WA NAKE SO CHAPTER 13

 WA NAKE SO CHAPTER 13

Su Mamah na zaune a falo PA ya shigo dakin. Yana ganin Mamah ya zube a kasa yana fadin

“Barka da Yamma Hajiya.”

“Yauwah!”

“Kun iso Lafiya?”

“Alhamdulillah!”

“Daman Martaba ne yace azo da likitoci”

“Maryama jeki fada masa”

Mikewa tayi ta hau sama. Xaune ta same shi yana tofawa Aliyu addu’a shiga tayi da sallama. Ya amsa tace

“Abba Doctors din ne suka zo!”

“Ok shigo dasu!”

Ta juya ta fita da sauri. Tana zuwa ta fda musu nan tai musu jagora. Suna shiga PA ya zube a kasa yana gaida Abba ya amsa sannan suma.suka gaishe su.

Gafon ya nuna masu yace

“Ku duba min shi ban san me yake damun sa ba.”

Duk suka rufa kansa kowa na aikin sa akan abinda ya kware sun kwashe awa daya akan sa sannan suka dago suna rubuce rubuce sannan suka koma. Wasu na masa tambayoyi wasu na masa gwaji a haka suka kara kwashe wani lokacin sannan suka dago.

Kiran sallah da suka ji ana yi yasa suka ce

“Let pray first Sir!”

Abba ya gyada kai suka fita. Mikewa yayi ya daga Aliyu sannan suka shiga bayi. Ruwan alwala ya hada masa suka fito ya shimfidda masa sallaya dan ko kadan bai da kuzari. Sannan Abba ya fita. Mikewa yake son yayi amman jin wani jiri dake dibar sa yana daga zaune yasa ya hakura kawai yayi a zaune yana idar wa kua ya kwanta a wajen.

*

**

***

****

*****

******

*******

Karfe biyin dare ta mike ya shiga ta dauro alwala sannan ta fito ta tada sallah bayan ta idar ta zauna tana addu’a. Ta jima zaune sannan ta koma ta kwanta. Karfr biyar saura ta mike ta shiga ta kara dauro alwala ta fito tayi raka’atanil fijir bayan ta idar ta tashi Nusaiba dake bacci.

Mikewa tayi ta shiga ta dauro alwala kan ta fito an tada sallah dan haka sallah kawai tayi tana idar wa ta koa gado. Fateema kuwa azkar ta fara yi tana gamawa ta mike ta fita. Falon gidan ta gyara ta saka turare sannan ta nufi kitchen masu aiki ta tadda suna aiki ta shiga duk suka zube suna gaishe ta. Ta amsa cike da girmamawa da fara’a sannan tace su kawo ta karasa da kyar suka bata ita ta hada break din.

Karfe takwas ta fito a kitchen bayan ta gama girkin ta wanke duk kayan da ta bata. Hajiya dake zaune a falo ta dago jin an fito fanin Fateema ta saki fara’a tana fadin

“Ashe kin tashi.”

Baba mai aiki da ta fito tace

“Tin dazu Hajiya yau ita tayi komai.”

Hajuya tace

“Kuka bar ta kuma?”

“To ta matsa Hajiya.”

Fateema tayi kasa da kai ta karasa ta zauna a kasa tace

“Ina kwana Mama?”

“Lafiya kin tashi lafiya?”

“Alhamdulilah!”

“Amman Fateema sai kiyi ta aiki?”

“Mama ai na saba ba komai a ciki ai.”

“To ai shikenan Allah yayi albarka.”

Kan ta a kasa ta amsa da Amin. Sannan ta mike tayi ciki. Hajiya ta bita da kallo tana girgirza kai. Tana son Fateema ko dan sanyin ta da tarbiyyar ta.

STORY CONTINUES BELOW

Tana shiga wanka ta shiga tayi sannan ta fito ta shafa mai ta gama ta dawo ta saka kaya. Wata doguwar riga ta saka ta atamfa blue black da adon pink a jiki. Dinkin doguwar riga ne ya amshe ta tayi kyau sosai. Hoda ta shafa ta saka lip stick sannan ta dauko irin turaren Fu”ad ta shafa ta zauna gefen gado tana daura dankwalin ta. Wanda damin gashi ta ya fito ta kasan dankwallin.

Nusaiba ce ta bude ido ta mike a hankali kallon Fateema tayi tace

“Kai Anty na kinyi kyau.”

Murmushi Fateema tayi kawai. Nusaiba tace

“Barka da safiyya Anty!”

“Barka kadai kin tashi lafiya?”

“Alhamdulillah! Ya kike?”

“Lafiya!”

Fateema ta fada.

“Kamshin turaren Uncle Fu’ad!”

Ido Fateema ta lumshe tace

“Shine ya dawo!”

Da sauri ta mike tana fadin

“Da gaske?”

Fateema tayi murmushi tace

“Da wasa nake ne ke amfani dashi.”

“Allah sarki!”

Fateema tai murmushi tace

“Ki tashi kiyi wanka ko?”

Mikewa tayi tace

“Toh!”

Toilet ta shiga ta fara wanka Fateema ta mike ta fara gyara dakin ta gama ta saka turaren wuta dake dakin. Nusaiba na fitowa tace

“Kai Anty da kin bari na fito na gyara ai.”

“Sai kace wani aiki mai yawa.”

Gaban mirrow ta karada ta shirya ta dauki kayan ta ta saka sannan tace

“Muje mu karya ko?”

Mikewa Fateema tayi tabi bayan ta. A falo suka samu Hajiya. Nusaiba ta gaishe ta sannan suka zauna. Hajiya tace

“Kuje kuci abinci mana.”

Mikewa sukai suka nufi dining zama sukai Fateema ta hada tea taa sha. Nusaiba ma ta hada tea sannan ta zuba pepper soup da dankali tana ci. Ganin Fateema bata zuba komai ba yasa tace

“Anty ya baki zuba ba!”

Bude flask din tayi ta zuba papper soup din kadan sannan ta fara ci. Nusaiba ta dago tace

“Dan kalin fa?”

Kan tayi magana ta fara zuba mata ta mika mata. Ido Fateema ta zato tace

“Tab ai yayi min yawa wanna!”

“Kai Anty wannan din kici ki rage.”

“A’ah rage shi dai.”

Ta rage ta ajiye mata. Kadan taci tace

“Alhamdulillah!”

Ta mike ta bar wajen ta koma falo. Nusaiba sai da tayi nak sannan ta taho Falo. Hajiya tace

“Acici!”

Nusaiba tace

“Ai abincin ne yayi dadi.”

“Antyn kice tayi ayi.”

“Haba nifa ince wallahi yai dadi.”

Murmushi sukayi. Hajiya tace

“Kuje ku gaida Hajiyar ko?”

“Eh!”

Suka mike a tare suka fita. Suna shiga bangaren Hajiya suka samu daya daga cikin yan matan jiya a compound din tana answering call.

Nusaiba tace

“Izzy ana ta zubawa flower ruwa ne?”

Tai murmushi kawai. Ciki suka shiga suka tadda yan matan jiya su uku zaune daga mai danne dannen waya sai mai kallon sai mai karatu a littafi.

Nusaiba tace

“Anty Sakina ina kwana?”

Wacce tayiwa Fateema tsaki jiya ita cr ta dago ta kalli Nusaiba ta ya mutsa fuska tace

“Lafiya.”

Sannan ta kalli Fateema ta dauke kai. Dayar tace

“A’ah Nusaiba an tashi lafiya?”

“Lafiya Anty Hibba. Ya kike?”

“Lafiya.”

Ta kalli Fateema tace

“Ina kwana?”

“Lafiya ya kike?”

Fateema ta fada. Dayar da jiya suke zaune ta dago ta dan saki fuska tace

“Ina kwana Dr?”

“Lafiya ya kike?”

“Lafiya!”

Ta fada tana kallon Nusaiba tace

“Sis ya kike?”

“Lafiya lou Mimie! Hajiya fa?”

“Tana ciki tana walha amman nasan ta idar!”

STORY CONTINUES BELOW

Gaba tayi tace

“Taho muje Anty!”

Bayan ta tabi. Sakina tabita da harara ta dan saki tsaki. Suna shiga suka tadda Hajiya na zaune tana jan carbi. shiga sukai da sallama. Ta amsa suka zauna a kan carpet din dakin sannan Fateema tace

“Ina kwana Hajiya?”

“Lafiya lou kin tashi lafiya?”

“Alhamdulillah!”

“Ya Hajiyar?”

“Tana lafiya.”

Nusaiba tace

“Ina kwana kakus?”

“Lafiya lou. Ai ba ruwa na dake tinda kika tafi kuma kika hana Fateema ta kwana.”

Dariya Nusaiba tayi tace

“Yau zamu kwana me zaki bamu na dadi?”

“Ban dashi ban baki?”

.”Haba Kishiyar ai kuwa zan saka mijin ya juya miki baya.”

“Ai dai da ta farko ake tin kaho.”

“Ina fa kin tsufa.”

“Wa ya fada miki ai da tsohuwar zuma ake magani.”

“Inda cuta ba.”

Tayi murmushi tace

“Tashi ki ban wajen”

Ta kalli Fateema tace

“Tashi kije dauki fura a firij kije ki shanye kada ki bawa wannan berar!”

Dariya Fateema tayi. Nusaiba tace

“Lallai kina so kiyi dakan fura kenan.”

“Akan me?”

“Shi zan saka yasa ki daka min da hannun ki.”

Murmushi Fateema tayi ta isa firij ta dauko furar a kwanon sha ta zo tace

“Nagode Hajiya!”.

“Je kisha abar ki kada ki sammata dan nasan halin ta da kwadayi.”

Fateema ta dukar da kai tace

“To sai anjima!”

“To mu jima da yawa. Allah yayi albarka!”

Ta mike ta fita. A falo ta same su kamar yadda suka barsu dazu. Sai da ta isa bakin kofa sannan tace

“Sai anjiman ku!”

Bata jira amsar su ba ta fice. Sakina ta saki baki.  Sauran suka amsa da

“Ki gaida Hajiya kan mu shigo.”

Ita dai bama taji ba sam. Tana fita ta samu Izzy zaune rike da waya a hannun ta. Rana ganin Fateema ta mike taba murmushi tace

“Antyn mu ina kwana. Ai jiya da kika shigo ina daki ina waya har kika futa ban samu na fito mun gaisa ba ya kike? Ya gida da kowa?”

“Alhamdulillah! Kin tashi lafiya?”

Ta tambaya itama da fara’a akan fuskar ta. Ta gyada kai tace

“Alhamdulillah!”

Sai tace

“To sai anjima.”

“Aha nima zan shigo anjima in gaida Hajiya banyi break bane.”

“Alright!”

Ta fada ta fice daga sashen.

*

Tana shiga falo ta tadda Hajiya na ciki. Cup ta dauko ta zubawa Hajiya furar sannan ta nufi da’kin ta. A zaune ta same ta akan dadduma tana Jan carbi. Zama tayi tace

“Sannu Mama!”

“Yauwah kun dawo?”

“Eh ga fura Hajiya ta bamu!”

“Madallah toh!”

Ta amsa ta ajiye. Mikewa Fateema tayi ta fita. A falo ta samu Nusaiba a zaune.

Cup ta dauko muku ta diba ta mikawa Nusaiba cup din tace

“Kisha Mana.”

Amsa tayi ta zuba ta fara sha. Suna zaune Nusaiba tace

“Anty Ina son ki bani labarin rayuwar ku da Uncle Fu’ad!”

Murmushi Fateema tayi tace

“Saboda me?”

“Ana yawan magana Akan rayuwar ku a gida wani lokacin da mamakin me ya rabaku da Uncle!”

Ajiyar zuciya Fateema ta sauke, sannan tace

“Nusaiba komai Kika ji an fada akan rayuwar mu hakane. Ban taba zaton akwai wata Rana da zata zo irin haka ba Wai ace bana tare da Fu’ad. Ban taba son abu a rayuwar ta kamar shi ba. Har yau da nake fada miki son Fu’ad na cikin zuciya ta ko Kadan bai ragu ba sai dai nace kullum Kara Jin son sa nake. Fu’ad mutum ne Mai hankali, hakuri da tarbiyya. Nayi rashin miji na kwarai. Ban San me yasa Fu’ad yai min haka ba bayan yadda nake son sa. Shima Kuma haka. Ban San me yasa yai min saki har uku da ya zamo rabuwar mu meyasa bai min daya ko biyu ba, nan gaba mu koma. Yanzu Dan Allah tayaya Zan koma wajen sa, tayaya yake zato bayan ba wani Namiji a gaba na shi kadai nake so shi kadai nake kalla a matsayin Namiji. Nusaiba Ina son Fu’ad son da baki na bazai iya fadi ba.”

Sai Kuma ta kifa Kai akan cinyar ta tana sakin kuka Mara sauti. Jikin Nusaiba ne yai sanyi ta Mike ta koma kusa da ita ta zauna.

Kasa magana tayi sai daga baya ta ce

“Kiyi hakuri Anty wannan ita ce taki kalar jarabawar kiyi hakuri ki daure ki cinye ta insha Allahu hakan zai zama Miki alheri Kuma Kika sani ko Nan gaba ku koma!”

“Tayaya Nusaiba? Tayaya? Abinda yafi damu na a yanzu bai wuce rashin Fu’ad ba. Akai na ya bar gida Yan uwan sa da iyayen sa tayaya Zan yafewa kaina Nusaiba….”

Ta fada tana rufe fuska da hannu. Mikewa tayi da sauri tayi daki.

Nusaiba ta Mike ta bita da sauri. Kwance ta same ta Akan gado tana kuka. Zama tayi a gefen gadon ta dafa ta tace

“Anty Dan Allah kiyi hakuri Anty bansan maganar zai saki kuka ba. Kiyi hakuri ki daina kuka.”

Shiru tui tana kuka. Can ya Mike tace

“Zan fada wa Hajiya to!”

Da sauri Fateema ta Mike tana fadin

“Zo nan Nusaiba!”

Dawowa tayi ta kama hannun ta tace

“Bana so kada ki fadawa Hajiya Dan Allah!”

“To ki daina kuka!”

“Na daina!”

Ta fada tana goge idon ta.

Murmushi sukai. Nan Nusaiba ta dinga bata labari har ta sake suna ta Dariya ba su Lura ba sai Jin Kiran sallah azahar sukai.

Mikewa suka yi sukai Alwala suka zo suka tada sallah. Sannan sukai fito falo.

Hajiya suka sama zaune. Tace

“Bacci kuke ne?”

“A’ah!”

“Amman ban Aiko kin Fadi abinda kike so ba?”

Murmushi Fateema tayi yace

“Mama komai zanci!”

“A’ah ki Fadi dai ko kina son wani Abu.”

“A’ah”

“To shikenan dazu su Sakina suka shigo ma nace su shigo ciki suka ce fita zasuyi in sun dawo sa zo gun ki.”

Kan Fateema a kasa tace

“Allah sarki nagodr!”

Da yamma suna zaune a daki suna hira Hajiya ta shigo. Kallon ta sukai. Fateema tace
“Sannu Mama!”+
“Yauwah Fateema wannan me surutub ta cika miki kunne ko?”
Murmushi Fateema tayi. Nusaiba tace
“Kai Hajiya!”
Hajiya tace
“Ku taso ku rakani gidan Hajiya Rukayya!”
“Toh!”
Fateema ta fada tana mikewa. Fita Hajiya tayi. Nusaiba ta isa gaban mirrow tana shafa hoda sannan ta dauki turare ta fesa.
Fateema kuwa mayafi ta dauka kawai ta tsaya kallon ta. Sai da ta gama ta juyo tace
“Anty ke ba zaki gyara fuskar ki ba?”
“Kai kyale ni haka!”
“Ai ke dan kina da kyau ne!”
“Kema kina da shi ai.”
Nusaiba tace
“To ki dan shafa hodar mana.”
Amsa Fateema tayi ta shafa.  Nusaiba tayi murmushi tace
“Kinga yadda kika kara kyau!”
Kai Fateema ta girgiza kawai tace
“Muje!”
Turaren ta ta dauka ta fesa mata. Tai murmushi tace
“Muje mun bar Hajiya a waje fa.”
Nan suka fita. A falo suka same ta zaune wannan yasa suka karasa gun ta ta kalle su da fara’a tace
“Kun fito.”
Fateema tayi kasa da kai tace
“Eh!”
Mikewa tayi tai gaba suka bita a baya. Mukullin motar ta ciro ta bude. Sannan ta budewa Hajiya gidan baya ta shiga,  Nusaiba ta shige gidan mai zaman banza. Fateema kuma ta zaga ta shiga wajen driver. Mai gadi ya bude musu. Fita sukai sannan tace
“Wacce unguwa ce?”
“Sharada phase 1 ki shiga ta layin yahya gusau.”
“Toh!”
Taja motar suka dau hanya suna tafe suna dan taba hira da Nusaiba har suka shigo titin Yahya Gusau din. Titin dake hannun daman su suka shiga nan ta nuna mata layin ta shiga. Wani katon gida ta nuna mata. Horn tayi mai gadi ya fito yana cewa
“Gun wa kika zo?”
Hajiya tace
“Lawan!”
Yana ganin Hajiya yace
“Ranki a dade ashe tare kuke barka da zuwa ina yini?”
“Lafiya ya aikin?”
“Alhamdulillah!”
Ya juya da sauri ya bude gate din. Shiga tayi tai parking a katon parking space din su da zai ci a kalla motoci sama da ashirin. sannan ta  kashe motar. Ta fita da sauri kan hajiya ta bude ta bude mata. Fita tayi ta rufe zatabi bayan su wayar ta tai kara tana dubawa taga Momy ce. Murmushi tayi tabi bayan su ta dauka tare dayin sallama.
Momy ta amsa tana fadin
“Wato kin samu Hajiya kin manta dani ko?”
Murmushi Fateema tayi tace
“Ina yini ya gida?”
“Alhamdulillah yasu Hajiyar?”
“Suna lafiya bari na bata.”
Ta karasa kusa da Hajiya ta mika mata waya tana fadin
“Momy ce.”
Amsa tayi ta kai kunne tayi sallama. Amsawa Momy tayi sukai gaisa sannan sukai sallama. Wayar Fateema ta kaa tace
“Momy mun fito ne!”
“To a dawo lafiya!”
Ta kashe wayar. Sai da sukai tafiya mai tsayi sannan suka karasa main parlon ba kowa a ciki dan haka suka kara shiga falo na biyu anan suka zauna.
STORY CONTINUES BELOW
Mai aikin gidan ce ta fito a kitchen tana ganin Hajiya ta saki fara’a tana fadin
“Sannu da zuwa Hajiya!”
“Yauwa ya kuke ya aiki?”
“Alhamdulillah! Bari na fada mata.”
Tayi ciki da sauri. Bata jima ta dawo tace
“Tace ki shigo.”
Mikewa sukai gaba daya sukai ciki. A wani katafaren Falo suka samu matar zaune ita da wasu yan mata guda biyu kyawawa da su.
Suna ganin Hajiya suka mike suna fadin
“Sannu da zuwa Hajiya!”
“Yauwah Jannah da Noor ya kuke?”
“Alhamdulillah.”
Suka fada sai da ta zauna sannan suka fara gaishe ta bayan sun gama suka kalli su Fateema suka gaisa cikin sakin fuska da fara’a. Suma su Fateema suka sakar musu fuska suka amsa.
Matar suka kalla sannan suka gaishe ta. Ta amsa cikin sakin fuska tana fadin
“Waccen Nusaiba ce wannan ce dai ban game ba.”
Hajiya tace
“Fateema ce!”
“Allah sarki ashe takwara ce. Sannu Fateema.”
Kan Fateema a kasa tace
“Yauwah!”
Jannah ce tace
“Ku taso mu shiga ciki mu kyale tsofin nan.”
Nusaiba ce ta fara mikewa. Ta kalli Fateema tace
“Muje.”
Mikewa tayi suka bi bayan su Jannah. A wanu madaidaicin falo suka zauna. Noor ta isa firji ta dauko musu lemo me sanyi sosai. Nusaiba ce ta dauka. Noor ta kalli Fateema tace
“Sis ki sha mana!”
“So nake ya huce yai sanyi!”
Mikewa Noor tayi ta fita sai gata ta dawo da mara sanyi, amsa tayi ta ajiye.
Jannah tace
“Please kisha mana. Feel free na!”
Murmushi Fateema ta saki tace
“Zan sha ai.”
Nan suka dinga hira tsakanin su amman Fateema tai shiru. Jannah ce ta kalle ta tace
“Why Silent dear!”
Nusaiba tace
“Kunsa Doctor somerimes basu fiya son surutu ba.”
“Is she a Doctor?”
Noor ta tambaya. Nusaiba tace
“Yes Babba ma dan har asibiti ne da ita. Kada kuce min bakwai sauraron program nata na *Mu tambayi likita* “
Jannah tace
“Dan Allah itace daman Dr Faterma Umar. Mai Umar Specialist Clinic?”
Kai Nusaiba ta gyada tace
“Sure.”
Da sauri Noor ta koma kusa da Fateema tace
“Kai am so Happy yau gani ga Doctor wallahi ina yawan jin program naki sosai dan yana taimaka mana har muma mu bada shawara mu taimakawa wasu. Allah ya taimaka Dear”
Murmushi Fateema tayi tace
“Amin thanks you!”
Jannah tace
“Tin kan na ganki kike burge ni na zata wata babba ce sai naga ashe ba babba bace sosai. Amman gaskiya ki burge ni Allah kara ilimi yasa ki gama da duniya lafiya. Allah biya miki bukatun ki na alheri.”
“Ameen Dear Thanks you!”
Nan suka fara mata wasu tambayoyi tana basu amsa sosai suke ganewa kuma suna jin dadi dan ba karamin karuwa suke da hirar tasu ba dan yawanci akan lafiya ne da shawarwari.
Hajiya Fateema da Hajiya na falo. Bayan shigar su Fateema tace
“Amman Hajiya ban gane Fateema nan ba.”
Hajiya tace
“Matar Fu’ad ce fa.”
“Ya dawo ne?”
“No tazo min kwana biyu ne dai kawai.”
“Allah sarki yarinya kyakyawa mai tarbiyya. Amman banji dadin rabuwar su ba wallahi.”
“Nima haka ina addu’a dai Allah yasa haka ne mafi alheri.”
“Amin Amin! Har yanzu batai wani auren ba.”
“Ina fa taki kula kowa ta tsaya jiran gawon shanu. Domin kuwa saki uku fa yai mata abinda ke batan rai kenan. Kinga dai dole ai tayi aure ko dan ko zai dawo a yau ba aure tsakanin su.”
“Ashsha. Allah sarki tana wajen ki ne?”
“A’ah tazo min weekend ne?”
“Allah sarki ta gama karatu ne?”
“Ta gama dan aiki take yi ma. Babbar likita ce.”
“Masha Allah Allah taimaka Allah ya zaba musu mafi alheri yayi musu albarka.”
STORY CONTINUES BELOW
“Amin! Ina Aslam kuwa kwana biyu ko gaishe bi bai zuwa yi ma.”
“Kinsan bai jima da dawowa ba. Yana nan.”
“Matar tasa har yanzu dai shiru ko?”
“Uhmm wallahi shiru Hajiya. Ni dai addu’a nake yi Allah ya basu haihuwa ko hankalin sa xai kwanta nima inga jikan Auta na.”
“Allah ya kawo masu albarka. Kinsan ana samun irin wannan jinkirin!”
“Haka ne. Amman Allah yasa ba wani abu yarinyar nan tayi ba dan naga rawar kanta tayi yawa.”
“Amin dai to! Amman in wani abu tayi ma ai tayiwa kanta.”
“Wallahi kuwa.”
Sallamar sa suka jiyo. Hajiya Fateema tace
“Kinji dan halak ko?”
Hajiya ta amsa sallamar ya shigo. Sanye yake da blue black din wando sai farar riga kayan sun amshe shi. Yana sanye da glass din sa na gado ko da yaushe sai tashin kamshi yake yi. Ya shigo a nuste Yana ganin Hajiya ya fara sosa kai yana murmushi sannan ya zauna a gefen kafar ta yana fadin
“Hajiya ta ina yini?”
“Lafiya lou Aslam ya aiki?”
“Alhamdulillah ya gida da kowa?”
“Alhamdulillah ya matar taka?”
“Tana lafiya!”
“Masha Allah.”
Kallon Hajiyar sa yayi suka gaisa ya mike yace
“Su Noor sun tafi ne?”
Hajiya Fateema tace
“A’ah suna ciki sun samu kawaye.”
“Su da su waye?”
“Ya’yan ka ne suma.”
Kai ya gyad ya mike.
Ciki yayi ya nufi falon da suke. Fateema na tsaka da magana aka bude kofar dakin da sallama ya shigo. Duk suka kalli kofar. Zaro ido Fateema tayi tana kallonsa gabanta na faduwa, ya mata kallo daya kafin yace komai Jannah tace
“Uncle meet Sis Fateema and Nusaiba.”
Yai murmushi ya shafa kan sa. Yace
“Ba gaisuwa sai surutu ko?”
Baki ta turo Noor tace
“Ina yini Uncle?”
“Lafiya lou! A ina kuka samo kawaye?”
Noor yace
“Tare suke da Hajiya fa. They are her granddaugthers!”
Kai ya gyada Nusaiba tace
“Ina yini?”
Yace
“Lafiya ya kike?”
“Lafiya lou!”
Fateema ta kasa dago kanta tace
“Ina yini?”
yace
“Lafiya lau”
Daga haka ya juya zai fita Jannah tace
“To ai ni ban gaishe ka ba.”
Yace
“Wa ya hanaki toh?”
Ta mike ta isa wajen sa ta kama hannun sa tace
“To ina yini?”
“Lafiya lou Jannah ya kike?”
Tai murmushi tace
“Lafiya Uncle ina Aunty?”
“Tana gida bayan kin ki kizo ki mata hutu!”
Ya fada yana fita, tace
“Ai zanzo ne!”
“Alright!”
Ya fada daga wajen.
Fateema dai bata dago ba. Kan ta yana kasa. Jannah ce ta dawo ta dauki lemon da Noor ta ajiye mata ta bude ta tsiyaya mata a cup ta mika mata. Amsa tayi tana murmushi sannan tayi sipping daya,  biyu ta ajiye.
Nusaiba ce tace
“Waye wannan?”
Noor tace
“He is my Uncle shine Autan Hajiya.”
Kai Nusaiba ta gyada. Jannah tace
“Matar sa daya sunfi eight years da aure but bata taba ko da bari ba. Baki ga yadda yake son kids ba.”
“Allah sarki!”
Nusaiba ta fada tana kallon Fateema. Sannan tace
“Anty ko akwai wani taimako da zaki iya.”
“Ai ban san matsalar ba har sai sun zo asibiti anji. Wani zaku ga daga Alah ne sai ya shekara masu yawa sai kuma ya samu wasu kuma ko sunyi planing shiyasa wasu kuma basa iya daukar ciki da dai sauran.”
Kai suka gyada.
*
Mai aikin Hajiya ce ta shigo tace
“Hajiya tace kuzo ku tafi.”
Mikewa sukai suka fito har dasu Jannah da Noor suna fitowa Jannah tace
“Granny ashe program din da muke ji na likitan nan da Sister akeyi.”
Ta fada tana nuna Fateema. Fateema tayi kasa da kai. Hajiya tace
“Ikon Allah ashe ‘ya ta ce. Allah taimaka ya kara basira ya kare ki.”
Duk aka amsa da
“Ameen!”
Noor Hajiya ta kira da Hannu ta karasa kusa da ita tai mata magana ta mike ta bar wajen. Bata jima ba ta dawo dauke da katuwar leda. Sannan suka mike dan raka su. A bakin kofa aka tsaya ana sallama sannan Fateema ta budewa Hajiya ta shiga itama ta zaga. Motar Noor ta bude ta ajiye Ledar hannunta tace
“Inji Hajiya ba yawa.”
Hajiya tace
” kai Hajiya har da wahala.”
“Ina wata wahalar take nagode sosai Hajiya Allah saka.”
“Amin nagode.”
Fateema ta tada motar tayi reverse suna kallon ta suna daga mata hannu har ta fita. A hanya taga mai sai da fruit ta tsaya ta siya sannan suka dau hanyar gida.”
Suna shiga gida tai parking ta fito ta budewa Hajiya ta fito. Nusaiba kuma ta debo ledojin dukka. Daya ta amsa suka bi bayan Hajiya. Suna shiga ana kiran Magrib dan haka anan falo suka ajiye kayan hannun su kowa ya nufi bandaki dan ya daura alwala. Fateema na fito ta tada sallah. Bayan ta idar ta zauna tana addu’oi.+
Tana zaune har aka kira isha’i sannan ta mike ta tada ta. Ta idar tayi shafa’i sannan ta zauna tana addu’a ta jima a zaune ta shafa ta jinginar da kan ta a jikin gado.
Ido kawai ta lumshe ta fara tunanin Fu’ad. Soyayyar da Hajiyar sa dake nuna mata shin ace suna tare da Fu’ad da ya kenan. Lallai tayi dacen uwar miji mai son. Ina ma ace Fu’ad ya dawo,  ina ma ace da sauran igiyoyin sa akan ta,  ina ma ina ma…..
Hawaye ne ya hau zubowa akan fuskar ta wanda bata san lokacin da suke sauko mata ba. Nusaiba a tazo tana sallama taji shiru ta shigo. Kallon Fateema ta tsaya yi tausayin ta ya kamata. Zama tayi a gefen ta tace
“Anty menene kike kuka?”
Da sauri ta dago jin hannun Nusaiba na goge mata hawayen idon ta,  hannu ta saka ta fara share nata tana girgiza kai.
“Dan Allah Anty ki cire damuwa a ranki. Allah fa yana sane dake.”
Kai kawai Fateema ta gyada mata. Nusaiba tace
“Hajiya tace ki taso muci abinci.”
Mikewa tayi a hankali ta bi bayan Nusaiba. A falo ta same ta zaune tana cin tuwo. Zama tayi a kasa Hajiya tace
“Ki zuba abinda kike so gasu nan.”
Zama tayi ta zuba turon itama kadan. Nusiaba tace
“Anty ba dai kya son cin abinci na lura.”
Hajiya tace
“Dan Allah Fateema ki sake kici ki koshi.”
Kai ta gyada ta fara ci. Nan mai aikin ta kawo musu fruit din da suka siyo a hanya ta gyara shi. Ajiyewa tayi ta juya kadan taci tuwon ta zame hannun ta ta fara shan fruit. Su ta danci da dama dama sannan ta mike ta kwashe kayan ta kai kitchen bata fito ba sai da ta dauraye su sannan ta fito. Zama tayi suna kallo. Can Hajiya ta mike tayi ciki.
Suna zauna aka bude kofar da sallama aka shigo dagowa sukai suka amsa. Izzy ce ta shigo tana fadin
“Ashe kun dawo? Tin dazu nake zuwa naga bakwa nan”
Nusaiba tace
“Munje unguwa da Hajiya.”
“Ina yini Antyn mu?”
Fateema ta saki fuska tace
“Lafiya lou ya kike?”
“Lafiya lou.”
Nan suka zauna hira sune har 12 basu lura ba wannan yasa Izzy ta kwana anan kawai.
*
*After Magrib*
Ya shigo gidan a falo ya same su suna kallo. Janna na ganin sa ta mike ta dawo kusa dashi tace
“Uncle sannu da zuwa!”
“Yauwa!”
Tace
“kasan wadan da suka dazun nan Allah Uncle suna da kirki dukkan su. Ashe daya ita ce wacce muke jin program nata gaskiya tana da ilimi she is young amman ba zaka ce ba saboda komai nata a nutse  da aji take yi. Gaskiya Dr Fatrema ta burge ni.”
Noor tace
“Malama zaki sa gaban ta yai ta faduwa tin da ta bar gidan nan sai maganar ta kike.”
“To ai ba gulmar ta nayi ba ko Uncle!”
Kai ya gyada ya lumshe ido. Sannan ya bude a hankali ya mike yace
“Am going where is Hajiya?”
STORY CONTINUES BELOW
“Tana ciki!”
Ciki ya nufa ya shiga dakin ta ya same ta zaune akan sallaya. Zama yayi a gefen ta yace
“Ni zab tafi Hajiya sai da safe!”
“To Aslam Allah ya tsare hanya agaida Jidda.”
“Zata ji!”
Ya fada yana mikewa.
Fita yayi Jannah na ganin sa ta mike tace
“Uncle baka ci abinci ba.”
“Bana jin yunwa Baby!”
“To muje na rakaka.”
Noor dake kallon TV tace
“Sai da safe Uncle a gaida Aunty Jidda!”
“Zata ji!”
Ya fada yana yin gaba Jannah na biye dashi a baya. Suna fita compound tace
“To Uncle gud nyt my regard to Aunty!”
“Ok thanks you!”
Ya fada yana sakar mata murmushi yayi gun motar sa ta tsaya tana kallon sa har ya shiga ta fara daga masa hannu sannan ya fice daga compound din. Ciki ta juyata koma.
Yana tafe a hanya yana tunanin ta ina Hajiya suka hada relation da Dr Fateema ko itama jikar ta ce. Kai ya girgiza yace
“Amman meyasa ban san ta ba?”
“Ka sani ko yar wajen yar Hajiya ce ta waje!”
Zuciyar sa ta bashi amsa.
Kai ya gyada yace
“It may be! But in haka ne abu yazo gidan sauki kenan.”
Baki ya cije yace
“Alhamdulillah Allah in Fateema Alheri ce a gareni Allah ka mallaka min ita in ba alheri bace Allah ka ciren son ta a zuciya ta.”
Ido ya lumshe ya bude yana sakin murmushi tuna moment din da suka dinga kasancewa a tare da irin tsiwar ta da shariyar ta. Ya da shafa kansa yace
“I like all ur attitude!”
Dai dai zuwan sa gida ya danna horn mai gadi ya bude masa. Parking yayi ya fito rike da wayar sa yana murmushi. A bakin kofq suka hadu da Jidda ta fito yi masa sannu da zuwa taci ado kamar wacce zata gasar kyawawa. Tana hango sa ta ga murmushi dauke akan fusmar sa dan haka ta karasa ta rumgomo sa tana fadin
“Dear me muka samu ne?”
“Me kika gani?”
Ya fada yana kissing kumatun ta. Tace
“Naga sai wani smiling kake!”
Kai ya shafa yace
“Ko?”
“Yes!”
Ya kama hannun ta tace
“Baka fadan ba!”
“What?”
Ya tambaya tace
“Abun da muka samu.”
Yaja hancin ta bayan sun shiga falo yace
“Just Jannah ta ban daroya shine nake ta dariya.”
“Ka tabbata?”
“Yes now!
Ya jata jikin sa yana kissing wuyan ta duk dan kada ya bata damar kara questining nasa dan yasan Hali jidda da tambaya kamar yar jarida……….
*
**
***
****
*****
******
*******
Bayan sun dawo daga sallah. zaune suke a falo Mama da Maryama na daki wajen Aliyu.
Doctor na farko yace
“Abinda na fara lura dashi a tare dashi shine rashin cin abinci wanda ya haifar masa da ulcer mai zafi dan naga ta ci jikin sa”
Kai Abba ya girgiza ya zuba tagumi,  na biyu yace
“Nayi BP sa naga jinin sa ya hau sosai,  agaskiya akwai abinda yake damun sa duk dana tambaye shi yace bakomai!”
Na ukun Yace
“Yallabai a gaskiya ba xan boye maka ba zuciya sa ta kamu da ciwo.”
“Ya salam!”
Abba ya fada yana dafe kan sa. Shiru dakin ya dauka wayar dake aljihun Abba ce ta fara kara wannan yasa ya dago a hankali ya zura hannun a aljihu ya zaro wayar. Abubakar ne dan haka ya daga a hankali ya kai kunnen sa yace
“Assalamau Alaikum!”
Yaa Abubakar ya amsa da
“Wa’alaikum salam! Abba nayi iyayi na amman ba zamu samu flight ba sai zuwa gobe da dare.”
“Yanzu ba za a samu ko private bane mu tashi da safe.”
“Zan kara dubawa.”
STORY CONTINUES BELOW
“Alright!”
Kallon likitocin yayi bayan ya katse wayar  yace
“Ku bashi wani madication din zuwa gobe dan zan fitar dashi ne.”
Yana fadar haka ya mike ya kalli PA yace
“Ka amso maganin ka sallame su. Nagode!”
Yayi ciki. Dakin da suke ya shiga. A kwance ya samu Aliyu yana bacci Mama zaune akan sallaya tana addu’a. Maryama kuma na zaune a gefen gadon.
Shiga yayi ya zauna akan kujerar dake daki yace
“Maryama ki samarwa Yayan ki abu marar nauyi yaci kan a kawo maganin da zai sha.”
Mikewa tayi ta fita. Abbah ya kalli Mamah da ta shafa addu’a tace
“Me suka ce yana damun sa?”
Ajiyar zuciya Abbah ya sauke yace
“Ulcer ce saboda baya cin abinci sai jinin sa da ya hau ban san me ya sa a ransa haka ba.”
Tagumi Mamah ta zuba tace
“Alhaji duk matsalar tana ga mai dakin sa na daya. Yanzu menene aibun gidan nan. Kalli fa ko gidan shugaban kasa sai haka amman ace ta gwammace zama a can shi yana nan tayaya kake ganin zai samu kulawar ta. In tana nan ai ko yaya ne zai samu wani sassaucin ko ga cin abinci da rage kadaici ko? Mace ai ba a ce dan tai girkin ko wani abu bane har da dan bashi shawara ko kuwa? Gaskiya abin na damuna. Bayan nan ni daman ba na son wannan mulkin da aka dada masa. Aliyu yana da hakuri da zurfin ciki nasan ba komai zai fito ya fada ba zai bar abu a zuciyar sa ne.”
Sai ta fashe da kuka tana fadin
“Allah ka tashi kafadun Yaro na. Allah ina rokar ka ka bashi lafiya mai dorewa. Allah ya kawo masa mata wacce zata tausaya masa.”
Mai martaba ne ya mike ya dawo kusa da ita ya dafa bayan ta yace
“To menene na kukan ai addu’ar taki ce mafita kawai.”
Nan ya dinga lallashin ta. Hawayen idon ta ta goge tace
“Allah ya yaye maka!”
Maryama ce ta shigo dakin hannun ta tray sannan ta koma ta dauko wani basket. Ta dawo ta dauki cup ta hada masa kunun da ta dama sai pepper soup da tayi ta yanka kananana kananana. Akan bedside ta ajiye ta zauna a gefen sa. Ta kai hannun ta kansa. Ba zafi dan haka ta yaye bargon da ya rufa dashi.
Ido ya bude a hankali tace
“Yaya ka tashi kaci abinci!”
Mai martaba ne ya mike yazo ya dago sa,  gyara masa zama yayi Mama tazo ta dauki cup din ta fara bashi a baki. Kadan ya sha ta bashi pepper soup din shima yasha.
Ji sukai anyi knocking Mai martaba ya nufi bakin kofar ya bude. PA sa ne dan haka ya bashi hanya ya shige. Ledar hannun sa ya shiga ya ajiye sannan ya kalli Aliyu yace
“Sannu ranka ya dade!
Kai kadai Aliyu ya gyada masa. Yace
” Allah kara sauki!”
“Ameen!”
Abba ya kalla yace
“Ga maganin nan Allah kara sauki!”
Mai martaba yace
“Angode. Allah saka da alheri. Ka tsaya kayi dinner!”
Kai yayi kasa dashi. Abba ya kalli Maryama yace
“Kije kiyi serving nasa!”
Mikewa tayi ta fita. Serving nasa tayi tace
“Angode!”
Ta fada ta koma daki. Maganin taga Momy ta balla ta mika masa. Amsa yayi ya sha ya lumshe ido.
Ya jima a haka sannan ya zame ya kwanta. Abba yace
“Sannu Aliyu!”
“Yauwah Abba!”
Yai maganar a hankali. Ba wanda yake son ya gani ko yaji muryar ta in ba Aisha ba.
*
Mikewa Mama tayi ta fita. A falon sama ta zauna ta zuba tagumi tana hawaye can ta dauki wayar ta ta kira Maryama dake daki ita da Mai martaba gun Aliyu.
Dauka tayi Mama tace
“Kizo ina falo”
Mikewa ta fita. Tana ganin mahaifiyar tata na hawaye ta karasa wajen ta cikin tashin hankali  tace
“Mama menene kike kuka ?”
“Maryama kiga halin da dan uwan ki fa yake ciki.”
“Haba Mama ke fa kika bamu kwarin gwiwa da yadda da kadda da jarabawar ubangiji ki godewa Allah kiyiwa Yaya Addu’a ke mahaifiyar sa ce addu’ar ki zai fi bukata amman kukan ki ba abinda zai sai in ya gani ya kara daga masa hankali. A halin da Yaya yake ciki yanzu dole sai an taimaka masa an bashi farin ciki da kulawa. Kinsan Yaya ba abinda yafi so kamar ya ga farin cikin ki dan Allah Mama yanzu ki tashi muje kici abinci kiyi wanka ki kwanta ki huta.”
Ta kamo hannun ta sukai dakin da Aliyu yake. Akan carpet ta jere musu abincin sannan ta zuba musu tace
“Bismillah toh!”
“Kema sauko kici”
Duk dan ta basu kwarin gwiwa ta sauko ta saka hannu bayan tai bismillah ta fara ci. Ba laifi sunci abincin sannan kowa ya mike Abba ya tafi dakin dake kusa da na Aliyu yai wanka. Mama ma dayan dakin ta shiga tayi wanka.
Maryama kadai suka bari tana gyara dakin bayan ta gama ta debe kayan takai ta dawo ta zauna.
Abba ne ya fara dawowa ya kalle ta yace
“Kema kije ki watsa ruwan ko?”
Mikewa tayi ta fita. Dakin da Mama take nan ta shiga ta tadda Mama ta saka kaya. Kallon ta tayi yace
“Kiyi wankan kema kinji bari naje wajen Aliyun.”
Ta fita. Wanka ta shiga tayi ta fito ta saka kayan bacci sannan ta dauki wayar ta. Number da Sha’awa ta tura mata ta Hajara ta fara kira. Sai da ta kira sau uku sannan aka daga da
“Hello!”
Maryama tace
“Assalamu alaikum!”
Tsaki Hajara ta saki tace
“Waye ne?”
“Maryama Kabir kanwa ga Aliyu Kabir!”
“To menene zaki kira ni da wannan daren na fara bacci na.”
Agogo Maryama ta kalla taga lokacin karfe goma saura tace
“Ke har kina cikin kwamciyyar hankalin yin bacci bayan baki san a halin da mijin ki yake ba? Wai ke wacce iri jakar macece wacce son abin duniya ya rufewa ido in ba dan haka ba ace baki damu da mijin ki ba. Kina can yana nan kuma baki damu da sanin halin da yake ba yanzu in ma mutuwa yayi shikenan! Amman tur da irin wannan halin naki to menene auren kenan a haka?”
Duk da jikin Hajara yai sanyi amman sai ta daka mata tsawa tace
“Ke kisan da wacce kike magana fa!”
Wani murmushi mai ciwo Maryama tayi tace
“Nasan da wacce nake magana ai. Ko ba Hajara bace,  ban cin zarafin na kasa dani ko wanda ya girmen amman da a  yau na tina miki da ko ke wacece da kika manta. Amman nan ko a haka na tsawa zaki tuna wacece ke. Ni kuma bana alfahari da matsayin uba na dan nasan gidan wani zani amman da a yanzu na fada miki matsayi na. Amman dai ke ko ba komai matar Yayana ce wanda na fi so kuma ke yar uwa ta ce a musulunci dan haka da wannan zan baki shawara tin wuri kiyi karatun ta nutsu ki gyara halin ki ki kula da mijin ki tin kan wata tazo ta kwace miki shi. Bayan nan na bugu ne daman na fada miki Yaya na ba lafiya dan naga ke baki damu ba. Har wani bacci kike mijin ki kwana da kwanaki baki ganshi kuma baki damu ba bare ki neme shi kiji a halin da yake.”
Kit ta kashe wayar tana mai lumshe ido. Can ta bude tana fadin
“Allah ya kawo mai kular min da Yayana.”
Kofar dakin aka budo Mama ce ta shigo tace
“Au ba bacci kike ba na jiki shiru!”
“Yanzu zanyi amman sai naje naga Yaya ya jikin nasa.”
“Yasha magani kinsan har da na bacci. Bacci yake yi.”
Mikewa tayi tace
“Bari naje naiwa Abba sai da safe.”
Ta fita. Alwala Mama tayo ta zo ta fara sallah tana addu’a Allah ya bawa Aliyu Lafiya.
Maryama bayan ta dawo ta hau kan gado ta kwanta karfe biyu ta farka akan sallaya ta samu Mamah tana sallah. Itama mikewa tayi ta shiga bandaki. Alwala tayo tazo ta tada sallah itama. Tana addu’a Allah ya tashi kafadun Yayan ta ya kawo masa mace ta gari mai tallafa masa.
Har asuba suna kan sallaya sai da sukai sallah sannan suka koma suka kwanta.Aisha na kwance da dare ta rasa me yake mata dadi. Ido ta a lumshe yake har ta gaji da kiran sa dan kullum sai ta kira yau ne da wayar ke a kashe kawai bata kira sa ba dan bata da caji amman yadda ta damu dan kawai wayar ta ba charge bata kira sa ba ka zata in ta kira suna waya ne.+
A cikin kwanakin nan ta rame sosai duk yadda Yaa Muhammad ke son ya debe mata kewa da ya bar wajen take komawa ruwa. Dan sai taji komai ya fita a ranta. Ita tana nan tana da me debe mata kewa shi kuma fa? yana wane hali? me yake? Abubuwan dake damun ta kenan.
Ina Yaa Muhammad ya bata dariya tayi sai taji ciwon yin ta dan tana tunanin dan me take dariya shi bata san a halin da yake ba. Komai ya dagule mata matuka. Tin Yaa Muhammad na yadda da abinda ta fada masa har ya fara karya ta abun. Yana lura da ita daga ya bar wajen sai tayi kuka ko tai ta tunani. Abinda ke damun sa kenan shima duk ya saka damuwa dan masoyiyar sa.
Juyi tayi akan katifar ta tana fadin
“Yaa AK please where are you? Come back soon ina kewar ka. Ina jin a jikina nima rashin ka zai iya zama ajalina amman wannan ba zai sa naki Yaya na ba. Na gwamace na bawa Yaya na farin ciki ni na rasa nawa.”
Zuciyar ta ce ta tunasar da ita tace
“Farin cikin Yaa AK fa?”
Ido ta runtse zuciyar ta tace
“In kika aure Yaa Muhammad farin cikin mutum biyu zai mutu amman in Yaa AK kika aure farin cikin mutum daya ne zai mutu.”
Kai ta girgiza ta toshe kunnen ta tana fadin
“Bana son wannan tunanin ni dai Yaa Muhammad yai farin ciki.”
“Tayaya zai farin cikin bayan kince rasa Yaa AK tambakar rasa rayuwar kine. A lokacin zaki kara saka mutum biyu a cikin wani Hali.”
Zuciyar ta ta tunasar da ita.
Hannun ta ta zame tana fadin
“Yaa Allah. Allah nagide maka Allah na mika maka lamura na ka zaba min abinda yafi alheri a gareni ni baiwar ka ce mai sabo a gareka Allah ka yafe min ka fitar dani daga cikin halin da nake.”
Shafawa tayi hawaye na zubo mata. Can tace
“Amman dan me ka tafi ka barni? bayan ban fada maka bana son ka. Kai ma kasan ina son ka ai.”
Ta kifa kanta tana kuka. Rasa wane tunani zatai dan haka ta fara saka suratul Baqara a wayar ta tana ji tana bin karatun a hankali ta fara samun sauki a abun da take ji a cikin zuciyar ta. Ido ta lumshe tana mai cigaba da karatun bata san lokacin da bacci ya dauke ta na.
*
Zaune ta ganshi a kan kujera yana miko mata hannu yana fadin
“Hasken idaniyya ta kizo waje na. Kece farin cikin raina rasa ki tamkar rasa rayuwa ta ce. Amman Aysher ba xan miki dole ba ki sani a duk lokacin da ban ganki zuciya ta na shiga kunci jiki na yana kamuwa da ciwon rashin ki. Ina kaunar ki Aysher kizo ki fitar dani daga halin da nake ciki ke kadai zaki iya ceto na Aysher na.”
Hannun sa ta kama taji shi zafi zau. Wannan yasa ta dago ta kalle shi sai taga ya rame baki ta bude a hankali tace
“Yaa AK jikin ka Zafi?”
“Aysher abinda nake ji a cikin zuciya ta yafi wannan zafi.”
“Me kake ji?….”
*
Zai magana kenan ta farka da sauri ta mike zaune tana kalle kallen dakin da take tana ganin ta a dakin ta ta fashe da kuka. Jin sautin kukan ta ke fita ta toshe bakin ta da hannun ta tana sakin hawaye.
STORY CONTINUES BELOW
Yaa Muhammad dake tsakar gida yana sallah yaji kukan ta. Yana idar wa ya mike ya nufi dakin ta. Sheshekar ya tadda ta tanayi tana sauke ajiyar zuciya.
“Yaa AK baka da lafiya ne? Ka dawo ka fadan me kake ji? Dan Allah kazo ka fada min ko naji sauki abinda nake ji.”
Dakin ya shigo da sallama. Mikewa tayi zaune a tsorace. Kallon ta yayi ya dauke kai ya karasa ya zauna a gaban ta yana kama hannun ta yace
“Aisha Lafiya kike kuka da daren nan?”
“Yaa AK…”
Sai tayi saurin yin shiru ta dafe bakin ta da hannun ta.
“Fada min menene kanwata.”
Ya fada yana janye hannun ta. Kuka ta fashe dashi. Ido ya runtse yana jin kukan nata har cikin zuviyar sa.
“Ki daina kukan nan ki fada min menene?”
“Mafarki nayi!
“Shine kike kuka? Wane irin mafarki ne?…. Ko da yake ba sai kin fada min ba. Kinyi addu’a da kika yi?”
Kai ta girgiza. Yace
“Kiyi addu’a ki tofa ki koma ki kwanta ai ba kowanne mafarki ne yake dai dai ba. Kinji!”
Kai ta gyada tayi yadda yace ta koma ta kwanta amman sam ta kasa yin baccin ganin ba zata iya baccin ba yasa ta mike ta fita. A kan sallaya ta same shi. Kallo ya bita dashi ta shiga bandaki tayi alwala ta dawo ta shiga daki ta hau kan sallaya ita ma. Sallah ta dinga yi da addu’a Allah ya Kare Yaa AK.
Tana zaune tana jan carbi bata san lokacin da bacci ya dauke ta akan sallaya ba. Sai jjin kiran sallah asuba tayi ta mike da sauuri ta tadda Yaa Muhammad zai fita. Kai tayi kasa dashi ta wuce tayi alwala ta dawo daki. Sallah tayi ta koma kan gado ta zauna tana azkar.
Bayan ta gama azkar din ta mike ta gyara dakin ta sannan ta fita ta samu Ummah ma tana hada break durkusawa tayi ta gaishe ta. Umma ta amsa tana bin ta da kallo. Mikewa tayi ta share tsakar gidan sannan ta wanke bandaki tazo ta hada wanke wanke.
Yaa Muhammad ne ya shigo yana ganin ta yayo gun ta.
“Ina Kwana Yayana?”
“Lafiya lou kin tashi lafiya?”
Amsar wanke wanken yayi ita kuma ta koma dauraya. A haka suka gama ba wanda yace dan dan uwan sa kala. Suka kwashe kayan tas.
Daki ta shiga ta cire kayan jikin ta,  ta saka hijab ta fito ta wuce bandaki. Wanka tayi ta koma daki ta shafa mai. Doguwar riga ta saka baka sannan ta dauki Ash Hijab ya saka har kasa.
Zama tayi a gefen katifar ta tana tunanin yadda zatayi ta fita taje ta dubo Yaa AK. Tagumi ta zuba can ta mike ta fito.
Umma na daki ta dan haka ta tafi gun ta. Kallon ta Ummah tayi tace
“Ina zuwa?”
“Gidan su Bilkisu zani zan amso abu nane.”
“To kada ki dade.”
“Toh Ummah!”
Ta mike ta fita.
*
Washe gari da sassafe Hajara ta kira PA ba a jima ba yazo iso akai masa iso.  A falo ya same ta ya gaishe ta ta amsa.
“Gidan Mai gida na nake son ka kai ni.”
“To ranki ya dade!”
Mikewa tayi ta shige daki ta dauko Mayafi sannan ta fito suka tafi.
A mota ta shiga baya shi kuma ya fara driving. Tinda suka zo bakin gate take kallon gidan dan ba karamin kyau yai mata ba. Bata zata yakai haka ba gidan yai kyau sosai dan har yafi gidan gwamnati kyau da tsaruwa wannan madaidaici ne kawai. Ciki ya shiga yai parking suka fito.
Masu aiki na ta aiki da yake safiyya ce suna ganin su suka fara gaishe su amman sam Hajara ko kallo basu ishe ta ba. Suna shiga falon kamshi mai dadi ya daki hancin ta.
Maryama dake duke tana saka turaren wuta ta dago kallon juna sukai ta dauke kai. PA yace
“Barka da asuba Gimbiya. Hajiya karama mai halin manya”
Murmushi tayi tace
“Ina kwana? Ya dawainiyya Allah ya saka!”
“Amin nagode!”
“Bismillah bari na fadawa Mamah kazo.”
Tayi sama. Tsaki Hajara ta saki tace
“Nayi sake ace gidan miji na ba zan iya iko dashi ba bama nasan yadda yake ba bare nasan dakin miji na.”
STORY CONTINUES BELOW
Kujera ta koma ta zauna tana cije bakin ta. Maryama na shiga ta tadda Har Abbah ya taimakawa Aliyu yai wanka ya saka kaya BCyana kwance idon sa a rufe. Mamah na zaune a gefen gadon tana gyara masa kwanciyya.
“Maryama kin gama aikin ne?”
“Eh daman PA ne yazo da matar Yaya!”
“Je ki shigo dasu.”
Mikewa tayi ta fita. A falon ta tsaya tace
“Bismillah!
PA ne ya mike ya kalli Hajara yace
“Bismillah Hajiya!
Mikewa tayi tabi bayan sa har suka isa dakin. A kasa PA ya zube
“Ina kwana Ranka ya dade!”
“Lafiya lou. Ya gajiyar ka ta jiya. Allah yayi albarka.”
“Amin nagode ranka ya dade! Ya mai jiki?”
“Alhamdulillah!”
Ya kalli Mama yace
“Ina kwana Ranki ya dade?”
“Lafiya Alhamdulilah!”
“Ya me jikin?”
“Alhamdulillah Allah saka da alheri.”
“Amin!”
Hajara ce ta durkusa tace
“Ina kwana Abba ya mai jiki?”
“Alhamdulillah!”
Ta kalli Mamah tace
“Ina kwana Mama ya me jiki?”
“Alhamdulillah!”
“Allah kara sauki.”
“Amin.”
Zama tayi a gefe kan ta a kasa. Maryama ce ta dawo tace
“Abbah na gama hada dining din.”
Kallon PA yayi yace
“Kaje ka karya kaji.”
Kaivya sosa yace
“Toh Ranka ya dade.”
Ya mike. Abba ya kallo Maryama yace
“Ki kawo mana namu nan. Da na Yayan naki.”
“Toh Abbah!”
Dakin yai shiru Hajara ta fara magana tana hawaye tace
“Wallahi ban san bai da lafiya ba na zata yayi tafiya ne da na ji shi shiru.”
Abba ne yace
“Muma haka mukai zato amman hankali na yaki kwanciyya saboda nasan duk da ba gida daya muke ba duk inda zai je yana fada min amman wannan shiru,  wannan yasa na taho.”
“Ikon Allah kuma ko PA bai fadamin ba sai da mukai waya da Maryama take fada min. Allah basa lafiya.”
“Amin Amin.”
Mamah dai batai magaba ba dan kome Hajara zata fada ba zai shige ta ba.
*
*
*
Tana zuwa bakin gate din taji gaban ta ya fadi. Hannu ta saka ta dafe kirjin ta sannan ta nufi kofar tayi knocking. Mai gadi ne ya karaso yana ganin ta ya ja baya yace
“Aisha!”
Kai tayi kasa dashi tace
“Na’am ina kwana?”
“Lafiya lou ya kike ya gidan?”
“Lafiya Alhamdulillah! Yaa AK yana gari kuwa?”
“Yana nan Ranki ya dade!”
Kasa shiga tayi sai ta dago ta kalle shi tace
“Zan iya shiga?”
Mai gadi Ya yi dariya yace
“Wa ya isa ya hanaki shiga. Kofar gidan nan a bude take in dai ke ce zaki shiga’’
   
Tayi murmushi tace
“A da da ake hanani fa?”
“Rashin sanine uwar daki na.”
Murmushi tayi tace
“Amman sai naga gidan kamar da mutane ko?”
Ganin mutane nata zirga zirga ba kamar da ba. Yace
“Haka ne! Mahaifin yallabai da Mahaifyar sa ne suka zo?”
Ido ta zaro tace
Amman dai lafiya ko?”
“Gaskiya yallabai ne ba lafiya.”
Ji tayi kamar zata fadi dan haka ta jingina da gate din tana fadin
“Tin yaushe kuma?”
“Wajen sati biyu kenan!”
“Amman shine bai fada min ba.”
Ta fada idon ta na kawo ruwa.
Shiru mai gadi yayi tace
“Please kai min iso mana.”
“Toh!”
Ya fada ya kira wanda ke taimaka masa a bakin gate sannan sukai ciki.
Wani makeken falo suka shiga. Mai gadi yayi sallama itama tayi tare da bin sa a baya.
Wata dattijuwa mai cikar kamala da kwarjini zaune a falon kan wata tafkekiyar darduma na alfarma mai kyau da laushi, Mamah kenan mace mai mutunci,  hakuri da sanin yakamata.
Ita ta amsa musu sallamar, cikin sakin fuska  suka suka zube a gabanta. Mai gadi ne ya fara gaishe ta ta amsa tana tambayar sa ya aiki. Sannan Aisha da kanta ke kasa itama ta gaishe ta.
Mai gadi ya kalli Aisha ya ce, ‘’mahaifiyar Yallabai ce’’
Nan Aisha ta kara fadada murmushinta, ta kara mata gaisuwa na musamman sannan ta ce,
‘’ya me jiki?’’
Mama ta amsa
“Da sauki’’
Mai gadi ta kalla tace
“Wacece ita?”
Kan sa a kasa yace
“Kanwar Yallabai ce.”
Mamah ta gyada kai kawai tana kallon Aisha da ta kasa dago kan ta can Maryama ta sauko ta kalle ta tace
“Maryama ki zo ki kai ta ta duba Yayan ki.”
Kallon ta Maryama tace yace
“Lah kamar Aisha ko?”
Aisha ta dago ta kalli Maryama ta saki murmushi kawai. Karasowa Maryama tayi da sauri tace
“Mama baki gane ta ba. Aisha ce fa wacce kuke gaisawa.”
“Ikon Allah ai ban gane ta ba. Aisha ya kuke yasu Umman taki?”
“Suna nan kalau!”
Maryama tace
“Taso muje!”
Ta kama hannun ta. Nan suka mike suka nufi sama.
A falon  sama suka tadda Hajara zaune tana waya. Aisha na ganin Hajara taji gaban ta ya fadi kamar yadda Hajara taji itama. Fuska ta tsuke tana hararar su.
“Ina zakuje bayan bacci yake?”
Hajara ta fada. Maryama bata kalle ta ba ta dauke kai kawai. Aisha kuma ta tsaya. Juyowa Maruama tayi jin Aisha ta zame hannun ta daga nata tace
“Taho mana.”
Bin bayan tatayi a ranta tana fadin
“Duk yadda akai wannan ita ce matar Yaa Ak!”
 
Dakin da yake suka isa. Maryama ta saka hannu ta bude dakin suka shga da sallama. Wani kamshi ya doki hancin su. Ido Aisha ta lumshe.
Abbah ne ya amsa suka shiga kwance yake a kan gado idonsa rufe, sai dai ba wai baccin yake ba yana jin duk abin da ake yi.
Dan Abba ne tsaye a kansa ya na masa addu’a. Jin muryar ta yasa ya bude idon sa ya maida kallon sa kanta, kamar a mafarki ya ganta bai kuma za ta zai iya ganin ta a wannan lokacin ba a kuma tsakar dakinsa ba.
Kallon ta yake ya kasa kau da kansa haka ya kasa daga idonsa daga fuskarta. Kallon da yake mata ya sa mai martaba juyawa don ya game ya dauke masa hankali haka da ya tattara hankalinsa, nutsuwarsa gaba daya ya mayar kansu.
Ya lura ita ma kallon sa take hankalinta tashe ganinsa cikin ciwo, hakan ya sa Mai martaba ya mike ya fita yana tunanin wace yarinya ce haka da ta tafi da hankalin dansa ta samu kulawarsa da nutsuwarsa.
   
Aisha kuwa bama ta san Abbah ya fita ba. Maryama dake tsaye a gefen ta ta janyo hannun ta ta kawo ta gaban gadon sannan ta juya ta fita.
*
Abbah na sauka kasa ya zauna,  a ransa yake fadin
“Wacece yarinya ce haka da ta tafi da hankalin dansa ta samu kulawarsa da nutsuwarsa?”
Haka nan ya lura da ganin ta ba karamin kwanciyar hankali da jin dadi ya saukar masa ba. Yana xaune Mamah ta fito daga daki. Dagowa Mai martaba yayi ya tsare ta da kallon tambaya.
Murmushi tayi tace
“Ranka ya dade na fa karance ka. Shekara arba’in da… ai ba wasa bane!”
Yai murmushi yace
“Shiyasa nake sonki ai.”
“Yanzu nasan akan yarinyar nan ne ko? Ni Aliyu bai fada mana komai akanta ba yana dai hada mu,  mu gaisa ne.!”
Shiru Abbah yayi yace
“Me kika fahimta?”
“To kasan Aliyu dai nayi mamaki da yake kula yarinyar duk da shi ba ma’abocin kula yan mata bane. Amman nima na fara zargin son ta yake kuma in har haka ne zanfi kowa jin dadi dan naga yarinyar akwai tarbiyya da hankali gata kyakyawa tin fara wayar mu ta shiga raina yau kadai da na ganta na kara jin wani sonta a raina.”
“Kedai kawai dan ‘danki na son tane kawai.”
“Yallabai kenan duk abinda Aliyu keso ai dole naso amman gaskiya yarinyar nan kawai ta kwanta min ba dan Aliyu na son ta ba.”
“Toh Allah tabbatar da alheri. Anjima zamu tashi dan Abubakar ya samar mana flight zan fita dashi acan a duba shi a bashi treatment me kyau.”
“Allah ya bashi lafiya dai.”
“Amin!”
A daki Aliyu dake kwance ya kalli Aisha ya mata murmushi, ita ma ta mishi, ta ce,
“Yaa AK ya jiki? Ashe baka da lafiya baka fada min ba. Meyasa baka fada min ba meyasa ka daina zuwa waje na bayan kasan zan shiga wani hali. Duk hanyar ganin ka ka toshen ta wayar ka a kashe sannan in nazo baka dawowa da wuri duk dan kar na ganka ne. Wannan shine son da kake min ehhee?”+
Ta fada hawaye na zubo mata akan fuskar ta. murmushin ya dan saki yace
“To menene na kukan ba gani ba.”
“Kalli yadda ka rame fa dan Allah tin yaushe kake ciwo ban sani ba da ban zo bama ba zan sani ba kenan. In da banyi mafarkin halin da kake ba tayaya zan sani.”
Ta fada tana kifa kan ta akan gadon tana kuka.
Duk yadda yake jin zafi a zuciyar sa kafin zuwan ta a yanzu yafi jin zafin saboda kukan da take. Duk yadda ba kwari a jikin sa haka ya mike zaune  ya matso kusa da ita ya dago kanta. Hannun sa ya saka yana share mata hawayen yana girgiza mata kanta.
“In kina kiukan nan kina dada min wani ciwon a cikin zuciya ta Aysher bana son kukan ki ko kadan abinda yasa na barki kenan. Dan ki samu nustuwa da cikar burin ki.”
Kai ta hau girgizawa tana fadin
“Tayaya zan samu cikar burina baka tare dani. Yaa AK ko karatu bana iyawa bana iya bacci bana iya cin abinci komai nake tunanin ka nake tayaya zan samu cikar buri na a wannan halin Yaa AK!”
“Ki daina fadar haka Aysher. Saboda me zaki saka damuwa haka. Kada ki manta buri na shine naga kin gama jarabawar nan kin samu sakamako mai kyau kin zama babbar likita kina duba marasa lafiya. Haba Aysher na in kina saka damuwa tayaya hakan zai faru…”
Tari ya fara ya dauki tissue ya rufe bakin sa da ita. Yana daukewa sai ganin jini sukai a firgce ta mike tana zaro ido.
Shima ya firgita amman ya basar ya mika mata yace
“Put it in dustbin.”
Amsa tayi ta saka ta dawo ta zauna a kasa tana kallon sa tace
“Me yake damun ka Yaa AK aman jini fa. Duk da ban san me yake damun ka ba amman nasan wannan matsala ce babba.”
“Ki kwantar da hankalin ki Aysher ni dai fata na ki gama jarabawa ki samu sakamako mai kyau ko ina da rai ko ban da rai zanji dadi nayi alfahari dake kuma zan bar wasiya ko na mutu a tsaya miki sai kin gama karatun ki. Ina fatan zaki bani hadin kai Aysher!”
“Yaa AK wacce magana ce haka. Bazaka mutu ba. Ba yanzu zaka mutu ba. Ai cuta ba mutuwa bace zan na maka addu’a Allah baka lafiya amman ba zaka mutu ba dan Allah kadaina fadar haka.”
Ta fada tana kuka. Hannun ta ya kamo ya rike yana mai lunshe idon sa. Knocking Kofar dakin taji anyi wannan yasa ta fara kokarin kwace hannun ta. Kin saki yayi. Sallama akayi aka bude. Maryama ce ta shigo hannun ta rike da lemo da ruwa ta ajiye mata sannan ta kalle ta ganin hawaye a idon ta ta karaso wajen su da sauri tana fadin
“Kuka kuma Aisha?”
Ido Aliyu ya bude ya kai hannun sa yana goge mata idon yana girgiza mata kai. Murmushi ya sakar mata itama ta sakar masa.
“Me zaki ya cewa ga rayuwar mu ta baya?”
Ya fada a hankali.
STORY CONTINUES BELOW
Shiru tayi can tace
“Yau na ga Mamanka da Kanwar ka wadan da muka dade muna waya ban san su ba., ban taba za ta Yaa AK din da na sani babba mutum ne haka ba, duk da na san kai dan’uwan gwamna ne ban za ta iyayenka manyan mutane haka ba.
Saukin kanka da saukin hali irin naka da yadda ka dauki rayuwarka mai sauki duk da ko kana dan manyan mutane masu arziki ya sa na soma ganinka da daukanka kamar wani dan’uwana, nagode da duk abinda ka min na kyautatawa da alkhairi.
Ka bani lokacin ka,  ka kuma bata lokacinka a kaina, duk dan ka koya min karatu da sauraron surutuna, har ma ka dau shawarata ka dinga ba gwamna shawara nagode.
Ta dalilinka na je inda matsayina bai kai ba, na jera nayi tafiya da wanda matsayi sa ya wuce nawa, na taka in da matsayina bai kai in taka ba, madalla da irin hali naka Yaa AK Allah ya biya ka.”
Shiru tayi sannan ta dago ta kalle shi tace
“Rayuwa ta da kai aba ce da ba zan taba mantawa da kai ba Yaa AK ka ban komai farinciki,   ka kulawa dani ka ban komai naka time, care har da soyayyar ka. Amman kash ni na kasa baka abinda kake nema aguna ba dan komai ba sai dan abin yafi karfi na. Ba zan taba cewa bana son ka ba kamar yadda ba zan taba iya fadawa Yaa Muhammad ba amman ka sani zan karasa rayuwa ne dakai a zuciya ta kuma rabuwa dakai tamkar….”
Sai kuma tayi shiru ta dago sannan tace
“Fatana da roko na Allah yasa ba ta dalili na kake kwance baka da lafiya ba dan in dai ta dalili na ne ba zan taba yafewa kai na ba….”
Idonsa suka kada su kai ja duk dauriya da jarumta irin ta sa sai da ya ji hawaye na shirin zuba masa, bai san yaushe ya sa hannu ya riko hannun ta ba, ya rike gam cikin sanyin murya ya ce,
“Aysher ina son ki,  Aysher son ki ne rayuwa ta. kar ki rabu da ni, Aysher bana so in yi rashin ki, Aysher ba na son rasa ki’’
Da sauri Maryama ta fice a dakin tana hawaye. A falon sama ta zauna ta kife kanta akan kujera tana kuka.
Aisha kuwa Zuciyarta ta ji yana bugawa da karfin gaske, wani abu ta ji yana yawo a jikinta wanda ta rasa menene, tuni ta ji zuciyarta ta karaya, tausayin kanta ya kamata.
Za ta fashe da kuka sai kuma ta daure ta runtse ido, a ranta tace
“ya Allah ka taimake ni, ya Allah me ke faruwa da  ni ne ?”
A hankali ta bude idon ta ta sauke kanta kasa. Hannun ta dake rike da nashi ta yi kokarin kwacewa amman ta gagara, ta sa daya hannun da niyar kwacewa amma sai taji jikinsa ya yi zafi kamar wuta, sai lokacin ta lura da cewa zafin jikinsa ya yi yawa. Ta kuma tuno da mafarkin ta na jiya. Da sauri ta dago takai hannun goshinsa, kamar zatai kuka tace
“Yaa AK jikin ka xafi. innalillahi! ina ruwa da towell ?”
Zata mike ya janyo ta tayo kansa. Ido ta zaro kan ta farga sai ganin ta tayi akan sa kwance. Jikin tane ya fara rawa. Tana kokarin sauka akan sa ya kara rike ta kam.
“Jikin ka zafi ka bari a saka maka ruwa!”
“Aysher wannan zafin ba wani zafi bane akan wanda nake ji a cikin zuciya ta……”
*
**
***
****
*****
******
*******
Sosai Fateema taji dadin gidan Hajiyar Fu’ad. Dan Nusaiba da Izzy ba karamin debe mata kewa suke ba. Hajiya ma taji dadin ganin ta sake sosai a gidan.
Ranar da zata tafi kuwa duk sai sukaji ba dadi. Dan tana hada kayan ta duk cirko cirko sukai akanta suna kallon ta jiki a sanyaye. Bayan ta gama ta dago tana kallon su. Sai ta saki murmushi tace
“Menene ne? Sai kace an rabu kenan naga bamu da nisa zamuna zumunci ko ba zaku na zuwar min ba.”
“Zamu zo Aunty!”
Izzy ta fada. Nusaiba shiru tayi kawai. Fateema ta dago kan ta tace
“Haba Nusy na smile mana ko mu tafi tare kawai daman kinga gidan babu Baba Uwani da Yasmeen daga ni sai Momy zaki bini?”
Kai ta gyada tace
“To sai mu tafi ko? Kiyi murmushi man baki san kin fi kyau da murmushi ba yar beauty nah.”
Murmushi ta saki ta mike tace
“To debo kayan naki!”
“No Aunty zan zo daga baya amman ba yau ba.”
STORY CONTINUES BELOW
Fuska Fateema ta bata tace
“Bayan kin sa min rai!”
“Kiyi Hakuri gobe Dad zai dawo kuma nayi missing nasa so much Aunty but i promise you da ya kwana biyu zan zo na yinar miki!”
“Just yini no yai min kadan kwanaki zaki min.”
“Naji!”
“Yauwah koke fa! Izzy fa?”
“Zan zo Aunty ki ban number ki!”
Wayar ta ta amsa ta saka mata digit din ta sannan ta bata ta mike tace
“To bari na tafi!”
“Aunty ki bari sai bayan magariba mana!”
Kafadar ta Fateema ta dafa tace
“Dear wallahi ban fiya son fitar dare ba bama driving in ta kama na kai dare a asibiti sai dai a dawo dani gida ko na hau motar haya.”
“Shikenan!”
Suka mike. Nusaiba ta kamo akwatin ta suka fito falo inda Hajiya ta ke.  Durkusawa Fateema tayi tace
“Mama na fito bari naje nayiwa Hajiya sallama”
“To shikenan!”
Ta mike suka bi bayan ta suka bi. A compound din Hajiyar cikin gida suka samu Hibbah da Mimie zaune kowa rike da waya yana daddanawa. Suna shiga Mimie ce ta dago tana ganin Fateema ta mike tana fadin
“Barka da Yamma Dr!”
Murmushi Fateema tayi tace
“Ya kike?”
“Lafiya lou ya gidan?”
Itama ta fada tana murmushi.
“Alhamdulillah!”
Hibba ta dan kalle ta tace
“Ina yini?”
“Lafiya lou!”
Kawai ta fada tayi ciki ta barsu da su Nusaiba suna magana.
Sallama tayi a kofar falon. Hajiyar cikin gida dake zaune tana jan carbi ta amsa sallamar tana kallon Sakina dake aikin latsa waya. Ta harare ta ta dagowa tana kalon Fateema dake shigowa.
Murmushi ta saki tace
“Ashe kice shigo mana.”
Ta karaso ta zauna a kasa kan carpet kan ta a kasa tace
“Ina yini Hajiya?”
“Lafiya Alhamdulillah ya kike ya gidan namu da dadi kuwa?”
Kai ta gyada tace
“Sosai kuwa Hajiya.”
“Masha Allah.”
Ta dago ta kalli Saiina tace
“Ke bakiga Auntyn kuba?”
Baki ta turo tace
“Sannu!”
“Yauwah!”
Fateema ta fada ba tare da ta kalle ta ba. Dan kar Hajiya ta yi magana tace
“Daman sallama nazo nai miki zan tafi.”
“Haba dai har an gama kwana biyu kai ni kuwa sai naga kamar ba ai kwanakin bama. Kai amman wallahi ba dadi dama Momyn taki zata bar mana ke!”
Nusaiba da ta shigo tace
“Tai miki me?”
“Tai min kaniyar ki!”
Hajiya ta fada. Dariya Nusaiba ta saki tace
“Dan ki shafa mata tsufa to ba zata zo ba.”
“Ni rufen baki ke bakya ma kewar ta ko?”
“Ni kuwa nake Hajiya yanzu na gamai mata kuka.”
“Ni rufen baki.”
Hajiya ta mike tayi daki bata jima ba ta dawo hannun ta rike da leda tace
“Ga wannan ba yawa Nagode Fateema!”
Ta kalli Sakina tace
“Ke tashi kije ki dauko min dambun naman nan yana cikin durowa a kitchen. Sauran ki diba kuma dan kowa na bashi nata ne na ajiye mata daman.”
Mikewa tayi tana turo baki ta shiga ta dauko ta dawo ta ajiye a gaban Hajiya tayi daki. Hajiya ta bita da kallo sannan ta dawo da kallon ta kan Fateema da kan ta ke kasa tace
“To Fateema mun gode Allah saka da alheri ki gaida Hajiyar taki mungode sosai.”
Kan Fateema a kasa tace
“Nagode Hajiya Allah saka da Alheri sai anjima!”
Ta mike Nusaiba da Izzy suka daukar mata kayan suka fita. Mimie ta mike tace
“Ashe tafiya zakiyi Dr to sai munzo!”
“Ina zuba ido!”
Hibba tace
“Allah kiyaye hanya!”
“Amin nagide!”
Fateema ta fada. Izzy da Nusaiba suka  fito Mimie ta mike tace
“Muje na raka Dr!”
Suka fita daga bangaren Hajiyar cikin gida. Falon Hajiya suka koma. Hajiya tace
“Har kun fito.”
Fateema tace
“Eh Mama ga kayan da Hajiya ta bani nan!”
“Kai madallah angode Allah saka!”
Ta mika mata wata katuwar leda tace
“Ga wasu nan ba yawa Fateema nagode sosai wallahi naji dadin zuwan ki.”
“Nagode Mama Allah ya saka da alheri Allah kara lafiya da girma da nisan kwana nagode sosai.”
“Fateema muke da godiya.”
“A’ah Mama ya’ya ne ya kamata suyi godiya ba iyaye ba. Nagode!”
“Ba komai Fateema Allah yayi albarka”
Suka amsa da Amin tace
“To Mama zan tafi.”
“Allah kiyaye hanya ya tsare!”
“Amin Mama!”
“Ki gaida Momyn taki kiyi mata godiya sosai.”
“Insha Allahu!”
Suka mike dukka suka kwashe mata kayan suka fita. Har Hajiya. A compound ta bude mota suka zuba mata kayan. Mimie tace
“Dr baki ban number ki ba.”
Ta mika mata wayar ta amsa tayi ta saka ta mika mata. Sannan ta rumgume Nusaiba ta shafa bayan ta tace
“Ina zuba ido.”
Ta kalli Izzy ta mika mata hannu ta rumgume ta tace
“You too dear!”
Mimie ta karasa ta rumgume ta tace
“Kema sai na ganki.”
“Insha Allah!”
Tayi gun Hajiya ta durkusa tace
“Nagode Mama Allah saka na tafi.”
“Allah tsare Fateema nagode sosai!”
Ta amsa da Amin ta mike ta wuce gun mota ta shiga mai gadi ya bude mata. Hannu suka hau daga mata har ta fice sannan suka juya suka koma.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *