WA NAKE SO CHAPTER 19
Www.bankinhausanovels.com.ng
Maganar ta, ta katse yin tozali da tayi dashi zaune akan two sitter wata baturiyya zaune kusa da shi ga wani Baby akan cinyar sa mai kama dashi sak.+
Gaban ta ne ya fadi take ta saki jakar hannun ta da wayar hannun tata saka hannu tana mutsa idanun ta ai kuwa da gaske shi take gani.
Cikin rawar murya ta nunashi da hannu tace
“Yaa Fauwaz..”
Sai ta karasa ta dauki Babyn hannun sa tana fadin
“So cute! You look alike.”
Kasa magana Yaa Fauwaz yayi ita kuwa daga haka tayi cikin dakin ta. Zaunar da yaron tayi tace
“Ya sunan ka boy?”
Shiru yayi tace
“What your name Boy?”
“Annur!”
“Nice name Boy.”
Ta mike ta dauko masa chocolate da da ice cream tace
“Take it let me take my bath!”
“Thank you!”
Ta mike ta shiga cire kayan ta bayan ta gama sannan ta shiga bandaki. Wanka tayi ta fito ta same shi yana ta shan ice cream din sa. Mai ta shafa ta saka farar doguwar riga marar nauyi ta saka karamin hijab iya wuyan ta.
Ta dauki Yaron suka koma falon ta. Zama tayi tana kunna musu kallo tana masa tambayoyi. Tana yi tana mamaki wai Yaa Fauwaz shine yayi aure har da ‘da lallai rayuwa kenan mutumin da yace ita kadai yake so amman kalli boy din su da ya kusa two years kenan since when yai aure. Ita da tai aure ta kasa samun nutsuwa saboda tunanin sa amman shi kalle shi yayi aure ya haifa yana zaune lafiya da matar sa.
Hawaye ne ya kawo idon ta hannu tasa ta share sannan tace
“Yanzu kenan Fu’ad ma zai iyai min haka.”
Kai ta hau girgizawa tana fadi
“In fu’ad yai min haka zai karya min zuciya.”
“Akan me zai karya zuciyar ki bayan shi ba aure a tsakanin ku Fauwaz fa? Da ya tafi ya barki bai tashi dawowa ba har da ‘da.”
Xuciyar ta ta tunasar da ita
“Yaa Allah ka jikai na in Fu’ad ya min haka zuciya ta fashewa zatayi. Allah ka kiyayen Fu’ad dina.”
Yaron ta kala mai kama da babban sa sak take taji zuciyar ta karye. Son yaran ya shige ta sosai. Suna zaune akai magrib wannan yasa ta mike ta shiga sukai alwala ita da yaron da bai kiwa.
Tare sukai sallah suna zaune har akai isha’i. Momy ce ta shigo ta same su zaune yana cin biskit da lemo ta ce
“Annur zo muje kaci abinci.”
“Am ok Granny!”
“Au ba zaka ci abinci ba?”
Kai ya gyada ta kalli Fateema tace
“Tinda kika dawo kin kule a daki ai sai ki fito ku gaisa ko?”
“To!”
Momy ta kama hannun suka fita. Gloria dake falo ita da Fauwaz dago suna kallon Annur da ya fito.
Gloria ta mika masa hannu tace
“Come my son!”
Ya karasa ta dauke shi tace
“Shine ka manta dani ko?”
“Ina gun Mum tana bani sweet bisket and ice cream she is so kind.”
Murmushi Fauwaz yayi yace
“Mom ina Fateema ne?”
“Tana daki yanzu zata fito.”
Baba ce da Yasmeen suka shigo dan tin safe Kamal yazo ya dauke su a gidan sa suka yini tana shigowa ta fara bin falon da kallo ganin Gloria zaune kai ya sha gyara da gashin doki sanye da wando da riga. Dagowar da zatayi sai taga Fauwaz ido ta zaro tace
“Wa nake gani haka?”
STORY CONTINUES BELOW
Yai murmushi yace
“Uwar gida na ai tin dazu nake neman ki.”
“A’ah kaje can ka nemi uwar gidan ka amman ni ina kasan da ni ka tafi ka barni shekara da shekaru ta bana auren.”
“Haba Uwar gida na zo ki zauna mu gaisa.”
Ya fada yana kamo hannun ta. Zaunar da ita yayi yace
“Mun same ku lafiya?”
“Alhamdulillah yaushe ka dawo ina kuma ka tafi.”
Dariya yayi ya kalli Gloria yace
“Meet my grandmother”
Ta kalle ta tace
“Sannu Hajia!”
“Yauwah wacece wannan kuma?”
“Matata ce.”
Ya fada ya dauki Annur yace
“Ga ‘da na nan Annur!”
Tafa hannu Baba ta hau yi tana fadin
“Na shiga uku Fauwaz yanzu kafira ka aura.”
Dai dai fitowar Fateema daga daki kenan ta tsaya a bakin kofa tana kallon Baba. Fauwaz yace
“Haram ne?”
“Ko da ba Haram bane amman ka auri yar mutunci wacce zata haifa maka ya’ya na gari baka san ana gadon hali da dabiu bane yanzu kai da ka auro kafura dan ka ya je ya zama kafiri ai mun shiga uku kaf zuri’ar mu ba kafiri amman kana son ka jawo mana su to wallahi da sake. Kai me ka gani a gun ta kalle ta duk a kekashe dan Allah.”
“Ka fadi alheri dai ko kayi shiru.”
Fauwaz ya fada sannan yace
“Kuma ke Baba ina zamu kai wannan rabon kuma.”
“Ni dai ba abinda zaka fada min me su hauwa da Ibrahim suka fada?”.
” me kike so su fada Baba.”
“Ai kawai su raba auren nan dan ni banga abinda zakayi da kafira ba.”
Gloria dake zaune sam bata gane mai Baba take fada ba.
Momy tace
“Baba ki bar maganar nan dan Allah.”
Mikewa tayi tana fadin
“Ni dai ba za a hanani magana ba kuma aurw be bana so ace kafira mai zakai da kafira amman sun Hauwa sun auri jaraba ace da ayaje ya haifo musu jafira kai wannan abu ba kyau bate dadin ji.”
Tayi dakin ta. Momy tace
“Ka tashi kuje ku huta.”
Mikewa yayi ya kalli kifar dakin Fatrema tsaye ya hange ta tana ganin ya kallo wajen ta dauke kai. Kallon ta ya tsaya yi sai ta wuce dakin Baba kawai. Mony ta kalli inda yakr kalla tace
“Kuje ku huta Fauwaz.”
Annur ya dauka ya kalli Gloria yace
“Tashi muje.”
Ta mike zasu fita Annur yace
“Dad ni a gun Mum zan kwana!”
Harara sa Gloria tayi tace
“Wacce Mum da ko gaishe mu batai ba.”
“But she is kind Mom”
“Shut up malam ba inda zaka je.”
Ajiye sa Fauwaz yayi yace
“Kaje kaji my Son gud nyt!”
Yana dire shi ya wuce a guje yana fadin
“Gud Nyt Mom gud Nyt Dad.”
Ya nufi dakin Fateema. Hannun ta ya kama suka fita tana masifa dan me zai ajiye mata yaro ya dauko mata shi.
Sai da suka isa Bangaren baki sannan ya kalle ta yaxe
“Baki da hankali ne. Kanwata ce fa her mom is my mother sister fa kina gani ai uwar su daya uban su daya dan me kin isa ki raba ni dasu ne ko kin isa ki raba ya’ya ba dasu ne ki shiga hankalin ki in ba haka ba ranki zai mummunar baci.”
Yana fadar haka ya shige bandaki ya yi wanka ya fito ya wuce kan gado yankwanta kawai
Yana kwanciyya da niyyar yin baccin sa amman sai yaji baccin ya tafi ba abinda yake gani sai Fateema tsaye a kofar dakin ta tayi kyau ta kara girma da wayewa da kyau. Ido ya lumshe sai ya hango ta lokacin da ta dauki Annur.
Juyi yayi yana fadin
“Dan me zuciya ta kwashen na rabu da Fateema na tafi na barta dan me?”
Shiru yayi can yace
“Wannan kaddarar tace yana daga cikin kadara ta amman i love you Fateema har yau son ki yana nan bai goge ba ba zan taba son wata kamar ki ba son ki a jinin jiki na yake.”
STORY CONTINUES BELOW
Ranar bai bacci ba juyi ya dinga yi kawai yana tuna rayuwar su ta baya da yadda ya so Fateema da kalar kishin sa. Wani abun yai murmsuhi wani ya bata masa rai wani har hawaye yake yi.
*
Tana shiga dakin Baba tace
“Ashe kin dawo Baba.”
“Na dawo nazo na tadda kafura a gidan nan ku kuwa wa yasa ku barta ta xauna ai wallahi da ina nan sai tabar gidannan.”
“Baba kenan to menene ai arziki ne kuma matar sa ce menene a ciki tinda ba haram bane.
“Ai daman ke bayan sazaki bi sai kuyi tayi ai.”
Mikewa tayi zata fita Annur ya shigo yana fadin
“Where are you Mum!”
Fateema ta dauke shi tana fadin
“Here am i. Ya akai baka jin bacci.”
Baba ta tabe baki ta ce
“Ni ku bani waje dan Allah.”
Fita Fateema tayi tana dariya kawai.
Momy ta sama a falo ita da Yasmeeb suna kallo Momy tace
“Me nace miki?”
“Momy na fito naga sun fita shiyasa na shiga gun Baba.”
“Kin kyauta.”
Dining ta isa ta zuba musu abincida zasuci gana ji Annur yai Bismillah sannan ya fara ci. Suna gama suka koma daki tai masa wanka sannan suka kwanta bayan tai masa addu’a.
Sam Bacci kin zuwar mata yayi domin kuwa itama deep down akwai son Fauwaz a ranta dan ya so ta ya bata kulawa sosai bazata taba manatawa da Fauwaz ba amman kuma dan me yaje yayi aure ya manta da ita bayan ita bata manta dashi ba. Tafiyar sa ita ta rusa mata komai na rayuwa.
Hawaye ta hau gogewa domin kuwa tayi kuskure a baya wanda yanzu take danasani. Fu’ad na son ta amman ta tsaya shaidan ya rude ta tai yi wasa da damar ta wanda gashi nan yanzu tana ji tana gani ta rasa Fu’ad din wanda ta rasa Fu’ad domin shi ga shi nan da matar sa da ‘dan sa yana rayuwa peaceful amman ita ba auren ba jin dadin rayuwa.
“Ka yafe min Fu’ad ka yafe min ka rike min alkawari na.”
Tayi juyi tana fadin
“Allah nagode maka. Allah ka yafe min.”
*
**
***
****
*****
******
Ta mike tsaye shi kuma ya fara hawa gadon bai an karaba sai jin rufe kofar toilet kawai yayi dagowar da zai sai ganin wayam yai. Tsayawa yayi kawai yana murmushi.
Mikewa yayi yace
“Bashi kika ci sai ki biyani.”
Zai fita Maryama ta shigo. Tana ganin sa ta sunkunyar da kai tana murmushi tace
“yaya ina kwana?”
“Lafiya dariyar me kike ki fito fili ki fada”
“Naga an takurawa Anty nane jiya ma fa zuwa kai ka dauke ta ina kallon ka ka rabani da bed partner na.”
“Oh ido kike saka min ko?”
“No ba ruwa na kayi hakuri.”
Ya fice ta bishi da kallo sai ta juya tana fadin
“Kaji Yayan nan borin kunya dai kawai.”
Yana fita ya shafa kan sa yana murmushi. Dakin sa ya nufa Hajara ta fito zata kitchen ko kula da ita bai ba sai da tace
“Sannu!”
Sannan ya dago yace
“Kin tashi lafiya?”
“Alhamdulillah.”
Ya juya yai dakin sa. Wanka ya shiga yayi ya shirya cikin kananu kaya blue black wando da bakar riga. Kayan sun masa kyau sun amshe shi yai wanka da turare sai tashin kamshin turare yake mai dadi da sanyi. Yana gama shiri ya fito dan yin breakfsst yau zai koma ganinbdoctor kamar yadda yace masa yana zuwa duk kwana biyu har ya cika satin
A dining ya same su suna karyawa dukkan su banda Aisha. Maryama ya kalla yace
“Aysher fa?”
“Tana daki!”
“Taci abinci?”
“Eh!”
“Ok!”
Sai sannan shima ya fara ci. Suna gamawa suka koma Falo. Mamah ya kalla yace
“Mamah zan tafi asibiti.”
“Ok sai ka dawo. Allah tsare!”
“Amin!”
STORY CONTINUES BELOW
Sai ya fara sosa keya yace
“Uhmm Mamah daman Aysher ce zata rakani.”
Abbah! Mamah ta kalla. Yace
“Ai ai ba matsala jeka kira ta ku tafi.”
Ya mike ya nufi dakin nata.
Mamah tace
“Meyasa Alhaji?”
“Me zai mata to Fulani matar sa ce fa.”
“Ni gaskiya na fi son komai in ta tare haka a titi.”
“Haka ba zai faru ba kuma ba gobe dai xaku tafi ba.”
“Insha Allah.”
“To kada ki damu.”
Yana shiga dakin ya same ta zaune tana karyawa. Tana ganin sa tayi kasa da kai Maryama dake gaban mirrow tana kwalliya tana fadin
“Ke kin kwace min Yaya yanzu bai da magana sai taki komai ke ke dazu fa kasa karyawa yayi wai kina ina? Nace kina daki da tahowa zai ban sani ba ko ganin idon su Mamah ne dai bai taho ba wai kinci abinci nace Eh. Uhmm har da ajiyar zuciya fa sai a lokacin ya fara cin abincin ni nake gani soyayya abun abin sha’awa muma Allah bamu irin taki.”
Jin shirun yasa ta juya sai taga Aliyu tsaye ya kurawa Aisha ido wacce ke zaune tai kasa da kai dan siket ne na under wear a jikin ta sai vest Maryama ta, ta kura mata ta fara cin abinci dan taiwa Yaa AK karyar taci abincin shine ta zauna ta fara ci sai gashi nan.
Maryama kuwa mutuwar tsaye tayi dan ta san ya gama jin ta ma kanan. Shi kuwa sam bai ji ta ba hankalin sa gana daya yana ga Aishan sa. Sum sum ta fice a dakin dan tana tsora in yaji ta kar yai mata fada.
Tana fita ya karasa ya dawo gaban Aisha ya zauna yace
“Dan baki karya ba Maryamabce kin karya.”
“Cewa tayi sai na dada.”
“Uhmm ke da ita ko?”
Ya dauki fork ya fara bata a baki da kyar take amsa Sai da ya bata da yawa tace
“Na koshi.”
“Me kika ci kenan?”
” Dazu fa naci.”
“Hmm shikenan. Fita zamuyi tashi ki shirya.”
“To ka fita zan shirya.”
Murmushi yayi yace
“Na tuna dazu.”
Fuska ta bata kamar zatai kuka tace
‘Please ai kaine kaki ka yadda sai nayi wanka.”
“Uhmm yanzu ai kinyi ina jira.”
“Kai da kace fita za muyi kuma.”
Hannun ta ya kama ya mike ya hada ta da jikin sa ya sa hannu daya ya zagaye kugun ta dasshi yana fadin
“Ina zaune ana min wayo ko?”
Kai ta girgiza kan ta ya dago yana fadin
“Bani abu na!”
Ido ta lumshe kawai. Ya kalle ta yai murmushi kan ya sauko dashi ya kai kan lips din ta. A hankali ya fara kissing lips din nata gentle wanda yaje suka mata da sakko mai kashe jiki take jikin ta ya mutum. Sai da ya dauki mintina sannan ya sake ta yana sauke numfashi kamar yadda itama take saukewa. Yana sakin ta ta juya masa baya.
Kan gado ya isa ya zauna yana fadin
“Ki shitya.”
Gun wardrobe ta karasa da sauri ta zaro wata doguwar riga milk kala ta saka. Ta dauki wani hijab madaidaici baki ta saka. Turare ta shafa ta jyyo taya ita yake kalla kawai. Kai tayi kasa dashi. Tace
“Na gama.”
Mikewa yayi ya karaso inda take yana kallon ta yace
“My Beauty kin yi kyau. I love you.”
Hannu ta ya kamo suka fita falo. Suna zuwa wajen dining ta fara kokari kwace hannu ta amma yaki saka. Duk kunya ta kamata. A haka suka karasa ta duka har kasa ta gaisar da su Mamah da Anba.
“Mamah mun tafi”
Aliyu ya fada.
“Allah kiyaye.”
Suka fita. Driver ne ya dauke su suka shiga baya gaba dayan su har lokacin hannun ta rike da nashi yaki sakin ta, suna shiga Muhammad da Faisal suka dawo daga zaga unguwar. Faisal ya karaso wajen motar da sauri.
Glass ya sauke ya kalle shi ya daga masa kai. Murmushi Faisal yayi yace
“Uhmm mu da muka taho mu raka ka.”
“Nagode. Amaryata zata rakani!”
Kai Aisha tayi kasa dashi tace
“Ina kwana?”
“Lafiya Aisha ya jikin?”
“Naji sauki!”
“Allah kara sauki.”
“Amin!”
Yaa Muhammad taji ya zo take taji gaban ta ya fara faduwa. Lekowa yayi yace
“Ina zai je ne haka?”
“Asibiti.”
Yana ganin Aisha yace
“Ah ashe tare suke da Madam da zance bari muzo mu rakaka.”
A hankali tace
“Ina kwana Yaa Muhammad?”
“No bana amsar mike sai a titi za a gaisheni”
Tai kasa da kai idon ta na kawo kwalla.
Aliyu yace
“Kuzo muje mana.”
“A’ah a dawo lafiya.”
Cewar Muhammad.
Faisal kuma yace
“Daman wasa nake sai kun dawo.”
Suka tafi. Driver ya tayar da mota.
Juyowa yayi yana kallon ta. Kanta ya dago yaga tana hawaye take ya rikice yana fadin
“Menene My Ayshh?”
Kai ta hau girgizawa yace
“Ki fada min dan Allah ko wani abu nai miki.”
Hannun ta sa ta fara goge hawayen idon ta yace
“A’ah Yaa AK!”
Sai kuma ta fashe da kuka. Jikin sa ya jata yana lallashin ta da kyar tayi shiru yace
“Nima fa Yayan kine fada min me yake damunki?”
“Bansan menayiwa Yaa Muhammad ba ya canja min kana gani na gaishe shi wai baya cin mike.”
Murmushi yayi yace
“Shine kike kuka to?”
Kai ta gyada yace
“To ai dai kinsan Yayan nan ba muharammin ki bane ko?”
Kai ta gyada yace
“Yauwah yanzu kin zama matar aure dole mu’amalar ku ta canja bama da ya kasamce yana son ki da aure kin gane?”
Kai ta gyada yace
“Wannan yasa yake janye jikin sa ba dan kin masa komai ba.”
“Baya jin haushi na?”
“Baya ji My Baby!”
“Da gaske?”
Kai ya gyada. Sai kuma ta bata fuskar ta yace
“Amman meyasa yace baya son mike!”
“Yana miki da wasa ne. Kuma kema har dake dan me daga kinji an aura miki ni sai kina gudun kowa. Kamata yayi kiba shi dama yai miki bayani kema ai ba a son ranki akai ba shine shaida ko?”
Kai ta gyada yace
“Good sai kije kice Yaya dan me kayi haka?”
“Zai fada miki hujar sa in ta miki shikenan ki masa godiya shikenan Yaya ya koma Yayan gaske.”
Kai ta gyada. Yace
“Amman kin boye kai a daki sai kace sabuwar amarya. Oh ashe ita ce no wonder. Yanzu in mun koma zan rakaki sai kuyi maganar ku kinji ko amman banda masa shagwaba ni kadai za anawa kinji my baby love?”
Fuska ta rufe tana murmushi yace
“I love you My Baby love.”
Ya bude kofa dan anyi kusan 1minute da zuwan su asibiti ya fita ya kamo hannu ta ta sauko sannan ya rufe suka nufi enterance din asibitin.
Direct office din doctorn sa suka nufa yana zuwa ya knocking aka basu izinin shiga aiki yake a system ya dago dan ganin su waye yana ganin Aliyu ya mike yana fadin
“Masha Allah my patient dai yaji sauki!”
“Alhamdulillah!”
Ya kalli Aisha yace
“Oh me jinya da ta narke ko?”
Sukai dariya yace
“Have a seat!”
Zama sukai sukai musabaha da Aliyu da Dr. Aisha ta gaishe shi kanta a kasa. Ya amsa yace
“Ya jiki Madam da ta gudu?”
“Alhamdulillah!”
“Masha Allah.”
Ya kalli Aliyu yace
“Ya jikin? Duk da naga Alhamdulillah nothing more kuma?”
Kai ya gyada yace
“Gaskiya ni ku sallamen na bar muku kasar ku.”
“Sai ka kara sati uku!”
“Wooo ba zan iya ba guduwa zamuyi Allah.”
Yai murmushi yace
“Ka daure ka zauna for a week kamar yadda na fada naga yadda maganin zai maka. Ka gane shigar ciwo lokaci daya ne amman fitar sa a hankali kamar ka ji ciwo ne kan ya warke sai a sannu gefe da gefe su fara bushewa sannan a hankali sauran wajen ya bushe ya koma normal kaima haka muke so muga komai ya zama normal.”
“Hmm shikenan Allah yasa mu dace.”
“Amin yanzu ba abinda kake ji ko?”
“Eh a waccan matsalar ba.”
“Oh akwai wata matsala yanzu?”
“Eh!”
“Me yake damun ka.”
Aisha ya kalla ya sauya magana zuwa da yaren da mutumin keji. Yace
“Doctor ina jin wani abu a jiki na a duk lokacin da na kasance da ita?”Aisha ya kalla ya sauya magana zuwa da yaren da mutumin keji. Yace
“Doctor ina jin wani abu a jiki na a duk lokacin da na kasance da ita?”+
“Who?”
Aisha ya nuna yace
“Ita sai in ji ba abinda nake so in ba naji ta a jiki na ba ko dai wani abu da bana ji. Abun mamaki jiya sai gashi ina releasing a jikina ba tare da nayi having sex ba fa nayi har sau uku. Doctor ba matsala kuwa?”
Dariya Doctor ya saki har da rike ciki yace
“Aliyu baka taba aure bane?”
“Na taba mana kusan four year ma.”
“Haba dai amman kake fuskantar wannan abun a yanzu a da baka jin su.”
Kai ya girgiza yace
“Gaskiya ban taba ji ba sai yanzu.”
“Kana son matar kuma?”
Murmushi yayi yace
“Is my secret but Babana ne ya zaba min ita so i have to obey!”
“Ita wannan fa!”
Aisha ya kalla ya saki wani murmushi da ya kara masa kyau ya dafe zuciya yace
“My HeartBeat kenan!”
“Oh really kenan ita ta kwantar mana da kai.”
“Of course Dr! Dan ranar da Abbah ya bar kasar nan bai dawo ba sai da aure na da Ita. Dr bansan menene so ba akan ta na sanshi kasan me ni mata ba su damen ba ko kallon su banayi.”
Ya juya ya kalli Aisha ya kamo hannun ta yace
“Amman kagan wannan yar Baby da ita ko ta rikitan tunani na a gaskiya in nace zan fada maka yadda nake son ta zanyi karya i love her more than myself and anything else.”
Ya kai hannun ta zuciyar sa dake bugawa da sauri da sauri. Da sauri ta dago tana kallon sa suka hada ido tai saurin dauke idon ta daga kallon sa dan kwanan nan wani abu daban take gani a idon Yaa AK da ta kasa gane menene.
Murmushi doctor yayi yace
“No wonder! Kada ka damu dan Gaskiya wannan ba matsala bane. Abun da yake faruwa shine a da baka jin feeling ne akan matar ka kila batai maka bane ko bata abin da zai motso ka wanda wannan yana dada karuwa ne in da soyayya. Wannan kuwa son da kake mata shi ke kara maka son ta da wutar sha’awar ta ba komai kake ji ba sai feeling, kuma kada ka bari yai maka illa she is your wife just get rest with her i hope she love you in dai tana son ka kaje mata zata amshe ka ta baka kulawa kar kayi la’akari da yarintar ta. Sai kaga tai maka abinda wata babbar batai maka ba. Releasing kuma da kake kai kadai bansan me ka gani ba amman wasu mazan ko muryar mace na tada musu hankali har suyi releasing wasu kallon tsiraicin su, wasu just ma. Dan haka kai ga maganin wannan matsalar taka nan just zance good luck.”
“Thank you.”
“Never mind sai kuma ka kiyaye shan maganin ka kaji. Nan da two day ka dawo za ai maka wani test daga shi ba zaka dawo ba sai three day in naga yadda test din da jikin ka yayi shikenan sai a baka wasu da zaka tafi dasu. Yana da kyau kana zuwa check off!”
“Insha Allah. Dan Abbah yai fada.”
“Gaskiya ne ai yana da kyau ana duba lafiyar jikin mu akai akai dan wani ciwon bai tashi nunawa sai yaci jiki kaga in kana zuwa check off za a tare shi before then.”
“Haka ne.”
“Ok shikrnan babmatsala zance aje asha amarci lafiya.”
“Haba dai ai sai mun tare ko Dr!”
“Matar kace fa wane tarewa zaka jira kawai in kana bukatar abar ka have it.”
STORY CONTINUES BELOW
Tafawa sukai yace
“Shikenan nagode. Zamu tafi sai nan da two days din in Allah ya kaimu.”
“Allah kaimu ya bada lafiya. Allah yasa a samar mana twins!”
“Kai Doctor to Amin thank you so much.”
Ya mike ya kamo hannu ta. Ta kalli Doctor tace
“Sai anjima.”
Yqce
“Bye!”
Suka juya suka fice. A haka suka karasa wajen mota ya bude mata. Suna shiga mota yace
“Kai wajen shakatawa mai kyau.”
Motar ua tayar suka bar wajen basu tsaya ba sai a wani waje mai kyau da tsari. Fitowa yayi ya kama hannun ta suka nufi wajen.
Waje ne mai kyau da tsari ga wajen hutawa wajen soyayya wajen liluka da abubuwa na ban sha’awa da yawa. Wajen hutuwa suka nufa aka basu wajen su su kadai ba mai ganin su. Kujeru ne a wajen sai can gefe inda grass carpet ne an saka wani carpet akai mai taushi har da pillow a wajen. Hannun ta ya kama suka zauna anan kan carpet din mai taushi kamar katifa.
Sannan yasa akai musu order din abubuwan ciye ciye da shaye shaye. Cikin minti biyar an cika musu gaban su da kaya kala kala iri iri.
“Bismillah my Heartbeat!”
Kai ta girgiza. Hannu ya dauke daga kan lemon zai dauka ya dago yana kallon ta ya juyo da ita gaba daya tana facing nasa. Ya dago kanta yana kallon ta.
“Me yake damun ki?”
Kai ta girgiza. Yace
“Kinsan kin canja kuwa?”
Nan ma kai ta girgiza yace
“To kin canja My Wife kuma ni canjawar nan zai cuce ni please ba dan ni ba dan Allah ki taimakawa rayuwa ta ki dawo Ayshern da mai min hira da bani nishadi please My Baby love.”
Fuska ta rufe da hannun ta yace
“Yes wallahi i love you with both your attitude but na asalin ko?”
Ya lumshe ido.
Ya bude yana fadin
” Allah da bakya nin kunya ta amman yanzu ban san dan me wannan kunyar tazo duk zata sa a ki kulawa dani ba!”
Ya karashe maganar yana turo baki da kamar shagwaba wanda yadda taji ya kai maganar ta dago. Ganin sa a haka kuwa yasa ta tuntsire da dariya tana fadin
“Kai Yaa AK sai kace wani Baby!”
“Eh mana zama da My Baby Love ta koyan nima zan fara.”
“Uhmm ni ba wani nan me na ke yi na koya maka ni ban iya ba.”
“Ahaf gashi na wallahi i love you My Heart Beat. I really love you hakika da na rasa ki Baby love mutuwa zanyi Allah na so na da ya bani ke nake rayuwa tare dake. Aah nagode maka da ka bani Baby love Allah ka bar min ita har karshen rayuwa ta. Allah ka bani ikon kulawa da sauke hakkin ta Allah ka bani ikon faranta mata. Amin!”
Hannun ta ya kama yace
“I love you Baby Love!”
Kai ta dauke yace
“Please My Heart beat kice you love me too.”
“But Yaa AK you know i do so!”
“I know but partially i want to hear it now with a romantic care nd love please say ita.”
Ya fada yana matsowa jikin ta. Kunya ya bata ma tai saurin yin kasa da kai yace
“Please My Heart beat.”
“Yaa AK I love you!”
Ido ya lumshe sai kuma ya bude yace
“Ba dan wani karya murya.”
Ido ta zaro yace
“Eh mana. Ki fada wanda zanji kamar in mutu ko in suma in dawo.”
Ido ta zaro tace
“No bana son kai ko daya.”
“Ok wanda zanji dadin da ban taba ji ba. Kinsan me My Baby love?”
Kai ta girgiza ya sauke ajiyar zuciya yace
“In na fada miki Abu zako yadda?”
“Haba Yaa AK why not?”
Hannun ta ya kamo yace
“Bansan so ba sai akan My Wife ban San menene shi ba Sam Sai akan ki na sani. Tin haduwa dake na fara son ki Amman da yake ban San menene son ba ban kawo komai ba nasan tin a Ranar da muka fara haduwa to daga Ranar na rasa kwanciyyar hankali ba Wai da wani abuba no da na rufe Ido Sai naji sautin muryar ki na yawo a kwalkwalwata na rasa Yaya zanyi.
Kinsan ban son surutu ko hayani Amman a Ranar ji nayi inama mu kwana tare ki nai min magana. My Baby love Allah ne ya hada mu a lokacin Kuma ya Sanya min son ki.
Lokacin da Kika tafi akan Zaki dawo gobe Baki dawo ba kinsan irin halin da na shiga. My wife na shiga halin da ban taba shiga a rayuwa ta ba har ciwo nayi a gun aiki ba wani aiki nake ba a gida so lonely abinda nake yake deben kewa in nayi baya min Sai naji ya gunduren!”
STORY CONTINUES BELOW
“Menene abun!”
Wani murmushi yayi yace
“A da Abu daya kesani nishadi shine na zauna a Waje Mai yalwar haske da iska da kukan tsuntsaye nayi shiru kawai wannan shi ke sani nishadi nai ta annushuwa da fara’a Amman bayan, shi ko Ina reciting of holy book. Bayan wannan nothing more makes me happy My Heart Beat!”
“Abun mamaki!”
Yai murmushi yace
“Wallahi Ina mamaki but tin Ina yaro haka nake shiyasa.”
Kai ta jinjina yace
“A haka na dinga damun my gate man akan kin zo Dan lokacin da ya barki Kika shigo na farko ni nasaka shi nace next in kinzo ya barki ki shigo saboda na Saba da na dawo aiki in na hau barrander Ina ganin ki kinzo kuna magana kawai naji kin fara burge ni har ta Kai wata Rana na sauko naji akan me kike magana akan zaki shigo ne. Nayi mamakin me Zaki zo ki min. Amman bayan tafiyar ki nace ya barki ki shigo wannan shine Yasa ya barki the next day.
A Ranar da muka hadu ban taba haduwa da yarinya Mai confidence irin ki ba.”
Ya ja hancin ta yace
“Kin burgeni My Love domin nayi mamaki ba wanda ya taba kallon Ido na yai fadan Abu kamar ke abun ya min shock but ya tsayan a rai. Aysherrr na rantse Miki da Allah ban taba tsayawa na kalli wata mace in ba Mamah da Maryam ba a duniya sai ke a Ranar. Dan ko Matata Hajara ba tsayawa nake Ina Kura Mata Ido ba Amman ke bansan me yasa ba na kasa Hana kaina kallon ki. Wanda daga Ranar Kika bace min Kikasa na shiga tashin hankali.”
Hannun ta ya kamo yace
“Kan na daura ki fadan wane Hali Kika shiga haka har ya sa Kika debe more than two month ban ganki ba?”
Hannun sa ta Kara rikewa tace
“Na fada maka ciwo nayi. But kasan me an samu matsala kamar yadda na nuna maka matsalolin asibitocin mu. Irin haka ta faru Dani da aka kaini kin amsata sukai sai chemist mukaje yazo ya samin ruwa duk da haka na dinga ciwo sai da kyar da hanya aka amshe a asibiti nayi kwanaki aka sallamo mu na dawo gida. Duk sai na rasa kwarin jiki na. Wannan yasa Baba shi Kai ni both Islamiyya da Boko kasan me Nima kana Raina Ina so na samu dama Nazo wajen ka Amman ban samu ba sai Ranar sukar mu Naga wani kamar Kai Amman kan na farga na nemeka na rasa.”
Murmushi yayi ya murza hannun ta yace
“Nine Kuma Nima ina zuwa da murya ki na fara arangama tana karatun alkur’ani Mai tsarki abinda nafi kauna kenan. An kawon katin gayyata Nima ganin sauka ce nice shi zanzo Ashe Allah yayi Zan ganki. Ranar ni kadai nasan halin da na shiga na farin ciki na ganki da anfara zata ma gamo nayi.”
Fuska ta Bata ta Kai Masa duka tace
“Ni din ce aljanna!”
“Ai ke din ce kamar ita at firrst seen kin sacen zuciya Kuma kin barmin Amon muryar ki na karaden zuciya kunne da komai gashi daga Ranar ban sake ganin ki ba. Dan Allah ko kece Kika irin haka me zaki ce?”
“Haka ne Amman kai kada ka Kuma ce min aljanna.”
Ido ya zaro yace
“Haba My Wife is not Spirit shikenan?”
Kai ta gyada. Yai murmushi yace
“Da kika dawo naji Dadi Kuma fara karatun mu ya kaean son ki da shakuwa dake duk ban sani ba. Kinsan me yake Karan sonki?”
Kai ta girgiza yace
“Surutun ki.”
Ido ta zaro tace
“Surutu na to na daina.”
“Haba my love sorry!”
“Yanzu a rasa Dame za a Soni sai talkative haba Yaa AK!”
“Ki tsaya kiji Mana. Ai your talkative is on important things My Ayshh in Zaki magana komai kankantar ta sai na Karu da ita Allah ka bani Baby like you My Heart beat!”
Ya daura hannu a kan cikin ta da sauri ta runtse Ido Dan ji Tayi kamar a fatar jikin ta ya daura hannu. Yace
“Sai ilimin ki kina da kwakwalwa da kin tashi a burni sosai da kune Wanda ake Kira gifted but yanzun ma Alhamdulillah. Hangen nesan ki, rashin son abin duniya, rashin son Kai, tarbiyyar, ladabi, biyayya, sai wannan hancin naki.”
Yaja hancin. Hannu ta fara yarfewa tayi kamar zatai kuka tace
“Da zafi fa!”
Hancin ya fara shafawa yace
“Ayyah sorry sorry nine ko Rama to.”
STORY CONTINUES BELOW
Kafada ta make. Yai murmushi ya shafa idon ta yace
“Wannan sun fi gold da lu’u lu’u da diamond kyau da komai My Aysher I love them. “
Ya shafi lips din ta soo romantic yace
“Wannan ni kadai nasan the secret behind them. I love it in Ina kissing Ina Jin kamar na cinye shi.”
Fuska ta rufe tana murmushi yace
“My Aysher ke dukkan ki kinyi Ina son komai da kike dashi komai da ya rabe ki komai da ya dangance ki. Son Allah nake Miki domin to gani na dake nan san ko ke wacece ba na kamu da son ki. Allah shi yasan me ya boye a tsakanin mu. Amman Ina son ki My Baby Love.”
“Kinsan me?”
“Aah!”
“Lokacin da naje Saudiyya anan muka hadu da wannan friend din nawa childhood friend Dina ne he is like a brother to me dqn Yana so na Yana tolerating all my attitude since then so shi ya ce min son ki nake I can’t believe Wai son ki nake sai da ya min tambayoyi na bashi amsa ya tillasta min da sonki nake. Daga baya ba yadda zanyi nayi accepting kawai na yadda Ina son ki daga Nan Zaki gani our relationship was changed at all Aysher kema daga lokacin kika fara Jin kunya ta. Tell me So na kika fara a time din.”
Kafada ta make Taki magana yai murmushi sa Mai kyau yace
“Wata Rana Zaki fadan ba sai na ce bama. Aysherrr I suffered for your love. But at the end you are mind I thank Allah, Baba, Muhammad, Mamah, Ummah and Abbah and also Mr President Allah duk ya biya su da gidan Aljanna sun nunan so da kauna.
At last Zan fada miki ban taba soyayya ba Aysherrr ni tsoron Mata nake Dan I having headed so many issue on Girls am so afraid of Girls Aysher shiyasa ko kallon su banayi Bare har nai falling in love with one of them
Ya ja numfashi yace
“daga lokacin da na hadu Na kalle ki daga lokacin na kamu da son ki daga lokacin Kuma ko na kalli mace tamkar Namiji na kalla haka nake gani. “
Ya shafa kirjin ta yace
“Duk da a lokacin ban san wata sura dake jan hankalin maza wajen mace ba. Dan ke kan ki lokacin u re too young, , Aysher ke Yar baiwace kin zo kin savce zuciyar Dan yaro ko?”
Ido ta zaro tace
“Waye yaron?”
“Gani!”
Hannu ta tafa tace
“Tab tsoho dai!”
Ido ya zaro yace
“Why nine tsohon ohhk kin auri tsoho Kinga Zan shafa Miki tsofan kema ki zama tsohuwa soon!”
“A’ah ni a’ah!”
Yai murmushi yace
“Ni ba tsoho bane kema Kuma ba Zaki zama tsohuwa ba har abada kinji ko?”
Kai ta gyada ya jawo ta ya rumgume ta. Kai ta kwantar a kafadar sa yace
“I love you My Sanam!”
“What it means”
“Masoyiya tah!”
“Oh ni in Zan ce masoyi fa?”
“Your Dil!”
“But ke da baka soyayya a Ina ka sani!”
“Ina Jin yaren ne naje garin nayi wani aiki for three years!”
“Oh!”
“Da kin fara kishi ko?”
Kai ta girgiza yace
“Fadi gaskiya dai.”
“Gaskiya na fada domin na yadda da duk abinda ka fada min”
“I love you My Sanam!”
“Love you My Dil!”
Da sauri ya dago ta Yana fadin
“Are you sure?”
Kai ta gyada sai ya Kuma rumgume ta kamar zai maida jikin sa Dan Sai da ta Dan saki Kara sannan ya sassauta rikon da yai Mata Yana murmushi itama murmushi yayi.
Tashi muci abinci ko ta mike. Ya dinga bata a Baki da ya Bata bakin ta zai sa harshen da lashe. A haka suka gaba suka Mike suka zaga wajen. Da akai azahar shi ya jasu sallah suka idar Nan suka zauna Yana Bata labarai tana ta Dariya.
Sosai ya dawo da ita Aishan sa ta baya domin kuwa ta sake dashi ta.
Da yamma suka Mike ya Kai ta ta hau Lilo ya dinga mata pictures sai da sukai sallah magarib sannan suka tafi wani restaurant sukaci abinci sannan suka shiga wani supermarket ya dinga jidar Mata Kaya kamar bai san zafin kudi ba. Sai da ya gama ya siyo Mata chocolate da ice cream kala kala sannan akai total sukayo gida.
*
Mamah kuwa tin yamma da taga Basu dawo ba ta daga hankali ta. Ta dinga zagaye dakin su Abbah na zaune ya na kallon ta daya gaji ya janyo ta yace
“Wai Menene Fulani na. Kada ki manta yaran Nan ma aurata ne komai ya faru ba matsala.”
“But Abbah bai Dace ba yafi ya sameta a dakin ta.”
“Kada ki damu Aliyu ba zai wani Abu ba.”
“Uhmm idan yake wannan rawar kafar fa?”
“Ni na fada miki kibkwantar da hankalin ki ga passport dinki gobe da yamma sai tafiya.”
“Allah kaimu.”
“To Nima azo a kupa Dani ana ta damuwa da amarya.”
*
Su Mamah na zaune a falo gaba dayan su suka dawo. Aliyu na rike da hannun ta suka shigo tana ganin su ta kwace hannun ta tayi kasa da Kai ta karasa tace
“Sannu da gida Mmah!”
“Yauwah Aisha kin dawo lafiya?”
“Alhamdulillah!”
Abban ta kalla tace
“Sannu da gida Abbah!”
“Yauwah Aisha kin dawo lafiya?”
“Alhamdulillah!”
Sannan ta mike tayi daki da sauri. Mamah ganin tana tafiya normal ta saki ajiyar zuciya.
Ya karaso ya durkusa yace
“Barka da dare Abbah!”
“Yauwah Aliyu kin dawo lafiya?”
“Alhamdulillah!”
“Ba wata matsala dai ko?”
“Babu Abbah!”
“Masha Allah!”
“Ya dai ce In je Nan da kwana biyu Kuma daga Nan sai kwana uku shikenan Kuma sai tafiya!”
“Masha Allah!”
Mamah Ya Kalla yace
“Barka da gida Mamah!”
“Yauwah Baba na kun dawo lafiya.”
“Alhamdulillah!”
Gun Faisal yayi suka tafa yace
“Ya gida?”
“Alhamdulillah!”
Ya mikawa Muhammad hannu suka gaisa yace
“Ya gida Inlaw?”
“Alhamdulillah!”
Yace
“Bari naje na watsa ruwa.”
“In ka watsa kazo Ina neman ka.”
“To Mamah ko nazo yanzu?”
“A’ah kaje ka dawo.”
“Toh!”
Yayi ciki. Dakin su Maryam ya kalla kai ya sa ya shiga ya samu Aisha zaune a gefen gado. Shiga yayi ta dago ya sakar Mata murmushi itama ta sakar Masa yace
“Ya dai?”
“Ba komai kawai ka barni da kunya ne!”
“Kunya kumw?”
“Eh Mana su Mamah!”
“Me suka ce Miki?”
“Sai sun fadayaa AK!”
“Matata ce fa me mukai!”
Mikewa tayi tace
“Kaga jeka ni wanka zanyi!”
“Nazo muyi!”
Ya fada Yana bin hayan ta tana juyowa taga haka ta diba a guje tayi toilet ta saka key.
Dariya yayi ya juya ya fita kawai. Yana fita ya shiga dakin hajara zaune ya same ta rike da waya. Mikewa tayi tace
“Ina kaje yau?”
“Asibiti na shigo kina Bacci time din?”
“Ok!”
“Bari naje nai wanka!”
Ya fada Yana fita. Yana Shiga ya cire Kaya yai wanka. Yana fitowa yai isha’i sannqn ya shirya. Falo yayo yaga an shigo da kayan da suka shigo dasu. Maryama da ta fito a kitchen yace
“Maryama kaiwa my heart beat!”
Duk kallon sa sukai jin sunan da ya fada. Maryamakam Bata damu ba tace
“Lah Yaya kun dawo sannu da zuwa!”
“Yauwah!”
“Abinci fa?”
“Na kos cuthi sai dai ko My Heart beat Dan Naga Bata son cin binci.”
“Haka take Yaya!”
“Shine Baki fada min ba!”
Kunne ta kama tace
“Am sorry!”
Yace
“Jeki Kai Mata in tana bukatar wani Abu ta fada miki sai a Samar Mata.”
“Angama Yaya!”
Ta juya ta kwashe ledar biyu manta tayi dakin su.
Mamah ce tace
“Baba na Daman gobe zamu tafi.”+
“Allah sarki Mamah na ai kinyi ma Allah ya kaimu ya tsare hanya.”
“Amin Daman nace zamu tafi da Aisha da Maryama sai mu bar maka Hajara ko?”
“Au har da Aysher za a tafi Mamah da kin barta itama.”
“A’ah da ita aka shirya tafiya Dan haka kayi hakuri kawai.”
“Mamah ai za’a iya daga tata.”
“Kawai kayi hakuri haka na tsara ba zan tafi na bar maka su dukka anan ba.”
“To ai da sai a tafi da Hajara ko?”
“Oh hakan bai ba kenan?”
“A’ah Mamah yayi Allah saka Amman!”
“Amman me?”
“A’ah shikenan!”
Ya mike yayi dakin sa. Yaa Muhammad yace
“Mamah ai da an bar ta.”
“Muhammad kyale shi sauran kwana biyar Kuma fa ku taho.”
“Shikenan!”
Ya mike yabi bayan Muhammad.
*
Zaune yake ya jingina Kai da kujerar dakin nasa. Da sauri ya karasa yace
“Haba Inlaw me yq faru?”
Ya dafa shi. Dagowa yayi yace
“In-law bana son Mamah ta tafi min da Matata wallahi.”
“Kayi hakuri kayi biyayya ga Mamah kaji.”
“Naji Amman ban San ya Zan kasance ba in Bata Nan.”
“Haba Mana kwana biyar fa ya rage kamar yau ne.”
“Kai kaga haka ni gani nake kamar shekara biyar.”
“Sorry In-law kayi hakuri.”
“Ya zanyi Dole nayi hakuri ai Amman I will miss My Heartbeat!”
“In ka koma ba shikenan ba Sai ku dauwama.”
“Nagode! Zauna ina zuwa!”
Ya mike ya fita. Dakin su ya shiga ya same ta sanye da kayan Bacci riga da wando da hula Akan tana ganin shine ta dauki hijab ta saka. Murmushi kawai yayi yace
“My Heartbeat manya! To zo muje!”
Maryama ta kalla tace
“Ina zuwa!”
“No kice Mata kawai sai da safe.”
“Ni ba Zan kwana a gunka ba.”
“Naji muje.”
Suka fice Maryama tana murmushi.
Suna fita. Suna fita ya Kama hannun ta. Dakin sa suka wuce suna shiga taga Yaa Muhammad ta kwace hannun ta. Shiga yayi ta tsaya. Aliyu yace
“Zauna Mana!”
Zama tayi a gefen gadon yace
“To ga shi Nan na kawo ki wajen sa Sai kiyi complain din ki.”
Ya juya zai fita. Yaa Muhammad yace
“Ka tsaya Mana.”
“No yazu Zan dawo ku gama.”
Yana fita tace
“Ina yini?”
“Lafiya Lou Kanwata ya kike?”
“Lafiya Lou!”
“Menene?”
“Uhm uhmm Daman Yaya nace me nai maka ka daina kula ni?”
“Au Aisha nine na daina kuka ki ba kece ba!”
Kai ta gyada yace
“Ni ai bana ganin kine!”
“Uhmm to Yaya meyasa ka yadda?”
“Na yadda da me?”
“Gashi Nan!”
Ta nuna dakin. Yai murmushi yace
“Aisha ki dauka haka Allah ya kaddarta. Kad maki manta wani baya auren matar wani Dan haka ki dauka kawai AK shi Allah yayi mijin ki ne. Ki godewa Allah da ba mutuwa nayi ba aka game aka aura Masa Baki san rabo na kisa ba. Wlhy in naki sai kiga na mutu an aura Miki shi Amman yanzu gani gaki lafiya Kuma an aura Miki shi. Aisha AK na son ki dan hakanl kema ki so shi ki masa biyayya mutum ne da in kin zauna Zaki gane Babu kamar sa. Allah Baku zaman lafiya kada kisa damuwar komai komai ya wuce a Guna ina muku fatan alheri Ina son AK ko Dan yadda yake son ki Ina fatan kema kina son Malamin naki?”
STORY CONTINUES BELOW
Fuska ta rufe tana murmushi tana Kuma hawaye. Yace
“Kinga ya Isa ki daina kukan Nan Dan Allah menene na kukan!”
“Yaya Kai fa?”
“Allah zai kawon wata insha Allah kinji.”
“Yaya ina tausayin ka saboda me kayi haka ka hakura ni nace ban son ka ne?”
“Aisha wanda yake Miki so irin na Aliyu ba karamin masoyin ki bane ki rike shi hannu biyu insha Allah ba Zaki danasani ba kinji ko?”
Kai ta gyada tace
“Yaya ka yafe min dan Allah!”
“Baki min komai ba Aisha ni nai Miki lafi ki yafen.”
“Ba kai minbKomai ba Yaya na.”
“To ki daina kuka. Allah ya Baku zaman lafiya kinji.”
Kai ta gyada. Ya mike yace
“Zanje na kwanta sai da safe!”
“Allah tashe mu lafiya.”
Ya fita. Yana fita ya samu Yaa AK d aFaisal a falo yace
“Har me?”
“Mun gama.”
“Ba wata matsala ko?”
“Babu!”
Suka dan taba Hira ya mike yace
“To ni sai da safe.”
“Allah bamu alheri.”
Dakin su ya shiga ya ga ko ta koma yaga Maryama ce kadai a ciki fita yayi yai dakin sa.
Kukan ta Tasha Mai isar ta tafi minti ashirin sannan ta goge fuskar ta ta Mike zata bude kofa kenan aka budo kofar shigowa yayi ya tsaya kallon ta can ya kamo ta yace
“Me akai miki?”
Kai ta girgiza, yai murmushi yace
“Ko na sake ki ki koma waje sa?”
“Saboda baka sona ko?”
Dariya ma ta bashi ai kuwa ya saki dariya bata taba ganin sa yana dariya kamar haka ba dan har da rike cike. Baki ta saki tana binsa da kallo sai da yayi mai isar sa sannan yakamo hannun ta kwacewa tayi ta juya masa baya wai ita tayi fushi yamike yana murmushi ya kamo ta ta kuma kwacewa.
Batai aune ba sai jin tayi ya dagata sama sai kan gado. Kafa tahau shushurewa tana kukan karya ya rumgumo ta yace
“To menene?”
“Ba kai bane?”
“Me nayi?”
“Kake min dariya!”
“Oh to bari na zane ni!”
Ya daga hannu zai mari kan sa ta rike hannun da sauri yace
“Ni nace kayi ne?”
“To ba ya saka ki kuka ba!”
“Na hakura!”
“Da gaske?”
Kai ta gyada ya koma ya kwanta ya mika mata hannu. Jikin sa ta fada yana fadin
“I love you My Heartbeat!”
“I love you More Yaa AK!”
Yai kissing goshin ta sai kuma sukai shiru na kusan minti biyar. Leka fuskar sa tayi taga idon sa biyu. Hannu tasa ta dan mazmsa cakulkili ai da sauri ya dago yana kallon ta.
“Me yake damunka Yaa AK?”
Abinda Hajara bata tabai masa ba kenan dan bata taba gane damuwar sa ba to bama kula take dashi ba bare har ta gane damuwar sa.
Shirun da yayi yasa ya mike zaune tana fadin
“Yaa AK me ya faru?”
Tai maganar kamar zatai kuka.
Mikewa yayi ya jingina da gado tare da janyo ta ya daura akan cinyar sa yace
“Baby love Mamah ce!”
“Toh abin Babba ne!”
Dariya ya saki. Tace
“Kayi hakuri kabi kome Mamah tace nasan ba zata taba yi maka abinda xai bata maka ko ya sosa maka rai ba ko wanda ya sabawa Allah. dan haka kayi hakuri kayi biyayya ga Mamah kawai. Kasan ance in kana so kagama lafiya lafiya ka farantawa Mahaifiyar ka, in kana son arzikin ka ya tsaya koman ka ya tsaya duk abinda ka sa a gaba kaga ya ci to ka zauna da iyayen ka lafiya dan haka Yaa Ak kaima kayi hakuri kabi abinda suke so!”
“Ina son ki Aysher abunda ke kara burgeni dake fadar gaskiya da nusar da mutum. Ina son Mamah da Abbah domin iyaye nane ban taba saba musu ba.”
“Haka nake so Yaya na!”
STORY CONTINUES BELOW
Ta fada tana kamo kansa tana shafawa. Yace
“Kinsan me tace min?”
“Uhm uhm amman ya shafen ne?”
“Sosai ma kuwa!”
“Dan mun fita dazu ko?”
Ta fada kamar zatai kuka. Yai murmushi yace
“A’ah!”
“To me mukai?”
“Dauke min ke zatai wai bazaku jirani ba. Gobe take so ki bar kasar!”
“Ka Yaa AK ni na zata wani abu ne!”
“Oh wannan ba wani abu bane?”
Kai ta gyada tana murmushi.
“Oh haka kika ce?”
“To ya za ayi su Mamah sunyi gaskiya ai sauran sati nawa ka taho kaga.”
“Au har sati kike kai ni. Shikenan in na dawo kowa zai ganni ban dake!”
Dariya tayi tace
“Ai ba zaka ka iya ba.”
“Au dan kinsan ba zan iya ba ko? Au ni waya kai ni fada miki irin son da nake miki yanzu duk zakina min wayo!”
Hancin sa taja tace
“Ba kai kadai ka fadan yadda kake so na ba. Maryama da Yaa Muhammad duk sun fada min kuma ba za suyi min karya ba kaga kuwa na gama gane ka.”
“Dan Allah to kada a na cin zalin dan bawan Allahn nan.”
Dariya kawai tayi ta kwanta a kirjin sa. Yasa hannu ya zare hular kanta jelar ya gani ta tufke nan ya fara warware ta, sai da ya ware tas sannan ya baza gashin a gadon bayan ta yana shafa gashin nata.
Hannu ya saka a ciki yana susa mata tare da mata wani irin abu a kan nata. Ido ta lumshe tana jin abun da yake mata yana mata dadi. Jin abun yaki ci yaki cinyrwa yasa tace
“Yaa AK bari naje na kwanta na fara jin bacci.”
“Kiyi abinki dan yau ma anan zaki kwana!”
“Anan?”
“Gobe fa tafiya zakiyi ki barmi My Heartbeart!”
“Uhmmm….”
“Please Baby love!”
Zamewa tayi daga jikin sa ta kwanta yaja musu bargo yana janyo ta jikin sa. Lafewa tayi a jikin sa. Take ya fara yin wani yanayi a tare dashi. Hannu yasa zai zare mata riga ta rike da sauri kirjin ta yana bugawa da karfi da karfi.
“Yaa AK…”
Ta fada a hankali. Yace
“Uhmm menene?”
“Ka bari!”
“Ba abinda zan miki Wife just want to feel your worm body!”
Ido ta runtse yai kissing wuyanta. Bata san lokacin da ta saki hannun sa ba shi kuma yai amfani da wannan damar ya zare mata rigar ta. Amman sai yaji half vest a jiki ta hannu yasa ya zare ta da sauri ta fada jiki da. Jin dukiyar fulanin ta a jikin sa ya sashi ya fara charge. Cikin sauri yasa hannu ya zare mata dogon wandon jikin ta.
“Yaa AK!”
Ta fada a dai dai kunnen sa wanda sautin da dumin numfashin ta yasa tsigar jikin sa tashi.
Jin yadda zuciyar ta ke buguwa yasa ya rumgume ta kawai, a hankali yaji zuciyar ta na dai daita. Can kuma yaji tana saukar da numfashi ta a hankali. Sai da aka jima ya daga ta ya fara kallon surar jikin sa. Kamar jiya sai da ya yi releasing wajen sau uku sannan yaje yai wanka ya dawo ya kwanta ya rumgume ta a jikin sa.
*
**
***
****
*****
******
*******
*
Da safe ta gyara gidan sannan ta hada break. Wanka ta shiga tayi ta fito ta tada Annur tai masa wanka ta shirya shi sannan tace Yaje ya dauko kayan sa. Duk da bata fiya fita aiki weekend ba wannan karan ji tayi ba zata iya xaman gidan ba kwara taje aikin ta kawai.
Fitowa tayi cikin shiri ta sanye da Hijab Maroon kala yai mata kyau Momy da ta fito daga Dakin Baba tace
“ina kuma zaki?”
“Asibiti!”
“Amman yau asabar ko?”
“Eh Momy akwai wandan da na bawa appointment ne kuma akwai wacce jiya nayiwa CS ina so naje naga jikin ta.”
“Amman Fateema… Shikenan sai kin dawo Allah bada sa’a.”
“Amin!”
Ta fada ta shiga ta gaida Baba tace
“Yau kuma ina zaki?”
“Asibiti.”
“Ke da bakya shiga asibiti asabar da lahadi.”
STORY CONTINUES BELOW
“Wani aiki xanje nayi.”
“To Allah bada sa’a. Allah kiyaye.”
“Amin Baba.”
Ta fita ta isa motar ta ta kunna tai worming nata sannan ta tayar ta bar gidan. Tana zuwa asibiti ba abinda tayi sai aiki da tayi a system din ta daga baya ta shiga ta duba patient dinta dake kwance da wanda tayi wa aiki sunyi mamaki ganin ta shigo yau weekend.
Haka ta yini a asibitin tana ta aiki dan bata son ta fiya saka abu a ranta yanxu ta daina yadda tana saka damuwa aranta ta gane kowa kansa ya fiso dan haka zata iya takun ta itama.
Karfe tara ya iso bangaren su Fateema shida Annur. Momy ya sama ya gaisar da ita ta amsa sannan Annur yayi dakin Teema yana shiga yaga bata nan ya fito ya shiga dakin Baba can ma bata nan dan haka sai ya fito ya kalli Momy yace.
“Granny where is my mum?”
“Ta tafi aiki.”
” ni akaini wajen ta.”
“Zo nan zan kai ka anjima kaji.”
Yasmeen ta da fito zata tafi tahfiz tasa ta kawo masa alawa da biskit. Ta gaida Fauwaz ta fice ta bar gidan.
“Kaje ka karya sai ka kaiwa matar taka nata ko?”
“Thank you Mom!”
Ya isa dining din ya fara cin abinci yana fara ci yasan girkin Fateema ne hakika yayi missiing girkin nata sosai. Yana ci yana lunshe ido. Bayan ya gama.ya kaiwa Gloria.
Ranar a bangaren su Fateema ya yini yana son ta dawo ya ganta amman har yamma bata dawo ba. Can wajen shida yace
“Sai yaushe Fateema take dawowa ne?”
“Yanzu zaka ganta dan bata kai dare kasan bata son driving din dare.”
“Haka ne. Allah dawo da ita lafiya.”
*
Har shida tana asibiti bata da niyyar tafiya gida ma. Tana zaune sai kawai jin kiran magarin tayi. Mikewa tayi tai sallah sannan ta zauna tana tasbihi jin ta tayi sam bata son komawa gida dan bata so ta kara ganin fuskar Yaa Fauwaz.
Tana zaune taji ana kiran isha’i sallah tayi sannan tayi shafa’i ta mike ta dauki kayan ta ta fice. A hankali take driving har ta isa gida karfe 8:15pm. Motar Yaa Kamal ta gani ta tabe baki ta fito kawai.
Jakar ta dauka tayi cikin gida ta shiga da sallama dukka suka amsa mata. Annur ya taso a guje ya rumugume ta yana fadin
“Welcome Mum i miss you.”
“Miss you too my so!n”
Ta fada tanandaga sa. Sai tace
“Kai ashe kana da nauyi.”
Yaa Kamal ta fara gani tace
‘Ina yini?”
“Lafiya ya aikin?”
“Alhamdulillah!”
Ta isa gun Suraiyya tana fadin
“Ina Dad dina?”
Yana wajen Baba.”
Juyawa tayi zata shige Fauwaz da tinda ta shigo yake binta da kallo ya kasa daina kallon ta dan Hijab din ba karamin kyau yaga tai masa ba yana son hijab yana son kuma yaga mace ta saka Hijab sai dai ko da wasa yasan bai isa yace Gloria ta saka Hijab ba.
“Sannu da xuwa!”
Ya fada lokacin da tazo zata wuce ta gefen sa ko kallon sa batai ba bare ya sa ran zata amsavmasa. Tana wucewa Annur yabi bayan ta.
Dakin Baba ta shiga ta dauko Twins ta nufi dakin ta dasu da Annur dake bin bayan ta. A kan gado ta ajiye su ta bawa kowa alawa da biskit sannan ta fara cire kaya. Wanka ta shiga tayi ta fito. Zaune ta samu Suraiyya a wajen ta hau shiryawa bayan ta gama ta zauma Suraiyya tace
“Dama kina shiga asibiri weekend?”
“in ta kama ina shiga!”
“Ke dai?”
dagowa tayi ta kalle ta tace
“Me?”
“Shukenan sai ga kuma Yaa Fauwaz ya dawo har da tsaraba Boy.”
Kan Annur Fateema ta shafa tace
“My son ba.”
Suraiyya tace
“Amman kuma wai ya auri Christian!”
“Menene a ciki to Sis ai yaga ta masa ne ko za ai masa dole ne?”
Murmushi Suraiyya tayi tace
“Ko kishi kike?”
“Kishi kuma akan wa? Wannan matar? Allah ya kiyaye yanzu wa zan wa kishi in ba Fu’ad.”
“Hmm Fateema kenan true love never end fa.”
“For Fu’ad ba.”
“Nasa fa?”
“Ina son sa amman da kenan yanzu na daina.”
“A’ah fa Sister.”
“Please Sis ki rabu dani da maganar nan ni yanzu ba aure ma a gabana karatu zanje na karo ma kwanan nan.”
“Ai kuwa sister auren shine cikar mutunci.”
“Uhmm haka ne amman ya zanyi ki fada min ya zanyi? Na cire rai da aure da ko wanne da namiji Uncle yazo ya running heart dina na amince amman kina ganin yadda abun ya kaya dai.”
Dafata Surauyya tayi tace
“Ki kwantar da hankalin ki ga Yaa Fauwaz nan ai ya dawo.”
“Ce miki yayi yana so na?”
“Wallahi Yaa Fauwaz yana son ki kuma ba zai taba daina son ki ba. Saboda son ki da kishin ki fa ya tafi.”
“Wai wannan wane irin so suke min shi da Fu’ad ne. shi yace ya tafi dan yana so na da son farin ciki na, and now kice Fauwaz ma haka shi dan me zai tafi na sani a time din shima haka yace. Ya tafi dan yana kishina ba zai iya tsayawa ya ganni da wani ba shin da kalaman wa zan yadda waye yake min son gaskiya kaina ya kulle haka Uncle fa yai min wai yafi kowa sona a hakan shi gashi nan muna rayuwa tare amman ya barni na yadda da ake cewa maza akwai dadin baki yanzu dawa zan yadda.”
Hawaye ya fara zuba a idon Fateema.Anuur ya matso yana goge mata yana fadin
“Stop Crying Mum.”
Murmushi tayi ta shada kansa. Suraiyya tace
“Haka ne wannan duk kaddarar kice ba kuma mu san akan wa zata fada ba dan haka kiyi hakuri amman zan kara fada miki bqkin da ya furta so ba zai taba furta ki ba indai son gaskiya ne. Kuma dukka ukun nan Fu’ad, Uncle Aslam da Yaa Fauwaz suna son ki, son gaskiya kowa akwai wani abu da ya boye a ransa ne Allah zaba mafi alheri ya tabbatar miki da alheri a rayuwa.”
“Amin nagode Sis sosai.”
Ba komai. Ta dauki Farouk tana fadi
“Baba na ya kara girma wata bakwai fa ya sun fara dabo.”
Waya ta zaro tace
“Ai na miki vedio na tura miki ta whatsapp ma dan baki hau bane.”
“Uhmm wallahi wayar ma sai a hankali.”
Ta nuna mata suna tattakawa. Tace
“Yee mun fara tafiya lallai zamuyi sadakar kaji kuwa.”
” a bani guda biyu a in cii.”
Suraiyya ta fada.
“Ina mabukata zan bawa bandake a ciki ko Baba na.”
Ta dauki Sadiq dake dariya tace
“Eh ma Sadiq.”
Annur yayo wajen ta shima yana taba kumatun yaran yana musu wada.
Suraiyya tace
“Mom din yara.”
Ta saita waya ta dauke su a picture.
*
10pm
Suna ta hirar su a daki Yaa Kamal ya shigo ya ce
“ko anan zaki kwana ne?”
“Da kuwa naji dadi.”
Fateema ta fada yace
“Ba sai kiji dadin ba to tafiya zamuyi.”
“A bar min Baba na.”
“Gashi nan cikin dare kya kawo shi kuwa.”
Tai dariya ta mike ta dauki Farouk Suraiyya ta dauki Sadiq Fateema ta basu ledar Biskit da Alawa ta kamo hannun Annur suka fito.
Ba kowa a falo dan haka suka je taiwa Baba da Momy sallama sannan suka fito. A bakin mota suka same su fateema ta bude baya ta kwantar da Farouk akan sit sannan Suraiyya ta bata Sadiq ta kwantar. Ta ajiye musu ledar su tace
“To Sai na shigo.”
“Yaushe?”
“In na samu lokaci.”
“Hmm shikenan.”
Kamal ya shiga ya tada motar suka bar wajen tana dagawa Suraiyya hannu. Sai da suka fita ta kamo hannun Annur tace
“Bacci ko Boy?”
Ya daga mata kai tace
“Muje ta nai maka wanka ko?”
Ta juya zasu tafi sai taji yace
“Fateemaa!”
Bata juyowa ba ta cigaba da tafiya ba tai aune ba sai ganin sa tayi a gaban ta. Ido ta zaro tana kallon sa.