WA NAKE SO CHAPTER 14

 WA NAKE SO CHAPTER 14

Tana fita ta hau kan titi tana driving tana dan girgirza kan ta domin yadda Hajiyar Fu’ad ke son ta har tausayi take bata. Take ta cije leben ta tana fadin

“Amman ban kyauta mata ba sam dan ni Ya tafi ya bar mahaifiyarsa. Mace mai hakuri karamci da mutunci Allah ka dawo mata da Fu’ad cikin gaggawa kasa yana lafiya.”+

Kwallar da ta taru a idon ta tasa hannu ta goge ta. Idon tane ya sauka akan wajen da ake gashin kaji. Sanin Momy naso yasa ta matsa gefe tayi parking sannan ta danna horn. Nan da nan yaran wajen suka karaso. Ya leka ta window da ta sauke ta fada masa ayi mata parkaging guda uku sannan ya tafi da sauri.

Ba ayi minti biyar ba ya dawo da babbar leda ya  mika mata. Amsa tayi tace

“But is like is more than three?”

Ta fada tana budewa.

“Yes Ma!”

Kallon sa tayi tace

“Why?”

Nuni yai nata dashi da ya fito daga wajen dagowa tayi dan taga me ake nuna mata daga kafar sa ta fara kallon sa wacce take fara tas tai kyau a cikin bakin takalmin da ya saka. Sau Ash kalar wando da bakar riga da suka kara masa kyau. Baya ya juya mata amman taga hannunsa da ya rike waya yana ansering call. Gaban tane ya hau faduwa tin kan tasan waye. Ta juyo da niyyar yiwa wanda ya kawo mata kajin magana taga baya wajen.

Juyowa tayi dai dai lokacin da ya juyo kenan yana kallon titi Idon sa sanye da bakin glass ba zata ce ga wanda yake kalla ba. Har lokackn waya na kare a kunnen sa yana dan sakin murmushu. Faduwar gaban tace ta dadu tai saurin dauke kai tayiwa motar ta key ta tayar ta bar wajen.

Da kallo ya bita yana murmushi ya zare wayar yana fadin

“Dr kenan!”

Sai kuma yai sauri yakara wayar a kunne yana fadin

“Hello are u there?”

*

Driving take amman sam bata san tunanin da take ba har ta iso gida tai horn mai gadi ya bude mata da sauri dan ya gane horn din ta kadai. tana shiga ta nufi parking space tai parking. Mai gadi na rufe gate ya karaso wajen ta a gudu gudu,  sauri sauri ya zo yana fadin

“Sannu da zuwa  Docta!”

“Yauwah Baba ina yini?”

Ta fada tana fitowa a mota.

“Lafiya lou kin dawo lafiya?”

“Alhamdulillah!”

“Masha Allah!”

Ledar da aka zubo mata nama ta dauko ta dauki daya ta mika masa tace

“Ga wannan ba yawa.”

“mai yawan kenan Hajiya nagode!”

“Ina Habib dan Allah kasa ya kwason kayan cikin motata.”

Ta fada tana yin cikin gida.

Tin a barrender ta fara kwadawa Momy kira tana fadin

“Momy nah! Momy nah!”

Momy dake kitchen ta leko tace

“Au Fateema ke kam ba zaki girma ba kenan…”

Ai Fateema na ganin Momy ta kwasa a guje ta nufe ta ta rumgume ta. Momy ta shafa kanta tace

“Kin ki girma dai Fateema ko? Ko da yake tayaya zaki girma baki aure kin haifa ba. Nasan in ba direwa ki kai ba, ba zaki yadda da kin girma ba.”

STORY CONTINUES BELOW

“Kai Momy dan kawai nayi missing naki.”

Ta kwantar da kan ta a kirjin ta. Murmushi Momy tayi tace

“Dagani ni girki nake yi.”

Ta dauke kan ta ta juya tayi kitchen. Bin bayan ta tayi tace

“Me ake dafa mana?”

“Sai kace ci zakiyi?”

“Zanci mana Momy kwana biyu kadai nayi kewar abincin ki.”

Momy ta juyo ta kalle ta tace

“Da yake abincin kike ci ba.”

“Allah da gaske Momy.”

“Uhmm ni kyale ni yasu Hajiyar?

Murmushi tayi tace

“Wallahi duk suna nan kalou sunce a gaishe ki.”

“Ina amsawa!”

Amsar mata girkin Fateema tayi tana bata labarin yadda taji dadin gidan. Momy na gefe tana jin ta tana ta murmushi. A haka suka gama girkin suka fita falo.

Nan taga ya shigo mata da kayan ta. Zama tayi ta dauki babbar ledar tace

“Ga wadda Hajiyar Fu’ad ta bani wannan kuma Hajiyar cikin gida ne!”

“Kai Madallah an gode har da wahala.”

Ta bude ledar Hajiyar Fu’ad atamfa da less ne da shadda sai kayan kwalliya da turaruka masu kyau da tsada.

Hajiyar cikin gida ma humra ce yar gaske da sabulun wanka da wanki sai dambun naman da ta bata. Momy ta ajiye tace

“Kwalliyar da bayi kike ba?”

“Kai Momy wacce kwalliya ni kam zanyi yanzu!”

“Saboda kin tsufa ko?”

“Ba haka bane wa zan wa to?”

“Ai ba wani akace kiyiwa ba kiyi dai ko?”

“Uhmm!”

Ta fada.

“Kenan ba zakina yi ba?”

“No Momy ni yanzu ina naga tym din yin wata kwalliyya in na fita tin safe sai yamma wataran dare ai cabewa zatai”

“Wannan da law kika karanta komai aka fada sai kin kare kanki.”

Mikewa tayi ta dawo kusa da ita ta daura kanta a kan kafadar ta tace

“To ai gaskiya na fada Momy na. Wallahi nayi missing naki alot.”

“Hmmm!”

“Ke fa?”

Fateema ta tambayi Momy.

“Ke ni dagani.”

Ta fada tana dauke kan ta.

“Ga tsaraba nan.”

Ta miko mata leda. Dauka tayi ta bude tace

“Azo a mikawa Malam Abdu.”

“Momy na bashi ai!”

“Amman kika siyo har kulli biyar Fateema mu kai ta ina bayan mu kadai ne a gidan!”

“A saka a firij ko?”

“Kudin ne yai miki yawa bayan akwai kaji a firij ma”

“Wancan na miya ne wannan kuma na marmarine.”

“To Antyn tsari.”

“Kai Momy kawo kulli daya a bawa Habib!”

“Gaskiya dai!”

Ta mika mata ta mike ta fita. Tana dawowa ana kiran sallah. Kayan ta ta kwashe ta kai daki. Ta cire na jikin ta ta shiga ta watsa ruwa ta fito ta saka doguwar riga marar nauyi sannan ta tada sallah. Tana idar wa ta zauna tana karatun alkur’ani har akai isha’i tana zaune.

Kofar dakin aka bude ta dago a hankali. Suraiyya ta gani ta mike da sauri tana fadin

“Maman hudu!”

“Bama biyu ba. Ki rufan asiri”

“Kai ni bana son langwai Sister!”

“Zakiga bakya son Langwai Allah nunan lokacin ki.”

Dariya tayi tace

“Ina Yaa Kamal?”

“Yana falo.”

“Bari naje!”

Ta fada tana fita. Mikewa suraiyya tayi tabi bayan ta. A falo ta tadda ta suna magana da Kamal. Can ta mike ta shiga kitchen ta kawo musu kulli dayan nama da lemo. tace

“Abinci a kawo nan ko zaku hau sama.”

“Ni naci wannan ai na koshi sai dai ko ita?”

Ya fada tana nuna ta.

“Gaskiya a raba ta gida uku a bani kaso biyu ka dau daya dan ni rabi tai min kadan!”

Ido Fateema ta zaro tace

“Kan uban can yaushe kika zama rumbu kace in zan zo gdn ki nayo guzurin kayan dadi na baza ki barni na taba naki ba.”

Ta fada tana rike haba.

STORY CONTINUES BELOW

“Gwara da tayi a gaban ki kika gani da dai tace sharri nai mata. Komai sai an raba uku taci biyu ta bar min daya dayan nawa ma tare muke cinyewa. Ke buhun shinkafa a kwanaki yake karewa.”

Duka Suraiyya ta kai masa tana fadin

“Kai Sweet sharri ina zan kai buhun shinkafa.”

Fateema tayi dariya tace

“Cikin ki. Anya ba yan hudu zaki haifa ba.”

“Dan Allah Sis ki rufa min asiri man.”

Suraiyya ta fada.

Momy ce ta sauko duk sukai shiru  gaisawa sukai momy tace

“Ku taso muci abinci.”

Da sauri Suraiyya ta mike tace

“Wallahi yunwa nake ji daman.”

Ta nufi dining.

Fateema ta mike ta bita tana dariya. Serving nata tayi ta fara ci itama ta zuba taci kadan. Sai da Suraiyya tayi dadi biyu sannan ta koshi ta tashi da kyar ta koma falo. A kasa ta zauna ta mike kafa tace

“Sis help me please!”

“Dame?”

“Massage!”

Ido ta zaro tace

“Ni kuma haba shi yai miki manan.”

Momy,  Suraiyya ta kalla sannan ta harare ta tace

“Please.”

“Gaskiya sai an biyani dan ba a aikin banza yanzu.”

“Nawa zamu naki naira asihirin.”

Yaa Kamal ya fada.

“Kai Yaa Kamal kar kasa na fasa.”

Ta fada tana saukowa ta farai mata tana fadin

“Gaskiya kizo wani satin nayi miki sceening kinga cikin ki kuwa wata bakwai fa.”

“Nima dai haka nace. Zan shigo da yamma.”

“Kambu dan kisa kar na dawo gida da wuri kawai kizo da safe mu gama abinda zamuyi mu taho gida.”

“To zan duba.”

“Au zaki duba. Ko gida zan zo nai miki?”

“Da kuwa kin kyauta.”

“Ai fa sai kinzo wai ni kuwa kina exericse?”

“Ina tabawa.”

“Gaskiya Sis kina yi dan zai taimaka sosai da sosai.”

“Insha Allah.”

“Kaga su Doctor!”

Yaa Kamal ya fada. Tace

“Kwarai kuwa kana zazzabi allura zan maka ba magani ba dan kaji.”

“Ba sai kiyi ba.”

“Ba fata ba amman zaka zo da kafar ka ai.”

“Ni ban san meyasa ma na yadda kikai min ba. Salon naje a zurmukan a wani waje.”

Tayi dariya tace

“Ba zan magana ba Yaya.”

Sukai dariya duk kan su. Sai karfe goma suka bar gidan. Har bakin mota Fateema ta bisu tana musu tsiya. Sai da suka tafi sannan ta juyo. A falo ta zauna tana kallo. Wajen goma da rabi Momy ta mike ta rufe kofa tace

“Ni na tafi bacci zanyi.”

“Sai da safe!”

“Allah bamu alheri.”

“Amin.”

Momy tayi sama ita kuma ta cigaba da kallo. Wayar ta ce ta hau kara tana dubawa taga bakuwar number. Kin dauka tayi. Kara kira akayi wannan ma taki dauka ganin an kira sau uku yasa ta dauka ta kai kunnen ta tana yin sallama.

“Wa’alaikum salam Gimbiyya ina fatan dai ba bacci kike ba!”

“Waye?”

Ta fada.

“Haba Dr haka kike bamu gaisa ba fa.”

Shiru tayi yace

“To ina yini?”

“Lafiya lou wa kake nema?”

“Doctor nake nema!”

“Ai doctor waya garesu wacce a ciki?”

“Doctor Fateema!”

“How may i help you?”

“Just call to hear your sweet voice before going to bed. I love you Fateema. Gud Nyt Sweet dream Love!”

Yana fadin haka ya katse wayar yana murmushi. Wayar tabi da kallon mamaki sai kawai ta ajiye wayar tana fadin

“Waye wannan a ina ya samu number ta?”

Tsaki ta saki ta maida kanta kallon da take amman sai taji duk ya fita a ranta mikewa tayi ya kashe wutar dakin sannan ta wuce dakin ta. Kan gado ta hau ta kwanta ta lumshe idon ta tana addu’a.

*

Tin asuba da ta tashi bata koma bacci ba dan yau tana da aiki sosai a asibiti yadda weekend din nan bata leka ba. Tana idar da azkhar ta mike ta fara gyara gida tana gamawa ta daurawa Momy abin kari dan ita azumi takeyi.

Tana cikin hada mata break Momy ta shigo kitchen din. Har kasa ta durkusa ta gaishe ta. Ta amsa tana fadin

“Ashe har kin tashi?”

“Eh Momy kinsan yau Monday!”

“Haka ne sannu Allah yay albarka.”

“Amin Momy nagode!”

Ta fita ta jere kayan akan dining sanna ta wuce dakin ta. Wanka tayi ta fito ta goge jikin ta da towel ta shafa mai sannan ta shafe jikin ta da humra ta saka sure ta bude wardrobe. Wata doguwar riga ta zaro maroon kala mai golding kalar stones.b

Skintie ta dauko da under wear ta saka. Sannan ta daura Rigar. Karamin hijab brown colour ta dauka ta saka ya tsaya mata a kafada sai brown cover shoe da ta saka mai maroon stone da jakar sa ta dauka ta fesa turare ta fito rike da wayar ta da keyn motar ta.

A dining ta samu Momy itama tayi wanka tana karyawa. Karasawa tayi tace

“Momy na fito zan tafi!”

“To Fateema Allah ya tsare ya bada sa’a a kiyaye mutunci dai.”

“Insha Allahu Momy nagode!”

Ta juya ta fice a falon Momy na mata addu’a ta amsa da Amin. Tana fita ta nufi motar ta ta shiga.

Tana zuwa bakin gate ta danna horn mai gadi ya mike ya leko yana ganin Fateema ce ya koma a guje ya bude mata gate din. Ciki ta shiva da adsu’a dauke a bakin ta ta nufi inda take parking tai parking sannan ta fito.

Mai gadi na rufe gate ya karaso yana fadin

“Barka da saiyya Hajiya!”

“Barka kadai Baba ka tashi lafiya ya aiki?”

“Alhamdulillah!”

“Allah taimaka!”

“Amin nagode!”

Tayi ciki nan ta dinga gaisawa da staff din wajen cikin sakin fuska da girmamawa a haka ta shige office din ta. Yana nan a gyare sai tashin kamshi yake kan kujerar ta ta isa ta zauna ta ajiye jakar hannun ta sannan ta jawo file din dake ajiye a gaban ta.

Na patients din ta ne da ta kwantar budewa tayi tana duba yadda akai treating nasu a weekend da komai da komai ta jima tana duba files din nata sannan ta mike ta dauki file din guda biyar ta fita dan yin round.Ta dawo office din nata bandaki ta shiga ta dauro alwala tazo inda take sallah ta shinfidda sallaya ta tada sallar walha raka’a hudu tayi ta sallame ta zauna tana adddu’a. Karfe sha biyu ta mike ta ninke sallayar sannan ta koma ta zauna akan kujerar ta.

Wayar ta dake office din ta dauka ta fara kira. Ana dauka tace

“Bring the files!”

Ta kashe wayar ba ai minti biyar ba ta shigo dakin da files a hannun ta.

“Dr Gasu!”

Ta ajiye akan table din dake gaban ta.

“Mutum nawa zan gani ne?”

“Mutane goma sha daya ne!”

“Sha daya kuma tayaya akai suka haura goma bayan nace kada suna haura goma.”

“Dr wani ne yazo ya dinga magiya wai a taimaka a bashi yau ya ganki shiyasa.”

“Shikenan.”

Ta dauki files din farko tace

“Ki tabbata masu zuwa su shigo a yadda files din yake please!”

“Insha Allahu!”

Nan ta fara ganin patient din da sukai booking ganin ta dan ranar monday sabbin patient take dauka ranar talata kuma masu appointment wanda ta duba zasu dawo laraba ma haka alhamis ma sabbi jumma’a bata duba marasa lafiya sai dai in ita ta ga dama ta baka lokaci.

Kan karfe daya da rabi har ta duba mutum hudu dan haka ta dakatar dan zatai sallah. Sallah tayi ta zauna tai addu’a. Sai biyu ta dawo ta daura daga duba patient din nata.

Karfe uku da rabi ta kara dakatar da masu ganin ta shima dan zatai sallah. Sai da tayi sallah tayi azkhar sannan ta daura akan files din da suka rage guda uku. Na farko ya shigo baiyi thirty minute ba ya fita sai na biyun karshe da ya shigo shine suka dau thirty minute yana mata bayani ta bashi test tace ya dawo ranar laraba.

File na karshe ne a gaban ta lokacin biyar har tayi ta gama yin likis dan gajiya taji wayar ta ta dauki kara dauka tayi  tana duba wake kira. Nusaiba ce dan haka ta saki murmushi tayi sallama. Bayan ta amsa tace

“Nusy nah!”

“Na’am Anty na ina yini ya gida da Momy da aiki?”

“Alhamdulilah aiki gashi har yanzu ban koma gida ba.”

“Haba ai na zata kin koma shiyasa na kira!”

“No sauran patient daya daga shi zan tafi gida.”

“Ok bari na barki in kin koma gida mayi waya.”

“To nagode Nusy agaida Mami!”

“Zataji!”

Ta kashe waya. Waya ta dauka tace

“Next!”

Nan akai sallama. Kan ta na kan file din bata dago ba ta amsa sallamar. Kan ta dago ta kara jin wata sallamar amman ita muryar namiji ne. Dagowa tayi jin muryar very familiar.

Tana dagowa suka hada ido dashi da sauri ta dauke kanta. Sanye yake da Brown kalar suit tai masa kyau sosai kafar sa sanye da sau ciki baki sai necktie maroon kala awuyan sa. Idon sa sanye da farin glass yai masa kyau kan kace me kamshin sa ya cika office din.

Duk da taji muryar mace kuma tana gaban sa amman da ta dago bata lura da ita ba kawai Aslam ta gani. Aslam ne ya kalli Jiddah yace

“Bismillah muje!”

STORY CONTINUES BELOW

Kallon sa tayi ta sakar mata murmushi ya gyada mata kai. Takawa tayi a hankali har suka karaso gaban table din nata. Dagowa tayi ta sauke kan ta akan Jiddah ta dan saki murmushi ta nuna mata kujera tace

“Have a sit!”

Zama tayi shi kam kan ta kalle shi ma ya zauna dan yasan ba lallai ta kalle shin ba. Ai kuwa. Bayan ta zauna tace

“Sannu!”

Jiddah itama ta saki fuska tana murmushi tace

“Yauwah sannu ina yini ya aiki?”

“Alhamdulillah kece ba lafiya?”

Kallon Aslam Jidda tayi shima ya kalle ta ya saki murmushi yace

“Eh to gashi nan dai dukkan m za a duba.”

Dagowa tayi ta kalli Jidda tace

“Ina jinki!”

Taki yadda ta kalli shi,  shi kuwa ya zuba mata ido yana sakin wani murmushi.

Shiru Jidda tayi tace

“Wanene wannan? Ko zai bamu waje ne?”

Kai Jidda ta girgiza tace

“No ya zauna ai miji na!”

Gaban Fateema ne ya fadi amman ta dake tace

“Me yake damun ki?”

“Akan matsalar rashin haihuwa ne!”

Kai Fateema ta gyada tace

“Ina sauraren ki. Menene matsalar.”

“Munyi aure more than eight years but ban taba ko barin wata ba.”

Jingina Fateema tayi da kujera tace

“Did you treat on some medicine?”

“No!”

“Kina yin al’ada?”

“Yes!”

“Kina da wata matsala ta rashin ganin al’ada abaya kan kiyi auren ko bayan kinyi?”

“Eh toh farkon auren mu na samu wannan matsalar dan da ina kwana biyar sai ya dawon kwana uku kan ya dawo kwana ukun yai min wasa ma.”

Shiru Fateema tayi tace

“Ba zai iya bamu waje ba kuwa?”

“Dr in abun nan ya kama fa har ni sai an tambaya aka sani ko matsalar dagani ne!”

Aslam ya fada yana sakin wani murmushi.

Kai Jidda ta gyada tace

“Gaskiya dai!”

Kafada Fateema ta dan daga tace

“Ina son ki ban amsa da zan miki tsakani da Allah in kina son na gano matsalar!”

“Insha Allahu Dr!”

“Alright before you marry ko after kin taba yin planning?”

A zabure ta dago tana kallon Fateema sai kuma tayi kasa da kai. Kallon ta Fateema ta tsaya yi shima Aslam haka.

Dan murmushi Fateema tayi tace

“Uhmm ina jinki?”

“Dr uhm daman….”

Sai tayi shiru.

“Don’t feel shy or something else sister matsala ake so a gano da bakin zaren in kin taba ki fada min ba wata matsa akwai abinda zan zauna in gani ne?”

Kan ta a kasa tace

“Eh nayi allura kafin bikin mu bayan bikin mu da wata uku na kuma yi?”

“Alright!”

Fateema tayi rubuce rubuce a file. Aslam kuwa in banda kallon Jidda ba abinda yake akan me tayi plannig dan me bada sanin sa ba saboda bata son ta hada jini dashi ko saboda me?”

Dagowa Fateema tayi ta kalle ta tace

“Kan na tabbatar da matsalar zan baku test ke dashi kila ku samu gobe zuwa jibi sai kuzo naga result din!”

Ta rubuta musu test din ta basu sannan tace

“Shikenan”

Amsa Jidda tayi tace

“Mungode!”

Sannan ta mike ta fita. A hankali Aslam ya mike. Fateema da ta lura da sauyawar sa tin maganar da Jiddah tayi  tace

“Kayi hakuri kasan mu mata wani lokacin sai ana hakuri damu.”

Juyowa yayi ya kalle ta sai ya sakar mata murmushi yace

“Thanks you Dr!”

Ya juya ya fita. Tausayi ya bata dan taga daga lokacin da Jiddah tace tayi allura sau biyu duk ya shiga tashin hankali. Kai ta giggiza yace

“Ko me yasa zatai planning ba da sanin mijin ta ba. Allah kyauta.”

Ta kalli agogo taga 5:57pm da sauri ta mike dan har an kusa shan ruwa kenan shida saura tana office. Jakar ta dauka ta fita ta kulle office din. Gun motar ta ta shiga ta tada tana zuwa bakin gate mai gadi ya hau mata addu’a. Jakar ta ta bude ta dauki 500 ta mika masa tace

“Sai gobe Baba!”

STORY CONTINUES BELOW

Kamar yai sujadda haka ya dinga mata godiya sannan ta fice. Tana daga masa hannu.

*

**

***

****

*****

******

*******

A hankali ta bude idon ta ta sauke kanta kasa. Hannun ta dake rike da nashi ta yi kokarin kwacewa amman ta gagara, ta sa daya hannun da niyar kwacewa amma sai taji jikinsa ya yi zafi kamar wuta, sai lokacin ta lura da cewa zafin jikinsa ya yi yawa. Ta kuma tuno da mafarkin ta na jiya. Da sauri ta dago takai hannun goshinsa, kamar zatai kuka tace

“Yaa AK jikin ka xafi. innalillahi! ina ruwa da tawul ?’’

Xata mike ya janyo ta tayo kansa. Ido ta zaro kan ta farga sai ganin ta tayi akan sa kwance. Jikin tane ya fara rawa. Tana kokarin sauka akan sa ya kara rike ta kam.

” jikin ka zafi ka bari a saka maka ruwa!”

“Aysher wannan zafin ba wani zafi bane akan wanda nake ji a cikin zuciya ta….”

*

Dagowa tayi da sauri tare da zaro Ido,  kai ya gyada mata.

“Duk abinda nake ji bakui san wanda nake ji a cikin ziciya ta,  ta ninka shi ba.”

“Naji yanzu ka tsaya a rage maka zafin jikin dan Allah!”

Sakin ta yayi ta mike daga jikin sa a hankali tana kallon kasa. Bandaki ta shiga ta debo ruwa a cikin bowl ta dauko towel a hannun ta.

Zama tayi rike da bowl din ta saka towel din ta jika towel din ta matse sannan ta manna masa a goshi da sauri ya bude idon sa da ya kada yai jajir. Kallon juna suka tsaya. Can ta dauke kanta ta kara jikawa ta kara daurawa a goshin sa kansa da wuya da kuma hannayensa, tana yi tana fadin

“sannu Yaa Ak!”

   

Duk da tana saka masa ruwan amman kamar zafi take karawa jikin nasa wannan ya bata tsoro ta cigaba da yi. Kofar dakin aka bude Maryama ce. Aisha ta kalle ta da sauri tace

“Dan Allah a kira Doctor jikin sa zafi sosai.”

Fita Maryama tayi da sauri ba a dade ba suka shigo dakin ita da Doctor. Mikewa tayi ta ajiye bowl din hannun ta tace

“Doctor ka taimaka masa jikin sa zafi kamar wuta.”

“Cool down Madam ai kin riga kin bashi taimakon da yake bukata.”

Allura yai masa sannan yace

“In ya samu bacci ya huta insha Allahu zai sauka.”

   

Zama tayi ta zuba tagumi Ta zura masa ido cikin tausayawa ta ce, ‘’sannu Yaa AK sannu Allah ba ka lafiya’’

Kallon ta kawai yake kamar ya sace ta ya boye, a cikin ransa yake fadin

“ya Allah har yau na kasa gane wani irin abu ne haka da nake ji game da wannan baiwar taka, wani abu mai karfi, haka wani abu mai zafi da sanyi, wani abu mai dadi da wuya. Ya Allah ka bar ni da wannan baiwar taka cikin ikon ka da isarka, ya Allah ka bar ni da wannan kauna da nake ji game da baiwar taka.”

Haka ya dinga sumbatu a cikin zuciyar sa. Tun yana kallon ta dishi-dishir har ya daina saboda allurar da aka masa ta sa shi bacci, bacci mai nauyi ya dauke shi.

Hawaye ke tsere a fuskar Aisha, Maryama ta zauna a gefen ta tana lalashin ta. Mamah da Mai marya ne suka shigo duk sukayi kan Aliyu dake Bacci. Sheshekar kukan Aisha sukaji wannan yasa suka juyo. Mama tayo wajen ta tana lallashin ta ita ma.

“Menene na kukan Aisha Addu’a zaki tayi masa Allah tashi kafadun sa kinji.”

Kai ta gyada. Mama ta rumgume ta tana shafa bayan ta.

Dai dai lokacin aka budo kofar dakin. Hajara ce. Kallon yan dakin ta farayi daya bayan daya kan idon ta ya sauka kan Aisha dake kwance a jikin Mama na sheshekar kuka. Mamah na shafa bayan ta.

Wani abu taji ya tokare mata ta juya kawai ta fita. Falo ta zauna tana tunanin wacece wannan kuma. Ita sam bata san ta ba a yan gidan su. Sai dai tana ganin kama kamar da Mamah da yarinyar.

Suna zaune Yaa Abubakar da Yaa Usman suka shigo dakin da sallama. Abba dake zaune gefen gadon ya dago yana amsa sallamar su. A kasa suka zube suna gaishe shi. Abba ya amsa sukai masa ya me jiki sannan suka gaida Mamah.

Kan gadon suka nufa suna kallon dan uwan nasu. Sallamar Umar da Farouk ne ya yasa su Mamah kallon kofa.

Bayan sun gaisa Yaa Abubakar yace

“Abbah munzo mu tafi ne na samar mana flight din na yamma zamu hau.”

“Alright yanzu zamu tafi can kenan ko?”

“Eh!”

“To shikenan. Maryama hadawa Yayan naki wasu kayan sa da wayoyin sa.”

Mamah ta mike rike da Aisha suka sauka Falo.

A falo ta zaunar da ita tai mata nasiha mai ratsa jiki sannan tace

“Yau zamu tafi Egypt muna bukatar addu’ar ki Allah bawa Aliyu lafiya.”

“Amin Mamah. Allah ya kaiku ya dawo daku lafiya. Allah yasa kuje a sa’a.”

Ta fada tana goge hawayen idon ta.

“Amin Aisha ki daina kuka kinji.”

Kai ta gyada mata sannan ta mike tace

“Zan tafi gida sai anjima.”

“Mungode. Ki gaida mutan gidan!”

“Zasu ji.”

Ta fita a falon. Maigadi ta gani ya kalle ta yace

“Har kin fito?”

Kai ta gyada masa tayi waje kawai. Da ido ya bita da kallo yana girgiza kan sa da tunanin wani abu a cikin ransa. Dan ko makaho ya shafa zai gane me ke tsakanin Aisha da Aliyu indai yagan su.Aisha na isa gida ba kowa har Umma ma ta shiga makwabta. Tunda da ta yi sallar la’asar tana kwance a wurin ta rasa me ke mata dadi, komai ya cushe mata, ta rasa ma me take so, meye ba ta so. Amma tabbas rashin lafiyar Yaa AK ya daga mata hankali sosai, kanta ya dau zafi ta kasa zaune da tsaye.+

Tana cikin wannan halin Yaa Muhammad ya dawo yayi sallama, tana daga daki ta amsa dan haka yayo dakin. Dagowa tayi suka hada ido ta mai da kan ta kasa. Shiga yayi ya zauna a kasa yana kallon ta can yace

“Aisha lafiya?”

Fuska ta shagwabe tayi shiru yace

“Fada min me yake damun ki Kanwata”

“Ba komai fa gidan ne ba dadi ni kadai. Duk wani tunani na hawa kai na wanda bana so.”

Murmushi yayi yace

“To meyasa ba ki bi ta ko kin fita wurin kawayenki, ga islamiyya ma me ya sa baki je ba ?’’

Da sauri ta dago dan yau ta manta da wata isilamiyya duk son zuwa da takeyi. Shiru tayi can tace

“Yaya ban san me yake damuna ba komai ya tsaya min.”

“To yanzu me kika so?”

“Ka zauna kai min hira mai dadi ko naji sanyi.”

Ta fada idon ta na cikowa da kwalla tana tunanin yanzu a wane hali Yaa AK yake. Shin ta masa adalci kenan ita tana da me debe mata kewa amman shi yana can a wani hali.

A wayance tasa hannu ta maida kwallar sannan ta dago. Duk da ya gani ya dauke kai yace

“My Aisha! My Daru girl!”

Baki ta turo,  yaja hancin ta yai murmushi yace

“Komai ya kusan zuwa Karshe kanwata sauran kwana nawa na zama angon Aisha ki kwantar da hankalin ki kinji. Amman kuma Aisha wani lokacin wani tunani na hawa kai na…”

“Wane irin tunani?”

“Yaya Kanwata zata kallen in munyi aure kullum Yaya! Yaya a lokacin fa zan canja daga Yaya na koma…!”

Ido ta rufe da hannayen ta tace

“Ai Yaya ba zaka taba tashi daga wannan Yayan nawa ba. Matsayin ka yawa garesu a guna. Tamkar Abbah na kake kuma tamkar Mamah ta kake haka nan Yaya nane kuma Miji na dan haka ni ba zaka taba tashi daga Yaya na ba. Sai dai a ko wanne lokaci da matsayin ka. Ina son ka Yaya na.”

Ta fada hawaye na zubo mata. Kallon ta ya tsaya yace

“Why crying?”

“Kukan farin ciki nake na kusan zama mallakin Yayana.”

“Kin tabbata!”

Kai tayi kasa dashi. Yai murmushi yace

“Ina so ki Aisha amman ki sani son da nake miki ba zai sa naki baki dama samun farin cikin ki da cikar burin ki ba. In har Allah ya kaimu mukai aure a lokacin zan nuna miki wata soyayyar ta daban Aisha wanda sai lokacin zaki ganta ki san kuma wane irin so nake miki.”

Hannu yasa ya dago kanta yace

“Fada min ke kuma fa? Kina bukatar hakan?”

Ya tsura mata idon. Dan murmushi ta saki ta kau da kanta

“Me kake nufi Yaya na. Komai kake so nima ina so.”

“Kina so na kamar da?”

Da sauri ta dago dan ta girgiza da tambayar tasa. Kallon ta yake kai ta dauke tace

“wannan wane irin tambaya ce Yaya?”

Ya tsare ta da ido, yace

“Eh ai gara in kara tabbatar wa kar inje kin rage so na ba kamar daba. Kinsan ni a duniya ban da kamar ki.”

STORY CONTINUES BELOW

Kallon sa tayi jiki a sanyaye ta ce,

“Me zai canja daga son da nake maka Yaya na. Son ka a jinin jiki na yake. Amman tabbatar wa ai an kusa a daura mana aure anan zaka gane komai.”

Tana fadar haka idon ta ya kawo ruwa. Kanta ya dago yaga ni nan hankalinsa a tashi yakira sunnan ta. Yace

“Aisha!”

Shiru tayi ya kara cewa

“Aisha!”

“Uhmm!”

“Kuka kuma kukan menene?”

Kai ta girgiza kai, tace

“Ba komai Yaya na!”

“Akwai Aisha me ya kawo kuka yanzu kamata yayi kiyi  farin ciki ba kuka ba.”

“Haka ne Yaya na amman ai ana hawayen farin ciki ko?”

Kai ya gyada tace

“To in shi nake fa?”

Yace

“Zan fi son dariyar ki a madadin sa.”

Shiru tayi yace

“Abun na dauren kai Aisha yadda yanzu kika canja bakya gajiya da kuka ki fada min kukan na menene?”

“In nace zan fada maka kukan menene a yanzu nayi karya abinda na sani kawai shine tambayar ka batai min dadi ba. Wai ina son ka kamar da in ban so ka ba wa zan so? Kenan baka yadda ina son ka ba ko me?”

   

“No Aisha kada kiyi min wannan fahimtar mana. akwai sabo, akwai kauna wanda muke gani kamar so ne, ta yiwu saboda shakuwar da muka yi da ke ki dauka so ne mu yi aure a kan haka.

Aisha ina son ki da farin cikin ki, duk abinda da kike so yana da matukar mahimmanci a wurina, don haka ban so ki auri wanda ba kya so. Ba na so ki aure ni don ni yayanki ne kin saba da ni a matsayina na yayanki. Ya na da matukar mahimmanci in ga kin yi aure a inda kike so. Ina so ki auri wanda zuciyarki take so.”

Gaban ta taji ya fadi. A ranta tace

“Kar dai Yaya ya gano ni”

A fili kuma murmushi tayi tace

“Yaya kada ka manta sabo da kauna suke haifar da so. Kuma kauna tafi so tasiri. Dan inda ba kauna ba za a samu so ba. Yaya na kasan ni kasan me nake so me nake ra’ayi da buri.”

“Na sani Aisha, Amman ki sani rayuwar aure daban rayuwar da muke yanzu daban. Ban so na cutar dake ko na tauye miki hakki.”

“Ina son ka ina kaunar ka. Amma me ya kawo wadan nan abubuwan!”

“Saboda aure zamuyi mu kara fahimtar juna Aisha kar abu yazo ya baci daga baya ina iya sadaukar da rayuwa ta da farin ciki na gareki.”

“Na sani Yaya shiyasa nima nake so na mallaka  maka komai nawa. Dan ka cacaci haka”

“Allah bar ni da ke Aisha. Allah ya cika mana burin mu”

“Amin Yaya na.”

Ya mike yace

“Wa yaga Muhammad ya zama angon Aisha. Muyi baccin mu tare wanka tare koma…”

Kunya ta sa ta fada kan gado ta rufe fuskar ta da pillow. Tana cilcilla kafa tana fadin

“Kaga Yaya bana so.”

Muhammad shi kuwa ba abinda yake sai dariya yana dada tsokanar ta Can ya mike ya fita. Gyara kwanciyya tayi ta daura hannu akan zuciyar ta tana fadin

“Kayi min nisa Yaa AK amman ka sani kana kusa da zuciyata. I miss u i will continue to miss u till my last breath. Love u Yaa AK. Allah ya baka lafiya. Ya sa haka shine mafi alheri.”

Ta fada tana fadin

“Ko sun sauka?”

Sai kuma ta lumshe ido tana fadin

“Ina ma yaa AK ne Yaa Muhammad. Da wane farin ciki da dadi zanji?”

Ta fada tana cije baki. Kiran sallah magariba da ta jiyo yasa ta mike ta fita dan dauro alwala.

Umma ta sama tana kwashe abinci. Tace

“Umma kin dawo?”

“Na dawo ina kika je kika zauna.”

“Wallahi Umma karatu mukai kinsan gobe akwai jarabawa.”

“Amman ai sai da nace kada ki dade ko?”

“Kiyi hakuri!”

“Shikenan!”

Ta wuce ta dauro alwala ta fito ta shige daki. Umma ta bita da kallo. Kan sallaya ta hau bayan ta idar duk addu’ar ta ta lokacin ta Yaa AK ce akan Allah ya bashi lafiya.

STORY CONTINUES BELOW

Tana zaune akai isha’i ta mike tayi nan ma yasha addu’a. Zama tayi ta zuba ta gumi sai ta tuna statement din sa da yake fadin

_””Ki kwantar da hankalin ki Aysher ni dai fata na ki gama jarabawa ki samu sakamako mai kyau ko ina da rai ko ban da rai zanji dadi nayi alfahari dake kuma zan bar wasiya ko na mutu a tsaya miki sai kin gama karatun ki. Ina fatan zaki bani hadin kai Aysher!”_

Hawaye ne ya zubo a idon ta tana fadin

“Bazaka mutu ba Yaa AK har sai kaga cikar burin ka akai na.”

Umma ce ta leko tace

“Ki fito ki zuba abinci kici!”

Ganin hawaye a idon ta yasa ta shigo daki da sauri. Hannu Aisha ta saka tana goge hawayen idon nata.

“Lafiya?”

Kai ta girgiza kawai.

“Bazaki fadan kukan me kike ba?”

“Nifa ba komai Umma!”

Durkusawa tayi tace

“Aisha in tambaye ki?”

Kai ta gyada sannan Umma tace

*”Wa kike so?”*

Zabura Aisha tayi ta dago da sauri tace

“Umma kamar ya *wa nake so?* “

“Eh kwanaki na fada miki kiyi nazari da tunani ki gane wa kike so?”

“Umma ni Yaa Muhammad nake so!”

Ta fada tana yin kasa da kanta. Mikewa Umma tayi tace

“Ba a karyar So Aisha kuma ko anyi sai an gane gaskiya alamarin.”

Tana fadar  haka ta fice a dakin. Hannu Aisha ta daura akan kirjin ta tana dafewa. Can ta saki ajiyar zuciya. Mikewa tayi ta dauki jakar makarantar ta ta dauki littafi ta fara karatu ba dan komai ba sai dan cikar burin Yaa AK.

Yaa Muhammad ne ya shigo ya kalli Umma yace

“Ina Aisha ne?”

“Tana daki!”

“Taci abinci!”

“A’ah!

Juyawa yayi ya fita bai jima ba ya dawo da leda a hannun sa guda biyu. Daya ya ajiye Umma daya yayi dakin Aisha da ita. Yana shiga ta dago yace

“Ana karatune?”

Kai ta gyada ya ajiye mata ledar hannun sa yace

“To kici wannan ba yawa.”

Murmushi ta saki tace

“Nagode Yaya na.”

Ya juya ya fita. Ledar taja taga fura ce sai nama a ciki dauka tayi ta fara shan furar ta dauki naman kenan ta kai baki taci daya,  biyu,  uku sai Yaa AK ya fado mata. Hannu ta zare a ciki tana tunanin to shi yaci abinci. Ji tayi ya fita aranta. Cikin ta ne yai kogi dan rabon ta da abinci tin safe shima kadan taci. Ido ta runtse ta zuke furar da take sha ta sauke ta ajiye robar.

“Allah yasa kaci abinci Yaa AK!”

Ta fada tana kulle ledar naman ta ajiye ta nan. Kan gado ta kwanta ta lulluba tana tunanin sa tana tuna bayanin sa tamike ta dauki littafi tana karatu. Tana cikin karatun zata fada tunanin da ta fara in ta tuna statement din sa sai ta dawo kan karatun nata. A haka ta gama da kyar ta ajiye tayo alwala tazo ta hau kan sallaya. Ranar kwana tayi yiwa Yaa AK addu’a Allah ya bashi lafiya.

*

*

*

Har aka fitar dashi daga gidan bacci yake kamar gawa haka aka saka shi a mota. A baya aka kwantar dashi. Tsakiya Mama da Maryama da Hajara. a gaba kuma Abbah da Yaa Abubakar.

Bayan su Yaa Usman ne da Umar da Farouk sai tawagar mai martaba masu bashi tsaro. Masu aikin gidan kuwa jikin su yai masukar sanyi ganin yadda aka fita da Aliyu kamar gawa. Duk addu’a suke Allah ya sauke su lafiya ya bashi lafiya.

Suna isa airport jirgi suka shiga suka daga kasar Egypt a cikin jirgi ya farka. Yana bude ido yace

“Aysher!”

Abbah dake gefen sa ya matsa yace

“Ka tashi Aliyu?”

Kai ya gyada yace

“Abba ina Aysher?”

“Wacce Aisha?”

“Yarinyar da tazo dazu dan Allah kada kace min mafarki nayi Abbah!”

“Oh ai kafin mu taho ma ta tafi Aliyu tana can gida menene?”

“Abbah ina son naganta yanzu ku kira min ita dan Allah!”

“Aliyu kasan a ina muke yanzu?”

Cikin jirgin ya fara bi da kallo wannan yasa ya fara kokarin mikewa zaune. Abba ya gyara masa kwanciyya yace

“Sannu!”

Ido Aliyu ya runtse yace

“Meyasa kuka baro ni da garin da Aysher take Abbah ni ku maidani in mutu a binne ni a garin da Aysher take!”

Mamah ce ta karaso tace

“Lafiya Aliyu?”

“Mama ku kira min Aysher dan Allah ku kira min ita.”

Maryama ce ta zauna a gefen sa tace

“Yaya zata zo daga baya ai ka kwantar da hankalin ka kaji.”

“Da gaske kike Maryama?”

Kai ta gyada ya rumgume ta yace

“Thanks you sister!”

“Sannu Yaya!”

Kai ya gyada mata kawai ya koma ya kwanta yana mai lumshe ido. Tin daga lokacin bai kuma magana ko bude ido ba. Dan sun zata ma bacci yake amman idon sa biyu shi kadai yasan me yake ji a zuciyar sa.

Suna zuwa asibitin da Abbah yai musu booking suka zo suka dauke su daki aka bashi aka fara bashi kulawa ta musamman kafin likita yazo ya fara dubashi. Duk da jikin sa yai zafi sosai. Su Abbah ba su bar asibitin ba sai da suka ga ya samu bacci sosai sannan suka tafi.

*

Maryam ce zaune a dakin da aka bata a kasar wayar Yayan ta ta kunna bayan ta saka a charge. Bata jima da kunnawa ba aka kira wayar.  _Faisal_ taga an rubuta akan screen din dauka tayi kan tai sallama taji yace

“Guy tinda na jika shiru Aisha ta amshi soyayyar ka ko?”

“Bashi bane!”

Maryama ta fada.

“Oh am sorry yana ina?”

“Yaa Aliyu ba lafiya yau muka sauka a kasar Egypt yana asibiti a kwance!”

Ta fada hawaye na zubo mata. Cikin firgita yace

“Ya salam since when?”

“Muma jiya mukaje muka same shi a haka yau muka taho asibitin!”

“Ya Allahu Allah ya bashi lafiya insha Allahu zan shigo zuwa jibi Allah ya bashi lafiya.”

“Amin nagode!”

Ta ajiye wayar tana share hawayen idon ta.

“Shin wai me yake damun Yaya gaba daya?”

Abinda take son taji kenan. Wanka tayi tazo ta tada sallah sannan ta fita. A falo ta samu Mamah da Mai martaba suna cin abinci amman da ka kalle su zaka san ci kawai suke yi.

Zama tayi ta hada tea kadai ta sha. Mamah tace

“Kije ki kaiwa Antyn ki abinci bata fito ba.”

Dibar mata tayi ta kai mata. Bata dakin tana toilet dan haka ta ajiye kawai ta fito. Suna zaune su Yaa Abubakar,  Yaa Usaman da Yaa Umar da Farouk suka shigo sun dawo daga asibiti wajen Aliyu.

Zama sukai kowa ya fara cin abinci amman da ka kalle su zaka san basa cikin nutsuwar su kowa damuwar sa Aliyu meyake damun sa.

*GWS ALIYU*Washegari tin safe suka tafi asibiti amman lokacin ko tashi Aliyu ma bai ba. Sai wajen sha daya ya tashi nurses ne duk suka kula dashi yai wanka suka bashi abinci kinci yayi wannan yasa suka saka masa ruwa. Sai karfe sha biyu sannan likitan da zai duba shi ya karaso. Daukar sa sukai suka shiga dashi daki. Dakin duk computers ne. Cikin wani engine suka zura shi sannan sukai swithing nashi. Likito sun fi biyar akan sa kowa akwai record din da yake gani daga computer dan tana yi tana printing out result din. Sunfi awa biyu akan sa sannan suka fito dashi aka maidashi dakin sa.+

Su Abbah suka shiga kallon su yayi da ido dan ko magana ya kasayi. Abinda ya tsinkar da Mamah kenan ta dinga kuka su Yaa Abubakar sukai ta lalabin ta da bata baki.

Hannu Aliyu ya daga ya kama nata sai ya lumshe ido. A haka bacci ya dauke shi. Zama Mamah tayi tana tofa masa addu’a sannan tace

“Alhaji gaskiya ya kamata a hada na da hausa kar naje jefe min shi sukai.”

“Ki kwantar da hankalin ki Aliyu yana tare da kariyar Allah insha Allahu amman za ayi abinda kike so ki daina saka damuwa kinga kema kin tsufa yanzu wani abu sai ya faru ai.”

“Kai ma kasan dole na damu Alhaji kalli fa yadda Aliyu ya dawo.”

Ta fada tana rike kanta tana mai hawaye. Maryama ce ta dafa ta tace

“Insha Allahu Yaa Aliyu zai ji sauki da izinin Allah dan haka ki daina kuka Mamah.”

Rumgume Maryama tayi. Ita kanta Maryaman da da hali kukan take so tayi amnan kawai ta danne take lallashin Mamahn tata.

*

*

*

Aisha kuwa ko a makaranta da ta shiga exam hall kasa komai tayi ta zubawa papper gaban ta ido sai hawaye. Can ta saka hannu ta goge tana mai kara tuna maganar Yaa AK da ta tsaya mata a rai.

_”Ki kwantar da hankalin ki Aysher ni dai fata na ki gama jarabawa ki samu sakamako mai kyau ko ina da rai ko ban da rai zanji dadi nayi alfahari dake kuma zan bar wasiya ko na mutu a tsaya miki sai kin gama karatun ki. Ina fatan zaki bani hadin kai Aysher!”_

Kai ta gyada ta bude question papper ta fara karantawa ta fara answering tana gamawa tace

“Nayi ne kawai dan kai Yaa AK Allah ya zama gatan ka ya baka lafiya. Allah baka lafiya.”

Ta mike tayi submitting tana bayar wa ta fita a ajin gida tayi kai tsaye bata tsaya jiran kowa ba. Jiki a sanyaye ta shigo gidan bama ta lura da Umma dake zaune ba tayi dakin ta. Kai Ummah ta girgiza kawai ta cigaba da gyara kayan miya.

*

Washe gari ne graduation din su amman sam Aisha bata wani farin ciki Yaa Muhammad sosai abin ke bashi mamaki. Ba abinda Aisha ke so a da in ba taga tayi graduation ba amman yanzu ko maganar batayi da yaje yana mata maganar ma shiru kawai ta tafi tunani.

“Aisha;”

Ya kira sunan ta amman sam bata amsa masa ba sai da ya tabo ta sannan ta juyo tana kallon sa da idon ta da sukai jajir!

“Menene?”

Mikewa tayi tace

“Ba komai!”

Ta fita a dakin bandaki ta shiga ta dauro alwala ta dawo ta hau kan sallaya. Kallon ta yake dan yasan tayi sallah. sallah me kuma zata karayi. Yana zaune tayi sallah tafi raka’a goma sannan ya mike ya fita. Tana idar wa ta dauki alku’rani ta fara karantawa wannan shi ya bata wani sauki a cikin zuciyar ta amman fa gaba daya bata cikin nutsuwar ta.

STORY CONTINUES BELOW

Kwaciyya tayi a wajen kanta na mata wani irin ciwo. Dafe kan tayi ta rufa saboda zazzabin da ta faraji na son ya shige ta.

Umma ce ta leko tace

“Bakya jin yunwa ne?”

Kai ta gyada tace

“Na koshi!”

“Ke haka zaki na zama ba zakici abinci ba ko?”

“Umma na koshi ne fa naci abu a makaranta!”

“Allah kyauta!”

Ummah ta juya ta fita tana kwance har akai la’asar ta mike tayi ta koma ta kwanta can ta dauki littafi ta fara karantawa duk da catering craft zasuyi a karshe ta dan taba karatu ta rufe saboda sanyin da take ji.

*

*

*

Mamah na zaune a gefen gadon ya farka saboda wani tari da ya taso masa kan ya dauki tissue ya fara tarin ai kuwa sai ganin jini Mamah tayi yana fitowa daga bakin sa da sauri ta karasa ta dago sa tana shafa masa baya. Tana fadin

“Innalillahi wainna ilahir rajiun jini kuma ni Rashida.”

Da kyar tarin ya lafa ta goge masa baki sannan ta fita a dakin da sauri a falon ta samu su Abbah yana ganin ta a giguce ya mike yana fadin

“Lafiya?”

“Alhaji Amman Jini Aliyu ke yi na shiga uku!”

Ta fada tana kuka. Kamo ta yayi ya kalli Abubakar yace

“Kaje ka fadawa likita!”

Mikewa yayi ya fita su kuma suka koma dakin da Aliyu yake. Dagosa Abbah yayi yace

“Sannu!”

Ido ya bude a hankali ya sakar musu murmushi sai kuma ya maida idon ya rufe. Kirjin Mamah ne ya buga tace

“Alhaji yana numfashi kuwa?”

“Haba Rashida dan Allah ki nutsu mana wacce magana ce haka wai yana numfashi bayan yanzu ya bude ido bacci ne kawai ya dauke shi.”

Shiru Mamah tayi ta zuba masa ido dan ita dai taga ba numfashin da yake yadda ya rufe idon sa ba yadda mai bacci yake ba.

Likitoci ne suka shigo da sauri,  suka amshi Aliyu a hannun Abbah. wanda ya amshe shi ne ya kalle shi sai ya fara lalluba shi. Dagowa yayi ya kalli su Abbah yace su bashi waje.

Jikin Mamah ya kara sanyi tana fita ta zube a kasa tana dafe zuciyar ta. Can ta mike tana leken su ta window,  magana taga sunayi can taga suna masa connecting computer. Ido ta kurawa computer taga tana layi layi bata yin alamar numfashi jikin tane ya fara rawa.

Can kuma sai taga yayi wa daya daga cikin doctors din magana wani abu ya dauko ya fara cire masa riga a kirjin da suka saka masa karfin suka jona shi ya dago abun sai Aliyu ya dago ya koma kan gadon. Sai da sukai haka sau uku amman numfashin nasa bai dawo ba.

Mamah ce ta sulale tana fadin

“Yaa Allah ka tashi kafadun Aliyu Allah ka jikai na ka tashi kafadun Aliyu Allah ka bawa Aliyu lafiya.”

Ta fada tana daga hannu sama. Abbah yayo gun ta ya dago ta rumgume ta yana lallashin ta. Doctor ne ya fito yana gumi wajen sa suka nufa ya daga musu hannu kawai ya fice daga dakin.

Kuka Mamah ta kuma saki tace

“Dan Allah kuce me yake faruwa ina Aliyu na?”

“Ya isa ki daina kukan to!”

Abbah ya ja ta suka fice a dakin. Maryama kuwa itama kuka kawai take. Jajara kuwa na zaune waya a hannun ta amman itama jikin ta yai sanyi.

Doctor ne ya dawo da sauri Yaa Abubakar yasha gaban sa.

“Me yake faruwa ne?”

Ya tambaye shi da turanci. Likitan yace

“Excuse me please!”

“Please ka fada mana wani abu”

“You just have to pray to him!”

Yana fadar haka ya shige dakin.

*GWS Aliyu*

*

**

***

****

*****

******

*******

A bakin titi taga mai fruit tsayawa tayi ta siya sannan ta dau hanya. 6:30pm ta shiga gida a gajiye. Tunanin ta me ma zataci in ansha ruwa. Tana shiga falo ta jiyo motsin Momy a kutchen. Kitchen din ta nufa tana ganin Momy ta ajiye ledar hannun ta sannan ta karasa tace

“Me Momy ke dafa mana!”

STORY CONTINUES BELOW

Juyowa Momy tayi tace

“Sannu kin dawo?”

“Na dawo Momy na gaji.”

“Sannu Allah taimaka! Allah bada lada.”

“Amin Momy.”

“Kije ki watsa ruwa kan asha ruwa ban san me kike so ba dai amman gashi nan na hada mika kayan shan ruwa kije yanzu ko watsa ruwa ki dan huta.”

Rumgume ta Fateema tayi tace

“Nagode Momy na I love you!”

Murmushi Momy tayi tace

“Kije kiyi wankan!”

Ledar hannun ta,  ta ajiye sannan ta fita. Daki ta shiga ta fara cire kayan jikin ta. wanka tayi sannan ta fito ta saka doguwar riga armless marar nauyi ta saka hijab.

Kiran sallah akai firij ta bude dake dakin ta dauki dabino tayi addu’a sannan taci tana gamawa ta sha ruwa kadan sannan ta mike ta tada sallah. Tana idar wa ta zauna tana addu’a.

Wayar tace ta dau kara wannan yasa ta dauka tana duba mai kira. Momy ce ta kira mikewa tayi ta fito kawai tana fadin

“Momy gani nan!”

A falo ta same ta tace

“Dan Allah kije ki sha ruwa ace haka za a sha ruwa amman sai kinyi isha’i zaki ci abinci haba Fateema wai ke wane laifi abinci yai miki?”

Dariya Fateema tayo tace

“Yi hakuri Mony yanzu zan fito daman fa.”

“To maza kije kici ni wallahi bana son ina ganin ki haka kullum a rame na fiso naga kin danyi kumari haba mana.”

Murmushi Fateema kawai tayi ta wuce dining ta hada kunun da Momy tai mata tasha. Ji tayi har cikin ta ya cika amman tasan Momy yanzu zatai ta fada dan haka ta zuba dankalin sai farfesun naman kaza ta fara ci da kyar ta dinga tosawa. Tana gamawa ta koma falon ta zauna tana fadi

“Alhamdulillah. Momy Allah ya saka da alheri ya biya ki da aljanna mafificiya. Amin!”

Murmushi kawai Momy tayi. Wayar ta ce ta dau kara ta duba taga Nusy ce bata dauka ba har ta katse sannan ta kira ta.

“Anty na kin koma gida lafiya ya aiki?”

Ta fada bayan ta amsa sallamar da Fateema tai mata.

“Alhamduliah ya gida dasu Mami? Dady ya dawo ko?”

“Ya dawo Anty ina Momy?”

“Tana nan?”

“Bani mu gaisa!”

Mika mata wayar tayi suka gaisa da Momy kamar sun saba da juna sannan sukai sallama. Fateema ta amsa suka dan taba hira  sannan ta kashe.

Momy tace

“Wacce wannan?”

“Yar Babbar yar Fu’ad ce!”

“Allah sarki dazu kuwa Hajiya ta kira tana ta godiya.”

“Allah sarki Momy na naga missed call dinta kuma na sha’afa ban kira ba bari na kira na kara godiya.”

Ta fara dailing number Momy. Bugu daya biyu ta dauka tana fadin

“Assalamu Alaikum!”

“Wa’alaikum salam ina yin Mama?”

“Lafiya lou Fateema ya gida da aiki da Momyn taki?”

“Suna lafiya Alhamdulillah!”

“Masha Allah!”

“Wallahi dazu ina driving naga kiran ki kuma da na shigo akai magariba sai yanzu na samu na kira. Nagode Mama Allah kara girma da arziki!”

“Ba komai Fateema. Allah yayi miki albarka. Sai da safe.”

“Amin Mama nagode!”

Ta kashe wayar.

*

Aslam da Jiddah na fita ya bude mota ya shiga ta zaga ta shiga suka nufi gida. Yana parking ya fita daga motar yayi dakin sa. Agogon hannun sa ya fara cirewa ya zare top din rigar jikin sa ya zauna a gefen gado ya sabule takalmin kafar sa. Zai zare safar kafar sa kenan ta shigo. Kai ya dauke ya zare daya ta durkusa zata zare masa dayar yai saurin janye kafar sa. Tsayawa tayi tana kallon sa ya tashi ya cire kayan sa ya shige bandaki. Wanka yayi ya fito ya shafa mai ya shirya cikin wasu kananun kayan ya bade jikin sa da turare sannan ya fice ya bar ta nan tsaye tana binsa da kallo ta rasa ta ina ma zata fara ta rasa tayaya zata tunkare shi.

Yana fita ta fashe da kuka tana danasin abinda tayi da jin shawarar kawaye. Fita tayi ta nufi dakin ta a bakin gado ta zauna ta dauki wayar ta,  ta fara dailing number wayar kawar ta Sadiya. Kira daya biyu ta dauka tace

“Sady na shiga uku!”

“Me ya faru Jiddah?”

“Sady,  Honey ya gane cewar nayi planning!”

“How comes?”

Ta tambaya. Nan Jiddah ta fada mata komai tana hawaye. Shiru Sady tayi tace

“Yanzu me ya faru?”

“Yayi shiru bai ce komai ba Sady bansan wane mataki zai dauka ba kinsan Aslam da zuciya ina tsoro Sady ina son Aslam ina kishin sa kar ya dauki wani matakin da ba zan iya jurewa ba.”

“Cool down Jiddah ba wani mataki da zai dauka ai shima yana son ki kuma wa ya kai ki daukar shawarar Khadija tin farko kisan da nai muku magana da ra kara tarar ki kika fada min sai da nai miki fada ko akan me kin auri mutum zaki hau wani yi planning ke ba karatu kike ba baki sani ba ma ko zaki iya haihuwar ko ba zaki iya ba bama wannan ba yanzu in Aslam yasan akan me kikai zai ji dadi. But koma me zakuyi ki fada masa gaskiya in yaga zai iya hakuri is ok amman zance boye boye bai taso ba dole kiyi hakuri ki fuskanci hukunci kadan ma kika gani wannan ki godewa Allah da ya tsaya a haka kiyi fatan kuma ya tsaya a hakan!”

“Sady kaina ya kulle wallahi kada Aslam yace zai aure in an gane a dalilin haka ba zan iya haihuwa ba.”

“Kina so kice zaki hana sane bayan ke kika cuci kanki.”

“No Sady ba zan iya ba bazan taba yadda Aslam yayo min kishiya ba dani kadai aka hallici Aslam dan haka dole ni kadai zai zauna da ita.”

“Kinyi wasa da damar ki Jiddah da ace matsalar nan daga Allah ne da sauki amman in har aka gano ta dalilin abinda kikai ne wallahi ko nice Aslam aure zan kara in auro wacca zata haifa min ya’ya.”

“Amman Sady sai yau nasan bakya so na wallahi.”

Murmushi Sady tayi tace

“Gaskiya daci gare ta amman in ba dan haka ba menene rashin so anan wallahi duk cikin friends dinki ki duba ki hanga zaki gane nafi kowa son ki su duk suna biye miki ne ki ta daukar shawarar su. Kiyi hakuri sai anjima.”

Ta kashe wayar ta. Wayar tabi da kallo ta saki tsaki tana sakin kuka tace

“Na shiga uku yaya zanyi.”

Wayar ta dauka ta fara kiran Khadija ringing daya, biyu ta dauka tace

“Amarya kuma uwar gida a gidan Aslam!”

Murmushi ta dan saki tace

“Da yardar Allah ni kadai ce bamai shigo min.”

“Ya kike?”

“Ba lafiya Khady ta inda aka hau dole tanan ake sauka!”

“Me ya faru?”

“Abinda mukai shekara takwas baya ne ya balle?”

“Me kenan?”

“Planning din da nayi!”

“Taya ya balle?”

“Last week Honey yazo min da zancen wani asibiti akan muje a duba aga matsalar me ya hanamu haihuwa da muka je yau shine fa garin tambaya ta tambayen wai na taba plabning…”

“Shin kika ceme?”

“Me kike zaton zan fada Khady bayan na tabayi.”

“Shit akan me kika fada sai kice a’ah in kun kebe ki mata bayani. Ke meyasa baki da wayo ne.”

“Khady ido na ya rufe neman mafita!”

“Ai gashi nan kin jefa kan ki cikin ruwa.”

“Ba kadan ba Khady domin tin acan Honey bai karai min magana ba yanzu mun dawo yai wanka ya fice.”

“Ya salam!”

“Ya zanyi yanzu?”

“Kinga dole mubi komai a sannu hakuri kawai zaki bashi daga baya ma san me zamuyi.”

“Amman kina ganin zai saurare ni.”

“Haba Jiddah sai kace ba matar sa ba kisan ta yadda zaki lallaba shi mana.”

“Shikenan nagode. Ni nasan in ina dake banyin kuka.”

“Wannan haka yake besty!”

“An kira sallah bari naje nayi sai anjima zakiji yadda mukai nagode!”

Ta kashe wayar ta mike ta dauro alwala. Sallah tayi sannan ta mike ta shiga kitchen dan samar masa abinda zai ci.

Tana fama girki ta fada dakin tai wanka ta taci kwalliya kamar me zuwa wani bikin ta zauna tana jiran zuwan sa. Tin takwas yake dawo gida in yayi dare tara amman abin mamaki har tara da rabi shiru gashi ta kira bai dauka tai test no reply duk hankalin ta ya tashi.Tana fama girki ta fada dakin tai wanka ta taci kwalliya kamar me zuwa wani bikin ta zauna tana jiran zuwan sa. Tin takwas yake dawo gida in yayi dare tara amman abin mamaki har tara da rabi shiru gashi ta kira bai dauka tai test no reply duk hankalin ta ya tashi.+

10pm taji mai gadi na bude kofa da sauri ta mike ta karasa window. Motar sa ce ta shigo ya nufi parking space ya ajiye ta ya fito yayo cikin gidan yana tafiya a hankali da ka kalle shi zaka gane yana cikin damuwa. Yana shigowa yayi tozali da ita. Kai ya dauke ya nufi dakin sa. Ruwan sanyi da lemo ta dauka ta kai masa dakin sa. A kwace ta same shi ya lumshe ido.

“Honey!”

Yai mata shiru matsawa tayi ta dan dafa shi tace

“Please Honey ka tashi kasha ko ruwa ne mana!”

A hankali ya mike zaune yace

“Tashi ki fita anan!”

Tsaya kallon sa tayo da mamaki dan kuwa Aslam akwai hakuri amman akwai zuciya zata ce tinda sukai aure bata taba ganin sa a irin wannan yanayin ba.

“Nace get out ko?”

Zubewa tayi a kasa tana fadin

“Haba Honey ni wallahi i can’t go  any where naji nai laifi amman ka hukuntani shirun ka yafi komai min zafi da ciwo please say it out ko naji dadi.”

Kai ya dafe yana jin kukan ta har tsakar kan sa da zuciyar sa.

“Am sorry Honey kayi hakuri dan Allah ban san haka komai zai faru ba shiyasa amman nima ai danasani nake yi.”

Dagowa yayi yana kallon ta idon sa jajir yace

“Jiddah you disappointed me! Na rasa ta ina zan fara why why?”

Ya dafe kansa yace

“Saboda bakya so na shiyasa bakya son ki haifa min ya’ya why are you pretending that you love me why Jiddah?”

Kai ta hau girgizawa tana fadin

“Please Honey kar ka kin mummunar fahimta you know i love u and i really do so you are my life my happiness wallahi i can give you my life to dan me zan hanaka ya’ya.”

“Jiddah kome zaki fada ina kallon su kamar a matsayin yaudara ne! To dan abinda nan da ya faru na rasa wane irin tunani zanyi kowanne nayi sai na karya ta meyasa kikai min haka ki fada min da kanki kada ki min karya in har kikai min karya ban yafe miki ba.”

A razane ta dago tace

“But Honey!”

“Na fison ki fadan gaskiya ko da zai breaking heart dina ko da zan rasa rayuwata kar kimin karya. Gani nake duk zaman da mukai kenan ba sona kike ba Jidda ki fahimtar dani dan Allah ki fahintar dani kinsan ina son ki meyasa kikai min haka me nai miki da zafi kikai min haka Jiddah?”

Kafar sa ta kama tana kuka tana girgiza kai.

Shiru yayi ya rasa mema zai yi.

“Nakasa tantance meyasa kikai min haka ki fadamin gasiya Jiddah ko na samu sauki.”

Hawayen idon ta ta goge tace

“Nasan ba zaka manta haduwar mu ta farko ba a resturant da ka ganmu mu hudu ni da Sady,  Khady da Najah wanda a lokacin shigowar ka ni na fara ganin ka but i pretend akan bangan ka ba kuma tin lokacin naji na kamu da son ka. Bamu gama cin abinci ba na azalzalasu ganin zaka fita wanda muka hadu a wajen biyan kudi kai zaka fita ni kuma zan biya mana kudi.

Bayan ka fita naga car key nan nace na waye?  Aka ce min kila naka ne na fito da niyar kawo maka muka hadu zaka zo ka dauka. Inda na baka ka amsa kai min godiya tin lokacin kai min kuma nake son ka. Da na tafi da tunanin ka na kwana na tashi. A haka nake rayuwa da kai a raina daga haduwar mu dakai. Wanda haduwar mu ta biyu a bikin abokin ka ni kuma kawata kana cikin abokan ango wanda a motar ka ka kai mu gidan amarya nan ma mun hadu ka tayar min da mikin son ka.

Haduwar mu ta uku kuma a shopping mall da muka hadu har ka gane ni muka gaisa muka je biyan kudi ka biya min da muka fito ka rage min hanya. Wanda wannan ita ce silar komai har mukai musayar nunber.

Daga nan muka fara soyayya Aslam kasan ba karya a soyayyar da mukai ban yaudare ka ba kuma bazan taba yaudarar ka ba.”

STORY CONTINUES BELOW

Aja majina tana fadkn

*Lokacin bikin mu ya kusa saura sati daya ne muna zaune da kawaye na Sady, Khady da Najah ana ta hirar rayuwa da halin maza anan aka sako halin mazan yanzu wanda wasu da sunyi aure suke canja halin su a waje wata kuma bata gama sanin waye ba ta saki jiki daga ta haihu ta fara fuskan tar kalubale na rayuwa daga mijin matsala dai kala ka. Wanda anan Khady tace

“Jiddah why not kan ki tare kuyi allura kan kiga wajen zama in abin ya daure shikenan.”

Tin a lokacin  Sady ta nuna rashin ryaddar ta amman Najah da Khady suka dinga zuga ni a haka har na amince  na fadawa Sady ta kara ja min kunne amman hudubar su Khady ta shigeni wanda ranar kamu akai min allura. Haka mukai biki aka tare. Na yadda kana sona kamar yadda nake son ka Aslam  bayan biki da wata uku Khady ta kara zuwa wai lallai sai nayi allura nace ni muna zaune lafiya tace ai duk da haka daga wata uku zan saki jiki har gidan na ta kawo wanda yai min allura wanda tin daga lokacin be period dina ya canja da ya dauke na lokaci sai kuma ya sauya daga five days to three days kaji yadda komai ya faru. Dan Allah Honey kayi hakuri ka yafe min dan Allah ba zan sake ba.”

Dagowa yayi ya zuba mata idanu sa da suka kada sukai jajir yace

“Wato baki yadda dani ba kika aure ni?”

“Ba haka bane Honey ka gane!”

“In gane me Jiddah daman baki yadda dani ba. Me na nuna miki da baki yadda dani ba duk son da nake miki.”

Ya fada yana zama tare da dafe kai. Yace

“Wato baki yadda dani ba sai daga baya ko?”

Yai shiru yace

“Kin kyauta. Tashi ki ban wajen!”

“Please Honey!”

“I say get out!”

Ya fada da zafi da sauri ta mike ta fice.

Kan gado ya fada yana runtse ido shi sam ba rashin haihuwa ke damun sa ba dan me zatai abu ba sanin sa sai yanzu da ya gane dalilin yin abin nata ya jima a kwace sannan ya mike ya shiga ya watsa ruwa ya fito ya fada kan gado yana tunanin rayuwar sa da Jidda dame ya rage ta tun awaje zuwa auren su. Ranar bai runtsa ba dan ko da wasa aka ce Jiddah zatayi  ba zai yadda ba.

Washe gari yana tashi da safe ya fice a gidan gaba daya. Office ya tafi sai dai duk ya kasa yin wani aiki. Karfe daya ya mike ya tafi asibiti duk test din da ya kamata ayi akai masa sannan ya fito har zai fita ya juya ya nufi office din ta. Ba kowa a bakin kofar sai mai shigar da patient tana ganin sa tace

“Barka da zuwa!”

Yai murmushi yace

“Tana ciki ne?”

“Eh tana ciki dan yanzu ta idar da sallah!”

Kofar yai knocking sannan yai sallama ya shiga. Zaune ya same ta akan sallaya sanye da ash kalar hijab da ya amshe ta fuskar ta tai haske a cikin hijab din. Addu’a take ta ji an shigo ta shafa ta dago kanta. Ido suka hada ya kasa dauke kansa daga kallon ta. Kasa tayi da kan ta tace

“Bismillah!”

Ta nuna masa kujera. Jingina yayi da bango yana kallon ta yace

“Wucewa zan yi nace bari na shigo na ganki da fatan kina lafiya?”

“Alhamdulillah!”

“Masha Allah!”

Ya juya zai fita tace

“Thank you!”

Juyowa yayi yai mata murmushi kawai ya fita. Mikewa tayi ta koma kan doguwar kujerar dake office din ta zauna ta jinginar da kanta da jikin kujerarr tare da lumshe idanun ta.

Yana cikin mota ya hanki Jiddah ta shigo tayi parking bata lura da motar sa ba ta shige wajen da za ai mata test din ta. Kallo ya bita dashi sannan ya tada mota ya fice daga asibitin.

Bata jima ba aka gama komai ta fito ta fita daga asibitin. Itama kana ganin ta kasan tana cikin damuwa ba kadan ba. Cikin kwana daya duk ta sauya. Gida ta koma ta rasa me zatayi. Can ta mike ta shiga daki ta fara hada masa abinci kala kala sai yamma ta gama ta shiga ta yi wanka taci kwalliya zama tayi dan tasan duk inda yamma zuwa bayan magariba yayi ya shigo gida.

Amman yau ma har akai isha’i bashi ba alamun sa. Tana zaune ta zuba tagumi duk abin duniya ya ishe ta taji horn dinsa da sauri ta mike ta fito a bakin kofa ta tsaya tana kallon sa. Ya fito yana tafiya a hankali da sauri ta karasa zata amshi jakar hannun sa sai taga ya janye yayi ciki kawai bin bayan sa tayi yana shiga daki ya saka key.

STORY CONTINUES BELOW

Zama tayi a falo ta saki kuka mai taba zuciya. Dan ta rasa ya kuma zatayi. Tana zaune a falon har karfe sha biyu tin inda ya bar ta ko motsawa batai ba aka bude kofar dakin da sauri ta dago tana kallon sa.

Kayan bacci ne a jikin sa hannun sa rike da plate da Apple akai bai kalle ta ba ya tafi kitchen wanke Apple din yayi ya yayyaka sa sannan yazo zai wuce bata falon dan haka ya shiga dakin sa ya saka key yana ajiyewa ya fara ci ta fito daga bandaki kallon ta ya tsaya yi.

Ta karaso ta durkusa a gaban sa tana fadin

“Dan Allah Honey kayi hakuri kayi min rai ka yafe min wallahi wannan shariyar da kake min ba zan iya jura ba baka san yadda nake ji ba nayi laifi amman na tuba ka yafemin ko Allah muna masa laifi kuma ya yafe mana dan Darajar Annabi da alkur’ani ka yafen ba dan ni ba, ba dan hali na ba.”

Shiru yayi tace

“Please Honey!”

Ta fadi tana kara fashewa da kuka dagota yayi yace

“Is alright Jiddah ya shige but don’t repeat it again. U know i love u and i always love but i can’t treat u the way some men treat their spouses. Kinsan hali na Jiddah ko wacce bana so ba zan mata haka ba balantana ke da nake son ki. i love you Jiddah in kina min haka zaki karya min zuciya ta kinji!”

Jikin sa ta fada tana fadin

“I will not honey i will not broke ur heart i love u. You know that i can’t do without your love am sorry please forgive me!”

“Is ok Jiddah i love u kuma ba zan taba rike ki a zuciya ta da wani abu marar kyau ba ina son ki,  nayi haka ne dan ki gane laifin ki amman na yafe miki Allah ya yafe mana gaba daya.”

“Nagode Honey Nagode!”

Ta fada tana kuka dago kan ta yayi yana lashe hawayen dake zuba a idon ta. Daga nan kuma ya hade bakin su.

2:00am ya fito daga wanka ya zo ya zauna a gefen ta yana fadin

“Ko nai miki wankan ne?”

Mikewa tayi zaune tace

“Baka ci abinci ba Honey!”

“Kina so naci ne?”

Ido ta zaro tace

“Wa zan so yaci in ba kai ba.”

“Kawon wani abu naci!”

Da sauri ta mike ta fita ya bita da kallo yana girgiza kan sa. Bata jima ba ta dawo hannun ta rike da flask ta ajiye a kasa ta dauko jug da ta hada masa lemon kwakwa. Ta zuba masa pepper soup din da tayi a bowl ta fara bashi. sai da ya ci ya koshi sannan yasha lemon ya mike ya wanke bakin sa ita kuma ta shiga tayo wanka. akan gado ta same shi tace

“Yau ba zakai sallah ba!”

Hannu ya mika mata yace

“Bayan kin hanani bacci come let sleep kinga uku saura fa.”

Kan sa ta fada yace

“Wayoo zata karyani.”

“Ina nauyi  yake Honey?”

“Gashi nan kuwa!”

Tayi dariya tace

“Zan yi dai nan gaba!”

Ya rumgume ta a haka bacci ya dauke su wanda suka kusan makara dan sai wajen biyar da kwata suka tashi da sauri ya shiga ya watsa ruwa ya daura alwala yai raka’atanil firij sannan ya fita zuwa masallaci.

Yana dawowa ma ya koma bacci. jidda kuwa aiki ta fara ta gyara gidan ta shiga kitchen dan samar masa da abincin da zai ci.

8:00am

Har tayi wanka taci kwalliya sai tashin kamshi take. dakin sa ta nufa ta zauna a gefen gadon sa tace

“Honey Baccin ne har yanzu!”

Ta fada yana shafa kansa. Ido ya dan bude yace

“Safiya tayi ne?”

“8:20 fa.”

Kansa ya daura akan ciyar ta yana sakin murmushi yace

“Lallai nasha bacci.”

Hancin sa ta dan ja tace

“Ka tashi kayi wanka jayi breakfast yau dai ka makara.”

“Thanks you wife.”

Ya mike ya shiga bayi har ta hada masa ruwa. Wanka yayi kan ya fito har ta gyara dakin ta saka turare. Shiryawa ya fara yana cikin shiryawa ta shigo ta karasa saka masa maballin sannan ta saka masa agogo ta dauki turare ta shafa masa. Rumgume ta yayi yace

“Thanks you Wife Allah miki albarka.”

“Amin Honey nagode!”

Suka fita parlour suka nufi dining a baki ta dinga bashi abincin har ya gama sai 9:00am ya fita a gidan.

Har gun mota ya rakashi yace

“Ki zama cikin shiri by 2:00pm zan zo mu tafi.”

“Sai ka dawo. Allah tsare ya bada sa’a honey.”

“Amin Thanks you!”

Ya tada motar ya fice. Ciki ta koma tana murmushi yanzu komai ya tafar mata yadda take so.

*

Da sauri ta fito daga dakin ta sa da doguwar riga peach kala mai dogon hannu tayi rolling milk mayafin ta da takamlmi milk sai jaka milk and peach wayar ta a hannun ta. Momy na zaune akan dining tana breakfast ta fito. A wajen kujera ta tsaya tana fadin

“Momy ni zan tafi dan na makara!”

“Me kika ci?”

“Ba komai.”

“Zo nan ki zauna ki karya.”

Momy ta fada tana hada mata tea. Zagawa tayi ta tace

“Momy na makara ne wallahi.”

“Allah Fateema na fara gajiya da rashin cin abincin ki gaskiya!””

“Momy….”

“Bafa zan jiki ba Fateema ki zauna kawai kici.'”

Ta fada tana mika mata tea din ta dauko bowl ta zuba mata dankalin da plantain ta tura mata wani bowl ta dauka zata zuba mata peppersoup din kifi tace

“Momy zan tafi dashi anjima naci a office.”

Mikewa Momy tayi ta shiga kitchen ta dauki karamin flask ta zuba sannan ta koma ta zauna da kyar take tusawa a haka har ta gama tace

“Momy na gama.”

“To Allah bada sa’a Allah tsare ki kula da kanki da mutuncin ki da aiki ki. Allah tsare ya kare!”

“Amin Momy nagode!”

Ta fada tana fita da flask din a kujerar gefe ta ajiye kayan sannan ta tada motar. Mai gadi ya bude ta karasa tace

“Baba ina kwana?”

“Lafiya lou Fateema Allah tsare ya kare!”

“Amin!”

Taja motar ta fice.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *