WA NAKE SO CHAPTER 16
Www.bankinhausanovels.com.ng
Yana shiga daki ya zauna a bakin katifar sa yana mai rike kan sa. Tausayin Aisha na kara ratsa zuciya da dukkan jikin sa. Hakika bai taba kawo wannan ranar a ran sa ba wacce zai iya cire son Aisha a ransa amman dole ya daure yayi haka ko dan yin biyayya ga Umma sannan ko dan samuwar farin cikin Aisha.+
Yana son Aisha har bai son adadi ba lallai zai mata abinda take so ko ta samu sauki a ranta. Yana zaune Umma ta shigo rike da kwanon abincin sa. dagowa yayi ya kalle ta. ta ajiye tace
“Ban fada maka wannan maganar dan kaima ka sa damuwa a ranka ba, na fada maka wannan maganar dana warware wannan matsalar ina fatan ka gane.”
Kai ya gyada yace
“Insha Allahu komai zai warware Ummah na.”
“Allah maka albarka ka ci abincin sai da safe!”
Ta juya ta fita. abincin ya dauka zai ci sai yaji ina ba zai iya ba taya zai iya cin abinci zai rabu da masoyiyar sa. Dukka tsarin sa da komai akan Aisha yayi su yanzun komai zai tarwatse masa kenan.
Alwala yayo ya kwanta amman sam ya kasa runtsawa tunanin Aisha ya gama cika masa zuciya da ruhin sa can wajen sha biyu ya mike ya dauro alwala yazo ya tada sallah ya jima yana sallah sannan ya fara karatun alkur’ani wanda ya sa ya fara jin sauki da nutsuwa a cikin ransa.
Har asuba idon sa biyu sai da yayi sallah asuba sannan ya dawo take bacci ya dauke shi mai nauyi kuwa.
*
*
*
Sosa jikin Aliyu ya tashi dan likitoci kansu sai da ya dau caji da kyar suka samu numfashin sa ya dawo sukai masa allura sannan yankoma bacci yana mai fadi
“Aysher!”
Sosai jikin yan uwan sa yai sanyi da ganin halin da yake. Abbah yana dakin da Mamah take sai lallashin ta yake. Sai da taji ance Aliyu na bacci sannan ta samu nutsuwa.
Tare suka je ta gansa sannan tai tayi masa addu’a tana tofa masa.ita kanta Hajara sai da Aliyu yai matukar bata tausayi yadda ta ganshi kwance sanye da oxygen dan har da hawayen ta. Haka suka kare zaman asibitin ranar sai wajen sha biyub dare suja tafi gida.
*
Washe gari da safe.
Zaune suke a falon dakin. Aliyu na ciki har lokacin yana bacci dan da ya farka suke karai masa allurai sai ruwa dake ta shiga jikin sa Maryama da Hajara na cikin dakin a wajen sa.
A falon kuma Abba ne da Mamah sai Yaa Abubakar, Yaa Usman, Umar, Farouk, Faisal sai Doctor dake duba sa. Bayan Doctor ya gamai musu bayanin duk abinda yake akwai ne ya mike yace
“You have to do your best to find out what he want or don’t want. I wish you all the best and Quick recovery to him “
Yana kaiwa nan ya fita. Shiru dakin yayi kowa akwai abunda yake sakawa can Yaa Abubakar yace
“Na tsorata jiya domin Aliyu har wasiyya ya fara barmin yadda naga jikin sa ya tashi yasa na fara zaton da gaske mutuwar zaiyi shiyasa ya bar min wasiyya amman abinda yafi dauren kai a wasiyar tasa yadda yake nananta min akan na tsayawa wata yarinya a harkar karatun ta. Shin wacece wannan yarinyar shine abinda nake so na sani.”
Shiru sukai. Faisal ne ya sauke ajiyar zuciya sannan yace
“Ban san me zai damuwa Aliyu ba har da zai kawo masa wannan ciwon amman ina zaton akan Aisha ne!”
STORY CONTINUES BELOW
Yaa Abubakar yace
“Yauwah sunan yarinyar da ya fada min jiya. Did you know something?”
Kai ya gyada yace
“Da jimawa mun hadu dashi a saudiyya tin bayan da muka gama secobdary school sai ta waya ko chat muke haduwa amman face to face bama haduwa tin a school ni nake iya rayuwa da AK. To zuwan sa saudiyya mun hadu wanda anan ne yake bani labarin Aisha shima bai fito ya fada min ba da farko ya nunan yana son ya koma gida nace yana missing family ne yace a’ah sister sa. The way yake fadan yadda yake missing nata na gane ba sister sa bace uwa daya uba daya wanda yadda yake fadar abu akan ta da kaji zaka san akwai soyayya da kyar Aliyu ya fada min ko wacece ita.
Ya hadu da ita a garin da yake yanzu wanda haduwar su Allah ne ya hada su kuma yarinya ce karama amman tana da kaifin basira da ilimi sosai ta canjawa Aliyu tunani da tsarin sa. Zan iya cewa ita ce babbar mai bawa gwamna shawara duk da bata san shine gwamna ba.”
“Kamar ya?”
“Yaje mata as a sibling to governor.”
Nan ya basu labarin akan haduwar tasu kamar yadda Aliyu ya tsokata mishi kadan daga labarin nasu.
“AK ya kasa bayyana mata wanda da kyar nayi convicing nasa ya fada mata amman fa bai fada mata ba. A haka ya cigaba da dawainiyya da soyayyar ta, ganin ba zai fada mata ba yasa na bashi shawara akan ya fara nuna mata so da kulawar sa wanda har ya bayyana mata yana son ta amman sai ta fada masa tana da wanda zata aura wanda wannan ya zama kamar yaya a gunta dan cousin nata ne kuma ita ba zata iya cewa ba zata aure shi ba. But a yadda na fuskanta lallai Aisha na son Aliyu kawai dai ba zata iya kin auren dan uwan nata bane.”
“Wacece Aisha?”
Abbah ya fada. Mamah tace
“Tabbas ita ce.”
“Ita wa?”
“Ita ce wacce tazo a ranar da muka baro garin.”
Mikewa yayi ya kalli Yaa Abubakar yace
“Ka samar min jirgi mai tashi a yau.”
Sannan ya fita a dakin. Fita Yaa Abubakar yayi dan samar masa jirgin. Mikewa Mamah tayi tabi bayan Abbah.
Tana fita taga zai shiga mota da sauri ta karasa ta shiga suka koma gida. A falo ya zauna ta zauna a gefen sa tace
“Ya dai Alhaji?”
“Kinsan tin ranar na lura da ganin ta da Aliyu yayi ba karamin kwanciyar hankali da jin dadi ya saukar masa ba. Kuma kiga yadda yake damun mu akan yaushe zata zo yana son ya ganta. Kuma kina jin yadda yarinyar ta canja rayuwar Aliyu lokaci guda da kuma irin mahimmancin da take da shi a rayuwarsa. Sannan ni kaina jiya naji duk wayar da sukai da abubuwan da ya fadawa Faisal. A da Aliyu bai san so ba kuma bai san yaga mace yaji wani abu game da ita ba dan ni nasan waye shi na tambaye shi zabin sa kan nai masa aure ya bani zafi dan bai da zabi akan mace yau Allah ya nuna min zabin Aliyu Alhamdulillah.”
Ya kalle Mamah ya ce,
“Wannan yana nufin Aisha ita ce samuwar lafiyar sa da farin cikin sa. Dan haka ba abinda zamuyi masa sai mu aura masa yarinyar nan, saboda ya na da matukar mahimmanci Aliyu ya cigaba da rayuwa domin karasa abinda ya fara ina son ganin iyayen yarinyar nan”
Umma ta girgiza kai ta ce,
“Alhaji yarinyar da an mata miji a yadda mukaji labari an kusa musu aure kuma itama ta fadawa Aliyun haka”
Abbah Ya kalle Mama yace,
“Wani miji ne da ya fi Aliyu, duk wanda ya samu Aliyu a matsayin miji ya dace yaro ne mai ilimi da amfani dashi ga tarbiyya. Babu wanda zai ki Aliyi babu wanda zai ki gwamna, babu wanda zai fi gwamna dan sarki ? Kuma ba zata taba samun miji mai son ta kamar Aliyu ba mutum da ya fi son farin cikin ta akan nasa, mutumin da ya yadda ya mutu ita ta rayu, mutumin da ya sadaukar da rayuwar sa akan ta, mutumin da ya bata lokacin sa, kulawar sa, soyayyar sa wanda bai duba matsayin sa da mulkin sa ba. Hakika Aliyu ya fi cancanta da Aisha.”
Numfashi Abbah yaja sannan ya kalle ta ya ce,
“Abinda Aliyu yake so zai samu ko aure aka daura mata za a warware shi bare kuma ba a daura mata aure ba”
Dogowa Mamah tayi ta kalle sa cikin fuskar damuwa ta ce,
“Ranka ya dade ban san ka da haka ba, na san ka da adalci da tausayi kar son danka ya makantar da kai, mu bi abin nan a hankali. Sannan shi kansa Aliyu bai son abinda zai taba ran yarinyar nan”
STORY CONTINUES BELOW
Ya kalle ta yace,
“Haka ne Fulani ni sarki ne mai adalci kuma zanyi bakin kokari na wajen ganin anyi adalci kuma adalcin kenan da zan mata ta auri miji irin Aliyu burin ko wace mace a duniya ta samu mijin da zai mallaka mata komai, kima, daraja, dukiya, daukaka, so da kulawa, tausayawa komai za ta same sa a karkashin inuwar Aliyu me ya fi wannan ? Bayan kinji ance itama tana son sa. Ba Aliyu kadai zan wa adalci ba zan yiwa ita kanta yarinyar adalci dan ta samu cikar burin ta da nutsuwar ta zanyiwa Shi wanda zata aura adalci dan na takaita masa wahalar da zai sha bayan ya auri wacce take son wanin sa, sannan zan takaitawa iyayen ta wahala akan fuskantar damuwa da zasu fuskanta a tsakanin ya’yan nasa a karshe zan yiwa d’a ba adalci dan ya samu mace mai ilini da tarbiyya wacce zata zama mai masa jagora ga aljanna Sannan ina son jika na dan Aliyu ya fito daga tsatson yarinyar nan. meyafi wannan adalaci Fulani?”
Kai Mamah ta gyada kawai dan ta kasa magana ma. Mai gidan nata yana da gaskiya kuma tasan ba zai abinda ba dai dai ba shi sarki ne adali. Ta yadda take godiya ga Allah kenan dukiyar su ko mukamin su bai sa sun canja daga yadda suke wajen riko da addini, tausayi da adalci ba.
Abbah yace,
“Tinda yake bawa Faisal labari nasan yarinyar ba banza ba domin duk Yarinyar da Aliyu ya gani ya yaba har ma ta birge shi, har ma ta iya canja masa rayuwa da tunani lokaci guda, har ta iya jefa shi a wannan hali saboda rashin ta ba karamar mai baiwai ba ce. Dole akwai wani abu, wata baiwa da Ubangiji ya mata wanda zan so hada zuriya da ita, jininta da na Aliyu zai haifar da wani abu mai daraja. Ya kike gani Fulani.”
Ita dai Mamah jin sa take kawai tana tunanin kar aje iyayen yarinyar suki yadda fa. Tasan Mai martaba zai iya komai dan samuwar yarinyar nan ga dan sa amman kar aje ayi ta wata hanya da bata dace ba. Kamar yadda take son Aliyu haka take ji wata soyayyar Aisha aranta sosai. Dan haka a zuciya take addu’a tana fadin
“Ya Allah ka gyara wannan al’amari ka tsira da wannan yarinya daga fadawa halaka ka zaba mata abun da yafi alheri, Allah ka tabbatar da alkhairi a rayuwarta.”
Wayar Abba ce ta dau kara ya zaro yaga Abubakar ne dauka yayi. Yaa Abubakar yace
“Abbah kana ina?”
“Ina gida!”
“Ok an samu nan da thirty minute zai tashi amman a Abuja zai sauka.”
“Ok gani nan bari na karaso.”
“To!”
Ya kashe wayar ya kalli Mamah yace
“Lafiya Fulani ta?”
“Ranka ya dade ina tsoro ne!”
“Tsoron me Rashida? Dan Allah kada ki karyar min da gwiwa mana ki bani kwarin gwiwa yadda zanje na gudanar da abun zai kai ni ki min addu’a.”
“Allah bada sa’a.”
“Aliyu Fulani na. Zan tafi airport zaki rakani ko zaki koma asibitin.”
“Muje na raka ka sai na koma asibitin.”
Suka fita suna zuwa airport din basuyi minti goma ba su Abbah su Abbah suka fara harama. Da zai tafi ya dafata yace
“Ina bukatar addu”ar ki Fulani.”
“Allah tsare ya bada sa’a!”
“Amin nagode sai kinji ni.”
“Ayi adalci ya sarkin mai adalci da tausayi da son talakawa.”
Juyowa yayi yace
“Insha Allah!”
Juyawa sukai suka tafi asibitin. Aliyu yana kwance tamkar gawa ba abinda yake motsi a jikin sa sai ta jikin computer da suke ganin yadda numfashin sa ke tafiya.
*
Tin kan su tashi ya fadawa President cewar gashi nan sauka a garin sa. Wannan yasa kan ya sauka an turo tawagar masu tarbar sa da bashi tsaro. Bagare guda aka sauki Mai martaba.
Wanka kawai yayi bai bi takan abinci ba ya dauki wayar sa ya kira mr president yana dauka yace
“Kazo yanzu please.”
Ya kashe waya.
Mamah ya kira yace
“Fulani na sauka lafiya.”
“Alhamdulillab kaci abinci?”
“Ba zan iya ciba har sai na cikawa Aliyu burin sa. “
“Haba Alhaji Ranka ya dade. Dan Allah ka daure kaci.”
“Wallahi ba zan ita ba. Ya jikin nashi ya tashi?”
“A’ah har yanzu dai nima dazu nai musu magana suka ce ba matsala baccin ake so yayi da yawa.”
“To Allah bashi lafiya ki cigaba da min addu’ar sa’a.”
“Allah bada sa’a.”
“Amin!”
Ya kashe wayar.
Ba ai minti biyar da gama wayar sa da Mr president ba ya shigo dakin da sallama amsawa Mai martaba yayi. Mr president yace
“Ai na barka ka ne ka huta ka dan samu nutsuwa sai in shigo.”
“Kasan ba zuwan dadi nayi ba.”
“Haka ne ya jikin Aliyun?”
“Da sauki Zuwan kenan daman.”
Kallon dining Mr president yayi yace
“Baka ci komai ba ai Alhaji Kabir!”
“Sam bana jin yunwa Alhaji Ahmad abinda ya kawoni nake so naje na aikata kawai.”
“Me ya kawo ka?”
“Akan danka ne Aliyu game da rasbin lafiyar sa.”
Nan ya fadawa Mr president komai a takaice sannan yace
“Yanzu haka zanje nemar masa auren yarinyar ne ina fatan za a dace”
“Haba Alhaji Kabir menene zaka tashi hankalin ka yar wacece ita yarinyar?”
“Ba yar kowa bace mahaifin ta mai rufin asiri ne.”
“Shine ka tashi hankalin ka. Ka kwantar da hankalin ka ko a yanzu kake son a daura auren zan iya sawa a dauko ubanta a daura musu auren.”
Murnushi Mai martaba yayi yace
“Nima ina da wannan ikon Alhaji Kabir amman ka sani mu muke nema dole mubi komai a sannu kuna aure zamu hada ba wani abu ba muna neman saka albarka da yin abu a mutunce.”
Shiru Mr president yayi. Mai martaba ya mike shima ya mike yace
“A gaskiya ban taba haduwa da mutane irin ku ba Alhaji Kabir Allah ya baku dukiya mulki da iko amman sam basa gaban ku komai kuna ui saffa saffa. Zamana da Aliyu ba karu da abubuwa da yawa kamar tsoron Alah gaskiya da rashin cin amana kuma na gane wannan gado yayi daga wajen ka. Ka sani dani za’aje nemarwa Aliyu aure ko a ina ne kuma zan tsaya masa da dukiya ta da komai nawa.”
Rumgume shi Mai martaba yayi yace
godiya nake.”
“Amman ai ya kamata kaci wani abu ko?”
“Bazan iya ba.”
“Haba a samo maka ko soft abu mana.”
“Muje kawai Alhaji Ahmad.”
Ba yadda Mr President yayi haka suka fita yasa aka dauko private jet nan suka hau sai garin su Aisha. Security na buye dasu wasu a kita suka mara musu baya wasu kuma na tare dasu.