WA NAKE SO CHAPTER 15
Www.bankinhausanovels.com.ng
Zaune take a office din nata tana duba wani littafi dake gaban ta bayan tayi round ta dawo. Wayar tace ta dau kara tana dubawa taga sabuwar number. Dauka tayi tayi sallama. Amsawa akai sannan akace
“Doctor An tashi lafiya ya kike ya aiki?”+
“Alhamdulillah amman ban gane waye ba?”
“Jannah ce!”
“Oh Jannah ya kike ya gida ina Noor?”
“Gata!”
Ta amshi wayar tace
“Ina kwana ya aiki?”
“Alhamdulillah ya gida da Hajiya?”
“Tana lafiya!”
“To agaishe ta!”
“Zata ji.”
“Aha nagode!”
Jannah ta amshi wayar tace
“Doctor ranar friday zan shigo muje radio station tare.”
“To shikenan sai kinzo!”
“Yauwah nagode ki gaida Momy.”
“Zataji sai anjima!”
Ta fada tana kashe wayar. Ido ta lumshe tana murmushi take ta tuna zuwan su gidan. Kenan su Noor yayan wannan mutumin ne Uncle wa ma taji suna cewa? Ohoo ta manta.
4:00pm
Aka shigo office din ta da sallama. Dagowa tayi tana amsa sallamar Aslam ne ya fara shigowa ya kura mata ido, kai ta dauke tana kallon system din gaban ta.
Dagowa tayi suka kara hada ido. Kai ta dauke ya saki murmushi ya harde hannu yana kallom ta. Aiki ta cigaba dayi bata yadda ta dago ba.
“Assalamu alaikum!”
Jiddah tayi sallama
“Wa’alaikun salam!”
Suka amsa. Jiddah tace
“Ya ka tsaya anan!”
Fateema ya nuna mata yace
“She didn’t welcome me!”
Kallon Fateema tayi. Fateema tayi murnushi tace
“Bismillah!”
Murmushi Jiddah tayi tace
“Thank you!”
Ta kama hannun sa suka karasa ciki. Zama tayi shima ya zauna.
“Ina yini Doctor?”
“Lafiya Alhamdulillah ya gida?”
“Alhamdulillah!”
Ta mika mata files din hannun ta tace
“Na shiga na amso result din ne.”
Amsa Fateema tayi ta zare envelope din sannan ta bude tana karata abinda ke a ciki. Idon ta akan takardar tana dubawa wanda Aslam ya tattara gaba daya hankalin sa ya maida kan fuskar ta yana kallon ta yana sakin murmushi. Itama Jiddah kallon ta take. Can ta dago tana kallon Aslam da ya kurawa Fateema ido. Zungurin sa tayi da hannu ya juyo a hankali ya kalle ta ya dage mata gira alamar
“Ya dai!”
Murmushi tayi tace
“Matar aure ce dai!”
“Waya fada miki?”
Fuska ta bata tace
“What did you mean to?”
Murmushi yayi yace
“Antyn kishi!”
Murmushi tayi tace
“Kar nayi kishin abinda nake so ne?”
“No kiyi!”
Tai murmushi. Fateema ta ajiye na Aslam ta dauki dayan na jiddah ta duba shima sannan ta ajiye tace
“To from dis result it shows that both of you are fine. Zaku iya haihuwa lokaci ne kawai bai zo ba.”
Ajiyar zuciya suka sauke. Fateema tace
“Sai dai kila matsalar wata kila daga baya ne abinda kika yi ne! Kisan planning yana da matsala wani lokacin allura tana sa jinkiri akan daukar samun ciki. Yanzu dai abinda zan ce baki da matsala tinda aladar ki ta saitu to ba matsala domin allura na bada matsala wani ta dauke miki zubar jini wani ta birkita miki wanda kila daga nan a samu matsala dan haka muke cewa aje cibiyar kiwon lafiya dan auna jinin ki aga wane tsari za’a a saka ki. Matsalar kuma ke kinga baki shiga dakin ki ba ace baki tabbatar ma kiina haihuwar ba amman kinje kin fara planning dan haka yana dakya ana wayar da kai akan wannan matsalar in har planning kake so kaje cibiyoyin kiwon lafiya dan a gane wanne ya dace. Yanzu ba abinda zance sai dai nace Allah ya kawo zuri’a mai albarka ya kawo haihuwa nan kusa Amin. Fatan alheri gareku!”
STORY CONTINUES BELOW

“Nagode Doctor kuma na dauki shawarar ki da izinin Allah za a kiyaye kuma nima zan na fadakar wa masu hali irin nawa Allah yasa su kiyaye kuma su gane nagode doctor allah ya baki kema zuri’a masu albarka Allah biya miki bukatun ki.”
“Amin Amin amman da an samu juna biyu nan zaki zo ina miki awo ko?”
“Insha Allahu doctor gunki zanzo har haihuwa ta.”
“To Allah kawo masu albarka.”
“Amin.”
“Mungode Doctor Allah saka.”
Aslam ya fada. Bata kalle shi ba tace
“Amin nagode ai ba komai.”
“Muje ko?”
Jiddah ta fada tana tabo Aslam dake kallon Fateema.
“Ok!”
Ya fada ya kasa tashi. Ita kuwa har ta mike ta kalli Fateema tace
“ko zaki ban number ki?”
“Ba matsala!”
Ta nika mata waya ta saka number ta Amsa tayi tace
“Sunan fa?”
“Fateema!”
“Ok Dr Fateema kenan!
Murnushi Fateema tayi. Jiddah ta kalli Aslam dake zaune tace
” muje ko?”
Tayi gaba. Wayar ta ce ta dau kara tana dubawa taga Khady ce dan haka ta fita da sauri dan ta dauki wayar. Mikewa Aslam yayi yace
“Doctor wa ya sani ko ta gun ji zamu fara samun ya’yan?”
“Kamar yaya?”
“In kin zama matata!”
“What?”
“Yea Doctor ban taba jin abinda nake ji akan ki ba doctor ki taimaka ki agaji rayuwa ta na fada miki am in pain of your love please ki bani maganin ciwo ba.”
“But na fada maka kaje ka nemi wasu likitocin su baka shawara dan abinda ka saka a zuciyar ka yana da illah gwara kaje ka nemi shawara yadda zaka fitar da abin kasa dangana.”
Ta fada tana dannan system din ta.
*
**
***
****
*****
******
*******
Sunfi awa nawa a dakin amman basu fito ba. Su Yaa Abubakar kuwa banda addu’a ba abinda suke dan sun leka sun gane meke faruwa dan haka jikin su yai matukar sanyi.
Mama ce ta shigo ta shimfidda sallaya ta hau ta fara sallah kara’a biyu tayi amman sai da ta dauki awa daya akai dan addu’a kawai take Allah ya tashi kafadun Aliyu. Allah maji rokan bayin sa bayan sun dauki wajen awa biyu akan sa ba alamun numfashi ko wani alamu na yana da rai sai kawai ji sukai ya sauke wata ajiyar zuciya take kuma ya fara tari wanda nan jini ya dinga fitowa daga bakin sa.
Cikin azama sukai kansa suka hau bashi taimakon gaggawa dan oxygen ma suka saka masa saboda yadda numfashin sa ke son daukewa. Yaa Abubakar duk abunda ake akan idon sa.
“Allahu Akbar! Alhamdulillah!”
Ya fadi yana rufe fuskar sa da hannun sa. Da sauri su Yaya Usman sukayo wajen suna leken dakin. Computer dake gefen gadon suka kalla sukaga yadda numfashin sa ke harbawa duk da ba sosai yake fita ba sai yayi layi sai kuma ya nuna alamar mutumin yana da rai. Sai da suka dauki wajen awa biyar akan Aliyu kan suyi masa allurar bacci sannan suka kara saka masa ruwa suka fito aka bar wasu biyu a dakin.
Yaa Abubakar da Usman ne suka bi bayan su. Office suka shiga suka zauna. Sannan Dr ya zauna ya dauko folder Aliyu wacce take da uban takardu a ciki. Budewa yayi yana nazartar ta sannan ya dago yace
“Jikin sa da sauki Alhamdulillah. Dazu numfashin sa ne ya dauke gaba daya to cikin ikon Allah dai yanzu ya dawo har ya dai dai ta da taimakon oxygen.
A binciken da mukayi jiya da muka saka shi a computer mun gane yana fama da matsalar ta damuwa. Wanda ya haifar masa da ciwon zuciya.
Sakamakon wani karamin bincike da muka gabatar na kungiyar masana ciwace-ciwacen zuciya na Tarayyar Turai ya nuna cewa masu fama da wani bacin rai suna iya mutuwa a cikin shekara guda.
Koda yake dalilai da dama suna iya haddasa ciwon tare da kara zafafa shi, masu binciken sun ce yana da muhimmanci a yi kokarin yaye ma majiyyata ciwon bakin ciken dake damun su. Ba zan ce ga abinda yake damun sa ba amman a gaskiya ya saka wani abu a ransa ne wanda ya haifar masa da ciwon zuciya. The worse part of it ma kaga ya fara aman jini ba anan abun yake ba ina tsoro kar ya kai stage din da zuciyar tasa zatai rauni ko jijiyoyin zuciya suka yi rauni ko kuma suka yi tsauri, abinda zai hana su harba jini ga sauran sassan jiki. Shi zai iya haifar masa da bugawar zuciyar tasa gaba daya.
A yayinda haka ta kasance, masu fama da ciwon kan yi laushi, wannan kuma zai iya kai su ga mutuwa.”
STORY CONTINUES BELOW

Ya dafe kai yace
“Yanzu dai ina son na gano menene asalin ya haifar masa da ciwon ta nanne zan gane akan treatment din zan daura shi.”
Kallon Juna sukai sannan Yaa Abubakar yace
“Zamuyi iya yin mu, mu gano hakan insha Allahu. Sai dai Aliyu zurfin ciki ne dashi sam ba a gane meke damun sa.”
Kai Dr ya jinjina sannan yace
“Sam baya son cin abinci dan haka ulcer ta shige shi dole yanzu ana samar masa wani abu da zai na ci. Ciwon ulcer babban ciwo ne wanda zai haifar masa da ciwon kai har da zazzabi da ciwon baya kunga matsalar zata hade masa biyu matsalar zuciya ga wannan kuma.”
“Insha Allahu Doctor za a kiyaye!”
“Muma zamu iya bakin kokarin mu wajen ganin komai ya dai daita. Insha Allahu.”
Mikewa sukai suka bashi hannu sannan suka fita. Suna shiga suka tadda kowa na cikin dakin da Aliyu yake.
Zama sukai a falon dakin Yaa Abubakar ya Kalli Yaa Usman ya ja nunfashi yace
“Yanzu ya zamuyi?”
“Kada mu fadawa Abbah da Mamah!”
“Menene ba za a fada mana ba Abubakar?”
Abbah ya fada yana fitowa daga dakin. Shigowa dakin yayi ya zauna ya kalli Abubakar yace
“Me yake damun dan uwan naku?”
“Abbah Ulcer ce daman sai….”
“Sai ciwon zuciya ko?”
Dagowa sukai suka kalli abbah. Abubakar yai kasa da kai. Usman yace
“A ina ka sani Abbah?”
Murmushi Abbah yayi yace
“Acan sun fadamin shiyasa na ce mu fito dashi waje. Dazu Mamahn ku tace daga tari sai jini fa.”
Kai suka gyada suka ce
“Eh Abbah haka ne.”
Shiru Abbah yayi yace
“Me suka ce?”
Nan Yaa Abubakar yai masa bayanin komai. Kai ya gyada yace
“To Allah yasa kaffara!”
“Amin Abbah!”
Mikewa sukai suka shiga dakin Mamah suka gani gaban gadon tana ta tofa masa addu’a idon ta jajir. Dafata Abubakar yayi yace
“Mamah kiyi hakuri zai ji sauki da yaddar Allahu!”
“Allah ya yadda!”
“Amin!”
Ya fada yana kamata ya zaunar yace
“Kina rage damuwar nan Mamah!”
Kai kawai ta gyada. Wayar Aliyu ce tayi kara dake hannun Maryama wannan yasa ta mike ta fita dan dauka. Faisal ne ta dauka tace
“Hello!”
“Maryama kuna wane asibiti ne ki turon address din na sauka.”
“Alright!”
Ta fada ta kashe wayar ta tura masa sannan ta koma daki ta kalli Abbah tace
“Abokin Yaa Aliyu ne Faisal zai zo!”
“Ok Allah kawo shi.”
Wayar hannun Maryama ce ta kara daukar kara ta duba taga an saka Pres Ahmad. Mikawa Abbah tayo tace
“Abbah kamar President ke kira.”
Amsa yayi yai sallama. Shugaban kasa ya amsa yana fadin
“Aliyu kwana biyu najika shiru Allah yasa lafiya.”
“Ba shi bane Alhaji Kabir ne!”
“Ah ranka ya dade ashe kai ne ya kake ya gidan?”
“Alhamduliah ya jama’a ya iyalai!”
“Alhamdulillah!”
“Madallah!”
“Ina Aliyun ne kwana biyu ba muyi waya ba ko na kira a kashe fa.”
“Ikon Allah ai ka ganmu nan bama kasar ma Aliyu ba lafiya shekaran jiya muka bar kasar.”
“Subhnallah amman ba labari meyasa bai fada min ba.”
“Abin ne yazo a korarren lokaci kuma duk ba nutsuwa.”
“Ya jikin nasa?”
“Alhamduillah!”
“Kuna wacce kasar?”
“Egypt!”
“To insha Allahu ina hanya ai Aliyu danane Allah yabashi lafiya zan turo da kudin kula dashi.”
“Haba Alhaji Ahmad ka barshi!”
“Nima fa ‘da nane!”
“To shikenan godiya muke!”
Ya kashe wayar. Maryama Abbah ya kira yace
“Ina Faisal yace yana ina?”
“Nima ban sani ba.”
Umar Abbah ya mikawa wayar yace
“Kaje ka dauko sa ka kai shi gida ya huta yaci abinci sai ku taho.”
Amsar wayar yayi ya fara kiran sa yace gashi nan sannan ya fita.
*
*
*
Aisha na exam hall suna final papper amman duk hankalin baya jikin ta yana can ga Aliyu. Ji tayi wani tari ya zo mata nan ta dingayi tana rike da zuciyar ya. Ta jima tana tarin sannan ya tsagaita. Karasawa tayi ta fito daga exam hall sai dai tana fitowa taji jikin ta na rawa kafafun ta suka kasa daukar ta durkushewa tayi a nan ta fashe da kuka.
Da sauri kawayen ta suka karaso suna fadin
“Lafiya Aisha?”
Kai ta hau girgiza musu tana fadin
“Na kasa tashi jikina duk rawa yake.”
Ai kuwa jikin ta rawa yake kar kar kamar me zazzabi. Daya a ciki tace
“To bari mu samo napep!”
Sa sauri ta fita ta samo suka dagata suka fita suka saka ta a napep din.
A kofar gida suka tadda Yaa Muhammad ya fito da katuwar leda zai fita yana ganin su ya karaso yana fadin
“Lafoya?”
Kuka Aisha ta saki ya karasa ya dauke ta sukai cikin gida. Bayan sa suka bi da jakar ta suka dauki ledar da ya jefar.
A tsakar gida ya ajiye ta ta dunkule waje daya jikin ta na ta karkarwa tana kuka. Umma ce ta fito tace
” lafiya?”
“Yanzu zan fita na ganta an dawo da ita daga makaranta.”
“To ikon Allah”
Kawayen ta ne suka shigo Umma tace
“Me ya same ta?”
“Tana fitowa daga exam hall ta zibe wai ta kasa tafiya jikin ta kuma sai rawa yake.”
“Inna lillahi wainna illahir rajiun”
Ta durkusa tace
“Aisha!”
Dagowa Taui ta fada jikin Ummah tana fadin
“Ummah tsoro nake ji zuciya ta sai bugawa take Ummahh!”
Sai ta fashe da kuka. Dagota Umma tayi tana fadin
“Kina addu’a Aisha. Muhammad ka kira Baban ku yazo kaji.”
Fita yayi suma sukai musu sallama suka tafi. Daki ta kamata ta shiga da ita zata fito ta rike mata hannu tace
“Ummah kada ki fita ki barni.”
“Ruwa zan debo nai miki tofi Aisha.”
Sakin ta tayi. Ta hade kai da gwiwa tana kuka hadi da dafe zuciyar ta dake buga mata da karfi.
“What is happening to me? Ko dai Yaa AK ne?”
Tana fadar haka ta kuma fashewa da kuka.
“Yaa Allah protect Yaa AK Get well soon Yaa AK Allah ka bashi lafiya.”
Ta fada tana dafe kirjin ta dan ji take kamar zuciyar ta zata fito. Ido ta runtse Umma ta dawo tai tofi ta bata ta sha sannan ta koma ta kwanta. Adsd’a ta dinga mata tana tofa mata.
Baba da Yaa Muhammad ne suka shigo Baba ya tsaya kanta yace
“Ya kike ji uwa ta?”
“Ni kawai zuciya ta ke bugawa dazu ne na kasa tafiya jikina yana ta rawa.”
“Ko asibiti zamuje?”
“A’ah Baba ya daina yanzu kawai zuciya ta ke bugawa.”
“To sannu Uwa ta.”
Ya kalli Muhammad yace
“Debon ruwa a kofi.”
Ya fita ya kawo masa. Amsa yayi yai tofi ya bata ta amsa ta sha yace ta shafa a jikin ta. Shafawa tayi sannan ya juya ya fita.
Ummah ma fita tayi Yaa Muhammad ya zauna a gefen katifar ta yace
“Sannu Aisha!”
Kai ta gyada ta lumshe ido kawai.
Mikewa yayi ya fita ta bude ido ta bishi da kallo hawaye ne ya zubo mata ta girgiza kai ta lumshe idon ta.
DUNIYATA*+
*Ina ma’abota karatun littafan hausa? Ku matso kusa kakarku ta yanke saqa.*
*shin kun karanta littafin FARAR TAFIYA?labarin soyayyar Amina da Isma’il wanda ta qullu bayan qaddarar fyade ta gifta tsakaninsu.*
*ga kuma littafin RUMFAR KASUWA wanda ya lakuto bangarori da dama na abubuwan da suke faruwada yara masu talla a kasuwanni da shaguna,ya fito muku da illa tallace tallace da kuma barin yanmata suna yawo sakaka babu kimtsi*.
*sannan ya fito muku da hanyoyin da za ku bi ku ciro wa yaranku hakkinsu idan aka zaluncesu musamman akan fyade ko yaudara.sannan ya fadada muku matakan aurar da yaran da kaddara fyade ko yaudara ya afka musu tare da jan su a jiki da kuma nuna musu kulawa ba tare da an qyamacesu ba*.
*TO YAU MA GA WATA SABUWA NAN*
*Littafin DUNIYATA labari ne da ya zo muku a lokacin da kuke bukatar irinsa a duniyar rubutu,ya zo muku da sabon jigo mai ma’ana.tare da warware kullin da aka zarga cikin ruwan sanyi da karfin addu’a.labarin ya zo muku ne da salo na daban da saura.ya kuma taho muku da abin lura da cewa ba mata kadai suke fuskantar qalubale a rayuwa ba,maza ma suna fuskantarsa wanda na Muktar Jarumin littafin ya bambanta.za ku ji yadda badaqala ta karke tsakanin ďa da mahaifinsa ,ya kuma fito muku da illolin rashin yarda da qaddara.gwagwarmayar ďa namiji tsakaninsa da mahaifinsa wanda ta kai uba ya yi wa dansa qazafin yunqurin kisa.*
*Kina bukata? ko kuna bukata?*
*Ku garzayo domin biyan naira dari biyu kacal ta wannan account number 0140772170 MURJA SALISU UNION BANK sai ku turo shaidar biya a wannan number 07034624830*
*Ko kuma katin MTN na naira dari biyu ta wannan number 07034624830 ku tura shaida kuma still ta wannan number din*.
***
**
*
Monday
Zaune take a office din ta sanye da maroon kalar less Wanda akai Masa ado da milk zare duk jikin sa stones ne Dinkin doguwar riga ne a jikin ta ya kamata daga Sama daga kasa a baje. Medium mayafi ta yafa a kafadar ta ta saka milk fashion da abin hannu da agogo. Tayi kyau sosai.
Juyi take akan kujerar ta tayi nisa a cikin tunanin ta taji an budo kofar dagowa tayi da sauri taga Aslam tsaye a bakin kofar sanye da maroon kalar suit tai Masa kyau sosai.
Kai ta dauke tace
Wai meyasa suka barin sa Yana shigo min ne?”
Ta saki tsaki.
“Good evening Doctor!”
“Evening!”
Ta fada fuska ba yabo ba fallasa.
Zama yayi yace
“Bani da lafiya Doctor!”
Paper ta yaga tai rubutu a jiki tace
“Kaje wajen Doctor Auwal ya duba ka!”
“Please Doctor ni ke nake so!”
“Lafiyar ka kalou kenan!”
Wallahi am sick Doctor!”
Dagowa tayi taga yai kalar tausayi dan haka tace
“what’s wrong with you?”
“Bana iya Bacci ga ciwon Kai in ta tunani!”
STORY CONTINUES BELOW

“Me kasa a ranka haka?”
“Tunanin ki Doctor!”
Mikewa tayi ta dawo tsakiyar dakin tace
“Shiyasa nace maka lafiya ka kalou!”
Ta juya zata fita cikin zafin nama ya mike ya kamo hannun ta ya hada ta da bango. Yai.mata rumfa. Kamshin turaren su ya gauraya ya bada wani kamshi mai dadi. Shi take kalla kamar yadda shima ira yake kalla. Kai ta dauke tana yin kasa da idanun ta dan ya matse mata hannu. Kokarin gwacewa take yace
“Fateema da gaske nake bani da lafiya Kuma duk abinda na fada miki su ke damuna please ki taimaka min please!”
Shiru tayi ya kama kafadar ta yace
“Fateema look into my eyes!”
Kin dgowa tayi yace
“Please ki kalli cikin kwayar Ido na kiga yadda nake son ki. Ki tausayan ni bani na daurawa Kai na son ki ba Allah ne Amman Dan me Zaki na min haka Dan Allah ya dauran son ki so kike na mutu ko me?”
Hawaye ne ya fara biyo kuncin ta yace
“Wallahi da gaske nake son ki ba da yaudara ba. Ki taimakan Fateema ko ban Miki ba?”
Kai ta girgiza yace
“To menene matsalar?”
Kan ta ta kwace ta juya Masa baya tace
“Kayi hakuri ba son Kane bana Yi ba Amman na daina soyayya in ma soyayya zanyi akwai Wanda nake jira kayi hakuri Dan Allah!”
Zata wuce ya Kara Shan gaban ta yace
“Waye wannan Fateema Yana Ina Ina yake Ina ya tafi ya barki da bai tsaya ya amshi soyayyar ki ba.”
“Nima ban sani ba ya tafi ya barni a lokacin da nafi son sa da bukatar sa a lokacin da nake Jin ban da Wanda ya kaishi. Ya tafi ya barni ban San inda yake ba Ina ka tafi ka barni Dan Allah ka dawo waje na.”
Ta fada tana durkushewa a wajen. Durkusawa Aslam yai ya dago kanta yace
“Ya tafi ya barki akan me?”
Kai ta hau girgizawa yace
“Dan sadaukarwa ko Dan son kan sa!”
Tai shiru in Dan wadan nan abubuwan ne ya kamata kema ki samu farin ciki Fateema Kar ki bar wani ya ruguza Miki rayuwar kila Wanda kike domin sa Yana can yai aure har ya haihu am….”
“Karya kake Sam Fu’ad will never do this to me. Ni kadai ce zabin sa. Ni kadai yake gani a matsayin mace ni kadai yake so ba zai tabai min haka ba. Kada ka kawon wannan tunanin kada kasa wannan tunanin yana running a Raina Dan Allah Dan zai ruguza min farin ciki na Dan Allah ka Bari ka barni a Yana can zai dawo Kar kasa na fara tunanin Yana tare da watata ba Zan iya jura ba.”
Ta fada tana hade Kai da gwiwa.
Dago kan ta yayi yace
“Is alright Fateema Ki daina kuka Fateema kinji komai yai Farko Yana da karshe kinji yanzu ki daina kuka Allah na tare dake insha Allah komai zai dai dai ta. Yanzu ki tashi a kasan nan mu koma can muyi magana.”
Mikewa tayi a hankali ta koma kan two sitter ya zauna akan one sitter yana kallon ta tana hawaye.
“Nifa ba kuka nace ki min ba!”
Hawayen ta hau gogewa yace
“Ina son ki fadan wani abu akan rayuwar ki da dalilin ki amsar soyayya ta duk da naso na gane!”
Shiru tayi yace
“Say it out doctor nasan zaki samu relief kema.”
Ajiyar zuciya ta sauke. A hankali ta fara bashi labarin ta har haduwar su da Fu’ad da soyayyar su da zuwan Yaa Fauwaz. Dramar da aka sha har da rasuwar Dady da kuma yafiyar Yaa Fauwaz da auren su da Fu’ad rayuwar da suka sha da zuwan su gida wanda shine rabuwar ta da Fu’ad. Tana zuwa nan ta kifa kanta akan cinyar ta ta saki wani marayan kuka.
Ido ya runtse yace
“Dan Allah ki daina kukan nan Fateema!”
Dagowa tayi tace
“Anya zan daina kuka kuwa ina jin ni da na daina kukan masoyi na sai ranar da na koma ga mahallaci na.”
“Ina jin ki har yanzu ba labarin sa.”
Nan ta cigaba da bashi halin da ta shiga har fara aikin ta da komai. Sosai tausayin ta ya kamashi.
Yanzu ya gane akwai wanda yafi shi son Fateema, amman shima yana jin sa a masoyin Fateema na hakika wanda shima zai iya bata farin cikin sa.
STORY CONTINUES BELOW

A labarin ta ya gane Fateema bata da masoyi sama da Fu’ad wanda ya sadaukar da farin cikin sa da rayuwar akan ta, ya gane Fu’ad yai zaton tafi son Fauwaz shi yasa ya tafi ya barta dan ta auri Fauwaz. To shi dan me Fauwaz ya tafi ya bar ta kishi ko sadaukar wa. Kai ya girgixa dan a farkon fara bashi labarin shi kansa yasan Fateema ta fi son Fauwaz amman yanzu kan sa ya shiga duhu domin kuwa ya kasa gane *Wa take so?* duk da a yanzu maganar Fu’ad take amman yadda rabuwar su ta kasance a lokacin da ta fara cire rai da Fauwaz ya barta shi yasa Fu’ad ya tsaya a ranta.
Hakika Fu’ad masoyin asali ne yayi saudakarwa amman yayi garaje meyasa bai tsaya ya bincike akai ba.
“Sai hakuri Fateema abu daya zan tunasar dake shine ki sani a yanzu ko Fu’ad ya dawo ba aure a tsakanin ku ko kina zaton haka zaki kare rayuwar ki ba aure. Kiyi hakuri ki amshi kaddarar ki ni a yanzu a matsayin Yayan ki kuma abokin ki nake dan haka zan baki shawarar da zan bawa kanwata kuma kawata ce. Addu’a ita ce karshen komai kuma akace inso cuta ne hakuri magani ne. Kuyi hakuri nasan kinyi rashin masoyi kuma bazaki maye gurbin sa ba sai dai kiyi tai masa addu’a duk inda yake Allah ta kareshi da fatan alheri.”
Kai ta gyada yace
“To ki daina kuka yanzu me kike kin gama aiki ne ko me?”
Kai ta gyada yace
“To in nemi alfarma a gunki?”
“Ta me?”
“Wata unguwa zaki rakani!”
Kallon sa tayi yace
“Please!”
Agogo ta kalla tace
“Yamma ai tayi!”
“Is just five fa! Ba dadewa zamuyi ba.”
Shiru tayi yace
“Nifa bana siyar da kan mutune!”
Murmushi tayi tace
“To kaje gani nan!”
Mikewa yayi yace
“Nagode!”
Bandaki ta shiga ta dauraye fuskar ta sannan ta fito ta goge fuskar ta shafa hoda ta sa man lebe. Fitowa tayi ta rufe kofar ta sannan ta nufi parking space.
A tsaye ta same sa yana ganin ta ya karaso yana fadin
“Kinyi kyau kanwata!”
Murmushi tayi ya bude mata gidan gaba ta shiga ya rufe sannan ya zaga ya shiga ya tada mota mai gadi yai musu addu’a suka tafi.
Wani park suka isa yai parking ya fito itama ta fito suka shiga ciki tin daga enterence din wajen zaka san wajen ya hadu ba karya kana shiga wani sanyn da ni’ima a wajen daman ga yamma tayi ido ta lumshe suka isa wajen zama kan wasu hadadun kujeru.
Zama sukai wata mata tazo cikin uniform din wajen ta kawo musu lemo da ruwa da paper a hannun ta. Amsa Aslam yayi ya mikawa Fateema amsa tayi ta kalla ta mika masa tace
“Bana bukatar komai?”
“Saboda me?”
Kai girgixa. Ticking yayi ya mika mata ta amsa ta bar wajen batai minti goma ba ta dawo dauke da katon tray. Nan ta fara jere kayan dake hannun ta tin daga kan abinci snacks da kayan ciyeye ciye ne.
Bayan ta tafi yace
“Ki ci abinda kike so?”
“Bana jin yunwa!”
“Me kika ci a office?”
“Am fasting fa!”
“Oh yau fa monday ko?”
Kai ta gyada yace
“Bari ai miki parkaging nasa.”
Ya kira daya daga cikin masu aiki agun yace in zasu tafu zasu amsa ayi parkaging nasa. Amsa tayi suka zauna yana dan shan lemon sannan yace ta tashi su zagaya wajen duk wanda ya gansu sai sun burge shi sai a zata mata da miji ne
Sosai wajen ya burgeta dan har lillo ta hau rabar ta samu refreshment sosai ta saki Aslam sai ganin dariyar ta yake har 6:30 suna wajen sau da yaga time ya kure kuma tana azumi sannan yace ta taso su tafi. Abubuwan ya amsa sannan suka fita. A hanya aka sha ruwa dan haka ta sha ruwa. Mai fruit ya gani ya tsaya ya siya mata. Har kofar gida ya kai ta ya mika mata ledojin ta amsa tana fadin
“To Uncle nagode Allah saka da alher.”
Murmushi kawai yayi ta juya tai cikin gida yabi ta da kallo anan layin su yai magarib a wani masallaci sannan ya tafi gida.
*
**
***
****
*****
******
*******
STORY CONTINUES BELOW

Tagumi yayi yace
“To fa! Me yake faruwa?”
“Da farko zan baka shawara domin kuwa ina son ka janye maganar auren ka da Aisha ka bata dama ta fito da wanda take so!”
A zabure ya kalli Umma yace
“Bangane ba?”
“Eh shawara na baka amman in kaga zaka dauka kenan!”
“Umma ki sani komai kika fada min zan dauka ba shawara bace kamar umarni ne amman ina neman wata alfarma.”
“Ina jinka?”
“Umma dan Allah ki fada min dalilin ki na yin haka.”
Dagowa tayi ta kalle shi tace
“Kamar yadda ka fada ba tun yau ba na gane Aisha na da damuwa kuma ta sauya. amman sai take nuna min babu anfi shekara biyu tana wannan halin nata.”
Kai ya gyada. Umma tace
“Nayi nayi da ita ta fadan menene amman taki sauyin ta ya cigaba har kwanaki na same ta inda ta fara bani labari akan wani abu da ya shige mata duhu ba akan kowa bane sai akan wani wai Yaa AK wanda yake koya mata karatu.”
Gaban sa ne ya fadi jin an kira Yaa AK shi kadai wani lokacin sai yaji sunan yai masa amsa kuwa a zuciyar sa da kunnen sa wanda har abun ya fara bashi tsoro.
Umma.tace
“Tana fada min halin da take shiga na rashin sa da abubuwa wanda nagane son sa take tin a lokacin na farai mata addu’a Allah yasa kada tayi son maso wani domin kuwa na gane shi Yayan nata dan masu hali ne kaga ita zata sha wahala sai tausayin ka ya kamani.”
Dagowa tayi ta kalle shi tace
“Kwanakin baya ta shigo gida tana kuka da na matsa mata ne take fada min komai tsakanin ta da Yayan nata.”
Nan Umma ta fada masa duk yadda sukai da Aisha. Sannan ta daura da fadin
“Tin daga ranar da abin ya faru Aisha bata kara samun wata nutsuwa da kwanciyar hankali ba ina lura da ita sosai. Zuwan ka ne ma ya dan sa ta sake amman na tabbata da baka nan zata shiga wai hali dan damuwar ta zata fi haka.”
Shiru sukai gaba daya. Umma ta mike ta duba pepper soup din da take sannan ta dawo ta duba zogalen da take turarawa ta dauki tunatur da albasa da cocumber tana yankawa sannan tace
“A gaskiya Muhammad na gane Aisha na tsananin son Yaron nan domin tin lokacin ban kara ganin walwalar Aisha ba kuma nasan ba zai rasa nasaba da rashin zuwan sa ba wanda na zata korar sa tayi amman tacr min a’ah bata kore shi ba.
Muhammad kada kaji haushin Aisha ko kadan domin tana son ka kaima amman a gaskiya yadda na lura tafi son Yaron can duk da akan ka ta danne komai ta kori komai ta sadaukar da farin cikin ta dan samuwar naka hakika Aisha na son ka so bakadan ba amman a gaskiya naga alamar son da take maka bai kai wanda takewa Yaron can ba. Kuma in ka aure ta tamkar ka auri gangarar jikin ta ne zuciyar ta da ruhin tana wani wajen. Na bata shawara akan ta duba ta gano *wa tafi so?* amman tace min kai kai bayan kuma nasan ba haka bane tana yin haka ne dan alkunyar ido na tana yin haka ne dan son da take maka tana son ta sadaukar da farin cikin ta gareka wanda da matsala Muhamad domin duk yadda taso kyautata maka za asamu matsala tinda da son wani a zuciyar ta, ni ba zan so dukkan ku ku shiga wani hali ba wannan yasa na baka shawara dan ance inso cuta ne hakuri magani ne. Kai na miji ne kai ya kamata ka hakura ita ta samu zabin ranta.
Ba dan na fison Aisha ba sai dan samar muku masalaha da nutsuwa ina fatan zaka dauki shawara ta. Kuma kana gani tin kan aje ko ina an fara samun matsala da karancin shekarun ta jinin ta ya hau gaba me kake tunanin zai faru ba dai fata nake ba.”
Shiru yayi zuciyar sa na bugawa da karfi da karfi shin yaya zaiyi me zaicewa Umma gaba daya kan sa ya dau caji yai masa nauyi. Itama Umma batai masa magana ba sai mikewa da tayi.
Kiran sallah magariba ya jiyo wannan yasa ya mike jiki a matukar sanyayeya isa yai alwala ya fita asallaci. A masallaci bayan an idar da sallah zama yayi kawai yai shiru gaba daya kwakwalwar sa ta kasa masa ko wannen tunani tunanin sa daya tayaya zai samar wa Aisha farin cikin ta.
Bai aune ba sai jin kiran sallah isha’i yayi haka ya mike akai sallah dashi sannan ya kara wani zaman. Har karfe tara sannan ya mike jiki a sanyeye ya fito har ya shiga gida sai ya juya ya koma gun mai fura ya sa aka saka mata nono da kwakwa da madara aka dama aka juye a roba ya biya ya taho gida.
A tsakar gida ya samu su Umma da Baba tin daga sallamar sa Baba ya gane ba lafiya ba. Durkusawa yayi ya gaishe su sannan ya mike ya nufi dakin Aisha. Umma ce tace
“Ga pepper soup din nata fa.”
Juyowa yayi dauki flask din ya nufi dakin nata ba tare da yai magana ba.
Tana cikin bargo ya shiga da sallama da kyar ta amsa masa saboda yadda kan ta yake ciwo. Zama yayi a gefen katifar ya yaye bargon yana kallon ta cikin so da tausayi. Hannun sa ya kai ya dafa kanta yaji zafi sosai har jikin ta.
“Kinci abinci?”
Kai ta girgiza sai hawaye ya fara bin fuskar ta. Dagota yayi ya zaunar yasa hannu ya fara goge mata hawayen yace
“Menene na kukan to Aisha? Ko jikin ne?”
Baki ta tabe masa zatayi kuka yace
“No don’t cry please kinji Aisha!”
Ya dauko Flask din ya fara bata pepper soup din. Nama daya taci ta kautar da kanta. furar ya bude ya dauki spoon ya fara bata tana sha tana masa shagwaba sai biye mata yake har tasha rabi sannan ya ballo magani ya bata da kyar ta sha sai da ya bari ya tsarga mata sannan ya maidata ya kwantar ya ja mata bargon ya mike ya fita. Yana fita bacci ya dauke ta da tunanin Yaa AK.