WA NAKE SO CHAPTER 2
Tin da sukai magana da Shugaban kasa bai kara zuwa ba. Sai katin daurin aure sa mai martabba ya aiko a kawo masa. Shi yasa aka kai office din su da wajen shugaban kasa.+a
Duk Aliyu bai san Mai Martabba ya aika ba. Mai martabba yayi aike da sati Aliyu bai da shirin bin sa.
Ranar juma’a ne daurin auren amman har labara Aliyu na Abuja. Mai martabba ne ya kira sa.
Yana ganin kiran yasan akan mene.
Dauka yayi suka gaisa kamar yadda suka saba.
“Abbah ya gida?”
Ya tambaya duk dan ya kawar da abinda Mai martabba yake son fadi.
“Aliyu ince dai ka taho ko?”
Mai martaba ya jefo masa tambaya.
Kai ya girgiza kafin ya ce,
“Abbah sai gobe in Allah ya kai mu.”
Dan sanyi Mai martaba yaji dan yasan Aliyu zai iya cewa bai zuwa in kuwa ya fada yasan ta zauna. Aliyu kaifi daya ne, in ya ce, eh ba mai canja masa wannan ra’ayin nasa.
“Shikenan. Amman dai da wuri zaka taho ko?”
“A’ah Abbah sai wajen dare dan akwai aiki da zanyi.”
“Aliyu ya kamata ka dau hutu fa?”
“Hutun me Abba?”
“Hutun Aure man!”
“No Abbah bana bukata.”
“Shikenan sai kazo.”
“Nagode. Allah kara girma da lafiya.”
“Ameen Allah yayi albarka.”
ajiyar zuciya ya saki ya ce, a ransa bari na kira Mamah.
Mamah ya kira Mamah da ke zaune Maryama na shiryawa zasu kamun amarya ta kalli wayar ta.
“Kinga dan halak.”
Maryama ta fada tana miko mata wayar. Amsa Mamah tayi, ta dauka tare da fadin
“Assalamu Alaikum!”
“Wa’alaikum salam. Mamah ina yini?”
“Lafiya lou Baba nah, ya wajen naku ya aiki?”
“Mamah Alhamdulilah!”
“Yaushe zaka taho ne?”
“Sai gobe in Allah ya kaimu.”
“To Allah kai mu.”
“Ameen!”
“Ga yan Kamu ana ta shiri gobe zamuyi dinner jibi ayi daurin aure da yini da yamma akai maka amaryar ka.”
Shiru yayi. Mamah tai murmushi ta ce,
“Babanah kayi dace mata ba ruwan ta sai dai muyi fatan Allah baku zaman lafiya da zuri’a daiyiba.”
“Ameen Mamah.”
“Me kake bukata zuwa gobe?”
Dan murmushi yayi wanda iya kar sa baki ya ce,
“Duk Abinda Mamah ta tana dar min ina bukata “
“Shikenan. Abbah yaso ka tare a gidan ka na can, amman ni kuma ban son kai nesa da ni. Ganin part din ka na gida babba ne, kuma da ragowar fili a gefe nasa aka hade su kawai, aka fitar da part din mai dakin ka. Ince hakan ya maka ko kafi son wancan na wajen?”
Ajiyar zuciya ya sauke yana godiya ga Allah da yasa acikin gida zasu zauna dan gidan sa wancan yana zuwa ya huta bama in bai son hayaniya da yawan damun bayin nan nasa.
“Mamah hakan ma yayi.”
“To Shikenan Allah yayi albarka.”
“Ameen!”
Sukai sallama.
Kwanciyya yayi yana mai lumshe ido. Sai kuma ya saki tsaki. Mikewa yayi cikin tafiyar kasaita ya karasa wajen firij din sa. Lemo ya dauko ya koma ya zauna yana tsiyayawa a cikin cup.
STORY CONTINUES BELOW
Sai da ya sha yaji sanyi sannan ya lumshe ido kamar mai bacci. Ba abinda yake so irin ya ganshi zaune shi kadai ba hayani.
Irin wannan moment din yafi komai masa dadi. Bai son hayaniya gashi ya fito daga cikin zuri’ar da dole sai ya kasance da mutane abinda baya so kenan.
Shi ba mutane ne baya so ba. A’ah yadda suke damun sa da magana da kirari hakan ne baya so. Shima fa kamar kowa ne ko kowa ake wa haka. taku daya sai anyi magana ko motsi yayi sai ance wani abu.
Ya jima kwance sanna ya mike ya fita. Gidan sa yake dan zagaye wa. Gidane kato wanda akai ginin kasashen turawa dan ginin kamar zane haka zaka gan shi.
Flat ne, wanda da ka shiga zaka tadda babban compound, inda mota a kalla ashirin zasu zauna. Sai yar barander da zata sada ka da cikin gidan. Sai wani Daki wanda anan securityn sa ke zama.
Katon falo ne, wanda ya gama gajiya da haduwa. An zuba masa red an ash kala komai red an ash ne.
Kofofi biyu ne, kowanne na facing each other sai wasu dake can gefe toilet da kitchen ne.
Masu kallon juna kuma da ka shiga zaka tadda dan coridor sai kofofi biyar
Daya toilet ne, daya kuma kitchen, sai dayan bedroom wanda akai masa ado da purple and black. sai dayan da yake da falo mai dauke da dining da bedroom Komai na dakin fari ne tas. sai dayan dakin kayan training din sa ne. Wannan shine part din Oga Aliyu.
Dayan part din ma yadda wannan yake haka yake, sai dai shi daga one bedroom sai mai parlour da bedroom da toilet da kitchen. shima duk ya zuba masu kaya masu kyau da tsada duk da ba shiga yake ba.
Sai bayan gidan sa inda yake babban garden ne sosai. Ba abinda babu acikin sa.
Duk gidan da unguwar sojojine zagaye da ita. Duk dan Aliyu aka saka wanda shi in da ta tashi ne ba abinda zai sa a ajiye masa su.
Wannan yasa ko sun tafi garin su tare baya yadda su shiga gidan su sai dai su zauna a can gidan sa ko kowa yaje inda yake da bukatar zuwa.
Ranar Alhamis bai tashi barin garin Abuja ba sai Karfe shida na yamma. Dashi da tawagar sojojin sa da suka mara masa baya.
Ai kam basu suka je ba sai wajen karfe tara da rabi a lokacin, kuma duk mutanen gidan ana wajen biki.
Tin a gate suka rabu da tawagar sojojin su suka kama gaban su shi kuma ya shiga cikin gida.
Sai gaisuwa ake kawo masa hannu kawai yake daga musu dan wannan in ya ce magana zai yi sai yayi ciwon kai.
Part din sa ya shiga yai wanka sannan ya shirya cikin dogon Brown wando da milk riga. Jikin sa ya bade da turare.
Dakin Mai martaba ya nufa kai tsaye. Yana zuwa ya zube a kasa yana kwasar gaisuwa.
Mai martaba cikin so da kaunar dan nasa yake tambayar sa ya hanya.
Daga nan ya dan ja shi da hira.
Tare suka ci abincin dare sannan suka shiga turakar sa hannun Abbah rike da hannun Aliyu.
Wani katon akwati Abbah ya janyo ya ajiye gaban Aliyu. Kan Aliyu kasa Abbah ya ce,
“Ga kayan fitar biki nan. Aliyu Allah maka albarka. Ba kowane dan ne zai bawa iyayen sa zabin akan matar da zasu aura ba. Amman Allah maka albarka.”
“Ameen Abbah.”
Sun jima zaune Abbah na masa nasiha game da aure sosai jikin Aliyu yai sanyi. Dan shima yasan menene aure yasan hakkin matar sa akan sa. Yanzu wannan nauyin ne zai hau kansa.
Sai wajen goma sannan ya tafi dakin sa bayan an bishi da kayan a baya. Yana direwa yayi dakin Mamah. Lokacin tana zaune a bedroom din ta tagama shiryawa zata dakin mai gidan ta kenan ya shigo.
STORY CONTINUES BELOW
Tana ganin sa ta saki murmushi, ta ce,
“A’ah yaushe Baba nah ya sauka.”
“Na jima a bangaren Abbah, na zata bakya nan ne.”
“Ai tin dazu na dawo. Ya hanya?”
“Lafiya Mamah na sameku lafiya.”
“Lafiya alhamdulilah.”
“Masha Allah!”
Zaman shiru sukai har Mamah ta mike ta ce,
“Zata gun mai martaba bane.”
Mamah ta bude firij din dakin ta. Wani kwanon sha ta fiddo wanda fura ce a ciki ta dama ta tasha madara tayi sanyi.
Kitchen ta shiga ta bude naurar gashi ta Wani gashin nama ta fiddo da shi. A wani basket ta zuba su ta miko masa.
Mikewa yayi sai ya amsa, yana mata godiya. Shi ya raka ta har kofar part din sa sannan ya koma nashi part din.
Yana shiga ya baje a daki yana cin nama da furar da Mamah ta bashi. Yana ci yana lumshe ido.
Sai da ya gama yaje ya watsa ruwa. ya haye gadon sa. Bacci ya dauke shi bayan yai addu’oin sa.
Karfe, Uku ya mike ya gabatar da ibadar sa har karfe, 5 sannan ya wuce massalaci sai karfe bakwai ya baro massalaci. Training ya shiga yi har karfe 10 sannan yai wanka ya saka kaya mara nauyi.
Bangaren Mamah ya nufa suka gaisa sannan yaje gun Abbah acan yau ma ya karya.
Sai wajen karfe sha biyu da rabi sannan ya mike ya shiga part din sa. Wanka ya kuma yi sannan ya shirya cikin daya daga cikin kayan da Abbah ya bashi jiya.
Wata blue kalar shadda ce wacce daga ido ma kadai kasan mai kyau da tsada ce gashi ta sha aiki irin na gidan sarauta. Wankan turare yayi.
Bangaren Mamah yayi bayan yayi duk addu’oin da ya saba in zai bar dakin sa.
Mamah na ganin sa taji wani sanyi da dadi. Yau ga dan ta zai zama ango ya girma kenan.
Albarka Mamah ta dinga sa masa bayan tai masa wanka da turaren ta. Bangaren Abbah yaje shima Abbah addu’u da sa albarka ssu ya dinga masa sannan suka tafi massalaci tare.
Sai da akai sallah juma’a sannan aka daura auren Major Aliyu Kabir da Amaryar sa Hajara Auwal.
Manyan mutane sarakuna gwamnoni duk sun hallaci daurin aure har da Shugaban kasa.
Anan gama daurin aure aka tafi liyafa, wacce sarki da kan sa ya hada. Anci ansha anyi hotu na amman ango fuskar nan a hade ba ko murmushi.
Daga nan gida suka wuce, sai da yai wanka sannan aka kara wani wanka ya shirya cikin ash kalar shadda yar ciki da babbar riga. Yai kyau sosai kamar ka dauke shi ka gudu. aka fito zaman angwanci. Wanda ango ne zai zauna azo ai ta masa Al”lah sanya alheri sanna masu bashi gudun mawa nayi. Ana kwasar gaisuwa.
Sai da akai sallah la’asar sannan aka kara wani wankan wanda shi kuma daba za’ayi amman kememe Aliyu ya ce, shi ya gaji bai hawa wani doki.
Mai martaba da yasan halin dan sa yasan tinda yace bai yi to bazai ba. Kuma yaga kokarin sa har da akai liyafa kkuma yai zaman angwanci lallai a barshi haka.
Wannan yasa ya shirya dai cikin farar shaddar sa wacce akai masa rawani. Acan filin da za’ai daba suka zauna Mai martaba a gefe sai Aliyu a gefen sa daya gefen kuma shugaban kasa ne da komai dashi akai bai tafi ba yana son su zan ta da Mai mataba.
Anyi daba wacce ta kayatar sosai abin ya burge duk wanda ya hallaci wajen.
Sai magariba sanna aka kara shiryawa da gudanar da walima wacce take ta masu mukami ce kadai wato gwamnoni da sarakuna da shugaban kasa da iyalan su.
Aliyu da bai san da liyafar ba yana can a kwance kni sa sai sara masa yake saboda yadda ya gaji sosai.
Mai martaba da kansa ya shiga dakin nasa. Yana kwance yana ganin Mai martaba ya mike da sauri.
Zama mai martaba yayi a gefen sa. Ya ce,
“Aliyu nasan ka gaji amman komai yazo karshe ka daure ka tashi muje wajen walimar can, kaga kowa na can na jiran ka.”
Dagowa yayi ya kalli Mahaifin nasa kamar zai kuka ya ce,
“Kuma dai?”
Kai ya gyada masa. Mikewa yayi a hankali.ya shiga ban daki. Ruwa kawai ya watsa sannan ya fito ya saka wata milk din shadda.
Mai martaba da kansa ya taya shi shiryawa sannan ya kamo hannun sa suka nnufi hall din da ake taro.
Manyan mutane duk a wajen. Sai yayun sa da kannen sa da yayan yayun sa sai Mamah da Kishiyar ta. Har da amarya wanda ango ko kallon ta bai ba.
A wajen anci an sha anyi hutuna. Sai karfe goma aka tashi kowa a gajiye dan ba karamin wahala akai ba tin safe ake fama daga wannan sai wannan.
Aliyu kuwa yana komawa daki ya haye gado. Da kyar ya tashi ya cire kayan jikin sa.
Wanka yayi ya dawo ya fada gado addu’a bacci yayi nan da nan bacci yai awon gaba dashi.
Amarya da kawayen ta a gidan suka kwana. Washe gari kuma suka tafi suka bar ta.
Ango ba shi ya tashi farkawa ba sai karfe hudu da rabi. Da mamaki ya kalli agogo ya manta rabon da ya makara bai tashi karfe uku kamar yadda ya saba ba.
Wanka ya shiga yayi ya fito ya hau sallaya. Sallah kadai yayi ya nufi massall”aci acan yayi lazumin da ya saba bai ba.
Yana gamawa ya koma daki bacci ya koma dan har lokacin gajiya bata kyale shi ba. Ya ce dan ma wai bai hau doki ba.
Mamah da taga har sha daya Aliyu bai zo ba tai ta mamaki. Da kanta ta mike tayi part din sa.
Tana shiga bedroom din sa yana bude ido. Yana ganin ta yai saurin mikewa zaune.
“Yi kwanciyar ka.”
Mama ta fada.
Zama yayi ya ce,
“Mamah ina kwana?”
“Lafiya lou. Ya gajiya. Lallai yau Babana ya gaji da yawa.”
Kai ya sosa.
Kafar sa ya zuro da ita daga kan gado ya ce,
“Da asuba ma sai da na kusa makara fa.”
“Sannu ai da kayi magana anzo an dan matsa maka jikin ka ko?”
Shiru yayi.
“Ga abincin ka nan ka tashi kaci.”
Kai ya daga mata ya mike ya shiga toilet kallon tabi sa da shi.
Yana shiga yai wanka ya fito. Tana zaune ya sameta. Shiryawa yayi cikin wata bakar shadda wacce akai mata aaiki da brown zare. Bakar hula ya saka sannan ya koma ya zauna a kasa.
Kunun da Mamah tayo masa ya hada ya bude yaga potatoes ball tai masa da farfesun kayan ciki. Sosai yaci sannan yai hamdala.
Falon sa suka nufa ya zauna Mamah ta ce,
“Bari naje sai anijima.”
Ta fita.
Kishingida yayi yana mai lumshe ido. Daya daga cikin fadawan sane ya shigo.
Ido ya bude,
“Ranka ya dade mai.martaba ya ce a fada maka Sirikin ka yazo yai maka Allah ya sanya alheri.”
Da sauri ya bude ido. Ba faden yai kasa da kai. A ransa ya ce,
“Siriki na.”
*Kuji fah wai suriki ne yazo yiwa mijin yar sa Allah sanya alheri daman haka ake?*
Uhmm ni dai ana danna yar star din na ita ce kadai hanyar da zaku nuna kin soyayyar ku a gareni. Ina ggodiya sosai
Gani nan zuwa.”
Kan sa ne ya kulle najin wai sirikin sa yazo masa Allah sanya alheri. Tab.+
A ina ya taba jin haka ai shi ya kamata yaje yai Allah sanya alheri da godiya. Lallai shi shiyasa bai son wannan mukamin da mulkin da Allah ya basu.
Sam mutane basu da tsoron Allah sai da son abin duniya. Da ace ba shi ya auri yar shi ba da ba abinda zai sai yaje yai wa wanda ya aura Allah sanya alheri amman da yake shi din mai mulki ne da kudi wai sirikin sa yazo gaida shi.
Haba ina wannan bai yi ba. Tin daga nan zai iya gane yar wane gida ya aura kenan.
Shifa a rayuwar sa bai son irin wannan abin bai son ya auri wacce dan abin hannun sa take son sa. Shiyasa duk matan da ke son sa yaki su saboda yasan duk ba dan Allah suke son sa ba.
Ko dan kudin sa ko dan kyan sa ko dan sarautar sa haka dai.
Ashe dai yayi gudun gara ya tadda zago ne. Tsaki yayi. Yafi minti talatin sannan ya mike ya nufi fada.
Mai martaba ya sama zaune da shugaban kasa. Sai da ya fara gaida mahaifin nasa sannan ya gaida shugaban kasa.
Mai martaba ya ce,
“Kaje mutane na ta neman ka.”
Mikewa yayi a hankali ya bar wajen. Inda ya zama kamar fadar sa nan ya nufa. Dan in yai baki nan Mai martaba yake sawa akai su kafin shigar sa.
Fadawan ne biye dashi a bayan sa duk taku daya suna masa kirari da addu’a har ya karasa dakin.
Dakine kato wanda yake da kujera kamar ta sarki da wajen zaman jama’a masu zuwa gaishe shi.
Dakin yaji kayan sarauta ga AC da kamshin turaren wuta na tashi.
Sai da ya zauna sannan aka je akai wa surikin nasa iso. Yana zaune sirikin nasa ya shigo.
Babban mutun ne a ido kamili sai dai zuciyar ba haka take ba. Abin da ya kara bashi mamaki shine ganin ya zube a kasa yana gaishe da shi.
Kai ya girgiza a ransa ya ce,
“Da sake. Wannan ba suriki na bane. Ya fison sirikin da zai rike matsayin sa ba yazo yana masa wannan shirmen ba.”
Bai saurare sshi ba ya ce,
“Baba ina yini?”
“Lafiya lou ‘dana ya hidima Allah ya bada zaman lafiya ina maka Allah ya sanya alheri tare da baku zuri’a ta gari.”
“Ameen na gode.”
Nan ya hau surutu sai kace ba Suriki ba to shi ko da iyayen sa bai fiya magana ba bare da sirikin sa. Shiru yayi kawai yana sauraran sa. A maganganun sa ya gane akwai abinda yake bukata.
Sun dauki awa daya sannan ya ce zai tafi. Wani akwati dake gefen sa ya bude ya dauko bandir din yan 1K guda uku ya mika masa.
Amsa yayi yana sa masa albarka ya zuba a riga kamar zai masa sujada ya tafi.
Kai Aliyu ya girgiza ya ce,
“Allah ya kyau ta.”
Daga nan aka dinga shigo masa da jama’ar da suka zo biki suna masa Allah sanya alheri. Duk wanda yaje yiwa Mai martaba sallama kuma za a hada masa babban bokiti da cincin dumlan alkaki da sauran kayan ciye ciye na masarsuta.
Ranar har yamma sallamar baki dai suke sam Aliyu shi an takura masa ne. Tin da yai la’asar ya shige site din sa ya bada sallahu duk wanda zai je gun sa ace baya nan ko yana bacci.
STORY CONTINUES BELOW
Haka ya shige yai wanka ya kwanta akan gadon sa daga shi sai gajeren wando da singlet.
Nishadi ya dinga ji bama na yadda ya kasance zaune shi kadai ga sanyin AC dake ratsa shi.
Ba dan yamma bace da yasan bacci ya dauke shi. Bai tashi ba sai da yaga mangatiba ta kunno kai. Wanka ya kara yi ya saka wata farar shadda ya nufi massalaci.
Acan ya samu Mai martaba da abokin sa shugaban kasa. Ya rasa mai ya hana shi komawa gida. Gaisawa sukai sukai sallah. Sai da akai sallah isha’i ya nufi bangaren Mamah.
Mamah na zaune ita kadai sai kuyangun ta. Suna ganin sa suka bar wajen
Zama yayi suka gaisa, Mamah ta ce,
“Baba nah a yau wani girma da nauyi sun kara hawa kan ka. Baba na ina rokan ka da ka rike amanar wannan matar ta ka. Sannan ka kula da ita da bata duk hakkin da ke kan ka. Dan Allah Babana kar naji kuma kar na gani.”
“Insha Allahi Mamah ta bangare na baza ki samu kowacce matsala ba.”
“Allah yasa Allah maka albarka.”
“Ameen!”
“Anjima za a kawovmaka ita nan sashen naka.”
Kasa yai da kai. Sun jima zaman shiru. Kamar yadda iyayen suka gane in suna son ya jima gun su to kar su dame shi da magana in kuwa suka ddame shi nan da nan zai musu sallama ya tafi.
Amman in sukai masa shiru zai jima zaune a gun. Ita Mamah gani take yanzu dai zai canja tinda yai aure.
Tasan kila matar sata canja masa wannan ba hagon halin nasa. Amman kuwa da taji dadi.
Daga ita har Mai martaba duk cikin ya’yan su sun fison sa duk da wanna halin nasa.
Suna son suna jan sa a jiki amman ina shi sam baya sa sakin jiki dasu bare har suji cikin sa. Ba wanda yasan komai game dashi kowa sai dai ya bishi da ido.
Kishiyar Mamah kuwa. Sam bata son sa, dan ita ta zata ita kadai yakewa wannan halin nasa.
Shi yasa shi ko gun ta bai zuwa dan bai san me zai ce mata ba in yaje yasan gaisuwa ce kawai yo in sun hadu Falon Mai martaba ko gun Mamah suna gaisawa kuma ya isar masa.
Sai wata yarinya da take riko wacce itama son sa take kamar me wanna ya karasawa ko part din ta bai zuwa.
Ita kuma sai take ganin kamar son ta ne bayayi shi kuma bai son *wa yake so ba* bai kuma san wanda baya so ba. Dan bai fiya tsayawa ya kula da duk abinda bai shafe shi ba.
Shifa aikin sa kawai yake bawa duk attension din sa daga shi kuma ba abinda yake kara bawa lokacin sa sai bautar ubangiji da in yana yin ta yakan debe lokaci mai yawa ba tare da ya gaji ko yaga ya dade ba.
Komai akai a gaban sa kamar ba ai bane. Bai san me kowa ke ciki ba. Dan shi kansa bai san me yake ciki ba.
A bangaren amarya kuwa banyan yan uwan ta sun tafi ya rage ita kadai. Bangaren ta ta shiga dube dube da kalle kalle.
A ranta tana cewa
“Wai yau ita ce a gidan sarauta ta auri dan gaban goshin Mai martaba.”
Dadi kashe ta. Daki ta shiga ita ce ci wancan cusa wanca, shafa wancan. Har isha’i sannan ta shiga ta sheka wanka, ta fito ta shirya cikin wata yaloluwar rigar bacci wacce da ita da babu duk daya.
Wani turare da Mahaifin ta da kansa ya bata shi ta shafa ta dauki alkebba ta daura. Bata dade da zama ba Jakadiya ta shigo.
Kara dan gyara ta tayi sannan tai mata jagora zuwa turakar mai gidan nata.
Aliyu kuwa daga bangaren Mamah yaje gun Mai martaba shima Nasiha yai mata akan aure sannan sukai salama. Bangaren sa ya koma.
Yana falo zaune yana kallon news Jakadiya tai sallama. Bai dago ba a ciki ya amsa sallamar.
STORY CONTINUES BELOW
Zubewa tayi,
“Ranka ya dade Allah kara girma da nisan kwana amaryar ka ce akaivvmata iso.”
Hannun sa ya daga mata kawai. Fita tayi ta shigo da Hajara. Hajara da kanta ke kasa sai kallon haduwar bangren nasa take wanda har yafi nata komai da komai duk yadda take ganin haduwar nata.
Zama tayi a daya daga cikin kujerun dake dakin. fita Jakadiyya tayi,
“Ina yini?”
Ta fada cikin wata murya mai sanyi da daukar hankali.
“Lafiya!”
Ya amsa ba tare da ya dago ya kalle ta ba. Sun jima zaune wajen ba wanda yace da dan uwan sa kala.
Sai da ya gama kallo news sannan ya mike ya shiga dakin sa. Wanka yayi yai alwala ya koma ya kwanta.
Fitilar dakin ya kashe. Ya tofe jikin sa da addu’oi sannan ya fara bacci mai dadi da nishadi.
Tana zaune a falo, ganin ya dau awa bai fito ba gashi ta fara jin bacci, ga wata matsanaciyar sha’awa da ta adabe ta saboda ciyaye ciye da cuse cusen da tayi.
Mikewa tayi ta kashe kayan wutan dakin. Ta kashe fitila dakin da yake ciki. Dakin da ya shiga nan ita ma ta nufa.
Dakin ba fitila sai wata dark blue dake a kunne. Hango shi tayi kwance cikin gado yana baccin sa cikin kwanciyar hankali.
Take taji nutsuwar ta ta fara gushewa. Idon ta sun jajir, baza ta iya ba, tinda Allah yasa tin tana budurwa bata watsar da mutuncin ta ba ta jure yanzu baza ta iya ba.
Kan gadon ta fada, ta kwanta a gefen sa. Jin numfashin sa na sauka a jikin ta ya kara daga mata hankali.
Rumgume shi ta fara aika masa da sakonni wanda ita ma bata san a halin da take ba.
Cikin bacci yaji bakon yanayi a tare da shi. Ido ya bude a hankali jin abin da ake masa na gaba yasa ya tina a ina yake sannan kuma wace.
Ganin yadda ta fita a haiyacin ta yasa ya tausaya mata dan yasan yanzu hakkin ta na kan sa.
Wannan yasa ya tura zuciyar sa har ya kusance ta. Amman a fargaba yake dan ganin ace budurwa ke wannan abu ga miji. Sosai ta nuna jarumta gare shi. dan shi din ba karamin jarumi bane.
Kuma a yadda ya shige tan bai nuna tausaywa dan bai zaci samun ta a matsayin budurwa ba.
Karfe biyu ya sarara mata. Wanka ya mike ya shiga toilet yayo. Alwala yayi ya hau kan sallaya. Ya jima yana sallah yana rokan Allah ya bashi ikon rike matar sa tare da kula da ita da sauke duk hakkin da ke kansa.
Ya jima yana addu’a sannan ya mike ya tafi massalaci. Acan suka hadu da Mai martaba suka gaisa sannan sukai sallah.
Ana idar da sallah suka fita tare da mai martaba kara gaisawa suka, mai martaba ya ce,
“Ya iyali?”
Sai yaji wani ban barakwai.
“Lafiya suke.”
Kasancewa har takwas tayi yasa yana shiga bangaren sa ya wuce dakin training din sa.
Hajara kuwa ba ita ta farka na sai karfe goma. Ba kowa a dakin, hakan yasa ta mike a hankali. Dakin tabi da kallo.
Dakin ba karamin burgeta yayi ba. Murmushi ta saki tina daren jiyan ta.
Duk da taci gidan su amman tasan ta auri jarumin namiji.
A hankali ta mike tana dan dingisa kafa har ta saka kayan ta sannan ta sauka ta fita falo.
Nan ma ba kowa sai karar AC da kamshin turare dake tashi. Fita tayi a hankali ta shiga part din ta.
Wacce aka bata dan kula da ita na ganin ta, ta mike,
“Barka da asuba Ranki ya dade!”
“Yauwah!”
Ta fada kawai tayi cikin daki tana dingishi. Ganin haka yasa matar tabi bayan ta. Ban daki ta shiga ta hada mata ruwan wanka sannan ta hada mata ruwan da zata zauna a ciki.
Sai da ta bata duk wani taimako da tasan zata bukata sannan ta gabatar mata da abincin ta.
Abinci ne kala kala na zamani dana gargajiya. Sai wanda ta zaba. Ko wannan rayuwar aka bar ta a ciki ma ai ta gode Allah. Komai sai dai ai maka.
Tana ci matar Iya Laraba ta bata magami ta sha. Iya laraba ta ce,
“Ranki ya dade zamuje ki gaida Fulani “
Ba dan taso ba haka ta mike ta kara gyara jikin ta ta saka alkebba ta fesa turare. Suna tafe Iya laraba da wasu masu mata hidima su uku a bayan ta.
A haka har suka karasa bangaren Mamah. Tana zaune a falon ta inda ta saba zama da safe.
Tunani take yau lafiya Aliyu bai zo ba. Sai kuma ta tuna yanzu fa yana da iyali.
Tunanin ta kawar ta ce,
“Kila bai tashi ba.”
Tana gama maganar zuci suka jiyo sallamar Iya Laraba. Amsawa su Mamah da masu hidima mata sukai,
Zubewa tayi ta kwashe gaisuwa sannan ta ce,
“Ranki ya dade, uwar gidan Yallabai ce ke tafe.”
Fara’ar kan fuskan Mamah ne ya dadu ta ce,
“Je maza ki shigo da ita.”
Da sauri ta mike ta fita, a hankali Hajara ke tafiya, wanda Mamah na kallon ta tasan akwai abinda ya wakana.
Dadi da farin ciki suka lullube Mamah. Hajara ta zaune can gefe tana
“Barka da Safiya Mamah!”
“Barka kadai Hajara, ya kuka tashi ya kwanan bakunta?”
Kan ta a kasa ta amsa da lafiya.
“Allah baku zaman lafiya da zuri’a daiyaba.”
“Ameen!”
Suna zaune Maryama ta shigo, tana ganin matar wanta ta saki murmushi ta ce,
“Anty ke ce?”
Kallon ta Hajara tayi ta danyi yake ta ce,
“Eh!”
“Ina kwana? Ya kwanan Yaya nah?”
Haushi ya kamata ta ce
“Lafiya.”
Ita dan me zata ce yayan ta. Mujahida dake bayan Maryama haushin Hajara ya kara turnuke ta.
Zama tayi Mamah ta ce,
“Ga matar Yayan kunan fa Mujahida.”
Dan kallon ta tayi ta ce,
“Au Anty barka da safiya. Ya kwanan bakunta.”
Harara ta Hajara tayi kasa kasa sannan ta amsa da
‘Lafiya na same ku lafiya?”
Duk sukai shiru ta zauna na minti talatin sannan Mamah ta ce, Iya laraba.
A kasa ta zube. Mamah ta kalle ta ta ce,
“Ki kai ta wajen Sakinah, kisa ai mata iso gun mai martaba.”
“To ranki ya dade!”
Ta mike. Hajara ta dan russuna ta ce,
“To Mamah sai anjima!”
“Mu jima da yawa.”
Ta mike tana sakar wa su Maryama da Mujahidda harara.
Mujahida ma hararar take sakar mata. Suna fita suka shiga bangaren Kishiyar Mamah Sakina.Suka fice sukai bangareb Momy wato kishiyar Mamah.
Iso akai musu sannan suka shiga. Bayan sun gaisa Sakinah ta ce,
“Sai dai kinyi hakuri da wannan mijin naki dan yan uwar sa dan duk kan su wani irin bakin hali gare su,”+
Hajara dai shiru tayi a ranta ta ce,
“Ai kam zasu san da wa zasu zauna.”
“In baki nuna musu ke wace ba komai anan gun ki zasu kwaso suyi miki. Su hanaki sakat da mijin ki ke in ma sun bar shi yaxo gare ki dan duk abinda Mamahn nan tasa ta ce shi yake har mai martaba duk sun asurce su bare kuma shi da yake dan ta haka Komai suce kiyi musu komai ke komai ke.”
Kai Hajara ta gyada mata.
“Yauwah sannan wannan Mujahidar in baki wasa ba sai ta kashe miki aure dan mugun son Aliyu take.”
Kai Hajara ta dago ta ce,
“Shiyasa take min wani gani gani.”
“Au ashe kin gane!”
Kai ta gyada.
Sha’awa ce ta shigo ta ce,
“Ah Momy bakowa kikayi ne.”
Ido ta dan kanne mata ta ce,
“Matar yayan kuce.”
“Lah Anty kece. Sannu da zuwa ina kwana?”
Hajara ta amsa da
“Lafiya!”
Cikin sakin fuska. Daga nan har da hira abin su dan wai ta ce, ita tafi yadda da Sha’awa akan su Maryama da Mujahida.
Sha’awa da take yar gidan Yayar Sakinah kuma ita ma son Aliyu take kamar zata mutu amman ta nuna duk duniya ba wacce take so da Aliyu sai Hajara amman fa agaban idon ta.
Wannan yasa Hajara ta kara aminta dasu ta ce,
“Tafi son ta akan Su Maryama. Har da cewa tana zuwa tana taya ta hira.
Ta jima a gun Dan har mai nartaba ya fita fada. Wanda haka yasa Momy ta ce, sai dai ta bari zuwa gobe taje su gaisa ko da yamma.
A gun Momy ta yini da sai la’asar ta bar gun. tana barin gun sha’awa har da kuka ganin yadda take tafiya hakan ya nuna komai ya wakana tsakanin Aliyu da Hajara kenan.
Momy ce ke lallashi ta ce,
“Haba sha’awa kinsan dan ke na tsaya da wannan yar talakawar amman kike kuka. In dai ina numfashi sai yarinyar nan ta bar gidan Aliyu kin shiga ki daina kuka mana,”
Jin kalaman Momy yasa ta daina kuka amman a ranta jin tsanar Hajara take kamar taje ta kashe ta,
****************************
Aliyu bai fito ba sai karfe sha biyu, toilet ya shiga yai wanka yayo alwala. Sai da ya zauna yana shafa mai sannan ya tuna da akwai fa mutum a dakin.
Dube dube ya fara yaga bata dakin. Ajiyar zuciya ya sauke ya gama shiryawa sannan ya nufi dining table din sa.
Sai da ya ci abinci sannan ya mike ya nufi part Mamah. Yana shiga Maryama ta tare shi da surutun yanzu Antyn ta tabar gun Mamah.
Zama yai ba tare da ya kula ta ba. Mamah ya gaisar, Mamah ke tambayar sa ya iyali ya amsa da lafiya lou.
Maryama ta gaida shi. Ya amsa a takaice haka ma Mujahida. Bai dade a gun Mamah ba saboda surutun Maryama yayi bangaren Mahaifin sa.
Mahaifin sa na zaune dan shi yake jira ya shiga ya zauna. Kan sa a kasa ya ,
“Barka da safiyya Abba!”
“Yauwa Aliyu ka tashi lafiya?”
STORY CONTINUES BELOW
“Lafiya Alhamdulilah!”
“Ya iyalan?”
“Lafiya suke!”
Gyaran murya Mai margaba yayi ya ce,
“Aliyu Shugaban kasa yazo min da wata magana wacce baka fada min ba.”
Gyara zama Aliyu yayi ya ce,
“Wacce fa?”
“Akan jihar da ya bude yace kuma kai zai bawa jagorancin ta.”
Kai Aliyu ya gyada.
“Ya ce, kace zaka je kuma yaji shiru wannan abin shi yasa yai kwanaki a garin nan dan mu samu mu tattauna kan maganar kuma mun tattauna. Nasan waye ‘dana nasan zai iya koma me aka sa shi. Dan haka na yanke shawara duk lokacin da yake bukata ya sanar dakai ka fara aiki acan inda aka bude.”
Aliyu da kan sa ke kasa ji yayi kamar yai kuka. Shi wai ya zai yi. Ga aure an bashi ga wani mukami ana neman bashi.
Wai basu san bai son yawan takura da hayaniya ba. Kai ya girgiza. Mai maitaba kamar yasan abinda yake fadi ya ce,
“Kayi hakuri Aliyu, ina son canjawar wannan halaiyar taka, na daya shi yasa na takura kai aure sannan wannan jagorancin da zaka amsa shima zai sa ka kara kusanci da mutane har ka canja dayawa daga cikin dabi’un ka.
Dabi’un ka masu kyau ne sai dai ban son rashin sakewar nan a cikin mutane. Mutane sai suna maka kallon kamar baka son mutane ni kuwa nasan dana nasan shi na mutane ne kuma shi nake sa ran ya maye gurbi na nan gaba kadan ko ina da rai ko ban da rai. Kayi hakuri kowa akwai kaddarar sa wannnan duk suna cikin kaddarar ka dan haka kayi hakuri na ce masa ya baka nan da wata daya ina fatan ba matsala.”
Kai kawai ya gyada masa.
“Allah maka Albarka.”
“Ameen!”
Ya amsa acikin ransa.
“Sai anjima!”
Ya fada kan sa a kasa
Mikewa yayi mai martaba ya ce,
“Mujima da Yawa.”
Bangaren sa ya nufa ya zauna ya rasa tunanin da zai yi.
“Ya Salam!”
Ya furta a fili. dan ji yake kamar an dauki wani dutse an aza masa a kan sa.
Ido ya lumshe yana ganin yadda rayuwar ke neman ta cakude masa, can kuma ya tino da amaryar sa.
Tsaki yayi, yai cikin daki. Alwala yayi ya nufi masallaci ya jima a masalacin dan har akai la’asar yana cikin massalaci.
Bayan anyi la’asar ne, ya mike ya fito, mota kawai ya dauka ya nufi gidan sa na can bayan gari,
Ba kowa a gidan sai sojojin sa da masu kula da gyara gida.
Yana zuwa suka fara kame masa, ko kallon su bai ba ya wuce ya shiga cikin main house din.
A gyare yake komai tsaf sai tashin kamshi da daukar ido wajen keyi. Yana shiga ya zube a babban falon da aka kawata su da wasu manya manyana kujeru kofi kala.
Ido ya lumshe ya jima zaune sannan ya mike, firij ya nufa ya dauko lemo bai saurari kofi ba ya kafa kai Kadai.
Sai da ya shan rabin jarkar sannan ya koma ya zauna. Kai ya dafe ya lumshe ido.
Yafi awa biyu kwance a gun yaji an kira sallah magariba mikewa yayi jiki a sanyaye ya nufi toilet yai alwala ya fita.
Kasancewa a massalacin dake gidan sa ake kiran sallah yasa ya nufi can. Acan ya zauna har akai I’sha’i yana ta addu’a da zikirai ga Allah mabuwayi da daukaka.
Sai karfe takwas ya fito daga massalaci. Cikin gidan ya shige, A hankali ya dinga ratsa Falo masu kyau da kayan alatu har ya kai wasu kofofi guda uku.
Daya ya shiga katon bedroom ne. Kan gadon ya fada yana fadin sunan Allah.
Idon sa a lunshe yana son yai bacci ko me ya tino kuma sai yai saurin mikewa.
Tsaki ya saki a ransa ya ce,
“Wallahi Abbah ya hadani da aiki!”
STORY CONTINUES BELOW
Fita yai ya dauki mota ya bar gidan, can gidan su ya nufa. Yana parking ya nufi part din Mamah.
Gaisawa sukai tai masa sai da safe sannan ya tafi. Agogon hannun sa ya kalla tara har da rabi wannan yasa ya nufi part din sa kawai.
Yana shiga ya wuce toilet yai wanka yayo alawala ya haye gadon sa.
Har bacci ya fara daukar sa ya tina da matar sa. Tsaki yayi ya gyara kwanciya kawai.
Hajara kuwa tin magariba ta shigo part din nasa ta tadda bayanan ta zauna har akai isha’i sannan ta koma bangaren yya.
Karfe tara ta mike ta kara wani wanka ta shirya cikin wasu kayan bacci masu kyau da fitar da sura.
Bayan tai wanka da turare tayi bangaren sa. Ba kowa a falo dan haka tayi hanyar dakin baccin sa.
Yana kwance ta same shi. Gadon ta hau tana mannewa a jikin sa.
Yau ma cikin bacci ya fara jin sabon abu.
Ido ya bude cikin jin bacci. Sanin wace ita a gare shi yasa ya biya mata bukatar ta.
Amman a ran sa yana mamakin yadda take kai kanta ko da ba’a neme ta ba.
Bama wannan ba ita da take amarya ai ya kamata taja ajin ta. Mikewa yayi ya fada bandaki yayo wanka ya hau kan sallaya baccin da bai koma ba kenan.
Ana assalatu ya dan tada ta ya wuce massalaci. Karfe bakwai ya koma ya shige dakin training din sa
Hajara kuwa ko da zai tafi ya tashe ta bata tashi ba har yanzu da ya dawo ma ba tashin tai ba.
Sai tara wannan ta mike tabar bangaren nasa. Sai da taje tai wanka tai sallah sannan ta kara komawa gado.
Iya Laraba ce ta shigo ta same ta ko karyawa batai ba. Zama tayi a kasa ta ce,
“Ina kwana Ranki Ya dade?”
“Lafiya!”
Ta bata amsa.
“Zuwa nai na raka ki gun Fulani.”
Fuska ta bata ta ce,
“Wai kullum sai anje ne?”
“Ranki ya dade sirikar kice fa.”
Dan hararar Iya Laraba tayi ta ce,
“Shine me? Ita nake aura to?”
“Ki dai yi hakuri haka ka’idar gidan take.”
Wani kallo ta zubawa Iya Laraba ta mike ba dan taso ba suka nufi Bangaren Mamah.
A shashare ta gaida Mamah ta mike suka nufi gun Mai martaba sannan suka shiga gun Momy Sakina.
Yau ma zama sukai suka kitsa mata abu kala kala kuma duk ta dauka.
Daga nan ta koma part din ta ta karya tabi lafiyar gado sai bacci.
Aliyu Kuwa sai goma ya fito, gadon duk a yamutse bata ko gyara ba. Tsaki yayi ya gyara da kansa ya shige toilet.
Ya jima a ciki yana wanka sannan ya fito ya shirya cikin Milk din shadda wacce ta amshe shi yai kyau. Wanka da ruwan turare yayi yafita zuwa falo.
Break din sa ya ci sannan ya shiga bangaren Hajara da ya tadda bata nan. Baki ya tabe ya fito kawai. Bangaren Mamah ya nufa.
Mamah kadai ya sama a gun wannan yasa bayan sun gaisa ya jima zaune a gun ta.
Sannan ya nufi bangaren Mai martaba. Mai martaba bayan sun gaisa ya ce,
“Aliyu jiya kuma sai akai min yaji!”
Kasa Yayi da kansa. Ashe dai Abbah ya gane abinda yasa ya bar gidan.
“Kayi hakuri Aliyu.”
“Abbah ka daina bani hakuri dan Allah komai kayi gareni ka isa da nine ni ba komai. Kuma hutu nake bukata kawai. Da na dawo kuma naga dare yayi shiyasa ban zo ba.”
“To shikenan Allah yayi albarka.”
“Ameen!”
“Abbah ina son wani satin zan koma gun aiki na,”
“Ah toh ba komai sai ka fadawa mai dakin naka ta zama cikin shiri ko?”
“Insha Allahu.”
Nan ma ya jima dan har sai da sukai sallah azahar suka isa fada. Acan ya zauna yana ganin yadda ake gudanar da zaman fada da karar raki da ake kawowa Mai martaba na sulhuntawa.
Ya sha mamaki ganin tinda mai martaba ya zauna bakin sa bai huta ba.
Duk mai matsala in ya dauko sai gunsa shi kuma kasancewa sarki adali mai son talakawa yasa kowa ya kawo masa kukan sa da bukatar sa yake kokarin magance masa.
Kowa kuma in zai tafi zai tai masa addu’a shi da iyalan sa da iyayen sa da duk wanda ya kusance sa.
Sai da sukai la’asar sannan suka kuma ciki tare suka ci abincin rana sannan suka zauna suna hutawa.
Sai can yamma sukai wanka suka canja shiga sannam aka koma massalaci kuma sunn jima suna zikiri da karatun alkur’ani sannan aka tada sallah.
Sai bayan isha’i suka rabu da mahaifin nasa. Aliyu ya yi haka ne duk dan ya cire shaku daga zuciya mahaifin nasa akan ba fushi yake da shi ba.
Sai da ya biya gun Mamah sukai sallama a can ya samu kannen sa sannan yai musu sai da safe.
Kallo ya zauna ya danyi sannan yai wanka ya haye gadon sa.
Washe gari duk abinda ya saba ya gabatar da su yaje gun Mamah da Abbah ya gaisar sannan ya koma part din sa dan yana bukatar hutu.
Sai da ya bada sallahu kan kowaye zai shiga a fada masa baya son takura.
Sha’awa kuwa duk hanyar da zata bi su kulle tsakanin ta da Hajara tayi dan har sirrin ta tsakanin ta da mijin ta fada mata take wanda hakan ke sa Sha’awa taji kamar zata mutu amman sai ta daure dan akwai abinda suke shiryawa.
Ita kuma Hajara da yake sakarya ce duk abinda Suke sa ta tayi na kar ta sakar wa ssu Maryama haka take yi.
Dan jiya ma bata je gun mijin ta ba dan wannan Sha’awa ce ta hane ta wai tana jan aji mana.
Yau da yamma da Maryama tazo dan ta dan debewa Antyn tata kewa.
A falo ta same ta tana shan fruit. Zama tayi ta ce,
“Ina yini?”
Kamar baza ta amsa ha da kyar ta amsa da
“Lafiya!”
Tin daga nan ta kulle bakin ta duk hirar da Maryama ke janta dashi tai mata banza daga baya ma ta mike tayi cikin dakin ta bar Maryama nan zaune ita kadai.
Maryama na zaune Sha’awa ta shigo ganin Maryama yasa ta ce,
“Ah kanwata ke ce anan?”
“Wallahi!”
“Ina Antyn?”
“Tashiga yanzu!”
Zama ta danyi taji shiru. Sai ta mike tabi bayan ta.
Maryama na zaune ta dinga jiyo shewar sa. Daga baya ta mike tayi bangaren su gun Mujahidda dake can wajen Mamah.
Wannan yasa Maryama tin daga ranar bata kara yin bangaren Antyn tasu ba.
Ba wanda zaka gani a bangaren sai Sha’awa da ta maida hangaren kamar sashen su.
Aliyu ba shigowa yake sosai ba dan yawanci sai safe da safe kuma tana can gun su Momy Sakina.
Haka da dare wani lokacin in yazo ya duba ta sai yai tajin hayaniya a falon ta abinda sshi kuma bai so kenan.
Haka in yana son hutu ko waye ba abarin sa shiga wajen sa.
Yanzu haka ya bawa Mai jiran kofar sa wannan dokar kar ya bar kowa ya shigo masa.Idon sa a lumshe yaji an shigo ba tare da anyi sallama ba. Zama tayi a gefen sa.
“Yallabai!”+
Ta kira sunan sa. Yana jin ta yai mata banza dan tayaya zata zo ta ganshi a haka bata sani ba ko bacci yake kome yake ta hau tashin sa.
“Yallabai!”
Ta kara kiran sunan sa. Jin bai motsa ba yasa ta fara dukan jikin kujerar.
Ido ya bude wanda suke jajir saboda bacin rai. Wani kallo ya aika mata.
Ta ce,
“Please kudi nake so?”
Wani takaici ne ya tunkare shi tana son kudi shine yana cikin hutawa zata zo ta tada shi. Kallon gefe yayi ya ce,
“Wa ya baki izinin shigowa?”
Kallon sa tayi da mamaki gun mijin nata sai an bata izinin shigowa.
“Dake nake nace waya baki izinin shigiwa?”
Shiru tayi tana tunanin me zata ce, bata samu amsa ba ya ce,
“Malama get out!”
Ya daga mata wata uwar tsawa wacce sai da ta fado daga kan kujera dan tsorata.
Da sauri ta mike zata fita ya ce,
“Ki turon mai jiran kofa.”
Jiki na rawa ta fita. Mai jiran kofa ta sama yana zaune.
“Kaje!”
Ta fada tana yin gaba duk jikin ta na rawa. Shima take yaji jikin sa yai sanyi.
A hankali ya mike ya shiga dakin hade da sallama. A zaune ya same shi fuskar nan a hade kamar bai taba dariya ba.
Jikin sa ya tsanan ta da rawa dan yasan halin ogan nasa. Ya ce,
“Ranka ya dade gani!”
Wani kallo ya watsa masa ya ce,
“Me nace maka da Zan shigo?”
Yai mai tambayar yana dan jin gina da bayan kujera. Jiki na rawa mutumin ya ce,
“Ka ce, kar wanda ya shigo.”
Kai ya gyada ya ce,
“Oh rainani kayi shiyasa ka barta ta shigo ko?”
“A’ah naga………”
“Keep quite malam!”
Ya daka masa wata razananiyar tsawa wacce tasa duk jikin sa ya dau rawa.
“Ka tashi ka bar min daki kuma ko a kofar gidan nan na kuma ganin ka zaka sha mamaki.”
Mikewa yayi ya ce,
“Nagode Ranka ya dade.”
Har ya kai bakin kofa ya ce,
“Kuma ina sauran wanda kuke jiran kofar?”
Bai saurarin amsar sa ba ya ce,
“Dakai dasu duk kar na kuma ganin ku. Sannan kaje ka kawon mutum biyar yanzun nan.”
“To Ranka ya dade!”
Ya fita.
A tozar ta ka kai godiya sannan a aike ka kuma sai kaje. Daman can yasan halin Yallabai yasan bai tsayawa yaji uzurin mutum da mutum yai laifi yake zartar da hukunci to shi yanzu ya zai yi.
Gidan da yake samun nacin abinci an kore shi. To wai ba matar sa bace. Ko da yake halin Oga kuma.
Sai da yaje ya turo masa mutum biyar sannan ya sanar da abokan aikin sa sakon da Aka basu.
Haka duk suka tafi jiki a sanyaye. Su kuma biyar suka nufi dakin Shugabn nasu.
Sun same shi a zaune. Sai da suka gaisar da shi ya amsa. Zasi hau wanna kirarin ya daga musu hannu alamar suyi masa shiru wannan yasa suka tsuke bakinsu kai a kasa cikin girmamawa suna jiran suji umarnin da za a basu. Sai da ya gama dane danen wayar sa sannan ya ce,
“Na kira kune dan ku zama masu jiran kofa. Ina da dokoki duk wanda aka saba min kai da gidan nan har abada. Kuna ji?”
STORY CONTINUES BELOW
Kai suka daga sannan suka hada baki wajen fadin
“Eh! Ranka ya dade!”
Kai ya gyada ya ce,
“Bana son in nace kar abar kowa ya shigo ku bar wani ya shigo. Ko waye indai ba mai martaba ko Fulani Mamah bane kuna ji?”
“Eh! Ranka ya dade!”
suka kara hada baki.
“Kowaye fa in ba wadan can biyun ba! Sai ko Maryama ko da yake ita bata fiya shigowa ta nan kofar ba. But in ta kama zaku bar ta ta shigo.”
Ya nana ta musu.
“Sannan ko a tsakanin ku ban son jin hayaniyar ku. Sam!
Ban yadda ko ina nanan ko bana nan wani ya shigon part dina.”
“Insha Allahu zamu kiyaye. Ranka ya dade.”
Kai ya gyada ya ce,
“Kuje!”
“Godiya muke ranka ya dade.”
Wani a ciki ya bude baki zai fara kirarin nan nasa ya daga masa hannu ya dan jijjiga kai ya nuna musu kofar fita.
Da sauri suka mike suka fita. A ransa yana mamakin Hajara shi da bai son in yana hutu ko bacci a tashe shi amman da yake ita jakace tazo yana hutawa tana tashin sa akan kudi kawai.
Tsaki yayi ya mike ya shiga bedroom. Toilet ya zarce direct ya watsa ruwa saboda magariba da ta gabato yai alwala kawai ya saka kaya masu saukin nauyi.
Sai da sukai isha’i sannan ya wuce gun Mamah.
Bayan sun gaisa yake cewa
“mamah ina Maryama?”
“Tana daki!”
Wayar sa ya dauka yai kira ta.
“Ki zo!”
Kawai ya fada ya kashe wayar. Mikewa tayi ta fito daga dakin ta.
Tana ganin sa ta saki murmushi ta zauna ta ce,
“Ina yini Yaya?
“Lafiya!!
Ya fada a takaice.
“Kije gun waccen, kice mata ta shirya jibi zamu tafi.”
Baki ta dan turo ta kalli Mamahn ta.
Mamah ta ce,
“Tashi kije man.”
Mikewa tayi tana turo baki ta fita. Bangaren Hajara ta shiga ba dan taso ba.
Tana shiga ta tadda Sha’awa zaune da Hajaran a falo. Sha’awa na ganin ta ta ce,
“A’ah kanwata kece haka da daren nan?”
Kai ta gyada ta dan russuna ta ce,
“Ina yini Anty sha’awa?”
“Lafiya.”
Hajara ta kalla ta ce,
“Uhmm Anty daman Yaya ne ya aiko ni.”
Kai ta gyada mata, ta ce,
“Ya ce, ki shirya jibi zaku tafi,”
Dam kirjin Sha’awa ya buga yanzu kenan tafiya zasuyi. Marayama kuwa tana bada sakon ta juya ta kalli Anty Sha’awa ta ce,
“Anty sai da safe!”
A duburburce ta amsa da
“Allah tashe mu lafiya.”
Kallon Hajara tayi ta ce,
“Bari na je na kwanta gobe ma karasa.”
“Kai dan Allah ki zauna mana.”
Kai Sha’awa ta girgiza ta ce,
“Bacci ne yazo.”
“Shikenan. Ki gaida Momy sai da safe.”
Mikewa tayi ta fita. Ita kuma tayi cikin bedroom din ta.
Maryama na komawa ta tadda Aliyu zai fito. Hanya ta bashi ta ce,
“Sai da safe!”
“Allah tashe mu lafiya!”
Ya fada yana yin gaba ba tare da ya juyo ya kalle ta ba.
Ciki ta shige ta tadda Mamah ma tayi dakin ta. Dan haka itama ta shige dakin ta.
Mujahidda ta tadda tana zubar da hawaye. Zama tayi ta ce,
“Ki zauna ki kashe kanki da wanda bai san kina yi ba.”
“Naji din!”
Ta fada tana fashewa da kuka.
Maryama sai ta tausaya mata ta ce,
“Haba Sis dan Allah ki mika komai ga Allah. in Allah yayi Yaa Aliyu zai aure ki zai aure ki. Amman wannan kuka duk bazai canja kaddarar ubangiji ba.”
STORY CONTINUES BELOW
Kwanciyya tayi kawai ta juyawa Maryama baya. Murmushi Maryama tayi mai cin rai ta kashe fitilar dakin ta kwanta. A ranta ta ce,
“Ko me gare shi ake son sa da wannan fuskar ta sa kullum a hade. Dan kyan nan kuma ai akwai wadan da suka fishi.”
Tsaki tayi ta ce,
“Nagodewa Allah da Allah bai dauran son kowa a rai na ba. So hana ganin laifi.”
Can kuma ta ce,
“Ko me ya hada Anty Sha’awa da Anty Hajara. Lallai Anty Hajara bata san wace Anty sha’awa matar da take son mijin ta take shigewa. Oho ma ba ita ba mu bazata ja mu a jiki ba mu da muke yan uwan sa na jini ba wani kishi ko cutar wa gareshi bare ita.”
Tsaki tayi ta ce,
“Allah shiga tsakanin na gari da mugu.”
Tai addu’a ta tofa ta kwanta.
A bangaten Aliyu kuwa tin da ya shiga yayi wanka ya kwanta sai karfe uku ya tashi.
Ya jima yana sallah yana rokar Allah ya taimake shi da cikar burin sa. Sannan ya mike ya tafi massalaci.
Da ya dawo yai Training yai wanka ya ci abinci yaje gun Mamah. Suka gaisa. Bayan sun gaisa Mamah ta ce,
“Babanah ya kamata ka bar Hajara taje gida tai musu sallama. Sannnan ka bata kudi ta basu ko?”
Kai ya gyada ya ce,
“Toh!”
Waya ya zaro ya kira Maryama da fitowar ta daga wanka kenan. Dagawa tayi ya ce,
“Kizo!”
Kamar yadda ya saba in yana son ganin ta. Riga ta zira ta dan shafa mai sannan ta fita.
A falon Mamah ta same shi dan haka ta tsugunna ta gaida shi. Kallon ta yayi ya ce,
“Kije part dina ta kofar bangaren nan. Ki shiga bedroom dina. Kinsan inda nake ajiye kudi ki dauko bandir din 1k guda biyu ki kaiwa Hajara kice taje gida tai musu sallama. Ki dau yadda zai ishe ki keda Mamah kuma.”
Ita fa bata son zuwa wajen matar nan tasa. Amman ta amsa da to ta mike ta fita. Dakin ta shiga ta nufi bedroom din sa. Bandir biyar ta diba ta fito.
Ba kowa a falon Hajara dan haka ta kara shiga dayan falon nata nan ma bata nan.
Bedroom din ta ta nufa tai knocking
“Waye?”
Aka tambaya.
“Nice!”
Ta bada amsa.
“Shigo!”
Aka fada ba dan an gane wace bace.
Suna zaune ita da Sha’awa kamar ko da yaushe. Sha’awa ta gaisar sannan ta kalli Hajara ta ce,
“Ina kwana?”
“Lafiya.”
Bandir biyu ta mike mata ta ce,
“Inji Yaya ya ce, ki shirya akai ki gida ki musu sallama.”
Ta juya ta fita. Hajara mamaki take wai haka rayuwar ta zata kasance ko da yaushe ace indai miji zai aike ko na menene sai kanwar sa.
Sha’awa kuwa ganin Hajara ta lula tunani yasa ta ce,
“Tunanin me kike?”
“Rayuwar da na tsinci kai na ace in za ai min aike shi bai iya tara ta sai dai ya aikon kanwar sa.”
Yar Dariya sha’awa tayi ta ce,
“Uhmm ba Momy ta fada miki ba sai kin mike dan komai nashi sai Mamahn sa da wannan kanwar tasa. in baki da gaske ba zaki sha wahala sosai.”
Kai ta girgiza ta ce,
“Ya zanyi.”
Wani murmushi Sha’awa ta saki ta ce a ranta,
“An zo wajen!”
A fili ta ce,
“Wai waya fada miki yanzu ana zama haka ne!”
Kallon ta Hajara tayu ta ce,
“Bangane ba?”
“Malama ki fidda kudi aje ai miki aiki wanda sai abinda kika ce Aliyu zai yi. Bazai taba ganin kowa da gashi ba sai ke!”
Kallon ta Hajara tayi ta ce,
“Da gaske!”
Dariya tayi ta ce,
“Wallahi.”
“To ni da zan tafi gobe!”
“Kar ki damu kibar komai a guna zan kawo miki duk abinda ya kamata har Abujan”
Tafawa sukai Hajara na ce wa,
“Amman gaskiya Sha’awa kina so na. Shiyasa nima nake son ki. Allah bar mu tare.”
A rai sha’awa ta ce,
“Ba Ameen ba.”
A fili kuma ta ce,
“Ameen!”
Nan Hajara ta mike ta fara shirin zuwa gida. Sai karfe biyu aka aiko driver yazo zai kai ta.
Fita tayi ita da masu kula da ita suka tafi.
Taje gida lafiya ta samu kowa yana lafiya. Sun zauna da mahaifin ta inda ya kara daura ta akan gurguwar shawara.
Har da cewa tana dan daukar duk abinda ta ga an ajiye ba a so. Dubu dari ta bashi ta bawa mahafiyar ta dubu hamsin ban da kayan abinci da Mamah ta hado musu har da shadda da atamfa.
Sai yamma sukai sallama bayan Innan ta tai mata nasiha sosai. Abban ta kuwa sam bai mata ba sai hanyar da zasu samu kudi ya nema musu.
Aliyu kuwa yaje yaiwa yayan sa sallama da godiya hadi da ban gajiyar biki da sukai.
Har gidan su Umar da Farouk yaje yai wa matan su kyautar kudi da ban gajiya sannan ya tagi ya bar su da kewar sa.
Ya tafi suna mai kewar dan Junan su. Haka yau ya jima gun Mamah da Abbah.
Sun masa nasiha sosai da addu’a sannan ya nufi bangaren sa. ba abinda yake diba daga nan gida saboda acan duk kayan uniform dinsa suke.
Dan haka wayoyin sa da laptop din sa kawai yake tafiya dasu. A jirgi ya shirya musu tafiyar tasu.
Hajara kuwa ana can sai shirye shirye ake za a je Abuja. Tasan acan zata fi sakewa da mijin ta.
Washe gari ma a gun su Mamah yai break sannan ya zauna Mamah na da dai masa nasiha.
Ita kuwa Hajara nacan wajen Momy tana dada daura ta a turbar banza wacce take gani kamar duk duniya ba mai son ta kamar Momy.
Sai karfe biyar zasu tashi. Wannan yasa tare sukai sallah la’asar da mai martaba sannan ya shige bangaren sa ya kara wanka ya saka kakinsa.
Wanda ya kara fito da shi a cikakken namiji. Fuskar nan tamau da ita ba alamar wasa.
Gun Abbah yaje yai masa sallama sannan yaje gun Mamah. Acan ta tadda Momy.
Momy na ganin sa ta hau murmushi tana cewa,
“Baba sai muji tafiya ba sallama.”
“No yanzu zan biya ai.”
“Allah sarki sai gashi mun hadu nan ko?”
“Eh!”
Ya kalli Mamah ya ce,
“Mamah zamu tafi.”
“Toh Babana Allah ya tsare ya kare. Kar ka manta da yawan zikiri da neman tsari da yawai ta yin azkar din ka. Allah maka albarka.”
“Ameen!”
Momy ya kalla ya ce,
“Sai anjima.”
“Allah kiyaye.”
Ya amsa da Ameen”Mikewa sukai gaba dayan su sukai fita dan taka masa. Motoci ne a kofar bangaren sa sojoji kewaye da wajen.+
Yana tsaye suna magana da mai martaba Maryama ta fito.
“Yaya!”
Ta kwada masa kira. Juyawa yayi ta karaso wajen sa hannun ta dauke da wata katuwar leda. Wacce in dai zai tayi haka take cika masa ciki da su cake, meat pie, donot, cin cin, dubulan, alkaki, nakiya duk dai.
Murmushin gefen baki yayi ta karasa. Ta ce,
“Zaka tafi baka tafi da kayan ka ba.”
Mota ya nuna mata inda kayan sa suke. motar ta nufa ta saka ta dawo ta ce,
“Zan rakaka.”
Kai ya daga mata kawai ya ce,
“Kira waccan!”
Tayi part din ta. Suna zaune ita da sha’awa ta shiga.
“Ki fito yana jira.”
Kawai ta fada ta fito. A mota ta same shi ta bude ta shiga. su Mamah na daga masu hannu.
Hajara na fitowa aka nuna mata motar bayan ta Aliyu ita da masu mata hidima suka shiga suka tafi.
Daga Mai martaba har Fulani kewar dan su suke ji kamar kar ya tafi. Haka suka koma ciki.
Hajara kuwa sai a airport tasan da Maryama ake kuma wai tana cikin motar mijin ta.
Tab ta fada. Ita ta debo masa kayan sannan ta bawa wani yaron sa kan ya rike masa. Sukai sallama tana ta zuba masa addu’a kamar yadda ta saba.
Rungume ta kawai yayi. Ya dan mata kiss a goshi yai gaba. Hajara bakin ciki kamar ya kashe ta.
STORY CONTINUES BELOW
Sai da taga tashin su ta koma aka maida ta gida su kuma sauran sojojin suka dau hanya masu jire masa gida kuma suka koma.
Su Aliyu na sauka ya wuce office dan haka Hajara kawai aka kai Gida. Dayan site din ya ce a kai ta.
Ba shi ya dawo gida ba sai karfe tara na dare. Bangaren sa ya shiga kawai yai wanka ya kwanta.
Yunwah ya dan ji ya mike ya shiga falon sa. Acan ya hango ledar da Maryama ta zubo masa kaya a ciki.
Dauka yayi ya shiga bedroom ya bude firij ya dau lemo yaci ya koshi sannan ya koma ya kwanta.
*
Sai washe gari ya kunna wayoyin sa. Nan yaci karo da sakon Mai martaba da Mamah da Maryama.
Kiran mai martaba yayi ya gaishe shi ya ce sun sauka lafiya aiki ne ya sha kansa bai kunna waya jiya ba.
Haka ya kira Mamah ita ma sannan ya kira Maryama wacce ta cika shi da surutun wai tayi missing nashi.
Bayan sun gama ya mike yai wanka ya fice. A office aiki da yawa yai dan yai sati biyu baya gari.
Dan haka yau ma sai dare ya dawo gida. Washe gari ma haka ke sai da takai sam baida lokacin zama gida saboda aiki.
*
Satin su biyu kenan da dawowa amman bata kara saka shi a idon ta ba, Duk sai ta damu wai daman haka ake aure kace har gwara suna can da nan.
Nan bata da kowa sai ita sai masu kula da ita miji kam sati biyu bashi a idon ta.
Tana xaune a falo kamar daga sama tajiyo sallamar sa ciki ciki yayi. Amsawa tayi ta bishi da kallo yadda yai kyau.
Yana sanye da manyan kaya. Farar shadda wacce dikin yai masa kyau ya amshe shi. Yai kyau.
Yasa hula mai multi kala brown fari baki sai bakin takalmi da bakin agogo. kasancewa yau Friday yasa daga massalaci ya dawo gida.
Ido ta bishi da shi. Duk sai taji sha’awar mijin ta ya tasar mata. Kasancewa Hajara macece mai yawan feeling.
Ganin bai fito ba yasa ta mike tabi bayan sa. Kwance ta same shi akan gado.Idon sa a lumshe.
Daga shi sai farin three quarter da riga ita ma fara tas. Zama tayi a gefen sa. Magana ta fara. Ta ce,
“Yanzu Ranka ya dade haka ake rike aure. Ace yau sati biyu da zuwan mu amman ko sau daya ban saka a ido na ba.”
Mikewa yayi ya watsa mata wani kallo. Shiru tayi sannan ta ce,
“Kadai san hakkina akan ka kuma ba iya na ci da sha bane kawai ka sani.”
Sai kuma yaji tausayin ta. Har ta mike sai ya kamo hannun ta. Juyowa tayi ta kafe shi da ido. Kan sa a kasa.
Zata iya cewa tin da suke da ita bai taba duban fuskar ta ba. Ko ya kalle ta na mintina ba.
“Zauna!”
Ya fada yana nuna mata inda ta tashi.
Zama tayi ya fara magana kamar baya so yace
“Ni nasan ina sauke hakkin dake kai na. Dan kullim sai na san a halin da kike. In bukatar aure ce tin da naga ke baki da kunya a wannan fannin duk lokacin da kike bukata ta i am ready tinda nasan hakkin ki akai na ba zan taba kin kusantar ki a lokacin da kike so ba sai dai in ina da lalura.”
‘Wayoo wai wannan wane irin mutum ne?”
Ta tambayi kan ta.
Shiru tayi. Gane tana bukatar tasa kuma ya ce bata da kunya yasa ta kasa aikata wani abu.
Wanna yasa ya janyo ta ya fara aika mata da sakonni wanda tini ta fita a haiyacin ta.
Tasan a bangaren jarumin namiji tayi dace dan kowacce mace zata so Ace Aliyu ne mijin ta. Bama in tana hannun sa yana sarrafa ta.
STORY CONTINUES BELOW
Takan manta da komai da komai sai dai ta jita a wata duniya ta daban. kuma duk lokacin da take bukatar sa baya taba kin amsa mata sai dai shi sam bata gane yaushe yake da bukatar ta.
Duk da in tana hannun sa tana jin maza amman da yake itama jaruma ce kuma mai yawan bukata yasa bata gajiya sosai.
Tin daga lokacin bata kara ganin sa a gida ba. Inba ranar juma’a ko lahadi ba.
Tin bata saba da wannan halaiya da dabi’un nashi ba sai gashi har ta saba. Amman da kyar ta sha wuya kafin ta saba.
Yanzu ta gane halin sa sam shi bai san zama da iyali ba kullum aiki daga aiki sai daki sai hutuwa yai rufe ido kawai ba tare da yace da wani kala ba.
Bukatar sa akan ta kuwa sai ta kai kanta take ganewa. Dan ba karamin kokari take da shi ba.
Cikin haka har sukai wata biyu a Abuja. Ita dai ba inda take zuwa sai gida ko in karshen wata yayi ya ce akai ta shopping zai ajiye mata kudi masu yawa.
Mai martaba da fulani kuwa kullum zasuyi waya da tambayar iyali haka nan Maryama kan kira shi Friday tai masa text.
Sam Hajara bata sam ta gyara dakin mijin ta ko tai masa girki ba. In tanemeshi to bukatar kan ta ce. Shima kuma dake ba mazaunin gida ba bai damu ba in yana gida yaji yunwa lemo ko nono da fura su yake sha shikenan abincin nasa.
Sha’awa taje ta kai wa Hajara kayan mallaka da asiri amman har ta koma bata hadu da mai gidan ba dan duk yadda kakai ta jiran sa wani lokacin sai ka hakura bama kuma da yake daga Abuja akwai inda zataje da wani saurayin ta wannan yasa bata jima ta tafi. Hajara na murna tana godiya. Nan bata san komai da akai da sunan sha’awa akai sai dan abin sha da ta hado mata sune kadai nata.
_________________
*Bayan wata Biyar*
Aliyu ya kara kyau da zama babba duk da karacin shekarun sa. Amman zakai tinanin babban mutum ne bama ta fannin halaiya da dabi’un sa da irin yadda yake gudanar da aikin sa.
A wannan lokacin ne kuma Shuguban kasa wanda shekarar sa ta biyu kenan da hawa mulki ya damka masa jihar da ya bude a lokacin.
Wannan kuma lokacin ya samu hutu dan haka ya tafi gida kafin ya tafi jihar da Shugaban kasa ya bude yasa a gina masa gidan sa.
Tafiyar mota yake sha’awa dan yana son yaga yana tafiya yana ganin jejika da garuruwa.
A haka har ya karasa garin su wanda tin da yaje ake murnar zuwan sa. Kai kace sarki ne gaba daya gidan sarki ya hargitse da murna.
Sai da yaje ya gaida mai martaba sannan ya wuce ya gaida Mamah da Momy.
Bangaren sa ya wuce wanda ba Mai gyara masa sai Maryama. Bangaren a gyare sai tashin kamshi yake. An jjere masa kayan abinci kala kala wanda Mamah da maryam da kan su ke masa abincin sa.
Wanka yayi yaci abinci sannan ya koma falo ya kwanta. Can sai ga mai martaba da kan sa yazo masa ban gajiya tare da murnar samun mukamin gwamna da yayi.
Yana ganin mahaifin nashi ya mike cikin girmamawa. Kujera ya bashi ya sauka kasa. Amman sai mai martaba ya kamo sa.
Zama yayi a gefen sa kan sa a kasa ya ce,
“Aliyu ina alfahari dakai. Saboda abubuwan da kake a gun aiki duk suna zuwa kunne na. Gashi gaskiyar ka da tsayawa akan aikin ka yasa har shugaban kasa ya baka jagorancin wata jiha. Ba abinda zance da kai sai addu’a Allah ya taya ka riko ai adalci da rikon amana. Dan duk wanda yai adalci da rikon amana baya faduwa kasa banza. Sai ka kai zuciyar ka nesa sosai.”
Nan mai martaba yai ta masa nasiha har ita ma Mamah ta shigo ta same sa
Anan Mai mataba ya ce, anjima ya fito akwai wadan da suka zo masa murnar wannan samun gwamnan da yayi.
STORY CONTINUES BELOW
Da toh ya amsa ba dan yaso ba. Sannan Mai mattaba ya fita ya rage daga Mamah sai shi.
Suna zaune Maryama ta shigo dawowar ta daga ckul kenan. Taji labarin ya dawo.
Da gudu tafado dakin tana fadin
“Yaya oyoyo!”
ta rumgume shi.
Shima rungume ta yayi ya ce,
“Ya ckul?”
“Lafiya Yaya ya hanya?”
“Lafiya Alhamdulilah!”
“Yaya kaci abinci?”
kai ya gyada masa.
“Yaya Allah ya tayaka riko. Allah sanya alheri.”
“Ameen!”
Kawai ya ce.
Mamah ta kalla ta ce,
“Mamah ya gida!”
“Lafiya ya makaranta?”
“Alhamdulilah!”
Sannan ta Mike ta ce,
“Yaya bara na kawo maka furar ka!”
“No barshi sai anjima da dare kya kawon.”
kai ta gyada ta mike ta ce,
“Mamah bari naje na watsa ruwa.”
“Nima yanzu zan taho.”
Ta tafi. Aliyu ya bita da kallo.
Shima yana son kanwar tasa. Kamar yadda take son sa. Insha Allahu shi zai nemo mata mijin aure nagari.
Sun jima da Mamah sannan ta mike ta fita. Tare da mai martaba sukai sallah magariba da isha’i sannan ya saurari bakin sa masu masa murna ya shige gun Mamah.
Maryama na ganin sa ta kawo masa damun furar da tai masa. Amsa yayi yana sha Mamah na masa magana har karfe tara sannan yai mata sallama ya tafi.
Washe gari kuwa tin safe ya tafi garin da aka bashi gwamna bai bi takan ginin gidan gwamna da ake ba sai bayan garin da yaje ya samu wani fili babba a gun.
Take ya nuna yana so aka siyar masa sannan ya bada kwangilar fara gini nan da lokaci kadan.
Ai kuwa cikin sati guda aka gama ginin gidan sa. Yaje ya gani inda ya sa akai masa order kaya daga waje aka kawo masu decoration suka je suka masa tsarin gidan.
Satin su biyu a garin su aka gama ginin gidan gwamna aka zuba komai da zai bukata.
Amman sam Aliyu ya ce, shi bazai tare a gidan gwamnati ba zai na dai zuwa duk abinda zai yi zuwa yamma ya koma gidan sa da ya sa aka gina masa.
Da Mai marataba yasu jin dalili sai cewa yayu,
“Abbah zama na a gidan na dan lokaci ne, haka kawai ina zaune ace na fita shikenan fa za a fara fitar min da kaya na. Ni kuwa na fi karfi haka dan ina da rufin asiri gidan kwana dai bazai min wuya a cikin garin ba.”
Mai martaba ya amince. Inda Hajara jin matsayin da aka bawa mmijin ta ya kara sawa ta kara girman kai da takama tana cewa hanyar samu zata dadu.
Mahaifan ta duk wata mai martaba sai ya aika musu da kayan abinci da kudi har da surtura amman haka bai hana mahaifinta sata bashi kudi ko ta debar masa ba.
************
Yau Yaa Muhammad ya dawo daga tafiyar da yayi zuwa makaranta dan sun samu hutu first Semester dan haka murna gun Aisha ba a magana. Ta rasa inda zata saka yayan nata.
Komai ta dauko ta kawo gaban sa. Shi kam sai dai ya bita da kallon son ta na kara shigar sa.
Suna zaune Muhammad ya ce,
“Aisha tah, ina jin burin ki ya kusa cika dan kinga an bawa garin mu jiha har an bamu gwamna sai dai kuma soja aka bawa. Dole sai munyi hakuri mulkin su akwai wuya ana shan wahala. Amman insha Allahu ina jin zai kula da harkar ilimi sosai tinda yasan dadin sa.”
Wani sanyi Aisha taji yana ratsa ta. Ta ce,
“Wai Yaya da gaske.”
Kai ya daga mata wani murmushi ta saki. Shi kuwa ya zuba mata ido ganin irin farin cikin da ke lullube a fuskar ya yasa ta jin dadi a zuciyar sa.
Bai da buri sai na yaga farin cikin wamnan yar kanwar tasa kuma masoyiyar sa.
“Yaya!”
ta kira sunan sa sai kuma tayi shiru.
Kallon ta yai ya gane da abinda take son fadi. Dan murmushi yayi ya ce,
“Yar gidan Yaya fadawa Yayan naki damuwar ki mana.”
Kasa tayi da kan ta ta ce,
“Yaya ina son naje naga Mamah na.”
Murmushi yayi ya ce,
“Insha Allau zan kai ki kiga Mamah.”
Murmushi ita ma tayi ta ce,
“Yaya kace kamar mu daya!”
Kai ya gyada mata,
“Yaya dan bani labarin ta.”
Nan ya gyara zama yana bata labarin Mamah tana ji tana dariya yadda sukai rayuwa da mahaifin ta da kuma yadda shima suka rayuwa tare
Can kuma sai ta hade fuska ta ce,
“Amman Yaya shine kuma Mamah ta manta dani bayan kace da zata tafi tana kuka bata so ta barni ba tatafi.”
“To menene na bacin ran kuma baga shi muna kula da ke ba. Ko Ummah da Baba na miki wani abu ne?”
Kai ta girgiza ta ce,
“Wallahi Yaya Ummah tana min abinda wata uwar batayiwa yar ta. Ba abinda zance da Ummah sai addu’a nima Allah bani ikon taimaka mata da faranta mata.”
Murmushi yayi irin wadan nan halaiyar Aisha na dada sa son ta acikin zuciyar ta.
Kallon ta yake yarinya kamar wacce ta shekara ashirin ko irin sha takwas din nan dan hankalin ta da kaifin basirar ta.
Kullum in suna tare basu da hira sai ta karatun ta. Ta saba da Yayan ta kamar me take jin sa wannan yasa take jin ko da aure sukai ba abinda zai ahiga tsakanin su.
Zuwan sa hutu komai tare suke yi, shara wanke wanke. Uniform ya wanke ya goge mata.
Haka homework ya koya mata, komai nata daban ne, dan haka tana zaton yar irin unguwar su ce.
Dan sam lomai nata daban ne. Baba da kansa yake shiga kasuwannin cikin gari ya siyo musu kaya masu kyau da yayin gari.
Wannan yasa Aisha daban ce a garin su dan sam kawar ta daya ce, Hauwa itama yar makarantar su ce. Baban ta abokin Baba ne.
Haka Yaa Muhammad ya gama hutun sa ya tafi. Da zai tafi har da kukan ta kamar yadda ta saba sanna ta ce,
“Yaya ban da kula yan matan garin nan naku dan Allah.”
Sai dai yayi dariya kawai.
Gidan Aliyu da yasa a gina masa a uguwar su Aisha yasa ai masa ginin. Amman da dan tazara tsakanin su.
Ya zagaye garin ya ga ba unguwar da tai masa sai unguwar su. Wannan yasa yasa a nema masa masu aiki da kular masa da gidan nashi dan bai son a san ko gidan waye.
Acikin wadan da aka diba aiki har da Baba da Baban Hauwa. Wannan yasa Baba ya fara aiki acan karkashin gwamna daga farko basu san gidan waye ba sai daga baya.
*
Aliyu ya fara mulki a cikin garin wanda shi sam tsakanin sa da gidan Gwamnati aiki ne. Amman Hajara ta ce, ita bata zuwa ko ina anan zatai zaman ta.
Wannan yasa ya bar ta. A gidan gwamnati duk sojoji zakai ta gani suna kula da komai na gidan wanda dayan gidan nasa daga masu gadi sai su Baba da ke kula masa da gidan wajen kula da dokuna da sauran kayan gidan.
*Ina jiran comment yawab comment yawan typing samun kwarin gwiwar da zan kara barin ku ba posting. Kuje kuyi following bawa a wattpad @MSIndabawa sannan kuyi voting ko wanne page sannan kuyi min comment. Ina godiya masoya*
*Yan Wattpad WA NAKE SO? ya dawo dan haka kucigaba da bibiyar sa hadi da voting with comment ina godiya.*
*Antty ce!*