya ina ka shiga yau i miss you!”

Hancin ta yaja yace

“Ko? Ina can zancen auren mu.”

Fuska ta rufe da tafin hannu yace

“Eh mana ko?”

Murmushi tayi tace

“Sannu da zuwa!”

STORY CONTINUES BELOW

“Yauwah kanwata!”

Ta mike kallon ta yayi yace

“Ina zaki kuma?”

“Abinci zan kawo maka.”

“Dawo ki zauna na koshi. Wanka zanyi zafi nake ji.”

“Toh Yaya.”

Ya mike ya fita. Kallo ta bisa dashi sai ta lumshe ido ta bude hawaye na zubo mata.

Sam ba zata iya cewa bata son Yayan ta akan Yaa AK ba dan wannan ba dai dai bane ba adalci bane Yayan ta shi ya fara son ta dan haka shi zai same ta.

“Allah ya baka hakuri Yaa AK nima ina son ka amman ba zan iya ba. Bazan iya ba.”

Ta fada tana goge idon ta.

*

*

*

Aliyu ya kira Faisal ya fada masa komai. Faisal yace

“Aliyu yarinyar nan tana son ka,  sai dai akwai wani al amari babba. Abinda na lura ba zata iya kin yayan ta ba dan tana ganin yai mata abu mai yawa a rayuwar ta. Bama haka ba tana ganin in taki shi a gida kuma fa? since kace iyayen sa ke rikon ta. Amman ni a gani na kaje musu kawai akan kana son auren ta.”

“No Faisal i can’t do that ba zanwa Aysher dole ba in har bata so ba zan mata ba ni na yadda na mutu ita ta rayu na yadda na shiga halin kunci ita ta kasance a farin ciki na yadda komai mai kyau ya same ta ni kuma opposite to that but i can’t do such things to her. Sam duk abinda ke faruwa ban jin haushin ta ko wani abu. Ina dai son tane dan haka zan iya komai dan samiwar farin cikin ta.”

“Sure! Kuma fa haka ne. Kayi tunani mai kyau gaskiya yanzu dai abinda zan ce maka shine ka dage da addu’a tinda tana sonka komai mai sauki ne. Addu’ar ka ita ce mafita akan Allah ya zaba muku abu mafi alheri. Kayi hakuri kuma kada ka sa damuwa. In Aisha rabon kace Allah zai baka in ba rabon ka bace zaka ga Allah ya saka maka dangana ya kawo maka mafita a rayuwa wish u all the best friend.”

Murmushin karfin hali yayi yace

“Thanks you Friend. Amman gaskiya ina ji a rai na in har na rasa Aysher kamar na rasa rayuwa ta ne. Bansan lokacin da Aysher ta zama jinin jiki na ba. Ban san lokacin da ta zamar min komai ba. Yaa Allah ka shiga lamari na. Nagode sosai Faisal. Sai anjima”

Ya kashe wayar. Idon sa na kawo ruwa. kan ya farga har hawaye sun fara zubo masa a fuska hannu ya saka ya shafo su sosai ya tsaya mamakin wai yau shi ke kuka akan wani abu. Ikon Allaj kuma akan mace bayan a da bai dauki mace a bakin komai ba.

Kai ya girgiza yana fadin

“Yau ni ke kuka akan mace duk aji na da matsayi na yau ni ke son wata mace. Allah nagode maka. Allah nagode da wannan jarabawar da kai min a rayuwa Allah ka ban ikon cinye ta.”

_Bayan sati daya_

Aliyu kuwa tin yana iya fita office har ya zamo ba inda yake zuwa. Daga daki sai bandaki kadai yake iya zuwa. Sam baya gane komai da kowa.

Zaman daki kadai yake ko wayoyin sa sam basa shiga. Gaba daya ya kasa gane kan sa. Shi baya jin haushin Aisha sam domin kuwa shima awannan lokacin ya dau dangana in har son Yayan nata zai faranta mata to shima yana son. (Wannan ita ce kauna da soyayyar gaskiya).

Domin ya yadda shi ya mutu ita ta rayu. Lokaci daya ya hadu da Aisha kuma Allah ya daurawa masa son ta a haduwar farko zuciyar sa ta aminta da ita. Son ta yai karko a zuciyar sa da ran sa tayo karko. Duk ajin sa da jin da kan sa yanzu bai jin su. Hakika a yanzu ya yadda ya mutu ita ta rayu indai zata samu farin cikin ta.

Duk yadda yake son ta ya danne son ta amman hakan ya gagara dan wani ciwo da yake ji. Sam bai jin dadi ga wani matsanan cin ciwon kai da kirji. Ko yaje office ba abinda yake sai kwanciyya wannan ya daina fita ko ina. Ya yadda in dai yana raye son Aisha bai barin sa to dan haka ya yadda shi ya mutu ita ta rayu,  son da yake mata sam ba zai kidayu ba.

Ba abinda yake so sai son jin muryar ta,  yaji kalaman ta da muryar ta mai laushi da dadi sai son ganin fuskar ta mai kyau amman kuma baya so yaje ya ganta ta fama masa wani abun dan in ya ganta kuma ya tuna cewa Aisha wani take so daban bai san ya zai ji ba.

STORY CONTINUES BELOW

Mai gadi kan sa ya gane mai gidan nasa bai da lafiya dan da kyar yake iya fitowa yaje massalaci shima kan ya karasa ya tsaya yafi sau nawa yana hutawa.

Wanda yau kwana sa biyu ko massalacin ma bai fito ba. Wannan ya daga hankalin sa ya isa kofar ya dannan bell amman ya danna yafi sau uku ba a bude ba. Bakin gate ya koma ya zuba tagumi yana fadin

“Ko dai na shiga ne?”

Can ya kuma mikewa ya je ya kara dannanawa amman shiru. Kara dannawa yayi aka zo aka bude mai gyaran gidan ne ya kalle shi yace

“Wai Oga lafiya kuwa?”

“Nima abinda nake magana kenan kusan sati ko girki in aka masa bai taba kayan ma. Ni gaskiya yau kusan sati biyu rabon da na saka shi a ido na ma. Daman dakin da yana nan da baya nan ba wani datti yake yi ba kawai ana gyarawa ne. Haka abincin ma baci yafiya ba amman yana dan taba wani abu amman kaga kwana biyun nan wallahi ko table din bai tabawa.”

“Ikon Allah. Ina ne dakin sa?”

Stair ya nuna masa yace

“Sama ne.”

Da sauri ya nufa yana hawa yaga dakuna birjik wajen guda biyar rasa wanda zai shiga yayi na hannu daman sa ya nufa kawai ya murda ai kuwa yana murdawa ya hange shi cikin bargo a lullube. Da sauri ya shiga dakin yana yin sallama. Kasa bude abin rufar ma Aliyu yayi.

“Ranka ya dade Lafiya dai ko?”

Ya fada. Jin shiru yasa ya bude shi. Yadda yaga ya rame abin ba karamin dukkan sa yayi ba dan haka yace

“Subhanallah baka da lafiya ne? A kira likita?”

“No..”

Ya fada a hankali muryar ma bata fita sosai. Sai kuma uace

“Taimakan ka hadan ruwan zafi nai wanka.”

Da sauri ya nufi bandakin ya hada masa ruwan wankan. Ya fito yace

“Na hada maka.”

Kai ya gyada amman ya kasa mikewa. Mai gadin yace

“Ko in taimaka maka nr?”

Kai kawai ya gyada masa. Dagasa yayi ya kaishi har bakin bandakin sai da ya shiga yana dafa bango sannan ya fito. Wajen mao gyaran gidan ya isa yace

“Kaje ka gyara masa dakin kan ya fito. A samar masa abu mara nauyi ya danci.”

Nan da nan kan ya fito har an gyara dakin Mai gadi ne ya dawo hannun sa dauke da kunun da akai masa. Ajiyewa yayi dan har lokacin bai fito ba dan haka ya fita. Yafi awa daya a bandakin dan kan yai wankan ma ya jima a zaune sannan yayi da kyar ya dauro towel ya fito daboda sanyin da yake ji yana fitowa ya saka jalabiya a zaune yayi sallah dan wani jiri dake dibar sa. Yana zaune akan sallaya Mai gadin ya dawo dan ya shigo yafi sau biyar bai fito ba. Kunun ya dauka ya bashi amsa yayi ya ajiye.

“Ka daure ka sha Ranka ya dade!”

Kai kawai ya gyada masa. Mikewa yayi yace

“Allah kara sauki “

Kai ya kara daga masa. Da kyar ya iya shan kunun sannan ya koma kan gadon sa yana mai rufe idanun sa.

*

A can gidan su Aliyu ma gaba daya basu da kwanciyyar hankali tin da sukaga sunyi kwanaki ba kira daga Aliyu bayan kusan kullum sai sunyi waya fin sau nawa amman yanzu kwata kwata wajen sati biyu baya kira kuma ko sun kira bata shiga.

Sosai hankalin Mamah da mai martaba har da Maryama ya tashi. Dan ma shi mai martaba namiji ne yana nuna musu babu komai fa. Duk da haka shima amman hankalin sa ya tashi.

Sun kira gidan gwamnati amman ba wani information akan sa duk kuma ba wanda yasan inda yake zaune. Abun da ya kara daga hankalin mai martaba kenan ya fara shirin zuwa.

Mai martaba ne zaune tare da Mamah. Mamah tace

“Yau kusan sati biyu fa bai kira ba bayan kullum sai munyi waya ni dai hankali na ya kasa kwanciyya na shirya yanzu za a kaini naga a wanne hali yake. Kullum na kwanta sai nayi mafarkin sa sam na kasa samun nutsuwa tsoro nake kada wani abu ya same sh.”

Ta fada hawaye na zubo mata. Mai martaba yace

“To menene na kukan Rashida. Insha Allah komai lafiya da izinin manzon Allah. Ki bari zuwa anjima sai mu tafi tare. Nima nayi mamaki dan na zata ko baya kasar ne ma amman nayi magana da can gidan gwamnatin ance bai ce zai fita ba suma kuma bai shiga kuma basu san inda yake ba shiyasa.”

“Kaga ko? Ni bansan irin halin Aliyu ba ya fiya zurfin ciki. Allah kasa Aliyu yana lafiya. Allah ka kare min shi.”

“Bakuyi magana da matar sa ba!”

“Na kira tace min kusan sati biyu itama rabon ta dashi. Ni ban san wacce irin shasha bace ace mijin ta na wani gida ita tana wani gida kuma ma ace bata san a inda yake ba gaskiya Abu-Aliyu wannan matar ta Aliyu sam bata kwanta min ba daga gani ba wani jin dadin ta yake ba.”

“Shi ya fada miki?”

“Sai ya fada min kasan halin sa ai da zurfin ciki ko abu na damun sa ba fada zai ba.”

Ajiyar zuciya ya sauke yace

“Allah ya kyauta yanzu dai ki bari zan yi magana anjima sai mu tafi.”

“Shikenan!”

Ta mike ta fita daga bangaren sa. Bangaren ta ta koma ta samu Maryama zaune ta zuba tagumi tana gani ta ta mike tae

“Mamah me Abbah yace?”

“Anjima zamu tafi ki shirya.”

“To Mamah shima ba wani dan information agun sa.”

“Babu Maryama. Gaba daya na kasa nutsuwa a tsorace nake ina fatan kada wani abu ya samu Aliyu. Ya Allah ka karen Aliyu a duk inda yake.”

“Amin ya Allah!”

Gab da magariba suka isa bakin gate din gidan nasa, mai gadi ne ya bude yana jin labarin maihaifin Aliyu ne ya hau murna har murnar sa ta kasa boyuwa. Har kasa ya zube ya gaishe su. Mai martaba ya amsa cikin sakin fuska yana tambayar sa
“Ya aiki?”+

“Alhamdulillah mungode Allah.”
“Allah taimaka.”

“Amim!”
Suka amsa. Kan mai martaba ya farga ai har su Mamah sun shige cikin gidan dan haka yace
“Ga baki nan kasa a sauke su a masaukin da ya dace.”
Ya fada yana yin ciki. Falo ya shiga ya samu kujera daya ya zauna.
Su Mamah na shiga falo suka ga ba kowa wannan yasa sukai sama dakin sa suka shiga yana cikin bargo a kwance da sauri Mamah ta karasa kan gadon ta zauna tana yaye bargon ido ta zaro tana taba jin sa zafi rau dan haka tace
“Aliyu!”

A hankali ya bude idon sa yana ganin mamah ce ya fara kokarin mikewa zaune
“Yi kwanciyyar ka Aliyu!”

Ta fada cikin tausaya masa. Komawa yayi ya kwanta tace
“Baka da lafiya ne?”

Ido ya lumshe sai kuma ya bude a hankali yace
“Mamah ina yini ina Abbah!”

Maryama ta kalla tace
“Je ki shigo dashi.”

Hannun sa ta kama tana fadin
“Me yake damun ka? Kaje asibiti kuwa?”

Bai amsa mata ba sai kallon ta da yake can tace
“Ina ita Hajarar?”

“Mamah ba fa wani sosai nake ciwon ba. Bata san bani da lafiya ba.”
Yadda yake maganar ma a hankali zaka san yana jin jiki.

Mamah tace
“Aliyu a hakan ne ba sosai kake rashin lafiya ba. Kwanan ka nawa baka kira ba duk saboda me to?”

Shiru yayi. Tace
“Ciwon ne duk yasa ka haka? Ka fadan me yake damun ka dan Allah?”

“Mamah ciwo ne kawai Allah ya kawo shi….”
Bai karasa magana ba Abbah da Maryama suka shigo. Abbah ne ya karaso wajen sa da sauri yana fadin
“Subhanallah Aliyu haka kake kwance da ciwo baka fada mana ba?”

“Abbah ai da sauki fa.”
“Wane likita ne yake duba ka?”

“No fa banje asibiti ba!”
“Kamar ya bakaje asibiti ba. Haka ka zauna a gida da ciwo a jikin ka? Haba Aliyu mutuwa kake so kayi kome? Ka taba ganin inda akai ciwo ba aje an ga likita ba bare ya ya taimaka maka da wani abu.”

Murmushin karfin hali yayi yace
“Abbah kun iso lafiya?”

Kan Abba ya bashi amsa ya kalli Maryama yace
“Kije ki bada order ai girki da yawa dan nasan kun taho da mutane gaku kuma.”

Abbah yace
“Ka tashi muje asibti ko da yake bami number doctor ka!”
“Nifa Abbah bani da wani likita.”

“Kamar ya Aliyu? Kenan kai ko checkup ba a maka anya Ali?”
Wayar sa ya dauka ya fara kiran PAn sa bai jima ba ya dauka yace
“Ka turon manyan likitoci guda biyar yanzun nan.”

Ya fada yana zama a gefen gadon. Ya yaye bargon da yake rufe dashi yace
“Tin yaushe ne baka da lafiyar?”

“Abbah nifa lafiya ta kalou zazzabi ne da ciwon kai ke dan damu na fa.”
“See you Aliyu. Daga kallo daya za a kalle ka a gane kana cikin rashin lafiya da damuwa. Kaga yadda ka rame kuwa? Ka fada min me yake damun ka Aliyu. Tukkuna kana cin abinci?”

“No Alhaji ina matar sa ma tukkuna.”
Mamah ta fada tana fita a dakin. Kasa ta sauka wajen Maryama dake bada order.

Mamah ce ta kalle ta tace
“Kina da number wayar Hajara?”

Kai ta girgiza yace
“A’ah sai dai na amsa wajen Anty Sha’awa.”

“Amso min!”
Wayar ta dake hannun ta ta fara dannanwa tayi searching sunan Sha’awa. Sannan tayo dailing number tata.

Dagawa tayi tace
“Ya dai sister?”
“Alhamdulilah number Anty Hajara zaki bani?”

“Ok bari na turo miki. Ina fatan dai lafiya?”
“Lafiya. Yaya ne bashi da lafiya.”

“Wanne Yayan?”
“Yaa Aliyu man.”

“Subhnallah! Me yake damun sa?”
“Nima bamu sani ba.”

“Alright bari na turo miki!”
Ta katse wayar. Number Hajara ta tura mata.

Wayar Aliyu,  Abba ya dauka ya kunna. Nunber PA ya dauka sannan ya fara dailng.ringind daya biyu ya dauka.
“Assalamu alaikum Ranka ya dade barka da yamma!”

“Wa’alaikum salam! Barka kadai. Ya aiki?”
“Alhamdulillah. Amman kamar mai martaba ko?”

“Shine me yake damun Aliyu ne?”
“Wallahi ranka.ua dadw nima ban sani ba. Sam ban san yana gari ko baya gari ba.”

“Is alright ka turon mayan likitoci guda bakwai yanzun nan dan naso na same shi bai da lafiya. Kwararru fa zaka samo min yanzu yanzu!”
“An gama ranka ya dade!”
Wayar ya katse sannan ya koma ya dago Aliyu yana kallon sa yace
“Aliyu me yake damun ka?”

Ido ya lumshe yace
“Abba nima ban sani ba. Ina zaton rayuwa ta tazo karshe.”

“No Aliyu ba zaka mutu yanzu ba insha Allah!”
Ido ya lumshe Abba yace
“Kana cin abinci kuwa?”

Kai kadai Aliyu ya kada masa. Komar dashi Abba yayi sannan ya gyara masa kwanciyya. Nan ya hau waya ya kira Yayan Aliyu. Yana dagawa yace
“Abubakar ina son ai mana booking flight da safe zamu bar kasar.”

“Abba Lafiya?”
“Aliyu ne ba lafiya?”

“Subhanallah meya faru?”
“Gamu nan dai yanzu likitoci zasu karaso.”

“Alright bari na samar mana flight din!”
“Alright Allah maka albarka.”
Ya kashe wayar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *