WA NAKE SO CHAPTER 20
Www.bankinhausanovels.com.ng
Su Mamah na sauka aka aiko aka dauke su. Lokacin da suka shiga gidan Aisha ba karamin mamaki tayi ba domin bata zata nan ne gidan ba bata san waye Abbah ba sai da taga yadda ake musu abu ne tace
“Wai ku daman jinin sarauta ne?”
Murmushi Maryama kawai tayi suka shige shasjen su ana tai musu barka da zuwa. Dakin su Maryama suka shige. Ruwan wanka Maryama ta hada mata ta shiga tayi wanka ta fito Maryama tayi. Sallah tayi tana idar wa Maryama ma ta idar.
Suna zaune daya daga cikin masu musu hidima ta shigo da kayan abincin su. Zama sukai suka ci suka koshi sannan suka bare suna hira. Maryama tace
“Wai baki san waye Yaa AK ba?”
“Eh! Please fada min!”
“Ba ruwa na kyaji daga bakin sa. Amman dai Abbah shine sarkin garin nan.”
“Sarki fa kika ce!”
Kai ta gyada Aisha tace
“Ikon Allah Amman Abbah ba ruwan sa ba wanda zai ce haka saboda bashi da wani izza da daukar kai.”
Dariya Maryama tayi. Aisha tace
“Wallahi kinga fa yadda muke rayuwa dasu daman haka sarakunan suke ikon Allah.”
Maryama tai murmushi kawai. Aisha tace
“Ko da yake dukkan ku ma haka kuke. Kai amman tab!”
Ta rufe baki kawai dan sai ta tuna farkon haduwar su da Yaa AK yadda ta kasance kawai sai taji tana jin kunyar haduwa dashi. Ashe haka yake babban mutum bata sani ba.
Gaskiya ba ruwan su basu da nuna su wasu ne ace duk zaman su da Yaa Ak bata sani shi dan sarki ba ne ikon ta. Maryama ta mike ta dauko waya tace
“Bari na fadawa Yaa Muhamamd mun sauka lafiya.”
Ta fita a dakin. Mikewa tayi ta hau kan gado tana mai lumshe ido. Sai taji wata kewar Yaa AK kawai take ji ba abinda take so taji ta ko ta kasance in ba a jiki Yaa AK ba. Bacci ne ya dauke ta a haka.
Maryama suna gama waya da Yaa Muhammad, Yaa AK ya kirata.
“Yaya nah!”
“Na’amvkanwata ya kuka sauka?”
“Alhamdulillah!”
“Masha Allah kaiwa My Heartbeat muyi magana.”
Ta shiga ta kira suna ta
“Aisha, in-law!”
Amman shiru lekawa tayi taga bacci take dan haka ta kara wayar tace
“Yayana bacci take.”
“Ayyah shikenan please in ta tashi ki hada mu.”
Ta kashe wayar tana komawa itama ta kwanta dan ta huta.
Basu suka tashi ba sai da safe. Dan sun makara da sauri sukayo alwala sukai sallah sannan suka koma suka daura daga inda suka tsaya. Dan sun gaji ba kadan ba.
Karfe goma suka tashi sukai wanka sannan suka karya Maryama da Aisha suka fita dan gaishe da Mamah da Abbah a falo suka samu Mamah anan suka gaishe ta, tana yiwa Aisha ya gajiya kai tayi kasa dashi. Sai can sannan suka mike dan zuwa wajen Abbah. Shima yana dakin sa suka same shi na suka gaishe yana tambayar su ya gajiya sannan suka mike suka tafi bangaren Momy.
A falo suka sameta da Momy da Sha’awa. A nan suka gaishe ta, sannan sukai sallama mike suka tafi. Momy da sha’awa suka bita da kallo. Suna fita tace
“Kinga kamar ko?”
“Na gani Momy abin ya daure min kai har tafi kama da Mamah akan Maryama.”
“Hmmm zanje naji koma menene tashi muje muyi mata barka da zuwa sai ki shiga wajen su muyi magana.”
STORY CONTINUES BELOW

Ta mike ta dauko mayafin ta Momy tayi gaba tana bin bayan ta. A falo suka samu Mamah tana ganin su ta saki fara’a tana fadin
“Ah Hajiya ashe kece tafe!”
” wallahi!”
Ta fada tana zama. mamah ta kalli Sha’awa tace
“Zonan daughter!”
Matsawa tayi ta zauna ta fara gaishe ta suka amsa sannan ta mike tace
“Su Maryama na daki ko?”
“Eh yanzu suka dawo!”
Ta shiga dakin. Zaune ta samu Aisha na shan fura Maryama kuma na debe kayan su daga akwati tana jerawa. Tana dagowa taga Sha’awa ta dauke kai. Maryama tace
“Anty!”
“Na’am. Munzo yiwa Mamah sannu da zuwq to kinsan Momy da Mamah in suka hadu shiyasa nace bari na shigo kan su gama gaisawar.”
“Ayyah!”
Ta zauna. Maryama tace
“Lah In-law jiya fa bayan mun gama waya da Yaa Muhammad Yaya yake cewa na kawo miki ina zuwa naga kinyi bacci “
“Ayyah wallahi a jiyan ne na gaji.”
Ta fada tana yatsina fuska. Maryama tace
“Yace na kira sa in kin tashi amman na manta bari na kira sa.”
Ta fada neman layin sa. Sai dai har ta gama ringing bai dauka ba.
Haka suka zauna Sha’awa da Maryama na dan taba hira kuma duk akan Yaa AK take mata tambayoyi. Aisha kuwa kishi ya cika ta wacece wannan dake tambaya akan Mijin fa.
*
Yaa AK kuwa yana can da kyar yayi bacci ranar saboda rashin Aisha. Yana tashi da safe ya shirya suka fice dasu Yaa Muhammad su suka rakashi asibiti basu suka dawo gida ba sai gari da suka shiga zagawa wani resturant suka shiga dan cin abinci sai da zasu ci abincin sannan ya hau duba wayar sa amman ina ya manta wayar sa a mota.
Basu gama ci ya bar wajen ya koma mota. wayar sa ya dauka yana dubawa yaga missed call din Maryama abinda daman jikin sa ya bashi kenan an kira shi. Layin ya fara kira Maryama ta dauki wayar tana duba mai kira tace
“Kinga dan halak!”
Ta kai wayar kunnen ta.
“Yaya na ka tashi lafiya ya jiki?”
Ta fada bayan sun gaisa.
“Alhamdulillah ya Matata?”
“Tana lafiya!”
“Bata wayar!”
Mika mata tayi ta amsa ta mike ta fice a dakinvwani karamin daki ta shiga ta kwanta akan kilishin dake dakin tare da lumshe idon ta tayi sallama. Amsawa yayi yai yana fadin
“Heartbeat ta manta dani.”
“Ni na isa Yaa AK!”
“Gashi nan kuwa jiya har kika iya bacci bakya tare dani.”
“Kai Yaa AK da kyar fa nayi!”
“Da gaske?”
Kai ta gyada ya ce
“Bani labari!”
“Uhmm ni kawai na kasa inason na ganka!…..”
” wai dan Allah da gaske?”
“Eh mana.”
” kace kema kinyi kewa ta.”
“Sosai ma Yaa AK!”
“Ai da nace sai nan da wata biyu haka!”
“Haba dai Yaa AK ai yayi nisa.”
“Yaushe zan dawo to?”
“Kai yaushe ne gama ganin likitan?”
“Nan da sati biyu fa.”
“To Allah nuna mana.”
“Ba matsala?”
“Eh Yaa Ak!”
“Oh baki damu dani ba wallahi Sweerheart a yanzu dai ba zan iya kwana goma bake ba. Dan haka ki shirya any time zaki ina gani na.”
“Allah nuna mana.”
“Ina wayar kine?”
“Tana gida a manta ta!”
“Oh ki rike ta Maryama zan kira ki.”
“Toh!”
“I love you!”
“I lo…”
Sai tayi shiru yace
“Uhm fada min mana!”
“Ina son ka nima.”
“Nagode kinci abinci?”
“Eh yanzu na gama shan fura.”
“Mamah ce ta dama ko?”
“Yes!”
“Uhmm dadi kenan. Ki ajiyen tawa.”
“Hmm to shikenan!”
“Bye anjima zan kira ki gasu Muhammad nan!”
“Ok my regard to them!”.
STORY CONTINUES BELOW

” insha Allahi”
*
**
***
Mamah da Momy kuwa bayan sun gaisa tai mata ya me jiki sai suka hau hira. Suna cikin hira ne Aisha ta fito daga daki ta shiga na kusa da nasu. Momy tace
“Yauwah nifa ban gane Aisha ba yar gidan wacece ne a kannen ki?”
“Muna kama ko?”
Kai ta gyada. Mamah tayi shiru kawai dan ita kan ta tana mamakin kamar da suke da Aisha. Sai ta basar ta dauko ta ciwon Aliyu.
Ba dan Momy ta manta ba ta biye mata amman tana zuci zucin ta sake dauko maganar kuma aka kira sallah la’asar dole suka mike ita ta tafi sashen ta Mamah ta shiga dan tayi sallah.
Haka akai a dakin su Maryama ma. Sha’awa tace
“Wai wacece wannan ne?”
“Hmmm Sister Aisha kenan!”
“A ina take? Yar uwar kuce?”
Kai kawai Maryama ta gyada mata, lokacin da Aisha ta shigo kenan ta ajiye wayar ta dauki Hijab ta saka tana fadin
“an kira sallah fa.”
Mikewa Sha’awa tayi tace
“Bari na tafi Maryama sai anjima.”
Ta fita. Mikewa Maryama tayi tayo alwala tazo ta tada sallah.
*
*
*
A cikin kwana biyun da suka taho kullum yini take makale da waya dan da sun gama waya zai kara kira komai ya gani zai fada mata sosai ta sake dashi suke hira ta waya dan har vedio call suke yi.
Mamah kuwa tini ta dauko mai gyaran amarya ta da a fara gyara Aisha. Wanda kwana su biyu da dawowa tazo ta farai mata amman kwana daya akai ana mata gaba daya ta fara sauyawa.
Ana gobe zasu dawo da safe suka fita ita da Maryama. Sashen Yaya Aliyu suka nufa nan Maryama ta hau gyarawa Aisha na taya ta sai da suka gama kintsa komai sannan suka koma sashen su.
Aliyu kuwa ji yake kamar ya janyo ranar gani yake kamar lokacin baya sauri. A ka’ida sai washe gari in Doctor ya duba shi zai taho amman ya saka daru shi a ranar zasu taho dan tinda su Aisha suka taho ya gama hada abubuwan tafiyar sa. Daga asibiti suka zarce Aiport dan ko Hajara a can suka same ta dan yace ba zasu koma gida ba.
Faisal anan suka rabu yace sai yazo gida sai tafiyar ta rage daga Hajara sai Muhammad da Aliyu. A haka suka sauka a garin su. Aka aiko da motocin da zasu zo daukar su.
Aisha fa yau tin safe take bacci dan jiya sam bata samu tayi bacci ba kusan kwana sukai suna waya da Aliyu kuma bai fada mata zai dawo ranar ba ya hana Maryama ma ta fada masa.
Tin da tayi break tayi wanka take baccin ta sai Mamah da Maryama ne ke kitchen suna ta shirya musu abinda zasu bukata.
Gidan kuwa ya cika da Matan su Yaa Abubakar Yaa Usman da Umar da Farouk duk suna Falo ana ta hira tsakanin su gwanin sha’awa.
Suna dawowa aka wuce dasu bangaren Aliyu suka shiga suka ajiye abun su sannan suka karasa fada suka gaishe da Abbah. Bangaren Mamah suka nufa tin daga kofa zaka jiyo yara da hayaniyar iyayen su. Da dane juyawa zai yi amman yanzu ko dan yaga Aisha ba zai iya juyawa ba. Ciki ya shiga Muhammad na bin sa a baya.
Yaran na ganin sa suka karasa suna fafin
“Oyoyo Uncle A!”
Tsayawa kallon su zai ya rasa wa zai fara dauka dai dai da dai dai ya dauke su duk wanda ya daula sai ya gaishe shi ya masa ya jiki haka ya gama sannan yace
“Meet Uncle M!”
Da gudu sukayi wajen Muhammad yadda Aliyu yai musu shima yai musu suka gaishe su ya ajiye su sannan su karasa falon da matan yayen sa da kannen sa suke. Yana shiga ya fara raba ido ta inda zai gano ta amman babu ita.
Gaisawa sukai suna masa ya jiki da hanya ya amsa zai mike kenan sai ga Mamah da Maryama nan. Tana ganin Yaa muhammad tayi wajen sa tana fadin
“Oyoyo Yaa Muhammad sannun ku da sauka.”
“Yauwah kanwata ya kike?”
“Lafiya ya hanya?”
“Alhamdulillah.”
Sannan suka gaisa da Mamah bayan ta gama gaisawa da Aliyu. Tace
“Ya kamata kuje kuyi wanka kuci abinci kan ayi magariba ko?”
STORY CONTINUES BELOW

“To Mamah!”
Suka mike suka fita su Yaa Usman da Yaa Abubajar suka sama a dakin Aliyu. Suna shiga suoa rumgume juna sannan sukai musu ya habya.
Daki Aliyu ya shiga yayo wanka ya shirya ya fito cikin kayan sa masu kyau Yaa Muhamamd yace
“İyee shine ka tafi kai wanka ka barni.”
Ya mike yana kallon Yaa Usman yace
“Bari na watsa ruwa na fito.”
Ya shige ciki zama Aliyu yayi yace
“ina Umar da Farouk ne?”
“Suna nan zuwa mai martaba ya aike sune.”
“Ok”
Muhammad bai jima ba shima ya fito cikin shirin sa yai kyau sosai nan ya nufi dining yana fadin
“Naga alamavkai baka jin yunwa.”
Dariya Yayi yace
“Sai naga matata zanci tukkuna.”
Yaa Abubakar yace
“Ah tana ina ne nifa ban ganta ba yau kwata kwata.”
Fuska ya marairaice yace
“Muma bamu ganta ba.”
Muhammad yai dariya yace
“Kasan ta boya take sai kace wata amaryar kauye.”
“A’ah Kanwata ba amaryar kauye bace.”
Yaa Abubakar ya fada
Su Umar ne suka shigo direct dining suka nufa wajen Muhammad dan wai yunwa suke ji. Sai da suka ci suka koshi sannan suka gaishe da Yaa Aliyu ya amsa yana fadin
“Ku kuwa wacce irin yunwa kuka kwaso.”
Sukai dariya. Tare suka tafi masallaci dan yin sallah isha’i.
Sai karfe shida ta tashi. wanka tayi ta shirya cikin wata doguwar riga sea green wacce akaiwa ado da red stone tai mata kyau sosai ta fesa turare. Falo ta fito nan taga su Anty Khadija, Hauwa, Nusaiba, da Fateema. Da fara’a ta karasa tana fadi
“Yaushe kuka zo banji ba.”
“Munzo kina ta bacci ai.”
“Ayyah!”
Nan ta hau gaishe su duk suka amsa suna musu ya hanya da me jiki.
Little Maryama ce ta karaso Aisha ta dauke ta tana fadin
“Baby so cute kamar ta daya da Abban fa.”
Sukai dariya. Maryama ce ta fito tana fadin
“Ah İn-law ashe kin tashi?”
“Na tashi da baki tashen ba.”
“Ai fitowar da nayi kenan.”
“Hmm shikenan!”
Kiran sallah magarib shi yasa suka tashi gaba dayan su har yaran su duk sukai sallah.
Basu fito ba sai da sukai isha’i dukkan su suka hadu a falo Mamah. Mamah na gefe sai Anty Khadiya da Hauwa. Aisha na tsakiyar Nusaiba da Fateema suna ta hira abin su tana dauke da Fulani R gefen ta kuma Gimbiyya Maryama.
Kayan abinci ake direwa tare da jagoranci Maryama. Bayan an gama Mamah ta kalli Maryama tace
“Kije ki kira Antyn ki!”
“To Mamah!”
Ta fita dan kiran ta.
*
Tin da ta dawo tana tare dasu Momy da sha’awa sai kulle kullen su suke yi. Ko sallah basuyi ba suna zaune a falon Momy. Bangaren Hajara ta je amman mai kula dashi tace tana bangaren Momy. Ba ta so ba ta juya ta nufi sashen Momy.
Tana shiga Sha’awa ta ce
“Ah Maryama ke ce.”
“Eh Anty ina yini?”
“Lafiya lou!”
Ta kalli Hajara tace
“Kun dawo lafiya Anty?”
“Lafiya.”
“Daman Mamah tace nazo na kira ki!”
“Ok gani nan!”
Maryama ta juya ta fita. Hajara ta bita da harara sannan ta mike tace
“Bari naje daga nan zan wuce na yi wanka na zan kwanta ko zaki shigo ne.”
“Kai A’ah ina da abinyi.”
“Shikenan!”
Ta fice ta nufi sashen Mamah.
Tana shiga taga matan yan uwan mijin ta. Jiki a sanyaye ta karasa ta zauna a gefe ta gaishe da Mamah. Mamah ta amsa tana mata ya hanya sannan suka gaisa da sauran a dan shashare Aisha kuwa da ta gaishe ta ma bata amsa ba kuma itama bata damu ba ta dauke kai.
Abinci aka hau serving matan duk suka hada a plate daya sannan kowa ya dauki spoon din sa sukai bismullah suka fara ci. Suna gamawa duka gyara wajen suka zauna suna hira.
Sallamar su Yaa Abubakar tasa su dagowa suna amsawa. Aisha na gefe ta dago sai suka hada ido daya Yaa Muhammad mamaki ne ya kamata dan bata san yaushe ya dawo ba sai ta tuna tare fa suka bar su da Hajara da Yaa AK kenan shima Yaa AK din ya dawo ko me?
Bata gama tunani ba taji Fulani R ta mike a guje tayi wajen su tana fad8n
“Uncle A oyoyo!”
Dagowar da zatai ta ganshi ya daga yarinyar yana fadin
“Mamanah ya kike?”
Ya fada yaja kure Aisha da kallo kai tayi kasa dashi. Nan suia zube suna gaishe da Mamah. Mamah tace
“Maryama a kawo musu abincin su ko? Ko akai mu dayan dakin?”
“No Mamah barmu muci anan!”
Cewar Aliyu. Yaa Muhammad yai murmushi ya tabo shi yace
“Kai malam ka nutsu dai.”
Kai ya shafa ya samu waje ya zauna yana fuskantar ta. Aisha ta kalli Yaa Abubakar ta gaishe shi ya amsa yana fadin
“Ya hanya ya me jiki?”
“Alhamdulillah.”
Ta gaishe da Yaa Usman shina yai mata ya me jiki. Kan ta gaisar da Umar da Farouk s7ka hada baki suna fadin
” ina yini İn-law?”
İta sai suka bata kunya kanta a kasa ta kara gaishe su suka amsa ta gaishe da Yaa Muhamamd sannan Yaa AK tai musu ya hanya. Tana gaishe su ta mike ta nufi dakin su.
Da kallo ya bita dan ji yayi kamar yaje ya kamo ta amman ba hali Mamah na zaune. Abinci aka kawo musu nan suka fara ci amman gaba daya hankalin Aliyu na ga dakin da Aisha ta shiga.
Mamah ce ta mike tace
“Bari taje wajen Abbah!”
Sukai mata sallama. Tana fita Hajara ta mike Aliyu ma mikewa yayi. Hajara ta nufi kofa shi kuma ya nufi dakin da Aisha ta shiga.
Umar ya tabo Farouk shi kuma ya tabo Yaa Muhammad suka saki murmushi. Umar ya ce
“Muhammad kanwar ka dai ta gama kama mana Yaya.”
Yai dariya yace
“Sun gama kama junan su dai.”
“Kuma fa haka ne. Allah ya daurar da soyayyar su.”
“Amin!”
*
Tana shiga daki ta zauna a gefen gado tana dauke numfashi sai ta lumshe ido tana sakin murmushi. Dan ba karamin dadi taji da dawowar Yaa AK ba kan gado ta kwanta tare da jan pillow ta rungume a jikin ta.
A haka aka budo dakin bata kawo Yaa AK bane dan haka sai ta kara gyara kwanciyya kallon ta ya tsaya yi take yaji wani abu na masa yawo a jiki a hankali ya hayo gado tana can duniyar tunani sai jin numfashin sa tayi yana gauraya da nata kan ta bude ido ta ji shi akan ta. Tana bude ido sukai hada ido kallon juna suka tsaya yi.
Ya lakaci hancin ta yace
“Ina kika shiga tin dazu muka dawo ina neman ki?”
Kokarin tashi tayi amman ya danne ta yana dage mata gira. İdo ta lumshe tace
“bacci naje ai bakace min zaka dawo ba.”
“Naso na baki suprise ne!”
“Uhmm sannu to ya hanya?”
“Alhamdulillah! İ miss you ya naga kin kara kyau ne?”
Ya fada yana shafa fuskar ta. Murmushi tayi yace
“Kai ka gama cin abincin ne?”
“A’ah na kasa ci sai nazo wajen Heartbeat dina.”
“To ka ganni kaje kaci abinci.”
” ban gama ba!”
“Mamah fa haka ka baro su kabiyo ni?”
“To meyasa kika taho.”
“Ba kai bane sai wani kallo na kake!”
“Au kada na kalle ki?”
Kai ta gyada. Yace
“Ai ban san lokacin da nake kallan ki ba bare ki hanani kallon naki.”
Kissing goshin ta yayi
Aliyu kuwa bashi ya bar sashen Mamah ba sai wajen sha biyu na dare, shima dan Aisha ta takura masa ne, kuma taki yadda ta bishi dole ya tafi.
Dawowar sa duk sai ya takura mata domin da ya gaisar da Mamah yake yo wa daki inda take ita kuma tai ta jin kunya haka zasu yini a daki in ba sallah zai je ba.
*
Bayan sati biyu
*
Mamah ce zaune da Mai martaba tace
“Ranka ya dade ya kamata ayi abinda za ayi yarinyar nan ta tare ni na gaji da rashin kunyar Aliyu duk yasa yarinya ta daina sakewa dani wallahi.”
“To Fulani ake nake jira. Ya dai kamata a hada mata lefe sannan ko walima ne ayi asan matar sa ce ta tare ko ya kika gani?”
“Hakan yayi amman kuma inda zata zauna anan fa?”
“Sai a kara jan ta can gefen sa a gina mata kan ayi hakan ta tare ko dakin sa ne tayi sharing me kika ce?”
“Hakan yayi anjima zanyi order kaya sai a kawo. Amman nan da yaushe kake gani za ayi?”
“Eh toh! Me zai hana a yi nan da sati daya kinga lokacin sai akai mata kayan can gida in yaso suma in suna da bukatar yin wani taron acan ko?”
“Shikenan Allah ya sa ayi lafiya a gama lafiya amman gaskiya nida tinda yaji sauki ya dauki matar sa su tafi kan nan a samu a gama gyara amarya ko?”
“Duk yadda kika yi dai dai ne!”
“Nagode!”
*
Da yamma ya shigo bayan sun gaisa ya mike zai shiga dakin nata
“Baba na!”
Juyowa yayi ya dawo ya zauna. Mamah ta gyara zama tace
“Munyi magana da Abbahn ku akan maganar tariyyar ku. Dazu nayi magana da me kawon kaya dan har na gama selecting wanda nake so yace nan da jibi kayan zasu iya zuwa. To za muyi Walima in yaso sai ta tare!”
Maryama da ta fito tace
“Haba Mamah walima kadai ni da na gama fitar da anko a’ah gaskiya event hudu na tsara sai a dada da walimar taku gaskiya.”
Aliyu dai kallon ta kawai yake. Mamah tace
“Shikenan sai ki tsara komai amman ranar da muka saka ranar za ai walima ba zamu daga ba sai kuyi before walima day din.”
“İnsha Allahu amman Mamah ni gani nake acan gidan su İn-law zamuyi wasu taron kinga acan friends din ta suke in yaso mother event, dinner da walima sai ayi nan!”
“shikenan sai kije ki fitar da komai ki tsarakan lokacin ko?”
“Thank you mamah nah.”
Ta mike ta bar wajen. Mamah ta sauke ajiyar zuciya tace
“Abin dai ba zai ja lokaci ba dukka baifi nan da sati biyu ba kaga yana da kyau kan lokacin ka koma bakin aikin ka kaga wajen six week baka kasar yanzu ya kamata kaje kayi wani abu kan lokacin in aka ce sai time din kai kuma aikin ka fa?”
“Haka ne Mamah amman da ita zamu tafi ko?”
“A’a A’ah kai da matar ka zaku tafi ita kuma ai sai dai a kawo maka.”
“Amman Mamah!”
“Kaga Baba na kayi yadda nace kawai kaje Allah tsare kaji.”
“Shikenan Mamah nagode Allah kara budi yanzu me kuke bukata na abun?”
“Bama bukatar komai wannan karan zaka halici bikin ne ko shima baka so.”
Kai ya sosai yai kasa da kai. Tai murmushi tace
“Shikenan sai ku fara shirin tafiya ko zuwa jibi monday ko?”
STORY CONTINUES BELOW

“İnsha Allahu.”
Ya mike sum sum ya wuce dakin da Aisha take.
Kwance ya same ta tana bacci ya zauna a gefen kafar ta ya fara jan yatsun kafafon ta ido ta bude sai ta ganshi zaune ta mike yace
“Baccin Yamma?”
“Bansan ya dauke ni ba “
“Ke kadai ko?”
Kai ta girgiza ya mike yace
“Taho muje garden dina kiga wajen shakatawa ta.”
Ya kamo hannun ta. Suka fito tare tana ganin Mamah ta kwace hannun ta tai kasa da kai. Wajen ta ta karasa ta durkusa tace
“Barka da hutuwa.”
“Yauwah Aisha!”
Sai sukai shiru. Aliyu ya kalle ta yace
“Taso mana!”
Kafada ta make ya kalli Mamah yace
“Mamah zamu dan zaga gidan ne wai dan ta ganki ta fasa.”
Kallon Aisha tayi tace
“A’ah tashi kije kinji Aisha!”
A hankali ta mike yai gaba tabi bayan sa. Kan ta karasa har ya fice ta kofar ciki. Tana fita taga ba kowa tafiya ta cigaba dayi sai kuma ta tsaya. Ji tayi an daga ta cak ta juyo a tsorace tana son taga waje. Dariya ya saki ya dire ta yana fadin
“Gaskiya baki da nauyi.”
“Uhmm a hakan?”
“Eh mana kalle ki fa yar baby!”
“Tab ni gani na nake katuwa.”
Dariya yayi ta tsaya kallon yadda yake dariyar. Tai masa mugun kyau. Shi komai nasa mai kyau ne. Ta fada a zuciyar ta.
Kallon sa ta tsaya yi ya dago ya dage mata gira sai ta dauke kai kawai ta tsuke fuska ya ce
“To menene?”
“Uhmm me kakewa Dariya?”
“Wai kince ke katuwa ce kina kallon kan ki kuwa a mirrow!”
“Ni babba nake gani na ai.”
Hannun ta ya kama suka nufi kofar sashen sa. Suna shiga ya wuce da ita falon sa. wani kamshi ma dadi ya daki hancin ta. Bai tsaya da ita ba sai a cikin bedroom din sa a gaban mudubi.
Kallon kanta ta tsaya yi yana bayan ta ta mudubin yake kallon ta ya daga mata kai ta dauoe kai daga kallon sa. Yace
“Kin ganki fa!”
Baki ta turo tace
“To dame ka fini ai kadan ne!”
İdo ya xaro yace
“Ni din bari na tube kiga yadda nake!”
Ya daga hannu zai cire rigar da sauri tace
“Me ni dai barshi kawai”
Tayi hanyar waje ya sauke hannu yabi bayan ta.
Har ta kai kofa ya janyo hannun ta yace
“Baki ga sashen naki ba ai?”
Da ido tai masa alamar tambaya yace
“Eh anan zaki zauna!”
Murmushi tayi ta dauke kai tace
“Muje ko?”
Janyo ta yayi ya rumgume ta, tare sa lumshe ido. Ajiyar zuciya suka sauke gaba dayan su.
Kofar dakin aka budo bai bude ido ba kamar yadda Aisha ma idon ta ke a lumshe. Hajara ce ta shigo ta tsaya tana kallon su. A hankali ya bude ido yana kallon ta, fuska ta tamke yace
“Fitar mun a daki in baki iya sallama ba.”
Da sauri Aisha ta bude ido tana kokarin ta kwace jikin ta amman yaki ya bata dama. Kallon su ta tsaya yace
“Nace ki fita ko?”
Da sauri ta juya ta fice daga dakin zuciyar ta kamar zata fashe. Sashen Momy ta wuce ta samu Momy da Sha’awa suna shiri zasu fita.
“Lafiya Hajara?”
Sha’awa ta tamnaye ta?”
Kuka ta saka musu ta zauna tana basu labarin abun da ya faru. A yadda ta basu labari har Sha’awa ta fita shiga damuwa da tashi hankali. Momy ce ta lallashe su tace
“Yanzu in sun fita zasu bi6a wajen malamin su.”
Wannan ne ya kwantar da hankalin Hajara. Da sha’awa suka tafi ita kuma ta koma dakin ta.
*
Tsaki ya saki ya sake ta ya koma kan kujera yana dafe kan sa lallai Hajara ta fara raina shi ya za ayi tana shigar masa daki ba salama sai kace dakin kafiri. Aisha da ya sake ta ta juya tana kallon sa. A hankali ta karasa ta zauna a gefen sa ta cire hannun sa tana fadin
“Kayi hakuri Yaa AK!”
STORY CONTINUES BELOW

Dagowa yayi yana kallon ta sai ta shige jikin sa ta rumgume shi tana fadin
“Kada kasa damuwa please kayi hakuri.”
“Na hakuii Aisha ai ba ke kikai min laifin ba.”
“Duk da bani nayi ba kayi hakuri.”
“Ya wuce.”
“Yauwah tashi muje to!”
Ta mike ta kama hannun sa. Ya mike suka fice. Garden din sula isa suka zauna akan kujera. Sosai sukaji dadin wajen sukai having fun tsakanin su. Basu sula bar wajen ba sai karfe sida da rabi shima dan an kira magarib ne.
*
Da dare ya shiga zaibwa Mamah sallama ya kira Maryama bayan tazo yace
“Kije kicewa Hajara gobe taje gida tai musu sallama dan jibi zamu tafi.”
“Toh Yaya!”
Har ta juya zata fita ya kira ta yace
“Ki debi kudu ki kai mata.”
“Nawa?”
“Duk yadda kikaga yayi.”
“To Allah kara gimma da arziki.”
“Amin! Ki dauki abinda kike bukata kema.”
” nagode Yaya Allah kara budi.”
“Amin!”
Ta fita. Ya kalli Mamah yace
“Ni zan tafi sai da safe.”
Ya juya zai fita Mamah tace
“Bakaiwa Matar taka sallama ba.”
Kai ya shafa sai ya juya ya nufi bangaren da take. Mamah ta mike ta wuce dakin ta kawai.
Yana shiga ya same ta kwance akan gado ta lumshe ido karasawa yayi ya zauna a gefen kafar ta tare da jan yatsan ta. Kafar ta janye ta bude idanun ta tana ganin shine ta mike zaune tana fadin
” yaya bakai bacci ba?”
“Eh nazo nai miki sai da safe sai naji ba zan iya kuma tafiya na barki ba.”
“Hmm me to?”
“Kizo muje bangarena ki tayani kwana yau!”
İdo ta zaro ta fara girgiza kai tana fadin
“Ni ba zan iya ba.”
“Ok!”
Ya mike ya kalle ta yace
“Gud nyt!”
Hannun sa ta kamo ya juyo ya dawo ya gyara mata kwanciyya ya ja mata abun rufa sannan yai kissing goshin ta yace
“Sai da safe kiyi bacci me dadi.”
Ya mike ya fice. İdo ta runtse sai ta mike zaune ta zuba tagumi. A haka Maryama ta shigo ta same ta. Kallon ta tayi tace
“Au baki baccin ba?”
“Eh!”
Ta koma ta kwanta. Har Maryama tai wanka tazo ta kwanta batai bacci ba sai juye juye take. Maryama tace
“Lafiya kuwa sister?”
Kamar jira take sai idon ta ya fara zubar da ruwa a tsorace Maryama ta tashi tana fadin
“me kuma ya faru?”
*
**
***
****
*****
******
*******
Washe gari Fauwaz yaje gun Uncle Aminu. Uncle ya amshe shi kamar yadda suke a da dan yana daukar sa tamkar dan sa. Bayan sun gaisa ya tambaye shi ya bayan saduwa sai daga baya yace
“Uncpe daman nazo ne akan ina son a bani auren Fatrema.”
“To ka gudu ka dawo kenan ko?”
Kan sa a kasa yace
“Haka ne Uncle”
“Shikenan zan yiwa Alhaji Muhammad magana kai nan da yaushe kake son bikin.”
“Uncle me za a tsaya ai da kunyi magana ko wani satin ne ayi kawai.”
“Ka shirya kenan?”
“Eh!”
“To shikenan Allah tabbatar da alheri. zan yiwa Fateema maganar.”
“To Uncle nagode.”
“Ba komai.”
Bayan tafiyar sa Uncle ya kira Fateema a waya tace tana gun aiki in ta dawo zata biyo. Karfe biyar da rabi ta shiga gidan Uncle lokacin baya nan na suka zauna suka gaida da Mama. A nan tai magariba sai bayan magariba ya shigo. Har dakin sa taje ta gaishe shi. Ya amsa sannan yace
“Ya aikin?”
“Alhamdulillah!”
“Madalla a karo na biyu an kara fitowa neman auren ki amman wannan ba kowa bane sai dan uwan kivme zakice Fateema?”
“Uncle duk abinda kukai yayi Allah yasa haka ne mafi alheri.”
“Amin Fateema Allah miki albarka ya jikin Yaya ya baki zaman lafiya.”
STORY CONTINUES BELOW

“Amin!”
“Shikenan neman kenan. Sai kije wajen Adam me furnitures dake can zoo road ki zabi wandavkike so!”
“Uncle ai da ka zabar min.”
“A’ah Fateemabkije ki zabi duk wanda yai miki shikenan.”
“Nagode Uncle.”
“Ba komai Fateema zan bawa Momy ki sai a siya miki kayan kitchen dan abun ba zai wuce nan da sati daya zuwa biyu ba.”
“Nagode Uncle Allah kara budi ya jikan iyaye.”
“Amin!”
Ta mike ta fito idon ta na kawo kwalla. Ita yanzu duniya ma tsoro take bata ta sadakar da wani farin ciki zata auri koma waje tai masa biyayya Allah yasa ta gama da duniya lafiya kawai.
Ko da taje gida daki kawai ta shige bataiwa kowa magana ba ta rufe abun ta.
Uncle, Fateema ba fita ya kira Alhaji Muhammad nan suka gaisa ya fada masa bukatun Fauwaxs Alhaji Muhammad yace
“Ikon Allah Fateema dai rabon sa ce kenan. Masha Allah ya tabbatar da alheri.”
“Yace nan da sati daya fa.”
“A’ah a abar yarinya ta shirya a saka wata daya.”
“A’ah Alhaji a bar satin dai.”
“To a kara sati daya lokacin sati biyu kenan yayi?”
“Yayi Allah kaimu.”
“Amin amin.”
Sukai sallama.
Washe gari Uncle da kansa yaje yayiwa su Momy da Baba bayani Baba tace
“Ita ta yadda to dan ba zan yadda ai mata auren dole ba.”
“Ta yadda Baba jiya munyi magana da ita.”
“To shikenan Allah sanya alheri.”
“Amin! Nan da sati biyu za a daura auren!”
“Allah kaimu ya sanya alheri.”
Momy ta fada.
Uncle na tafiya Mami ta kira tace
“ashe Fauwaz ya nemi auren Fateema.”
“Wallahi Yaya.”
“To masha Allah ina nan zuwa na da sati kan bikin insha Allahu.”
“Allah kaimu me za ayi kenan.”
“Me kuwa za ayi Yaya ai daurin aure kawai sai yini a ranar ko?”
“Ita Fateeman ba abinda take bukata?”
” sai dai a tambaye ta amman kinsan halin ta ai.”
“Shikenan zan kira ta.”
“Ok!”
Fateema Ba wanda ta fadawa ko Suraiyya haka ta cigaba da rayuwar ta. Adam da Uncle yai masa magana akan Fateema tai masa magana yace a’ah shi da kansa ya tura mata hadaddun kayan daki kala kala wai ta zaba. Tana office dan haka sai ta turawa Suraiyya. Suraiyya tai mamaki ta zabar mata ta tura masa.
“Na menene kayan?”
“Nawa ne?”
“Kayan daki zaki canja.?”
“Hmm aure na fa nezt week!”
“what amman baki fada min ba. Da waye?”
“Dawa kike tunani!”
“Badai Yaa Fauwaz ba.”
“Shi!”
” ikon Allah. Allah tabbatar da alheri anjma zan zo ya kamata a fara gyaran jiki.”
“Dan Allah sis ni a kyali da wannan gyara gyaran.”
“Anki ki jira ni anjima zanzo gidan.”
“Sai kinzo Ya Dad dina?”
Yana nan sai fitina yake min.”
“Baba nawa.”
Tai dariya kofar office din aka budo ta dago tana kallo sa tsaye a bakin kofa sanye da bakin wando da yellow kalar riga yai kyau. Sai kamshi yake. Dariyar ta katse tace
“Sai anjima din.”
Ta kashe wayar fuska ba yabo ba fallasa tace.
“Ina yini?”
Kallon ta yake kawai dan yau sati daya rabo sa da ita tinda ya shiga dakin ta bai kara ganin ta ba. Zama yayi yace
“Amarya ta.”
Ta danyi murmushi kawai. Yace
“Bamu zauna ba tin ranan bana ganin ki sai buyar min kike ke haka ake ne!”
“Ai gwara na gudar maka kan na shiga a makale ni ko?”
“Wannan haka ne amman a sassauta min.”
“Anyi!”.
“Nagode!”
Ya kura mata ido ta danyi fari da ido tace
“Kallon fa Yaa Fauwaz!”
Tai maganar a shagwabe. Ido ya lumshe ya bude yana murmushi yace
“Wallahi Fateema kin kara kyau.”
“Ko?”
Kai ya gyada. Sannan yace
“Me kike ganin za ayi ne a bikin nan.”
“Oh har wani shagali za ayi?”
“Ah ya za ayi bikin Fateema da Fauwaz ba wani shagali kema kinsan dai sai anyi.”
“Me za ayi?”
“Bridal shower, Arabian night, Dinner da yini.”
Dariya ya bata tace
“Gaskeiya Yaa Fauwaz sunyi yawa kasan me abu biyu za ayi kawai ko ayi bridal shower da yini, ko Arabian night da yini ko dinner da yini?”
“Why?”
“Nifa ba budurwa bace!”
“Agun wa? A guna ai a budurwa zan dauke ki?”
“Uhmm to abu biyu dai gaskiya.”
“Shikenan Dinner da Yini!”
“An gama.”
“Lefen ki yana nan zuwa dis weekend in Momy xata zo.”
Ido ta zaro tace
“Wai har da wahala?”
“Matata ce fa kuma kanwata menene wahalar ai da akwai ne kawai.”
Murmushi tayi tace
“Godiya nake.”
“Nike da godiya.”
Ranar tare suka koma gida.
Suraiyya ta zo ta kawo mai gyara tace kuma ta ajiye aikin nan sai bayan biki tinda ance zai kama mata gida anan amman a lagos zai zauna inda shima Dad din sa ya kai takardun sa aka dauke shi aiki a Baban asibitin su.
Duk da a can lagis din ma an gina masa gida mai katon kowa da bangaren sa. Na nan kano ne na Fateema kawai.
Gloria ta koma Lagos wajen Mami dan tace tafi son can duk dan kishin Fateema.
*
Jidda dai ana ta kula da ciki dan asibitin Fateema ma take zuwa awo duk da ba Fateema ke duba ta ba amman in taje takan shiga su gaisa. Yau ma bayan an gama awo ta tafi da katon cikin ta zata shiga office din Fateema ta hadu da securityn ta tace
“Ai bata nan!”
“Lafiya dai ko?”
“Lafiya lou bikin tane wani satin shine ta dauki hutu tin yanzu.”
“Ah Masha Allah sanya alheri.”
“Amin”
“Nagode in naje gida na kira ta.”
Ta juya ta wuce. Ta shiga mota ta bar asibitin.
Da dare suna zaune a falo tace
“Ka tina doctor da ta duba mun nan?”
Gaban Aslam ne ya fadi yace
“Eh!”
“Wannan satin bikin ta fa?”
” wadin?”
“Dr Fateema mana.”
“Wannan satin kamar ya?”
Ya fadar haka ya mike ya fice sai gidan su.
*Me wannan kuma yake shirin yi ne? Ku tambayar min shi please*