WA NAKE SO CHAPTER 25

 WA NAKE SO CHAPTER 25

              Www.bankinhausanovels.com.ng 

Hannu ta daura akan cikin ta,  ta dago tana fadin

“Yaya da gaske ciki ne dani?”+

Kai ya gyada mata. Hawaye ne ya zubo a idon ta na daya na farin ciki itama zata zama uwa, na biyu zata haifawa Fauwaz Baby, na uku na tinawa da Fu’ad. Yau inda Fu’ad ne ya zai ji. Dan Bata San shi da Fauwaz Wanda yafi son Ya’ya ba. Kuma kila wannan rabon shi ya raba ta da Fu’ad.

Dago ta Fauwaz yayi yace

“Ki daina kukan Nan.”

Shesheka ta fara. Yace

“Baby menene ko akwai wani abun?”

“Yaya Nima Zan cika maka buri na Haifa maka Baby.”

“Allah ya rabaku lafiya Allah yai miki albarka.”

“Amin Amin! Yaya nah.”

Yai kissing lips din ta. Daga Nan suka wuce gida.

Daren ranar kwana sukai suna Shan soyayyar. Wanda Fateema har tsoro Fauwaz ya dinga bata. Yadda yake Mata kamar bai taba sanin ta ba. Sunbatu da kuka gashi kamar zai maida ta cikin. Har goshin asuba suna Abu daya sai da yaga ta galabaita ya sarara mata ai kuwa ko Alwala batai ba bare wanka Bacci ya dauke ta.

Fauwaz kuwa da yai wanka dawowa yai ya Kura Mata Ido. Addu’a yai Mata ya koma kan sallaya. Kwana yayi akan sallaya. Dan da aka kira assalatu ma shi ya tashe ta ya taimaka Mata Tai wanka ya tafi. Tana idar ta dawo ta kwanta.

Shima Sai da ya dawo ya koma yai bacci. Karfe takwas ta tashi da sauri ta shiga kitchen ta fara hada Hadar daura abincin safe.

Karfe goma ta Gama Tai wanka ta shirya cikin atamfa Mai kyau. Tai dauri ta Kara Yin kyau.

Tana gaban mirrow ya karaso ta juya tana kallon sa cikin Shirin sa na manyan Kaya. Yai Mata kyan da bai taba Mata irin shi ba.

Murmushi tayi ta karasa tana fadin

“Yaya na ka ganka kuwa kamar sabon ango yau kayi wani kyau na daban.”

“Angon kine Baby. Yadda kike ko da yaushe sabuwa ce a waje na haka yasa nake zaton kamar kullum a leda nake bare ki.”

Ya kamo hannun ta Yana fadin

“Dan Allah menene sirrin? Kullum a sabuwa nake Jin ki tamkar a lokacin nake Kara sanin ki with a special test Baby.”

Hannu ta daura akan bakin sa tana fadin

“Yaya kana ban kunya.”

Ta fada tana juyawa baya. Ya daura kan sa a kafadar ta yana fadin

“Wai kunya yau ni ake Jin kunya Baby.”

“Kai Yaya ai kullum Ina Jin kunyar ka.”

Ya juyo da ita yace

“Da gaske?”

Dagowa tayi ta Harare shi tace

“Ni kake tambaya.”

Kan gado ya zauna yace

“Haka ne fa. Na Tina Baby na akwai kunya wanda ita ke Kara Miki kyau. Ina kaunar ki Baby da sonki zan mutu.”

Ya daura hannun sa a kan cikin ta yace

“Ina kaunar ka Baby na. Ina ma Zan kasance dakai da na nuna maka so da kauna.”

“Me zai hanaka kasancewa dashi.”

Janyo ta jikin sa yayi ya hade bakin su. Wani kalar kiss ya fara bata wanda bai tabai mata shi ba. Nan da nan ya kashe mata jikin ta.

STORY CONTINUES BELOW

Ta shiga maida Masa da martani.  Nan suka jiyar da Junan su wani dadi. Sai da ta farai Masa kukan yunwa ya kyale ta. Wanka sukai Bata saka komai ba da towel ta fita falo ta hado tea. Shi tasha sannan ta mike Sai ga Yaa Fauwaz Nan ya shigo sanye da kayan sa daban ba Wanda ya cire ba.

“Ina Zaki?”

“Kaya Zan saka!”

Ya kamo ta ya yo dining ya zauna ya daura ta akan cinya abinci ya fara Bata tana ci Shima Yana ci. Yana gamawa ya dauke ta sukai daki.

Akan gado ya ajiye ta ya dauko Mai ya fara shafa mata. Baya ta juya ya lakata Amman sai ya mike da aika Mata da wani Abu ta Bayan ta.

Nan ta fara Mika Dan yadda sakon ke shigar ta. Nan ta shige jikin sa. Haka suka Kara samun nutsuwa sai da suka nutsu suka Shiga Dan suyi wanka.

Suna fitowa ta tsaya a gaban Mirrow zata shafa Mai. Ya fito Yana aika Mata da wani kallo. Kallon sa tayi tace

“Yaya Wai wannan fitinar dake idon ka ta Taki ta kyale ka.”

“Na kasa samun gamsuwa dake ne. Mararin ki nake. Bana son na takura Miki ko Dan unborn Baby na.”

Tai murmushi tace

“Yaya kenan am all yours ko kana son na daga tafiyar ne?”

“No no no ba za ai haka ba zamu tafi zuwa anjima.”

“Hmm in da takura Yaya na hakura zuwa wani lokacin.”

“A’ah Baby na. Ki karasa Shirin ki zuwa Sha biyu zamu daga.”

“Toh!”

“Ko na shafa Miki man ne?”

Ya fada yana kanne mata ido daya.

Tace

“Hmm in kana so.”

“A’ah Kar Baby na yace Dady ya fiya takura.”

Tai murmushi ya shafa Mai ya shirya ya fita. Yana fita yaga Gloria ta taho daga parking space tana Kad’e hannayen ta.

Kallon ta ya tsaya har tazo wucewa ta sashen Fateema ta dago sai sukai Ido hudu da Fauwaz da sauri ta nufi sashen ta tana zuwa ta shige kitchen ta wanke hannun ta.

Bayan ta ya biyo yana shiga ya tsaya kallon dakin. Annur ne ya fito yana ganin Dady ya zo ya gaishe shi yace

“Dady Ina Mum?”

“Tana daki!”

“Dady naje na gaishe ta?”

“Jeka.”

Ya fita a guje. Yana fita Gloria ta fito tana goge hannun ta da karamin handkachief.

Kallon ta ya tsaya ta fito ta zauna akan kujera. Ya Kara kallon ta sai ya matsa Yana kallon ta. Yace

“Me Kika fita kikai a parking space!”

“Ban gane ba shikenan ni bazan fita ba?”

“A’ah ai Naga bakya fita ne.”

“Yau to na fita shine me?”

Murmushi ya saki Dan ya manta yaushe rabon ta ya bashi amsa kamar haka. Wannan yasa ya ji dadi yace

“Is ok yanzu kin tashi lafiya?”

“Ina ruwan ka?”

“Haba Gloria mijin kine fa Wanda kike so Fauwaz ko na canja Miki ne?”

Kallon sa ta tsaya yi, yace

“Kiyi hakuri in Ina Miki ba dai dai ba Amman ki sani kamar yadda nake son Fateema kema Ina son ki kace fa uwar ‘da na Wanda nafi so haba Gloria kina tausayi na Mana. Kinsan Ina son ki da kinfi mutunci. Please ki dawo kamar da macece Mai hakuri da mutunci da tausayi Amman yanzu kin daina tausayi na fa meyasa?”

Kai tayi kasa dashi yace

“In na Miki ba dai dai ba ki yafe min. Auren Fateema da nayi addinin mu ya yadda Kuma kada ki manta Ina son ta. Na dawo na same ta cikin matsanacin Hali auren ta da nayi ya ceto ta bakya ganin zan samu lada Kuma iyayen ta da nawa sunji Dadi. Fateema na da hankali da hakuri Bata da hayani ko bana Raye ita Mai kula dake da Anjur ce in Kika Bata dama Zaki gane hakan.”

Nan ma shiru tayi  yace

“Ki zo mu zauna zaman lafiya nawa rayuwar duniyar take. In mune gobe ba mu bane. Dan Allah kiyi hakuri kizo mu zauna lafiya Gloria my love.”

STORY CONTINUES BELOW

Kai tayi kasa dashi. Yai murmushi yayi yace

“Any way yau zamu tafi Zan maida Fateema kan na tafi Ina neman yafiyar ki, ki yafen Kinji.”

Batai magana ba ya dago ya kalle ta ya mike ya zaro kudi a aljihu sa ya dire Mata yace

“Sai na dawo.”

Ya juya ya fita. Bangaren Fateema ya Shiga ya dauko akwati Nan ta ya saka a mota sannan ya koma suka fito ya kamo ta suka Shiga Bayan mota. Driver da Annur suna gaba. Driver ya tada motar suka fice. Fauwaz ya fita Yana kallon gidan.

Annur dake gidan gaba yace

“Dady ba da Mom zamu ba?”

“Eh Kai ka koma Kano ma kenan.”

“But Dad banyi sallama da Mom ba.”

“Kwayi waya!”

Fateema ce ta kalle shi tace

“Yaya Bata san tare zamu tafi ba kenan.”

“Kinsan halin ta. Yanzu zata ce Bata yadda ba. Amman yanzu in na dawo na fada mata.”

“Amman Yaya da ka fada Mata ko?’

“Don’t worry komai zai Yi normal na fara ganin canji a tare da ita.”

“Allah yasa.”

Ta kwantar da kanta a jikin kujera ta lumshe Ido. Janyo ta jikin sa yayi ya gyara Mata kwanciyya ta lumshe Ido suna tafe suna Hira har Bacci ya dauke ta.

Har ta farka taji hannun sa a kan cikin ta. Ta Waiwayo tana kallon sa. Tace

“Yaya!”

Kiss yai Mata a goshi Yana fadin

“Ina Jin lafiyar Baby nane!”

Murmushi tayi tace

“Annur Bacci yayi ne?”

“Eh!”

Ta daura hannun ta akan hannun sa tana fadin

“Ni dai Yaya in na Haifa maka Baby nasan shi zaka fi so.”

“Ita dai zan fi so. Amman ba xanfi son ta akan ki ba.”

“Kar kasa na fara kishi da ita fa.”

“Babyn tamu?”

Baki ta turo ya duka yai kissing lips din ta yace

“Ina kaunar ki Baby na.”

“Me too!”

“Allah Miki albarka!”

Tace

“Amin!”

Ya dauko mata maltina ya mika mata yana fadin

“Baki fara jin yunwa bane?”

“Wallahi na fara naga ban dauko komai bane.”

Bari mu shiga Kaduna sai a samar miki wani abu ko?”

“Malt din ma is ok Yaya.”

“No Baby na fa?”

Tai murmushi.

Sha tayi ta koma jikin sa ta lafe kamar me bacci shi kuma yana shafa bayan ta a hankali

*

Sun gauta kaduna driver na sharara gudu yazo wani waje ya hangi wani Rami. Burki yazo ya Danna Amman ya dannan yaki dannuwa suna Shiga Ramin wani karfe ya caki tayar ta fashe take motar tayi ciki daji ta bugi wata bishiya take gaban ta ya kama da wuta duk yan ciki suka sume sakamakon.buguwar da sukai.

Wata mota da tazo wucewa ta hangi motar su Fauwaz na cin wuta. Da sauri suka tsaya suka nufi motar duk a sume suka fito dasu.

Nan aka Kira motar emergency take suka wuce dasu asibitin Kano Dan sun kusa shigowa sosai.

*

**

***

****

*****

******

*******

********

*********

**********

************

Bayan ta kawo Masa ta koma gefen Mamah Yana ci suna Hira. Har ya gama ya kalli Aisha yace

“Mu tafi ko?”

“Ni anan Zan kwana!”

Mamah ya kalla yace

“Mamah Dan Allah haka ake Yi?”

Aisha ta kalla tace

“A’ah Aisha tashi kibi mijin ki sai da safe!”

A hankali ta mike tace

“Sai da safe.”

“Allah bamu alheri.”

Ta fita ya mike yai wa Mamah sallama ya fita. A hanya ya same ta ya karasa yace

“Da ki tsayani.”

“Allah Sweetheart ka daina bani kunya!”

“Me nayi?”

“Gashi Nan.”

Janyo ta jikin sa yayi ya daura kan sa akan kafadar ta yace

“Ko?”

STORY CONTINUES BELOW

Ya zura hannu ya dago ta ya dauke ta. Kafa ta fara wuntsilawa tana fadin

“Ni dai ka sauke ni.”

Bai kula ta ba suka shige bangaren su. Bai ajiye ta a ko Ina ba sai akan gado.

Nan ya fara romancing nata tin tana nokewa har ta bada Kai bori ya hau.

Washe gari da safe suka d’aga. Haka suka koma suka cigaba da soyayyar su tana kula dashi Yana kula da ita.

Satin da suka dawo ta fara wani zazzabi da ciwon Kai sosai abin ya fara damun ta tin tana boyewa Aliyu har ya gane haka ya tada hankali

Yana dawowa ya ganta ta sanye da riga Mai dogon hannu da dogon wando. Saboda yanayin zazzabin da take ji. Yana rumgume ta yaji jikin ta da dumi yace

“Baby love jikin ki zafi fa!”

“Weather ne kawai Sweetheart!”

“A’ah fa yau kwana biyu kina fada min haka fa.”

Tai murmushi ta Kama hannun sa tace

“Kaga muje ka watsa ruwa kada a Kira magariba a Ina ka tsaya yau ma?”

Tayi gaba. Hannun ta ya janyo ya jingina da bango Yana bin ta da kallon sai Kuma ya zura hannun sa a cikin rigar ta yaji zafi.

Daukar ta yayi ya ajiye Akan kujera tare da daukar wayar sa ya fara neman layin Doctor su.

“Please kazo gida yanzu!”

“Ok Sir.”

Ya kalle ta yace

“Me yake damun ki?”

“Ni fa ba komai!”

Ido ya tsare ta dashi tace

“Yaya zazzabi ne fa kawai.”

“Meyasa Kika boyan!”

“Bana son ka damu me.”

“Kinsan rashin sanin ai zai fisa na damu ko?”

“Kayi hakuri love Amman ya ma fa daina na Sha paracetamol. Kasan me?”

“A’ah.”

“Gobe Mujahida zata zo fa.”

“Ah haba lallai kina da bakuwa gobe.”

“Muna da ita dai Kuma ma ai Mujahida ba bakuwa bace Yar gida ce.”

Hancin ta yaja yace

“Ya kike ji yanzu?”

“Yaya ni fa normal.”

“Ba wani normal kalli fa yadda Kika fada Amman shine Baki fadan ba nake takura Miki ko?”

“Kai Baby ai Zan iya mn.”

“Ni dai kada ki Kara.”

Kunne ta kama tace

“Insha Allah. Muje kai wankan ko?”

“No sai yazo ya duban ke. Kila ma yawan aikin da kike Yi ne.”

“Ba ruwan aiki Yaya.”

“Bari yazo Allah in yawan aiki ne kin daina.”

Kiran sallah magariba Yasa ya mike yai Alwala itama tayi sannan ya tafi masallaci.

Tare suka dawo da Dr. Ya Shiga ya Kira ta, ta fito Sanya da hijab har kasa. A kan two sitter suka zauna ya farai Mata tambayoyi ta bashi amsa. Jinin ta ya dauka yace zai je ya dawo.

Bayan isha’i Aliyu na dining Yana cin abinci Aisha na Shan hadin da tayi na Zuma da Aya da Madara tana Sha Dr ya dawo. Hijab ta saka ya shigo. Falo suka koma ya zauna Yana murmushi yace

“Congratulations Sir your wife is pregnant!”

Ido ya zaro yace

“What?”

Kai ya gyada yace

“Yes!”

Juyawa yayi Ya rumgume ta Yana fadin

“Alhamdulillah Alhamdulillah Alhamdulillah Allah nagode maka Allah ka bani yara na gari masu albarka.”

Ya mike yai sama ya dawo da check na kudi masu yawa ya Mika Masa yace

“Nagode Doctor yanzu ka Bata magani zazzabin nan na damun ta sannan me kake ganin zata daina aikin nan bai daga cikin ciwon nan kuwa.”

“Kai Sweetheart Dan Allah.”

Ta kalli Doctor tace

“Wai Dan aikin gida ne Shima fa dakin mu kadai nake sharewa sai girki Amman ba abinda nake komai yi ake ya hana ni “

Yai murmushi yace

“Ba matsala wannan akai stage din da in taje za ana cewa tana motsa jikin ta ma. Zan Bata magani da zai Kara Mata jini da lafiya. Allah ya inganta.”

“Amin!”

Ya Kama hannun ta Yana sakar Mata murmushi. Magani ya Bata ya mike Aliyu yai Masa sallama.

Washe gari kuwa shi yayi komai. Break ma hanata hadawa tayi sai lallabata yake kamar kwai. Da Rana Sai ga Mujahida nan Aisha tai ta murna ta cika Mata gaba da kayan motsa Baki bayan ta gama ta Kai ta dakin da zata zauna.

Suna zaune kan yamma zazzabi Mai zafi ya rufe Aisha. A haka Aliyu ya dawo ya same ta hankalin sa ya tashi Nan ya Kira Dr ya fada Masa. Dr yace ba wata matsala a sannu zata daina tana Shan maganin da ya Bata.

*

Hajara ta Shiga tashin hankali Dan da ta je gida wajen su Momy ma a falo suka shanya ta Basu fito ba daga baya suka aiko ace Mata ba zata samu damar ganin su ba.

Washe gari da ta zo shine ta samu Sha’awa zata tafi gidan Aisha kamar yadda suka shirya ita da Momy dan su fara aikin su na bata maganin hana daukar ciki.

Wani kallon suka bita dashi. Hajara ta zauna tana fadin

“Ina Kuma Zaki?”

“Gidan Yaa Aliyu!”

“Wanne Yaya Aliyun?”

“Wannen kika sani tsohon mijin ki.”

“Me zakije kiyi? Na zata zaki tayani kishi.”

“Ni da gidan wana!”

“Haba Sha’awa gidan Aliyu wajen Aisha fa kenan ke da kike tayani kishi.”

Wata Dariya tayi tace

“Wa ya fada miki tayaki kishi nake. Ina kishin dai dake da Aishan!”

“Kamar ya?”

Ta Kuma sakin wata dariyar tace

“Ke bari na fito Miki a mutum ni bana son ki wallahi Sam. Ina tare dake ne kawai dan na rabaki da Aliyu Kuma Alhamdulillah cikin sauki kin rabu dan haka yanzu zanje na raba Aisha dashi kamar yadda na rabaki dashi. Dan haka ina son na fada miki kada ki Kara shigo nana nan dan ba gidan ku bane.”

Ta juya ta kalli Momy tace

“Na tafi.”

Ta fita ta bar Hajara tsaye ta kasa tunanin komai ma.

*

Suna zaune a falo da kyar ta sa Aliyu ya tafi aiki. Wanda take kwance Mujahida na kitchen tana soya Mata wainar fulawa. Wayar Mujahida ce tai Kara tana dubawa taga Shu’aibu dauka tayi yace

“Ina waje fa.”

“Gani nan to.”

Ta fito da plate ta ajiye Mata tace

“Bari na canja Kaya Shu’aibu yazo Yana Waje.”

“Oh ba zai shigo ba.”

Ta fada tana cin wainar.

“Zai shigo man bari naje Kar na shanya shi a Waje.”

Tayi dakin ta. Bata jima ba ta fito. Twce

“Bari naje.”

“Kice Dan Allah ya shigo.”

“To.”

Ta fita. A bakin kofa suka hadu da Sha’awa zata shigo da kallo ta bita. Wani kallon banza Sha’awa ta sakar mata. Ta bangaje Mujahida

Ido ta zaro tace

“Ikon Allah.”

Ciki ta shige. Ta bita da kallon Mamaki to me ya kawo Mujahida gidan.

Gate ta ji an bude ta kalla taga Yaya Aliyu ne. Shu’aibu ne ya Karasa ya fito yace

“Ah yau Kaine a gidan?”

“Wallahi nazo wajen Mujahida.”

“Au bama gun Baby love ba ko?”

“A’ah Yaya har ita.”

Yai murmushi yace

“Shikenan!”

Ya karaso wajen Mujahida yace

“Menene tsakanin ku ne?”

“Kai Yaya zumunci kawai!”

“Kema fada.”

Yai ciki. Aisha na cikin cin waina taji sallamar Sha’awa. A tsorace ta dago tana amsa sallamar.

Murmushi Sha’awa ta saki tace

“A’ah Antyn mu ya naga kamar bakya murna da zuwa na.”

“A’ah sannu da zuwa Bismillah!”

Ta zauna tana fadin

“Ya hanya?”

“Alhamdulillah!”

Ta mike tana fadin bari na kawo miki lemo da ruwa.

Tayi firij ta dauko mata ta ajiye Akan tray da cup tazo a ajiye Mata.

Zata koma ta zauna taji sallamar Aliyu da sauri ta dago tana amasawa.

Aliyu tsaye ya bude Mata hannu. Da sauri ta karasa ta fada jikin sa. Ya rufe hannun Yana kissing wuyan ta.

Sha’awa dake kallon su taji kamar zuciyar ta zata buga. Daukar ta yayi ya karasa dakin ya dire Akan kujera yana fadin

“Sha’awa dake kallon su taji kamar zuciyar ta zata buga. Daukar ta yayi ya karasa dakin ya dire Akan kujera Yana fadin

“Me kike ci?”

Ya dauko plate din. Tace

“Wai Sweetheart har ma yaushe ka fita.”

“Tunanin ki ya hanani na sake dole na dawo naji dumin jikin ki naji ya ajiya ta take?”

Hancin sa ta ja tana fadin

“Kai Love!”

Ya ajiye plate din ya fara kissing nata. Gyaran murya Sha’awa tayi da sauri suka dago suna kallon Sha’awa.

Fuskar Aliyu ya Bata. Ta saki murmushi tace

“Ina yini Yaya?”

“Lafiya kece yau a gidan?”

“Wallahi nace Bari nazo na gaida Antyn mu.”

“Kin kyauta!”

Ya mike Yana kamo hannun Aisha. Plate din ta dauka sukai sama. A bedroom suka zauna ta fara cin wainar.

Ya zauna Yana kallon ta yace

“Menene wannan?”

“Waina zaka ci ne?”

“A’ah a’ah ai sai ku.”

“To shikenan ka bar Dadi.”

“Wai me ya kawo Sha’awa ne?”

“Nima ban sani ba Bakaji me tace ba?”

“Ni dai bana son ki yadda ta shige Miki.”

“Haba Yaya Yar uwar kace fa.”

“Duk da haka.”

“Naji to.”

Sai ta ajiye plate din tana bata fuska tare da daura hannu akan kirjin ta yace

“Ah lafiya?”

Da sauri ta mike tayi bandaki kan ta karasa ta fara shara amai. Nan ya bi Bayan ta ya kamata Yana Mata sannu. Bandaki ya kai ta ya gyara jikin ta ya cire Mata kayan jikin ta. Kan gado ya kawo ta ta kwanta ta lulluba da bargo saboda zazzabin da take ji.

Shi ya gyara wajen ya dauko Mata Kaya ya saka Mata. Nan wani Aman ya Kara zuwar Mata. Kan ta Kara tashi ta Kara sakin wani Aman. Sai da tayi Aman fin sau uku duk hankalin Aliyu ya tashi.

Ya Kira Doctor yace gashi Nan. Bai jima ba ya zo har dakin ya kawo shi. Yace

“Me taci?”

“Gashi Nan yana da matsala ko?”

Wainar ya kalla yace

“A’ah kawai tambaya nayi.”

“Ok yanzu ya za ayi sai amai take.”

“Bari ai Mata allura ko?”

“To!”

Ya fada ya karasa wajen Aisha tace

“Baby love ayi allurar?”

Kai ta gyada tana rawar sanyi. Ya dago ta ya daga rigar ta ya zame zanin jikin ta ya soka Mata allurar ta shige jikin sa tana sakin Yar Kara. Ya fara mulmulawa Yana Mata sannu.

“Zazzabin fa Doctor!”

“Tasha Paracetamol ya Isa ma.”

“Ba wani Abu da za a Kara?”

“Kar ka damu zai sauka. Na sauyin da ta samu ne.”

“Ok shikenan!”

“Allah Kara sauki.”

Ya fita. Sannu ya dingai Mata. Sunyi minti ashirin sannan zazzabin ya sake ta. Sai gashi ta mike tana fadin

“Yaya muje kaci abinci.”

“No Love kwanta ni bana Jin yunwa.”

“Haba dai me kaci.”

“Kawai.”

Ya Mai da ta ya kwantar. Aisha ta ce

“Ni Yaya muje please!”

STORY CONTINUES BELOW

*

Mujahida da Shu’aibu ne suka shigo. Ya kalli falon tace

“Bismillah.”

Ya koma ya zauna. Ta harari Sha’awa tayi sama. Dakin da suke tayi knocking. Aliyu yace

“shigo.”

Shigowa tayi ta kalli Aisha tace

“Ah lafiya?”

“Wallahi sai amai take yanzu Dr yai Mata allura ma kuma zazzabi ne a jikin ta.”

“Ayyah sannu Antyn mu. Daman Shu’aibu ya shigo ku gaisa.”

Da sauri ta dire kafa a kasa tana fadin

“Haba Bari naje.”

Kamo hannun ta yayi Mujahida ta fita yace

“Kiyi a hankali.”

Kai ta langabar ya mike ya Kama hannun ta. Suka sauka.

A kasa suka same su har Sha’awa. Aisha tace

“Lah mun barki nan ko. Please Mujahida nuna Mata dayan dakin da ke kusa da naki sai ta zauna.”

“Ok Antyn mu!”

Ta kalli Sha’awa tace

“Muje!”

Ta mike suka tafi Aisha tace

“Ki watsa ruwa sai kizo ki ci abinci.”

“Ok!”

Tayi ciki. Suna shiga Aisha ta kalli Shu’aibu tace

“Yaya nayi fushi.”

“Am sorry Kanwata yaushe na dawo dududu.”

“Ni ba wani Nan zuwan Mujahida ya kawo ka.”

Mujahida na kai ta dakin tace

“Ni ban San me ya kawo ki gidan Yaya ba Allah dai ya tsare Mana Antynmu.”

Tana fada ta fita

*

A falo suka zauna suna Hira. Sai yamma sannan Shu’aibu ya tafi yacewa Mujahida zai dawo da dare.

Lokacin da zasuyi sallah magariba tana Alwala ta tado da zazzabin ta. Dan da kyar Tai sallah ta haye kan gado ta rufa da bargo. Har akai isha’i tana kwance

Sai da ya dawo yaga Bata falo sai Sha’awa. Tana ganin sa ta mike tana gyara riga tare da turo kirji shi ko Lura da itama bai ba. Ya nufi stair tace

“Yaya?”

Juyowa yayi tace

“Sannu da zuwa.”

“Yauwah!”

Kawai ya fada yai sama. Ta koma ta zauna tana tsaki. Mujahida da ta fito daga dakin ta saki Dariya tana fadin

“Iska na wahal da me kayan Kara. Wallahi Yaa Aliyu yafi karfin ki nidai nasan ba zuwan Allah kikai ba.”

Wani kallon ta wurga Mata Tai sama.

Aliyu na Shiga ya same ta kwance Akan gado Nan ya Isa da sauri. Yana  bude ta.

Jan bargon tayi tana kuka yace

“Zazzabin ne?”

Kai ta gyada ya dafa kanta yace

“Sannu Baby love.”

Kai ta gyada. Yace

“Me Zaki ci kan Kisha magani?”

“Ni Fura nake so!”

Knocking akai Aliyu yace

“Waye shigo!”

Mujahida ce ta shigo ta ce

“Ah lafiya Kuma?”

“Wallahi zazzabin ne ya dawo!”

Ya fada kamar zai kuka!

“Ayyah sannu Antyn mu!”

Kai ta gyada yace

“Please Mujahida samo mata fura ta Sha.”

Ta amsa masa ta fita. Kitchen ta shiga ta debo mata a wacce aka dama Masa. Tayi sama amsa yayi ya Bata tana gamawa ya balli magani ya Bata

*

Tana Sha ta dafe kirji. Yace

“Lafiya!”

“Amai nakeji.”

Janyo ta yayi jikin sa Yana shafa bayan ta a hankali.

Aman ne ya yunkuro ta janye jikin ta da sauri tayi bandaki a guje.

*

Nan ta hau kelayashi. Yabi bayan ta yana shafa Bayan ta gama ya dauraye Mata Baki sannan ya dauko ta ya ajiye ta akan gado. Bandakin ya shiga ya gyara sannan ya dawo ya kamo hannun ta yace

“Me Zaki ci to?”

Kai ta girgiza yace

“Haba dai ba abinda kikaci fa tin Rana.”

“Ni bana Jin yunwa.”

“Sannu to. Ba abinda kike Sha’awa.”

STORY CONTINUES BELOW

Kai ta gyada. Take Bacci Kuma ya dauke ta. Yana zaune a wajen Yana ta kallon ta. Mamah ce ta Kira suka gaisa ta tambayi Aisha. Kallon ta yayi yace

“Mamah Aisha Bata da lafiya yau sai amai take Yi komai taci.”

“Subhanallah Jikin ne?”

“Eh!”

“To gobe Zan zo na duba ta. Allah Bata lafiya.”

“Amin.”

“Tana Ina?”

“Bacci take!”

“Ok ai Mata sannu!”

“Zataji.”

Ya kashe wayar. Mikewa yayi ya Shiga Tai wanka ya fito ya saka kayan baccin sa. Zaune ya same ta ya karaso yace

“Kin tashi Baby love?”

Kai ta gyada ta ce

“Yaya me kaci?”

“Ba komai!”

Kafar ta, ta saukar tace

“Bari na kawo maka abinci!”

Kamo hannun ta yayi yace

“A’ah Yi zaman ki Bari Zan dauko fura.”

“A’ah Yaya baka ci komai bafa tin dazu Kadan kaci abincin!”

“Barshi Zan dauko.”

“Dan Allah ka Bari na kawo maka.”

Sakin ta yayi yace

“Ki kula!”

Ta gyada kai. Tana sauka taga Sha’awa ta zubowa stair kallo. Kai ta dauke tace

“Kina zaune na barki ke kadai ko?”

“Wallahi fa.”

“Wallahi zazzabi ya kwantar Dani Ina Mujahidar ai da kunyi Hira.”

“Ta fita ne!”

“Ok kinci abinci to.”

“Eh naci!”

“Ba abinda kike bukata?”

Kai ta gyada. Ta wuce kitchen ta daukar wa Aliyu abinci sa ta fito tai Sama. Akan carpet ta ajiye ta zuba Masa. Sai da yaci sannan ta mike tayi Alwala tai sallah.

Lafiya suka kwana Amman da safe ko kitchen bata samu ta leka taga me ake girkawa ba saboda zazzabi. Aliyu na kanta a tsaye duk ya rasa Yaya zai Yi. Ya Kira likita yazo ya saka Mata ruwa ya tafi.

Karfe Sha biyu ya zare Mata ta tashi a Bacci ruwa ya hada mata Ttai wanka sannan ta zauna ya kawo Mata tea da dankalin da aka soya. Dan kalin kawai taci ta Sha magani. Nan taji zuciyar ta, ta fara tashi ta Bata fuska yace

“Menene?”

Kai ta girgiza sai ta daura hannun ta akan bakin ta, ta mike a guje tayi Bayi. Kai ya girgiza ya mike yabi bayanta. Amai take ta shararawa. Bayan ta gama ya wanke bakin ta ya dawo da ita ya gyara wajen.

Dr ya Kira yana dauka yace

“Am sorry Dr wallahi Aman nan yaki ya tsaya da taci Abu fa Sai ta dawo dashi.”

“Ikon Allah.”

“Wallahi.”

“Aman ne sai a sannu zai lafa Amman zan zo ko allura ce ai Mata ko?”

“Dan Allah kazo.”

“To gani Nan.”

Kofa sukaji ana Knocking ya mike zai bude tace

“Yaya Bari na bude.”

“Haba Baby love Yi zaman ki.”

Ya mike ya bude kofa Yana budewa yaga Mamah da sauri ya matsa Yana fadin

“Sannu da zuwa Mamah!”

Ciki kawai ta shige tana fadin

“Yauwah Ina Aisha?”

Aisha na Jin sallamar ta mike ta dire kafa. Mamah tace

“Yi zaman ki Aisha.”

Ta sauka ta durkusa. Mamah ta karasa ta dago ta. Maryama da Mujahida suka shigo tace

“Ya jikin?”

“Da sauki Mamah. Ina yini? Ya hanya?”

“Alhamdulillah!”

Maryama ta karaso tana fadin

“Allah sarki sister har kin fada kuwa. Sannu ya jikin?”

“Da sauki ya kike ya hanya?”

“Alhamdulillah!”

Ta mike tace

“Bari na kawo muku ruwa ko?”

“A’ah dawo Aisha zamu dauka da kan mu ke da Baki da lafiya.”

“Mamah ai naji sauki.”

STORY CONTINUES BELOW

“Wallahi Mamah haka take yau tin safe fa zazzabi ya rufe ta yanzu ne ma ya suaka tai wanka Shima tana karyawa ta amayar Amman sai tace za tai aiki.”

“A’ah Aisha kina bi a sannu fa.”

“Toh Mamah. Dan Allah ki Bari na kawo muku.”

“Haba Aisha ki zaman ki Dan Allah.”

Mujahida ta sauka ta kawo musu lemo da ruwa da abinci anan suka faraci. Sai da suka Shiga suka watsa ruwa sannan suka fito suka zauna a falon sama har da Aisha dake kwance Akan kujera bayan likita yai Mata addu’a.

Sai yatsina fuska take. Mamah na Lura da ita. Tace

“Yadai Aisha?”

Mikewa tayi Tai daki a guje Aliyu ya bi bayan ta. Amai ta shiga tana yi Yana wanke Mata Baki ta fito ta fada saman gado tana Mai da numfashi.

Aliyu ya fito fuskar sa kamar zai kuka yace

“Sannu Aysherr!”

“Yauwah Yaya!”

Ta fada tana lumshe idon ta. Fita yayi yaje gun Mamah. Mamah tace

“Ya dai?”

“Mamah ni Aman nan na damu na ba wani abinci fa take ci ba.”

Aisha ce ya fito ta koma ta zauna Kai ba kace ita bace taje tai amai.

“Aliyu sai a sannu fa.”

“Yanzu ba wani Abu da za ayi!”

“Hmm Baba na kenan.”

Sha’awa ce ta shigo dakin. Mamah ta bita da kallo. Dan bata San tana gidan ba.

Takaraso tana fadin

“Mamah Ashe kunzo ya hanya?”

“Alhamdulillah!”

“Wallahi Bacci nake sai yanzu na tashi Naga su Maryama a kitchen.”

Ta kalli Aisha tace

“Ya jikin Antyn mu?”

“Da sauki.”

“Allah Kara sauki.”

“Amin!”

Ta kalli Aliyu tana kashe Ido tace

“Yaya Ina kwana?”

“Lafiya!”

Ya fada Ya nufi gun Aisha Yana taba jikin ta. Yace

“Sannu Heartbeat!”

“Yauwah!”

“Baby love me Zaki ci?”

Kai ta girgiza ya kalli Mamah yace

“Mamah me za a Samar Mata taci?”

“Bari naje kitchen din Naga.”

Ta mike ta sauka. Ya dago Aisha ya saka ta a jikin sa. Sha’awa dake zaune ta mike ta bar falon a fusace.

Daki ta Shiga ta dauki waya ta Kira Momy. Tana dauka yace

“Momy kamar fa ciki ne da Aisha yanzu ya zanyi?”

“Ciki Bayan Wanda Hajara ta zubar?”

“Eh wallahi.”

“Ai kawai Kisan yadda zaki zubar dashi!”

“To Momy tayaya?”

“Kije ki samo magani ko a chemist ne.”

“To sai anjima!”

Ta kashe wayar tana zaga dakin. Mamah na Shiga tayi Mata faten wake Wanda ta saka hanta da alayyahu da dankali.

Ta gama ta bawa Maryama ta Kai Mata. Aliyu da kan sa ya amsa zai Bata. Aisha ta girgiza Kai tace

“Yaya amai!”

“Ba zakiyi ba Aisha Kadan Zaki ci.”

Da kyar ya lallaba ya Bata ta fara ci. Ta danyi spoon uku ta dauke kai. Yace

“Dada Mana.”

Spoon daya ta Kara ta dauke Kai. Sai da sukai haka Sai uku sannan ya barta ta kwanta a kirjin sa Yana shafa Bayan ta. A haka har ya lafa Kuma batai aman ba.

Da dare ma kunu Mamah tai Mata tasha. Kwanan Mamah biyu ta koma Bayan taje ta gaida Umma.

Anan ta bar Maryama ta cigaba da kula da Aisha.

Tin da sha’awar taji Aisha na da ciki ta shiga tashin hankali sosai. Sai ta fara tunanin tayaya zatai ta zubar da cikin jikin ta, ta Kuma raba Aliyu da Aisha.

Aisha Kuma sosai Maryama da Mujahida suke kula da ita. Duk da da taci Abu take Aman sa.

Kwance take da safe Akan gadon ta. Bacci take sosai. Sha’awa ce ta shigo dakin ganin tana bacci yasa ta juya tana kallon kofa sai ta matso kusa da gadon tana Kara kallon kofa alamar dai rashin gaskiya.

STORY CONTINUES BELOW

Bakin gadon ta karasa aka budo dakin a tsorace ta juyo tana kallon kofar. Mujahida ce ta shigo hannun ta rike da plate ta soyo wa Aisha plantain. Kallon ta, ta tsaya yi.

Aisha ta bude idon ta tana kallon su. Sha’awa ta wayance tana fadin

“Uhmm Daman na shigo nai Miki sannu ne Naga kina Bacci. Ya jikin?’

“Da sauki!”

Ta juya ta fice ta gefen Mujahida.

Shigowa Mujahida tayi tana bin ta da kallo. Mikewa Aisha tayi tana fadin

“Yaa AK bai Gama training din ba?”

“Bai fito ba.”

“Me kuke dafa Masa.”

“Maryama ce keyi tana kitchen plantain din na kawo miki!”

Amsa tace

“Nagode.”

Ta mike ta shiga bandaki. Wanka tayi sannan ta fito ta shirya.

Aliyu na dakin training din sa aka budo dakin. Shi ya zata ma Aisha ce ya juyo Yana fadin

“Wai har kin tashi?”

Sha’awa ya gani tana sakar Masa murmushi. Fuska ya Bata tace

“Ina kwana Yaya?”

“Lafiya Lou!”

Ya juya ya cigaba da abinda yake. Shiru tayi can tace

“Yaya Daman gani nayi tinda ka saki Hajara me zai Hana ka Kara wani auren!”

Da sauri ya juyo Yana fadin

“What? Ni nace Miki Ina bukatar wata matar ne?”

“No Yaya Amman zama da Mata biyu Yana da fa’ida bama yanzu da Antyn mu ke laulayi dole ka nemi wani Abu ka rasa a wajen ta kaga in kana da wata matar zata taimaka maka.”

Wani kallo ya wurga Mata. Wanda yasa Tasha jinin jikin ta.

Yace

“Na fara Wasa dake ne? Malama get out of my side!”

Jiki na rawa ta fita a dakin.

Plate din plantain din ta dauka ta fita. Dakin training dinsa ta nufa a bakin kofa ta ga Sha’awa ta tsaya kallon ta,  to me ta hau sama take musu Bayan dakin su na a kasa.

Tana ganin ta tace

“Lah kin fito kenan!”

“Eh!”

Ta bude dakin ta shiga da sallama. Juyowa yayi ya sakar mata murmushi tare da amsa sallamar tata ya mike ya karaso Yana fadin

“Kin tashi kenan!”

“Eh Yaya!”

Plate din hannun ta ya amsa Yana fadin

“Yau Kuma shi Zaki ci.”

Kai ta gyada ya zaunar da ita yace

“Tea fa?”

“A’ah!”

“To lemo fa?”

“Yauwah gwara shi a kawon na mixed fruit Yaya!”

“Ai akwai a firij din dakin Nan Bari na kawo miki.”

Ya mike ya dauko Mata lemo da ruwa ya ajiye Mata. Ta ce

“Zo muci.”

Ya dauki plate din yana fadin

“A’ah zo in Baki.”

Ya dauki fork ya fara Bata tana amsa.

Sosai taci sai kuma ta Bata fuska yace

“Menene?”

Hannu ta daura a kirjin ta ya dauko Mata sweet ya Bata ta amsa ta fara Sha sai taji ya lafa Mata tana shanyewa ta karaji Aman na taso Mata. Ba yadda ta iya da gudu ta karasa toilet ta fara Aman.

Yabi bayan ta Yana shafa Bayan ta har ta gama ya dauraye Mata bakin ta. Ya gyara wajen daukar ta yayi sukai dakin su.

Akan gado ya kwantar da ita ya kalle ta cike da damuwa Yana fadin

“Baby love Aman Nan na damu na.”

“Haba Yaya ai ba wani Abu bane.”

“Ni wani Abu ne a guna.”

“Muje na hada maka ruwan wanka ko?”

Komar da ita yayi yace

“A’ah Yi zaman ki.”

Ta bata fuska yace

“Yaya kana hanani abubuwa da yawa na samun Lada.”

“Baby Love ko kallon ki da nake Ina Jin Dadi ma Zaki samu lada. Allah Miki albarka kinji!”

“Amin Yayan mu.”

Yai kissing goshin ta ya mike ya shiga yin wanka. Tana kwance ya fito ta mike ta sauka ta dauki towel ta goge masa jikin sa ta dauko Mai yace

“Baby love bakya gajiya ko?”

“Ina aikin yake?”

“Hmmmm ai ke haka Zaki ce.”

Ta karasa ta saka Masa Kaya tana fadin

“Yaya Dan Allah ka koma aiki yau sati daya fa baka je ba.”

“Ina jinyar matata nane!”

“Ni lafiya ta kalou.”

“Ban yadda ba.”

“Allah please ka koma kaji Yaya.”

“Sai Monday!”

Ido ta zaro yace

“Yaya yau fa Tuesday!”

Ya hade kan su dogon hancin sa Akan nata yace

“Eh Mana!”

“Yaya ka tafi yau.”

“Korata kike Yi ko?”

“A’ah Yaya!”

Ya kamo hannun ta suka fita. A falo suka samu Maryama da Mujahida.

Dining suka nufa. Aisha tace

“Sannun ku da aiki ni dai kun hanani komai ko?”

“Ba ruwan mu Momy ce ai.”

“To ni naji sauki kuma Zan fada Mata.”

“Allah Kara sauki.”

Maryama ta fada tazo zatai serving din Aliyu. Aisha tace

“Ni ki barni nayi kada na sangarce ku tafi ku barni da aiki komai kuyi min ai abin yai yawa.”

Sukai murmushi. Tace

“Kedai kice Zaki serving mijin ki kawai.”

“Naji.”

Ta zuba Masa ta koma ta zauna yace

“Kefa?”

“Na koshi.”

“Dan plantain din da Kika ci?”

“Yaya duk wannan da naci.”

Ta kalli Maryama tace

“Ku zauna ku karya Ina Sha’awan ku kira ta.”

Kan Maryama ta tafi ta fito. Ta karaso dining din ta zauna a gefen Aliyu tana wani kwarkwasa. Ta kalli Aisha tace

“Antyn mu ke me Zaki ci? In dafa Miki.”

“No ni na koshi!”

“A’ah Anty ki Fadi ko menene Zan dafa Miki.”

“Yanzu na koshi anjima ko wanai lokacin naji yunwa Zan fada Miki. Yanzu kuci abinci.”

Aliyu ne ya gama ya mike Aisha ta mike tana fadin

“Yaya zaka je aikin ne?”

Ya kamo hannun ta yace

“Heartbeat!”

Ta fada jikinsa ya janye ta sukai sama. Maryama ta tabo Mujahida sukai Dariya. Mujahida tace

“Yaya da Antyn mu Yan soyayya.”

“Allah barsu tare.”

Tsaki Sha’awa ta saki ta mike tayi ciki. Mujahida ta saki Dariya tana fadin

“Banza.”

Ta fada jikinsa ya janye ta sukai sama. Maryama ta tabo Mujahida sukai Dariya. Mujahida tace
“Yaya da Antyn mu Yan soyayya.”
“Allah barsu tare.”
Tsaki Sha’awa ta saki ta mike tayi ciki. Mujahida ta saki Dariya tana fadin
“Banza.”
Maryama tace
“Bana son tsokana Mujahida.”
“Tsokanar me nayi?”
“Ina ruwan ki da ita harkar ki ta shiga?”
“Hmm nifa ban yadda da zaman ta a gidan Nan ba.”
“Ki kyautata zato please.”
“Ai shikenan!”
Suka debe kayan wajen suka gyara. Sannan suka wanke su. A falo suka zauna suna Shan hirar su.
Aisha da Aliyu kuwa suna daki suna Shan soyayyar su tinda suka hau Basu sauko ba sai da aka Kira azahar kowa ya canja shiga ta rakashi har bakin kofa sannan ta juyo.
Maryama tace
“Antyn mu Yar soyayya.”
Hararar ta tayi tace
“Tashi kuje kuyi sallah me kuka dafa mana?”
“Dambu Mujahida tayi.”
“Ah zamuci Dadi kenan!”
Tayi sama tayi sallah tana idar wa ta sauko ta samu Aliyu zaune a falo shi kadai. Zuwa tayi ta zauna a gefen sa ya janyo ta Yana fadin
“Baby love ya kamata kici abinci fa. Me Zaki  na fada Miki da Kai na.”
“A’ah Mujahida ta Mana dambu Yaya shi nake Sha’awa.”
Daukar ta yayi ya ajiye Akan dining. Dai dai fitowa Sha’awa daga kitchen kenan. Ya dauki plate ya zuba Mata ya zauna Yana Bata. Har Sha’awa ta wuce Basu San ma da ita ba. Tana ci Yana Mata Hira sosai taci ta koshi Shima yaci.
Mikewa tayi dafe da kirji ya janyo ta jikin sa Yana shafa Bayan ta a hankali a hankali. Sai Kuma taji ya fada yace
“Yaya ya fada!”
“Da gaske?”
Ya dago ta Yana tambayar ta.
Kai ta gyada yace
“Alhamdulillah!”
Suka karasa kan kujera ya Jata jikin sa. A haka su Maryama suka fito. Ta janye jikin ta a jikin sa. Dibar abinci sukai suka koma daki dan su barsu su dan sake.
*
Washe gari sai da Ta turasa wajen aiki da kyar ya yadda ya tafi.
Bayan ya tafi su Maryama sun gama abincin Rana suka ce zasu je su gaida Umma.
Aisha tace
“To in kin dawo kwa min wainar fulawa ita nake Sha’awa.”
Sha’awa da ta fito taji tana fadar haka tace
“Ah haba dai Antyn mu har sai sun dawo nima na miki.”
Maryama tace
“Yauwah Anty Sha’awa godiya muke.”
“A’ah nima Anty na ce fa.”
“Haka ne.”
Ita dai Mujahida batai magana ba Amman Bata so ba. Haka suka tafi. Sha’awa ta koma daki ta dauko wani Kullin magani sannan ta fito ta shiga kitchen. Da kyar ta kwaba wainar  dan albasa ma sai masu aiki ta bawa suka yanka mata. Da ta fara suyar sai ta yage Dan ta zuga ruwa.
Sai da ta Kira Momy ta fada Mata yadda zatai sannan ta Kara kwabawa ta zuba garin maganin da ta dauko ta soya. Tana suyar ma Sai da ta kone a hannun ta.
STORY CONTINUES BELOW
Aisha na kwance a falo taji sallamar Yaa AK da sauri ta mike ta kalli agogo taga karfe uku. Da sauri ta karasa ta fada jikin sa tana fadin
“Oyoyo Yaya na.”
Ya Jata jikin sa sosai Yana fadin
“Ya gidan?”
“Lafiya Lou!”
Ya dauke ta Yana fadin
“Nayi kewar ki da yawa.”
Taja hancin sa tace
“Yaushe ka fita.”
“Duk da haka.”
Ya ajiye ta akan gado. Tace
“Bari na kawo maka wani Abu!”
“Kiyi zaman ki.”
“A’ah Yaya me kaci?”
“Gashi yanzu Zan Sha milk!”
Hararar sa tayi ta mike ta fita Bata jima ba ta dawo dauke da kayan abincin sa. Ta ajiye. Ta zauna ta fara bashi. Suna tsaka da ci Sha’awa tayi knocking.
Izinin shiga suka Bata ta turo ta shigo tana ganin Aliyu ta danyi turus. Aliyu yace
“Shigo Mana!”
Ta shiga ta ajiye plate din tace
“Anty gashi na gama.”
“Nagode Sosai!”
Ta juya ta fita. Aliyu ya kalli Plate din yace
“Ni bana son kina cin wannan fulawar da yawa fa.”
Fuska ta Bata tace
“Nima fa dazu naji Ina so Amman yanzu duk ta fita a rai na.”
“Sai ki ajiye ai.”
“Daman!”
Ta matsar da kwanukan suka zauna suna Hira ta soyayyar su.
Da sukai la’asar ma gidan suka Bari ya dauke ta suka zaga garin sai magariba suka wuce gidan Umma. Acan suka samu Maryama da Muhammad a compound. Mujahida da Shu’aibu a bakin part din su.
Aisha tace
“Sannun ku kun barni ni kadai ko?”
“Ai yanzu zamu taho.”
Suka gaisa da Yaa Mustapha da Shu’aibu sannan sukai ciki.
Umma da Baba na zaune a falo suka shiga. Nan suka gaisa suna tambaya ya gida. A falo suka zaune har akai isha’i Baba da Aliyu suka tafi masallaci ita da Umma suka wuce daki Dan yin sallah.
*
Sha’awa na komawa daki ta buga tsalle yace
“Soon zan kwace Aliyu ke Kuma Zaki mutu.”
Ta koma ta kwanta tana fadin
“Wai yaushe Yaya ya zama haka Ashe ya iya soyayya. Ina ma nice Aisha yake min abubuwan da yake Mata.”
Tayi juyi tana fadin
“Hmm Allah Kai damo ga harawa.”
Daga nan Bacci ya dauke ta tin wajen uku da Rabi ba ita ta tashi ba sai bayan isha’i tayi mamakin baccin da tayi.
Sallah tayi la’asar, magariba da isha’i sannan ta zauna tana tunanin ko yanzu maganin yai aiki ko bai ba duk da dai ba na wani Abu bane na Hana daukar ciki ne da Malamin su ya Bata Amman Kuma tasan zai iya illa ga cikin dake cikin ta.
Tare suka koma da Aliyu. A falo ya zauna. Umma da Aisha na daki. Umma na Karai Mata nasiha.
Jin su Baba sun shigo suka fito. Aliyu yace
“Mu zamu tafi.”
Umma tace
“Ku tsaya kuci abinci ko?”
Kan sa a kasa yace
“Umma ni dai na koshi.”
Aisha tace
“Umma ni dai Zan tafi dashi nasan tuwo ne ko?”
“To je kizubo.”
Taje ta zubo ta fita tana fadin
“Ina su Maryama ko anan zasu kwana me?”
“Suna Waje muka Baro su.”
Aisha ta durkusa tace
“Baba sai da safe!”
“Allah tashe mu lafiya.”
Tayiwa Umma sai da safe Aliyu ma haka suka fita.
A compound suka samu su Maryama Yaa Aliyu yaiwa Muhammad da Shu’aibu sallama sannan ya nufi mota.
Aisha tace
“To Yaya mu zamu tafi. Ku Kuma Anan zaku kwana?”
“Tare zamu tafi!”
“To ku taho.”
STORY CONTINUES BELOW
Ta nufi Mota ta shiga. Ya fito da motar. Maryama tace
“To mu zamu tafi sai goben?”
Kai ya gyada yace
“Zan shigo ai.”
“Allah kaimu!”
“Amin!”
Sukai cikin gida sukai wa su Umma sallama  ita da Mujahida sannan suka fito Maryama ta  nufi mota. Mujahida tabi Bayan ta tana dagawa Shu’aibu hannu.
Ya tada motar yace
“Shine kuka zo kukai zaman ku kuka bar min Mata ita kadai Bayan kusan Bata da lafiya.”
“Ni lafiya ta kalou. Kuma ai kazo ko?”
“Eh da ban dawo ba bansan me zai sameki ba ke kadai fa.”
“Yaya yanzu na Saba zama ni kadai ne?”
“Duk da haka.”
“To ayi Hakuri Yaya!”
Maryama ta fada. Mujahida tace
“Bazamu Kara barin Anty ita kadai ba.”
Tara saura suka shiga gidan
Ba kowa a falo sama sukai suka bar su Maryama a falo. Tana shiga ta cire mayafi. Mujahida ta dauki ledar abincin da Aisha ta taho da ita ta nufi sama.
Knocking tayi Aisha ta mike ta bude. Hanya ta Bata ta shiga ta ajiye ledar ta dibi kwanukan ta bar musu plate da spoon ta juya za ta fita.
Aisha tace
“Ki zo ko dauki tuwon.”
“Anty ai sai ku!”
“Au shikenan naci dumame!”
“Yaya fa?”
“Shima baya ci ko?”
Kallon su kawai yayi ya shiga bandaki.
Aisha ta mike ta zo ta bude ta zuba a plate. Hannu ta wanko kan ta dawo ta sami Aliyu zaune Yana cin tuwon da ta zuba. Tace
“Yaya Kai da kace baka ci.”
“Wa yake kin tuwon Umma.”
“Eh ai ka hanani Yi ni.”
“No ai Dan Baki da lafiya ne.”
“Ni lafiya ta kalou.”
Yai murmushi yace
“Taho kinji Honey!”
Ta zo ta zauna ya dinga bata tana ci suna har suka gama. Maryama tazo ta kwashe kayan. Aisha ta shiga tayo wanka sannan ta fito ta shirya ta haye gado tana fadin
“Yaya kaji yau ban Aman ba.”
“Allah yasa ya tafi.”
“Amin Yaya!”
Ya Jata jikin sa ya rumgume ta Yana shafa Bayan ta. Bacci ne ya dauke ta. Ya zare jikin sa daga nata ya mike ya shiga yai wanka. Kayan Bacci ya saka sannan ya fito ya nufi falo.
Ba kowa a falon. Kitchen ya shiga ya dauko furar sa ya zauna Akan kujera Yana kallon TV. Furar yake Sha Yana kallo.
Sha’awa ce ta fito zata dauko Abu a kitchen tana ganin Aliyu a zaune ta koma daki a guje. Wasu kananun Kaya ta saka ta fito tana wata tafiya. Sam bai ma kula da ita ba har ta shiga kitchen ta fito. Ganin zata wuce bai san da ita ba. Yasa ta taho ta gaban TV zata dauki wani Abu dake kan TV stand din.
Ganin ta yayi ya dago Yana wurga Mata wani kallo yana fadin
“Mene haka?”
A duburburce ta dago ya daka Mata tsawa yace
“Get out malama!”
Juyowa tayi tace
“Yay………”
Bata karasa ba yace
“Nace ki bacen a gani ko? Nonsense.”
Jiki na rawa na ganin yadda ya hargitse ya sa ta juya Tai daki. Tsaki ya saki ya kashe kayan kallon yai dakin sa
*
**
***
****
*****
******
*******
********
*********
**********
***********
Fu’ad tin da ya bar Fateema ya tafi Abuja jinya ya kwanta sosai dan hotel din da ya dauka su suka lura da rashin motsin da suka Kai Masa ziyara suka same shi a wani matsanacin Hali.
Ko da aka Kai shi asibiti ba abinda yake damun da sai hawan jini Wanda yai mugun Kama shi har da ciwon zuciya. Nan suka fara bashi taimakon gaggawa sai da yayi wata daya a asibiti Yana fama da kan sa. Da kyar da taimakon wani likita da ya bashi counseling Akan damuwar sa Wanda da shawarar da ya bi ya dan samu dama dama Amman fa kullum ya kwanta ba abinda yake sai mafarkin Fateema.
STORY CONTINUES BELOW
Duk ya rame ya zama abin tausayi. Ya Gama fitar da rai ga rayuwar sa. Dan ya yadda in bai samu Fateema ba zai mutu Wanda yasan a yanzu Fateema ta Masa nisa domin kuwa ba zai manta saki nawa yai Mata ba.
Dan me yai mataa saki ta har uku dan me yayiwa kan sa tambayar Nan tafi a kirga Amman amsar dai daya ce Dan Yana son ta ya fita son bukatar ta akan tasa.
Watan sa biyu a boye a garin Abuja ya bar gasar gaba daya. Sam bai bi wajen da tasan za a nemshi ba sai ya canja shiya.
Wanda inda yake ma rayuwar kadaici tai Masa yawa Wanda ya sa duk ya zama so emotional har ya fara zaucewa.
A kasar da yaje ne wani makwabcin sa yaso ya koya masa shaye shaye. Dan kwanan sa uku da zuwa kasar Amman ko Bacci na minti biyu bai taba samu ya dauke shi ba abinda ya fara sa shi ya kasa nutsuwa da ka gashi zaka yana da damuwa karara.
*
Zaune yake a compound din gidan nasu ya rasa me yake damun sa kwata kwata ya kasa zaune ya kasa tsaye.
Karasowa yayi yace
“Hey bro!”
Fu’ad ya dago ya kalli saurayin ya daga Masa hannu kawai. Zama yayi yace
“Ya dai na ganka haka?”
Wani kallo Fu’ad yai masa Amman bai basa amsa ba. Yai Dariya yace
“Na gane kana cikin damuwa Amman ka ban dama Zan kawo maka karshen damwar ka.”
Wani kallo Fu’ad ya aika masa dashi, sannan ya mike ya bar wajen. Anyi haka shi da wannan makwabcin nasa wajen sau biyar kenan. Kuma har a lokacin Fu’ad idon sa bai Kara samu ya runtsa ba. Duk yayi jajir ya rame ya birkice.
Zaune yake akan kujera a compound din nasu. Ya zauna ya tashi yafi sau biyar Amman ya rasa ya zai Yi zuciyar sa tayi zafi tayi nauyi ya rasa me zai yi yaji dadi. Hawaye kawai yake so ya fitar ko zai ji Dadi Amman ya nemi hawayen ya rasa.
Kansa ya jingina Akan kujera ya lumshe Ido dake masa zafi kamar barkono. Makwabcin sa ne ya karaso hannun sa rike da lemo guda biyu.
Sallama yayi ya zauna Amman Fu’ad bai dago ba sai da yace
“Bro!”
Sannan ya dago Yana kallon sa da idon jajir. Lemon ya Mika masa. Kallon lemon yai ya dauke Kai Dan Sai ya yini bai sa ko ruwa bama.
“Ba kyau Mai da hannun kyauta baya.”
Ido ya lumshe ya mika masa. Hannu ya saka ya amsa sai ya ajiye yace
“Thanks!”
Ya Mai da Kai ya jingina. Yace
“Kasha Mana.”
Kai ya girgiza Masa kawai Dan bai son magana ma sam. Yace
“Baka yadda Dani bane?”
Murmushi Mai ciwo yayi yace
“No ba haka bane.”
“In ba haka bane kasha!”
Dauka yayi ya kurba yace
“Shikenan!”
Kai ya gyada yace
“Eh Amman ka dada.”
Dauka yayi ya kwankwade sannan ya koma inda yake. Makwabcin nasa na zaune ya kasa tashi yana jiran yaga a halin da Fu’ad zai Shiga Amman sai yaga ya mike Yana kaiwa da komawa abin ya bashi mamaki Dan kwayar da ya saka Masa ba karamar ‘kawaya bace Amman kamar Abu ya Kara Masa sai abun ya bashi tsoro kawai ya mike zai cikin gida.
Dayan makwabcin nasu ne ya fito Dan yaga duk abinda ya faru tsakanin su ba tin yau ba Yana Lura da yadda Lukman ke shigewa Fu’ad duk da yasan Lukman ba yaron kirki bane yana shaye shaye da naman Mata bayaso Sam ya koyawa Fu’ad.
Fitowa yayi suka hadu yace
“Me ka bashi?”
“Me kuwa Zan bashi!”
Ya kalle shi yace
“Allah shirya.”
Wajen Fu’ad ya nufa ya same shi zaune nan ya bashi shawara akan duk damuwar da yake da ita ya fauwalawa Allah. Kuma ya sani duk abinda ya samu bawa mukaddari ne.
STORY CONTINUES BELOW
Hakan abokin Nan nasa ya dinga Masa nasiha a Koda yaushe.
*
Satin sa biyu kenan rabon da ya runtsa idon sa.
Kuma kwanan sa biyu ko Waje bai fito ba. Anwar da yaga haka ya nufi bangaren Fu’ad Dan bayaso Lukman ya shige Masa har ya koya masa dabi’un sa.
Yayi knocking yafi sau biyar Amman ba amsa wannan yasa ya murda handle din ai kuwa take ya bude. Turawa yayi. Kwace ya samu Fu’ad akan kujera yayi dai dai dashi daga kallo daya zaka gane he is restless gaba daya.
Anwar ne yai gyaran murya Amman not respond form him. Dafashi yayi da sauri ya dago ya mike Yana bin sa da kallo.
Idon sa jajir dan rashin Bacci ga kuka ga damuwa. Zama Anwar yayi yace
“Fu’ad please ka dauki rayuwa a sannu! Baka fadan me yake damun ka ba Amman nasan duk yadda akai Akan soyayya ne “
Da sauri ya dago ya zuba Masa Ido. Kai ya gyada yace
“Ni likita ne Kuma na karanci bangaren halayar Dan Adam gaba daya. Ina da saurin gane halin da Dan Adam yake ciki.”
Yaja numfashi yace
“Kana son ka mutu akan wacce Bata son ka?”
Kai ya hau girgiza yace
“Fateema will never stop loving me kada ka Kara fadar haka!”
“Naji Amman zan baka shawara.”
Shiru Fu’ad yayi. Anwar yace
“Baka so!”
Nan ma shiru yayi. Anwar yai murmushi yace
“Ko kana so ko baka son zan fada maka Kuma nasan zai zama solution ko yai reducing your problem.”
Komawa Fu’ad yayi ya kwanta. Anwar yace
“Da farko Yana da kyau ka kasance a raye saboda a yanzu ka dauki layin da zai jefa rayuwar ka a hatsari Wanda zai iya zama barazana ga rayuwar ka. Kuma kasan me hakan zai faru? Zai kasance ka mutu in ka mutu wane Hali kake tunanin ita masoyiyyar taka zata Shiga? Bayan masoyiya, Mahaifiyar ka, Bayan ita Mahaifin ka, Bayan su Yan uwan ka. Ka taba gwada yadda zafin rabuwa yake ai. Ya kake tunanin zasu ji in akace musu baka duniyar gaba daya. Ba muna rayuwa dan Abu daya ko mutum daya ba. Ko da wani yace baya son mu to zai kasance tare damu in Kai nazari zaka gane me nake nufi.”
Ya mike yace
“In kana bukatar wani guidance or counselling am always available!”
Ya mike ya nufi kofar fita. Har ya Kai bakin kofa ya tsaya yace
“Ya kamata kaga likita fa.”
Yana fadar haka ya fice. Kwanciyya Fu’ad ya gyara sai Kuma ya mike Yana dafe kan sa dake barazanar tsage masa.
Haka yake gudanar da rayuwar tasa so lonely rana tayi tsayi dare ya ninka tsayi rana.
Abu daya ke sawa yaji sanyi in ya tuna yayiwa Fateema abinda take so. Amman matsalar sa daya ita ce in ya kwanta yai ta mafarakin ta cikin wani mawuyacin hali abinda ke daga masa hankali kenan.
Fita yayi kawai sai ya dauki hanyar plat din Anwar. Yana zuwa ya dannan bell. Anwar da dawowar sa daga aiki kenan ya nufi kofar ya bude. Yana ganin Fu’ad ya saki murmushi Yana
“Welcome Fu’ad!”
Ya bashi hanya. Sai Kuma Fu’ad ya tsaya kallon wajen me ya kawo shi ne.
“Bismillah!”
Anwar ya fada yana nuna Masa kujera.
Karasawa yai ya zauna. Anwar ya kalle shi yace
“Me Zan kawo maka?”
Kallon sa yayi kawai ya dauke kan sa. Mikewa Anwar yayi ya bude firij ya dauko Masa juice ya ajiye Masa sannan ya zuba Masa a cup Bayan ya daurayo shi.
“Bismillah!”
Kallon drink din yayi ya dauke Kai. Anwar yace
“Please!”
Ya dauka ya kurba sanyin lemon ya ratsa cikin zuciyar sa. Ido ya lumshe. Anwar yace
“Ya gida?”
“Alhamdulillah!”
Ya fada. Anwar yace
“Yanzu na dawo daga aiki Bari na na rage kayan jiki na two minutes!”
Kai kawai ya gyada. Kayan kallo ya kunna Masa ya shige ciki. Bai jima ba ta fito gani yayi ya kashe kayan kallon ya kalle shi yace
“Ya ka kashe?”
“Bana son hayaniya!”
Murmushi Anwar yayi yace
“Me yake damun ka ne idon ka kullum ja.”
Ido ya lumshe Wanda yake Jin sa dinshi dishi kamar ba a jikin sa ba. Can ya bude yai shiru.
Anwar yace
“Ko ciwo yake maka?”
“Yana min zafi kamar ba a jiki na yake ba.”
“Kana samun Bacci kuwa?”
Damuwa ce ta bayyana akan fuskar Fu’ad yace
“Sati na biyu rabon da nayi Bacci in kaga nayi Bacci to na mintina Kadan ne Wanda tsayin dare Ina yin sa Ido biyu.”
Ido Anwar ya zaro yace
“Subhanallah Amman kake zaune haka baka je asibiti ba!”
Shiru Fu’ad yayi. Anwar yace
“Wannan matsala ce fa ba karama ba.”
*To masu neman Fu’ad ga Fu’ad nan fa bamu san ya, ya kare rayuwar sa ba amman mun fara jin kadan daga halin da ya shiga. Me zakuce gareshi*
Ido Anwar ya zaro yace
“Subhanallah Amman kake zaune haka baka je asibiti ba!”+
Shiru Fu’ad yayi. Anwar yace
“Wannan matsala ce fa ba karama ba.”
“To ya zanyi?”
Mikewa Anwar yayi ya Shiga daki. Sai gashi ya fito da abin auna jini. Zama yayi ya auna Bp Fu’ad.
Jinin sa ya hau sosai. Yace
“Kaga ko kana son jefa rayuwar ka a halaka.”
Ya mike ya fita bai jima ba ya dawo hannun sa rike da leda. Ya zauna ya bude dayar leda ya dauko pack din abinci ya ajiye masa a gaban sa ya dauko Masa lemo da ruwa yace
“Ka ci abinci sai kasha magani ko?”
Abincin ya kalla ya manta yaushe rabon sa da abinci daga tea sai lemo su kadai yake Sha. Ja yayi yai spoon daya biyu sai ya ture ya Sha  lemo.
Anwar yace
“Ya dai?”
“Am ok!”
“Haba dai maganin da zaka Sha Yana da karfi sai kaci abinci!”
“Bana iya cin abinci wallahi.”
“To saboda me?”
“Da na fara nake koshi.”
Magani ya Ballar masa ya bashi yasha sannan ya koma ya jingina da kujerar ya yi hamma. Ido ya lumshe yace
“Kai na kamar zai fashe ga kirji na ciwo yake min yai min nauyi Abu ya tsaya min a makoshi Sam yaki ya saukar min Yana damu na.”
“Sannu!”
Ya gyada Kai idon sa a lumshe yace
“Ina son Fateema ita ce buri na farin ciki na abar alfahari na ni nasan da son ta Zan mutu Ina fatan ta kasance cikin kwanciyyar hankali da Jin dadi.”
Ya fada Yana hamma ya gyada zaman sa. Sai Kuma yai dif. Anwar dake zaune a gefen sa duk tausayin sa ya Kama shi sai kallon sa yake Yana girgiza kai.
Haka tin Yana sunbatu Yana Fado matsalar sa har yai dif Bacci ya dauke shi. Gyara Masa kwanciyya yayi ya mike ya Shiga yai wanka ya fito ya shirya cikin kayan baccin sa.
Fitowa yayi ya same shi Yana sharar baccin sa. ‘Daga sa yayi ya Kama shi suka daki
Shiga ya kwantar dashi. Gwaje gwaje  yai Masa sannan ya saka Masa ruwa ya koma ya kwanta.
Sai da Fu’ad yai kwana biyu Yana Bacci sannan ya farka. Dakin ya fara bi da kallo. Anwar ya shigo sanye da kayan sa. Yana ganin ya tashi ya karasa Yana fadin
“Ka tashi?”
Kallon sa Fu’ad yayi kawai. Yace
“Sannu!”
Sannan ya shiga bandaki ya hada Masa ruwan wanka.
Ya fito yace
“Ka Shiga Kai wanka ko?”
Ya mike Yana dafe bango ya shiga. Anwar yabi bayan sa ya nuna masa sabon toothbrush da soso sannan ya fito. Ya gyara dakin ya Shiga kitchen ya debo Masa kayan abinci ya ajiye. Ya jima a bandaki ya fito ya samu Anwar ya ajiye Masa kayan ya saka ya hau kan sallaya yai sallah.
Yana kan sallaya ya shigo ya ajiye Masa kayan abinci. Ci yayi ya bashi magani ya Sha ya koma ya kwanta take Bacci ya kara dauke shi. Sai da yai kusan sati ba abinda yake Yi daga sallah wanka sai cin abinci da ya Sha magani sai Bacci.
Kan sati biyu sai ga Fu’ad ya yi kyau ya Dan ciko kuma ya samu nutsuwa sosai. Ranar da ya gama Shan magani a Ranar bayan ya gama cin abinci ya kalli Dr yace
“Nagode!”
STORY CONTINUES BELOW
Anwar yace
“Dame?”
“Everything naji kaso sabain a cikin dari na damuwa da abinda ke damu na ya ragu. Na rage jin nauyi a zuciya ta Amman fa Ina ji duk da haka.”
“Zamuje asibiti a maka check up sai muga under wane medication zamu saka ka.”
“Nagode Sosai.”
“Ba komai. Amman me ya kawo ka kasar Nan.”
“Na Rasa inda zani shiyasa na taho Nan.”
Kallon sa yayi yace
“Kamar ya?”
Nan ya bashi labarin komai Akan sa. Anwar Bayan ya gama ji yace
“Kayi ganganci Fu’ad!”
“Ganganci kuma?”
“Eh domin Fateema ba Wanda take so sama da Kai. Kuma ba Mai son ta da kaunar ta sama dakai. Barin ta da kayi babban kuskure ne kamar yadda ka shiga wani Hali sai ta shiga kamar yadda ka damuwa Sai ta fika damuwa Sai ta fika shiga damuwa. Meyasa ka rabu da ita. Mata suna da karanci fahimta ba kasafai aka gane su ba. Sai kaga suna son Abu Amman bazasu fito su nuna ba. Wallahi ba karya zan maka ba Fateema tafi son ka wani Abu ne kawai yasha kanta ta nuna son da damuwar waccan a fili. Domin kuwa shi dan ta rasa shi ne da ta kwana biyu ta Shiga hankalin ta zata gane Kai ne masoyin ta na gaskiya daga nan zata shiga damuwa kenan ba Mai cire Mata wannan damuwar sai Kai kadai. Ko ta cire sai dai pretending gashi yanzu bakin alkalami ya Riga ya bushe dan me Kai Mata saki uku!”
Ido Fu’ad ya rufe hawaye ya hau zubo masa yace
“Ban San ya akai nayi ba nayi ne dan samuwar farin cikin ta.”
“Hakika to ba haka bane.”
“Tayaya zaka ce ba haka bane. Na Bata chance na ta kasance da Wanda take so ne fa.”
“Hmmm ba zaka gane ba Fu’ad Amman yanzu ka cire damuwa Allah na tare dakai. Zai duba sadaukarwar da kayi ya kawo maka mafita. Kayi hakuri kaji!”
Kai ya gyada yace
“Nagode!”
Ya jingina kan sa da kujera hawaye na zuba. Anwar yace
“Haba Fu’ad ka daina kukan Nan!”
Yasa hannu Yana goge masa Kallon sa yayi Yana Jin son Anwar yadda yake kula dashi babu hadin komai a tsakanin su.
*
Sunje an gwada shi sosai Inda aka gane Ya kamu da ciwon zuciya Mai tsanani. Nan aka daura sa Akan magani. Anwar ne ya dinga kula dashi Yana bashi counseling Wanda duk yadda yake debe Masa kewa haka bai hanasa tunanin Fateema da Hajiyar sa ba. Sai dai bai kwanta ba Amman sai yayi tunanin su.
Sai da ya Shekara ba abinda yake kullum Yana gida Yana fama da jinyar kan sa. Ciwon sa da ya lafa yake Kara tashi saboda damuwa.
Da kyar da taimakon Allah dana Anwar ya samu ya dawo dai dai.
Lokacin da ya fara jin sauki  sai Anwar ya sameshi yace
“Fu’ad zaman ka haka ba zai yiyu ba ka fito da takardun ka Ka nemi aiki Shima zai rage maka tension kaji.”
“Nima na fara tunanin haka Amman da Ina son na canja lined ne!”
“Kamar ya?”
“Eh Ina son na samu wani horo a bangaren jinya na zama likita!”
Murmushi Anwar yayi yace
“Me ka karanta I mean wanne bangare kake!”
“Economic nake ina da masters.”
“Haba Friend ka fito da takardun ka mu nemi aiki kaje ka Karo karatu ka zama babba kawai.”
“Zanyi haka Amman in na zama likita.”
Zama Anwar yayi yace
“Saboda me kake son zama likita?”
“Saboda Fateema likita ce.”
“Kai likita itama likita!”
Yai murmushi. Anwar yace
“Abun da yawa Amman in baka shawara!”
Kai ya gyada yace
“Akwai wani bangare da za a bude a hospital din da nake aiki but shi ba na likita bane na masu bada counseling ne a harkar lafiya where not Kai joining abun bashi da dadewa baifi kayi month Kadan ba ka zama a qualified.”
STORY CONTINUES BELOW
“Ba zance ba Zan ba Amman da na gama Zan juya sai na zama likita ka tayani da addu’a.”
“Wish you all the best!”
Daga haka ya dauki Fu’ad yaje ya fara karatun Yana gamawa aka bashi aiki da haka ya fara aiki yana Kuma Karo karatun sa. A dayan bangaren yana kasuwanci sosai ya zama busy akan aiyukan sa. Dan ma aikin part-time yake zuwa. Makaranta ma bai fi a sati sau uku ba sai kasuwa.
Tunanin Fateema bai taba barin zuciyar sa ba. Wani lokacin in Yana tunanin yakance
“Kar naje Ina tunanin matar aure. Dan bana fata Fateema ta zauna har yanzu ba aure. Allah ya Baki farin ciki Teemah.”
Addu’ar sa Bata taba Kare kan Fateema a Koda yaushe.
Yan Mata kuwa yadda sukai Masa caa aka abun har tsoro yake bashi. Shi Kuma Sam basa burge shi. Dan in ba Fateema ba baya ganin ko wacce macce a matsayin mace. Ita kadai yake kalla a matsayin mace.
Duk yadda suke tusa Kai guje musu yake shiyasa wasu kance ya fiya tsoron Mata wasu Kuma suce wulakanci ne. Amman shi ko daya macece in ba Fateema ba sam baya ganin ta a matsayin mace.
Duk shekara sai yaje aikin hajji Yana addu’a Akan Fateema kullum addu’a yake Allah ya cire Masa tunanin ta a ransa Amman kamar bayi yake ba tin Yana Yi har ya daina.
Duk yadda ya samu abinda yake so Amman bashi da kwanciyyar hankali Sam. Kuma yasan dalilin hakan zai kasance dan ya bar Hajiyar sa ne Amman ba zai iya rayuwa a kasar da Fateema take rayuwa ita da wanin sa ba. Ba zai iya ganin Fateema a matsayin matar wani ba. In ya tuna Fateema na can a matsayin matar wani har ciwon sa sai ya tashi. Anwar da yanzu suka zama Aminan juna Dan gidan su daya ma yanzu yai tai Masa fada sai dai  ya tsaya kallon sa kawai Dan ba ya Jin zai taba daina tunanin Fateema his first love.
In ya zauna ya fara tunanin ta kuwa mantawa yake da komai. Anwar tin Yana fada ya dawo nasiha daga nasiha ya dawo lallashi. Amman duk a banza. Shi duk shekara Yana zuwa gida Amman Fu’ad bai taba cewa zai je gida ba.
Mace kuwa ko a gun aiki daga aiki sai aiki in Anwar yaso kunna sa Nan zai ce
“Nifa Naga Dr kaza kamar son ka take.”
Ai fa daga Ranar ba zai sake sakar Mata fuska ba. Abin har mamaki yake bawa Anwar da ya gane haka sai ya daina Masa wasan yake tayashi da addu’a kawai.
*
Cikin Shekara uku Fu’ad ya zama babban Dan kasuwa Dan har kamfani ya bude Wanda sukai hadin gwiwa har Anwar da wasu likitoci guda biyu shine Akan komai saboda bangaren da ka karanta tin a gida Dan haka shi yake dealing da business din nasu gaba daya.
Kan kace me *ANFA* Group of companies ya shura a fadin duniya kowa yasan da kamfanin Dan yadda suke kera abubuwa masu kyau da inganci.
Kuma hakan bai hana shi yin karatun sa ba cikin hukuncin Allah, nasara da sa’a take zuwar masa cikin sauki. Duk karshen wata zai turawa da Hajiyar sa kudi Amman bai taba zuwa ba sai aike.
Lokacin da company din su ya Shekara daya da budewa Kuma ya samu award da ban girma daga kasar sai suka shirya party Dan za a karrama kamfanin. Kowa Yan gidan su yazo har Yan gidan su Anwar iyayen sa da kannen sa haka duk sai yaji wani iri.
Amman yadda Mahaifiyar Anwar ta dinga Masa sai yaji kamar Hajiyar sa ce dan yadda take ji da Fu’ad ko da Anwar Bata ji.
Kanwar Anwar da aka zo da itabta dinga shagwaba Wai ya kwace Mata Hajiyar ta shi Kuma sai Kara tsokanar ta yake Hajiyar tana biye Masa.
*
**
***
****
*****
******
*******
********
*********
**********
Yana shiga ya samu Aisha ta fito daga bandakin.
“Ina kaje?”
“Naje kasa ne!”
Ta karaso ta kwantar da kanta a kafadar sa yace
“Shiyasa na kasa baccin ai.”
“Sorry kinji. Taho mu kwanta.”
Suka kwanta.
STORY CONTINUES BELOW
*
Washe gari da safe yana dakin training Aisha na daki tana bacci Dan yanzu duk safiyya da wani zazzabi take tashi Tai ta Bacci sai wajen goma Kuma yake sakin ta. Sunje asibiti Tasha magani Amman duk a banza. Hankalin Aliyu duk ya tashi. Amman dai duk da haka. Likitoci sun fada Masa sai a sannu sannan zata daina.
Sha’awa kwana tayi tana zulumin akan Aisha shin taci wainar me yake damun ta ya take yanzu ba Wanda ya fada Mata Aisha ba lafiya.
Sama ta nufa Dan Maryama da Mujahida na kitchen suna aiki. Ba kowa a falon saman Dan haka ta wuce dakin Aisha ta bude a hankali. Kwance ta same ta cikin bargo. Juyawa tayi ta nufi dakin da Aliyu yake.
Yana zaune Akan kujera Yana daga wani karfe ta shiga ba ko sallama dagowa yayi dan yaga waye ya shigo ba sallama haka.
Sha’awa ya gani ya ajiye karfen ya hade fuska kamar bai taba Dariya ba.
“Me ya kawo ki Nan?”
“Daman nazo gaishe ka ne!”
Wani kallo ya wurga Mata yace
“Kin rainani ko Sha’awa? To ki fita Kika sake zuwa inda nake sai ranki yayi mummunan baci.”
“Get out!”
A guje ta fice. Ya saki tsaki ya mike ya koma daki ransa a bace. Wanka yayi ya fito yana shiryawa.
Motsin sa yasa Aisha ta mike tana kallon sa. Agogo ta kalla ta dire kafar ta tana fadin
“Yaya har ka gama?”
Juyowa yayi ya sakar Mata murmushi ta sauka ta fara gyara Masa buttons din rigar sa tana fadin
“Me yake damun Mijinane?”
“Me Kika gani?”
“Haba ai nasan Miji na ba haka yake ba!”
“Yaya yake?”
“Yafi haka fara’a.”
Yai murmushi ya Jata ya zauna ya zaunar da ita Akan cinyar sa yace
“Ke Kika sa Sha’awa tazo ne?”
Kai ta girgiza tace
“Me ya faru?”
“Ina son ta koma ne.”
“Akan me?”
“Kawai.”
Hannun sa ta kamo tace
“Yaya please ka barta har tace zata tafi. Kaga su Maryama suna Nan ita in aka ce ta tafi ai ba Dadi ko?”
“To shine me?”
“Ni dai dan Allah Yaya ka barta.”
“Shikenan!”
“A’ah in kaga baka so shikenan!”
“A’ah for your sake!”
“Thank you!”
Ta rumgume shi ta mike tana fadin
“Bari nai wanka.”
Yace
“Muje nai Miki.”
“Yaya kada ka Bata jikin ka.”
Buttons ya fara cirewa Yana fadin
“Ai Kayan ma zan cire.”
Tazo ta taya shi cirewa suka shige. Tare sukai break anan falo sannan ta rakashi har kasa ya tafi aiki.
Da Rana suna zaune a falo Maryama da Aisha. Aisha ta kalli Maryama tace
“Ina Mujahida ne?”
“Bacci take!”
“Sha’awa fa?”
“Itama haka.”
Kai ta gyada tace
“Yauwah Wai da matsala zaman Sha’awa anan ne?”
“Me Kika gani?”
“Na tambaya ne kawai.”
“Eh to ni dai zance kada ki sake Mata Dan Kinga kawar Hajara ce.”
“Nagode Kuma Daman ni ba wani sakewa muke ba gaisuwa ce kawai!”
“Yafi dai.”
Haka suka cigaba da hirar su.
Da yamma tare suka shiga suka shiryawa Aliyu abinci Mai Rai da lafiya ta fito ta tafi tai kwalliya kamar wacce zataje biki. Tai kyau sosai.
Ana gab da magariba Aliyu ya shigo gidan da sauri ta fito daga sama. Kofa ta nufa ta nufi wajen motar sa. Ta bude tana fadin
“Welcome back my dear Ina kashiga yau.”
STORY CONTINUES BELOW
“Welcome Baby Love. Am sorry kinji.”
Ya rumgume ta, hannun sa ta kamo sukai ciki.
Akan kujera ta ajiye shi tace
“Sannu ya aiki?”
“Alhamdulillah jiki yai sauki ko? Kinyi amai?”
“Banci komai ba. Zazzabin Kuma bai dawo ba.”
“Good Allah Yasa ya tafi gaba daya Amman me yasa bakici komai ba.”
“Bana Jin yunwa ne.”
Ta fada tana dauko Masa lemo da ruwa.
Ta bude ta fara zuba Masa. Ta Mika Masa ya amsa Yana fadin
“Yanzu me kike so.”
Cup din ta amsa ta Kai masa Baki ya kurba ya lumshe Ido Yana godiya ga Allah abinda ya rasa a da kenan. Kula da tarairayar Wanda yanzu ya same su Alhamdulillah.
Ba abinda zai ce ga Aisha sai addu’a da saka Mata albarka domin ta kawo Masa canji da nutsuwa a rayuwa sosai. Alhamdulillah.
Ido ya bude tace
“Tunanin me kake?”
“Tunanin me kike zaton zanyi?”
“Anty na.”
“Wa kenan?”
“Hajara.”
Yai murmushi yace
“Tab na manta da ita wallahi.”
“Hmm to tunanin me kake?”
“Ke!”
“Ni kamar ya?”
“Tunanin ki nake!”
“Haba dai Yaya gani gaka wane tunani na zakai?”
“Gashi kuwa.”
“To sabode me kake tunani na?”
“Saboda yadda kike kyautata min.”
“Kai Yaya me nayi?”
Ta kamo hannun sa tace
“Muje ka watsa ruwa kan a Kira magariba ko?”
Ya biyo ta suka nufi stair suna kusa da stairs din Sha’awa ta fito daga dakin su. Ta karaso gano Aliyu. Tana karasowa taga Aisha a jikin sa sai tayi turus ta ja baya tace
“Sannu da zuwa Yaya!”
“Yauwah!”
Kawai ya fada ya dauki Aisha sukai sama. Suka shige daki.
*
Washe gari da safe ta rakoshi zai fita. Sanye take cikin riga da siket English wear sai ta yafa mayafi akan ta kan ta ba dankwalli Tai kyau duk da ba make up tayi ba. Compound suka fito suka samu Sha’awa a compound Kai Aliyu ya dauke ta karaso tana fadin
“Ina kwana Yaya?”
“Lafiya!”
Ya fada kawai ya shige mota. Aisha tabi bayansa tana Masa addu’a ya fita ta dawo tayi dakin ta.
*
Da yamma ma tayi kwalliya abin ta ta sauko Dan Aliyu na gab da dawowa sai kamshi take Yi. Maryama tace
“Kai Antyn mu kina kashe Yaya da kwalliyar Nan fa.”
Hararar ta tayi zatai magana kenan taji horn din Aliyu. Da sauri ta mike tayi sama taje ta Kara shafa turare ta sauko da sauki tana zuwa bakin kofa ya bude Yana ganin ta ya rumgume ta Yana kissing nata. Maryama ta rufe Idon ta. Sai da ya sake ta yaga Maryama yace
“Ah Ashe kina Nan.
“Sannu da zuwa Yaya!”
“Yauwah ya gidan Ina Mujahida?”
“Tana daki.”
Karar bude kofa sukaji. Duk suka juya. Sha’awa ce ta fito cikin wasu Riga da wando sun Kama ta. Kai ya dauke ya kamo hannun Aisha sukai hanyar stair. Sha’awa tace
“Sannu da zuwa Yaya!”
Bai amsa ba sukai sama. Suna zama Aisha ta kawo masa ruwa ya amsa ya Sha. Ta ce
“Yaya Wai me Sha’awa Tai maka ne?”
“Me Kika gani?”
“Naga baka sakar Mata ne.”
“Kawai.”
“Ka tabbatar.”
Kamo ta yayi ya zaunar a gefen sa yace
“Na tabbata.”
Sha’awa suna barin ta, ta wuce daki. Akan gado ta zauna tana fasa ihu. Waya ta rarumo tana Kiran Momy. Momy ta dauka tace
“Ya dai Sha’awa komai ya dai dai ta?”
“Tayaya fa? Momy ba abinda maganin yai Mata Dan Allah ki samo min maganin da Zan saka Mata cikin ya zube.”
“Kada ki damu yanzu Zan samo nafita zanje wajen Dr naji wane magani zai bayar daga Nan Zan rubuto Miki ki nema anan.”
“Thanks Momy. Dan wallahi kallon yarinyar Nan kawai na konan Rai kamar na mutu haka nakeji I hate her Baki ga yadda yake Mata ba Momy kamar zai maida ta cikin sa fa. Yana son ta da yawa”
STORY CONTINUES BELOW
“kada ki damu kema zai so ki kamar haka.”
“Anya kuwa?”
“Eh mana
Itama kina tunanin haka ta barshi muma ba zamu barshi haka ba.,”
“Yauwah Momy na. Ina jira “
“To kada ki damu.”
Ta kashe wayar ta koma ta kwanta tare da lumshe Ido burin ta kawai taga ta kawar da Aisha ta zama matar Aliyu kamar yadda ta kawar da Hajara.
*
Gaba daya rayuwa ta juyawa Hajara baya. Domin Mahaifin ta yanzu ya fita a harkar ta gaba daya. Gidan ba Dadi Sam.
Daman Bata ja Yan uwan ta ba da tayi aure Dan haka Suma yanzu da ta dawo Sai duk suka juya Mata baya basa wani shiga harkar ta. Bare Mahaifiyar ta da take Mata fada itama ta fita da hannu Akan ta kallon ta kawai take.
Yanzu ta rasa Jin Dadi a da sai dakin da ta zaba zata kwana Amman yanzu daki daya ne ita da kannen ta Kuma suke akan gado ita tana kasa. Bayan a gidan ta katifu sai Wanda take so manya ga laushi. Abinci kuwa sai dai a zubo Mata a Dan kwano wani lokacin ko nama Babu in da akwai ma bai fi guda daya ko biyu ba. Wanda a gidan ta sai ta cinye kaza daya. Itace a dafa Mata abinci kala nawa Amman yanzu babu wannan halin.
Tin tana hakuri da zaman Amman Kara lokaci kudin hannun ta duk ya fara karewa dan ta Debi a kalla wata biyu a gida. Tayi Baki ta rame.
Wajen Baba ta je tana zaune ta zauna tace
“Baba Dan Allah ki Kira Aliyu ki bashi hakuri.”
“Wa ni? Allah ya kiyaye kije wajen ubanki da ya duare Miki gindi shi sai ya bashi hakuri Amman bani ba. Ko Kinga Ina shiga harkar kune.”
“A’ah amman kema ki taimaka.”
“Tashi ki bani Waje ba abinda zanje nai masa. Ai ke Kika jawa kanki da kin zauna kinyi biyayya menene mijin ki baya Miki ko mu Nan duk wata sai an kawo Mana kayan abinci da sutura In sallah ce haka da Shanu ga zuwa aikin hajji Amman duk kin Baki duba wannan kin zauna lafiya da mijin ki ba. Ai bakiga komai ba bama in kin zalunce shi. Tashi ki ban Waje kada na mangare ki.”
Ta mike sum sum tayi dakin su ta zauna a gefen gado. Mariya kanwar ta ce tashigo ganin ta zaune a gefen gado tace
“Haba Yaya ya na gyara gado Zaki hau ki Bata man ai bake kike gyarawa ba.”
Dagowa tayi tace
“Ni kike fadawa haka?”
“To ai gaskiya na fada.”
Ta Harare ta ta fita. Hajara ta zuba tagumi zuciyar ta na Kuna kamar zata fashe Dan bakin ciki.
Wayar ta ce ta hau Kara ta dauko taga Alhaji Lukman. Dauka tayi gaban ta na Faduwa yace
“Nace Miki Ina bukatar kudi Kuma najiki shiru.”
“Nifa bani da kudi.”
“Kamar ya Baki da kudi.”
“Eh bani dashi Mana.”
“Saboda me?”
“Yanzu bama tare da Aliyu fa”
‘kamar ya?”
“Ya sake ni.”
Wata Dariya ya sheke da ita yace
“Kamar ya ya sake ki. Kinga ba Aliyu juya ne da kin yadda Dani da yanzu ko ciki ne kina dashi Kinga ko ta dalilin cikin Maci kudin sa Amman kin kasa yadda.”
“To yanzu ya zamuyi.”
“Ai kuwa tinda ba kudi dole kina bani kanki Dan da kudin Daman nake neman masu ragen zafi.”
“Kai Alhaji Lukman a yanzu ba Zan iya ba dama dai da aure banbi maxa ba haka kawai naje na samu ciki gaskiya a’ah.”
“Dan kin samu ciki shine me?”
“A’ah ince na wane!”
“Wa yace miki Zaki zamu zamuna dabara ko a zubar.”
“Kai ni Ina tsoro.”
“Ki je kiyi tunani.”
“Shikenan sai anjima!”
Ta kashe wayar.
Ta zuba tagumi. Tana kwance ta mike ta dauki mayafin ta, ta fita tsakar gida Sadaf Sadaf ta fice a gidan.
Gidan Sarki ta tafi tana zuwa ta nufi bangaren Momy. Ba kowa a dakin sai Momy dake zaune a falo tana waya ta juyawa Hajara baya.
“Ga maganin Nan na turo miki kije ki samu ki siya ki sa mata ko a lemo ne insha Allahu sai cikin ya zube.”
STORY CONTINUES BELOW
“Nagode Momy Ina kaunar ki yanzu ya za ai da Aliyun?”
“Zan Kira malam na fada Masa muna bukatar Aliyu ya karkato wajen ki Kuma a fitar da Aisha ke Kuma da Tasha maganin Kinga a halin da take ki Yi karya kice ita ta siyo Tasha Dan Bata son cikin. Nasan yadda Aliyu ke son cikin Nan ba zai so haka ba kila daga Nan ya sake ta Kinga me muke bukata mun kawar da Hajara sai itama ko ya?”
Juyawa Hajara tayi a hankali ta fita sai ta fara sallama. Momy ta kashe wayar ta amsa Mata shiga tayi tana ganin Hajara ta hade fuska. Ta shiga ta zauna a kasa tana fadin
“Ina yini Momy?”
‘lafiya waya Baki damar shigo min?”
“Gaishe ki nazo Daman nace Ina Sha’awa?”
“Bata Nan tashi kije na gode.”
Ta mike yace
“Sai anjima.”
Tana fita ta tsaya a bakin kofar part din Momy tana mamaki kenan Aisha suke so su zubar wa da ciki ko wa? Dole tayi wani Abu Mai kyau Dan tsairatar da rayuwar Aisha da Dan Aliyu. Duk da tana kishin ta Amman ko Dan ta kun tatawa Sha’awa da Momy. Bangaren Mamah tayi sai dai tai rashin sa’a bata Nan wannan yasa ta tafi kan zata koma ta fadawa Momy komai
Sha’awa na ganin ta fita da kanta taje ta nemo phermacy ta siyo maganin ta dawo ta saka a cikin kayan ta.
Maryama da Mujahida da Aisha na falo ta shiga. Aisha tace
“Ina Kika je ne?”
“Na zaga garin ne tinda nazo ban fita ba.”
“Ai kuwa dai da kinyi magana ai da ko Maryama ta rakaki.”
“Wallahi ma je wata Rana.”
“Allah kaimu!”
“Amin!”
Aisha ta kalli Maryama tace
“Sister anjima kiyi min wannan kunun!”
“Angama Anty na.”
Ta Harare ta tace
“Ki cigaba kema lokaci na zuwa kanki.”
Mujahida tace
“Wallahi Kam.”
Haka suka cigaba da Hira abinsu.
Karfe biyar da Rabi Aliyu ya dawo. Yana shigowa Aisha ta karasa tana Masa sannu da zuwa. Ya rumgume ta Yana kissing dinta sannan ya sake ya.
Maryama Tai Masa sannu da zuwa ya amsa cikin sakin fuska haka ma Mujahida. Har sunyi hanyar sama Yaji muryar Sah’awa tace
“Sannu da zuwa Yaya.”
“Yauwah!”
kawai ya fada ya wuce. Mujahida ta saki wata Dariya daga Maryama har Sha’awa suka bita da kallo. Ta mike tayi dakin ta.
Sha’awa tace
“Yaushe Zaki dama kunun Zan Taya ki.”
“To Zan Miki magana.”
Haka suka cigaba da zama a dakin
Suna shiga Aisha ta tayasa ya rage kayan jikin sa yai wanka ya Sha ruwa da lemo sannan y tafi masallaci.
Bayan ya dawo a sama suka zauna yaci abinci suka fito falon sama suna kallo shi da Aisha dake jikin sa a kwance.
Maryama ce ta shiga dakin Sha’awa a kwance ta same ta tace
‘Anty zanyi kunu.”
“Ok gani Nan.”
Ta fada ta mike ta ballo maganin guda hudu duk da biyu aka ce Mata za a Sha sannan ta wuce kitchen din. Ba abinda ta Taya ta sai surutu. Bayan ta gama ta ajiye ta tafi Dan dauko sugar a store na gidan ya Kare anan Sha’awa ta daka maganin ta zuba ta juya a kunun. Sannan ta ajiye kan Maryama ta dawo. Maryama na dawowa ta zuba sugar ta juya sannan ta dauka.
Sha’awa tace
“Kawo na kai Maya.”
Maryama ta Bata ta nufi sama ita Kuma ta gyara kayan wajen. Yana Hawa ta samu Aliyu zaune Aisha a jikin su tai sallama. Aisha ta amsa ta Ajiyewa Aisha Tai mata sannu sannan ta juya ta fita.
“Menene wannan?”
“Kunu nasa Maryama ta dama min.”
Kai ya gyada. Maryama ce ta shigo tana fadin
“Anty na kinsha kunun?”
“Zan dai Sha.”
“Ta zauna tana fadin
“Kada ya huce fa.”
“So nake ya Dan sarara Ina Mujahida ne?”
“Tana kasa Shu’aibu yazo.”
Aliyu yace
“Yauwah wai me yake tsakanin ku da Mustapha ita Kuma da Shu’aibu?”
“Kai Yaya zumunci kawai.”
“Yayi kyau. Allah ya kulla to.”
Tai Dariya tace
“Ai a kulle ma muke”
Sha’awa tana shiga daki ta fara safa da marwa ta kasa tsaye ta kasa zaune.
*
Hajara Bayan magariba ta koma gidan Mamah duk da bata dawo ba ta zauna a falo tana jiran dawowar ta. Har akai isha’i tana zaune tana jiran dawowar ta. Karfe takwas da rabi Mamah ta shigo gidan. Kallon Hajara ta tsayayi. Hajara tace
“Sannu da zuwa!”
Zama tayi tace
“Yauwah Hajara lafiya dai ko?”
“Lafiya Mamah tin rana nazo akace bakya nan sannan da magariba na dawo bakya nan.”
“To meya faru?”
“Mamah nayi nadama akan duk abinda na aikata kuma ba komai yasa nake haka ba sai zugar shaidan da tasu Momy da Sha’awa.”
“Momy da Sha’awa?”
Kai ta gyada tace
“Tin da nazo gidan nan suka ce kada na sakar muku wai ba zaku barni na huta ba kuma kun mallake Abbah da Aliyu in na sake muku nima sai yadda kukai dani haka suka dunga zugani suna nunan bakin ku wanda na dauka masoya nane Mamah har gun Malami muke kai Aliyu ai masa aiki. Ban tashi gane gadar zare sukai min ba sai bayan Aliyu ya sake ni suka nuna min ba sona suke ba abinda suke so kenan Aliyu ya saken.”
“Hajara bana son karya fa.”
“Wallahi Mamah na rantse da Allah ba karya a magana ta. Kuma a lokacin da nazo dan su samar mafita a lokacin suka nuna cewa basona suke ba Sha’awa ta fito fili ta nuna min ita take son Aliyu kuma sai ta aure shi ko ta halin kaka ta raba ki dashi kuma ta raba shi da Aisha.”
Shiru Mamah tayi tana kallon Hajara can tace
“Toh shikenan Allah ya shiga tsakanin mu dasu.”
“Amin Mamah sai abu na biyu da dazu naji Momy na magana a waya akai.”
“Menene?”
“Akan Aisha ne!”
“Me ya faru?”
“Momy kinga ban san ko sha’awa na nan ko bata nan ba amman yau da naje naji Momy na magana akan ta sakawa Aisha maganin zubar da ciki.”
Ido Mamah ta zaro tace
“What?”
“Wallahi Mamah dazu naji tana waya kuma da sha’awa take yi wai in ta sha sai suyi mata sharri suce maganin take sha kinga daga nan Aliyu zai iya sakin ta kinga abinda su ke nema ya samo sai su aura masa Sha’awa.”
Gumi Mamah ta fara ta dauki waya tana neman layin Maryama amman ina bata dauka ba dan ta bar wayar a daki ita kuma tana wajen su Aisha.

Gumi Mamah ta fara ta dauki waya tana neman layin Maryama amman ina bata dauka ba dan ta bar wayar a daki ita kuma tana wajen su Aisha.
Layin Mujahida ta fara nema a gigice amman shima ba a dauka ba. Layin Aliyu ta fara nema cikin tashin hankali.
*
Zaune suke suna hirar su sosai. Aliyu ya kalli Aisha yace
“Wai bakya jin yunwa ne?”
Fuska ta dan bata. Ya kalli Maryama yace
“Wayayi wannan kunun?”

“Nice nayi kuma ita tace tana so.”
Cup ya dauka ya zuba mata ya miko mata. Fuska ta bata yace
“Haba Baby love kisha ko yaya ne kinji Heartbeat ko akwai abinda kike so?”

Kai ta girgiza tace
“A’ah!”
Ya kai mata kofin baki kenan wayar sa ta hau kara. Maryama ce ta miko masa tana fadin
“Lah Mamah ce.”

Cup din ya sakar mata ya amshi wayar ya kai kunnen sa. Tare da sallama. Mamah ta amsa a firgice tana fadin
“Aliyu kana ji na?”

“Eh Mamah lafiya?”
Aisha da ta kurbi kunun ta hadiye da kyar tana dagowa jin a yadda ya tambaya dan daga muryar Mamah zaka san ba lafiya ba.

“Ina Aisha ya take?”
“Gata nan tana lafiya.”

“Ba dai abinda yake damun ta ko?”
“Eh Babu menene Mamah?”

“A’ah shikenan.”
“Dan Allah ki fada min Mamah.”

“Babu komai fa. ka kula da Aisha kawai ban yadda daga yanzu ta kara cin komai na cikin gidan nan ba.”
“Bangane ba Mamah!”

“Eh kada ta kara cin komai na gidan nan daga yanzu kanaji na.”
“Eh Mamah amman saboda me?”

“Ni dai na fada maka.”
“To shikenan”

Ya kashe wayar da sauri ita da Maryama suka ce
“Lafiya Yaya?”
Kallon su yayi yace
“Lafiya lou!”

Maryama tace
“Amman Yaya….”
Karar wayar sa ta katse mata maganar da zatayi ya duba Mamah ce ya dauka ya kai kunne sa. Mamah tace
“Ina Maryama?”

“Gata nan!”
“Bata wayar!”

Mika mata yayi ta amsa tace
“Mamah lafiya?”

“Lafiya lou ina wayar ki?”
“Tana daki.”

“Shikenan kina jina ko Maryama ki kula da yar uwar ki sosai. Ban yadda ta kara cin komai na gidan na ba har ruwa da lemo in tana so a fita a siyo kina jina ko?”
“Eh Mamah amman saboda me?”

“Ba komai kawai.”
Ta kashe wayar. Kallon Aliyu ta tsaya shi kuma ya dafe kai. Sai aka bar Aisha a cikin zulimi. Ta kalli Aliyu ta kalli Maryama da kyar ta bude baki tace
“Yaya lafiya wai?”

Hannun ta ya kama yace
“Ba komai fa.”
“Amman naga damuwa a fuskar ku.”

“Ba lomai fa.”
“To Allah yasa.”

Ta daga cup din ta kara kurbar kunun. Tana hadiyewa ta kara dagawa zata sha Maryama ta zaro ido ta mike da sauri ta amshi cup din hannun ta. Fuska Aisha ta bata tace
“Menene haka in sha zakiyi ba ga wani nan ba ki diba mana.”

STORY CONTINUES BELOW
Flask din ta dauke tayi kasa dashi. Aisha ta kalli Aliyu tace
“Yaya kai mata magana.”

“Kyale ta yanzu me kika so kici?”
“Ni kunun kawai nake so kuma na hannun ta.”

“A’ah banda wannan!”
Ta saka masa rigima nan ya hau lallashi da kyar tace
“To a yi min wani tinda ka hanani shan wancan.”

“Bari na fadawa Umma ai miki ko?”
Ya dauki waya ya fara neman layin Yaa Mustapha yana dauka yace
“Please kacewa Umma kunu Aysher ke so kuma garin ya kare tai mata yanzu zan zo na amsa.”

“Ok!”
Ya kashe wayar ta mike tana fadin
“Yaya tare zamu mu amso bari na watsa ruwa.”

“To ko nazo na tayaki.”
Kafada ta make tana fadin
“Naki wayon”

Tayi ciki. Wanka ta shiga tayi ta fito tana zaune a gaban mirrow ta fara shada mai taji cikin na murdawa. Baki ta cije tana taba cikin nata. Ji tayi kamar an soka mata allurori da sauri ta mike tana dafe cikin. Sai kuma taji ya lafa. Wardrobe ta karasa ta dauki kayan ta, ta saka ta dawo gaban mudubi zata shafa turare kenan taji cikin ta ya kuma sokawa sai kuma taji kamar ana jijjiga mata kayan cikin bata san lokacin da ta zube a kasa tana juyi ba.

Sosai cikin ke murda mata wanda yasa ta kwanta tana juyi rike da cikin ta bakin ta a cije ta kasa tashi bare ta kira Aliyu.

Yana zaune mitin goma bayan gama waya da Mustpha ya kira wayar yace
“An gama na kawo muku ne?”
“A’ah Madam tace tare zamu zo bari mu zo mu amsa.”

“Alright.”
Aliyu ya mike da niyyar shiga daki dan kiran ta. Maryama ce ta shigo tace
“Yaya ina Aishan?”

Tana daki menene?”
“A’ah ba komai.”

Ya juya yai ciki ita kuma ta zauna anan falon kofa ya bude yana fadin
“Ko kin fasa zu….”

Maganar sa ce ta tsaya ganin Aisha kwance a kasa tana juyi. Da gudu ya karasa yana kiran sunan ta abinda yaja hankalin Maryama kenan ta mike tabi bayan sa. Durkushe ta ganshi gaban Aisha yana fadim
“menene Baby love!”

Hannun sa ta kamkame tana fadin
“Yaya ciki na wayo zan mutu. La’ilaha illaha muhammad rasulillah.”
Sai jumfashin ta ya dauke take ya gigice yace
“Maryama fito mana da mota.”

Ya dauke ta a guje Shi ma ya rufa mata baya dauke da Aisha a hannu. Mujahida da Shu’aibu dake compound suka karaso suna tambaya lafiya. Ba wanda ya kula su Aliyu ya shiga baya shi da Aisha Maryam ta tada motar Mujahida ta shiga baya shuaibu ya shiga gaba.
Horn ta dannan mai gadi ya bude gate kan ya matsa ta fararo saura kadan tabi ta kansa. A guje ta fice a gidan ta hau titi sai government house.
Akan idon Sha’awa komai ya faru dan haka sai jikin ta yai sanyi. waya ta daga ta kira Momy tace
“Momy na shiga uku kada ta mutu.”

“To ai da zata mutu mu da yafi ma. Kinga ba ta rage mana wani abun ko?”
“Momy baki ga a yadda aka fita da ita bane kaar gawa.”

“To sai ki je ki tonawa kanki asiri ko?”
“A’ah.”

“To kiyi shiru kiyi pretending yanzu kije ki samu ki zubar da ragowar kunun in bata shanye ba.”
“Toh!”

Sama ta nufa ta duba falo ba flask din ta duba bedroom nan ma babu. Kitchen ta shiga ta duba nan ma babu kwata kwata. Sai ta tsaya tana tunanin to ina aka kai flask din. Daki ta koma ta kira Momy ta fada mata. Momy tace
“Ko an wanke ne?”

“To kila.”
“Shikenan yanzu ki dauki ragowar maganin ki kai dakin ta ki ajiye in komai ya lafa sun dawo gida sai ki tona mata asiri kice daman kinga tana sha kinji!”

“To Momy.”
Ta kashe wayar.
*
*
*
Mamah na gama waya da su Aliyu ta mike ta kalli Hajata tace
“Taho muje wajen Abbah!”
Ta mike tabi bayan ta.

STORY CONTINUES BELOW
Ba kowa a dakin sa sai shi kadai dan haka suka shiga suka zauna yace
“Ah Fulani an dawo.”

“Na dawo ranka ya dade.”
“Ya dai na ganki a haka.”

Hajara ta nuna masa ya kalle ta yace
“Ai Hajara ce.”

Kai ta gyafa ta kalli Hajara tace
“Yi masa bayani.”
Nan tai masa bayanin komai. sosai Abbah hankalin sa ya tashi tayaya za a ce da matar sa ake hada duk wannan abubuwan
“Innalillahi wainna illahir ajiun.”
shine kawai abinda Abbah ke fadi yace
“Yanzu ya za ai Hajiya?”

“Ai dole gobe muje can dukka azo nan a tara su.”
“Haka za ayi. Yanzu kin kira su Aliyun?”

“Na kira nace kada su bari taci komai na gidan.”
“Hakan ma yayi Allah ya kare ya tsare”

“Amin!”
“Bari muje sai da safe.”

Ta mike Hajara tabi bayan ta a hanya suka hadu da Momy zataje wajen Abbah dan ita ke da girki. Tana ganin Hajara tare da Mamah tace
“Ah Hajara ce a gidan namu.”

“Ita ce!”
“Kina lafiya dai ko?”

“Lafiya lou.”
Suka wuce daki ta bisu da kallo tana tabe baki

Suna shiga daki Mamah tace
“To Hajara dare yayi ko zaki kwana anan.”
“A’ah Mamah bance zan kwana ba a gida”

“Ban number na kira in sun.m matsa sai akai ki.”
Ta fara kiran layin nan Baban ta ya dauka. Mamah tai masa bayani cikin rawar jiki yace
“Ba ko.ai Allah kaimu.”

*
**
***
****
*****
******
*******
********
*********
Ranar Partyn anan suka kaddamar da komai da tarihin company inda suka ce su sun hada ne dan daga Fu’ad ba Dan kansu ba Amman shi Kuma yace Sam ba za ai haka ba domin kuwa yadda aka fara dole su Kare tare. Fu”ad ya samu ban girma sosai ba ga gwamnatin  ba haka nan ba ga yan uwa abokan kasuwancin sa ba, sai da yai hawaye dan sai ya tino da yau Yana tare da iyayen sa da Fateema wane Dadi da farin ciki zasu Shiga.
Haka akai party lafiya aka tashi suka rankayya gida dasu Anwar da Maman sa da kanwar Anwar. Ranar a gidan ma walima sukai da dare.

Kwana biyun da su Maman Anwar sukai sun Saba sosai da Fu’ad haka Nusaiba da Fu’ad ya dauke ta tamkar kanwar sa uwa daya uba daya.

Ranar da zasu tafi suka kaisu har airport duk suka tafi suna Jin ba Dadi.

Daga Nan suka cigaba da gudanar da aikin su, cikin aminci tsakanin Anwar da Fu’ad.

*
Nusaiba tin da ta koma gida ta fara fuskantar matsala domin kuwa sai ta fada tunanin Fu’ad duk ta rasa nutsuwa Wanda har Mama ta gane ta na cikin damuwa Dan haka ta Kira ta. Zama tayi kanta a kasa.

Mama tace
“Me yake damun ki Nusy?”

Kanta ta Kara kasa dashi Mama tace
“Ki fada min Mana Auta ta!”

“Mama ban San ta Ina zan fara.”
“Zaki iya ta ko Ina  Nusy Zan fahimce ki.”

Kai tayi kasa dashi tace
“Mama na kasa cire Yaa Fu’ad a zuciya ta da tunani na.”

“Fu’ad Kuma wanne Fu’ad?”
“Mama Fu’ad din Yaa Anwar!”

Mama tai murmushi tace
“Gaskiya ne Auta ta tana da hankali sosai.”

“Kamar ya Mama?”
“Saboda kin Yi zabe mai kyau. Fu’ad ya cika na miji Wanda ya cancanci a so shi Kuma Zan goya Miki baya Amman ba za ki fito fili kice kina son sa ba. A’ah sai dai ta siyasa Zaki tusa Masa kan ki ba ta fili ba Shima da kin gane Yana da wacce yake so ko baya ra’ayin ki sai ki hakura ki Mika lamuran ki da addu’a ki cigaba da addu’a Allah zaba mafi alheri bana son kije inda ba za a soki ba kamar yadda kike nagartaciyya haka ma Fu’ad Dan ba yana da halin sa. Dan Haka zan so mu hada zuri’a ta da Fu’ad Allah bada sa’a”

STORY CONTINUES BELOW
“Amin!”
Mama ta dafe Baki tace
“Ba kunya!”

Fuska Nusy ta rufe da hannu Mama tai Dariya tace
“Shikenan?”

“Mama tayaya Zan tusa Kai na.”
“Ki samu number sa kina yawan kiran sa Kuna gaisawa sannan Kina bashi kulawa ta musamman daga Nan Zaki fara shige masa. Sauran ai ke macece ko?”

Da gudu Nusy ta mike tayi dakin su. Mama ta saki murmushi tana fadin
“Allah tabbatar da alheri!”

Nusy na Shiga daki ta dauki wayar ta. Number Fu’ad ta tsaya kalla Sai ta dannan Dailing sai ta katse. Can dai da kyar ta runtsa Ido ta fara Kira. Yadda wayar ke din din haka zuciyar ta keyi.

Yana dauka taji muryar sa Mai dadi da sanyi tai Mata sallama. ajiyar zuciya ta sauke. Amman sai ta kasa amsawa.
“Hello hello!”

Fu’ad ya fada. Shiru sai ya dauke wayar ya katse. Sai da sukai haka sau uku ana hudun ta daure tayi sallama. Ya amsa Yana Mai son ya gane wacece.

Ganin ya kasa gane wacece yace
“Wacece Dan Allah?”

“Haba Yayan mu ai ma gaisa tukkuna ko?”
“Ok ya kike?”

“Alhamdulillah!”
“Good wace?”

“Wai Yayan mu baka gane wacece ba?”
“Wallahi ban gane wace ba.”

“Nusaiba ce fa.”
“Oh Nusy ya kike ya Mama ai dazu ma munyi waya ya karatun?”

“Komai lafiya. Au shiyasa nace ni Bari na Kira na gaishe ka tinda Kai kaki.”
“Affuwan to bani da number kine ai.”

“Saboda baka dauken a kanwa ba ko?”
“No ba haka bane Kanwata.”

“To Yaya ne?”
“Aiki ne yai yawa kinsan bana samun zama daga wannan sai wannan.”

“Haba dai yakamata kuna Dan hutawa sannan ku dauren kuyi aure Dan ma Naga Yaya shi ya fara shiri.”
“Aure ai sai ku Kanwata.

“Kai fa?”
Yai murmushi yace
“Yanzu Ina aiki Zan kiraki later ki gaida min Mama please.”

“Ok Ina jiran kiran naka. Mama zata ji.”
“Nagode!”

Ya kashe wayar. Kai ya dafe sai Kuma ya koma kan system din sa da aiki.

Tin tana jiran call na shi har ta cire Rai Dan kwana biyu kenan tazarar da Kiran Sa da tayi.

Yana aiki wayar sa tayi Kara. Ya duba ya dauka ba tare da ya gane number ba yai sallama. Sai da ta lumshe Ido sannan ta amsa.

Shiru yayi Yana son tuna muryar Amman Ina sai kawai yace
“Wacece?”
“Wacece Kuma Yayan mu!”
Ta fada tana Yi kamar zatai kuka.

“Am sorry Kanwata ai ban dau muryar ba.”
Shagwabe murya tayi tace
“Ni dai Yayan mu bai kanwar Dani ko?”

“A’ah Kanwata kiyi hakuri kinsan yanayin abun namu.”
“Shikenan ya aikin?”

“Alhamdulillah ya gida da su Mama.”
“Duk suna lafiya.”

“Ya ckul fa?”
“Alhamdulillah!”

“Yauwah ana dagewa kinji Kanwata.”
“Naji Yaya nagode!”

“To sai anjima ko!”
“Kira nayi fa muyi Hira.”

Kai ya dafe yace
“An sorry Kanwata Zan Kira in na Gama aiki.”

“Haka fa kace ranan Kuma baka Kira ba.”
“Zan Kira wannan Karan insha Allahu. In ban Kira ba ki Tina min kinji.”

“To nagode!”
“Bye!”
Ya kashe wayar.

Ilai kuwa Sam ya manta Dan Sai da yai Shirin baccin wayar sa ta fara Kara dauka yayi Dan Bacci yake ji. Kunne ya Kai Yana sallama ta amsa tana fadin
“Na Tina maka.”

STORY CONTINUES BELOW
“Thanks let me call you “
Ya kashe ya fara neman layin nata. Bayan ya Kira ta dauka ta Kai kunne tana fadin
“Yayan mu ya aiki?”

“Alhamdulillah!”
“Masha Allah!”

“Kefa?”
“Nima haka.”

“Good!”
“Yaya Kai Dan wane kasa ne?”

“Kasar ki Mana.”
“Hmm kasan kana kama da larabawa.”

“Bana son tsokana kanwata.”
“Da gaske nake Yaya.”

“To ni Dan Nigeria ne mahaifi na Dan Hadeja ne Mahaifiyya ta ma haka. But mu fulani ne.”
“Good Kaine first born?”

“No am last born Autah kamar yadda kike Autah!”
“Baka kaini ba.”

“Hhh in nace nafiki kada ki Musa min.”
“Saboda me?”

“In Kika ganni Akan ciyar Hajiya ta Zaki zata Baby ne.”
Ta dauka hannu Akan Baki tana fadin
“Shine kake son ka kwacen Mama ko to daga Hajiyar ka har Mama nice Autar su.”

“Ki tsaya Wasa duk Zan kwace su ne.”
“Hhh haba dai.”

“Eh Mana.”
“Zamu gani.”

Yai hamma yace
“Kwanwata bakya Jin Bacci ne?”

“Ina tare da Yayan mu tayaya zan yi Bacci.”
“To ni dai bacci nake ji.”

“To Yaya sai da safe.”
“Allah bamu alheri.”

“Amin nagode!”
Sukai sallama. Daga haka kullum sai Nusy ta Kira shi tin tana takura Masa har ya fara sabawa sosai suka shaku da Junan su sosai.

Nusy Bata da magana a ko Ina sai Yayan mu kowa Yayan mu haka take sai dai baka zauna da ita ba.

A haka bikin Anwar yazo Amman Sam Fu’ad yace ba zai je Nigeria ha har fada sukai da Anwar ya tafi ya barshi Amman yaki ya bishi. Duk da komai na tsarin bikin dashi akai wasu event din ma shi yasa ayi shi.

Nusaiba ma tana can tana jiran zuwan Fu’ad Dan duk wayar da suke bai taba ce mata bazai zo ba. Dan haka ta tanadi lokacin Dan ta bashi kulawa ta musamman. Amman me a wajen dinner tai ta zuba Ido bashi. Wajen Yaya taye tace
“Wai Ina Yayan mu ban Ganshi ba.”

“Bai zo ba.”
Tai Dariya tace
“Wasa kuke min dai ko?”

Murmushi yayi Mai ciwo yace
“Zan miki wasa ne.”
Idon tane ya kawo ruwa. Ta bar wajen ta fita.

Sabir abokin Anwar dake son ta Wanda ita ta dauka Wasa ne na abokin Yayan ta. Yana tsaye yaga Nusy ta fita, Dan haka yabi bayan ta. A waje ya same ta tana kuka ya Karasa Yana fadin
“Subhanallah me ya faru sweetheart?”

Dogowa tayi hawaye na bin kumatun ta. Hannu tasa ta fara goge hawaye yace
“Wa yasaki kuka Beauty.”

Kai ta girgiza yace
“Kina son zuciyar sweetheart din naki ta fashe.”

“No Sweetheart ba komai fa.”
“Meyasa kike kuka to my beauty Kinga fa duk kin bata kwalliyar.”

Juyawa tayi. Ya koma gaban ta Yana leka fuskar. Tai murmushi ya amshi jakar ta ya bude yace
“Ga powder ungo shafa kinji ki koma yadda kike haka kawai za a bata wa sweetheart rai.”

Amsa tayi ta shafa yace
“Masha Allah Kinga My beauty.”

Tai kasa dakai. Yace
“Muje to.”
Suka koma ciki. Haka aka karasa dinner ba Dadi jikin ta a sanyaye

Da ta koma gida ta shige daki. Fara neman layin sa tayi sai dai duk Kiran da tayi bai dauka ba.

Haka ta hakura ta cire ta Kaya ta Shiga Tai wanka.

Lokacin da ta Kira yana asibiti dan sai da ya koma gida ya dauki waya ya shiga. Zama yayi a kan gado ya dauko system Dan zaiyi aiki wayar sa ya dauko ya Dan duba Abu anan yaga missed ba adadi.
Dubawa yayi yaga Anwar ne da Nusaiba. Hakika shi kan sa ya san bai kyauta ba. Fara neman layin Anwar yayi sai dai a kashe. Layin Nusy ya fara nema. Fitowar ta daga wanka kenan taji karar dauka tayi zata kashe wayar sai taga Fu’ad ne da sauri ta dauka ta Kai kunne. Sai kawai ta sakar Masa kuka.
“Ya salam me yake faruwa?”
“Yaya mu meyasa baka zo ba?”

“Am sorry Kanwata wallahi aiki ne ya rike ni.”
“Amman Yayan mu kwana biyu zuwa uku kawai.”

“Kiyi hakuri Mana Nusy nima naso nazo abinda Nan za a kawo Mana amarya Zan tsaya a wajen event din Nan da zamuyi da abokan aikin mu kinga au zai fi ko?”

“Ni Yaya mu da kayi shawara Dani bai yi ba.”
“To ayi Hakuri Kanwata.”

“Uhmm ni ba ruwa na da kai.”
“Haba Kanwata Yayan kine fa!”

“To ba Kai bane.”
“Ai na baki hakuri ko?”

“To na hakura yaushe zaka zo.”
“Sai wata Rana.”

“Kasa lokaci “
“Ba sai na saka ba Zan zo.”

“Ok shikenan.”
“Kije ki kwanta kinji.”

“Ok nagode.”
Haka aka gama biki Ango Anwar da amaryar sa Husnah suka tare satin su biyu suka daga.

Gida guda ya samu ya siya aka saka duk abun bukata. Yaso su tare da Fu’ad Amman kememe Fu’ad yaki aminta.
Da suka sauka a airport Fu’ad yaiwa text Nan Fu’ad yaje dauko su. Suna zuwa suka rumgume juna. Fu’ad yace
“Allah Sanya alheri friend kayi hakuri.”

Janye shi yayi yana hararar sa. Ya kalli Husnah yace
“Amarya barka da zuwa.”

“Yauwah aminin Ango muna fushi.”
“Haba dai Amarya ke da Zaki bashi Baki.”

“Ba Zan amsa ba.”
Anwar ya fada. Husnah tace
“Da Wasa nake ba ruwa na ai kun fi kusa.”

Anwar yai gaba. Husnah da Fu’ad suka bi Bayan sa suna Hira. Mota suka Shiga suka tafi. Gida suka Shiga shi Kuma ya tafi bayan ya Kai musu kayan abinci.

Kwanan su biyu da dawowa akai party na abokan aikin Anwar Nan aka watse.

*
Yana office yana aiki Anwar ya Shiga. Tsayawa yayi a jikin kofa yana fadin
“Ka tashi muje muci abinci ko?”

“Abinci kuma haba dai. Kaje kawai ni bana Jin yunwa.”
Waje Anwar ya samu ya zauna yana fadin
“Kamun abubuwa da yawa Ina dauke Kai daga wannan in Kai min ba ruwana da Kai wallahi da gaske nake!”

“Me nayi Kuma?”
“Many things Kuma Kai ma ka sani ka tashi mu tafi .”

Mikewa yayi yace
“Muje kada ka cinye ni.”

Suka fita. Fu’ad yai driving har gidan. Suna Shiga suka samu Husnah taci kwalliya ta mike tana fadin
“Ah ah ah yau waye a gidan?”

“Husnah bana son haka fa kada ki Kara hada mu please.”
Anwar yai ciki yace
“Ai ba sai ta hada ba mun Gama haduwa ma ko Sweetheart?”

Kai ta gyada. Fu’ad yai kwafa yace
“Zan dauko Nusy tana shigar min.”

“Ayyah Nusy ba abinda zata shigar maka dama dai Fateema ce.”
Nan take mood din Fu’ad ya canja.

Anwar yace
“Kaga tashi muje muci abinci nasan zaka shiga school ko?”

Kai ya gyada. Suka karasa. Husnah tayi serving nasa sannan ta barsu.

Haka komai ya dinga tafiya Nusaiba da Fu’ad sun shaku sosai a dayan bangaren Kuma Sabir na ta budirin sa Amman Sam Nusaiba Bata San Yana Yi ba ita ta Fu’ad take kamar yadda Shima bai San tana yi ba.

Haka suka dinga rayuwa na tsawon shekaru. A shekarun nasarori masu yawa sun same shi. Ya hada karatun sa inda ya zama likita ga business da yake Yi.

Abin da yasa yaji Yana son tafiya gida shine da zarar ya kwanta bai da aikin yi sai mafarkin Fateema. Gaba daya bai da sukuni

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *