WA NAKE SO CHAPTER 26
Www.bankinhausanovels.com.ng
Abin da yasa yaji Yana son tafiya gida shine da zarar ya kwanta bai da aikin yi sai mafarkin Fateema. Gaba daya bai da sukuni ya zama
Duk sai a hankali damuwa tai Masa yawa. Wanda daga haka ta tayar Masa da ciwon sa kwaf daya tai masa ta kwantar dashi
Anwar ne ke ta Kai komo Akan sa Wanda Anwar ganin jikin nasa yai tsanani yasa ya same shi yace
“Fu’ad ya kamata iyayen ka su San a halin da kake!”
“Nima nayi wannan tunanin kada na mutu ba tare da wani nawa ba.”
“A da in nace ka ban address din ka kana ki Amman Dan Allah yanzu ka bani address din ka!”
“Zan baka Anwar Amman Ina son in kaje ka daukon Hajiya ta kawai!”
“Kada ka damu Amman tayaya Zan tafi na barka anan.”
Tari yayi yace
“Haba Anwar kada ka damu kasan Yan uwan mu Suma suna tsaye akai na. Ga Nura da Abdul Nan duk suna kula Dani kaje ka kawon Hajiya!”
“Shikenan bani address!”
Nan ya bashi. Hakan yaje yai booking flight inda washe gari zai tashi.
Hakan ya tafi ya bar Husnah da Fu’ad tare da su Nura inda suke kula da Fu’ad.
Lokacin da ya sauka a Nigeria ya Kara Hawa jirgi ya tafi Kano. A hotel ya sauka Dan shigar dare yayi. Sai da ya kwana washe gari da safe ya nufi gidan su Fu’ad.
A gate ya tsaya yasa aka fadawa Hajiyar Fu’ad tayi bako. Nan ta fito sanye da hijab. Tana ganin sa ta saki murmushi tana fadin
“Sannu da zuwa!”
“Yauwah Hajiya!”
Ya fada Yana durkusawa tace
“A’ah tashi mu shiga ciki tukkuna.”
Tayi gaba yabi Bayan ta. A falo suka zauna ya zauna a kasa yace
“Ina yini Hajiya?”
“Alhamdulillah ya kake ya gida?”
“Alhamdulillah!”
Ta mike ta shiga kitchen sai gata Nan ta fito ita da wasu yan Mata. Suka fito hannun su rike da plate ba lemo. Suka dire mishi.
Hajiya tace
“Bismillah!”
Yace
“Nagode!”
Ya Sha lemo kadai. Tace
“Amman ban gane ka ba!”
“Eh Hajiya Baki sanni ba.”
“Toh!”
“Fu’ad ne ya Aiko ni!”
“Fu’ad da gaske Fu’ad Dina?”
Kai ya gyada yace
“Tin da ya bar kasar Nan da wata uku Muna tare, tare muke rayuwa.”
“Ikon Allah Yana lafiya dai ko?”
“Eh toh! A yanzu dai bashi da lafiya dalilin zuwa nawa ma kenan.”
“Ya salam me yake damun sa?”
“Ciwon sa ne ya tashi!”
“Wane ciwo Fu’ad din yake fama dashi?”
“Hajiya ki kwantar da hankalin ki da sauri. Jiya na sauka ya nazo yau Zan maki Visa zamu tafi tare sai kiga a yadda yake yanzu dai Zan Baki number sa.”
Ya dauki waya ya nemi number Husnah ta dauka tana fadin
“Dear ka sauka lafiya?”
“Alhamdulillah kina Ina?”
“Yanzu nazo asibiti kawowa Fu’ad abinci!”
STORY CONTINUES BELOW
“Masha Allah bani shi.”
Ta mikawa Fu’ad waya. Amsa yayi yakai kunne yace
“Bro ya hanya?”
“Alhamdulillah gani a dakin Hajiya!”
Da sauri ya mike zaune sai Kuma tari nan ya dinga tari wayar Husnah ta amsa Fu’ad ya dinga tari. Hannu ya saka ya rufe Baki Yana tarin Yana lafawa ya dauke hannun sai yaga jini a tafin hannun sa.
Ido Husnah ta zaro. Tana fadin
“sannu!”
Fu’ad ya lumshe Ido ya bude ya dauki tissue ya goge hannun sannan ya kalle ta yace
“Kira min Anwar!”
Wayarta ta dauka ta fara neman layin nasa. Tana fara ringing ta ya dauka ta mikawa Fu’ad. Fu’ad yace
“Bawa Hajiya muyi magana!”
Yace
“Toh!”
Sannan ya mikawa Hajiya. Amsa tayi takai kunnen ta.
“Hajiya ta!”
Ya fada murna a sanyeye.
“Na’am Fu’ad Kai ne Fu’ad!”
“Nine Hajiya ya kike Hajiya Ina Fateema!”
“Lafiya Lou Fu’ad. Fateema tana nan jiya tazo min. Tazo ta gaishe Dani.”
Ido ya lumshe yace
“Hajiya ya Fateema take?”
“Tana lafiya Fu’ad ya jikin?”
“Da sauki Hajiya ta. Hajiya ta Fateema tana lafiya kuwa Ina mafarkin ta a wani Hali Hajiya ki fadan Dan Allah ya Fateema take “
“Ka kwantar da hankalin ka Fateema tana nan lafiya.”
Zai magana sai tari daga Nan ya mikawa Husnah waya ta fita ta Kira likitoci.
Hajiya ta kalli Anwar tace
“Har yanzu Fu’ad bai bar zancen Fateema ba!”
“Hajiya Fu’ad ba da Wasa yake son Fateema ba.”
Nan yai ta bata labarin tin haduwar su da Fu’ad sai da Hajiya Tai hawaye Dan tausayin Fu’ad.
Bayan ya Gama tace
“Itama yarinyar baka ga halin da ta Shiga ba na rashin Fu’ad yanzu bata Dade da aure ba. Yarinyar tana da hankali wannan kawai kaddarar suce Allah yasa hakan shine mafi alheri domin kuwa ban ga ta yadda Fu’ad da Fateema zasu rabu da juna ba. Sai hukuncin Allah. Jiya jiyan Nan tazo ta gaishe ni. Ni kaina Ina son Fateema da Fu’ad Amman Allah yasa ba zasu kasance tare ba.”
Kai Anwar ya girgiza yace
“Allah sarki. Allah yasa haka ne mafi alheri!”
“Amin!”
Yace
“Bari naje na fara Samar Miki visa.”
“Ka tsaya kaci abinci an kusa gamawa!”
Kai ya shafa yace
“Hajiya gwara naje can da wuri Dan a Gama komai da wuri.”
“To Amman Dan Allah ka dawo kaci abincin!”
“Insha Allahu!”
Nan ya mike ya fita. Bai dawo gidan ba sai da ya gama komai sai Bayan magariba ya dawo. Ya aika acewa Hajiya Anwar ya dawo tace maza aje ace ya shigo.
Anan Falo ya zauna ta fito ta same shi ta zauna tana fadin
“Ai Ina ta zuba Ido “
“Wallahi Hajiya abin ne da wuya.”
“Sannu Allah maka albarka.”
“Amin nagode!”
Masu aiki ne suka hau kawo Masa kayan abinci kala kala. Aka jera Hajiya ta mike tace
“Kaci kaji Bari na shiga daga ciki.”
Tayi ciki yaci ya koshi. Yana cikin ci aka Kira sallah kan ya gama an idar. Dan haka anan falo yai sallah.
Hajiya ta fito ta same shi zaune tace
“Sannu Anwar ka koshi ko a Samar maka wani Abu!”
“Ah Hajiya wallahi Alhamdulillah na koshi.”
“Kai dai!”
“Na koshi.”
Mikewa tayi ta bude firij din dakin ta dauko kwanon Sha ta ajiye Masa a gefen tace
“Ga fura to!”
Ciki ya shafa yace
“Hajiya Fura Kuma ina son Fura Dan na jima rabo na da ita sai dai ciki na ya cika.”
“Sai a ajiye zuwa da safe.”
“Godiya nake Hajiya.”
Ya fada ya fara tattara kayan wajen yace
“Ni Zan tafi sai gobe Zan shigo na gaishe ki jibi ne tafiyar mu.”
STORY CONTINUES BELOW
“Ah haba dai. Ai anan zakai zaman ka ko akwai Wanda ka sani ne?”
“A’a na sauka a hotel ne.”
“A’ah a’ah anan zakai zaman ka ga dakin su Fu’ad nan Yana Nan kullum ana gyara shi Kai kadai zakai zaman ka.”
Kai yai kasa dashi tace
“Tashi muje kaga dakin kaji!”
Mikewa tayi ta mike. A jikin dakin Hajiya dakin Fu’ad yake na da. Falo ne da bedroom da toilet har da karamin kitchen.
Suka Shiga tace
“Gashi nan kayi manaji da dakin abokin naka. In akwai abinda kake bukata sai kayi magana.”
Durkusawa yayi yace
“Godiya nake Hajiya Allah saka da alheri.”
“Amin nagode! Sai da safe.”
“Allah bamu alheri.”
Ya rako ta har bakin kofar dakin ta ta shiga ta rufe ya juya ya koma ya rufe kofar sa. Wanka yayi sannan ya dauki kayan Fu’ad ya saka ya wuce kan gado ya kwanta.
Waya ya dauka ya Kira Husnah nan sukai waya yace
“Baby kin koma gida?”
“Na koma Dear jikin Fu’ad ne ya tashi!”
“Ayyah ya jikin?”
“Kan na dawo ya dawo dai dai Yana ta Bacci.”
“Masha Allah. Zan Kira asibitin naji ya jikin nasa.”
“Ok ya garin?”
“Alhamdulillah jibi zamu dawo.”
“Allah dawo daku lafiya.”
“Amin”
Hakan suka cigaba da soyayya sannan yace
“Bari ya Kira Fu’ad kan yai Bacci.”
Kira asibiti yayi ya Kira Nura ya Kai yace
“Kana asibiti ne?”
“Eh Ina tare da Fu’ad!”
“Thank God shi nake son nai magana dashi kenan.”
“Ok Bari na bashi wayar.”
Ya Mika Masa wayar.”
“Bro ya Hajiya ta? Ina Fateema?”
“Suna lafiya Bro ka kwantar da hankalin ka.”
“Shikenan kaga Fateema?”
“No Bro ban ganta ba.”
“Yaushe zaku dawo?”
“Jibi!”
“Please kaje ka gano min ita”
“To zanje ka kwantar da hankalin ka zanje. Ya jikin?”
“Da sauki.”
“Gani a dakin ka na da.”
“Haba a gida kake Ashe. Ya garin namu?”
“Alhamdulillah!”
“Ok ya kamata ka zagaya shi gobe. Ka nemi Sani cousin din Fateema Zan maka sending number sa.”
“Ina jira sai anjima ko?”
“Nagode!”
*
Washe gari Anwar ne ya dauki Hajiya ya Kai ta taiwa ya’yanta sallama duk ta fada musu zata wajen Fu’ad kowa ya dinga Masa addu’a manyan ya’yanta maza biyu suka ce tare zasu taho.
,*
Washe garin ranar gaba dayan su suka daga. Lokacin da Hajiya taga Fu’ad kwance yana bacci kuka ta saka dan Dan kwanakin da yai ba lafiya kadai yasa duk ya Kara ramesa sai Wanda ya Ganshi
Ido ya bude yana ganin Hajiyar sa ya mike Yana fadin
“Hajiya tah!”
Ya bude hannayen ya rumgume ta yana fadin
“Hajiya ta ki yafe min!”
Hannu ta daura akan sa tace
“Na yafe maka Fu’ad ban rike ki ba. Allah baka lafiya!”
Yaya Ado da Yaya Baffa suka karaso suna fadin
“Sannu Fu’ad!”
Ya gyada masu Kai. Anwar ya karaso Yana murmushi hannun sa ya Kama Yana fadin
“Ya jikin?”
“Da sauki!”
Ya Kama hannun ya duba ya duba idon da. Yace
“Wake kula da Kai?”
“Nura ne?”
“Ok Bari na Kira sa naji ya condition din naka. Ga Hajiya Nan ko?”
“Nagode Friend no ba komai!”
Ya juya ya fita. Wayar sa ce tayi Kara ya zaro yaga Nusaiba ya dauka yace
“Ya dai Sister?”
STORY CONTINUES BELOW
“Yaya kwana biyu ya kake ya Anty na?”
“Duk lafiya. Yasu Mami?”
“Suna lafiya!”
“Masha Allah.”
“Yaya Ina Yayan mu kwana biyu wayar sa a kashe!”
“Ayyah yana kwance ba lafiya ne!”
“Meyake damun sa. Ya jikin nasa? Ka hadamu please!”
“Da sauki fa. Yanzu Yana ciki shi da Hajiyar sa sai zuwa anjima!”
“Ok Dan Allah ka hadamu.”
“Insha Allahu “
A bakin kofa suka hadu da Nura ya ja baya Yana fadin
“Wai har me?”
“Mun dawo!”
Ya koma office yana fadin
“Ya hanya?”
“Alhamdulillah. Ya jikin Bro?”
“Da sauki. Dazu Abdul ya duba shi ai.”
“File nasa nake son gani ai!”
“Ok!”
Ya dauko yace
“Gashi Amman Fu’ad na fama da ciwon zuciya fa”
“Na sani ya kaga stage din da yake.”
“Gaskiya abin yayi yawa tayaya yaci jikin sa haka.”
Kai ya girgiza yace
“Allah dai ya bashi lafiya. Tare muke da Hajiyar sa da Brothers nasa.”
“Oh haba muje mu gaishe su ko?”
“Ok muje!”
Suka mike suka fita. Anwar r8ke da file din Fu’ad. A bakin kofa suka hadu da Abdul zai shiga dakin da Fu’ad yake.
Suka gaisa da Fu’ad Yana fadin
“Ka dawo lafiya?”
“Alhamdulillah ya aiki ya me jikin?”
“Da sauki!”
“Masha Allah! Muje Hajiyar Fu’ad na ciki da yayen sa.”
“Oh really muje yau dai zamuga iyayen Fu’ad!”
Suka Shiga. Har kasa suka gaishe da Hajiya da yayen Fu’ad sukai wa juna ya Mai jiki sannan suka fita.
Suna zaune Husnah ta shigo da kayan abinci. Har kasa ta gaishe da Hajiya da yayen Fu’ad. Fu’ad ya nuna ta yace
“Hajiya ga matar Anwar fa!”
“Ah Masha Allah! Allah bada zaman lafiya.”
“Amin!”
“Hajiya kizo kije ki huta ko?”
“Gaskiya Kam!”
Husnah ta fada.
Yace
“Yaya Kuma kuzo muje ku huta ko?”
“Ah ah zamu zauna a hotel!”
“Haba dai Yaya ko gida na ya ishe ku bare gidan Fu’ad da yake Kato.”
“Ai gwara mu sauka acan din!”
“A’ah Dan Allah kuzo muje “
Ba yadda suka iya suka bi Anwar. Daki guda aka sauki kowa aka bashi kayan abinci da komai. Shima ya samu ya kebe da matar sa da sukai missing juna.
Da yamma ya kuma wajen Fu’ad da ya ce zai kwana Fu’ad ya Hana yace ga Abdul Nan Yana dutyn dare su kyale shi yaje ya huta da matar sa.
Washe gari ya daura sa akan magunguna. Da dare Bayan su Hajiya da Yaya Sani sun tafi ya kalli Fu’ad dake shan tea yace
“Bro a yanzu mun wuce abokai Dan haka Ina son in baka shawara ka dauka.”
“Me ya faru?”
“Kai likita ne kuma nasan kasan sign din abinda ke damun ka Dan haka zuciyar ka tana cikin matsanancin Hali Dan haka dole ka kula me yake saka ka tunani ka fada min?”
“Rashin sanin a halin da Fateema take ciki!”
“indai haka ne ka kwantar da hankalin ka domin a Dane Fateema ke cikin matsanancin Hali. Ke flda Fateema Kuna son juna Allah ne ya kaddarta muku rabuwar ku ba Dan bakwa son juna ba. Amman Hajiya ta bani labarin komai Dan Ranar da naje ma kwanan ta daya da zuwa ta gaishe ta. Mun hadu da Sani ya bani labarin Mai yawa akan Fateema hakika Fateema na son ka Kai ne ka kasa ganewa a Baya Kai abinda kake ganin shine solution Amman ba haka bane.”
“Ya take yanzu?”
“Tana lafiya tayi aure watanni da suka shige tana zaune lafiya Kuma tana aikin ta!”
“Alhamdulillah damuwa ta kenan. Damuwata shine na San Ya Fateema take. Allah ka cigaba da Bata farin ciki da kwanciyyar hankali!”
STORY CONTINUES BELOW
“Amin Bro! Sai Abu na gaba!”
“Inaji.”
“Since you know how is Fateema doing sai ka tsaya wajen kaima Gina rayuwar ka.”
“Me ya rage min a duniya Bro mutuwa kawai nake jira tinda Naga Hajiya ta sa min albarka Fateema na cikin kwanciyar hankali to ni me Zan nema Kuma.”
“Jin dadin rayuwa da cigaba da farantawa Mahaifiyar ka ta neman aljanna.”
Ido ya runtse. Anwar yace
“Dan ka Rasa Fateema bashine yake nuni da ka rasa komai ba a yanzu kaima zaka fara rayuwa cikin Jin Dadi tinda ka San halin da take yanzu ne zakai aure kaji Dadi Kai ma.”
“Aure Anwar? Aure fa kace?”
Kai ya gyada.
Fu’ad yace
“Never Bro never ba zan taba aure ba in ba Fateema ba. Dan Fateema aka Yi ni kawai tinda ban samu Fateema ba kuwa babu wacce Zan aura jikina da zuciya ta da komai nawa na Fateema ne ita kadai nake gani a matsayin mace duk wata mace Namiji nake ganin ta. Anwar kasan yadda nake son Fateema kuwa. Fateema duniya ce wallahi ko Kai ka same ta ba zaka so rabuwa da ita ba. Ka tayani addu’a Allah ya bani dangana Kuma Allah yasa na jure da cire ta a Raina Dan a yanzu ta zama matar wani. Wani ya zama mijin Fateema.”
Ya karasa maganar Yana dafe zuciya.
Anwar yace
“Ka gani ko? Ni so nake ka cire damuwar condition din da kake ciki yai tsamari yadda Shan magani ba zai taba magance problem din ba sai dai an hada da gudunmawar ka shine ka na danne komai kana cire abubuwa a zuciyar ka.”
“Tayaya zan na cirewa Anwar wallahi da da yadda Zan Yi da na jima da cirewa ko Dan Kai ma.”
“Shikenan yanzu ma Dan Allah, Hajiya Dani da Fateema ka cire damuwa.”
“Zanyi kokari insha Allahu nagode Bro. Nagode Bro Ina son ka.”
“Mene na godiyar kada ka damu!”
Ya rumgume shi Yana sauke ajiyar zuciya kawai
*
Tin daga lokacin ya cire damuwa ba Dan komai ba sai Dan yadda yaga Hajiyar sa na damuwa Kuma Shima baya son Yana Bata Mata rai. Dan haka ya dauki shawarar Anwar.
Yaya Ado da Yaya Baffa suka koma suka bar Hajiyar. Bayan an sallame sa gidan Fu’ad ya koma yaso ya dauke Hajiya Amman Anwar da Husnah suka ki.
Satin sa daya da warkewa Sai ga Mamin Anwar Nan da Nusaiba. Nusaiba ce ta dage ita dan dole suka zo duba Fu’ad. Lokacin Fu’ad na daki a kwance Anwar ya Kira shi.
Dauka yayi yace
“Bro ya naji voice din ka haka ne?”
“Bacci nake!”
“Ayyah na zata ka tashi kazo gida!”
“Ok gani Nan!”
Ya Mike ya Shiga yai wanka. Ya fito ya shirya yai tsaf dashi.
Gidan Anwar dake gefen nasa ya karasa, sannan ya shiga. Tin daga kofar falo yake Jin hayaniya yai mamaki Dan yasan ba Wanda zai zo.
Ciki ya shiga da sallama. Tana Jin muryar sa ta mike Tayo wajen sa tana murmushi. Yana shiga yai tozali da ita. Kallon juna suka tsaya Yi yace
“Kanwata ya kike?”
Baki ta turo tace
“Yayan mu ka rame ya jikin?”
Kai ya shafa ya kalli dakin ya hango Hajiyar sa da Mami. Yayi ciki Yana fadin
“Bari naje na gaida su Mami na.”
Ya karasa ya durkusa aka kasa yace
“Ina kwana Mami ya hanya?”
“Alhamdulillah!”
“Ya jikin?”
“Alhamdulillah!”
Ya kalli Hajiya yace
“Ina kwana Hajiya?”
“Alhamdulillah yau Bacci Kai tayi ne haka?”
“Wallahi jiya ban kwanta da wuri ba!”
“Me kake haka?”
Mami ta tambaya. Kai ya shafa yace
“Aiki nayi.”
“Ayyah da ka Bari ka Kara Jin dadin jikin!”
“Ai jiki yai sauki Mami.”
“Amman ka rame fa.”
Kai ya shafa. Nusy da ta karaso yace
“Wallahi Mami duk yai Baki ya rame.”
“Sannu Yayah!”
“Yauwah.”
Ya mike yai dining yana fadin
“Yana Ina ne nifa yunwa nake ji.”
Nusaiba ta karasa tana fadin
“Shiryawa yake. Yayan mu yabjiki?”
“Naji sauki Kanwata.”
Ta bude fulas tai serving nasa ya fara ci. Ta zauna ta zuba Masa Ido.
Yana cikin ci ya dago Yana kallon ta. Tai murmushi tana fadin
“Yayan mu!”
“Ya akayi ne Kanwata!”
“Uhmm……”
“Ashe kazo!”
Anwar ya fada Yana karasowa. Yace
“Wallahi yau wani Bacci nasha.”
“Maganin da kake Sha ne ko?”
“Eh to Kuma jiya banyi Bacci ba Ina ta research akan wani Abu.”
Dafa kafadar sa yayi yana fadin
“Kana hutawa dai yaushe ka tashi a ciwon.”
“Haba sai kace ba jarumi ba. Ai naji sauki.”
“Haka nake so. Zaka zo mu fita ne?”
“No Mami tazo sai na Sha dumin ta.”
“Gaskiya Kam Yayan mu ka zauna muyi hirar mu.”
“Yauwah Kanwata.”
Ya mike yai falo. A gefen Mami ya zauna. Nusaiba tayi gefen Hajiyar Fu’ad tana fadin
“Ai na fada maka Nima sai na kwace maka Hajiyar ka.”
Ta kalli Hajiya yace
“Hajiya kingan shi ya kwacen Mami Nima na kwace ki.”
Mami tace
“Wa zai dauke ki.”
Hajiya tace
“Gani Nan.”
Fu’ad yace
“Mami kyale ta ya kuka zo ya hanya? Ya Nigeria?”
“Alhamdulillah! Komai lafiya.”
“Masha Allah.”
A haka sukai ta Hira har Anwar yazo yai musu sallama aka bar su da Husnah.
Can wajen twelve Nusaiba da Husnah suka tafi kitchen Dan yin abincin rana. Aka bar Mami da Hajiya da Fu’ad kawai. Suna ta Hira abinsu. Bayan sun dawo ya fita ya koma gida
Bai koma ba sai yamma. Mami da Hajiya ya sama a falo yace
“Sannun ku da hutawa!”
“Yauwah Ina kaje ne?”
“Naje na hutane.”
Nusaiba ce ta fito tana fadin
“Yayan mu kazo ka zaga garu Dani!”
“Akan me shi da baya Jin dadi.”
Hajiya tace
“A’ah dan dai ya zagaya da ita.”
“Ba inda zai Kai ta.”
“Dan Allah Mami!”
Fu’ad yace
“Hajiya Bari na Kai ta in ba haka ba bazata bar ni na huta ba.”
Ya mike yace
“muje ko?”
“Yayan mu baka ci abinci ba.”
“In na dawo naci.”
“Ok!”
Tayi ciki a guje Bata Dade Bata dawo sanye da mayafi. Ya mike yace
“Hajiya sai anjima.”
Ya kalli Mami yace
“Mami sai mun dawo.”
“Allah kiyaye!”
Suka amsa Masa. Ya juya ya fita. Nusaiba tabi Bayan Sam
Sosai suka zagaya garin gab da magariba ya Kai ta Tayo shopping karfe shida suka dawo gida. Motar Anwar ya gani yace
“Anwar ya dawo kenan.”
“Yes ga motar sa nan ma.”
Yai parking ya fita ta fito suka Shiga ciki. A falo suka same su dukka. Ya Shiga da sallama ya zauna Yana fadin
“Mun dawo!”
“Ina kaje!”
“Ga wacce ta sata yawo Nan.”
Mami ta fada.
Hararar Nusaiba yayi yace
“Kai ina ruwan ka da Kanwata tashi kije ki Yi sallah kinji.”
Ya mike ya fita. Anwar yabi bayansa
Tare sukai sallah sannan suka fito suna hira abinsu.
Anwar yace
“muje kaci abinci ko?”
“Bana Jin cin Abu Mai nauyi zanje na Sha tea sai na kwanta!”
“Why?”
Kai ya dafe yace
“Sai a hankali Kam!”
Suna kaita asibiti aka shiga emergency da ita. Tare aka shiga da Aliyu dan sam yaki sakin ta. Hannun ta cikin nasa aka shiga da ita ya daura ta akan hado. Yana zaune a gefen ta yana ta mata addu’a yana gyara mata gashin kan ta. Kan kace me likitoci sun rufa a kan ta kowa akwai abinda yake yi.
Sun debe awa biyu akan ta sannan suka gama aka sa a canja mata gado. Sai anan sukaga jini ya fara zuba a jikin ta. Da sauri aka canja mata gado suka makala mata oxygen ya fara janyo numfashin ta. Haka suka ci gaba sai karfe biyun dare suka gama bayan sun mata allurar bacci tare da fadin insha Allah zata farka lafiya.
Suka fita suka bar Aliyu dake zaune rike da hannun ta daya an saka mata ruwa daya na hannun sa. Kissing hannun nata yayi ya daura kan da akan gadon da take.
Maryama ce ta shigo dakin a bakin kofa ta tsaya idon ta jajir saboda kukan da ta sha. Aisha take kalla yadda duk ta fita hayacin ta ga oxygen dake makale a hancin ta. Mujahida ta shigo tayi ciki itama daga ganin idon ta tayi kuka.
“Sannu Anty Allah tashi kafadun ki.”
Aliyu ne ya dago idon sa duk hawaye yasa hannu ya goge. Maryama ta karaso da kyar ta dafa shi tana fadin
“Kayi hakuri Yaya zata tashi insha Allahu.”
Hanmun ta ya kama yana fadin
“Maryam she is bleeding kar naje na kara rasa wannan cikin yaya zanyuli i love him.”
“Insha Allahu yana nan Yaya ka daina kuka.”
Tasa hannu tana share masa ido. Yace
“Kalle ta fa Maryam kamar gawa dazu muka gama magana ta shiga fa tai wanka muje amsar kunu amman yanzu kalle ta”
Take zuciyar su duk ta kara tsinkewa. dan in da mutuwa ce ma da shikenan haka za a ce ta mutu. Juya masa baya Maryama tayi hawaye na zuba a idon ta. Mujahida ma haka. Shu’aibu dake bakin kofa ya shigo yana fadin
“To me kukan zai kara mata. Addu’a zakuyi mata kawai Allah tashi kafadun ta.”
“Amin Amin!”
Suka fada gaba daya. Gaba dayan su a asibitin suka kwana kowa yana kan sallaya. Aliyu in yai sallar sai ya dawo ya kama hannun ta ko yai huging ko kuma yai kissing nasa. A haka har akai sallar asubahi da kyar ya iya tafiya masallaci. Yana idar wa ya dawo dakin da suke.
*
A firgice Mamah ta mike tana salati. Dakin ta fara bi da kallo dan mafarkin da taui na Aisha na cikin wani mawuyacin hali. Zuciyar ta ta dafe ta fara neman layin Aliyu amman meta kira yafi sau goma baa dauka ba.
Maryama ta kuma kira itama ba a dauka ba Mujahida ta nema itama same take hankalin ta ya tashi ta mike tayo alwala dan har an shiga masallaci tana idarwa ta saka kaya kawai ta nufi bangaten mai martaba. Dawowar sa daga masallaci kenan suka hadu a kofar part din sa. Kallon ta yayi yace
“Lafiya Hajiya?”
“Ina fa Lafiya Alhaji nayi mafarkin Aisha wallahi da matsala.”
“Haba Fulani wa ya fada miki mafarki gaskiya ne.”
“Hmmm ni dai nazo na fada maka yanzu zan wuce can.”
“Haba Fulani ki bari ba kince za a kira su yau ba.”
“Tayaya za a kira su duk ina kira ba wanda ya dauka. Dan Allah kai min izini yanzu na tafi.”
Numfashi yaja yace
“Muje.”
Suka fita. Waya ya dauka ya fara neman layin drivern sa. Yana dauka yace
“fito da mota gamu nan karasowa.”
STORY CONTINUES BELOW
Kan su karasa ma har ya karaso dan haka suka shiga sai garin su Aliyu. Karfe takwas a bakin gate din gidan Aliyu tai musu dan yadda suke gudu kamar me? Suna shiga sukai parking mai gadi ya zo suna gaisawa.
Mamah ta nufi ciki sai dai me ba kowa a gidan da sauri ta fito tana fadin
“Ina mutanrn gidan?”
Mai gadi yace
“Eh toh tin jiya da dare suka fice basu dawo ba.”
“Innalillahi wainna illahir rajiun!”
Mamah ta fada ta zube a kasa tana sakin kuka. Abbah ya karasa yana fadin
“Menene haka Hajiya?”
“Wallahi mafarki na ya tabbata Alhaji. Yau ya zanyi in Hafsa ta rasa Aisha la’ilaha illah muhammad rasulillah Salllahu alaihi wasalam.”
Ta fada tana kara fashewa da kuka.
*
Ganin safiyya tayi yasa Maryama da Mujahida tafiya dan suyo abin da za a ci kada Aisha ta tashi itama tana bukatar abinci.
Nan suka tafi. Horn din su ne yasa mai gadi kowamawa bakin gate dan ya bude yana budewa Maryama taga su Mamah ta karasa tayi parking a guje ta fito Mamah na ganin ta, ta mike Maryama tazo ta fada jikin ta sai ta fashe da kuka.
Mamah tace
“Maryama ina yar uwar ki?”
“Mamah tana asibiti….”
Sai ta kara sakin wani kukan. Bayan ta Mamah ta hau shafawa.
Mujahida ta karaso Abbah yace
“Me yake faruwa ne Mujahuda?”
“Anty Aisha ce ba lafiya.”
“Me yake damun ta?”
“Ciwon ciki ne tin dai jiya bata farka ba.”
“Yanzu tana asibiti?”
Kai ta gyada. Abbah yace
“To muje muga jikin ko?”
Maryama ta mike ta shiga mota Tace Mujahida ta hada abincin. Suka tafi.
*
Suna zaune Aliyu ya zubawa Aisha ido Dr ya shigo. Gaisar da Aliyu yayi ya bude file yana dube dube. Can ya dago yace
“Har yanzu bata farka ba.”
Kai ya gyada masa. Yai rubuce rubuce yace
“Garin yaya ta sha wannan maganin?”
“Wane magami kenan?”
“A gaskiya a binciken mu ya nuna ta sha maganin zubar da ciki.”
Da sauri Aliyu ya mike yana girgiza kai. Dr yace
“Shi ya sa ga shiga wannan halin.”
“Karya kake Aysher ba zata ta taba shan abinda zai zubar da cikin ta ba.”
“Ba dai ka sani ba mata ai ba a iya musu kila bata shirya haihu….”
Wani mari Aliyu ya sakar masa yana nuna sa da yatsa yace
“Kada ka kara cewa matata zata zubar da ciki…”
Abbah ne ya shigo ya samu Dr dafe da kunci ya karaso da sauri yana fadin
“me ya faru Aliyu?”
Jikin Abbah ya fada yana fadin
“Abbah wai Aysher tace zata zubar da ciki dan Allah Abbah tayaya?”
Mamah da Maryama dake bakin kofa suka kafe a wajen suka kasa shigowa. Abbah yace
“Shine ka mare shi.”
Dr yace
“Am sorry sir.”
Ya kalli Abbah yace
“Naga shi baya cikin nutsuwar sa. Ina fada masa abinda ya faru da matar sa ne.”
“Me ya faru?”
“Abbah ya tambaya.
“Munyi gwaje gwaje mun gane tasha maganin zubar da ciki ne.”
“What? Cikin ya zube?”
Mamah ta fada tana karasowa gaban Dr.
Kai ya girgiza yana fadin
“Am sorry to say…..”
Shako sa Aliyu yayi yana fadin
“Kada kace cikin nan ya zube dan Allah kada ka fada.”
Abbah ya cire hannun Aliyu a wuyan Dr yace
“Aliyu ka nutsu mana.”
“Abba dan Allah kada cikin nan ya zube na rasa wancan kada na rasa wannan shima.”
Mamah tace
“Shikenan Sha’awa da Momy sunyi abunda suke so burin su ya cika.”
“Me kika nufi Mamah?”
Aliyu ya fada yana tasowa daga jikin Abbah. Mamah yace
“Jiya Hajara tazo min da zancen taje wajen Momy taji tana waya Sha’awa zata sakawa Aisha maganin zubar da ciki shiyasa na kira nace kada Aisha taci komai na gidan nan naku.”
STORY CONTINUES BELOW
A zabure ya mike yayi waje Abbah na kiran sa amman ina sam baya ji yana fita ya samu wani securuty nan ya ce
“Kai ni gida.”
Ya wuce ya bude mota ya shiga ya tafa motar tin yana driving slowly yace yayi gudu ya kara wuta amman gani yake kamar ba gudu yake ba daga baya sa shi yayi yai parking ya amshi motar ya bar wajen a guje.
*
Mujahida na shiga ta wuce kitchen ta bada order abinda za a girka tana tsaye suna aiki Sha’awa ta shigo. Wani kallon banza ta watsa mata tace
“Ya da kallo ne?”
Mujahida bata kula ta ba ta fice dan yin wanka. Tea ta hado ta dawo falo ta zauna sai ta fara tunanin
“To ya Aisha take cikin ya zube ko yaya?”
*
Abbah na ganin fitar Aliyu yabi bayan sa sai dai kan ya karasa har ya bar wajen. Gun driver sa ya karasa yace
“Bi min bayan sa.”
Suka dauki hanya.
*
Yana zuwa bakin gate ya dannan horn kafin Mai gadi ya bude ma tuni ya fita a motar yayi cikin gida.
Ta daga tea din zata sha kenan sai jin mug din tayi ya fashe har ya yanke ta a baki saboda dukan cup din da Aliyu yayi. Da sauri ta tashi dafe da bakin ta dake mata zafi. Tana dauke hannu taga jini ta saki wanivihu kan ta farga sai ji tayi ya janyo ta yana kila kamar an aiko shi. Haka ya dinga jabgar ta.
Mujahida na saka kaya taji ihu a falo tsayawa tayi sai ta kara jin wani da sauri tafito tayi falon dai dai shigowar Abbah kenan. Da sauri ya karasa da kyar ya janye Sha’awa a hannun Aliyu duk ya canja mata kala tana rike da hannu tana ihu. Fuskar ta kuwa duk tayi taruwar jini saboda farin da ta dinga sha.
Kan ta Aliyu ya karayi Abbah yace
“Aliyu ka bari mana ka shiga hankalin ka.”
“Abbah ka barni na kashe ta kamar yadda ta kashe min da na.”
“Amman kasan hukuncin wanda yai kisa ko?”
“Itama shi tayi.”
“Nace dai ka bari ko?”
Kasa ya fadi yana dafe kansa sai kuma ya mike ya fice a gidan da sauri mota ya dauka ya koma can gidan gwamnati.
Abbah ne ya kare ta yadda take kukan zuciya dan kukan yaki fitowa sai ajiyar zuciya da take saukewa hannun ta rike da dayan hannun. Mujahida Abbah ya kama yace
“Taimaka mata ta shirya muje asibitin ko?”
Ta karaso ta kama ta suka shiga daki. Hijab ta zako mata suka fito suka bar gidan.
*
Momy tinda ta tambaya aka fada mata Abbah ya tafi gidan Aliyu take murna dan tasan kwanan zancen cikin ya zube kawai kuma yanzu komai zai zo karshe. Dan tin jiya da wayar sa tayi kara take cewa Aliyu ne. Tin bai mamaki har yace
“Tayaya kike zaton Aliyu zai kirani.”
“Naga kwana biyu bakuyi waya ba.”
“To a wannan daren zai kira.”
sai ta fara kame kame daga baya ta yawance kawai da tayi kewar sa ne. Kallon ta Abbah kawai yayi.
*
Yana komawa ya samu su Mamah awaje suna tsaye ta taga suna kallon dakin da Aisha take da sauri ya karasa ya bude dakin. Wani Dr yace
“Please get out.”
Da sauri ya karasa wajen Aisha dake rike da ciki tana juyi.
“Sannu Baby love. cikin ne?”
Ido ta bude wanda suka zama jajir dan azaba dan ko kuka ta kasa hannun sa ta kama tana fadin
“Yaya mutuwa zanyi Yaya ka yafe min.”
“Ba zaki mutu ba Aysher ba yanzu zaki mutu ba sai kin cika burin ki sai kin haifa min ya’ya masu yawa tare zamu mutu Aysher bazaki tafi ki barni ba. in kika barni nima mutuwa zanyi.”
Wata murdawa da cikinta yayi yasa ta saki salati tana kai karshe kuma numfashinta ya dauke.
Cak Dr’s din suka tsaya Aliyu ya fara kallon ta sai ya kalli Dr’s din tana fadin
“Menene?”
Wani ne yaja zanin dake kan gadon ya rufe mata fuska. Ido Aliyu ya zaro ya yaye zanin da sauri yana fadin
“Menene haka?”
STORY CONTINUES BELOW
Dafa sa yayi yace
“Sai dai kayi hakuri ta rasu!”
Ture shi Aliyu yayi yana fadin
“Karya kake Aysher ba zata mutu ta barni ba in ta mutu nima mutuwa.”
Sai ya fara girgiza ta yana fadin
“Aysher! Aysher!! Baby love! Baby love!! Heartbeat! Heartbeat!!”
Wani Dr ne ya dafa sa yace
“Kayi hakuri dan Allah.”
Dagowa yayi yace
“Me kace nayi hakuri. Hakuri dame?”
Kamo hannun sa yayi yace
“Kayi hakuri Allah yai mata rahma.”
“What?”
Sai kuma ya juya yana kallon gadon idon sa ne ya fara lumshewa yayi kasa da sauri Dr ya kamo sa ya dago sa yana fadin
“Ranka ya dade!”
Amman ina ya sume dayan gadon dake dakin suka kai shi. wasu likitocin sukai kan sa. Mamah dake ta window ce ta
“Inna lillahi wainna illahir rajiun. Ya Allah kada ka sa wannan abun ya faru Allah kada ka dauke mana Aisha Ya Allah ka tashi kafadun ta.”
*
Abbah da Mujahida suna zuwa suka wuce da sha’awa emergency da ita. Nan aka amshe ta suka shiga dubata sukai sukaga ta karye a hannu sannan ta gurde a kugu ga ciwukan fukar ta nan akai mata dressing sannan suka bata daki dan ta huta.
Abbah Bayan sun gama da wajen Sha’awa an Bata gado suka karaso wajen su Mamah.
Mamah na tsaye ta durkushe ta fashe da kuka haka ma Maryama Abbah na shigowa yayi wajen su yana kallon su da Mamaki.
Mujahida ta karaso wajen tana fadin
“Mamah lafiya?”
Abbah ya karasa ya dago ta Yana fadin
“Me ya faru ne?”
Dakin ta nuna musu da hannu dai dai fitowar daya daga Cikin likitocin ya karaso yace
“Alhaji sai dai hakuri Dan Allah ya Mata rasuwa.”
Wani kuka Maryama ta Kara saki Mujahida na taya ta. Mamah kuwa hawaye take kawai.
Abbah yace
“Haba Fulani Kuma shine kike kuka ke da Zaki lallashe su.”
“Abbah Aisha ce fa ta mutu.”
Hannun ta ya Kama yace
“Ki nutsu Mana.”
Kai ta gyada. Dai dai zuwan Baba da Umma da Yaa Muhammad. Umma ta karaso wajen Mamah da sauri tana fadin
“Lafiya Hajiya!”
Wani likita ne ya fito yace
“Ya kamata ku zo kuyi cike cike ku fitar da gawar ko?”
Abbah yace
“Toh!”
Sannan ya kalli Baba yace
“Aisha ce ta rasu.”
Mutuwar tsaye Yaa Muhammad yayi Umma ta dago da sauri. Wajen likita suka je aka gama komai. Dakin da za a dauki Aisha suka shiga gaba dayan su. Mamah da Umma suna hawaye. Maryama da Mujahida suna ta kuka. Yaa Muhammad na tsaye a wajen jikin sa a sanyaye.
Baba ne ya dauki Aisha suka fita. Suka bar Yaa Shu’aibu a wajen Aliyu. Suna zuwa gida aka wuce da Aisha. Sannan aka fara sanar da Yan uwa da abokan arziki.
Mamah da Umma na daki zasuyiwa Aisha Wanka. Mamah na tsaye Umma ta Soma cirewa Aisha Kaya.
Hannun Aisha taga ya motsa da sauri Mamah ta karasa tana kallon hannun nasa Dan haka tace
“Masa’uda kamar hannun ta na motsi.”
Nan Umma ta kalli hannun ta taga Yana motsi da sauri ta fita Mamah ta maida Mata Kaya. Baba ne ya shigo da sauri ya dauke ta suka koma asibiti.
Aliyu na kwance ya bude Ido da sauri ya mike yana kallon Shu’aibu. Sai ya kalli dakin da yake. Da sauri ya kalli gadon da Aisha take. Mikewa yayi zaune Yana fadin
“Tana ina? Ina suka Kai ta?”
Sai Kuma ya dafe kan da. Da sauri ya dire kafar sa kasa
Yaa Shu’aibu ya kamo sa dai dai lokacin da Baba ya shigo da Aisha a hannu. Gadon da aka daukata ya ajiye ta da sauri Aliyu ya mike ya karasa Yana fadin
“Bata mutu ba ko? Na fada muku Bata mutu ba. Ba zata tafi ta barni ba.”
STORY CONTINUES BELOW
Sai ya Kama hannun ta dayan hannun ya dafa kan ta yace
“Heartbeat!”
Ido ta bude ahankali murmushi ya saki Yana fadin
“Sannu!”
Likitoci ne suka shigowa wannan Yasa duk suka juya suka fita. Aliyu kawai aka Bari tare da Aisha idon sa na akan ta, ta lumshe Ido tana sauke numfashi. Sun kusan awan daya a dakin suna gwaje gwaje sannan suka gama magani aka Bata ta Sha sannan suka fita.
Aliyu ya kamo hannun ta yana fadin
“Dan Allah Baby love kada ki tafi ki barni in Kika barni mutuwa zanyi.”
Hannu ta daura Akan sa ta dago ta sakar Masa murmushi. Ummah da Mamah da Baba da Abbah ne suka shigo tana kallon su sukai mata sannu.
Maryama ce ta shigo da Mujahida Bayan su Yaa Shu’aibu duk sukayo wajen gadon. Sannu suke Mata. Kofar ta tsaya tana kallon Muhammad dake tsaye ya zuba Mata Ido. Kallon kofar Aliyu yayi ya masa alamar da yazo da hannu. Ciki ya shigo ya karaso.
“Sannu Kanwata ya jikin?”
“Da sauki!”
“Allah Kara sauki. Sannu!”
Kai ta gyada. Yaa Aliyu ya dafa kanta Yana fadin
“Sannu!”
Kai ta gyada sai Kuma ta lumshe Ido take Bacci ya dauke ta.
Ganin tayi Bacci Yasa duk suka fita aka bar Aliyu. Bata jima ba ta tashi. Lokacin ana Kiran sallah azahar. Waya ya dauka ya Kira Maryama akan ta zo ta zauna da Aisha kan ya dawo. Sai da yai Mata Alwala sannan ya ajiye ta Akan sallaya. Yai kissing nata kan ya fita. Duk Maryama da Mujahida na tsaye suna kallon su.
Sallah Maryama ta tayar Mujahida tana zaune bayan ta idar Mujahida Tayo Alwala ta Taya. Aisha kuwa na kan sallaya tana sallah.
Ana fitowa daga massalaci Ya fito motocin su Yaa Abubakar ne suka fito. Da kallo ya bisu domin yai mamakin Dan bai San har an fada musu mutuwar Aisha ba. Suna hanya aka Kira akace musu doguwar suma tayi.
Yaa Abubakar ya rumgume Aliyu Yana fadin
“Ya Mai jikin?”
“Da sauki!”
“Allah Kara sauki.”
“Amin Yaya!”
Yaa Usman ma yai Masa ya jiki. Haka Umar da Farouk sannan sukabgaisa da su Anty Khadija, Fateema, Nusaiba, da Hauwa. sai sukai ciki. Momy ce ta fito daga mota tabi bayan su.
Suna shiga daki ya hange ta a kan dardumar, Maryama na gefen ta ita da Mujahida. Mamah na gefen gadon a zaune. Karasawa yayi ya zauna a kusa da ita tare da Kama hannun ta.
Su Yaa Abubakar ne suka shigo tare da matan su. Akan katuwar darduma da aka shimfidda suka zauna. Mazan suka zauna akan kujera, Mamah suka gaisar dukka sukai Mata ya mai jiki. Sannan sukai wa Aisha da ta Jingina da bango. Ta amsa tana Mai musu murmushi.
Momy ce ta shigo Mamah ta bita da kallo.
“Ina yini Yaya?”
“Lafiya kunzo lafiya?”
“Alhamdulillah Ashe Aisha bataji Dadi ba.”
“Eh ai kin San da hakan ba.”
Mamah ta fada ta mike ta fita. Momy da duk Yan dakin suka bita da kallo. Mujahida ta kalla tace
“Zo ki rakani wajen Mamah!”
Mikewa tayi tabi Bayan sa. Aliyu ne ya kalli Aisha ya sa hannu ya janyo ta ya kwantar akan cinyar sa. Har da gyara kwanciyya.
Yaa Muhammad ne ya shigo shi da Yaa Shu’aibu. Umar na ganin sa yace
“Ah aboki na!”
Ya karasa duk suka gaisa ya gaishe da su Yaa Abubakar da matan su. Suka zauna suka fara kuskus Shima da su Umar da Farouk.
Suna zaune Dr ya shigo, ya kalle gadon yana fadin
“Ah Ranka ya Dade Kune a tafe?”
“Mune Ya aiki?”
“Alhamdulillah Ina yini ya hanya?”
“Alhamdulillah! Ya Mai jikin?”
“Da sauki gata can wajen mijin ta.”
Ya kalli Aliyu yace
“Barka da Rana Ranka ya dade.”
“Barka ka dai.”
“Ya jikin nata?”
“Da sauki.”
“Cikin bai Kara tashi ba ko?”
Kallon ta yayi ta gyada Masa Kai yace
“Bai Kara.”
“To Allah Kara sauki.”
“Amin!”
Yace
“To sai anjima.
“Mun gode.”
Suna zaune aka Kira la’asar duk suka Mike suka fita. Aliyu ne yace
“Baby love Zaki Alwala ne?”
“Ina da ita.”
“To tashi kiyi kinji me kike so kici?”
Kai ta girgiza tace
“Sannu!”
Kai ta gyada. Ya mike Yana fadin
“Ga Baby love Nan ki kular min da ita.”
“Insha Allah Yaya.”
Ya juyo yai Mata kiss a goshin sannan ya juya ya fita.