WA NAKE SO CHAPTER 27
Www.bankinhausanovels.com.ng
Fulani ki shiru kawai!”
“Bazan ba Ranka ya Dade kayi ba dai dai ba Kuma dole nai magana.”+
“To kiyi!”
“Ai nayi Dan haka baka kyauta ba ka dawo da ita.”
Kan gadon ya hau yace
“Bacci nake ji Fulani kinzo Zaki hanani Bacci taho mu kwanta.”
Ya fada Yana kamo hannun ta.
Kwacewa tayi ta mike tsaye ta karasa bakin kofa tace
“Ban yadda ba Kuma Ina kan baka na ka dawo da matar ka shikenan Kuma ba a laifi Dan tayi kuskure mu Allah ne ya dauke Mana da bamuyi ba. Kana zaune Allah zai iya jarabtar ka shin a lokacin me zaka so? So zakai a yafe maka! Dan Allah ba Dan ni ba ka sassauta mata.”
Ta fada tana hade hannayen ta biyu.
“Ban San saki nawa kayi ba Amman ina fatan bai haura daya ba. Sai da safe!”
Ta fada ta juya ta fita a dakin. Kallon Kofar yabi da kallo ya girgiza Kai yana fadin
“Ko Zan dawo da ita ba yanzu ba.”
Ya koma ya kwanta Yana Jin son Mamah a ransa Dan yadda take saka sa a hanya in ya kauce. Addu’a yayi bacci ya dauke shi.
Tin asuba Mamah Bata koma ba domin sai da tayiwa Yan asibitin break ta aika sannan ta hau girkin tarbar su Aisha.
Tana gamawa tai wanka ta shirya Dan zuwa gaida Abbah. Ba kowa a falo tayi cikin daki. Samun sa tayi yana saka Kaya ta karasa ciki ta saka masa kayan.
Ta Gama yace
“Allah Miki albarka!”
“An tashi lafiya Fulani ta kwana tana fushi Dani!”
Ya fada Yana janyo ta.
“Ni ba fushi nake dakai ba.”
“Gashi Nan!”
“Kaga muje kaci abinci kasan yau Muna da babban ba’ki.”
“Suwa fa?”
“Sirika ta Kuma ‘ya ta!”
“Ah lallai Allah kawo su lafiya shine Basu fadan ba.”
Nan ta hau zuba Masa abinci, ya fara ci Yana santin girkin ta da yabo ita Kuma sai share shi take. Sai da ya gama ta mike tace
“Zani dubi Sha’awa.”
“Ai Mata sannu!”
Ta juya ta fita ya bita da kallo.
Da taje asibiti ta samu Momy ta fito da Sha’awa daga wanka. Momy ta gaishe ta, ta amsa tana Mata ya me jikin.
Sannan ta Karasa gadon ta dafa Sha’awa tace
“Ya jikin?”
“Da sauki!”
“Allah Kara sauki.”
Mai hannun Momy ta amsa ta fara shafa Mata Dan hannu daya a daure yake.
Hawaye ta fara Mamah dake shafa Mata Mai ta kalle ta yace
“Kuka Kuma?”
“Mamah tsoro nake nasan mutuwa zanyi ban San tayaya Zan rayu har na tuba wajen Allah.”
“Haba Sha’awa menene na kukan to wayace Miki cuta mutuwa ce. Wa yace miki Zaki mutu ko a yanzu ki tuba ga Allah. Allah gafuru Rahim sai kiga ya yafe Miki.”
Hannun Mamah ta Kama tace
“Ina ma kece uwa ta. Ina ma ke na rike Dan Allah Mamah ki yafen ki nemar min affuwar Yaa Aliyu da Aisha. Na cuci Hajara sai gashi Kai kayi ya koma kan mashekiya. Akace in zaka Gina ramin mugun ta ka gini dai dai Kai. Mamah ni na dinga sawa Hajara maganin Hana daukar ciki a abun Sha Dan Kar ta haihu ga Aliyu sai gashi ni da kyar ma na haihu. Kaico na kaicon son zuciya. Meyasa ban bi Allah ba na dinga Saba Masa Ina zina Yaa Allah ka yafen.”
Story continues below

Ta karasa maganar tana kuka. Momy dake gefe ma hawaye take. Mamah tace
“Ki daina kuka Sha’awa Zaki warke Kuma Zaki aure har ki haihu insha Allah tinda kin tuba ki ta addu’a Allah ya amshi tuban ki ya yafe Miki sai Hajara itama ki nemi yafiyar ta. Aisha da Aliyu baki da matsala Zan musu magana nasan Aisha tana da sauki Kai Kuma zata saka Aliyu ya yafe Miki. Allah ya yafe Mana gaba daya ya shirya zuri’ar mu Baki daya.”
“Amin!”
Ta fada jikin Mamah. Nan Mamah tai ta lallashin ta. Momy na gefe nadama ta kamata ga kunyar Mamah.
Ita ta shirya ta ta Bata abinci da magani sai Sha biyu ta bar asibiti Dan su Aliyu sunce Mata suna hanya.
Daya da kwata suka shigo gidan. Gaba daya bangaren Mamah suka wuce anan falo suka zauna. Aisha duk ta galabaita Dan tafiyar mota sukai tana shigowa ta kwanta anan kan kujera.
Aliyu na shigowa ya karasa ya durkusa a gefen ta Yana fadin
“Sannu Baby na ai duk ke Kika janyo mukai tafiyar mota.”
Tai murmushi tace
“To ni me nace bafa wani Abu na gaji ne kwanciyya nake son Yi.”
“Taso mu tafi part din mu.”
“Tab ai na daina wannan rashin kunyar.”
Ta mike zaune. Mamah ta shigo tana fadin
“Sannun ku da zuwa.”
Gaba dayan su suka zube a kasa suna gaishe su. Ta amsa cikin sakin fuska tana musu ya hanya. Sannan ta kalli Aisha tace
“Kai kin gaji ko? Tashi kije ki watsa ruwa kici abinci sai ki kwanta ki huta ko?”
Kai tayi kasa dashi. Mamah tace
“Tashi Mana.”
Ta mike a kunyace tayi dakin Mamah ya bita da kallo kamar ya bita. Mamah tace
“Kaje ka watsa ruwa kada ka rasa jam’i ko?”
Ya mike Yana kallon Maryama yace
“Kisa a kawo Mana kayan mu bangaren mu.”
Tace
“Toh!”
Ya fita.
Tana Shiga Tai wanka ta saka wasu kayan Alwala tayi Tai sallah. Anan aka kawo mata abinci taci tana gamawa ta haye gadon Mamah sai Bacci.
Aliyu ya shigo dakin sau nawa Bata falo daga baya ya kalli Maryama Yana fadin
“Ina Babylove?”
“Tana dakin Mamah tana bacci.”
Ya nufi dakin. Ganin tana bacci ya fito ya bar dakin. Kiran sallah la’asar yasa Ta tashi tai alwala tayi sallah. Mamah ce ta shigo tana fadin
“Au kin tashi?”
“Eh Maman!”
“Bari Maryama ta kawo miki pepper soup din da nayi Miki in kinci sai ki fito muje duba Sha’awa.”
“Toh!”
Mamah ta fita Bata jima ba Maryama fa shigo ta ajiye bowl din tana fadin
“Yaya sai zarya yake.”
“Hmm ai kuwa yau anan Zan kwana.”
“Ki rufa Mana asiri.”
Ta ja ta fara Sha. Ta lumshe Ido tana fadin
“Uhmm Dadi gaskiya Nan Zan dawo wajen Mamah Ina cin Dadi na.”
“Waye zai barki? Yayan tab!”
Ta mike tana fadin
“Gidan Zan bari Dan ba za ai wannan a gabana.”
Ta fice. Dariya Aisha tayi tace
“Ba sai kin gudu bama.”
Ta Gama ta wanke hannu ta dauki kwanon ta fitar tana fita Mamah tace
“Maryama amshi kwanon!”
Maryama ta amsa ta kalli Mamah tace
“Na fito Mamah.”
“Ok muje ko?”
Ta mike itama ta mike tabi ta.
A bakin kofar Mamah mota ta dauke su daga Nan sai asibiti. Suna zuwa suka wuce bangaren da Sha’awa take. Momy suka sama a bakin kofar dakin Nan Aisha ta gaishe ta, ta amsa a kunyace. Tai Mata ya jiki sannan Mamah ta tambaye ta ya jikin Sha’awar sannan sukai ciki.
Kanwar sha’awar ta samu zaune a gefen ta. Sha’awa na kwance Aisha da Mamah suka Shiga.
Tana ganin Aisha ta mike zaune tana fadin
“Aisha Dan Allah ki yafen min Dan Allah ba Dan ni ba.”
Story continues below

Karasawa Aisha tayi tana fadin
“Haba Sha’awa ba komai ni na yafe Miki “
“Da gaske kike?”
Kai ta gyada Mata.
“Nagode nagode Dan Allah ki nemar min yafiyar Yaa Aliyu.”
“Kada ki damu ya jikin?”
“Da sauki!”
“Allah Kara sauki.”
Kuyangar da suka zo tare ce tashigo da kayan da Mamah ta kawo Mata Tai Mata sannu sannan ta fita.
Anan asibiti suka jima, Dan Sai Bayan magariba suka bar asibitin daga Nan suka wuce gidan Kawar Mamah.
Suna zuwa aka hau musu sannu da zuwa. Nan akai musu tarba ta musamman aka kawo musu kayan motsa baki kala kala.
Hajiya Hauwa ce ta shigo dakin cikin Shiga ta musamman tana ganin Mamah tace
“Ah yau kece a gidan Fulanin marayu fulanin talakawa da marayu.!”
Murmushi Mamah tayi tace
“Hajiya Kulu kina da abin Dariya ai kece uwar marayun.”
“In babu ku ba.”
“Ko da mu din.”
Ta zauna ta Mika Mata hannu tace
“Ina yini Fulani ya Mai girma sarki?”
“Alhamdulillah ya iyalai?”
“Suna lafiya.”
Aisha ta durkusa tace
“Ina yini?”
Mikewa tayi ta daga ta tace
“Lafiya Lou! Yi zaman ki ya kike?”
“Alhamdulillah!”
Mamah ta kalla tace
“Wacce wannan Naga Kama sosai tin lokacin biki nake son nai Miki magana ko ba matar Aliyu bace.”
Murmushi Jin Dadi Mamah tayi tace
“Ita ce Yar Hafsa ce?””
“Wacce Hafsan?”
“Kanwata.”
“Haba Amman shine Baki fadamun yar ta Aliyu ya dauko ba.”
“Ayi hakuri.”
“Masha Allah wallahi har kunfi Kama da ita Akan Maryama.”
“Haka ake cewa.”
“Masha Allah!”
Nan suka taba Hira har akai isha’i sannan sukai sallama suka tafi ta cika Aisha da turaruka masu kamshi da tsada.
Aliyu ya shiga bangaren Mamah yafi a kirga ba Mamah ba su Maryama. Shima dayaga Bata nan yai gidan su Yaa Abubakar.
Karfe Tara suka karasa gida. Suna shiga ta wuce dakin Mamah Tai wanka ta kwanta take Bacci ya dauke ta.
Mamah Kuma a falo ta zauna tana cin abinci. Karfe goma ya shigo gidan tare dasu Maryama da suka dawo daga gidan Umar da Farouk.
Zama yayi yace
“Wai Ina take ne?”
Maryama Mamah ta kalla tace
“Je kiga me Aishan take ne?”
Ta mike ta Shiga Bacci ta tadda tana Yi Dan haka ta fito tana murmushi tace
“Mamah tayi bacci!”
“Ai fa yau ta gaji Dan munje dubo Sha’awa.”
“Sha’awa Kuma Mamah?”
“Eh ko da matsala ne?”
“Amman Dan me taje.”
“Saboda yar uwar tace.”
Shiru yayi tace
“Kaje kaima ka kwanta ka huta ko?”
“Mamah a tason ita.”
“Haba Babana a taso ta tana baccin kada ka manta ba ita kadai bace fa ba a duk lokacin da ta kwanta a wannan lokacin ba a son a tashe ta dan haka ka kayi hakuri kawai ka barta anan.”
“Mamah Nima na kwana anan din.”
“A’ah a’ah! Kaje gobe kwa hadu.”
Da kyar ya tafi sai da ya fita Maryama tace
“Ai nasan za a rina.”
Tayi dakin su.
*
**
***
****
*****
******
*******
********
Haka ta dauki dangana na rashin mijin ta Wanda kullum da tunanin sa take fama. In ta daura hannu akan cikin ta, sai tausayi abin cikin ta ya kamata. Duk yadda Fauwaz ke son ya ganta da ciki yau gata da ciki Amman baya nan babu ta yadda zai nuna wa cikin so bare yaron.
Story continues below

Sai ta tuna yadda suka dinga jayayya akan cikin Nan tana fadin Bata dashi Yana fadin da akwai. Lokacin da Kuma yai awo yagane tana da ciki yadda ya nuna Mata so da kauna na kwana daya Wanda daga shi basu Kara rayuwa ba ya tafi ya barta ita da Babyn ta.
Ido ta lumshe hawaye ya zubo Mata tana fadin
“Alhamdulillah Allah nagode maka da kake jarabta ta da abubuwa kala kala. Allah ka bani ikon cinyewa Allah ka bani ikon kula da tarbiyyar ‘dan Nan nawa Allah ka rabani da cikin Nan lafiya.”
Fu’ad na ta taga yaga duk abinda take. Da sauri ya juya Yana Jin zuciyar sa ba Dadi.
Office ya koma yana jin sa duk ba dadi tausayin Fateema ya Kama shi bama in ya tuna labarin ta. Hakika taga jarabawa kala kala.
Hawayen da ya Dan kawo idon sa yasa hannu ya maida Yana fadin
“Allah ya rabaki da cikin Nan lafiya!”
Wayar sa ce tayi Kara Yana dubawa yaga Hajiyar sa dauka yayi tace
“Fu’ad kazo ka kaini na kaiwa Fateema abincin nan taci da dumi tinda shi tace tana so.”
“Toh Hajiya!”
Ya mike ya fita. Gida ya koma ya same ta ita da Husnah. Yace
“Muje ko?”
Tare suka fito da Husnah suka Shiga mota. Suna sauka Hajiya da Husnah sukai ciki suka manta da kayan abincin da suka dauko.
Ledar ya gani ya saka hannu ya dauka. Dakin da suke ya nufa waige waige ya fara yana duba ko zai samu wata nurse ta Kai Mata. Ganin ba kowa kawai yasa hannu ya bude ya Shiga dukkan su ne suka dago tana ganin Fu’ad ta kura Masa Ido domin yaushe rabon da ta Ganshi. Zata iya lissafa ganin sa Shima iya Kar sa bakin kofa.
Kan sa a kasa ya karasa ciki ya ajiye basket din. Yana dagowa suka hada Ido da sauri ya dauke kansa Yana Jin zuciyar sa na bugawa. A hankali yace
“Ya jikin?”
Kasa amsawa tayi ya dago ya kalle ta tace
“Da sauki!”
Juyawa yai ya fita ta bishi da kallo. Husnah ta zuba Mata abincin ta Mika mata tana fadin
“Sannu Maman biyu!”
Murmushi ta sakar Mata tace
“Yauwah. Ai Yaya na Yana kawon sakon ki yace min kema bakya Jin dadi shiyasa kwana biyu Baki zo ba shine nake cewa ko Baby na yayi kanwa ne?”
Tai murmushi ta saci kallon Hajiya sai Tai sauri tace
“Ki Taya mu addu’a Allah raba lafiya. Kema Allah sauke ki lafiya.”
Hannu ta dauka Akan cikin ta take Babyn ya motsa Tai murmushi tace
“Amin insha Allah. Kinji Baby Yana motsi.”
“Har Baby ya kake kwana biyu!”
Motsi ya Kara Fateema tace
“Kinji ko. Kwana biyun Nan yai ta motsi haka yake.”
“Allah sarki!”
Nan ta fara cin abincin ta.
Tin daga Ranar Bata Kara ganin Fu’ad ba ko ta taga ma domin kuwa ya daina zuwa sai ya tabbatar tana bacci yake zuwa. Sai dai duk abunda yasan me ciki na bukata ko sha’awa yana siya mata.
Cikin hukuncin Allah haka cikin Fateema yai wata Tara. Wanda a wata taran Nan Hajiya ce ke Kula da ita komai ita take Mata su Mami da Momy sai dai suzo su duba ta su tafi.
Cikin na Shiga wata tara Anwar ya samu Fu’ad a office yace
“Bro aiki fa za ai wa Fateema!”
“Amman saboda me?”
“Saboda yanayin da take ciki zata iya Shan wahala in muka barta ta haihu da kan ta.”
Shiru Fu’ad yayi. Anwar ya dafa shi yace
“Me kake tunani nothing bad will happened.”
“Da bana son ai Mata aiki ne!”
“Haba Bro sai kace ba likita ba Kai da zaka Bata gwarin gwiwa meyasa kake son sarewa?”
“Shikenan Allah yasa ayi a sa’a yanzu yaushe za ayi kenan?”
“Since tayi wata tara zamuyi gobe ne Dan kada nakuda ta same ta.”
“Allah ya kaimu Zan yiwa su Momy magana.”
Lokacin da ya Kira su Momy yai musu bayani duk suka amince itama Fateema da aka fada Mata Bata ji wani tsoro ba sai addu’a kawai da take Yi Akan Allah yasa ayi a sa’a.
Story continues below

A Daren da ana gobe za ai aikin Bayan su Hajiya sun tafi ita kadai ce a dakin sai nurse Mai kula da ita. Kofa yai knocking nurse taje ta bude.
Ya Shiga tana ganin ya shiga ta juya ta fita. Kallon ta yayi ya rufe kofar yayi ciki. Akan kujerar dake gefen gadon ya zauna. Kallon sa tayi tace
“Ina yini?”
“lafiya ya jikin?”
“Alhamdulillah!”
Ta fada tana Wasa da yatsun hannun ta.
“Gobe za ayi, aiki ko? Ina Miki fatan alheri da fatan ayi a sa’a!”
“Nagode!”
“Ba komai ‘dan ki ai ‘da nane kuma in har Ina raye ‘danki ba zai taba yin maraici ba. Insha Allahu.”
Dagowa tayi ta kalle shi idon ta cike da hawaye.
Kai ya girgiza Mata yace
“Kukan fa please kada kiyi!”
Kai ta gyada yace
“Yauwah!”
“Ina ka tafi ka barni tsawon wannan lokacin?”
Kai ya shafa yace
“Ina kasar Nan Teemah.”
Ya mike yace
“Sai da safe ko?”
Batai magana ba wannan yasa ya juyo. Hawaye yaga tana Yi da sauri ya dawo yace
“Dan Allah ki bar kukan Nan.”
Kai ta gyada. Ya Mika Mata hankercheif yace
“Goge hawayen kinji!”
Kai ta gyada yace
“Sai da safe!”
Ya juya ya fita. Rumgume hankercheif din tayi a kirjin ta. Da shi ta kwana a kirjin ta.
Fu’ad kwana yayi Yana wa Fateema addu’a Alllah yasa ayi a sa’a.
Washe gari da safe aka fara shirye shiryen aikin wanda su Hajiya, Mami, Baba, Husnah da Momy duk sun zo.
Lokacin da aka fito da ita za akai ta dakin aikin tana kwance taga Fu’ad da karfi ta kwala Masa Kira. Juyowa yayi Yana ganin ta ya karaso yazo ya durkusa a waje ta yana fadin
“An fito?”
Kai ta gyada Masa.
“Allah yasa ayi a sa’a!”
“Amin nagode. Dan Allah ka yafe min Fu’ad ban sani ba ko Zan tashi “
“Ki daina fadar haka Teemah Zaki tashi Kuma ni baki min komai ba na yafe Miki.”
“Nagode Fu’ad Zan fada maka wani Abu ko ban tashi ba ka fadawa su Momy na fadawa Baba cewar in har Namiji na Haifa sunan ka za a saka!”
Kai ya girgiza yace
“A’ah Teemah a saka Masa sunan Abban sa.”
“Kai ma Abban sa ne. Kuma jiya Kai kayi min alkawarin zaka kula min da shi tamkar Babyn ka. Kai kuma Abban shii dan haka in ban tashi ba in har Namiji to sunan ka za a saka Masa.”
“Fateema zama ki fito lafiya. Tare zamu kula da Babyn mu.”
Murmushi ta sakar Masa tace
“Ka yafe min!”
“Na yafe Miki kema ki yafe min!”
“Ba Kai min komai ba.”
“Sir zamu tafi!”
Wata nurse ta fada.
Kai ya gyada Mata yace
“Allah yasa ayi a sa’a!”
Ta fara gangara gadon Yana tsaye suka wuce bai daina kallon su ba har sai da suka Shiga dakin da sauri yayi office din sa. Kaya yai saurin sauyawa.
Fateema da tana kwance akai Mata allura nurses suka rufu Akan ta. Fu’ad ne ya Shiga dakin cikin shigar sa ta aiki fuskar sa boye da facemask Yana zuwa ya tsaya ya farai Mata aiki. Duk abinda ake tana Jin Dan har hira take da wasu nurses din ma.
Kukan yaro da taji ta lumshe Ido tana fadin
“Allah shirya ka yai maka albarka. Allah yasa ka zama abin alfahari a gare mu.”
Fu’ad na ciro sa ya bada shi a gyara shi. Ta dinke Fateema sannan ya juya ya amshi Baby boy din Yana Jin son sa na Shiga zuciyar sa. Yaron ya kalla Yana murmushi yace
“Welcome to the world namesake. Allah ya Raya mana Kai ya sa ka zama mahadacin alkura’ani Mai ibada Allah maka albarka!”
Yai Masa kiss a goshi ya fita da yaron Baba ce ta fara mikewa tana fadin
“Me aka samu Fu’ad?”
“An samu Namiji su Mami ne sukai miji.”
“Ashe takwaran ka aka samu.”
Ta amsa tana fadin
“Allah ya Raya Fu’ad.”
Momy ta amsa da Amin ta leka Babyn tana Masa addu’a. Mami ta amsa tana fadin
“Allah ya Raya ka ya jikan Mahaifin ka.”
Ta mikawa Hajiya. Hajiya ta amsa tana fadin
“Masha Allah. Tubarkallah ya Raya yai maka albarka.”
Husnah ta leko tana kallon kyakyawan Dan kamar balarabe dashi fari tas ga hanci. Tace
“Masha Allah!”
Hajiya ta Mika Mata ta amsa tana cewa
“Masha Allah. Allah ya Raya mana Kai!”
“Amin!”
Momy dai Bata dauka ba sai da Husnah tace
“Momy Baki dauka ba ko kunyar Yar fari ce.”
Momy tace
“Ai Naga sun kwace min shine!”
“A’ah wannan mijin naki ne ko Hajiya Dan nasan Dady ba zai yadda ba.”
Mami tai murmushi tana fadin
“Ai fa Bari na fada Masa.”
Gadon Fateema aka gangaro zuwa dakin da take. Duk suka bi Bayan su aka daura ta a gadon ta dago tana kallon su.
Sai Kuma ta kalli Husnah tace
“Me aka samu?”
“Namiji!”
Ido ta lumshe tace
“Fu’ad kenan!”
Sai ta saki murmushi mai ciwo tuna dagar su da Fauwaz na cewa Mace zata Haifa ita Kuma tacewa Namiji. Allah yayi namijin ne.
“Allah ka Raya min Fu’ad!”
“Amin!”
Husnah ta amsa tana nuna Mata Babyn me Kama sak da Mahaifin sa Fauwaz. Sai da zuciyar ta ta buga da ta kamar tasu har tai yawa. A hankali idon ta ya fara lumshewaa take Bacci ya dauke ta
Mami ganin Fateema normal yasa ta Kira Dady ta fada masa. Cikin murna yace
“Alhamdulillah Ina Nan zuwa kuwa!”
Momy ta Kira ta fadawa su Suraiyya Murna kamar sayi me? Suma suka ce suna hanya.
Tin yamma da ta farka take son taga Fu’ad Amman Bata Ganshi ba. Dakin kuwa su Mami ne duk a ciki.
Kwana ta biyu da haihuwa Amman Bata ga Fu’ad ba. Fu’ad kuwa da safe da rana duk sai ya sa Anwar ya Kai Masa Baby ya jima a wajen sa.
Kwanan su bakwai da haihuwa akai yankawa yaro rago aka saka Masa Fu’ad. Dady ya hada mata kaya na haihuwa haka ma Fu’ad ya musu ita da Baby. Anwar ma sai da yayi musu sannan Suraiyya ma da tazo ta basu kayan barka. Ranar Fateema Tai kuka ya rumgume Fu’ad a jikin ta.
A Ranar Kuma aka sallame su sai dai zatana zuwa postnatal da Kuma karasa Bata treatment.
Lokacin da suka koma gidan Fu’ad tayi mamaki da taji ance gidan Fu’ad ne. Domin gidan ba karamin Kato bane ga kyau an zuba kayan more rayuwa.
Satin su biyu da sallamo su, Mamin Anwar ta sauka ita da Nusaiba. Nusaiba na ganin Fateema da Babyn ta taji a duniya ba Wanda take so kamar su.
Haka ta yini a gidan rike da baby har dare tana jiran Fu’ad ba alamar sa.
Sai wajen goma na dare sannan ya shigo gidan Yana zuwa ya shige bangaren sa. Har Sha daya tana rike da Baby tana jiran Fu’ad Amman ba shi ba alamun sa. Gashi Mamin ta sai Kira take da kyar ta, ta tafi ta bar Fateema da Babyn.
Tana Shiga Mami tace
“Ke Baki da hankali ko?”
“Me nayi Mami?”
Dakuwa tai mata tace
“Shige muje.”
Nan sukai ciki yace
“Me Kika zauna Yi?”
“Mami Ina gun Baby fa Baki ga Babyn ba Mai kyau “
“Ba Fu’ad Kika zauna jira ba?”
“Haba dai ni bashi na zauna jira.”
“To ki shige kije ki kwanta.”
Ta wuce. Washe gari da safe taje Amman har ya fice domin Shima bai zama a gida Dan baya son Yana ganin Fateema. Amman da safe kan ya tafi aiki sai yaje yaga Baby Fu’ad Wanda suke Kira da Annur
Haka in ya dawo zai sa a kawo Masa yaron sosai yake Jin yaron tamkar dan cikin sa. Dan kullum ya fita sai ya shigo Masa da Kaya kala kala masu tsada da kyau. Fateema ba karamin Dadi take ji ba haka Nan ba Wanda take so ta gani in bashi ba.+
Yau ta kafa ta tsare sai taga Fu’ad Wanda tana daki Nusaiba na wajen ta tare da Annur dake hannun ta Baba ta shigo tana fadin
“A kawo shi Baban sa ya Ganshi.”
“Baba ya dawo ne?”
“Eh!”
Ta amshi Annur ta fita dashi. Nusaiba ta kalle ta tace
“Waye babban sa?”
“Fu’ad!”
“Oh ya dawo. Daman Ina son ganin sa bari naje.”
Ta mike ta fita Fateema ta bita da kallo zuciyar ta na bugawa. Bayan minti talatin ta kasa zama dan haka ta mike tayi dakin Fu’ad.
A falo ta same shi zaune a kasa gefen Nusaiba Yana magana kasa kasa. Abinda ta iya ji kawai yace
“Banyi dan na Bata Miki rao na kema kin sani.”
Annur ta Shiga ta dauka ta juyo ta fice kawai. Da kallo suka bita. Yace
“Muje ba rakaki dare yayi ko?”
Ya mike tabi Bayan sa. Yace
“Kin fiya daru Autar Mami.”
Baki ta turo yai Dariya Yana fadin
“Sai na cire bakin!”
Fateema dake tafiya tana Jin sa tai sauri ta shige ciki. Nusaiba race
“Bari nai wa Anty Fateema Sallama.”
“Kyale ta muje kawai!”
Suka fice.
Fateema na Shiga daki ta rumgume Annur ta saki wani kuka. Ta rasa kukan menene ji take kamar zuciyar ta zata fashe dan damuwa. Ranar gaba daya batai Bacci ba kan safiyya kuwa idon ta ya kumbura saboda kuka da rashin Bacci.
Da safe Bayan tayi wanka ta saka bakin siket da Riga highneck long sleeve baka da fara gaban ta zip ne ta saka hula akan ta.
Dakin Baba ta Shiga ta dauko Annur suka fito falo dan ta karya. Zama tayi ta ajiye tea da dankalin da ta debo akan stool. Ta daga Annur tana fadin
“Baka Jin yunwa Baby nah?”
Ta daura shi Akan ciyar ta, ta zuge zip din dake gaban rigar ta, ta fito da maman ta tasaka Masa a Baki yaron ya amsa yana lumshe Ido. Ta shafa kan sa tana Masa addu’a.
Fu’ad ne ya fito daga dakin sa Dan Shima jiya Sam bai Bacci ba Kuma ba zai ce ga dalili ba Amman ya kasa Bacci Yana fitowa falon yai tozali da Fateema na bawa Annur nono. Cak ya tsaya Yana kallon su yadda tayi kyau ga kirjin ta fari tas dashi.
Dagowa tayi suna hada Ido yai sauri ya dauke Kai yayo cikin falon. Itama ta cirewa Annur a Baki tana zuge rigar ta.
Kitchen ya Shiga ta daura Annur Akan kafadar tana shafa Bayan sa. Hajiya ce ta fito ta ce
“Baki karya ba.”
“Wallahi na tsaya bashi ya Sha ne.”
“Kawo shi sai ki karya ko?”
Ta mika Mata shi sannan ta dauki tea din ta kurba. Hajiya ta kalle ta tace
“Me ya samu idon ki?”
Zatai magana Fu’ad ya fito daga kitchen rike da cup. Tayi kasa da Kai. Cup din ya ajiye Akan stool din gefen kujerar yayo gun Hajiya yace
“My boy!”
Story continues below

Hajiya tace
“Me ya same su?”
“Ba komai.”
Fu’ad ta kalla yace
“Yau ba zakaje aiki bane?”
Ya shafa Kai yace
“Zani yau na makara ne!”
“Yauwah yau Fateema zata ganin likita sai ku tafi ko?”
“Hajiya Zan biya wani wajen sai dai na Aiko a dauke ta.”
“To shikenan gata nan yau ta tashi idon ta a kumbure!”
Kallon ta yayi ta gefen Ido kawai ya dauke Kai Yana kallon Annur yace
“Baby ka tashi lafiya?”
Nan yai tai Masa Wasa. Fateema na gefe ta kasa cin abincin ma daga baya ya dauki Annur sukai ciki. Bai jima ba ya dawo rike da wayar sa ya kalli Hajiya yace
“Hajiya ni Zan fita!”
“Sai ka dawo”
Ya nufi kofa. Hajiya tace
“Annur din fa?”
“Zan kaiwa Nusaiba zata dawo dashi.”
“Oh to shikenan!”
Fateema kuwa da ba Dan Hajiya bace da ba abinda zai Hana ta amso Dan ta. Fita yayi ya Shiga mota. Kofar gidan Anwar ya Isa yai parking waya ya dauka ya Kira sa.
Yana fitowa ya Mika Masa Annur yace
“Ka Kai shi Nusaiba ta Mai dashi gida.”
“Alright!”
“Yaushe zaka taho ne?”
“Nima yanzu Zan fita.”
“Ok ka Shiga ka taho da Fateema please yau zata ganin likita!”
“To Kai Banda abinka ga ka wa zataje gani.”
Motar ya tayar yace
“Ni!”
Ya bar wajen. Anwar ya girgiza Kai yai cikin gidan. Nusaiba na falo tana ganin shi ta mike tana fadin
“A Ina ka samo min yaro na.”
“Abban sa ya kawo shi!”
“Yana Ina?”
“Ya tafi!”
“Amman da ka Kira ni ko?”
Mika Mata yayi yace
“Ki Kai shi gida ki cewa Fateema ta shirya yanzu zan fito.”
Yayi ciki. Ta fita ta nufi gidan su Fateema tana zaune a falo ranta a bace Nusaiba ta shigo. Kai ta dauke Bayan ta amsa sallama ta Shiga ta gaida Hajiya sannan gaida Fateema. Fateema ta amsa adakile ta mike zatai daki.
Nusaiba race
“Anty Wai ki shirya yanzu Yaya zai fito.”
“Toh!”
Ta fada ta shige. Tana Shiga ta fada saman gado ta fashe da kuka.
A ranta take fadin
“Shin menene tsakanin Fu’ad da Nusaiba.”
Dayar zuciyar tace
“Kamar ya? Soyayya suke!”
Baki ta cije ta rufe fuskar ta. Hajiya ce ta shigo ta kalle ta tace
“Wai me yake damun ki ne?”
Da sauri ta mike tana goge fuskar ta. Kai tayi kasa dashi tace
“Ba komai!”
“Shikenan Anwar yazo ki tashi kije.”
Ta mike jiki a sanyaye ta saka doguwar riga akan kayan ta, ta yafa mayafin ta, ta saka sandal Baki Tai kyau ta fito kamar balarabiya. Sweater ta daukar wa Annur ta fita. A hannun Nusaiba ta amshe shi ta saka Masa sannan ta fita.
Mota ta Shiga tace
“Ina kwana?”
Kallon ta yayi yace
“Lafiya Lou Amman me yake damun ki?”
“Ba komai!”
Ta fada tana kallan taga. A haka suka fice a gidan yace
“Amman kinsan ba haka kike ga ko?”
“Yaya yanayin garin ne kawai.”
“Me kike bukata?”
“Ba komai!”
“Zan fadawa Fu’ad ya dada kula dake Dan kina lacking wani Abu.”
Tai murmushi tace
“Ina kewar Yaya Fauwaz ne kawai!”
Ta fada Idon ta na kawo ruwa.
“Ayyah sorry kina Masa addu’a kinji.”
Kai ta gyada a Haka suka karasa asibiti yai parking sannan ya fito ya bude Mata ta fita. Yai gaba tana bin bayan sa
Daya daga cikin nurses din dake kula da ita ce tazo ta amshi Annur tana fadin
“Fine Boy!”
Suka gaisa da Fateema office din Fu’ad suka nufa suka Shiga ba kowa a ciki.
Story continues below

Annur ya zauna ya kalle ta yace
“Zauna Mana.”
Ta zauna sai ya mike yace
“Bari naje na dawo.”
Ya juya ya fita. Nurse din ta fita da Babyn. Tana zaune taji an budo kofar ta dago da sauri tana kallon kofar. Fu’ad ne ya shigo juna suka kurawa Ido shine ya fara karfin halin janye idon sa. Ya shigo ya zauna a kujerar dake facing nata yace
“Me ya samu idon ki?”
Fuska ta hade tace
“Ba komai.”
Sai ta bashi Dariya ya girgiza Kai yace
“Ba komai fa Kika ce?”
Kai ta gyada. Yace
“Ok to me ya hanaki Bacci jiya Bayan nan kukan me kike ta tayi?”
Dagowa tayi ta Harare shi tace
“Ka kaini nai abinda zanyi na koma gida Dan Allah.”
“Ni zan duba ki ai.”
“Kai kuma!”
“Kina mamaki ne Dan na duba ki?”
Kai ta dauke daga kallon sa. Yai murmushi yace
“Ki na dai cire damuwa Kuma ba komai ya kamata kina sawa a ranki Yana damun ki ba. Bama in Kika tuna matsayin ki a wajen abun. Dan haka kina kular min da Baby na.”
Wata harara ta dalla Masa yace
“Ni kike harara.”
Bata tanka Masa ba ya mike yace
“Ki hau kan gadon can.”
Mikewa tayi ta hau. Ya karasa ya balle Mata after jikin ta sannan ya dage rigar ta da sauri ta mike tana fadin
“Wai Menene haka Fu’ad?”
“Me Zan Miki Teemah?”
“Amman menene na buden jiki?”
“Duba ki zan!”
Kallon sa ta tsaya yace
“Please kwanta ni na duba ki Ina da abubuwa.”
Komawa tayi ta kwanta ya Kara bude rigar tata Yana kallon inda akai Mata aiki. Hannu ya daura a akai Wanda daga shi har ita ya saukar musu da wani irin Abu a jiki Dan haka da sauri ya janye hannu ya juya Yana fadin
“Tashi!”
Itama jiki a sanyaye ta mike ta gyara rigar tana zaune yace
“Ina Annur?”
“Yana wajen Nurse!”
“Wa Kika bawa?”
Shiru tayi. Yace
“Magana nake fa!”
“Kaje ka duba.”
Yai murmushi yace
“Hmmm ko? Ai da nane dole na tambaya wa aka Kai wa.”
*
**
***
****
*****
Washe gari da safe. Aisha ta tashi Tai wanka. Dakin Maryama ta Shiga tace
“Ina akwati na?”
“Yana bangaren ki?”
“Kije ki daukon Zan saka Kaya “
“Toh!”
Ta juya ta fita. Itama ta koma dakin Mamah.
Bata jima ba ta komo ba akwatin ta kalle ta tace
“Ina akwatin?”
“Wallahi ban Ganshi ba “
“To ai da kin daukon Kaya na a daki na ko?”
“Dakin a rufe yake.”
“Oh rufe dakin yayi shi Yana Ina?”
“Bai tashi ba.”
Agogo ta kalla tace
“Har yanzu?”
Ta mike ta nufi kofa sai ta juyo tace
“Wai jiya ya shigo ne?”
“Kema kin sani cewa yayi sai ya kwana anan ma Mamah ta hanasa.”
Ido ta zaro tana murmushi ta fita. Bangaren sa ta wuce tana zuwa ta taba kofar dakin ta a rufe dakin sa tayi ta Shiga.
Kwance ta sameshi Akan gado. Ta hangi akwatin ta acan kuryar dakin.
Murmushi tayi ta girgiza Kai ta wuce a hankali ta bude akwatin ta zata dauki kayan ta yayi juyi ya bude idon sa.
Ajiyewa tayi tace
“Morning!”
Kallon ta ya tsaya yi. Ta kalli kan ta Riga ce armless a jikin ta sai gashin ta da ya baje a gadon Bayan ta.
Tai murmushi tace
“Ya dai Yaya?”
Mikewa yayi ya zaune yana kallon ta. Tace
“Yaya yau baccin safe kasha!”
“Ba dole ba jiya na kasa Bacci saboda rashin ki.”
“Ayyah sorry Bacci ne ya dauke ni a dakin Mamah.”
Ya mike ya karaso wajen ta ya yaye gashin dake gaban goshin ta yace
“Ko? Daman kinso haka ne. Kuma Mamah ta hanani kwana da Matata!”
Story continues below

“Ayyah sorry Banda abinda kwana biyu fa zamuyi mu koma.”
“Me kike nufi?”
“Ina nufi daga Nan Muna tare “
“Yanzu fa?”
“Ni ta Mamah ce.”
Rumgume ta yayi yace
“Kin ma Isa. Kinsan halin da na Shiga jiya kuwa?”
Jikin ta take son ta kwace ya dauke ta cak ya daura Akan gado Yana fadin
“Sai naji dumin Heartbeat!”
“Haba Yaya Mamah nacan na jira na fa.”
Bakin su ya hade kawai. Take ya dauke Mata wuta Nan ya fara romancing nata har jikin ta yai sanyi itama ta fara maida Masa da martani. Sai da suka jiyar da juna Dadi sannan ya dauke ta suka shige bandaki. Wanka sukai sannan suka fito.
Shi da kan sa ya shirya ta cikin wani blue material doguwar riga Tai Mata kyau. Ya saka shadda blue. Anan ya zaunar da ita ta karya sannan suka wuce bangaren Mamah.
A falo suka same ta. Duk sai kunya ta Kama Aisha ta karasa gefen ta tana gaishe ta amsa tana fadin
“Ashe kin fita.”
“Naje dauko Kaya nane.”
“To.”
Aliyu ya gaishe ta sannan suka tafi gaida Abbah. Bayan ta gaishe da Abbah ta koma ciki ta bar Aliyu da Abbah.
Aliyu ya gyara zama yace
“Daman Akan Maryam da Mujahida nazo.”
“Me ya faru?”
“Abbah! Shu’aibu da Mujahida soyayya suke haka ma Maryama da Muhammad”
“Kai Masha Allah.”
“Shine nace Zan zo na fada maka Dan Shu’aibu yaki ya koma makaranta saboda Sha’awa Dan haka Mai zai Hana a aura Masa ita sai suyi tafiyar su tare.”
“Wannan shawara ce me kyau yanzu yaushe kake ganin ya Dace ayi?”
“Abbah kada ya wuce sati biyu ayi komai a Gama har su Maryama din tinda Muhammad ya gama service itama ta Gama karatun ta.”
“Shikenan zanyi magana da Baban su zakaji komai daga gareni.”
“Godiya nake Abbah.”
Sukai sallama.
Ranar da su Aliyu zasu koma tare suka tafi da Abbah Dan zai je wajen Baba. Bayan yaje sun gaisa ya gaya masa bukatar sa Nan Baba yai murna yasa albarka yace
“Amman ban ki sati biyun ba sai dai yai kadan kaga za ai shirye shirye ko?”
“A’ah ba matsala Aliyu yace ya dauki nauyin Basu gida da laife. Ni Kuma Zan Basu sadaki da duk wani shagali da za ai.”
“Amman Alhaji abun yau yawa.”
“A’ah Nima Ya’ya yanane fa kada ka manta Aliyu Yayansu ne ni dai nazo na fada maka ne kawai.”
“Madallah Allah Kara girma Allah ya taimaka.”
“Amin!”
Nan Umma ta fito suka gaisa. Daga Nan ya tafi ya koma can gida. Dan Sai ta waya ya fadawa Aliyu komai. Nan fa ya sanar da Mamah. Mamah tayi murna sosai.
Kwanan su Aliyu biyu da dawowa suka daga Dan hado kayan lefe. Wanda duk inda sukaje shi da Aisha sai ya jidi Kaya kala uku iri daya. Har akwatuna duk iri daya aka hadu set tara da red, blue, pink. Ko wannen an cika shi da Kaya na gani na fada masu tsada da kyau.
Ranar da suka dawo a Ranar ya sa Yaa Umar yazo ya kaiwa Umma kayan Dan a satin ake so akai lefe. Lokacin da Yaa Shu’aibu ya gani kuka ne kawai bai ba. Dan an musu Kara ace akwati set uku dukka cike da Kaya wajen akwati guda ashirin Kaya sun fi kala dari wane dari. Hakika wadan nan mutanen kirki ne.
Aisha Bata San me ake ba. Tana fitowa a wanka taga set din akwatuna adakin ta takalli Aliyu tana tsane jikin ta tace
“Yaya ya Kuma aka hau dasu sama bayan kace wucewa za ai dasu.”
“Wannan naki ne?”
“Nawa Kuma Yaya?”
Mikewa yayi ya karaso yace
“Ko sunyi Kadan?”
“No Amman Yaya Ina Zan Kai Kaya!”
“Ai tai min kwalliyya Ina gani Ina Jin Dadi.”
Story continues below

Ta fada jikinsa tana Fadi
“Allah Kara budi ya kiyayen Kai Yaya!”
“Amin Baby love!”
Ya shafa Mata Mai ta dauko wata doguwar riga purple kala ya saka Mata. Ya zura hannu a aljihu ya zaro wani Dan box me kyau ya fito dashi ya bude. Wani Dan kunnen diamond ne aka kerashi aka rubuta A biyu daya tashiga cikin daya.
Nuna Mata yayi tace
“Wannan fa?”
“Taki ce?”
Ido ta zaro tace
“Yaya….”
Hannu ta daura akan bakin ta yace
“Shittt!”
Ta hadiye maganar ya saka Mata ta kalli mirror yadda Tai Mata kyau tace
“A biyu!”
“Yes Aliyu and Aisha!”
Ya saka Mata dan kunne da zobe. Juyowa tayi ta rumgume shi tare da hade bakin su tana bashi wani kiss na daban. Wanda daga Nan ta Shiga nuna Masa godiyar ta ta abinda yai Mata Ranar sun Sha soyayyar kamar me da kyar ya kyale ta
Taje gidan Umma aka fadaMata Ranar da za aje akai kayan lefe sai dare yaje ya dauko ta.
Suna kwance Akan gado kan ta Akan kirjin sa tace
“Yaya nah!”
“Ni ki canjan suna wane Yaya ne. Na barwa Muhammad da su Yaa Abubakar.”
“Kai Yaya me zance maka to?”
“Gasu Nan da yawa bani suna Mai matsayina a wajen ki.”
“My Soulmate!”
“Mahadin rayuwar ki?”
Kai ta gyada yace
“Nice name ba.”
Tai murmushi tace
“Yaya Dan…..”
“What?”
“Au My soulmate Dan Allah Ina son na tafi can gurin Mamah!”
“Me zakije yi?”
“Wai in za a Kai lefe kaga sai nabisu bayan biki ma dawo tare ko?”
Mikewa zaune yayi Yana kallon ta yace
“Baby Love kiyi hakuri wallahi ba Zan iya kwana ba tare da najini a jikin ki ba. Dalilin da yasa na dakatar da karatun ki kenan sai na sauka Nan da wata shekara sai mu tafi can Abuja kiyi karatun ki Ina aiki na gani gaki Amman yanzu ba Zan iya ba.”
“Yaya…”
“Au My Soulmate! In dai Akan karatu ka ajiye duk lokacin da ka samu lokacin muka kasance tare nayi. Nima bana son nayi nesa da Kai kamar yadda baka so. Amman Yaya yanzu Kai yaushe zakaje bikin?”
“Ranar daurin aure.”
“Daurin aure Kuma?”
Kai ya gyada. Shure Shure ta fara tana fadin
“Gaskiya ban yadda Yaya so kake kace nima sai lokacin kenan ba za ai biki Dani ba haba My soulmate Mama fa zatazo ka barni naje da wuri Dan Allah.”
Yai murmushi yace
“To Yi shiru Amman da sharadi in zamu kan lokacin”
“Wanne sharadi?”
“A guna zakina kwana.”
“Haba dai Soulmate.”
“Ko? Indai haka ne ba inda zamu sai Ranar daurin aure da yamma mu juyo.”
Kuka ta saka ya janyo ta yace
“To ki yadda da abunda nace.”
Kai ta gyada yace
“To yaushe zamu tafi?”
“Gobe!”
“Ah haba dai? Gobe fa. Bikin sauran kwana takwas ran yaushe za a fara event?”
“Talata!”
“Au sai mu tafi Ranar ko?”
Kai ta girgiza tace
“Haba Soulmate!”
“To yaushe kike so?”
“Gobe!”
“A’ah Ranar Monday ma tafi dai ko?”
“Haba Yaya!”
“Kinga Zan tafi na bar aiki.”
“To shikenan Allah kaimu.”
“Amin My love.”
Ya rumgume ta.
*
Ranar Monday ta sauka Wanda Mama tin Friday ta sauka. Suna sauka ta wuce bangaren Mamah acan suka rumgume juna su ita da Maryama.
Tana ganin Mama ta karasa da gudu ta rumgumeta. Mama tace
“Haba Aisha Kina Yi a hankali Baki gani ne!”
Fuskar ta, ta boye a jikin Mama tace
“Mama ba komai ba.”
Story continues below

Mama tayi Dariya tace
“To shikenan kun sauka lafiya?”
“Alhamdulillah Ina Basma?”
“Tana ciki ana Mata lalle.”
Mamah ce ta fito a daki Aisha ta karasa ta durkusa. Mamah ta dago ta tana fadin
“A’ah kin Iso lafiya?”
“Alhamdulillah!”
“Ya jikin?”
Mama ta kalla sai Tai kasa da Kai. Mamah tace
“Shiga ki watsa ruwa Bari a kawo miki Abinci.”
Tayi dakin Mamah da sauri. Mamah da Mama suka saki Dariya.
Tana Shiga Tai wanka ta fito ta saka Kaya. Abinci aka kawo Mata taci Tai sallah. Maryama ce ta shigo tace
“Anan za ai Miki lallen ne?”
“A’ah Bari nazo Nan ina Mujahida?”
“Taje amso Mana kayan mu!”
“Nawa fa?”
“Har dashi.”
“Wai ba a Gama ba har yanzu?”
Kai ta gyada.
“Kai har na gobe?”
“A’ah fa. Na daurin aure ne kawai acan”
“Ok!”
Ta dauki waya ta fara Kiran Aliyu Yana daukar wayar tace
“My Soulmate kaci abinci?”
“Ai Baki zo kin bani ba.”
“Gani Nan.”
Ta kalli Maryama tace
“Bari naje wajen Yaya na bashi abinci sai Nazo ai min.”
Ta fice. Kwance ta same shi a kan kujera. Ta karasa tace
“Yaya tashi kaci kada yunwa ta Kama ka.”
Ta kamo hannun sa ta mike ta nufi dining ya bita da kallo. Zuba Masa tayi ta juyo ta Ganshi zaune Akan kujera. Komawa tayi tace
“Yaya bakajin yunwar ne?”
“Ina ji Mana Amman ta ki;”
“Tawa Kuma Yaya?”
Kai ya gyada. Ta kamo hannunsa ta ya mike ta daura kan ta a kirjinsa tace
“To ai am all yours!”
“Da gaske?”
Kai ta gyada Masa. Ya dauke ta cak sukai daki. Sai uku ya bar ta nan sukai wanka suka shirya tazo suka karacin abinci. Tayi cikin gida shi Kuma yayi bangaren Abbah
Acan akai Mata lalle har dare wajen karfe goma ana Mata kitso tana cikin Yan Mata ana ta Shan Hira.
Wayar tace tayi Kara tana dubawa taga Aliyu ne dauka tayi tace
“Yaya na.”
“Kina Ina ne?”
“Ina bangaren Mamah.”
“Ya mukai?”
“Yaya kitso ake karasa min!”
“Kitso Kuma menene kitso?”
“In nazo ka gani an kusa gani Nan kaji Soulmate Dina.”
“Ina jiran ki ko na zo na taho dake.”
“A’ah da an gama Zan karaso.”
“Shikenan Ina Mama?”
“Tana dakin Mamah.”
“Ok sai kin dawo.”
Karfe goma da kwata aka Gama kitson kowa dake dakin yai ta yabon kitaon Dan yadda yai kyau har gadon bayan ta
Mikewa tayi taiwa Mai gyaran kan sallama. Maryama tace
“Ah Wai ba anan Zaki kwana ba.”
“Kinsan halin Yayanki ai.”
“Lallai Kam! Sai da safe.”
Ta fice. Suka hadu da Mujahida tace
“Ah an gama?”
Kai ta gyada tace
“Sai da safe.”
“Ah ba Zaki kwana anan ba.”
“In bar miji na shi kadai me zan muku?”
“Lallai Kam shi ai kinada abun Masa ko?”
“Eh kema kwanan Nan zaki faraiwa mijin ki.”
Ta wuce tana fadin
“Kada ya gaji da jira na.”
Ta fice. Tana shiga baya falo ta wuce dakin sa Tai wanka ta fito ta shirya cikin kayan baccin ta.
Dakin sa ta nufa. Yana zaune akan gado gaban sa system Yana danne danne ta bude kofa ta Shiga ta tsaya a jikin kofar tana kallon sa. Kamshin turaren ta shi yasa ya dago da sauri. Yana ganin ta ya mike ya bude Mata hannu ta karasa ta fada jikin sa.
Story continues below

Hannu ya daura Akan kan ta Yana shafa kitson ta. Tace
“Kayi hakuri Yaya na, na jima ko? Na tsaya Ina maka kwalliyya ne!”
“Na gani!”
Ya fada Yana dago ta. Zama tayi a gefen gado ta nuna Masa kanta tace
“Kaga kitson!”
“Wow wannan ne kitson Daman Amman yai kyau sosai Masha Allah.”
Ta nuna Masa hannu ta yai kissing ja da bakar fulawar Yana fadin
“Nima Baby na ta dawo amarya.”
Kafar ta, ta dago Masa tace
“Kaga kafar.”
Ta Mika Masa ya rike Yana kissing tindaga toe har sangalalon kafar zuwa cinyar ta daga Nan wasan ya canja salo.
Washe gari akai bridal shower Wanda amare suka shirya cikin white gown angwayen Kuma cikin black colour suit sunyi kyau.
Aisha tayi kwalliyya cikin doguwar riga baka Mai kyau Dan daga Kasar waje ta siyo ta. Ta hadu iyakar haduwa.
Aliyu sam bai je ba Aisha tayi tayi yace mutane sunyi yawa kuma itama da taje taga yan Mata sai Tai kishin zuwan Yayan nata dan kuwa tasan Aliyu karshe ne sai dai ba aganshi ba Amman zai sace zuciyar Yan Mata.
Washe gari akai kamu anan cikin gida akai ankon atamfa. Aisha tayi kyau Dan wacce taiwa amare makeup ita Tai mata ta Sha kyau.
Tin safe rabon sa da ita duk ya damu ya kira ma wayar ta Bata Shiga Sam. Sai Bayan isha’i suka dawo a gajiya sallah tayi sannan ta nufi bangaren ta
Tana Shiga ta zube Akan kujera tana maida numfashi Dan ta gaji. Ido ta lumshe kan kace me Bacci ta dauke ta.
Karfe takwas da Rabi ya dawo daga masallaci number Maryama ya Kira tana dauka yace
“Ina Heartbeat?”
“Yaya ta tafi ai muna dawowa.”
“Ok!”
Ya kashe wayar ya wuce dakin su. Yana Shiga ya hange ta Akan kujera tana bacci. Karasawa yayi ya gyara Mata kafa ya tsaya yana kallon ta.
Daukar ta yayi yai dakin sa da ita Akan gado ya ajiye ta tayi juyi sai ta bude Ido. Tana ganin sa tace
“Yaya!”
Yace
“Bacci tin yanzu?”
“Na gaji ne.”
“Ah kace gobe ba inda Zaki.”
“Haba dai Yaya na. Gobe fa dinner Kai ma zakaje “
“Wa? Ni ba inda zani. Kema ba inda Zaki.”
“Haba dai Yaya nidai a’ah daga ni har Kai za mu je. Kuma kasan har kayan da zamu sa fa na amso.”
Ta fada tana Bata fuska yace
“Eh gashi Nan sai wahalar min da Kai kike.”
“Ba Zan Kara ba.”
“Ina Kira Baki dauka ba ma!”
“Wayata fa tana daki ne Yaya.”
Hancin ta yaja yace
“Ba fa inda za a.”
“A’ah Yaya ni dai dan Allah gobe fa na dare ne!”
“Hmmmm.”
“Please Yaya na.”
Yaja hancin ta yace
“Sai ana kula Dani.”
“Wallahi zanyi.”
“To shikenan gobe ba inda Zaki sai lokacin dinner.”
“Na yadda!”
“Shikenan.”
Ta mike tayi juyi a gaban sa tace
“Yaya nayi kyau?”
“Kinyi Baby na. Sosai da sosai fa”
Tai murmushi ya janyo ta yace
“An min picture ko?”
“Da yawa kuwa Yaya.”
“Bari nai wanka!”
Ya mike ya fara cire Mata Kaya. Shima ya cire suka shige sukai wanka.
Washe gari dinnerbGaba daya Bata fita ba suna tare. Sai da akai magariba Mai makeup ta Gama yiwa amare tazo Tai mata ta shirya cikin wani cream kalar less mai kyau. Tayi kyau sosai. Aliyu da ya dawo daga masallaci ya shigo. A gaban Mirrow ya same ta tana kallon kan ta.
Tsayawa yayi yace
“Wacece wannan?”
Ta juyo ya zaro ido Yana fadin
“Masha Allah Baby love tayi kyau!”
Tai murmushi tace
“Yaya kazo ka shirya kada mu makara.”
Ta fita ta dauko masa kayan sa kallar less din sa. Tai kyau sosai.
Kallon kayan yayi yace
“Wannan fa?”
“Ni nayi maka.”
“Ah haba Baby love tai min Kaya. Kai masha Allah.”
Ya rumgume ta Yana kissing wuyan ta.
“Yaya…”
Bai ma San tana yi ba. Tace
“Yaya….”
Nan ma dai. Hannu ta daura akan sa tana fadin
“Soulmate!”
“Uhmmm!”
Ya fada Yana dagowa. Tace
“Ya dai?”
“Uhmm Ina son Matata.”
“Nima haka Yaya amman kaga fita zamuyi yanzu.”
“To shikenan!”
Ya fara cire Kaya. Ta Shiga yai wanka ya fito ya zauna. Ta shafa masa Mai sannan ya saka kayan. Yai kyau sosai.
Ta kalle shi tace
“Wow my soulmate yayi kyau shi na daban ne.”
“Kin fini kyau.”
“Kaji ana Kiran sallah muyi ko?”
Anan ya jasu sallah. Sukai sallah ya dauke ta suka tafi wajen dinner. Da suka je ma a mota suka tsaya tace
“Yaya!”
Ya juyo tace
“Muje ko?”
Ya bude ya fita yace
“Ina zuwa.”
Ya fita ya zagaya ya bude Mata ta fito. ya Kama hannun ta suka nufi gate din.
Lokacin har amare da ango sunje suka karasa ciki su Mamah suka hanga suka karasa suka Kara gaisar dasu sannan suka wuce wajen da Yaa Abubakar yake zaune shi da matar sa da Ya’ya sa. Sannan suka karasa wajen Yaa Usman daga nan suka wuce bangaren da aka tanada musu.
Zama sukai, Nan MC yace
“Muna yiwa Yarima Aliyu barka da zuwa tare da Mai dakin sa Gimbiyya Aisha. Kanwa ango da Amarya.”
Umar da Farouk ne suka zo suka gaisa sannan suka wuce wajen zaman su haka sauran ma Yaa Ibrahim da Umar da Mustapha duk suka zo suka gaishe su.
Haka aka cigaba da tafiyar da taron. Aisha ta mike ta kamo hannun sa tace
“Yaya muje ai Mana picture.”
Ta Kama hannun sa sukai ciki wajen Marayma da Muhammad. Maryama ta kamo hannun Aisha tace
“Kinyi kyau.”
Kema haka. Ta matsa tace
“Yaya kayi kyau.”
“Nagode!”
Nan suka gaisa da Aliyu sannan akai musu picture wajen Mujahida da Shu’aibu sukaje Suma akai musu pictures din sannan suka tashi suka koma wajen su.
MC ne ya Kira Yaa Aliyu da Aisha Akan su fito su Yi wa angwaye da Amarya liki. Nan suka fita suka farai musu ruwan kudi suna tsaye Yaa Abubakar da Matansu suka fito Suma sukai hau liki haka suka koma ma zaunin su.
Karfe Tara da Rabi ya matsa Mata sai sun tafi haka ta mike suka koma gida.
Washe gari akai yini Ranar asabar akai daurin aure da yamma akai walima. Sam Aliyu ya Hana ta Kai amare. Dan Dukkan su can garin su Aisha aka Kai su.
Gidaje ne iri daya ya gina musu guda biyar. Anan ya bawa Yaa Umar da Ibrahim da Mustapha ma key. Aka Kai Maryam da Mujahida can.
Gida ne manya wanda yake dauke da part biyu gini yai kyau na zamani Mai kyau. Abbah ya zuba musu Kaya masu kyau da tsada.
An Kai amare gidan su kowa an barsu da angwayen su duk a Daren suka more amarcin su. Kowa yaji dadin yadda ya samu amaren sa da mutuncin su.
Washe garin Kai amare da safe tana kwance a daki Aliyu ya shigo ya kalle ta yace
“Ya dai Baby Love?”
“Na gaji Yaya.’
Kallon ta ya tsaya yace
“Da yake an gama biki ko?”
Kai ta gyada tana murmushi. Yace
“Muje mu dawo nai Miki tausa ko?”
Kai ta gyada tace
“Ina zamu?”
“Dady ne yazo zaku gaisa.”
“Waye Dady?”
“Mijin Mama.”
“Allah sarki.’
Ta dire kafar ta tace
“Muje.”
Ya dauko Mata mayafi ta yafa sannan suka Fita. Falon Abbah suka isa kai tsaye. A bakin kofa sukai sallama aka amsa suka shigo. Tinda suka shiga Dady ya zuba mata ido tayi kasa da kai ta karasa ta zauna.
Story continues below

Nan ta gaishe su. Dady yace
“Masha Allah kaga kamar su daya da Yaya Rashida!”
“Haka ne har tafi Kama da ita akan maman ta.’
“Haka ne. Ya gidan Aisha?”
“Alhamdulillah!”
“Allah yai miki albarka.”
“Amin!”
Ya Miko Mata leda yace
“Ga wannan ba yawa.”
Tace
“Nagode Allah Kara budi.”
“Amin shikenan!”
Ta mike ta Kara godiya ta fita. Bangaren Mamah ta shiga, anan falo ta same su ta zauna suka gaisa sannan ta nuna musu abinda Dady ya bata.
Nan sukai godiya tare suka yini Dan Sai da akayi magariba sannan ta koma sashen ta ta hau shirin tarbar mijin ta.
Washe gari Mama ta tafi. Aisha da Aliyu Kuma suka tafi gidan Yaa Abubakar. Acan ta yini ranar sai dare suka dawo.
The next day suka je gidan Yaa Usman. Shima yini sukai. Sai upper day suka je gidan Umar da Farouk. Yini sukai tare Shima sai dare suka dawo
Washe gari duba Sha’awa sukaje ita da Mamah. An sallame ta Dan Momy ta koma gidan su. Suna zaune ita da Sha’awa a daki daya sai dai zaman gidan duk ba Dadi ba kamar yadda suka saba acan gidan su ba. Domin kuwa acan masu aiki ke musu komai daki sai Wanda suka zaba haka abinci sai Wanda suke so. Anan kuwa Mahaifiyar Momy ta Hana masu aiki Yi musu komai Kuma abinci Wanda akai shi ake Kai musu. Rayuwar gidan sai tayi musu kunci. Ga Sha’awa na fama da jinyar hannu Dan ma jikin ta da sauki Dan har an daura ta akan magani tana sha.
Lokacin da sukaje dakin Mahaifiyar Momy suka je Hajiya Barira. Tana ganin Mamah ta ce
“Barka da zuwa Rashida.”
Mamah ta durkusa tace
“Yauwah Hajiya Ina yini?”
“Lafiya Lou Alhamdulillah ya gida ya iyalai?”
“Alhamdulillah komai lafiya.”
Aisha ta durkusa itama ta gaishe ta. Hajiya ta amsa tana fadin
“Wacce wannan Naga dai ba Maryama bace.”
“Ba ita bace. ‘ya ta ce ta wajen Hafsa kanwata.”
“Masha Allah.”
Tace
“Bari a kawo muku lemo ko?”
“A’ah Hajiya ya jikin Sha’awar?”
“Da sauri suna can dakin su na da ai.”
“Allah sarki. Dan Allah Hajiya kuyi hakuri nayi nayi da shi ya janye yaki Amman insha Allahu kwanan Nan zata dawo.”
“Ba komai Rashida. Ai maganin ta kenan ta fada min duk abinda sukai Suma sai da Mahaifiyar Sha’awa tazo ta fada sannan ta fadan sauran. Hakika Bata kyau ta ba Amman ai yau ta girbe Abinda ta shuka tinda zaman mu take so tare ai shikenan.”
“Hajiya sharrin shaidan ne nasan ba halin ta bane.”
“Wai ke wacce irin zuciya ce dake. To Bari ma fada Miki daman can haka take haka take da bakin hali.”
“Hajiya ki daina fadar haka Dan Allah.”
“Gaskiyar Zan daina fada. Ko ni uwa ta hakuri nake da ita.”
“Ki Kara hakuri Hajiya zata canja insha Allahu.”
“Allah ya yadda!”
Nan masu aiki suka hau shigo da Katon din madara, maltina lemuka. Hajiya Barira tace
“Daga Ina?”
Mamah tace
“Ni na kawo wa Sha’awa “
“Allah sarki. Allah saka da Alheri ‘
Ta kalli masu aikin tace
“Ku Mika masu dakin su.”
Mamah ta mike tace
“Bari mu Shiga daga ciki.”
Suka nufi dakin Momy. A falon ta suka samu Sha’awa zaune rike da hannu. Suna Shiga ta mike tana fadin
“Sannun ku da zuwa.”
Mamah tace
“Yauwah jiki yayi kyau ko Sha’awa?”
“Eh Mamah ina yini?”
“Lafiya Lou ya jikin?”
“Alhamdulillah!”
Aisha tace
“Sannu ya jikin?”
“Da sauki ya gida?”
Story continues below

“Alhamdulillah!”
Mamah tace
“Ina Momyn Taki!”
“Tana ciki.”
“Yi mata magana.”
Ta mike ta shiga dakin. A kwance ta samu Momy idon ta yai jajir alamar tayi kuka. Sha’awa tace
“Wai kizo!”
Ta juya. Momy ta mike zaune tace
“Inji wa?”
“Mamah ce ta zo.”
Ta fita. Momy ta shiga ta wanka fuskar ta sannan ta fito ta nufi falo. Tana ganin Mamah tasaki murmushi tace
“Sannu da zuwa Yaya.”
“Yauwah ya kike ya gida?”
Ta zauna tace
“Alhamdulillah!”
“Ya me jikin?”
“Da sauki.”
Ta fada tana kallon Sha’awa.
Aisha ta juyo tace
“Ina yini?”
“Lafiya Lou ya gida ya Aliyun?”
“Alhamdulillah! Ya me jikin?”
“Da sauki.”
“Allah Kara suaki.”
“Amin.”
Ta kalli Mamah tace
“Ya taro?”
“Alhamdulillah ai Baki zo ba.”
“Bansan da idon da Zan kalle ku ba. Ina Aliyu “
“Yana Nan.”
Ta kalli Aisha tace
“Aisha Dan Allah ki yafen Mana.”
“Ba komai Momy ni ba kuyi min komai ba. Allah ya yafe Mana.”
“Amin. Ina son Naga Aliyu na nemi yafiyarsa.”
“Ai fa Yana Nan zan Masa magana yazo ya duba Sha’awa ai.”
Mamah ta fada.
Momy tace
“Ai kuwa su Abubakar sun zo da zasu kara dawowa har da matan su.”
“Allah sarki Kuma Basu fada min ba.”
“Allah sarki bakiga ba sun kawo kudi da kayan dubiya masu yawa wallahi.”
“Allah ya aka da alheri.”
“Amin Amin.”
Sai yamma suka tafi. Da Momy taje rakasu ta Kara neman yafiyar Mamah. Mamah tace
“Kiyi hakuri kema da abinda Alhaji yai Miki wallahi ina ta fama dashi insha Allahu Zaki dawo dakin ki.”
“Anya kuwa Alhjajii zai yafe min.”
“Akan me ba zai yafe miki ba Allah ma muke Masa laifi ya yafe Mana bare shi Dan Adam.”
“To Allah yasa ya yafen.”
“Amin. zamu tafi sai anjima”
“Nagode Allah kiyaye hanya.”
“Amin!”
Da dare suna zaune a daki. Aliyu zaune a gefen gado gaban sa system Yana aiki. Sanye yake da three quarter wando da riga armless. Ita Kuma tana gaban Mirrow tana shafa turare ta juyo tana kallon sa tace
“Soulmate yau munje duba Sha’awa ni da Mamah.”
“Ya jikin nata?”
“Da sauki!”
Ya rufe system ya dago Yana kallon ta. Murmushi ya saki yace
“Masha Allah kinyi kyau.”
Tai murmushi ta karasa ta zauna Akan cinyar sa ta sakala hannun ta a wuyansa tace
“Yaya Yana da kyau muje kaima ka dubo ta.”
Fuska ya tauke yace
“Saboda me?”
“Hadisi ne fa. Manzon Allah (SAW) yace Mai duba Mara lafiya Yana kan tafarkin aljanna harsai ya dawo.”
Shiru yayi tace
“Toh Yaya zamu.”
Nan ma Tai shiru tace
“Zafa mu samu lada.”
“Baby love!”
“Na’am!”
“Zani!”
Ta rumgume shi tana fadin
“Nagode Yayana.’
Kissing nata ya fara yana fadin
“Kece farin ciki na Mai haskakan rayuwa ta da daura ni a hanya in na kauce ki bani shawara akan aiki na kwana biyu bakya bani shawara kinsan kece babbar me bawa gwamna shawara dai ko?”
Tai murmushi tace
“Komai kanayi Yaya na. Ai da an haska maka Abu kake daukar haske ba abinda zan baka shawara yanzu sai addu’a Allah Taya riko ban taba ganin shugaba adali ba kamar ka.”
Yai murmushi. Wayar Aisha ce Tai Kara Yasa hannu ya dauko yaga ansa Sister!
Kallon ta yayi tace
“Bani sister Maryama ce kada ta katse.”
Received ya dannan ya Kai kunne yace
“Ina Kika bar mijinki Kika taho damun mu da wannan Daren?”
Story continues below

Shagwave murya tayi tace
“Daman Kai ka Hana ta Kirani ko ka hana ku dawo Kuma ko Yaya!”
“Kukan me zakiyi to?”
“Ba komai Yaya kud dawo Dan Allah.”
“Hmm rayuwar mu Kadan ce a garin Nan Dan ni ko a yanzu naga dama zamu tafi mu barki kada ki manta sauran watanni muyi gaba mulki mu tafi mu barki.”
“Allah Yaya bin ku zanyi.”
Aisha tasa hannu ta amshe wayar tana fadin
“Sorry sister Muna tare kinji.”
“To In-law Amman fushi nake dake.”
“Am sorry na barki Kisha amarcin ku.”
“Uhmm uhmm Allah Yayan ki ko baya Dagan kafa Sam.”
“Haba Kanwata ki zama Mai dauriyya Mana. Ki Bari jibi zamu dawo Zan zo zamu zauna kinji.”
“Nagode Sai da safe Daman ya Dan fita ne nace Bari na Kira ki.”
“To ki gaida Yayan kinji.”
“Zaiji sai da safe.”
“Allah bamu alheri.”
Ta kashe ta kalli Aliyu dake kallon ta.
Yace
“Menene yake damun ta?”
Murmushi tayi tace
“Kasan ta girma Kuma abun yazo Mata a sabon shiga.”
“Kamar ya?”
Tai murmushi yace
“Ke me yasa hakan bai faru ba.”
“Saboda Ammi na tare Dani.”
“As?”
“Ba zaka gane ba wannan sirrin mune.”
Gira ya dage yace
“Ko?”
“Eh Yaya yaushe zaka kaini Nijar din ne?”
“Sai kin haihu.”
Ido ta zaro tace
“Haba dai Yaya Dan Allah ka kaini Nan kusa Haihuwa har Nan da wata shida ko sama fa.”
“Shine me?”
“Ni dai ka Kai ni Ina son naje wajen ta.”
“Bakya son zuwa wajen Mama.”
“Yaya ai can akwai kashe kudi.”
Gyara zama yayi yace
“Ban gane ba?”
“Yaya can da nisa saboda acan kudin jirgi zamu biya, Kuma…..”
Hannun ta ya Kama yace
“Me Kika dauken Aysher!”
Da sauri ta dago Dan yaushe rabon da ya Kira sunan ta. Yace
“Ni a ganin na ko da auren da mukai mun zama daya. Bare a yanzu da kike jinana Kanwata Kuma Matata. Komai naki nawa ne kamar yadda komai nawa yake naki. Zan iya Baki komai a rayuwa ta. Yau ko kasa dari kike so na Kai ki Zan Kai ki ko da a gadon Baya na bare inada kudin da Zan Kai ki. Daga yanzu ki cire komai a ranki ki na fadan komai kike so nai Miki ko nayiwa wasu kinji ko?”
Hannunsa da ke rike da nata ta murza tace
“Kayi hakuri Yaya bazan sake ba zan kiyaye.”
“Ki fadan yanzu me kike so? Ki fada min.”
Shiru tayi ya janyo ta jikin sa yace
“Baby love Ina da kudin da ban San iya karsu ba. Dan haka ki fada min me kike so nai Miki ko wasu.”
“Yaya rayuwar matan garin mu nake so a gyara a inganta!”
“Kamar me?”
“Kamar iyayen mu a Basu horar wa da jari wasu a basu sana’a a inganta a wayar da da kan iyayen mu abar ya’tan su syluyi karatu sannan a duba Wanda Basu da kokari akai su makarantu da zasubkoyi sana’a da abubuwa. Shine abinda nake burin gaba ka Gama da iyayen mu maza da yayen mu wannan shine abinda naga baka duba ba.”
Kai ya gyada yace
“Wannan haka yake. Za a bude foundation wanda zai zamo under ke. Kece jagora Taki kice Zan bude Miki account Zan na sakabmiki kudi kiyi abinda kike so. Ki tsara komai Zan nemar Miki masu taimaka Miki.”
Rumgume shi tayi ta fara romancing nasa daga Nan suka Lula duniyar masoya
*
**
***
*****
******
Kallon sa ta tsaya yace
“Please kwanta ni na duba ki Ina da abubuwa.”
Komawa tayi ta kwanta ya Kara bude rigar tata Yana kallon inda akai Mata aiki. Hannu ya daura a akai Wanda daga shi har ita ya saukar musu da wani irin Abu a jiki Dan haka da sauri ya janye hannu ya juya Yana fadin
“Tashi!”
Story continues below

Itama jiki a sanyaye ta mike ta gyara rigar tana zaune yace
“Ina Annur?”
“Yana wajen Nurse!”
“Wa Kika bawa?”
Shiru tayi. Yace
“Magana nake fa!”
“Kaje ka duba.”
Yai murmushi yace
“Hmmm ko? Ai da nane dole na tambaya wa aka Kai wa.
Shiru tayi tace
“Me kike ji?”
“Ni fa am fine ba abinda yake damu na.”
“Sure?”
“Yes!”
“Zan Miki allura sai ki mike.”
“Kai min a hannu!”
Kallon ta ya tsaya yi. Ta Kara daure fuska tace
“Please ni Ina son na tafi gida in Kuma ba kai zakai min ba ka Kai ni inda za ai min.”
Murmushi yayi ya koma ya zauna. Knocking akai ya bada izinin Shiga. Nurse ta shigo rike da Babyn Annur. Yana ganin ta ya mike Yana fadin
“Ashe Yana wajen ki!”
Kai ta daga tace
“Wallahi.”
Ta mika Masa Babyn. Ya amsa yana fadin
“Baby na me iyaye da yawa Ina ka baro Momyn ka Nusy?”
Kai Fateema ta dauke tana Kara daure fuska. Shi Kuma ya amshi Annur Yana tai masa magana kamar yana ji.
Fateema kuwa ta cika tai taf, kamar zatai hawaye. Can ya dauki waya ya Kira nurse. Tana zuwa tace
“Ki mata allurar.”
Ya mike ya fice. Allurar tai mata sannan ta fita. Zama tayi tin tana jiran su har ta fara Jin Bacci. Akan table ta daura kan ta take Bacci ya dauke ta Dan bashin da ta ci nasa. Sai da ya dauki awa wajen biyu sannan suka dawo Shima da Annur ya fara nuna alamun yana son shan abincin sa. Yana shigowa ya bita da kallo baccin ta take hankali kwance. Karasawa yai ya zauna. Ya kalli Annur da ya saka hannu a Baki Yana tsotsa.
Agogo ya kalla taga har daya tayi so yake yai sallah Amman Annur fa. Ganin har Bacci ya dauke shi yasa ya kwantar dashi.
Yana mikewa ta mike tana Mika. Ban daki ya Shiga yayi Alwala yazo ya tada Sallah. Office din ta kalla ta hango Annur kwance Yana bacci.
Karasawa tayi ta leka sa, daukar sa tayi ta koma ta zauna. Yana idar wa yai addu’a sannan ya mike ya karaso Yana fadin
“Muje na Kai ki gida ko?”
“Ni bana so Yaya Anwar ne zai Kai ni.”
Ta fada ta mike gaban ta yasha yace
“Wai yaushe Fateema ta zama haka ne. Fateeman da nasani Mai sanyin Hali ce.”
Wani kallo ta wurga masa ta zagaye shi ta fita. Office din Anwar ta Shiga Yana zaune ya dago ta Shiga tace
“Yaya kazo ka kaini gida!”
“Ok!”
Ya fada ya mike sannan ya ce
“Muje!”
Ya fita tabi bayan sa, Fu’ad na tsaye ta taga Yana kallon su. Har suka fita sannan ya koma ya zauna Yana girgiza Kai.
Murmushi ya saki yace
“Hmmm ni Fateema take son ta tuhuma ko me? Hmmm anyway na gano ki kina so na Kuma kina kishi na.”
Kafada ya dage ya juya kan system din sa.
Anwar na dire ta ce
“Nagode!”
Ta fita. Tayi ciki. Baba da Hajiya ta sama a falo Dan haka Tai musu sannu da gida. Har ta wuce Baba tace
“Wai yau akai Kika Dade!”
“Wallahi abubuwan ne da yawa”
“Ok ba dai wata matsala ko?”
“Eh Babu!”
“Madallah!”
“Bari naje nai sallah!”
“Toh!”
Tayi dakin ta ta ajiye Annur ta Shiga Tai Alwala Tai sallah sannan ta zauna tana addu’a. Tana kan sallaya Annur ya tashi ta mike ta Isa wajen sa ta dauke shi ta fara bashi nonon.
Tana cikin bashi aka budo kofar da sallama. Amsawa tayi Bata dago ba Dan Nusaiba ce. Sai da ta gama bashi ta dago tace
“Ki zauna Mana.”
Zama tayi ta amshe shi ta daura shi a kafada tace
“Annur I miss you!”
Story continues below

Ta mike ta sauka kasa ta zubo abinci tai zaman ta. Nusaiba kuwa na sama tana ta kula da Babyn ta Annur.
Baba dake zaune ta kalli Fateema tace
“Wai me yake damun ki?”
“Ba komai Baba!”
Hajiya tace
“Allah yasa to!”
Nusaiba tana can har Annur yai Bacci ta goya shi sai da ya tashi suka sauko ta bada shi aka bashi abinci sannan ta Kara daukar sa. Yini tayi a gida Dan har dare tana gidan.
Da magariba Fateema na sama ita kadai sai Annur dake hannun ta. Nusaiba ta shigo tace
“Anty Yayan mu ne yace na Kai Masa Annur!”
“Kije kice yayi bacci!”
“Toh!”
Ta sauka ta fada Masa. Yai murmushi ya mike ya nufi dakin ta.
Tana zaune rike da Annur Hannu dake kallon ta. Kofar aka budo ta dago da sauri. Fu’ad ta gani ta hade fuska ya karaso yasa hannu ya zare Annur yace
“Tayaya za a Hana Dady ganin Babyn sa. Dan Momyn sa na fushi dashi sai Kai ma kayi Dani. Haka ake my son. ka fadawa Momyn ka in an Mata laifi ta fito fili ta fada ba ta kullaci mutum ba.”
Ya juya ya fita ta dalla Masa harara sai Kuma ta fada saman gado tana kuka. Ta rasa kukan me take Yi. A haka Bacci ya dauke ta. Bata San an kawo Annur ba sai da ta tashi sannan Dan yin sallah dare. Gyara Masa kwanciyya tayi sannan tayi Alwala tazo tayi sallah.
Nusaiba ce zaune a kan kujera Fu’ad na tsaye yace
“Fateema na fushi dani!”
“Saboda me?”
“Saboda tana kishi na!”
“Kishi Kuma Yaya?”
“Eh!”
“Menene tsakanin ku da Fateema na zata kanwar ka ce!”
“No Matata ce…..”
“Matar ka?”
Kai ya gyada yace
“Amman mun rabu, mijin ta Kuma ya rasu!”
“Zan iya sanin labari ku!”
“Why not…”
Nan ya Bata labarin komai Akan soyayyar su. Jikin Nusaiba ne yai sanyi domin kuwa daga labarin da Fu’ad ya Bata ta gano daga shi har Fateema na son juna kaddara ce kawai ta raba su Kuma a yanzu tasan Dole Fateema ta komawa Fu’ad shin ita Fu’ad na son ta ne? A’ah Dan bai taba nuna Mata alamu ba in ta aure shi zatasha wahala ne kawai domin kuwa ta gane Fu’ad ba Wanda yake so sama da Fateema zai iya komai Dan Fateema Dan haka gwara ta cirewa kan ta son shi Dan tasan wahala kawai take Sha. Amman tayaya zata cire shi a zuciyar ta.
Hawaye ne ya ke zuba a idon ta ya durkusa a gaban ta Yana fadin
“Nusaiba menene kike kuka Dan Allah?”
Kofar aka budo. Fateema ce, wani kallo ta aikawa da Fu’ad sannan tace
“Hajiya tace ka Bata maganin!”
Nusaiba ya kalla yace
“Ina zuwa!”
Sannan ya dauko ya Mika Mata. Amsa tayi ta juya ta fita.
Ya koma gaban yace
“Nusaiba fada min mana menene kefa Kanwata ce.”
Mikewa tayi ta fita a guje Dan yadda kuka yaci karfin ta. Fateema dake ta taga taga fitar ta taga Fu’ad ya bi bayan ta sai abin ya Kulle Mata Kai.
Kan ya karasa ta shiga gida. Dan haka ya juyo ya koma. Washe gari ma Sam bata Shiga gidan ba Fateema ma Sai taji ba Dadi domin kuwa tana Taya ta kula da Annur sosai.
The next day da Yamma Mamin Nusaiba ta shigo domin Yi musu sallama. Ta tafi Amman har dare Babu Nusaiba wannan yasa Fateema ta bude kayan da akai Mata na suna ta debar Mata dogayen riguna masu kyau da tsada. Sannan ta saka Mata turare ta fita. Tana fita compound ta samu Fu’ad zai shigo. Kai ta dauke domin itama rabon ta da shi tin Ranar da ta amso wa Hajiya magani. Da kallo ya bita ta fice.
Gidan ta shiga ta samu Mami da Nusaiba a falo. Fateema ta zauna suka gaisa da Mami sannan ta kalli Nusaiba dake gaishe ta ta amsa tana fadin
“Shine kwana biyu Baki shigo ba ko? Dan ki Yana ta kewar ki.”
Story continues below

“Wallahi Anty Ina son nazo nai muku sallama ma.”
“Ai shine ni nazo na Miki sallamar.”
Mami tace
“Ai zata shigo ne. Ki tashi kije kiyiwa su Baba Sallama suma.”
“Toh!”
Fateema ta Mika Mata leda tace
“Gashi ba yawa.”
Ta mikawa Mami ledar turarukan Mami ta ta amsa tana godiya. Sannan suka mike suka tafi can gida. A can Nusaiba Tai musu sallama ta juyo zata fita sashen Fu’ad ta kalla ji tayi kamar taje Amman sai ta fice kawai.
Washe gari sai Ji yayi ance sun tashi. Ba karamin mamaki yayi ba shin me yaiwa Nusaiba me yayi ko itama tana Taya Fateema Jin haushin sa ne to shi me yayi. Shima Sai kawai ya share ta.
Lokacin da Fateema Tai shekara da haihuwa suka so su koma saboda ta gama amsar treatment din ta Annur ma haka duk da ance Faterma zatana zuwa ana duba ta bayan wata shida shida. amman Mami kememe ta hana tace Baba da Fateema su Kara zama. Kuma Dan har lokacin Fateema na zuwa asibiti ai Mata check up. Haka suka zauna ba Dan sun so ba bama Fateema saboda yanzu Sam basa shiri sa Fu’ad sai suyi kwana biyar ko sati Basu hadu ba. Annur kuwa in Yana gida yini suke tare in kuwa zai je aiki kan ya fita sai ya Ganshi haka da ya dawo zai dauke shi. Kuma in Yana gida shi kai shi yai Masa shopping. Wannan yasa Annur ya gane Fu’ad Dan ko kuka yake yana Jin muryar sa yake shiru. Haka in Yana Shan nono Shima da yaji muryar sa yake fara waige waige.
Fateema kuwa zuwa lokacin son Fu’ad Yana gab da Mata illa ganin abun Yana neman mata yawa Yasa ta Dan saukowa Fu’ad amma shi Kuma sai Fu’ad ya nuna bai ma san tana Yi ba domin kuwa shi ta dan sa kawai yake.
Zaune yake a office wayar sa ta hau Kara. Dauka yayi yakai kunne tai Masa sallama ya amsa Yana fadin
“Kanwata tace?”
“Ita ce baka manta Dani ba.”
“Haba dai tayaya Zan manta dake Nusy!”
“To Yaya ya kake ya aiki Ina Anty na da Annur?”
“Suna lafiya Lou.”
“Ina ta zuba Ido naji ance za ai bikin ka da Anty!”
“Wacce Antyn?”
“Momyn Annur!”
Yai murmushi yace
“Ai ta daina so na.”
“Akan me?”
“Haka kawai.”
“Da Wasa kake Yaya Antyna tana son ka.”
“Saboda me Kika ce haka.”
“Wallahi Yaya daga labarin da ka bani ya tabattar min da haka.”
Ajiyar zuciya ya sauke yace
“Fateema tana wani tunani akai na.”
“Me kake tunani!”
“Ta bani laifin Akan sakin da nai mata.”
“Yaya a yanzu Anty ba abinda take bukata sai kulawa Kuma kulawar ta masoyi a wannan lokacin tana bukatar kulawar mijin ta tinda ya mutu Kai zaka maye gurbi sa. Dan Allah ka kula da ita.”
“Shikenan Amman me yasa kika daina kulani.”
“Yaya ba Zan boye maka ba. da na kamu da soyayyar ka Amman tinda naji labarin ka da Anty na hakura da Kai saboda na gane kafi karfi na. Na koma gida nayi fama da kai na kan na cire ka. Ina muku fatan alheri Kai da Anty na.”
“Ina godiya Kanwata Allah Baki miji na gari!”
“Amin Yaya nagode!”
Sukai sallama ya jingina da kujerar Yana lumshe ido. Baki ya cije yace
“A haka Fateema ke so na tana share ni. A hakan.”
Kowa sai yace Fateema na son sa to zai gwada ya tabbatar da hakan. Yai murmushi ya mike ya koma kan aikinsa.
Shekarar Annur daya da wata takwas amman ya zama katoto Dan har ya fara tafiya ko ina ga kyan sa dake Kara fitowa. In Fu’ad ya fita dashi aiki sai yamma suke dawo wa Dan Yana tafi Masa da abinda yake ci.
Lokacin da ta yaye Annur ma duk Fu’ad ne ya dinga dawainiyya dashi tare suke kwana in ya tashi da dare ya bashi madara ko abincin sa a haka har ya saba da yayen ya daina damun maman sa da zai sha nono.
*
Wai Ina Gloria ne. Lokacin da ta bar gidan Fauwaz hotel taje ta Kama daki sannan taje airport tayi booking flight.
Bayan nan ta koma dakin da ta Kama Tana zaune Tana kallon news taga ana nuni akan hatsarin su Annur. Kuka ta saki da taji ance yaro daya da Mai gidan sun mutu. Sannan matar Tana cikin mawuyacin Hali ba a San a halin da take ciki ba. Hakan ta kwana tana kuka washe gari ta tafi airport ta bar gasar.
Da taje gida ta fadawa iyayen ta Fauwaz sunyi hatsari ne shi da Annur sun rasu. Haka Dad din ta yai ta tausayin sa.
Bayan su Mami sun nutsu suka je har gidan su Gloria Mahaifin su ya amshe su Nan sukai musu gaisuwa sannan suka ce suna son a tsare musu Gloria na wata hudu da kwana goma kan ta kula ko wannen Namiji Dan a ga ko tana da cikin Fauwaz ko babu.
Lokacin da Fateema ta haihu aka gane Gloria Bata da ciki wannan Yasa aka raba gadon Fu’ad aka bawa Gloria da Fateema da Annur amman Fateema tace su Mami su ajiye na Annur.
Dadyn Fauwaz yace
“A’ah za ana juya Masa kudin wani aka siyi gida wasu aka saka a business aka bude Masa account ana zuba Masa profit din sa.
Gloria da farko ta zata taci bulus Amman sai ta fara mugayen mafarkai Annur Yana zuwa Yana ce Mata meyasa ta kashe shi. Tin Bata tsorata har ta fara tsorata duk ta fige. Mahaifiyar ta da Baban ta suna ta neman Mata magani Amman abu yaki ci yaki cinyewa Sam ta daina Bacci Dan da ta kwanta Take wannan mafarkin. Duk sai ta zama kamar mahaukaciya.
Ganin in ba fada tayi ba zata mutu yasa ta fadawa iyayen ta cewa ita ta kunce burkin motar su Fauwaz sukai hatsari suka mutu. Mahaifin ta ya shiga tashin hankali na abinda ta aikata.
Dan haka ya Kira su Mami cewa suna tafe. Bayan sunje sukai musu bayani komai sannan yace
“Gata Nan ku dauke ta kukai ta hukuma ta dauki mataki Akan ta.”
Mami Tai shiru. Dady yace
“Ni da kyale ta akayi kawai.”
“Wallahi ko kun kyale ni ba Zan kyale ba Zan shigar da kara a yanke Mata hukunci.”
“To shikenan zai akai ta.”
Dad din Gloria shi ya shigar da komai na kara aka Kai ta aka shigar da kara Ranar zama ba a wani Bata lokaci ba ta amsa laifin ta Wanda alkali ya yanke Mata kisa ta hanyar rataya. Wanda aka tafi gidan yari da ita Dan Sai gwamnan garin ya saka hannu tukkuna.
Da labari ya jewa Fateema sai taji mutuwar Fauwaz ta dawo Mata saboda Wanda duk sai ta kadaita kan ta. Fu’ad da yake Yana yawan bibiyar ta Dan ko dare ko Rana Yana sanin a halin da take ciki. wannan yasa ya fara shige Mata Yana son ya Bata agaji Amman a lokacin ita Kuma zuciyar ta duk ta kuntace Dan ko magana ma Bata son tayi.
Lokacin Husnah ta haifi Yar ta mace ta tafi gida ma tana wanka.
Zaune take a dakin ta ya Shiga ta dago ta kalle shi sai ta dauke Kai. Zama yayi yace
“Teemah ya Kama mu ajiye komai mu fuskanci rayuwar mu.”
Kallon sa take Amman batace kala ba. Yace
“Teemah har yanzu kina so na?”
Wani kallo ta wurga masa ta mike tace
“A’ah!”
Ta fice a dakin kawai. Girgiza Kai yayi Yana mamakin Wai yaushe Fateema ta zama Mai tsiwa haka ne.
Mikewa yayi ya fita Shima. Tin daga lokacin bai Kara Shiga harkar ta ba Wanda in yaga tana wajen ma baya zama.
Zaune yake a main falo Yana kallo ta shigo ta zauna ta dawo daga gidan Husnah Dan ta dawo jiya Ido ta lumshe. Kallon ta yayi yaga yadda tayi kyau. Sanye take cikin wata doguwar riga milk kala tai Mata kyau ta yafa mayafin rigar kanta yasha gyara wani Abu yaji ya tsarga Masa.
Wayar sa ce tayi Kara ita ta dawo dashi daga kallon Fateema itama ta dago tana kallon sa. Received ya dannan ya Kai kunne yace
“Hello sweetheart!”
Intisar da ke dayan gefen Tai mamaki Anya kuwa Fu’ad ne yace Mata sweetheart
+
*Nace Fu’ad wata aka samu ko kuma me?*
1
Bro Yaa Aminu Allah yasa an fara bikin nan naka a sa’a Allah yasa a gama lafiya ya sanya alheri Amin