WA NAKE SO CHAPTER 24
Www.bankinhausanovels.com.ng
Yana shiga yaji gidan shiru kamar ba kowa. Falo ya shiga nan ma tsit ba kowa. Dakin ta ya nufa yana bude kofa ya hango ta kwance a tsakiyar gado ta rumgume pillow tana baccin ta hankali kwance. Karasawa yayi ya zare pillow ya shige jikin ta yana jin ta har da kara shigewa jikin sa. Hannun sa ya zura a cikin Kan ta ya farai mata tafiyar tsutsa. A hankali ta fara bude ido ta sauke akan Fauwaz. Ido ta bude gaba daya tana kallon sa. Yace
“Eh ke baccin kima kike yi cikin kwanciyyar hankali ko?”
Ta mike tana fadin
“Kai Yaya!”+
Ya janyo ta jikin sa tace
“Ya hanya. Ashe kana tafe ai baka fada min ba.”
“Dan ki hanani zuwa.”
“Kai Yaya ai na daina.”
Ya fara kissing wuyan ta yana shakar kamshin ta dake hargitsa masa tunani. Take ya saukar mata da kasala da wata muguwar sha’awar ta. Nan suka zube akan gadon suna romancing junan su. Daga nan suka hau faran tawa junan su.
Sai da suka shafe lokaci mai tsayi sannan suka wuce sukai wanka. Ya tafi masallaci ita kuma ta yi anan dakin. Tana idarwa ta wuce kitchen dan ta samar masa abu mai sauki. Fried supegette tayi masa wacce ta saka matan yankakken nama da vegetables. Sai lemo da ta hada masa na mango ta tace ta saka suga kadan sanman ta jere kayan akan dining.
Daki ta shiga tai sallah sannan tayi kwalliyar ta cikin wasu kananun kayan ta masu kyau. Ta shafa turare. Falo ta fito ta zauna tana kallo a TV.
Tana zaune taji sallamar sa ta mike tana amsawa ya shigo ta fada jikin sa tana fadin
“Ina kaje ne?”
“Masallaci na hadu da neighbor din mu ne na tsaya mun gaisa.”
“Oh nifa nace. Kaje ka zauna baka ci abinci ba.”
Ciki ya shafa yace
“Kuma yunwa nake ji ba, dan ba abinda naci na tsaya sai abincin ki.”
Hannun sa ta kama ta nufi dining ta zaunar tana fadin
“Kai ne da ka zo ba abinda kake nema sai ni.”
“In ban same ki ba ai ba abinda zan iya. Kuma in na same ki komai dai dai yake koma min har yunwa daina ji nake yi”
Fulas ta bude kamshi ya cika wajen. Ido ya lumshe. Fateema tace
“Ai sai kayi tayi.”
Ya kura mata ido tana zubawa sai kuma ya saki dariya yana fadin
“Zo kiji ji na tuna miki wani abu!”
Ya kamo hannun ta ya zaunar a cinyar sa. Ta mike tana fadin
“Kai ko Yaya? Ka bari ka gama sai muyi maganar!”
Ta ajiye ta zuba masa lemo ta zauna ta zuba masa ido yana cin abincin. Dagowa yayi yana dage mata girar ta.
Ta saki murmushi tace
“Yaya yasu Mami na? Da Annur da Mamin sa?”
“Kowa lafiya. Tare muke dasu suna gidan Momy.”
“Ah haba da ka kawo su nan ga waje nan availble.”
“Ni nan gidan ki ne.”
“Itama ai.”
Ya cigaba da cin abincin sa. Ya gama ta saka tissue tana goge masa baki ya mike yana fadin
“Alhamdulullah. Sai yanzu naci abinci tinda na bar garin nan.”
“Kamar ya?”
Ya kamo hannun ta sukai falo. Yace
“Eh duk abinda nake ci ji nake tamkar ba abinci ba. Naki ne kawai mai dadi da gusar min da yunwa.”
Story continues below
Ta kwanta a kirjin sa tana fadin
“Me kace zaka fada min dazu?”
Magana ya fara a kunnen ta yace
“Wani abu na tuna nake son nai miki tambaya!”
Ido ta lumshe tace
“Me fa?”
“Nace zan tambayi akan!….”
Ya kanne mata ido daya
“Nifa bangane ba.”
Yace
“Kin tina kina amarya da nace zan tambaye ki abin da dadi bayan lokaci mai tsayi.”
Dukan wasa ta kai masa kirji tana fadin
“Kaji ka Yayan nan!”
Ta kifa kan ta a kirjin sa. Ya dago ta yana fadin
“Eh mana fada min! Ko da yake nima zan iya fada yadda ake min sambatun da kukan dadi ko?”
Mikewa tayi daga jikin sa tayi daki a guje. Ya mike ya bi bayan ta yana fadin
“Eh amman a bani sweet nasha.”
Ya rufo kofar yana shiga ciki.
*
Washe gari tare sukai komai na gidan sukai hada breakfast. Sai da suka gama sannan suka shiga sukai wanka. Suka shirya anan dining suka karya.
Karfe sha biyu suka shige gidan Momy. Bangaren Momy sukai gaba daya. Momy da Baba na falo sai Annur dake dining yana jin sallamar su Fateema ya rugu yazo ya rumgume. su yana musu oyoyo. Ta dauke shi tana fadin
“My son ya girma miss you “
“Miss you too Mum! Ina yini?”
“Lafiya lou ya kake?”
“Alhandululah!”
Ta dire shi yayi wajen Dady din sa. Ita kuma tayi ciki. Ta zauna a kasa tana gaisar da Baba da Momy. Suka amsa suna tambayar ya gida.
Suna falo sai ga sallanar Suraiyya nan tana shigowa ta gaida su Momy da Baba suka gaisa da Fauwaz da zai fita. Kamal ya shigo suka gaisa yace
“ashe ka shigo “
“Wallahi yanzu nake son kiran ka ai “
“Gani ai!”
“Ina zuwa to.”
Ya fice yayi dakin da Glotia take.
*
Fateema tace
“Sister ina Dad dina?”
Banza tai mata. Fateema tace
“Au wai fushin ne dan Allah kiyi hakuri wallahi ni bani da lokaci na kaina. Ranar aiki ina wajen aiki weekend Yaya yazo ina zani.”
“Ai ni ina zuwa kullum ina hanyar gidan ki ko?”
“To kiyi hakuri wannan week din zanzo shikenan.”
“Bana so.”
Momy tace
“Ai Faterma ban san me yake damunta bata son zumunci wallahi. Ina jin tinda kikai aure ma kinje gidan Hajiyar Fu’ad kuwa?”
“Momy kinsan aikin nan fa wallahi shi ke hanani fita tin safe sai yamma na dawo na gaji weekend kuma kinga Yaya ya dawo ya zan fita na barshi. Hajiya naje ranar da zamu bar garin nan.”
“Ahab tin kina amarya kenan ita kuma Suraiyyan fa?”
“Sau daya tazo Momy.”
“Allah shurya ki.”
Momy ta mike ta fita. Fateema tace
“Kinji dadi banza!”
“Naji!”
“Kuma ma na fasa zuwa.”
“Kada kizo din!”
Ta mike tayi ciki. Suraiyya ta mike tabi bayan ta tana fadin
“Zo kiji yar uwa.”
Dakin ta ta shiga ta fada kan gado tana fadin
“Nayi kewar daki na fa.”
“To dauke ki, ki tafi gida dashi.”
“Ai wallahi da ana dauka da na dauka.”
Tai murnushi tace
“Banza wani abu nasamo mana fa”
“Yana ina?”
“Sai kinzo zaki amsa.”
Fateema ta mike tana fadin
“Baki niyyar bani ba ai da kinsan gida na.”
“Naji sai dai kinzo.”
“Ai zan shigo ko monday in Allah ya kaimu.”
“Allah kaimu.”
Fateema tace
“Yaya fa yace tare suke da matar sa ko zamu shiga mu gaisa.”
“Ba inda zani wannan matar tasa wata banza da ita.”
“Me tai miki?”
“Kawai batai min ba kuma ina taya ki kishi.”
“Tab ai kuwa ni bata gaba na dan Allah tashi muje.”
Ta kamo hannun ta suka mike suka fita. dakin da take suka shiga suka samu ba kowa a falo duk da Gloria taji su taki ta fito tai zaman ta. sun jima suka mike suka tafi dan suna zaton ko bacci take
Story continues below
Ta window ta lake ta kalle su. Ji tayi kamar zuciyar ta zata buga bata kaunar Fateema bata burin ta gan ta kwata kwata a rayu. Da zata iya data shake ta ta mutu kowa ya huta ma.
Daga nan gidan Uncle Aminu suka je sai magariba ma suka koma gida.
*
Sai dare su Kamal suka dawo. Abinci suka ci sannan Yaa Fauwaz ya nufi bangaren Gloria. Tana kwance a falo tana kallo ya shiga ta dauke kai. Zama yayi yace
“Ni zan tafi sai da safe ba wata matsala ko?”
Ko kallon sa batai ba ya mike ya fita ta buga tsaki tana cije lebe. Ciki ya koma sukai wa Momy da Baba sallama duk suka debe matan su duk suka tafi tare suka bar Momy da Annur.
Washe gari ba inda suka je a gida suka yi suna shan soyayyar su. Kwance take kan ta akan cinyar sa yana wasa da gashin kan ta. Sanye take da vest fara tas sai three quarter wando red. Kan fa ya sha gyara. Shima daga gajeran wando sai singlet ne a jikin sa. Hannun sa ya dauke daga kan ta ya daura a kan kirjin ta yana latsawa. Sai yace
“Honey Bae tashi na duba ki!”
“Me nayi zaka dubani?”
“Wani abu zan gani.”
Ta mike zaune ya zuba mata ido sai ya kamo hannun ta ya matsa kuwa da ita ya bude idon ta yana gani. Hannu ya daura akan marar ta yace
“When last rabon ki da period?”
Kai ta daga alamar tunani yace
“Ya kamata yazo tin on 12 but yau 18 bai zo ba bayan yana miki reducing two days since last month kinyi on 14 wannan on 12 but bai zo ba me kika gane?”
Jikin sa ta kwanta tace
“Jin kiri kila yayi kasan abun!”
“Tin da mukai aure bai taba jinkiri ba.”
“Kai ne dai baka sani ba Yaya!”
“Aah fa Baby!”
Dariya tayi tace
“Wai kana zaton ko ina da ciki. Ba wani ciki Yaya fa.”
“Gobe zamu asibiti na duba ki!”
Ta saka hannu ta wuyan sa tace
Yaya kenan sai kace baka taba haihuwa ba kana son yara!”
“Hmm ina son naga Baby na from you ne. A yanzu ban da buri da ya wuce naga kin haifa min Baby na dauke shi wallahi Honey Bae wannan shine kadai burin da nake da shi. Sai na in cigaba da faran ta miki da baki duk abinda kike so!”
“Yaya ai kana faran ta min duk abinda nake so kake min. Zan taya ka addu’a Allah ya bani Baby”
“Da kin ga mai min komai a duniya. Fatana na ganni dauke da Babyn ki. Allah ya bami me kama dake Baby girl!”
“Ni na fison Boy me kama da kai!”
Yaja hancin ta yana fadin
“Bari to mu zuba muga wanne zamu samu?”
Ta kwanta a jikin sa tana dariya. Ya dago ta yana fadin
“In yayi kama dani zan baki kyau kema haka.”
“Naji!”
Ya dago kanta yace
“I love you Honey Bae.”
“Love you More Yaya!”
Ya hade bakin su yana bata wani hot kiss. Dagowa yayi yace
“Au na manta ban fada miki ba.”
“Me?”
“Na sa an min transfer to one of our branch in kaduna.”
Ido ta zaro tace
“Da gaske?”
“Yes kinga yanzu muna kusa ko kullum naso naga Baby na zan zo.”
“Ban yadda ba sam kada ka soma Yaya. Kana yin wata.”
“Kinsan wata yai min nisa. Ba zan iya wata ban sha milk and honey din ki ba.”
“sati uku to.”
“Bafa zan iya ba.”
“Uhmm uhmm Yaya biyu gaskiya kada ma kace ba zaka iya ba.”
Murmushi kawai yayi ya rumgume ta yana fadin
“Ni dai ki kyale ni in da nake so ina zuwa duk ranar girkin ki.”
“Allah ban yadda da haka ba in haka ne zan hakura da aiki na in dawo nan kawai.”
“No no ba za ai haka ba.”
“To ka zauna two weeks din!”
“Ya zanyi!”
Ya fada kamar zai kuka. Ta janyo shi jikin ta tana kissing nashi nan ya kara kamkame ta.
*
Ko monday bai so ya tafi ba dan ana neman sa a kadunan ne ya fara shirin tafiya. Gloria yai wa waya kan ta hada kayan ta gashi nan.
Story continues below
Tana kitchen yazo ta bayan ta ya rumgume ta. Tace
“Wai ka tashi?”
“Uhmm mana. An kirani daga Kaduna!”
“To lafiya?”
Ta fada tana ajiye abun hannun ta ta juyo.
“Am sorry Baby tafiya zanyi yanzu!”
“Hmmm to shine kake ban hakuri Haba Yaya ni baka hanani aiki na ba nice zan hanaka naka.”
“Ai kinga baki zaci tafiyata yau ba.”
Tai murmushi tace
“To muje dai yanzu kai wanka kan nazo nai sauri na karasa hada maka break ko?”
Rumgume ta yayi yace
“Kiyi komai a sannu Baby aibyanzu safiyar tayi nan zuwa one ma zan iya tafiya.”
“Muje to kayi wankan ko?”
Ta kama hannun sa sukai ciki ta hada masa ruwa ya shiga ita kuma ta koma ta cigaba da abunda take yi.
Tana gamawa ta jere ta wanke abunda da ta taba ta koma daki. Shiryawa taga yana yi ta shiga tai wanka ta fito ta shirya cikin wata doguwar riga baka ce saman ta an mata da material kirjin kuma duk an cika sa da stone manya da kananu. Kirjin ta ya turo sosai. Tai mata kyau ta saka dan kwali tai rolling kan ta.
Juyowa tayi taga Fauwaz ya zuba mata ido. Turare ta dauka fa shafa ta kafaso tana fadin
“Ya dai Yaya?”
“Ina son ki Fateema.”
“Na sani Yaya.”
“Hmm baki san yawan so da yadda nake jin sa a zuciya ta ba.”
“Hmm to Yaya ai nima ina son ka.”
“Na sani Baby. Amman nawa yafi yawa bana zaton zan iya rayuwa babu ke a yanzu kece rayuwa ta nunfashi na.”
“Ka daina fadar haka Yaya!”
“Hmm saboda me?”
“Kada Alah ya dauke maka ni!”
“Da kuwa mutuwa zanyi.”
“Mutum baya mutuwa lokacin sa bai ba kuma Allah kan iya jarabtar mu ta ko wacce hanya in Allah yai zan mutu ba zaka kashe kan ka ne? Kome zakai kai ka rayu ni kawai ka rage min wannan mugun son Yaya.”
“Honey Bae tayaya zan rage Allah shi ya daura min kuma bana fata ya rage min kuma ina son abu na a haka domin ke din abar so ce.”
“Hmmm nagode da soyayyar ka yaya a baya na zata nayi ban kwana da masoya da farin ciki. Amman ka dawon da wano farin cikin da jin dadin. Ina godiya Yaya Allah barmu tare.”
“Amin! Allah bamu ya’ya masi albarka.”
“Amin muje ka ci abinci kada ka makara ko?”
Ta kama hannun sa suka fita nan ta fara feeding nasa sai da ya koshi ta karasa hada masa kayan sa. Driver ne ya kai su gida suna zuwa suka gaisa da Momy yace mata tafiya zai ana neman da. Tai masa addu’a da fatan alheri. Wajen Gloria yaje ta dauko kayan ta aka saka a mota. Ciki ta shiga taiwa Momy sallama ta fice ba tare da ta kalli Fateema da Annur ke hannun ta ba.
Suna zaune Yaa Fauwaz yace
“To Momy mu xamu tafi.”
“Allah kiyaye ya tsare Fauwaz!”
“Amin!”
Ya mike ya fita fateema tabi bayan sa hannun ta rike da na Annur. Suna karasawa compound ta tsaya a bakin kofa tace
“My son safe journey!”
“Thank you Mum! But Momy ina son zama a wajen ki.”
Fauwaz da ya karaso yace
“Jeka Boy!”
Ya kalli Fateema yace
“Bye!”
Ta daga masa hannu shima ya daga maga. Ya sake ta ya nufi motar su a guje.
Suka bishi da kallo. Fauwaz yace
“Ina tunanin dawowa da Momy Annur!”
“Saboda me?”
“Ina son yaro na ya samu karatun addini sosai Baby bana son ya tashi a inda karatun bai da karfi. So nake yazo nan yayi karatu a inda kukai naga school din suna da kyau.”
“Hakan yayi kyau amman why Momy ni kuma fa?”
“Baki da lokaci ke!”
“Haba Yaya wane bani da lokaci yanzu inda na haifi nawa fa wa zai min ni ka bani shi kawai in zaka kawo shi kaga before zuwan nawa na saba.”
“Hmmm a yanzu abin zai miki yawa ga shirya shi ga aiki!”
“Yaya zan iya.”
“Shikenan ki wa masu makarantar magana duk yadda ake ciki in na dawo sai muji sai na taho dashi kawai.”
Murmushi ta saki tana fadin
“Yauwah nagode Yaya!”
“Zan tafi da son ki da kaunar ki Baby Ki kular min da kanki.”
“Insha Allahu nima ka kular min da kan ka.”
Ya rumgune ta ya dago ta yai kissing goshin ta hancin ta da lips din ta ta lumshe ido ta bude. Ya ja baya yana daga mata hannu itama ta fara daga masa tana fadin
“Allah kaiku lafiya ya dawo daku lafiya. Allah bada sa’a ya kiyaye.”
“Amin Honey Bae.”
Ya fada ya juya ya shiga bayan mota yana daga mata hannu har suka fita gate shi da Annur na daga mata hannu itama tana daga masa tana murmushi sannan ta juya ta koma ciki.
Suna sauka ya kira ta tai ta murna suka dan taba hira sannan ya tafi meeting din da zasuyi.
Sai dare aka mai da ita gida tana komawa wanka kawai tayi ta haye gado sai taji duk kewar Fauwaz bata taba jin kewar sa kamar ta yau ba. Ta janyo pillow ta rumgume amman sai taji wani iri. So take kwai ta ji ta a jikin sa kamar yadda yake mata.
Wayar tace ta fara kara ta janyo jiki a sanyaye ta dauka
“Honey Bae!”
“Na’am Yaya!”
“Shine baki neman ba”
“Yanzu na dawo Yaya kuma ban sani ba ko kuna tare da matar ka!”
“Shine me?”
“A’ah ba dadi kuna tare ai na kira ko?”
“Kema fa matata ce.”
“Amman Yaya ni bazan ji dadin muna tare kaga nima kwarai nai hakan ko?”
“Uhmm baki dai damu dani bane.”
“Haba dai ni kuwa ni na damu dakai Yaya.”
“Uhmm gani na kasa bacci ina kewar ki da jikin ki mai taushi. Na ja duk pillown dake kan gado na amman na kasa samun wanda zai maye min gurbin ki. Baby ina matuwar kewar ki da kaunar ki ina ma da na rufe ido na ganni a kusa dake da yau bazaki bacci ba.”
“Yaya abinda nake fama kenan nafi awa da kwanciyya na kasa bacci sai juyi nake. Ina son ka Yaya ina kewar ka. Kayi hakuri nan da kwana ki zamu kasance sai mu kwana idon mu biyu muna shan soyayyar mu.”
“Allah nuna mana Baby. Ban taba jin kewar ki kamar yadda nake ji a yau ba duk da a da ma ina ji amman ta yau daban ce. Ina kaunar ki Baby.”
“Nima haka Yaya gaba daya jikina kai yake bukata da marari. Ya aikin kuwa?”
“Alhamdulilah mai asibitin ne ya zo yau mukai meeting zai yi tafiya na tsawon wata biyu ya bani gaba daya asibitin na kula dashi aiki ya dadar min Baby komai yana kaina ni zan kula da duk staff ga aikina kuma.”
“Masha Allah. Ya yadda dakai ne tinda kaga haka. Ni dai fatana Allah ya bada sa’a ya taimaka. Ka kula sosai Yaya.”
“Nagode Baby!”
Nan suka cigaba da faran tawa junan su har bacci ya fara debar su lokacin daya da wani abu wannan yasa sukai sallama da junan su. Bacci mai dadi ya dauke su
*
*
*
Zaune yake a lambu kamar yadda ta saba ganin sa sanye da wata farar shadda yai kyau. Ya kara haske yai kiba fuska sa dauke da murmushi.
Karasawa wajen sa tayivtace
“Fu’ad me sona!”
Juyowa yayi yana ganin ita ce ya fara lafiya. Kallon sa ta tsaya yi sai kuma tace
“My please ka tsaya kaji!”
Juyowa yayi ya tsaya tana gab da karasowa ya juya ya fara tafiya tana bin sa amman kan ta cimmasa ya shige wata kofa.
*
*
*
Da salati ta mike tana bin dakin da kallo. Kai ta kife tana sakin wani kuka wanda ita kadai tasan na menene.
A da ta daina mafarkin Fu’ad amman yau ya dawo mata ta jima batai ba. Amman yau tayi me kenan. Meyasa tazo mata meyasa baya bari tai masa magana meyasa.
Ta cigaba da kuka ita kadai. Tana tsaka da kuka taji an tada sallah a masallaci. Jiki a sanyeye ta dire kafar ta ta nufi bandaki tai wanka ta dauro alwala ta fito ta saka kaya ta hau kan sallaya sallah tayi. Bayan ta idar ta jima tana addu’a ga iyayen ta mijin ta Fauwaz da yan uwa musulmai. Ta jima tanawa Fu’ad addu’a Allah dawo dashi.
Bayan ta idar da addu’a ta yi karatun alkur’ani tayi azhkar sai shida da rabi ta tashi ta fara gyara gidan. Duk aikin da take jikin ta a mace. Zata fita a dakin taji wayar ta na kara. Komawa tayi ta dauka