WA NAKE SO CHAPTER 18

 WA NAKE SO CHAPTER 18

Www.bankinhausanovels.com.ng 

Zaune suke Najah da Khady sai Jidda. Jidda ta zuba tagumi tana kallon su. Najah ce ta ce

“Ji yadda kika koma akan kishiya kawai na fada miki ki kwantar da hankalin ki amman kinki ko?”+

“Hmm tayaya hankalina zai kwnata daga cewa jibi zakizo yau sati nawa Najah kenan damuwa ta ba taki bace ko?”

“It is not that Jidda ki tsaya kiji me ya zaunar dani.”

“Ina ji.”

“Na raka matar Sarki china ne.”

Tsaki ta saki tace

“Dan ta fini arziki kenan ko?”

“Dan wa naje in ba dan ke ba Jidda wallahi danke na bita.”

“Ni kuma?”

“Eh mana wajen wani malami na rakata nima anan na bada bukatar ki kuma yace in jira kawai amman fa da matsala.”

“Tame?”

“Yace kan bikin dole na koma kamar da sati biyu haka!”

“To ya za ayi Najah ina naga kudin da zan baki kije china.”

“Hmm kada ki damu zamu koma da ita to kinga dalilin da yasa kika jini shiru fa.”

“Amman nagode na zata kin manta dani ne.”

“Wallahi kina raina.”

“Thank you.”

“Yanzu saura wata nawa?”

“Wane din wata nawa? Wata nawa aka saka ma?”

“Oho?”

“Wata biyu aka saka fa. Gashi mun shigo sati na uku!”

‘Kenan nan da sati uku zan koma ko?”

“Eh mana.”

“To ki tuna min.”

“Insha Allahu.”

Khady ce ta dago tace

“Ke Najah dadi na dake karya fa.”

“Kamar ya karya!”

“Eh mana duk malaman garin nan sai kinje china.”

“Sunfi aikine!”

“Karyar kenan. Ai sai dai baki hadu malami mai kyau ba.”

“To me kenan!”

“Naje wajen wani malami wanda nace so nake a sa yarinyar taki aminta da auren kunsan me yace min cewa yayi ita daman ba son auren take ba iyayen ta ne da shi mijin naso ai aiki a kanta dan ta kara kin abun ammam yace yarinyar ba zaune take ba tafi karfin sa. Wanda yanzu nace afara aiki akan Iyayen kawai.”

“Good job Khady.”

Jidda ta fada. Najah tace

“Amman meyasa akan iyayen ba akan mijin ba.”

Jidda ta zaro ido tace

“A’ah kul wallahi kada a taba lafiyar miji na a yi iya su dai can.”

“Hmm!”

Najah ta fada ta mike tace

“Ni zan tafi Jidda ki tunamin fa.”

“Ok nagode.”

Ta fita a bakin gate suka hadu da Sady sama sama suka gaisa tayo cikin ita ta fita.

Khady na ganin Sady ta mike ta rumgumota. Suka zauna tana kallon jidda tace

“Uwar kiga a gidan Alslam!”

“Amarya kuma ba.”

“Ke ni ba da wani abu na fada ba.”

“Koma dai dame kika gada.”

“Ina sauri ne ina kan hanya.”

Ta fada tana bude haka.

Invitation ta dauko ta ajiye akan cinyar Jidda sannan ta mikawa Khady tace

“My weeding next week!”

STORY CONTINUES BELOW

Ta fada ta mike ta fita. Jidda ta bita da kallo Khady tace

“Sady ta yadamu fa.”

“Hmm kyale ta zata dawo ne. Wai ai ita ta Allah.”

“Yanzu ya ake ciki?”

“Yana gunki ai nidai na baki wuka da nama please Khady!”

“Kada kiji komai Jidda.”

“Thanks!”

Ta shafa ciki tace

“Yunwa nake jifa.”

“Shiga kitchen ki zubo abinci.”

Ta mike tayi kitchen din.

*

2 weeks

Har lokacin sam Fateema bata taba tambayar waye mijin ba. Kullum suna tare da Aslam sosai ta saba dashi dan in bai zo ba da kanta take kiran shi su sha hirar su ko su fita ta samu farin ciki. A lokacin kuma aka kai lefe gidan Uncle Aminu lefen da ya amsa sunan sa lefe domin akwati set uku aka cika da kaya masu kyau da tsada da gwala gwale.

Kowa yaga kaya sai sam barka yana fadin Fateema tayi goshi sai kace ba bazawara ba Hajiyar Fu’ad kanta tazo taga kaya tai Allah sanya alheri ta yi Fateema fada sosia. Fateema kuwa ji take kamar a mafarki wai an kawo lefen ta. Zata kuma aure da wanin Fu’ad ikon Allah.

*

Tayi zurfi a tunain da take ya shigo office din duk sallamar da yayi bata ji shi ba har sai da yazo gaban desk din ta ya dan buga sanna ta dawo tana kallon sa. Zama yayi yace

“Wannan tunanin fa?”

Murmushi ta saki tace

“Ba komai!”

“Kin tabbata?”

Kai ta gyada. Yace

“Ya aikin?”

“Alhamdulillah!”

Shiru sukai can yace

“Ina son muyi magana ta fahimta Doctor!”

Juyawa tayi ta bashi duk attention din ta.

“Wa zaki aura ne Fateema?”

Hannu ta daga tai alamar bata sani ba. Kai ya dafe s ransa yana fadin

“Da akwai matsala kenan.”

Sai kuma ya dago yace

“To zan fada miki wanda zaki aura.”

Kallon sa ta tsaya yi ta kasa ko da magana ne bare wani motsi.

Yace

“Ni nan nine wanda naje neman auren ki Fateema!”

Ido ta zaro tana kallon sa. Ya gyada mata kai yace

“Eh nine Fateema boye boyen yai yawa na zata Uncle zai fada miki ashe bai fada ba harda aka kawo kaya naga baki sani ba a haka kika amsa zakiyi biyayya auren wanda baki sani ba. Ina son na samu soyayyar ki koyaya ne Fateema.”

Wani murmushi tayi kawai ta girgiza kai. Yace

“Eh na taba fada miki ina son ki soni ko yaya ne ko da bai kai kashi 1 a cikin kashi goma da kikewa Fu’ad ba. Fateema da gaske nake son ki ina son ki ina son na fitar dake daga damuwar da kike ciki ina son naga kina walwala ko da yaushe ban zo neman auren ki dan na raba ki da Fu’ad ba sai dan samuwar nutsuwar ki da kare ki.”

“Nagode sosai!”

Ta fada tana janyo system din gaban ta da sauri ya mike ya rufe system din ta dago tana kallon sa. Hannu yasa ya mikar da ita yace

“Ya zanki ce min kin gode kawai Fateema.”

“Me kake so ince Uncle ai na riga na hakura da komai a rayuwa na mika komai ga Allah na bashi zabi dan haka kome yazo min ina addu’a Allah ya bani ikon dauka me kake so nace maka bayan wannan Uncle?”

Tausayin ta ne ya kamashi ya hau girgiza kai yana fadin

“I want you to love me.”

Murmushi tayi tace

“Ai aure zamuyi Uncle,  kamar yadda ranan kafada ban san adadin lokacin da zamu dauka tare ba kila har tsufa watakila dai mutuwa to kaga akwai lokaci mai yawa a gaba. Amman ina godiya da son da kake min sosai.”

Ta koma ta zauna kallo ya bita dashi kawai ta bude syatem tana aiki komawa yayi ya zauna ya kasa magana sai kallon ta da yake haka suka kare yinin ranar dan sai da zata tafi ne tai masa sai da safe ta shige matar ta ta fita yabi bayan ta kamar yadda suka saba.

*

Sai da taje bacci ne abubuwa suka hau dawo mata kawai sai dai tai murmushi dan yanzu ta riga ta gama sarewa ta cire hope a rayuwar ta kawai ta fauwalawa Allah komai.

STORY CONTINUES BELOW

Shi kan sa Aslam abin ya bashi mamakin ganin har kwana biyu bata kara maganar ba sai dai suna mu’amala kamar yadda suka saba. Yanzu ma suna zaune a sitting room ne da yake yau weekend yazo gidan su. Tana zaune tana danna waya tana bashi labarin wata mara lafiya. Shi dai ya tsaya kallon ta kawai yana mamaki domin kuwa yanzu mamaki take bashi yadda take karfin halin yin abu ta nuna kamar bata da damuwa. Dagowa tayi jin yayi shiru taga yana kallon ta.

“Lafiya dai Uncle?”

Ido ya lumshe sanna ya bude yace

“Me yake damun ki fateema?”

Kallovjikin ta tayi itace

“Kamar yaya?”

“Kina boye abu a ranki tinda nai miki maganar auren mu baki ce komai akai ba.”

Murmushi tayi tace

“Na barwa Allah komai Uncle duk abinda ya faru dani shi ya zaba min.”

Shiru yai yana kallom ta sannan yace

“But you have something deep in you.”

“Ba komai araina Uncle.”

“Hmmm!”

“Yes ka yadda dani”

“Shikenan me kike ganin za a yi a bikin?”

Ido tayo waje dasu tace

“Kar ka manta ni ba bazawara ce ko Uncle?”

“Shine me zamuyi celebrating wedding dinmu as budurwa kike.”

“Haba dai ni bana bukata daurin aure ya isa kawai sai traditional sitting a gida.”

“Saboda bakya murna da auren ko”

Da sauri ta dago tace

“Don’t say so Uncle !”

“To in ba haka ba dan me za a kiyin shagali.”

“Dan neman albarka Uncle. Yinin ma is ok!”

“In haka ne a matso da abin next week kawai,”

Murmushi tayi tace

“Sauran fa two week in har aka dawo da shi zuwa week  ai munyi gajen hakuri me ya cinye sati dayan.”

“Hmm!”

“Da next week da upper duk daya ne Uncle.”

“Gaskiya ni da banbanci.”

“Ba kyau dai gaggawa.”

“Hmmm shikenan yanzu sai gyara da zakiyi ko nawa kike bukata.”

Murmushi tayi taxe

“Zanyi lissafi na turo maka.”

“Me zai hana kiyi yanzu?”

“Saboda kar na kasa zuba maka kudi masu yawa.”

Yai dariya yace

“Kamar gaske.”

Tai murmushi kawai.

*

Yau saura sati daya biki tin da ta tashi taji zuciyar ta na bugawa. Addu’a tayi kawai ta hau shiryawa amman gaba daya jikin ta a mace yake. Bayan ta gama ta fito tayiwa Mommy sallama.

Mota ta shiga tana tunanin me ta manta ko batai wani abu ba amman ta kasa tina ko menene. Haka ta karasa tayi aikin ta duk jikin ta a sanyaye sai da ta koma bayan tayi walha ne ta zauna ta jinginar da kanta a jikin bango ta lumshe ido. Da sauri ta bude idon ta ta mike domin yau kwata kwata basuyi waya da Aslam ba tin jiya da dare da sukai.yake fada mata baya jin dadi sai fama yake da faduwar gava. Tace yana addu’a to ko dai jikin ne?”

Ta fada tana daukar wayar ta dailing number sa tayi amman har tayi ringing ta gama ba a dauka ba. Ta kara yi shiru ajiyewa tayi ta koma ta zauna ta fara attending patient din ta amman duk ka bata cikin nutsuwar ta. Ganin bata iya abinda ya kamata ta tarkata patient din ta aika su wajen Dr Auwal.

Sallah azahar tayi ta zauna tana jan carbi bata tashi a gunvba sai kwanciyya da tayi har akai la’asar tayi sallah ta tashi ta gyara fuskar ta dan tasan ko wanne lokaci zai iya zuwa. Azhkar na yamma ta fara har ta gama bai zo ba. Shiru shiru har shida saura.

Wayar ta, ta dauka ta kara trying number amman bai dauka ba in hankalin ta yai dubu ta duk ya tashi. Jiki ba kwari ta koma ta zauna har shida da kwata tana asibitin ganin magariba ga gabato yasa ta mike ta kwashi kayan ta tayi gida hankalin ta a tashe.

A falo ta samu su Momy tai musu sannu da gida sannan tayi dakin ta kawai. Tana shiga ta watsa ruwa sannan ta dauro alwala. Sallah aka kira ta sha ruwa sannan ta hau kan sallaya. Tana zaunebhar akai isha’i bata da niyar tashi duk da azumi tayi amman bata jin yunwa.

STORY CONTINUES BELOW

Momy ta hada mata kayan shan ruwan ta nufi dakin ta. A gaban ta ta ajiye ta kalle ta da damuwa tace

“Me kuma ya faru?”

“Ba komai Momy bana jin dadi ne kawai.”

“To kici abinci ki sha magani ki kwanta sannu.”

“Yauwah.”

Ta juya ta fita. Tea kadai ta sha ta sha magani ta koma gado ta kwanta. Har karfe tara tayi goma tayi bai kira ta ba kamar yadda ya saba. Wayar ta ta dauka ta duba ko ya kira ita ce bataji ba amman abu mamaki ba missedcall.

Fara dailing number tayi ta shiga tana ringing ba a dauka ba sai da ta krra a na biyu sannan aka dauka

“Ina ka shiga Uncle?”

Ta fada a shagwabe. Wani tsaki taji an saki sannan akace

“Gidan ubanki ya shiga ke wacce irin dabba ce zaki hau kiran miji na da wannan lokacin in ke akayiwa zakiji dadi kinsan by dis time kowanne miji dai yana tare da matar sa ko amman ke kin kirashi saboda iskan….”

Bata karasa ji bata katse wayar kawai ta koma ta kwanta. Tunanin ta ne ya kasu kashi biyu to shi ina Aslam din ya shiga dan tasan bata taba waya dashi taji koda muryar matar sa bane Ita dai ta rude Allah yasa yana lafiya amman da bai da lafiya ai ba zata tsaya wannan haukan ba. A haka bacci ya dauke ta da tunani kala kala.

*

Washe gari ma abun mamaki ba kiran sa ko daya ita ma kumavbata neme shi ba dan tasan ai yaci ace yaga missed call dinta. Wannan yasa ta share shi amman again bai zo ba bai kira ba har dare.

*

The nest day ma same to yesterday Fateema duk ta rude ta tashi hankalin ta bata san ta damu da Aslam ba sai a kwana biyun nan da yai mata nisa har wani ciwo ciwo take ji na rashin ganin sa da rashin kiran ta.

Tunani ta hau yi sai kawai ta kira Noor bayan sun gaisa take fadin

“Antyn mu ya gida ga shirun biki? Wai me kuke shiryawa ne dazu Uncle ya shigo na tambaye shi ya min banza nace bari na tambaye ki.”

“Uhmm Noor kenan ya kuke yasu Jannah da Hajiya.”

“Suna lafiya.”

Sai tayi shiru can tace

“yaushe Uncle din yaxo?”

“Ai bai jima da fita ba.”

“Ya yake?”

“Kamar ya yake?”

“Eh mana yau ban ganshi ba.”

“Oh kila ai yazo yanzu ma inajjn.”

“Ok yana lafiya dai ko?”

“He is fine!”

“Masha Allah. Bari sai anjima.”

“Aha mu jima da yawa.”

Sukai sallama. Ta kashe wayar sannan tace

“To me yake faruwa meyasa bai dauki wayata ba bai kirani ba kuma bai zo ba ko dan yaga an bashi ni.”

Kai ta kife a kan desk din ta batai aune ba taji hawate na zubo mata dagowa tayi tana mamaki ta hau gogewa. Mikewa tayi ta kalli agogo har xata fita ta dawo ta zauna tana fadin

“Kar kuma yazo bana nan.”

Amman har bakwai bai zo ba tayi sallah ta tafi gida. Momy ta sama a falo tace

“Sannu da gida!”

‘Yauwah ya kike wai meyasa kike kai dare kwana biyun nan ne Fateema? Kefa haka kike da zurfin ciki da saka damuwa a ranki haba Fateema me kuma ya faru?”

“Bafa komai Momy kawai bana jin dadi ne.”

“Tayaya zakiji dadi kina da damuwa kin ki ki fadawa kowa?”

Idon ta ne ya kada yai ja sai kawai tayi kasa da kai. Momy tace

“Menene Fateema?”

“Momy yau kwana uku bamuyi waya da Uncle ba kumabko zuwa bayayi!”

“Shine kike damuwa Fateemabkika sani ko aiki ne yai masa yawa.”

“Aiki Momy da da yake zuwa din fa kuma yai ta kirana a waya fa.”

“Kinga ki kwatar da hankalin ki yana lafiya ba wani abu bane kila abubuwa ne sukai masa yawa ba yace wannan satin zai kawo invitation ba ki tsaya ki gani zai kawo miki ki daina wani damuwa kinji. Allah na tare dake.”

STORY CONTINUES BELOW

“To Momy nagode.”

Ta mike tayi daki.

Wanka tayi ta fito dan ta samu ta debe kewar dake damun ta na suka zauna su da su Baba da yasmeen ana ta hira sai goma suka koma daki kowa ya kwanta.

Wayar ta aduba ko zataga kiransa amman babu dan haka ta ajiye kawai.

*

Washe gari tana office ta dauki wayar amma ta fara kiran layin sa. Ba a dauka ba dan haka ta ajiye kawai sai kuma ta kara dauka ta kara dailing amman har ta katse ba a dauka babajiyewa tayi tana fadin

“To me hakan yake nufi?”

Shiru tayi tare da dafe kan ta dake mata ciwo dan damuwar da ta saka. Take Fu’ad ya dawo mata duk rashin Fu’ad ne ya jefa ta a wannan halin da take ciki da tana tare dashi da ta ina ma zata san wani Aslam da har zai zo yana kin daukar wayar ta.

“Come back soon My Fu’ad!”

Ta fada tana fashewa da kuka. Tare da fadin

“I miss you i really missed you.”

Mikewa tayi ta kwashe kayan ta ta fita ta shiga mota  ta tayar gidan Suraiyya ta nufa kai tsaye kawai Tana shiga ta same ta a falo tare da yan biyun ta Umar da Abubakar da aka kiran su Farouk da Sadeeq.

Daukar Umar tayi tana fadin

“Babana ya kake?”

Tai kissing nasa a kumatu sannan ta dauki Abubakar ta ce

“my son ya kake kaima”

Suraiyya tace

“Daga ina?”

“Asibitii nazo duba ya’ya na.”

Tai mumusrshi tace

“Ko!”

Ta mike ta kawo nata ruwa da tace

“Uhmm amarya ai na zata kin ajiye aiki sai bayan biki.”

“Uhmm!”

Ta fada ta dauki ruwa ta sha sannan ta daura Farouk a kafadar ta tana fadin

“Sleep swt Dad!”

Kamar yasan me tace ya rufe ido cikin minti kadan yai bacci. Ajiye shi tayi ta dauki Sadiq shima tana jijjiga shi take yai bacci.

Ta ajiye shi shima. Tace

“Yunwa nake ji amman bana son cin komai Sis.”

Dariya Suraiyya tayi tace

“Tin yanzu kin daina cin abinci haba sister fargabar me zai dame ki uhmm?”

“Ke yar iska ce ni bace ina fargabar wani abu to me zanyiwa fargaba ehhh?”

“Uhmm wai ke baki fara dan gyaran nan ba da hade hade kina cin abinda na kawo miki ma kuwa?”

“Dan Allah kyale ni da wannan tarkacen.”

Ido Suraiyya ta zaro tace

“Hmm bari ki shiga zaki nema da kanki ne.”

“Naji.”

Suraiyya ta mike ta shiga daki Fateema ta zuba ta gumi ta tafi tunanin da ta saba. Suraiyya ta dawo rike da leda tace

“Yauwah ga hadin sabulun da na sa akai miki zai kara miki taushin fata da shekin ta wannan kuma kina sha da madara wannan kuma ki jika ki kina kama ruwa dashi kin gane?”

Jin shiru yasa ta dago taga sam Fateema ma bata san abinda take yi ba. Kallon ta ta tsaya sai ta ga ta kara ramewa akan yadda take mikewa tayi ta koma kusa da ita tace

“Sister!”

Sannan ta dafata dagowa tayi da sauri tana mai sauke ajiyar zuciya.

“Menene yake damun ku kin sauya ga shi duk kin rame tunanin me kike?”

Kai ta girgiza. Suraiyya tai murnushi tace

“Kada ki manta ba zaki boyen komai ba domin nice abokiyar shawarar kickamar yadda kike tawa. Rashin fadamin zaisa nima na rasa sukuni na na shiga damuwa dan Allah ki fadamin meyake damun ki?”

Dagowa tayi ta kalle ta sai ta dauke kai tayi shiru. Hannun ta,  ta kama tace

“Please!”

Idon ta ne yayi ja tace

“Ba son sa nake ba amman ya sabar min da kasancewa dashi ya sabar min da kulawar sa ya sabarmin da bani lokacin sa amman yanzu ya daina.”

“Waye?”

“Uncle mana!”

“What meya faru ni bangane ba.”

“Sam bana son Uncle Sis amman ya shiga rayuwa ta ta karfi da yaji ya zamo kullum muna tare in ya tashi a aiki kulawar sa ba wacce bana samu zai kiran safe rana dare weekend kuwa da kyar yake kaiwa har ta kai ta kawo ya fara zuwa gida bansan ya aikai yaje ya samu Uncle ba kawai sai ji nayi wai an badani ban san wa aka bawa ni ba sai ranar da aka kawo lefena yake ce min shine to zanyi haka na amshi shi amman cikin kwana ukun nan na kasa gane kan sa Sis ya daina daukar waya ta. Da na kira shekaran jiya da dare bai dauka ba da rana ma haka sai da dare matar sa ce ta dauka ta zage ni,  da nayi fushi nima jiya ban kira shi ba kwata kwata amman na kasa jurewa yau na kira da safe shiru yanzu ma fa na kira shiru.”

Ta fada cike da damuwa. Suraiyya da kanta ya kulle tace

“Ikon Allah kuma yana nan lafiya?”

“Yana nan wallahi dazu munyi waya da Nur tace yanzu yazo ya tafi. Na tambaye ta ya yake tace yqna lafiya to me nai masa nayi tunanin na hanga na hango banga laifin da nai masa ba dan Allah yaya zanyi Sister?”

“Inna lillahi wainna illahir rajiun.”

“Ya zanyi ni kwai na damu da rashin kiran sa ne ya riga ya sabar mun tayaya lokaci daya zai janye jikin sa dan Allah.”

“Indai haka net to akwia dole abinda kikai masa”

“Wallahi ba abinda nai masa. Kinji na rantse.”

“Ok give me his phone number!”.

Wayar ta ta dauka ta saka mata number sa sannan ta bata. Dailing ta farayi.

Wayarta ta dauka ta saka number sa sannan ta bata. Dailing ta farayi. Ringing daya biyu ya dauka da sallama. Amsawa tayi sannan tace

“Ina yini?”+

“Lafiya Alhamdulillah!”

“Ya aiki?”

“Alhamdulillah!”

“Suraiyya ce sister Fateema.”

“Oh ya akayi?”

“Uhm daman na bugo ne naji ya zancen tsare tsaren bikin ita taki ta fada min komai”

“Oh bata fada miki ba to ina jin bata shirya ba shiyasa ki kyale ta duk randa ta fada miki sai ayi.”

Murmushi tayi tace

“Kamar yaya?”

Wayar ya kashe dan haka ta shiga mamaki sai ta nuna kamar suna wayar tai dariya tace

“Shikenan in kun gama tsarawa aji tinda bakwa so aji shirye shiryen!”

Sannan tayi sallama ta dauke wayar. Fateema ta kalla da ta zuba mata ido tace

“Ya baki masa maganar ba?”

“Ki bari zan masa amman ba yanzu ba ai yanzu na tina masa dake nasan kila anjima ya kira ki dan jin shirin da kike zai neme ki dan Allah kada kisa damuwa ki mika komai ga Allah.”

“Insha Allah.”

“Yauwah me zan dafa miki?”

“Komai ma”

“Tashi muje kitchen din to”

Tare suka shiga suna girki suna hira har suka gama suka fito suka ci tare sai yamma ta koma gida. Tai mamaki da taga har lokacin bai kira ta ba. kai har ta kwanta bai kira ba. Text ta dauki wayar ta ta tura masa sai da taga delived report sannan ta ajiye tana jiran repley har bacci ya dauke ta.

*

Washe gari ma ba kiran sa bare reply bata kira sa ba sai Suraiyya da ta kara kira ta kai mata complain.

“Bari na kara kiran sa.”

Nan ta fara neman layin sa yana dauka suka gaisa tace masa Suraiyya ce yace

“To ya akayi ne?”

Da yadda yake amsa mata a tsatsaye ya bata mamaki dan suna yawan gaisawa ta wayar Fateema yadda suke hirar su cikin wasa da dariya da barkwanci dan haka sai jinin jikin ta ya tsinke daman tin jiya ma.

“Nace me yake faruwa tsakanin ka da Fateeman ne?”

“Ita tace miki akwai abinda ke faruwa to ta fada miki in akwai mana.”

“A’ah ka tsaya muyi maganar fahimtar juna. Fateema tace min baka daukar wayar ta ka daina kira da zuwa, in wani laifi tai maka ka fada mata dan Allah zata gyara.”

“In laifin tayi sai an fada mata ita ba zata iya dubawa ta gani ba.”

“Kasan….”

“Kinga ni ina da aikin yi dan Allah ki kyale ni.”

Ya kashe wayar.

Ido ta zaro tana fadin

“inna lillahi wainna illahir rajiun. Anya kuwa wannan Aslam ne?”

Kai ta girgiza tace

“Ni ya zanyi da Fateema.”

Bata rufe baki ba wayar ta ta hau kara dauka tayi taga Fateema ce gaban tane ya fadi ta danne ta tace

“Haba Amarya ki kwantar da hankalin ki na kira bai dauka ba kila yana busy ne amman zan kara kira anjima.”

“Shikenan dan Allah kada ki manta zan kira naji ko lafiya.”

“Insha Allahu.”

Sukai sallama.

*

Bayan awa biyu ta kara kira Suraiyya har fargabar dauka take. Dan kada taga bata dauka ba yasa ta dauka tace

“Kin kira?”

STORY CONTINUES BELOW

“A’ah ina aiki ne bari na kira.”

Ta kashe. Bayan thirty minutes ta kara kira tace

“Sis ya dauka?”

“Wallahi har yanzu bai dauka ba.”

“Ok bari na kira to.”

“No kada ki kira ki bari anjima zan kara trying kada ki damu.”

“Alright”

Kan ta koma gida ma sai da ta kara kiran Suraiyya amman Suraiyya tace bai dauka ba dai. Can ganin kar ta shiga damuwa da ta kara kira tace mata sunyi magana yana busy amman yace zai kira ta.

*

Ikon Allah har washe gari ba respond daga Suraiyya dan haka ta kara shiga damuwa da kyar ta dau shawarar Suraiyya ta kara kwana biyu bata kara neman sa ba amman duk a kage take wanda hakan yasata damu sosai abinda yafi bata mamaki har an shigo satin bikin ba wani magana daga gidan su Aslam sam.

Yau da safe tana fita ta zarce gidan Suraiyya. Suraiyya na ganin ta gaban ta ya fadi dan ita bata san kuma me zatace mata ba. Welcoming nata tayi ta zauna tace

“Suraiyya ya zanyi ne?”

“Me ya faru?”

“Uncle mana wlhy am missing him please ki kara kira muji ko lafiya kina gani satin bikin fa ya shigo yau tuesday fa.”

“Ok!”

Waya ta dauka ta fara dailing yana dagawa suka gaisa tace

“Suraiyya ce.”

Taaki ya saki yace

“Please Suraiyya kada ki kara kirana akan wata Fateema ki kyale ni dan Allah haba kullum ku kenan ku isheni da kira.”

“But Fateema tana cikin damuwa sosai wallahi.”

“Ta mutu ina ruwa na!”

Yana fada ya katse wayar. Shiru tayi fateema kuma tace

“Me ya faru?”

“Fateema ki kyale shi yana busy ne amman shawara zan baki kada ki kara kiran sa”

“Why?”

“Ni dai na fada miki.”

Ta mike tace

“Bari na karasa wanke wanke.”

Tayi ciki Fateema ta bita da kallo to me yake faruwa kenan. Kai ta jingina da kujera sai kuma ta mike ta bita kitchen din a a bakin kofa ta tsaya tace

“Ki fada min yaya kukayi Sis?”

“Yace yana busy ne fa kawai abinda ya ban haushi kenan shi kenan busy busy haka zakuyi tayi anyi auren.”

“Kira shi dan Allah ki karai masa magana kice muna satin bikin ina jiran sane fa.”

“Sis!”

“Dan Allah kinga ni in na kira bai dauka.”

“Daukon wayar.”

Tana daukowa ta fara dailing number sa yana dauka ta mika mata tace

“Amma kasan satin bikin ku ne ko?”

“Da wa?”

“Fateema mana!”

Tsakai yayi yace

“Na fasa to.”

“What?”

“Nace na fasa.”

Ya kashe wayar. Tai murmushi tace

“Yace yana sane ai.”

Kallon ta ta tsaya yi sai kuma tace

“Thank you. Bari na tafi asibiti.”

“To sis ki gaida Momy.”

Ta fita. Suraiyya ta jingina da bango tana tunanin ta yadda zata fadawa Fateema yadda sukai da Aslam. Mafita daya ta kira Momy tai mata bayani ita tasan yadda zasuyi in ma za aiwa iyayen sa magana ne su turo aji yake ciki to.

Hannu ta goge ta dauki waya ta fara kiran layin Momy. Momy na dagawa suka gaisa sai kuma tayi shiru momy tace

“lafiya Suraiyya.”

“Momy daman wata yar matsala ce.”

“To me ya faru?”

“Akan Fateema da Aslam ne!”

“İna ji!”

“Momy akan rashin kira da kuma rashin zuwa da bayayi ne shine ta kawon korafi da farko na kira akan zance shirye shiryen biki na kira naji ya ake ciki amman momy a yadda mukai waya ba dadin ji ya nuna wai ita  ta shirya ta fada mana me ta tsara sai ayi

Na biyu da na kira dan jin ko tai masa laifi ya nunan in laifi tai masa ita bata sani ba. Kuma fa ita bai daukar wayar ta.

Yanzu na kira na uku akan lokaci yayi sai ya nuna  shi bai san da wani zancen biki ba dana nuna masa sai cewa yayi to ya fasa.

Ni a ganina Momy ayiwa Abba magana yayiwa magabatan sa aji meyake faruwa dan a gyara barakar ko?”

STORY CONTINUES BELOW

“Inna liahi wainna iahir rajiun. Haka ne Suraiyya zan je yanzu wajen Aminun kan ya fita na fada masa.”

“To Momy.”

Sukai sallama. Hijab ta sako ta nufi dakin Baba a zaune ta same ta bayan ta idar da walha ta zauna tace

“Baba daman zani gidan Aminu ne akan zancen auren nan.”

“Toh. Meya faru?”

“Baba sam yanzu ya daina kira da daukar wayar ta kumabda sukai magana da Suraiyya sai cewa yayi ya fasa to abin dai yara kinsan zanje nai masa bayani in yaso a kira shi da magabatan sa aji ko menene ko?”

“Eh Haka ne. Kije ki masa bayani sosai a kuma kira iyaye  yaron aji me ya ke faruwa dan kinga wannan satin shine satin karshe a saka ranar da akayi ko?”

“Shine.”

“To maza kije. Allah ya kiyeye ya zaba abinda yake mafi alheri.”

“Amin!”

Ta fita sai gidan Su Suraiyya tana zuwa matar sa ta tarbe ta bayan sun gaisa tace

“Aminu ya fita kuwa?”

“A’ah yana ciki.”

“To ki min magana dashi.”

Ta shiga ta fada masa ta fito tace

“Kije.”

Dakin ta shiga da sallama sannan ya amsa ta zauna suka gaisa sosai. Har sun taba hira sannan tace

“yauwah akan Fateema nefa!”

“To to meya faru?”

Nan ta fada masa komai sannan tace

“Yanzu kai me.kake ganin za ayi.”

“To zan musu waya inji ko menene akwai insha Allahu amman ku kwantar da hankalin ku yaron yana son yarinyar dan da aka saka lokacin bikin cewa yayi yai yawa da kyar ya hakura dan mahaifin ya fadamin wai a kara neman a rage sukaki amman akan me zai ce ya fasa koma dai menene zan kira baban nasa baricma na kira kiji komai.”

Ya fada yana daukar wayar sa. Number Alhaji Yahya ya fara kira. Yana dauka suka gaisa yace

“Af kaji ni shiru ko dazu nake cewa ya kamata a fara rabon kati zan kira Baban nawa naji me ake ciki.”

“Daman wata matsala ce ta taso nake son kazo mu hadu muji kome za a yi akai.”

“To Allah yasa ba wata babba bace.”

“Eh ba wata babba bace.”

“To shikenan insha Allahu anjima ina tafe.”

“Allah kaimu.”

“Amin!”

Sukai saama. Uncle Aminu ya kalli Momy yace duk yadda ake ciki zakiji insha Allah. Komai zai zo da sauki.”

“Allah yasa.”

Nan tace

“To ni zan tafi sai naji kan.”

Ta fita tayiwa matar sa sallama ta koma gida. Baba tayiwa bayanin komai Baba tace

“To Allwb yasa muji alheri.”

“Amin.”

Momy ta amsa.

*

**

***

****

*****

******

*******

Murmushi kawai Aisha tayi ta gyara kwanciyya kamar ba zatai magana ba sai tace

“Ina son sa amman kuma Yaa Muhammad fa?”

“Wane Yaa Muhammad din? Yanzu fa ke matar wani ce ki daina kiran Yaa Muhammad ki cire shi a zuciyar ki.”

A zabure ta mike zaune tana fadin

“Kamar Ya?”

Ajiyar zuciya ta sauke tace

“Yaya ya shiga mawuyacin hali akan son ki. Duk ciwon da yayi akanki ne Aisha ya sadaukar da son ki dan samuwar farin cikin ki. Ya hakura dake ba dan baya son ki ba sai dan ki samu nutsuwa da cikon burin ki,  kokarin cire ki da yake so yi a ransa shi ya jefasa a hali da yake domin sonki shine rayuwar Yaya rasa ki tamkar rasa rayuwar kine. Tin a gida nigeria aka fada wa Abbah Yaa AK yana fama da hawan jini da zuciyar sa dake son tabuwa. Anan ma da muka zo matsalar dai ita suka ce domin kuwa Yaya har aman jini ya fara. Akwai lokacin da muka zata ya mutu Allah yayi da kwanan sa a gaba amman Yaya ya sha wahala sosai amman ki kalla daga zuwan ki ya warke me zaki ce akan wannan alamatin?”

“Wannan wani ikon Allah ne abinda na ke son na sani da kika ce ni matar wani ce!”

“Eh. Ke matar Yaya ce!”

A zabure ta mike tana fadin

“Tayaya?”

STORY CONTINUES BELOW

“Kowa yasan kina son Yaya daga Umma da Baba har Yaa Muhammad sun gane kina son sa ba zaki iya fitowa ki fada bane. Lokacin da su Abbah suka je dan neman auren ki sun fadawa Baba komai wanda ya nemi a kira a ji ta bakin ki. Lokacin da Baba ya shiga dakin yaji statement din da kike akan Yaya amman ya nuna bai ji ba da aka kira ki dan jin bakin ki kika kasa magana dan ba zaki taba cewa bakya son Yaa Muhammad ba. Kada ki manta Umma na yawan miki magama akan ki tsaya ki zabi wanda kike so amman ke sai kice sai Yaa Muhammad kinsan manya abinda zasu hango mu ba zamu hange shi ba. To Umma ta gane kina son Yaya na son da bakyawa Yaa Muhammad shi amman da taga ke zurfin ciki yasa ta samu Yaa Muhammad tai masa bayani wanda shima ya fara fuskantar akwai matsala a tare dake. To wannan yasa suka yanke hukunci aka bawa Yaya na auren ki a take kuma aka daura. Ba sunyi haka dan son kai ba sunyi haka dan samuwar farin cikin mutane da yawa da bawa iyayen mu kwanciyyar hankali.

Yanzu ke da kike son ki auri Yaa Muhammad alhalin son wani na aciki  zuciyar ki ya kike so kiyi tayaya zaki iya kulawa da yaa Muhammad har ki bashi farin ciki bayan zuciyar ki da tunanin ki na wajen wani kina zaton zaki samu abinda kike nema kwanciyyar hankali da farin ciki wallahi duk pretending din da zaki za a gane kuma iyayen ki zasu fuskanci kina da damuwa suma zasu shiga damuwa ba ma haka ba kinsa ciwon da kika jini ki ya hau saboda yawan saka tunani gaba me kike ganin zai haifar wanna yasa suka aurawa Yaya na ke zaki samu kwanciyyar hankali kuma shima haka iyayen ki ma haka. Akan da da iyayen ki zasu rasa kwanciyyar hankali kema haka Yaa Muhammad haka Yana ma haka. yaa Muhammad shi yace ya barwa Yayana auren ki dan ya gane shi masoyin kine na gaskiya.

Ba yabon kai ba wallahi ba zaki samu wanda yake son ki kamar Yaya na ba wallahi yaya na yana son ki. Yaya na bai taba soyayya ba mace bata gaban sa ko auren farin sa Abbah ne ya zaba masa kuma yake masa biyayya zaki ji dadin Yaya na ki saka a ranki kin auri me son ki kuma dangin mijin ki basu da matsala in kin zauna damu zaki sani.

Ban taba zaton Yaya zai fada tarkonbsoyayya ba sai gashi yau an wayi gari Yaya na yana son ki. Naji dadi Sosai Abbah ma yaji dadi kuma yai murna duk macen da Yaya zai gani yace yana son ta hakika ta cika mace abar so ce. Dan Allah sis inlaw ki amshi Yayana a matsayin miji nasan zakiji dadi.”

Kuka ta fashe dashi ta rasa kukan farin ciki take ko na me? Wata bangare na zuciyar ta na cike da farin ciki dayan kuma yana cike da tausayi da son Yaa Muhammad. Yanxu duk son da Yaa Muhammad ke mata ya hakura ya barwa Yaa AK shin wa yafi son ta? Wane irin so suke mata kowa da yafi son yaga samuwar farin cikin ta.

Me zatayi murna ko farin ciki ta samu yaa AK wanda take so ko kuwa kuka da bakin ciki ta rasa Yayan ta. Hannun ta Maryama ta kama tace

“Ki nutsu Sister ki gane duk abinda ya faru ga bawa mukaddari ne kuma ki dauka akan haka shine mafi alheri tinda ko da yaushe addu’ar mu kenan da fatan samun abunda yake alheri a rayuwar mu. To ki dauka auren Yayan na shine alheri a rayuwar ki.”

Hawaye ne ya zubo mata Maryama ta sa hannu ta goge mata tace

“Nasan ba zaki taba dana sani da auren Yaya na ba domin Yaya na mutum ne mai sani da amfani dashi zai baki dukkan kulawa wacce baya so ma ya bata bare ke Fatana ki masa biyayya Sister.”

Rumgume Maryama tayi tana kuka tana fadi

“Na shiga rudani na kasa gane me yake faruwa na kasa sanin me zanyi farin ciki ko akasin haka nima ina son Yaa AK amman Yaa Muhammad fa? Wa zai maye masa gurbi na wa zai bashi farin ciki.”

“Gani ni nai miki alkawarin kula miki dashi. Tinda Yaa Muhammad ya sadaukar da fari cikin sa ga Yaya na naji duk duniya ba wanda nake so da ganin girma kamar sa. Ji nayi ba wanda ya taba fatanta min a duniya kamar shi. Hakika naji dadi kuma nai farin ciki sosai kuma gane waye shi da sanyin halin sa ya kara sa min son sa dan haka ki daina damuwa ni zan kula miki da Yaa Muhammad fiye da yadda zaki kula min da Yaya na.”

“Are you sure?”

“Yes!”

Rumgume ta tayi tana fadin

“Thank you Sister Allah saka muku da alheri am really appeciate your kindness.”

“Kada ki damu ai yiwa kaine. Kaso mai sonka akace.”

“Haka ne.”

STORY CONTINUES BELOW

“Yauwah kinsan me zan ce miki?”

Kai Aisha ta girgiza. Maryama tace

“Ke yarinya ce mai karancin shekaru akan mijin ki da abokiyar zaman ki amman nasan duk da haka ke ba zakiyi wasu abubuwan da abokiyar zaman ki take yi ba. Zan baki shawara ne ki rike mijin ki kada kiji kunya wajen faranta masa kiyi masa bibbaya da kyautata masa. Zama suke da matar sa amman tana wani gidan shima haka fa ta haka zaki samu ki rike mijin ki.”

Kai kawai ta gyada dan ta fara jin bacci. Hamma tayi ta mike ta shiga bandaki alwala ta dauro ta dawo tace

“Bacci nake ji.”

“To ki kwanta sai da safe.”

Kwaciyya tayi amman duk baccin da take ji sai taji ta kasa bacci sake sake ta dinga yi. Maryama kuwa  mkewa tayi dakin Yayan ta. Sallama tayi amman sam bai ji ta ba. Shiga tayi ta same shi Zaune  yai shiru. Karasawa Tayi ta zauna a gefen sa ya dago a hankali.

“Ya akai Maryama baki bacci ba?”

“Eh magana nazo muyi!”

“Ina ji!”

Sai tayi shiru hannun ta ya kamo yace

“Menene feel free mana.”

“Uhmm Yaya akan Sis inlaw ne.”

“Me ya same ta?”

“Nothing na fada mata komai ne!”

“Saboda me?”

“Saboda naga ya kamata ta sani kuma kaima zaka bukaci kulawar ta.”

“Amman bakya tunanin ta shiga wani hali?”

“Yaya na ganar da ita. Daman kasan ai ita matsalar ta Yaa Muhammad ne kawai.”

“Haka ne!”

“Na fada mata zanyi handling issue nashi abinda take tunanin zai shiga wani hali xanyi kokarin ganin bai shiga ba.”

“To me tace?”

“Yaya kasan Ai tana son ka dan haka ba wata matsala sai dai Yaya Naga yarinya ce sosai dole kai zaka kara saka ta a hanyar abubuwa?”

“Kamar me?”

“Uhmm ka gane mana Yaya!”

Murmushi yayi yacw

“Sai kema ki taimaka mun.”

“Insha Allahu.”

“Nagode Maryama yanzu tana ina?”

“Ta kwanta!”

“Ba abinda yake damun ta ko?”

“Babu Yaya.”

“Nagode Maryama!”

Mikewa tayi tace

“Kasha maganin ka?”

“Nasha!”

“To sai da safe!”

Ta juyata fita. Ido ya lumshe yana jin wani dadi a ransa yanzu Aysher ta san ya zama mijin ta yanzu kenan zai iya komai da matar sa. Ji yayi kamar ya tafi wajen ta.

Mikewa yayi ya dauro alwala ya dawo ya tada sallah ta godiya da Allah da ya fara kawo masa komai da sauki. Tunani ya fara tayaya rayuwar su zata tayi da Aisha. Murmushi ya saki ya lumshe ido yana hango su cikin jin dadi. Alhamdulillah ya dinga fada yana godiya ga Allah da ya bashi Aisha Allah yasa ta zama tafarkin shigar sa Aljanna.

Aisha ta zama farin ciki a rayuwar sa ta zama haske mai haske masa gaban sa da taimaka masa. Me zaiwa Aisha ne yaji dadi ya faranta mata.

*

Hajara ce zaune rike da waya a kunne tace

“Kinsan Aliyu baya karya dai ko?”

“Na sani amman kuma gani nake wasa yake miki.”

“Is better dai dan a gaskiya ba zan iya zama da kishiya ba haba ni ai min kishiya ba zan yadda ba. Amman kinsa me?”

“A’ah!”

“Kinsan Aliyu ba dan iska bane a jikin sa fa naga yarinyar ni yarinyar yanayi naga tana min da Mamahn sa.”

“Ina zaton ya yar uwar sace.”

“Haka ne.”

“Ki dai tashi tsaye dan daga haka zasu tusa mishi ita kinsan sa shi ba kula mata yake ba tinda kikaga yana kula yarinyar akwai wani abu a kasa ko kanwar sa ba wani hira fa suke ba amman tayaya za ai kice kinga yarinyar a jikin sa.”

“Abinda yake damuna kenan. Bakiji yadda na tsani yarinyar ba.”

“Kinga zanje wajen wani malami a kara kauda idona daga kanya mata.”

“Thank you Sha’awa shiyasa nake sonki.”

Sallama sukai ta ajiye wayar sai ta fashe da kuka. Momy ce ta shigo taxe

“Lafiya Sha’awa?”

“Momy yanzu Hajara take fada min wannan yarinyar sai shigewa Yaa Aliyu take!”

“Shine me?”

“Kada su Mamah suce ya aure ta.”

Komawa tayi ta zauna tace

“Kuma fa haka ne yanzu ya za ayi?”

“Momy nifa na gaji ko Hajara na tsani ina ganin ta tare dashi ayi abinda za ayi gaba dayan su a cire su a rayuwar sa.”

“Shikenan kada ki damu.”

“Ni da Momy ki san abinyi damuwa ai dole ce.”

“Shikenan zan san abinyi yanzu ki kwanta zan samo mafita zuwa gobe da safe.”

“Yauwah yanzu naji batu.”

Ta haye gado yaa fadin

“Gud night!”

Momy ta mike ta fita a dakin. Dakin ta ta shiga tana safa da marwa. Dole ta san yadda zatai Sha’awa ta auri Aliyu kuma kan nan dole su kame shi dan yadda Aliyu yake sam in ta aure shi a haka ba zata ji dadi ba. Sam batai bacci ba tana tunani abin yi.Tin daga ranar Aisha bata kara yadda su  hadu da Aliyu ko Muhammad ba da taji motsin su take guduwa daki ko abinci ta daina yadda taci a falo tare dasu. Ga wata kunyar Mamah da take ji.

Sai ta zamata daka ta daka Aliyu kuwa ba karamin damuwa yayi ba dan ko dakin taji za a shigo take shigewa bandaki ta buya.

Kwana biyu sukai amman duk ya damu ji yake kamar wanda ya shekera biyu bai ganta ba. Mamah na lura da shi da ita haka Yaa Muhammad da Maryama ma suna lura dasu.

A kitchen ya samu Maryama tana aiki,  tsayawa yayi a jikin kofa ya harde hannu a kirjin sa yace

“Wai Ayhser bata gidan nan ne?”

Juyowa tayi tana murmushi tace

“Ina zata Yaya?”

“To naga bana ganin ta ko dakin ku na shiga bana ganin ku.”

“Hmm tana nan kila kunyar ka take ji.”

“kunya ta?”

Sai ya girgiza kai yace

“Ya za ayi na ganta wallahi na shiga wani hali nayi missing nata alot!”

“Ai kawai shammatar ta zakai ka shiga dakin ka rutsa ta.”

“Oh but nasha shiga bata ciki ba.”

“Ka gwada dai Yaya na. Kada ka damu fa tana son ka.”

“Na sani amman ni ina son nagan ta.”

“Ok shikenan zan turo maka. ita.”

“Thank you!”

Ya juya ya nufi dakin sa har zai shige dakin su sai ya dawo ya koma kofar dakin su tsayawa yayi sa kuma ya kai hannu ya murda kofar a hanlali ya shiga. Ba kowa a dakin dan haka ya rufe kofar ya haye gadon su ya kwanta yai lamo.

Be yi minti biyar da kwanciyya ba aka bude kofar toilet yana kwance ya kalli kofar. Aisha ce ta fito daure da towel a jikin ta wanda yake iya gwiwar ta. Gashin kanta ta wanke shi sai digar da ruwa yake yi. Gaban mirrow ta nufa kawai ba tare da ta kalli gado ba. Karamin towel ta dauka ta dan tsane kan ta sannan ta fara shara mai a jikin ta.

Ta duka tana shafawa a ci yar ta zuwa kaurin ta kawai taji an dago ta a tsorace ta dago abinda yasa towel din ya subuce ya fadi kenan bata damu da daular sa ba sai na ta duba taga waye dan ta gudu tana juyowa taga Yaa AK ai da sauri ta fada jikin sa ta kamkame shi.

Hannun sa ya daura akan hips din sa. Hannu ta saka tana ture hannun sa tana fadin

“Dan Allah ka daukon towel din.”

Kan sa ya daura akan kafadar ta yana shakar kamshi  sabulun da tai wanka dashi da shampoo da ta wanke kai. Take idanun sa ya fara sauya kala yaji wani abu na tsikarar sa. Mirrow ya kalla ya ganta naked a jikin sa. Wani vibration jikin sa ya saki. Dago ta yayi daga jikin sa tana nonnokewa idon sa na sauka akan dukiyar fulanin ta yaji joystick nashi na son mikewa abinda bai taba ji ba dan ya kalli surar Hajara amman yau ganin surar Aysher duk ta sauya masa yanayi da tunani me kenan me yake faruwa dashi dan shi bai taba sani ana shiga wani hali makamacin haka ba. Ya gama dago da ita ta zame ta durkushe durkusawa shima yayi ya dauko towel din nata sannan ya dago ta.

Hawaye ya gani a idon ta,  take yaji ba dadi towel din yai rapping mata a jiki sannan yace

“Menene kike kuka dan na ganki?”

Kai ta gyada yace

“To rama!”

STORY CONTINUES BELOW

Da sauri ta juya masa baya tana fuskantar mudubi. Idon ta ya gani a runtse ya saki murmushi ya karaso yace

“Eh mana ba shikenan ba.”

Kafada ta make ya dauki comb ya fara taje mata gashin ta mai tsawo da laushi bakikin wannan shine karo na farko da ya taba taba gashin mace. Wanda kuma ya burge shi sosai dan har gadon bayan ta yake. Haka ya dinga jagwalgwala mata ita dai duk a takure take gashi kunya ta hana tace ya tafi ya barta ma.

Kofar dakin aka turo Maryama ce ta shigo tana fadin

“Gaskiya Sister Mijin ki ya kawon karar ki.”

Ai tana dagowa  ta gansu a haka da sauri ta juya baya. sannan tace

“Am sorry!”

Ta nufi kofa ta bude ta fice tana tuntube. A falo ta samu Yaa Muhammad ta karasa tana fadin

“Kana nan ashe?”

“Eh ina kika shiga ne?”

“Ina kitchen.”

“Lina bani mamaki duk da kin tashi a gidan sarauta ban zata zakina aiki haka ba.”

“Hmmm ai baka sani ba Mamah ita ta sabar min domin itama bata yadda wani ya girkawa Abbah abinci ba abinda zamuci mu muke dafawa masu aikin mu aiyakar su aikin waje amman cikin bangaren mu muke gyara abin mu. Mama kan yawan cewa gwara mu koya in muka auri wanda bai son masu aiki fa? Ko tace duk aikin da kukai lada ne a gidan ku to kaga ai gwara mu samu ladan ko.”

Kai ya gyada na nuna alamar ya yadda da bayanin ta. Tayi murmushi. Yace

“Wai ina Aisha ne?”

“Tana daki na baro ta yanzu.”

“Oh naga bata fitowa.”

“Kunya take ji!”

“Kunyar wa?”

“Mutane da yawa.”

“Wa da wa?”

“Kaga Yaya na,  Mamah, Abbah da kai.”

“Ni kuma?”

“Eh mana tinda na fada mata aure ta, ta daina fitowa kuma ku take buyar wa ji ni tare da ita dazu yaya na ke min maganar ta fa.”

Kai ya girgiza yace

“Aisha kenan!”

“Eh!”

“Ina fatan ba wata matsala.”

“Kar ka damu ina kular muku da ita. Da farko ta shiga rudani da damuwa. Damuwar ta wa zai kula mata da Yayan ta.”

Tai murmushi yace

“Sai da na dauki alkawarin kulawa dakai sannan ta samu ta dan nutsu amman ta shiga rudani tana tunanin ma tayaya ka yadda.”

Yai murmushi kawai yana fadin

“Haka Allah ya tsara Allah yasa haka ya zama mafi alheri.”

“Amin.”

*

Aisha da Aliyu kuwa suna can daki. Da kyar tace

“Yaa AK zan shirya.”

Kan sa ya saka awajen kafadar ta yace

“Ki shirya mana kinga sai na taimaka miki ko?”

Ido ta zaro ya kalli mirrow ya juyo da ita yace

“Menene in miji ya shirya matarsa.”

Ido ta runtse tana fadin

“wayoo Yaya dan Allah ka daina.”

Wani abu yaji na yadda tai maganar da shagwaba kamar zatai kuka. Yace

“Uhm me zan daina.”

Juyawa take son yi ya rike mata kafada yana binta da kallo. Yadda yake jin abu na taso masa da wani tunani na shigar sa yasa ya sake ta da sauri tare da juya baya yace

“Kishirya.”

Dagowa tayi tana kallon sa tace

“Ka fita mana.”

Kan gado ya koma ya kwanta yace

“Akwai maganar da zamuyi ki shirya kizo kiji.”

Kallon sa tsaya yi taga ya juya baya yana shafa kan sa. Juyawa tayi ta jufi wardrobe inners ta dauka tana yi tana dubawa ko ya juyo tana gamawa ta dauki wata doguwar riga baka ta shige bandaki da sauri. Ido ya bude tare da juyowa yaga bata dakin. Murmushi ya saki kawai ya kara mikewa akan gadon. Kayan ta saka yai mata kyau  sannan ta fito dan ta gyara kan ta.

A hankali ta karasa gaban mirrow ta dauki mai ta shafawa kanta ta dauki ribon zata saka kenan taji ya kama hannun ta. Amsa yayi ya saka mata ya fito da zilin wasu ta gaba wanda yai nata kyau. Dagowa tayi ta kalli mudubin suka hada ido da sauri tayi kasa da kanta. Turare ta mika hannu ta dauka ya amsa ya fara fesa mata. Sai da ya gama ya janyo hannun ta ya tsayar da ita yana kare mata kallon tin daga sama har kasanta.

STORY CONTINUES BELOW

Rigar ta mata kyau ta dan kama saman ta dan yadda take da cikar kirji sai ta sai ta baje a hips din ta tai mata kyau. Fuskar ta da batai mata kwalliya ba tai yau ga gashin da ya sakar mata matsawa yayi ya zaro wayar sa ya dauke ta sannan ya koma kusa da ita ya dauke su tare hannun ta ya janyo ya zaunar a gefen gado.

Hannun ta ya kama sannan ya fara magana.

“Lokacin da na gane kin fara jin kunya ta nayi mamaki amman da aka fada min kunya na daga cikin so naji dadi. Domin a lokacin ya  una kin fara jin wani abu akai na. Kunya taa da kyau kuma tana yiwa mata kyau sosai amman Ayshh ina rokar ki da Allah a rage ta dan naga alama zata cutar dani. Yanzu me yasa kike boye min kanki bayan kin san na zama mijin ki ba abinda zan bukata sai kulawar ki. Kina gani fa bani da lafiya.”

Ya karashe maganar da kwantar da murya kamar mara lafiya ta gefen ido ta kalli shi taga har da langwabar da kan sa. Dan murmushi ta saki tace

“Ya jikin?”

Kafada ya make yace

“Meyasa bakizo kin duba ni ba.”

“Ba komai!

“To ban yadda ba.”

“Haba Yaya na!”

“Eh daga yanzu zakina zuwa waje na safe da rana da dare kina duba lafiya ta da bani magani kina ji na?”

Kai ta gyada yace

“in ba haka ba nan dakin zan taho muna kwana tare.”

Ido ta zaro tace

“Kayi hakuri.”

“Nayi My Ayshhh! Ina kaunar ki my wife.”

Ya fada yaba kama hannun ta. Wani abu taji ya tsarga mata har tsigar jikin ta na tashi.

Kallon ta yake kawai kan ta a kasa ya sa hannu ya dan dago kan ta yace

“Ya kika ji da kika ji kin zama matata?”

Hannu ta saka ta rufe fuskar ta tana murmushi.

Hannun ta ya dauke yana murza su yana fadin

“Fada min!”

Kafada ta make tace

“Ni dai Yaa AK ka kyale ni.”

“Sai kin fada min Allah.”

Shiru tayi yace

“Uhmm ina jin ki!”

“Naji dadi!”

“Dame?”

“Farin ciki!”

“Da gaske?”

Kai ta gyada yace

“Show me!”

Dagowa tayi ta kalle shi sai

Kuma tai saurin yin kasa da kanta tace

“Tayaya?”

“Ki min abun dadi!”

Fuska ta dan bata tace

“Kamar me?”

“Komai!”

“Nifaban sani ba.”

Daga ta yayi tsaye ya zaunar akan cinyar sa mutsu mustu ta fara dan rashi sabo. Ya sa hannu ya tallafi kanta ya hada goshin sa da nata sannan ya hada hancin sa da nata ya tura bakin sa yai dan lashi lips din ta. Da sauri ta bude ido tana kallon cikin idon sa dake kallon ta. A hankali ya kama lips din kasan ta ya fara kissing da sauri ta runtsa idon ta jikin ta ya fara rawa da wani iri.

Kokarin zare bakin ta take ya dafe kanta dole ta hakura ya cigaba da kissing nata kamar ya samu sweet ita kuwa in banda dukan uku uku ba abinda kirjin ta yake jikin ta sai rawa yake ta rikice taji abinda bata taba jiba wanda yasa jikinta yai sanyi sosai ta kasa kwatar kanta.

*

Su Maryana na falo sukaji ana kiran sallah magarib wannan yasa Yaa Muhammad ya mike ya tafi daura alwala itama ta tashi har zata bude daki ta tuna Aliyu yana ciki. Tsayawa tayi tace

“Na tafi ko na shiga?”

Wata zuciya tace

“Ki fada musu an kira sallah saboda kar suje suna can soyayya basu ji ba wata tace ki kyale su.”

A hankali tayi knocking wanda sam daga Aisha har Aliyu ba wanda yaji.

Ita Aisha saboda tsorata da yanayin da take ciki yasa bata ji ba shi kuma Yaa Aliyu abinda yake ji ba zai misaltu ba bai taba samun kansa yana kissing wata mace ba Sai Aisha sai kuma yaji abun da dadi sosai dan har bayaji baya gani.

Tin tana yin knocking a hankali har tayi da karfi wanda Aisha taji tai firgigit ta dago. Hannu ta saka ya tabo shi. A hankali ya bude idonsa da ya sauya yana kallon idon ta da itama ya sauya ya juye zuwa na ma bukuciyya. Knocking Maryama ta kara wannan yasa yace

“waye?”

STORY CONTINUES BELOW

“Yaya ana kiran sallah!”

“Ok gani nan!”

Ya fada yana dawo da kallon sa kan Aisha da tayi kasa da kanta.

“Uhmm Maryama ta katse min jin dadi na!”

Ido tai saurin rufeewa. Ya daga ta tayi baya zata fadi yai sauri ya taro ta ya rumgume ta. Zaunar da ita yayi yana kallon ta taki yadda ta hada do dashi. Dagota yayi ya kama hannun ta ya isa bakin toilet da ita yace

” kiyi wanka ki daura alwala zanyi sallah anjima zan dawo.”

Yana fada ya juya ya nufi dakin sa. Yana shiga ya cire kaya ya shiga yayi wanka ya daura alwala sannan ya fito. Da sauri ya tafi masallaci yana zuwa raka’a daya ya samu sannan ya cika ta.

Toilet ta shiga ta zare rigar ta. Sannan ta cire under wears din ta. Wanka tayi ta fito daure da towel tana goge kan ta da karamin towel. Maryama ce ta shigo ta kalle ta tace

“A’ah wani wankan kika sake!”

Hararar ta tayi tace

“Ke kika turon shi ko?”

“Ni!”

Ta fada tana nuna kanka. Sai kuma ta girgiza kai tace

“ba ruwana!”

Kwafa tayi ta hau shiryawa da sauri ta saka wasu kayan ta tada sallah. Tana zaune akan sallayar bayan ta idar Maryama tace

“Allah Anty ki daina abinda kike Yaya yace boyar masa kike!”

“Uhmm to yanzu me zanyi?”

“Ai kawai ki tattara ki koma dakin sa ni ba zaku takura min ba.”

“Ai sai ki dauken ki maidani.”

“Dagaske?”

Banza tayi mata tayi dariya tace

“Uhmm ku ko? Kwa dai ji dashi.”

“Anji.”

Ta mike tana dariya tace

“Allah dai ya baku zaman lafiya nan da next night month mu samu Baby Allah yasa ya amsa addu’a ta.”

Ido Aisha kawai ta zaro ta kasa magana ma. Maryama kuwa sai dariya take mata. Lokacin aka kira isha’i ta tashi tayi ta zauna tana addu’a.

Basu baro masallaci ba sai bayan sunyi isha’i A hanya Faisal yace

“Ya nga ka makara?”

“Kai kuwa mai mata. Ina can ana bani kayan dadi.”

Tsaki Faisal yayi yace

“Kaji dashi banza sabon shiga har yaushe kayi auren kai.”

Yai tsaki yace

“Zakaga iskanci nima zan koma gun matata da kake min rashin mutunci.”

Muhammad Ya Kalla yace

“Dan Allah wane rashin mutunci nai masa in ba rashin tsoron Allah ba.”

Muhammad dai dariya yake dan Faisal da Aliyu in suka hadu sun tayi kenan a da Aliyu bai biye masa sai dai yai tsaki amma avyanzu da yai masa yake mayar masa.

Faisal yace

“Yaro baki sai buduwa yake.”

“Waye yaron!”

“Sorry ranka ya dade.”

Yai dariya yace

“Haka kake so ko? To bazan fada ba wavyace maka ko president ka zama zance maka ranka yadade AK na kawai.”

“Allah rufan asiri da zama president wannan kujerar ma dan ba yadda zanyi da ita ne nayi nayi wannan juyin da akai a cire ni anki da masu so suka kai motion gun president cewa ma yayi ayi zabe abin mamaki da ina murna zan sauka sai gashi sun kara daura ni. Wannan shekaru biyun da suka rage ji nake kamar wasu shekaru ne marasa adadi. Gaskiya bana son wannan mukamin su barni na koma inda nafi karfi kawai.”

“Ai ranka yadade mu muna son ka muka rasa ka a garin mu garin mu ya rushe zabin ka da President yayi ya mana gata kuma daga kai har shi ba abinda ake muku sai sa albarka kayi hakuri ka daure ka karasa Allah yasa wannan ya zama tafarkin shiga aljannar ka.”

Ajiyar zuciya ya sauke yace

“Uhmm mulki ba wasa bane mulki jaraba ne ko na gidan ka yaya bare gari guda ni kadai nasan a halin da fargabar da nake. A lokacin da na gane irin barnar da ake a garin ji nayi rayuwa ta tagama baci a lokacin tunani na daya in na mutu naje nace wa Allah me?”

Ajiyar zuciya ya sauke yace

“Hmmm Aysher ita ta fara ankarar dani irin avunda ke faruwa a garin nan ta nuna min matsalolin mutanebn gari wani waje har kai ni take ita ta taimaka min duk da bata san waye ni ba wannan ya fargar dani na gane ashe duk wanda na daura ba aiki suke ba kansu suke ginawa. Na shiga tashin hankalin da ban taba shiga ba. Har yanzu ban samu nutsuwa ba domin duk yadda nakai ga kyautawa mutane nasan akwai wanda ban taba kyautata masa ba inje incewa Allah me? To kaga fa as state kenan ina kuma ace National ne gaba daya ai mutuwa zanyi.”

“Haka ne amman Ai kana yi kuma na gani ana yabawa ba a garin kawai ba har a sauran kasashe maganar ka ake wasu garuruwa na fatan akai ka garin su. Ranka ya dade ka godewa Allah kawai.”

Cewar Muhammad

Faisal ya gyada kai yace

“Gaskiya kam. Ba a taba gwamna na kaki kai har na farin hula da yake aikin da kayi ba. Dan haka ka godewa Allah kana cikin shugabani adalai.”

Ajiyar zuciya ya sauke yace

“Nagode wa Allah kuma ina godewa Allah da ya hadani da Aysher a rayuwa ta a komai nawa dole na sako Ayaher ta bani gudunmawar da ba wanda ya taba bani a harkar mulki na. Ku daina yaba min kada naji na samu wani abu in dakata a haka. Ku na nunan hanya da bani kwarin gwiwa kawai.”

“Insha Allahu Allah kara dafawa.”

“Amin!”

Suka amsa gaba daya  abbah ne ya shigo ya kalle su yace.

“Me ake tattauanawa ne!”

“Akan harkar mulki ne.”

Abbah yai murnushi yace

“Allah taimaka to.”

Ya shige ciki.

Abinci suka ci suka zauna hira. Aliyu da ada surutu ke saka shi ciwon kai sai gashi ya sake a cikn su suna ta hira abinsu. Sai karfe goma kowa ya mike yayi dakin sa. Dakin sa ya shiga yai wanka ya fito yasa kayan bacci. Kan gado ya hau yaji shi wani iri dan ba abinda yake son taji a jikin sa,  sai Aysher. Juyi yayi ya dauki wannan pillow ya dauki wancan amman duk a banza mikewa yai yana kallon kofar dakin sa.

A hankali ya mike tsaye ya nufi kofar ya bude dakin su Aisha ya shiga. Maryama na bandaki tana wanka Aisha kwance da kayan baccin ta riga iya gwiwa sai net da ta saka akan ta sai tashin kamshi takeyi. Idon ta a lumshe amman ba bacci take yi ba.

Jin mutum tai kawai a kanta da sauri ta bude ido a tsorace. Hancin ta ya ja yace

“Kin fiya tsoro Ayshh!”

Kokarin mikewa tayi ya danne ta ta marairace masa fuska kamar zatai kuka tace

“Kana da nauyi fa.”

Bakin ta ya kurawa ido yana tuna moment din su na dazu shafa lips din yayi yace

“A haka kuma zaki dauke ni ba.”

“In dauke ka tab ba zan iya ba.”

Yai murmushi. Kofar bandaki ta kalla tace

“Yaa AK kada Maryama fa ta fito ta ganmu a haka.”

“To sai me ba matata bace.”

“Uhmm amman dai ni…”

“To tashi mu tafi!”

Ido ta zaro tace

“Ina?”

“Daki na.”

“Kai Yaa AK gaskiya ba zan iya ba.”

“Oh haba shikenan na kwana anan kenan.”

Da sauri ta mike tace

“Kai Yaa AK kai wallahi ko?”

“Ni wallahi me?”

Kafada ta make. Ya mike yace

“Bari mu tafi kada Maryama ta fito ko?”

“Ka tafi dai Yaa AK!”

Ai batai aune ba taji ya dauke ta cak kamkame shi tayi tana fadin

“Dan Allah ka sauke ni.”

Bai sauke ta ba sai hanyar fita da yayi da ita. Tsoro ya kara kamata kada wani ya gansu a haka tace

“Dan Allah ka sauke ni Yaa AK!”

Kan sa ya daura akan ta yace

“Saboda me?”

“Kada wani ya ganmu fa!”

“To shine me? Matata ce fa.”

Ido ta runtse kawai dan yadda take jin tsoro kunya da fargaba kirjin ta kuwa sai dukan uku uku yake. Yana kaiwa kofar dakin sa Hajara ta fito daga dakin ta zata kitchen kamar ance ta juyo ta ganshi dauke da Aisha. Still tayi a wajen tana mamakin me yake shirin faruwa ne. Daki ta koma da kunar rai sai kuma ta mike har zata fita kuma sai ta koma ta zauna tayi haka yafi sau hudu kafin ta dauki waya ta kara a kunnen ta.

“Sha’awa akwai matsala fa!”

“Tame fa?”

“Aliyu man abubuwa gaba suke karayi a da ina zaton Aliyu bai neman mata amman a yanzu na fara mamaki anya kuwa?”

“Me ya faru?”

“Dauke fa na ganshi da yarinyar na a hannu!”

“What!”

“Wallahi.”

“Anya kin gani dai dai kuwa?”

“Hmm na gani mana wa zai dauka a gidan nan in ba ita ba.”

“Tab din yanzu ina suka tafi.”

“Dakin sa!”

Wayar ta kashe kawai sai ta fashe da kuka. Me yake faruwa ne? Wacece wannan yarinyar? Kenan Aliyu bayan Hajara ma akwai wace yake so a da bata damu da batun Hajara ba dan tasan ba son Hajara yake ba amman wannan yarinyar tabbas da alamun wani abu a kasa. Dole kuwa ta raba Aluyu da kowa ba dan ba dan kowa aka hallici Aliyu ba sai dan ita. Haka ta dinga sake sake.

Hajara ma tunani ta fara abubuwa suka cakube mata kan ta ya dau zafi kishi ya bayyana sosai Ji take kawai taje ta kashe su ta huta wata zuciyar na gargadin ta.

Suna shiga daki ya ajiye ta akan gado. Da sauri ta mike zaune taja baya ta jingina da pillows din kan gadon. Hawa yayi yana fadin
“Taho muyi baccin mu.”
“Yaa AK bazan iya ba ni dai ka barni na tafi dakin mu.”
“In kuma kika tare fa dan kunga ina daga muku kafa shine kuke barina kwana ni kadai ni ba gauro ba ko? To na gaji yanzu anan zakina kwana.”
İdo ta zaro tace
“Yaa AK su Mamah fa suna nan ni dai gaskiya ba zan iya ba.”
“To menene dan su Mamah suna nan!”
Fusla ta rufe da hannu tace
“Kunya nake ji.”
Murmushi yayi a boye a fili kuma yace
“To dan kunya sai ki tauye hakki na ko?”
Fuska ta kwabe kamar zatai kuka yace
“Eh in kina son kuma ki dauki hakkina shikenan kofa a bude take sai da safe.”
Ya kwanta tare da juya mata baya yana wani murmushi domin yasan ya kulle ta da jijiyo yin ya. Ta jima a zaune sannan ta koma ta kwanta tare da juya masa baya.
Juyowa yayi a hankali yana kallon ta sai kuma ya matsa kusa da ita yana fadin
“Ya zaki juya min baya!”
Ya fada yana juyo da ita. Idon ta a lumshe kamar me bacci murmushi yayi kawai ya zura hannun sa ta kasan rigar ta da sauri ta bude idon ta, kallon juna suka tsaya yi ya kashe mata ido daya ido tai saurin runtsewa jin yana cigaba da zura mata hannu yasa tai saurin rike hannun.
Tana jin idon sa akan ta wannan yasa ta shige jikin sa kawai. Hannun sa ya dago ya zagaye ta dashi. Ido ta lumshe tana addu’a zuciyarta kuwa sai bugawa take. Yana jin yadda take bugawa dan haka bai kara wani motsi ba sai hular kan ta da ya cire ya cusa kan sa a ciki yana shakar kamshin shanfoo da man da take amfani dashi.
Tin tana jin bacci na dibar ta tana kin yadda tayi har bata san lokacin da baccin ya dauke ta ba. Aliyu kuwa shi kadai yasan a halin da yake bai taba jin abubuwan da yaje ji ba sai a yanzu da yake tare da Ayshern sa. Sai yake zaton to ko baida lafiya ne.
Wani feeling yake ji wanda bai san da shi ba dan bai taba jin sa ko makamancin sa ba. Abu yaji yana taso masa wannan yasa ya kara rumgume ta a jikin sa kamar zai balla ta dan duk da tana bacci sai da ta saki wata yar kara. Rasa inda zai saka kan sa yayi ya mike ya shiga ya watsa ruwa amman yana fitowa yaga tana bacci ta dunkule yaji komai ya dawo masa yana jin wani abu dan har joystick din shi yaji tana mikewa kan gadon ya hau ya janyo ta jikin sa ya rumgume ya sam a jikin sa kamar zai maida ta cikin jikin sa.
Wani abu yaji yana kara taso masa. Kansa ya kara tusawa a kanta yana shakar kamshin kanta amman sai yaji kamar ana dada ingiza shi ba abinda yake bukata sai mace. Rasa yaya zai yi yayi. Rigar ta ya soma cirewa yana gama cirewa ya tsaya kallon surar jikin ta wacce take a cike dukiyar fulanin ta a tsatsaye farare masu kyau haka nan hips din ta a bude kallon surar ta ya tsaya kallo wace bai taba ganin irin ta ba. Ko Hajara  ta girme mata bata da sura mai kyau da daukar hankali irin ta ba. A kallon yaji yayi releasing daga kallon ta. Duk da haka bai ji abinda yake ji ya tafi ba. Yana mamaki menene haka dan bai taba yin releasing shi kadai ba haka kawai.  Bai san lokacin da ya kai hannu yana latsa dukiyar fulanin ta ido ya lumshen jin taushin su da yayi can ya saka kansa a tsakiyar su yana juyi hannun sa na bayan ta. Ya jima a haka sannan ya kara jin ya samu nutsuwa yayi release. A hankali kuma ya rumgume ta bai san lokacin da bacci ya dauke sa ba.
STORY CONTINUES BELOW
Bai tashi farakawa ba sai karfe biyar da minti goma a gaugauce ya mike ya fada bandaki yayi wanka tare da dauro alwala. Yana fitowa ya nufi gadon ya bude fuskar ta. Kallon ta ya tsaya ji yayi jikin sa yai masa wani iri da sauri ya mike sai kuma ya dawo ya tsaya kallon ta sai kuma ya taba fuskar ta. Jin hannun sa a fuskar ta yasa ta bude idon ta. Murmushi ya sakar mata yace
“Morning Princess!”
Ido tai saurin lumshe wa jin ana kiran sallah yasa ya mike ya wuce ya saka jallabiya yace
“Ki tashi kiyi sallah.”
Yana fada ya fice sai da ya kusa makara kan ya karasa har an tayar da sallah. A hankali ta mike ganin jikin ta ba riga yasa tai saurin dubawa ta ganta acan gefe. Da sauri ta dauka ta saka ta fice ba tare da ta duba Hular ta ba.
Tana shiga daki ta tadda Maryama a kan sallaya bandaki kawai ta shige ta tayi wanka.
Ta fito ta dau riga ta saka ta hau jan sallaya ta tada sallah. Tana idar wa ta mike ta zare hijab din ta kunna hand dryer ta fara busar da kan. Maryama dake zaune tana kallon ta sai dariya take sama sama tace
“Jiya kuma sai kika gudu kika barni.”
Aisha dai batai magana ba har ta gama ta wuce kan gado zata kwanta. Maryama tace
“Ai ki koma dakin mijin ki dan Mamah ma cewa tayi ki koma can kawai da kwana.”
A zabure ta mike tace
“Mamah kuma taya ta sani?”
Dariya ta ta danne tace
“Ta shigo jiya taga bakya nan tace ina kika tafi nace kila Yaya ne yazo ya tafi dake na kare ki.”
Kamar zatai kuka tace
“Kai Sis kinsan dai ba zanje ba ko? Shine fa yazo ya dauken!”
Dariya Maryama ta saki tace
“To shine na kuka”
” To kince Mamah tazo”
“Da wasa fa nake!”
“Da gaske?”
“Eh”
Hararar ta tayi ta koma tai kwanciyyar ta. Maryama tace
“Wai wanka me kike da kike ta jika kanki.”
“Jeki tambayi Yayanki.”
“A’ah ba ruwa na.”
Ta mike ta fita tana fadin
“A huce gajiya Anty nah!”
Ido kawai Aisha ta lumshe bacci ya fara dauke ta. Yana dawo daga massalaci ya shiga dakin sa. Ganin bata nan direct ya taho dakin su. A kan gado ya hango ta tana baccin ta. Mika yayi tare da salati sannan ya haye gadon tare da shiga cikin bargon da take bacci rumgume ta yayi suka fara baccin su.
Maryama kuwa tana can kitchen ita da mai aiki suna hada kayan break flask. Mamah ce fito ta shiga dakin su.
“Maryama! Maryama!!”
Aliyu ne ya bude kansa yana fadin
“Mamah tana kitchen.”
Ido ta zaro tana fadin
“Me ya kawo ka nan?”
Kai yadan sosa. Ta girgiza kai tana fadin
“Allah ya kyauta.”
Ta juya ta fita. Aisha kam tana bacci bata san me yake faruwa ba.
Kitchen ta shiga ta samu Maryama ta fada mata abinda take so tai mata sannnan ta wuce daki. Abbah ta sama yana shiryawa. Mamah ta zauna a gefen gado tana fadin
“Ya kamata mu koma tinda mara lafiya yaji sauki har bin matar sa yake dakin su.”
Dariya Abbah yayi yace
“Ke me ya kaiki shiga dakin yara?”
“Menene dan na shiga dakin yarana ai ba dakin masu aure na shiga ba meyasa zai biyo ta ai da sai ya dauke ta su tafi can.”
“Kinsan yar taki ba zata yadda ba in kika bibiya ma ba da sanin ta yaje ba. Na rasa gane kan Aliyu tinda yai auren nan yanzu bai da kunyar komai a gaban mu na gane yana son ta ne sosai wanda yake kasa boye sa agaban ko waye”
“Haka ne tin ba yanzu ba na gane hakan Allah ya bata ikon kulawa dashi.”
“Bani da haufii akan haka. Gidan yarinyar gidan girma ne da karamci sai ma kinji duk da basu da hali amman suna da rufin asiri da wadatar zuci.”
STORY CONTINUES BELOW
“Masha Allah.”
“Duk wanda ya samu ya aure daga gidan yaji dadi gaskiya basu da zalama ko son abun duniya.”
“Masha Alah.”
“Ni dai fatana Allah yayi adalci dan naga Aliyu na son Aisha sosai.”
“Insha Allahu ai yasan ke yake yi dan yasan dole son daya yafi daya!”
“Kamar yadda naki yafi ko?”
“A’ah ni dai ba ruwa na.”
“Da gaske nake.”
“Kar ka fasan kai kasa na daga kai kuma ba haka bame.”
“Nasan matata ba za tai hakan ba kuma itama ta san don gaskiya na kan ta.”
“Godiya nake ranka ya dade.”
“Tare da naki Fulani na.”
Sukai dariya tace
“Nidai gaskiya na matsu mu tafi ba xan iya sati tare da yaran nan yana matsawa yarinyar nan ba zan dauke ta mu tafi kawai.”
“Duk yadda kika ce haka za ai amman bakya ganin zaki shiga hakkin sa.”
“Ranka ya dade ai ya bari ta tare ko? Yanzu ta kura mata zai”
“Shikenan!”
“A shirya mana tafiya ni da Maryama da Aisha gobe mu daga. Hajara ta xauna sa taho tare.”
“Angama.”
“Nagode.”
*
Karfe tara da rabi ta farka,  zatai juyi ta jita a jikin mutum da sauri ta bude idom ta, ta sauke akan Aliyu da ya rumgume ta tsam a jikin sa. Kura masa ido tayi tana kallon kyakyawar fuskar sa.
Idon sa dake a rufe sun dan bullutso alamar yana da idanu,  sai hancin sa dogo madaidaici siriri da yake a tsaye,  ga bakin sa madaidaici pink kala. Fatar sa fara mai kyau wacce taji dadi da hutu ta kara yin luf da ita. Sai girar sa dake cike da gashin Kan sa kwantacen gashi ne wanda yake da saje da ya kara masa kyau da kwarji jini. Murmushi ta saki tare da lumshe ido. Domin Yaa AK yana da duk abinda take so a namiji. Gashi dogo cikakken namiji wanda bai da rama.
Hannu ta saka ta shafa sajen fusoar sa sannan ta daura akan idon sa. Sai kuma ta dauke hannun tana mai kallon sa. Murmushi ta kara saki dimple din ta ya lotsa. Batai aune ba sai jin hannun sa tayi a kumatun ta ya saka a wajen dimple d8n ta. Da sauri ta dago ai kuwa suka hada ido.
Kunya ce ta kamata taivsaurin runtse idon ta. Kallon ta ya tsaya yi. Ya yadda Aishan sa mai kyau ce dan dukbyadda xai kwatanta tafi nan a wajen sa da idanun sa.
“Hae Bae open ur eyes!”
Kara runtse idon tayi dan yadda taji maganar tasa a tsakiyar kanta.
Hannu ya saka ya dago fuskar ta yana kallon yadda eyes lashes nata masu tsayi danyawa suke ke ta karkadawa. Murmushi ya saki yai kai bakin sa gefen nata. Tana jin numfashin sa tai saurin bude idon ta,  tana ja baya. Hannun sa ya saka ya janyo ta jikin sa ta fada kansa.
“Mu fara gaisawa ko? Gud morning!”
Kan ta ta kife a kirjin sa yace
“Kin tashi lafiya?”
Kai ta gyada masa yace
“Good. Sai ki ban morning kiss dina.”
Kafada ta make yace
“What?”
Ba tai magana ba kuma bata dago ba yace
“Uhmm let me tell you since now ki shirya dan kullum sai kinyi more than hundred. İn the Morning,  afternoon, evening, and night,  kan fin azo na musamman.”
Mikewa tayi da sauri zata bar wajen yai saurin janyo ta yana fadin
“Ai ban gama ba.”
“Yaa AK wanka zanyi rana yana yi fa.”
“Ai ni zan miki.”
Ido ta zaro tana girgiza kai. Yace
“Eh!”
“Ni dai…”
“Ke dai me?”
Kafada ta make yace
“Alright ki zabi daya a cikin biyu ko kiyi kissing dina ko nai miki wanka?”
“Ok zan maka amman ka bari na fara wankan.”
“Naki wayo.”
“Kai tayaya zan maka wayo.”
“Gashi nan kuwa.”
STORY CONTINUES BELOW
Tai murmushi. Shima yi yayi yace
“Na kama ki ko?”
Kai tayi kasa dashi yace
“Zabi daya.”
“Naji na zaba zan yi kissing naka amman kasan me?”
“Me?”
“Ka rufe idon ka!”
“Kai ji dai a’ah.”
“To ni ba zan iya a haka ba.”
“Mu koma bargo.”
“No ai sauri nake zan wanka.,”
“A can din ma ba za a jima ba.”
“Ok muje!”
Ta mike tsaye shi kuma ya fara hawa gadon bai an karaba………..
*
**
***
****
*****
******
*******
Da yamma Alhaji Yahya yana dawowa daga aiki ko gida bai zarce ba ya nufi gidan Uncle Aminu. Iso akai masa nan sitting room. Bayan sun gaisa suka taba hirar duniya sannan Uncle Aminu yai gyaran murya ya farai masa bayanin komai.
Shiru Alhaji Yahya yayi yace
“Ikon Allah kaga ni kuma bai ce min komai ba amman na kira shi nasan duk inda yake anjima zai zo dan haka ka jira ni zuwa gobe zan dawo maka insha Allahu.”
“To Alhaji Yahya Allah ya tabbatar mana da alheri.”
“Amin Amin.”
Ya mike yace
“Ni zan tafi.”
Uncle Aminu ya mike ya rakashi har bakin kofa suka kara musabawa sannan ya shiga ya tafi.
Karfe 8pm.
Aslam ne zaune a kan karfet kan sa akasa. Hajiya Fateema da Alhaji Yahya zaune akan kujera sun zuba masa ido. Can Alhaji Yahya yace
“Ina sauraran ka.”
“Dad ni auren ne naji kwata kwata yanzu bana so su jira na dan wani lokacin in naji ina so kuma yanzu a kara d’aga lokacin a saka ko nan da shekara biyar ne haka.”
“What? What are you saying?”
Alhaji Yahya ya fada a zafafe.
Kai ya hau sosawa yace
“Dan Allah Dad ayi abinda nace. Ni dai yanzu ban shirya ba. aje a daga bikin nan da five years!”
“But you are mad ko Aslam?”
Hajiya Fateema ta fada itama rabta a bace. Tace
“Ko ka fara shaye shaye ban sani ba. Kai da kazo kana fadin a matso da bikin shine zaka zo kana fadin a daga bikin dagawar ma not a week ko month a’ah har more than one years to wa ka raina yanzu mu ko su iyayen yarinyar.”
“Ask him!”
Dad ya fada yana binsa da kallo. Sannan yace
“Akan wane dalili kenan na rashin shiryawa rashin kudi kome? Nasan ba rashin kudi bane gida gasu nan ka zabi wanda kake so in bazaka hada su ba sai kuma me?”
“Dad ni all ba wannan bane a yanzu naji ban shirya kara auren bane kawai a dan daga min kafa kayiwa su Uncke din nata magana dan Allah.”
Shiru sukai. Mony tace
“Kaga Aslam fada min ko kun samu sabani ne.”
“No Momy Wallahi Dr bata taba bata min rai ba yarinya ce mai hankali da nutsuwa bata da hayaniya.”
Shiru tayi can tace
“To ka daina son ta ne?”
“No Momy I love her wallahi i really love her kawai dai ni a yanzu ne bana son bikin ku basu hakuri su dan dada min lokaci zuwa lokacin da zan shirya.”
“You are very stupid ita yarinyar sai ta tsaya jiran ka. Kaga malam ta shi ka bani waje.”
Alhaji Yahya ya fada cikin bacin rai.
Durkusawa yayi ya hade hannaye yana kallon mahaifin nasa yace
“Dan Allah Dad kayi hakuri kada wannan yasa kayi fushi dani am so confused a yanzu dai bana son auren amman wannan ba yana nufin bana son ta bane please….”
“Nace ka tashi ka bani waje!”
“Kayi Hakuri Dad.”
Ya fada yana yowa wajen Hajiya Fatima yace
“Ki tayani bawa Dad hakuri da ganar dashi please ku rokar min alfarma a d’aga bikin dan Allah.”
“Is ok tashi kaje.”
Ya mike ya fita. Komawa Alhaji Yahya yayi ya zauna. hajiya Fatima ta mike ta dawo kusa dashi ta dafa shi tace
“Please Alhaji ka kwantar da hankalin ka kada kasa damuwa.”
“Dole na damu yaro yana son ya maidani karamin mutum.”
“Kayi hakuri.”
Kai ya dafe yana huci can ya dago yace
“Yanzu me zance wa iyayen yarinyar ban.”
STORY CONTINUES BELOW
“Kai musu bayani in sun yadda to in basu yadda ba shikenan amman gaskiya kada ka soma cewa za ka hada auren nan ba da sanin sa ba kar aje a jefa yarinyar cikin tashin hankali.”
“Wa ni na aura masa ita Allah ya kiyaye tinda bai shirya ba kuwa duk lokacin da ya shirya yaje ya samu wani uban ya shige masa gaba amman bani ba.”
“Ayi hakuri Alhaji.”
“Ya wuce Hajiya gobe zanje nai masa bayani.”
“To Allah yasa haka shine mafi alheri.”
“Amin Amin”
Washe gari ko aiki Alhaji Yahya bai je ba ya kira Uncle Aminu ya fada masa yana nan zuwa yace yana jiran sa. Karfe sha daya yana kofar gidan Uncle Aminu waya yai masa sai gashi nan ya shigo yace
“Bismillah Alhaji!”
“Nan suka shiga daki suka zauna sannan suka gaisa sosai. Alhaji Yahya yace
” akan maganar da mukai jiya.”
“Eh to madallah yabkukai da shi?”
Eh toh Alhaji ni dai na kasa gane kan alamarin dan a fatko yaron nan zuwa yayi yana min korafin wai an saka lokaci da yawa amman a jiya da na kirasa sai cewa yayi yana don a daga bikin nan saboda bai shirya ba. Na rasa wane irin shiryawa ne bai ba Alhaji shi ba kudine bai dashi ko wajen zama ba wane shirin yake bukata.”
“Ikon Allah har yaushe yake son a kara masa.”
“Alhaji ai abun ya zama kamar wasa shifa maganar shekaru yake!”
“Shekaru Alhaji?”
“Wallahi Shekara Biyar ma.”
Kai Uncle ya hau girgizawa yana fadin
“Haba ai ko yar JS 1 sai haka ace Fateema ta zauna har nan da wata shekara biyar ba aure ai bana mata fata. Gaskiya Alhaji ina jin sai dai a hakura da abin nan zanje nayi magana da mahaifiyar yarinyar da kakar ta duk yadda mukai zakaji ni,  amman yanzu ace a bar kudin wani akan ta ai kamar an daure ta ne bata da damar samar wani kila ba shine alheri ba. Ko ba rabon sa bace. Zanje dai duk yadda mukai zakaji in ma zamu dawo da kayan auren ne to! Allah yasa haka ne mafi alheri. In Fateema rabon sa ce shikenan gaba inda rabo za a hadu in kuma ba rabonsa bace Allah yasa haka ne mafi alheri.”
“To Alhaji Amini na godiya da yadda ka fahimce ni batun kayan aure ku ai a barsu kawai.”
“A’ah Alhaji ba za ai haka ba za dai kajini.”
“To ina godiya amman a barwa Fateema dan Allah ina fatan wannan ba zai kawo karshen zumuncin mu ba.”
“Insha Allahu.”
“To madallah ni zan tafivAlhaji Allah bada hakuri ayi hakuri dan Allah.”
“Ba komai Alhaji ai wani baya auren matar wani.”
“Haka ne. Suka fito a tare Uncle Aminu ya rako shi ya shiga mota sannan sukai sallama cikin aminci.
Daga nan Uncle Aminu gidan su Fateema ya isa. Fatrema yau ko asibiti bataje ba dan yadda take fama da jikin ta duk dauriyya take dan kar su Momy su gane a halin da take amman ita tasan me take ji kawai. Duk ta kara ramewa. Tana kitchen tana dafa indomie dan sai yanzu ta fito daga daki tin jiya da dare.
Tana kitchen taji shigowar Uncle Aminu bata fito ba taji ya zauna suna gaisawa dasu Baba Umani da Momy. Bayan sun gama gaisawa ne Uncle Aminu yace
“To Alhamdulillah yanzu mahaifin Ahmad ya bar gida na munyi magana akan Ahmad din.”
Indomie ta dauke ta bare kwan ta zuba ta dauki stool din kitchen ta daura akai ta fara ci amman sam ba jin dadin ta take ba.
Baba Uwani tace
“To me ya faru me ake ciki yanzu?”
“Jiya ya kira Ahmad din akan zancen auren amman sai ya nuna yana son a daga bikin bai gama shiryawa.”
“To dan haka yake kin daukar wayar Fateeman me Fateeman zatayi ai ita bata da Matsala.”
fateema da ta taso zata fito dan takasa cin taji Babana maganar wannan yasa ta tsaya tana jin ta.
Uncle yace
“Baba ai abun yazo kamar da rainin wayo ne wai har shekara biyar fa yake maganar a kara masa tayaya Fateema zata zauna har shekara biyar bqtai aure ba a gidan nan. Bana mata wannan Fatan fatana ta samu tayi aure ta samu nutsuwa ina tausayin yarinyar nan. To kinji yadda mukai tin can na nuna muma ba zamu bari Fateema tai ta jiransa har wannan lokacin ba yanzu ina son zan mai da musu da lefe da kudin auren su ya kuka ce.”
Baba tace
“Ai haka za ai daman ba son ta Aslam yake ba.”
Fateema sai yanzu ta gane me take fadi dan haka take taji kanta ya sara tana jin juwa batai aune ba sai jin ta tayi ta fadi.
Da sauri Momy ta mike tayi hanyar kitchen din faduwar abu Fateema ta gani kwance a kasa da sauri tayi kanta tana kiran sunan ta.
“Fateema Fateema!”
Da sauri Baba da Uncle Aminu sukayo kitchen din. Dagota Uncle Aminu yayi ya taho falo da ita sannan yace
“A kawon ruwa.”
Baba ce ta miko masa ya yayyafa mata sai ta sauke ajiyar zuciya amman bata bude ido ba.
“Fateema!”
Ya kira sunan ta. Ba amsa bare respond.
“Fateema!”
Nan ma shiru. Momy ya kalla yace
“Bari muje asibiti.”
Ya dauke ta ya fita Momy da Baba suka bi bayan sa.
Asibitin ta suka je suna zuwa suka kira doctor Auwal nan aka kawo gado aka gangarata sukai emergency da ita.

*It’s your Day Yasmeen Autah. Wish you loads of fun and smile. Happy birthday May Allah bless you*
Da kyar ta dawo daga sumar da tayi sai dai tana dawowa sukai mata allurar bacci kawai. Sai a sannan hankalin su Momy ya kwanta bayan sun ganta tana bacci.

Sai yamma ta farka Momy ta taimaka mata ta tashi ta zauna tana dafe kai. Momy tace
“Bari na kira Dr Auwal!”

Ta fita sai gasu tare ruwan ya cire mata yace
“Me yake miki ciwo?”

“Kai nane!”
“Ga magani nan kisha sannan ki cire damuwa kinji ko?”

“Insha Allah! Nagode.”
Ya fita. Ta mike momy ta taimaka mata shiga bayi tayo alwala ta zo tayi azahar da la’asar ta zauna tana azhkar Uncle Aminu ya shigo. Yana ganin ta zaune yace
“Masha Allah ta tashi kenan?”

“Eh Momy ta fada. Fateema tace
“ina yini Uncle?”

“Lafiya lou ya jikin?”
“Alhamdulillah!”

“Allah kara sauki. Kiyi hakuri ki amshi kaddarar ki insha Allahu nan gaba zakiji dadi da izinin manzon Allah. Allah baki hakuri da juriyya yai miki sauyi mafi alheri kada ki soma saka damuwa a ranki kinji ko?”
Kai ta gyada tace
“Nagode Uncle.”

Ta kalli Mony tace
“Mu tafi gida Momy!”

“To amman da kinci abinci ko kinsha magani.”
“Gaskiya kam.”
Uncle ya fada.

Abinci ta zubo mata ta bata ta amsa ta dan tsakura sannan tasha magani. Tana zaune staff din sukavdinga shigowa suna mata sannu da Allah kara lafiya. Tana amsawa tana godiya sannan suka fito suka dan tafiya.

A compund din ma.mvdaga staffs har masu jinya zuwa suka dingayi suna mata sannu da jiki sannan ta shiga mota suka koma gida.
Tin da ta shiga daki ta dauki wayar ta ta nemi number sa tayi deleting sannan ta ajiye. Sam bata saka damuwa ba amman abin na damun ta a can kasan zuciyar ta.

Sam Taki ta bawa kowa face din da zai mata magana Momy kuwa tsoro take kar rashin maganar ya zama matsala. Amman da ta fara mata magana akan abin sai tace
“Momy ni fa na yadda da kaddarar Allah. Daman Allah yayi ba miji na bane Allah yasa haka ne mafi alheri.”

Sai ta kashewa Momy baki. Momy sunyi waya da Suraiyya ta fada mata duk yadda akai sosai suraiyya ta shiga damuwa dan ta gane Fateema ta kamu da son Aslam tinda take damuwa da rashin kiran sa da zuwan ta.
Fateema sai duk ta koma lonelly kullum tana daki in ta fito kitchen zata dinga duba littafi sai aiki a system tana maida kanta busy ta yadda ba zata bar tunanin Aslam ya rinjaye ta ba duk da tana fama da abun sosai dan kyar take yakice abin tasan tana missing nasa sosai dan ya riga ya sabar masa da rayuwa da shi.

Tana zaune akan gado tayi dai dai tana aiki a system tana duba wani littafi a gefen ta. Sanye take da dogon siket da farar vess a jikin ta. Sai hula da ta saka akai.

Kofar dakin aka bude aka shigo ana sallama. Amsawa tayi ta dawo tana fadin
“Ummu twins where is my Dad?”

“Yana wajen su Momy.”
Mikewa tayi tace
“Bari na dauko Dad dina.”

STORY CONTINUES BELOW
Ta fita bata jima ba ta dawo da yaron yana ta bangala mata dariya tana masa wasa. Zama tayi tana fadin
“Dad dina ya girma ya fara gane Yar sa.”

Suraiyya tace
“Lallai kam ya aiki?”

“Kwana biyu ma banje ba wallahi tinda na yi ciwon nan.”
“Ayyah ya jikin?”

“Naji sauki.”
“Ashe haka abu ya faru?”

Murmushi kawai tayi. Suriayya tace
“To Allah yasabhaka ne mafi alheri Allah ya kawo mana Wani cikin gaggawa.”

Dariya tayi ta daga Farouk tana fadin
“Dad dina me zan baka ne?”
Ta dauko jaka ta dauko Chocolate tana fadin
“Zan koya maka shan zaki tin kana yaro ko?”

Ta bare ta bashi. Suraiyya tace
“Wai ya kukai da shi?”
“Wa fa?’

“Uncle Mana!”
“Sis please ki kyale ni da zancen Uncle wallahi ni mantawa ma nake bana son ana dawon da maganar sa.”

“To ai shikenan! Kiyi hakuri”
“Baki min komai.”

To haka take duk wanda zai kawo mata maganar Aslam sai ta tare shi ta dakatar har su Jannah da suka zo gida bata basu dama ba duk yadda suka so da sun dauko maganar zata kawo wata hirar suma sai suka share.
Haiiyar Fu’ad har gida tazo tayi matavjaje da addu’a Allah bata wani mijin na gari. Tare suka zo da Nusaiba ai kuwa suka kule daki suna hira abin sha’awa.
*
Bayan sati biyu da abun Uncle Aminu ya hada kan kaya su da kudi ya kai amman sam Alhaji Yahya yace ba za a amsa ba ya barwa Fateema halak malak Haka Uncle Amiinu suka maida dawo da kayan Fateema kuwa ko ta kan kayan bata bi ba dan ita tinda aka kawo basu burge ta ba bare yanzu.
*
Jiddah kuwa ta dinga bin didigi har ta gane an fasa auren wannan yasa ta dinga murna har da hada party ita da kawayen ta. Ta cigaba da bashi kulawa da gayya tai masa maganar auren ba su rabu lafiya ba.

Suna zaune a falo ne ta kawo masa lemo ta ajiye ya kalle ta yace
“Thank you my wife!”

“Love wai ina kanwata ne kwana biyu baka cewa zakaje!”
“Wacce kuma kanwar ki.”

“Amaryar da zakiyi mana.”
Tsaki ya daki yace
“Ban sani ba kada ki karai min maganar ta kinji ko?”

Yana fada ya mike ya shiga dakin sa. Tsalle tayi ta mike tabi bayan sa akan gado ta same shi ya kwanta idon sa a lumshe zama tayi tace
“Haba Honey daga magana sai fushi dan na tambayi kanwata.”

“To ni bana so in kika karai min magana aka wata kanwar ki sai ranki ya baci kinji na fada miki.”
Yana fada ya mike ya shige bandaki. Dariya tayi ta mike ta fita tana fadin
“Alhamdulillah koma wacece na rabaki da miji na.”

*
8 month later
Sanye take da doguwar riga baka ta yafa mayafin rigar ta fito daga cikin mota,  ta nufi office dinta bayan su gaisa da mai gadi da wasu staffs dake wajen tana shiga ta ajiye ta zauna tana duba files din gaban ta tashi tayi ta fara round sai twelve ta dawo ta zauna tana duba wanda zasu zo wajen ta.
Sai bayan tai sallah azahar sannan ta fara duba patient din nata. Mutum daya,  biyu na ukun Jidda ta shigo. Tana shigowa gaban ta ya fadi. Amman tayi addu’a ta saki murmushi kamar yadda take mata.
Zama tayi sannan tace
“Ina yini doctor?”

“Alhamdulillah ya kike ya gida?”
“Alhamdulillah! Tinda na amshi wayar ki ban kira ba ko? Wallahi abubuwa sukai min yawa!”

“Ayyah amman yanzu komai normal ko?”
“Alhamdulillah daman fa aure ya dauko zai yi baki ga yadda hankali na ya tashi ba. Allah ya rufa asiri ma dai yanzu an fasa.”

“Ayyah Allah yasa haka ne mafi alheri.”
“Amin! Nayi nayi ya rakoni yau yaki.”

“Hmm to ke banda abinki ba gashi kinzo ke kadai ba.”
“Ai kuwa kam. Daman bani da lafiya ne kwana biyu ina fama da ciwon ciki ga yawan tashin zuciya da naci abinci sai naji zuciya ta na tashi in banyi sa’a bama sai amai shine nace bari nazo ko zaki ban magani dan da ba haka nake ba.”

STORY CONTINUES BELOW
“To kina zazzabi ne?”
“Sai dare da safe naji ya tafi.”

“Kasala fa?”
“Eh da safe kan nayi aiki sai na sha bacci tukkuna.”

“Yaushe rabon da kiga period din ki?”
“Eh to wancan watan nayi 19 wannan ya kamata nayi 18/17 amman kinga yau har 20 bai zo ba.”

“Ok!”
Tayi rubutu ta bata paper tace kije ai miki test sai ki dawo gobe in Allah ya kaimh.”

“To Doctor yanzu ba abinda zan samu da zai na kwantar min da zuciya?”
“Ki tsaya da shan komai yanzu ki na shan ko sweet ko cingum dan ya kwantar miki da zuciyar.”

“Ok Doctor nagode.”
Ta fita cigaba tayi da duba patient har lokacin tashin ta yayi ta koma gida.

*
“Me akace yana damun ki?”
Aslam ya fada yana aiki a system. Zama tayi tana shan lemo tace
“Test ta bani nayi gobe zan koma na amso result sai aga menene akwai.”

“Allah jara suaki.”
“Amin!”
Ta fada tana kallon sa dan yai bala’in sauyawa tinda aka fasa auren sa duk ya zama so silent bai da walwala komai yana yi ne aman ba kamar yadda ya saba ba.

Jidda tace
“Doctor Fateema na gani yau wallahi Doctor nan na da mutunci.”

Tinda ta ambaci suna Fateema yai tsaye ya daina abinda yake yi. Ita kuwa jidda bata san ma yana yi ba sai labari take bashi tana kallon film din da bollywood keyi. Dagowa yayi yana kallon TV sai ya ga Film din da Fateema ta taba cewa shi take kalla har ya ce bari ya taya ta.  Mikewa kawai yayi ya shige daki ya kwanta.

Tana zaune har karfe goma sannan ta mike ta dauke masa system ta bisa. Kwance ta same shi yai rigingine ya daura hannu a kan sa idon sa a lumshe ko kayan jikin sa bai cire ba.

Zama tayi yace
“Au daman ba wanka kake ba.”
Ido ya bude ya soma cire rigar jikin sa sannan ya shiga yai wanka yana fito ya haye gado yana juya mata baya.

“Love!”
“Uhmm yane?”

“What wrong with you?”
“Nima ban sani ba.”

Ya fada hawa gadon tayi ta shige jikin sa tace
“Muyi bacci to.”
Ya rumgume ta yai musu adsu’a suka fara baccin su.

*
3:30pm
Ta shigo office din sanye da doguwar riga ta yafa mayafin ta hannun ta rike da jaka da result din  ta amso. Zama tayi bayan ta shigo. Suka gaisa friendly sannan ta mika mata result din amsa tayi tana dubawa sai ta zaro ido tana sakin murmushi ta kalli Jidda tace
“Masha Allah congratulation kina da ciki na kwana ashirin da bakwai!”

Ido Jidda ta zaro ta mike tare da daka tsalle sai kuma ta kalli Fateema tace
“Dan Allah da gaske?”

Kai Fateema ta gyada masa ai sai ta fashe da kuka tana fadin
“Alhamdulillah Alhamdulillah”

Ta isa wajen Fateema ta rumgume ta tana fadin
“Nagode Dear”
“Ki bar kukan to. Zauna na baki magani da zai kara miki kwarin jiki”

Komawa tayi ta zauna ta rubuta mata sannan ta bata sukai sallama tana ta murna da yiwa Fateema Addu’ar gamawa da duniya lafiya.
Tin a hanya ta fara kraye kirayen waya har ta karasa gida. wanka tayi taci kwalliya ta zauna jiran Aslam.

Sai karfe tara da kwata ya shigo gidan yana shigowa ta rumgume shi tana fadin
“Albishin ka Honey!”

“Goro!”
“Ni bana son goro!”

“Ok fadi abinda kike so?”
“Zan fada amman kasan me?”

“No sai kin fada!”
“Ina da ciki Love!”

“What?”
Ya fada da karfi.
Dariya ta saki tace
“Am serious!”
Ta dauko result din da aka bata ta mika masa. Amsa yayi ya bude yana karantawa yagani ai bai san lokacin da ya zube yana sujudul shukur bayan ya dago ya daga Jidda yana juyi da ita yana hamdala ga Allah. sai da ya jima yana juyi da ita sannan ya ajiye ta ya fara kiraye kirayen gida yana shaida musu cikin farin ciki.

STORY CONTINUES BELOW
*
Yadda Fateema ta taya ta murna kai ka rantse da Allah ita ce ta samu karuwa domin ta taya shi murna sai taji ina ma ace suna tare da tai masa albishir taga wane farin ciki zai shiga domin kuwa Aslam ba abinda yake bukata kamar Haihuwa yau Allah ya bawa matar sa ciki bayan kusan shekara goma da sukai ba haihuwa ai wannan abun a taya shi murna ne ai masa barka ne.

Kwalla ce ta zubo mata a ido ta sa hannu ta goge tana fadin
“Alhamdulillah ni kuma tawa kalar kaddarar kenan ba zan samu abunda ke sona ba. Da farko na rasa masoyi na Yaa Fauwaz ko yana ina. ina yake oho. Son da Yaa Fauwaz ya nuna min yasa na kasa gane komai da kowa in bashi ba amman duk da haka ya tafi ya barni da son sa azuciya ta.
Fu’ad kai da nake da hope akan ka na baka ragamar rayuwa ta amman ka kasa ganewa sai ka sauwake min duk son da kake min kana zatan sauwaken da kayi zai kawon farin ciki zuciya baka san sai tarwatsa rayuwa ta da yayi ba. Na rasa farin ciki tinda na rasa ka ba zan kara samun wani farin ciki ba in ba kai ka dawo rayuwa ta ina son ka Fu’ad kaine rayuwa ta farin ciki na ina ka tafi ka barni ina ka tafi ka bar matar ka ka dawo duk rashin ka shi ya bawa Uncle damar shiga rayuwata wanda ya kara rusan sauran farin ciki na. Ya zanyi sai na gama saka rai da na samu farin ciki sai ya gudu ya barni.
Alhamdulillah Alhamdulillah Allah ina godiya Allah.”

Ta fada tana share hawayen ta. Mikewa tayi ta dauki key din ta ta fice sai gidan Hajiyar Fu’ad.

Tana isa tayi parking ta fito ta nufi ciki tin a kofa take jiyo hayaniyar yan matan gidan dan haka ta shiga da sallamar saboda yadda suke hira sam bama suji ba. Hajiya da ta fito ce ta lura da ita tace
“Ah Fateema kece a gidan.”

Kai tayi kasa dashi ta shigo tace “Wallahi Hajiya na dawo daga daga aiki nace bari nazo na duba ki.”

“Allah sarki sannu da zuwa Bismillah.”
Nusy ce ta dago tana ganin Fateema ta mike tana fadin
“Oyoyo Anty!”

Sauran yan matan sukai mata sannu da zuwa. Hajiya tace
“Bismillah.”

Ta karasa ta zauna a kasa ta gaishe ta cikin girmamawa sannan yan matan suka gaishe ta. Babbar ciki khairat tace
“Ni kuwa a ina nasan ta?”

Nusy tace
“Matar Small Uncle ce fa.”

“Tabbas ina yini ya gida?”
“Alhamdulillah.”
Sauran yan matan ma duk suka gaishe ta cikin girmamawa. Nusaiba tace
“Wadan nan ya’yan babbar ‘yar Hajiya ne dake london.”

“Ayyah kunzo lafiya?”
“Alhamdulillah.”

Hajiya tace
“Kinga kawo mata abinci daga aiki fa take.”

“Hajiya a koshe nake.”
“A’ah Fateema ki kara dai tin safe fa kina ta fama kawo mata maza Nusaiba.”

Ta shiga ta kawo mata abincin dan dole ta tsakura taci sannan ta shiga ta gaida Hajiyar cikin gida ta fito tace
“Zata tafi.”

Har bakin mota suka karata sukace zasu zo su gaishe ta har gida. Nan sukai ban kwana ta tafi.

*
Sam Momy ta kasa gane kan Fateema ta dada ramewa ko abinci bata ci duk matsa matan da zatayi in tasa abu a cikin ta bai wuce maltina ko fresh yoo ba ita kanta ta rasa me yasa sam bata iya cin abinci kuma take jin ta gaba daya bata da sukuni ga yawan faduwar gaba da take fama da ita
Momy na kitchen ta fito cikin shirin ta na zuwa wajen aiki. Sanye take da maroon kalar doguwar riga sai mayafin ta hannun ta rike da brown kalar jaka kafar ta sanye da brown kalar samdal yai mata kyau sai tashin kamshi takeyi. gidan sai kamshi yake motsin Momy ta ji a kitchen ta leka ta same ta tana soya dankali shiga tayi ta bude firij ta dauko freah yoo sannan ta ce
“Momy na shirya zan tafi sai na dawo.”

“Tanzu Fateema ke shikenan kin daina cin abinci shikenan haka rayuwa zata yi dan Allah kiga yadda kike kara bushewa dan Allah’

Murmushi Fateema ta saki ta karasawa wajen Momy ta daura kanta a kafadar ta tace
“Momy bana iya ci din ne duk ban son abincin kiyi hakuri zan gyara insha Allah.”

Kanta ta shafa tace
“to Allah kiyaye ya bada sa’a Fateema.”
“Amin Momy nagode.”

Ta dago kanta ta mata kiss a kumatu sannan ta daga mata hannu tace

“Bye!”
Ta juya ta fita kai Momy ta girgiza tana tausayin ‘yar ta. Ita kuma tata kalar kadddarar kenan lokacin da aka kawo mata Aslam ta nuna bata so da tai mata nasiha ta amshi abun sai gashi abun bai je ko ina ba. To Alhamdulullah Allah yasa haka ne mafi alheri. Allah kawo mata wani mai son ta Amin. Haka ta karasa aikin duk da tunanin yar tata da tausayin ta.

Ko da taje ba abinda tayi dan duk aikin ta rabawa sauran doctors din tahi. Fresh Yoo ta bude ta fara sha sai kuma ta ajiye. Wayar ta ta dauka ta kira Doctor Auwal yana dauka tace
“Ina kwana Dr?”

“Lafiya lou ya kike?”
“Lafiya lou.”

“Dan Allah Doctor kazo ka saka min ruwa mana.”
“Baki da lafiya ne?”

“A’ah wallahi bana iya cin abinci ne.”
“Kamar ya? Ko da yake gani nan.”

Ya kashe wayar bai jima ba ya shigo. Zama yayi ya kalle ta yace
“Me yake damun ki?”

“Bansani ba doctor amman bana jin dadi ka sa min ruwa ko naji kwarin jiki na rabona da abinci yau kwana uku bana iya ci sam.”
“Gaskiya Fateema.ki cire duk abind ake damun ki ko so kike ki kashe kankix

Murmushi tayi tace
“Allah ni yanzu ban da wata damuwa.”
“Shikenan ki kiywye dai.”

“Nagode.”
Nan ya fita bai jima ba ya dawo ya saka mata ruwan bayan ya saka ya fita ya barta. Sai yamma ta cirr sannan tayi sallah ta tada sallah tana sallah ya shigo ya kawo mata abinci ya ajiye yace
“Ki daure kici.”

“Nagode Dr!”
Ya fita. Dr Auwala abokin Dadyn ta ne duk da Dadyn ta ya girme shi mutum ne ma mutunci ya dauki Fateema tamkar ‘yar sa. Abinci ta budeta ganshi lafiyaye ga half kaza a ciki. Diba tayi ta ci ko cokali uku batayi ba taji ta koshi. Rufawa tayi kawai ta dauka ta bar asibitin gaba daya.

*
Sai da akai kwana uku yana kara mata ruwa a kwana a hudun ne ya rufe ta da fada kuma yace in har bata cin abinci har gida zai je ya fadawa Momy ya gaji da sa mata ruwa da yake yi. Dan dole ta hakura haka ranar ta yini duk jikin ta ba kwari.

*
A gajiye ta dawo gidan da yake yau friday bayan ta tashi daga aiki ta wuce radio station ta dauki program din ta. Sanye take da wani hadadden less peach kala sai zare da akabi da adon da maroon kalar zare dinkin bubu tayi ta yafa medium din mayafi da takalmi. Parking tayi ta dinga bin motar dake compound da kallo take taji gaban ta ya fadi. Addu’a tayi ta fito hannun ta rike da jakar ta dayan hannun kuma wayar ta ta nufi kofar gidan yadda take nufar kofar gidan haka gaban ta yake faduwa.

Da kyar ta kai ga karasawa ga kofar tanajin haki dan ji take kamar wacce tayi tsere dan a jiya da dai da ba akara mata ruwa ba duk jikin ta ya kara zama so weak a hankali ta sa hannu ta bude kofar dakin ta shiga da sallama. Momy ce ta amsa mata sannan ta kutsa kai cikin dakin ta shiga ta dago tana fadin
“Sannu da gida Momy!”

“Yauwah kin dawo lafiya ya aiki?”
“Alhamd….”
Maganar ta ta katse yin tozali da tayi dashi zaune akan two sitter wata baturiyya zaune kusa da shi ga wani Baby akan cinyar sa mai kama dashi sak.

Gaban ta ne ya fadi take ta saki jakar hannun ta da wayar hannun ta, ta saka hannun tasa tana mutsa idanun ta ai kuwa da gaske shi take gani.

Cikin rawar murya ta nunashi da hannu tace
“……”
*To fa wai waye wannan ne?*

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *