WA NAKE SO CHAPTER 4

WA NAKE SO CHAPTER 4

Aisha kuwa suna rabuwa ta cigaba da tafiya tana dan tsale tsalen ta har ta karasa gida. Tana shiga da sallama ta shiga wacce ta nuna alamar tana cikin jin dadi da farin ciki.

Ummah ta gani tana kwashe kayan wanke wanke sannan ta karasa ta ce,

“Ummah ya gida?”

“Lafiya yar gidan Yayan ta. Ya makarantar?”

“Lafiya Alhamdulilah!”

Tayi cikin dakin ta. Ta  cire kaya cike take da murna da nishadi. Ta fito ta shiga bayi, Wanka tayi kamar yadda ta saba ta. Sannan ta fito ta shafa mai ta saka doguwar rigar atamfa batai kwalliya ba dan bata dame ta ba.

Gun Ummah ta Karasa dake bakin murhu tana kada miyar amsa tayi ta ce,

“Ummah tin da na dawo ai sai na karasa.”

Murmushi Ummah tayi ta ce,

“Lafiya na ganki cikin nishadi haka?”

Shiru Aisha tayi can ta ce,

“Ummah murna nake na bada hadda ta. Kuma Ummah Malam ya ce, an kusa tsayar mana da lokacin sauka “

Murmushi kan fuskar Ummah ne ya dadu ta ce,

“Ah Alhamdulilah Allah yasa Yayan ki na nan.”

“Ameen!”

Haka suka karashe abinda zasu yi. Aisha ta wuce tayo alwala sannan ta hau kan sallaya.

Akan sallaya ta zauna har akai isha’i tana lazimi. shigowar Baba yasa ta shafa.

“Sannu da zuwa Malam!”

Ummah ta fada.

“Yauwah Masa’uda ya gidan?”

Baba ya fada yana zama a inda ake shimfida masa tabarmar sa.

Ummah ta ce,

“Lafiya lou.”

Aisha ce ta mike ta karasa gefen Baba ta ce,

“Sannu da zuwa Baba ya kasuwar?”

“Alhamdulilah yar gidan yayan ta ya makaranta?”

“Lafiya Alhamdulilah!”

Ta mike ta dauko masa kwanon sha wanda suka zuba masa ruwan randa.

Amsa yayi ya sha yana sanya mata albarka sannan ta gabatar masa da abinci ita ma ta dauko nasu ita da Ummah suka fara cin tuwon masara miyar kuka wacce aka zuba mata wadatacen wake a ciki miyar tai kauri da dadi.

Sai da suka gama kowa yai hamdala suka wanke hannu da kuskure baki sannan ta zauna Baba yana kara mata karatun ta.

Sun jima sannan yai masu tarihi kamar yadda ya saba da jan hanakali akan hakuri da rashin son abin duniya wanda wannan ya zama kamar a jinin Aisha yake dan duk irin abubuwan da Baba yake fadi sam bata bari su tafi ba tare da tai amfani da su ba wanda suke sa mata jin dadi in tana aiki dasu.

STORY CONTINUES BELOW

Allah ya basu hakuri sannan abin duniya baya gaban su duk abinda suka samu godiya suke ga Allah su amshi shi hannu bibbiyu.

Sai tara da rabi ta mike tai alwala ta shige dakin ta ta saka kayan bacci sannan ta kwanta. Bayan tayi addu’oin ta.

Karfe biyun dare kamar yadda ya zama al adar gidan duk sukan mike suyo alwala su hau kan sallaya su mika bukatun su gurin Allah maji rokan bayin sa. Wanda a wannan lokacin Allah kan sakko kasan al arshi dan jin bukatun bayin sa tare da biya musu. Wacce addu’a a irin wadan nan lokutan bata da hijab.

Addu’ar Aisha bai wuce biyu zuwa uku ba. Na daya Allah ya jikan mahaifin ta sai mahaifiyar ta da kuma iyayen goyon ta da suka rike ta tamkar yar cikin su ba wani banbanci dan abinda zasu yi mata ma dan su basa masa. Wannan ita ce bukatarta ta farko.

Sai kuma akan cikar burin ta wanda burin bai wuce kyautatawa al umma ba. Tana rokan Allah ya bata ikon da zata wahaltawa al umma ta samar da abin da zata taimakawa mutanen su sam bata ta tata rayuwar sai ta mutane.

Sai addu’ar ta ta uku jama’a da mamata da marasa lafiya shikenan sun ta dada bai fi tayiwa Yayan ta akan karatun sa ba sai kuma ita tayi akan Allah ya bata miji na gari dukka da tasan Yayan ta miji na gari ne amman kullum bata fasa wannan addu’ar.

Har karfe uku sannan ta kwanta wanda tin daga lokacin ta fara jin wani matsanan cin ciwon kai da zazzabi da suka rufar mata. Da kyar ta samu bacci ya dauke ta.

Karfe biyar da minti ashirin ta farka da rawar sanyi. Fita tayi jikin ta lullube da hijab alwala tayi tana rawar sanyi sannan ta shige daki. sallah tayi, Tana idar wa ta haye kan katifar ta ta lulluba da bargo.

Ummah ce ta leko ta ce,

“Au har kin kwanta.”

“Eh!”

Ta fada cikin sanyin murya.

Juyawa Ummah tayi ta nufi murhu dan daura abin kari.  Karfe bakwai dai dai Ummah ta juye kokon da ta dama acikin kular da suke zuba abinci dan kada yai sanyi kan ta gama siyar kosan ta.

Ummah tana aikin tana mamakin rashin fitowar Aisha har lokacin. Bakwai da rabi ta gama har dudamen tuwon ta.

Ruwan wanka ta hadawa Baba sannan ta shiga ta fada masa ta kai masa. Dakin Aisha ta shiga wacce ba bacci take ba saboda yadda kan ta ke ciwo ga zazzabi.

Zama Ummah tayi a gefen ta ta ce,

“Wai yau lafiya baki tashi ba har yanzu ko ba zaki tahfiz din ba?”

Ta fada tana yaye zanin da ta rufa dashi. Idon ta ta kalla ta gansu jajir da su da sauri ta daura hannun ta akan ta taji zafi kamar wuta.

“Subhanallahi baki da lafiya?”

Kai Aisha ta gyada tana lumshe ido wanda take jin zafin ciwon kamar a cikin sa.

“Bari na shirya mu tafi asibiti amman sai kin sha koko da dan panadol.”

Ummah ta fada tana fita. Lokacin Abbah ya fito ta ce,

“Malam Aisha ce ba lafiya!”

Da sauri yayi dakin Aisha yana

“Uwa ta sannu!”

Kai ta gyada masa kawai. Ummah ta shigo hannu ta da kofi. Malam ta mikawa ta fita ta dauko maganin. Malam da kan sa ya bata kokon Ummah ta bata maganin tana hadiyewa ta dawo da shi da kokon da ta sha.

Ummah ce ta gyara mata jiki sannan ta mike tai wanka suka fito suka nufi aisbiti wanda yake da tazara sosai da su.

Ko da suka je ma sai uban jama’a ba wasu likitocin kirki. wasun su na zaune ma suna ta hira duk da ga patient nan da yawa.

Sun jima amman har yamma basu samu damar ganin likita ba. Ummah tai ta roka amman suka ce su sun tashi.

Ga jikin Aisha da yai zafi sosai. Wata mata ce tai mata kwatan cen wani chemist wannan yasa Ummah suka nufi can.

Yadda zazzabin yaci jikin ta ya ce, sai an kara mata ruwa sannan ya bata magunguna. Gida suka nufa tare ya saka mata ruwa sukai sallama. Kan anjima zai dawo ya cire mata.

Ummah ta mike ta hau gyara gida sannan ta daura abinci. Kan magariba ta gama ta komai da Aisha take anan suka jiyo sallama. Mai chemist ne ya dawo ya cire mata wanda sai da ya zauna na minti goma sha biyar sannan ya kare ya cire yai mata allura ya tafi.

Wannan dalilin yasa sam Aisha bata je gun Gwamna ba. Duk da abin na ranta.

*

A bangaren Aliyu shima sosai ya shiga damuwa har damuwar yasa a ransa sai gashi shima zazzabi ya kamashi.

Wanda har rawar sanyi ya dinga ga shi tunanin yarinyar yaki fita aran sa.

Washe gari daman lahadi ba inda yaje. Sai dr da ya kira yai masa treatment.

Haka duk ya damu cikin lokaci kadan ya rame wanda ko ran Monday mutane da yawa sai da suka tambaye shi ko lafiya ya rame haka ya ce ya dan kwanta ciwo ne.

Haka talata a barander ya yini dan son ganin ta zo duk da bai da lafiya amman haka ya yini gun.

Laraba kuwa da ya fita hankalin sa na ga yarinyar kar ya fita tazo. Dan haka karfe biyu ya dawo nan ya hau tambayar Baba mai gadi ba wanda yazo neman sa. amman ya ce ba wanda yazo.

Har ranar Juma’a haka bai da sukuni da ya gaji dai ya fito ya fadawa Baba mai gadi wannan yarinyar bata dawo ba. Ya ce,

“Bata dawo ba.!”

“Kasan gidan su ne?”

kai ya girgiza ya ce,

“A’ah ranka ya dade.”

“Sunan ta?”

Nan ma haka ya ce,

“Ban sani ba wallahi Ranka ya dade.”

Kai ya jinjina Mai Gadi ya ce,

“Ko a je a nemo ta ne.”

Hannu ya daga masa alamar A’ah sannan ya shige ciki. A ransa ya ce,

“To ko dai aljanna ce.”

Kai ya girgiza ya ce,

“Ina A’ah mutun ce.”

Da ya rufe ido sai yaga Aisha haka ko yaji voice nata a cikin kunnen sa.

Sosai ya damu ya tada hankali abu sati daya sati biyu har ya fitar da rai amman har hirar da sukai a gidan da kuma ya tafi raka ta in ya tino shi kadai yai ta dariya.

“Kana namiji amman kana tafiya sai kace mace. Macen ma mai ciki!”

Ta fada lokacin da yana raka ta.

Murmushi kawai yai mata. Ta ce,

“Wai in nai magana baka ban amsa nifa bana so.”

“To shikenan kiyi hakuri.”

Kai ta gyada ta ce,

“Kokai fa!”

Dariya ya kwalkwale da ita

“Wai ko kai fa.”

Kamar wani yaro. Can kuma sai ya hade fuska tina yafa nemi yarinyar ya rasa.

Aisha kuwa sosai ta kwata jinya har tsawon kwana biyar bata warke ba inda da suka je asibitin garin aka kara wulakanta su.  Wannan yasa suka tafi babban asibiti suna zuwa aka kire su tare da basu gado.

Har da karin jini akai mata dan ance jinin ta yai kasa saboda bata cin abinci. Haka ta sha allurai sai da sukai sati biyu a asibiti sannan ta fara jin sauki.

Dan ma Aisha akwai dauriya duk ciwon da take kamar zata mutu nunawa iyayen take jikin ta fa Alhamdulilah.

Duk ta rame ta dada fari ta zama kamar ka gure ta ta fadi dan rashin jiki.

Satin su biyu da kwana uku aka sallamo su suka koma gida nan suka hada mata da na gargajiya.

Cikin hukuncin ubangiji sai jiki yai sauki amman har loacin bata fara fita ba dan jikin sam ba kwari.

Sai da tai wata daya sannan ta samu saukin jiki har ta fara shirin komawa makaranta.

Da makarantar isilamiyya ta fara zuwa dan an farai musu interview ta saukar su. Wanda ranar da taje akai mata kuma tana daya daga cikin wadan da suka ci za ayi dasu.

A ranar hankalin ta na ga taje gidan gwamna ko zataga mutunin da bata san sunan sa ba ya ce zai taimake ta.

Amman kuma bata jin zata iya tafiya mai nisa yanzu Ma Baba ne ya kawo ta akan keken sa. Ana tashi ta fito kuma ta tadda shi ya dawo daukar ta.

Haka ko boko shi yake kai ta ya dauko ta. A haka aka sa ranar saukar su sati biyu masu zuwa.

Ankon atanfa suka fitar kalar ta blue da ja da baki. sai fararen hijab maza kuma shadda ce kalar blue.

Nan Baba ya siyo mata komai aka adana dan jiran ranar kawai suke. Taso Yaa Muhammad na nan amma taga alamar baya nan za ai gashi a lokacin suna SS 1 first term.Aliyu kuwa yana can duk ya rasa nutsuwar sa. Kullum cikin zuba ido yake har yanzu da akalla sun debe sati biyar na haduwar sa da Yarinyar da bai san ta bai san yar ina bace.+

Duk wanda ke tare da shi tabbas yasan ya canja duk da shi ba mutum bane mai sakin fuska ko jiki ga mutane amman daga kallon yanayin sa zaka gane akwai abinda ke damun sa.

Matarsa kuwa Hajara ita sam bata gane ba dan ita ma yanxu ta fita harkar sa in ya zo gare ta gaisuwa ce kawai sai in tana bukatar abu daga nan daman ba hira suke ba shikenan zai mike ya bar ta.

Akan halin nan nasa har malamai tabi amma sai asarar kudi da tayi dan sam ba wani abu da take ganin canjin sa.

Haka ta hakura ta zubawa sarautar Allah ido tinda dai in kudi ne tana samu, kuma bayan nan mijin ta bai da wani ruwan ido akan mata dan tasan indai ta Aliyu ne bazai taba kara aure ba. Wannan yasa ta kara sakarkar ce wa ta fidda shi a ranta.

Duk lokacin da sha’awa tazo tana kara sata a hanya mara kyau haka Momy ma. Wanda ita a ganin ta take ganin kamar so ne.

Maihaifinta kuwa sai abinda yace yana bukata duk wani kwangila da zata bayar ta hannun sa suke fita.

Dan sai yazo gidan yai kwanaki ma haka nan duk yan uwan ta bata kulawa saboda ita ta zama matar gwamna kumamai kudi wanda si take musu habaici bama da ba uwa daya suke ba. Ba abinda take musu duk da tana da hali dan sai yar banzar rowa a cikin ta.

Su Maryama kuwa basu taba cewa ma zasu zo ba bare ta wulakanta su dan su ma abin duniya baya gaban su.

***********

Aliyu ne zaune a office din sa wanda haduwar sa da girman sa kadai abin kalla ne.

Katon gaske ne, wanda daga wajen da yake zama yana rubuce rubuce wato bancin sa da kujeru.

Daga can kuma an masa kamar falo dan an zuba masa duk abin bukata a wajen.

Shi kansa bencin sa abin kalla ne banda kujerun da ke ciki da labulayen da sanyi da kmashin da ke tashi a ciki.

Ido sa a lumshe ya lula tinanin yarinyar da ya zame masa jiki kullum dare rana da safiya duk yadda yaso ya cire ta ya kasa.

Ido ya bude ya kalli kan bencin dake gaban sa. Invitation letters ne kala kala a gaba sa.

Daya ya dauka yaga daurin aure ne, haka ma dayar sai dayar kuma ta gayyatar sa taron saukar alkur’ani da za ai ne.

STORY CONTINUES BELOW

Murmushi ya saka a ransa ya ce,

“Wanne zani?”

dan duk rana daya ne.

Can ya ce,

“Saukar Alkur’ani zani.”

Dan haka ya dau wayar sa ya shiga calendar yai ticking akan date din ya sa remender dan ya tina masa.

Mikewa yayi ya ga agogo ya nuna masa karfe hudu da hamsin da biyar. Wayar sa ya dauka da key din mota ya nufi fita.

Yana fita masu tsaron suka yo kansa. Hannu ya daga musu kawai ya nufi motar sa.

Haka ya shiga ya tada ta yayi gida cike da tunane tunane da sake sake.

Yana zuwa gida yai horn mai gadi ya bude masa, yana packing ya fito yayo gun Mai gadi.

Mai gadi na ganin sa ya mike ya ce,

“Sannu da zuwa Yallabai!”

Hannu ya daga masa kawai sai kuma yai shiru ya kasa magana. Can ya ce,

“Wannan yarinyar wai bata zo bane?”

Wani kallo Mai gadi ya bishi da shi. Fuska Aliyu ya hade ya koma asalain Major AK din sa.

Kai Mai gadi yai kasa da shi ya ce,

“Ranka ya dade ban gane wa kake nufi ba!”

“Yarinyar da nace ka bar ta ta shigo!”

“Oh wallahi Ranka ya dade bata kara zuwa ba!”

“Ok jeka!”

Ya fada. Har Mai gadi ya fara tafiya, sai kuma Aliyu ya ce,

“Kaga!”

Juyowa yayi da sauri ya karaso gun sa. Aliyu ya dan gyara tsayuwa ya ce,

“Kasan sunan ta?”

“A’ah ranka ya dade!”

“Gidan su fa?”

“Shima haka ranka ya dade!”

Kai ya dafe.

Mai gadi ya ce,

“Yallabai in neman ta kake ai sai a bada cigiya”

Kai ya girgiza ya fara tafiya sannan ya ce,

“No!”

Ya shige cikin gidan sa. Wanka yayi ya koma falo ya zauna tare da lumshe ido. Duk yadda yake son kadai ci yau abin bai bashi nishadi kamar yadda yake ji da. Yau yarinyar nan kadai yake da burin tazo tai masa magana da sautin ta mai dadi ta sashi nishadi ya kalli idanun ta masu kyau. Da nuna rashin tsoro da bada umar nin ta.

Murmushi ya saki ya ce,

“Wannan yarinyar duk yadda akai tana da jinin sarauta!”

Sai ya kuma dariya lokacin data kure shi da idanun ta wanda har tsoro suka kusan bashi dan zai ce bai taba kallon idon wata ya mace ba in ba ita ba,

Haka ya zauna tunanin Yarinyar nan har ya shagalta sai jin kiran sallah kawai yayi. Mikewa yayi da sauri yai alwala ya nufi massalaci.

Acan ya zauna yana lazumi har akai sallah isha’i sai tara saura ya dawo.

Yana shiga falon sa yajiyo sautin wayar sa. Jiki a sanyaye ya karasa ya dauka. Mai martaba ne wannan yasa yai sauri amsa kiran

“Barka da Dare Abbah!”

“Yauwah barka kade Aliyu! Ya kake ya iyalai da aikin?”

Ido Ya lunshe sannan ya amsa da.

“Lafiya Alhamdulilah!”

Mamah ce ta amshi wayar ta ce,

“Babana kana lafiya dai ko?”

“Mamah ina lafiya ina lil sis nah?”

“Tana can bangaren su. Ya iyali?”

“Alhamdulilah!”

“Amman son lafiyar ka kalou kuwa?”

Yar dariya yayi ya ce,

“Me kika ji?”

“Your voice man!”

Shiru yayi.

“Ka fada min meke damun ka?”

“Ayyah Mamah ba komai na dai gaji ne kawai.”

“Anya Baba nah!”

“Eh!”

“To shikenan kaje ka kwanta Allah bamu alheri.”

“Ameen Mamah!”

Ya kashe wayar.

STORY CONTINUES BELOW

*

Mamah ce ta kalli Abbah ta ce,

“Yaron nan akwai abinda ke damun sa!”

Gyara kwanciya yayi ya kwantar da kan ta akan kirjin sa sannan ya ce,

“Kinsan halin zurfin cikin sa ai. Abinda zaki masa shine addu’a kawai.”

“Haka ne! Allah ya yaye masa kome ke damun sa. Allah da an tambaye ni ba zan yadda akara masa nauyin gwanan nan ba!”

Murmushi Mai martaba yayi ya ce,

“Bazaki gane manufar hakan ba sai nan gaba.”

“To Allah taya shi riko “

“Ameen!

suka rumgume juna suna masu addu’ar bacci.

*

Aliyu suna gama waya yabi wayar da kallo. Tabbas ya yadda uwa uwa ce. In ba uwa ba shi ba canjawa yayi ba ko wani abu amman har ta gane akwai abinda ke damun sa.

Tabbas akwai abinda ke damun sa shine tunanin yarinyar nan.

“To wai me hakan ke nufi?”

Ya tambayi kan sa yana mikewa.

(Fans ku bashi amsa!)

*

Wanka yayi ya fada gado yana salatin annabi. Al kur’ani ya dauka ya fara karantawa har karfe goma sanna ya ajiye ya addu’a ya tofe jikin sa da ko ina ya kwanta bacci.

Karfe uku ya tashi yai wanka yai alwala sannan ya hau kan sallaya. Har aka kira sannan ya fice zuwa massalaci.

Sai karfe takwas ya dawo ya shige dakin training nan ma sai goma ya fito yai wanka ya shirya cikin kakin sa sannan ya dan sha tea da cake ya fita.

Tin a haraba suke zubewa suna gaida shi amman hannu kadai yake daga musu dan yau fuskar nan a murtuke ba wanda yasan me akai masa.

Shi kansa bazai ce ga dalilin hade fuskar tasa ba dan ya riga da ya saba.

Haka ya isa gidan gwamnati yayi duk abinda zai yi. Masu masa hidima dai kaf kaf suke kar suyi wani abu da ba dai dai ba dan yau ogan ba sauki.

Hajara na bukatar kudi amman da ya shiga taje gun sa ganin fuskar sa yasa batai masa magana ba dan ita kanta tana shakkar sa in ya hade wannan fuskar ta sa.

Haka ta koma tana mita

“mutum kullum fuska a hade dan bakin hali. Iyalin ka ma baza ka sakar musu ha.”

(Ni kam nace kece baki niyya ba duk da halin irin wadan nan akwai wuyar shawo kansu.)

Ranar haka ya gama komai ko PA din sa daga baya baya ya dinga tsayawa dan kar yai wani abun.

Haka har yamma ya shirya ya tafi gida. Yana zuwa duk abinda yake na al adar sa ya gabatar sannan ya zauna a falo,

Shiru yayi can kuma sai ya saki fara’a wacce har sai da hakoran sa ssuka bayyana baki ya cije yayi kwafa kawai.

*

Aisha ce zaune a tsakar gidan su ta zuba tagumi hanya da zata samu taje gun Aliyu kawai take nema gashi babu.

Dan har yanzu Baba shi ke kai ta ko ina har makaranta kuma kan a tashi yaje dauko ta.

Ba komai yasa ba sai dan da tayi tafiya mai yawa sai ta fara haki. Wannan yasa yake kai ta da dauko ta.

Addu’a take Allah ya bata lafiya ko Baba ya huta ita ma kuma ta samu damar zuwa dan ganin gwamna.

Cikin haka har satin sauka ya shigo murna gun Aisha kamar me sai dai ba Yaa Muhammad. Duk abinda ya kamata Baba yayi mata ya mata. Duk da kayan sawar ta ne kawai sai kayan da za a ci na walinar da kuma da safe na ranar sauka.

Ranar Asabar aka saka saukar da misalin karfe goma na safe. Ummah taiwa Aisha kitso tai mata lalle tai kyau abin ta.

Ranar sauka tin safe gidan ya cika da yan uwa da abokan arzuki sai hada hada ake sai kace biki

Karfe takwas Aisha tai wanka. Kan karfe tara har ta shirya cikin dinkin ta na riga da zani wanda yai mata kyau

Bata jima da shiryawa ba kawayen ta suka biyo mata. Hijab ta saka ta fito suka tafi.

Ranar ne ta fara fita a kafa tin da ta tashi daga ciwon ta. Suna tafe suna dan taba hira har suka karasa makaranta.

A wani aji suka zauna har wajen ya fara cika. Sannan suma kowa ya hallarta.

Cikin tafiya a layi suka jera har wajen da aka tanadar wa yan sauka.  Nan suka. Zauna sannan aka fara gabatar da abubuwan taro.

Da karatun alkur’ani aka bude wajen inda Aisha ce ta fara karatun cikin muryar ta mai zaki da dadin sauraro duk wanda ke wajen dadin muryar ta ya sa ya saurara yana mai jin dadin kira’ar ta.

*

Yau yana dawowa daga massalaci wayar sa ta dau kara har ya wuce sai kuma ya dawo ya dauka. Allon wayar ya tsaya kalla.

Murmushi yayi ya shige ddkin training din sa. Karfe tara ya fito yai wanka ya shirya cikin farar shadda wacce ta masa kyau ya bade jikin sa da turaruka masu dadin kamshi.

Tea kadai ya sha ya fita ya rasa dalilin sa na zumidin son zuwa gun saukar nan. Yana halakan ta haka da dan wajen ambaton Allah zashi.

A haka ya karasa gidan Gwamnati. PAn sa ya fadawa akwai fita nan da nan aka fito da mota aka tsaya jiran fitowar sa. Karfe goma dai dai har ya fito.

Katin ya mika musu dan suga inda zasu sannan ya shige cikin mota aka rufe suka dau hanya.

Aisha na tsaka da karatun al kur’ani motar su Aliyu ta karaso. Parking aka yi aka sanar da zuwan mai girma gwanna.

Wanda shi Yana cikin mota tinda yaji sautin muryar ta yaji kirjin sa ya buga. A ransa yana fadin Allah yasa ita ce.

Wata zuciyar ta ce,

“In ita ce kai mata me a cikin wannan jama’ar?”

Ajiyar zuciya ya sauke dai dai lokacin da ta kai aya ta mika loudspeaker.

Amsa akai sannan akai mata godiya da addu’a. Sai da aka sanar da malamin zuwan gwamna.

“Muna yiwa mai girma gwamna barka da zuwa.!”

Haka malamin ya fada nan kuma aka tafi shigo dashi. Dan ai masa iso.

Sojoji da sai da suka kewaye wajen suka duba gun da zai zauna wasu suka take masa gaba wasu baya a haka ya fito. Cikin tafiyar sa ta kasaita ya shigo wajen ana ta kare shi har ya zauna a inda aka tanadar masa. Wajen da ya kayatu iya kayatuwa.

Sai bayan ya zauna sannan aka cigaba da gudanar da abinda ake.

A cikin Maza wani ya mike yayi karatun sannan aka bada tarihin makaranta da gwagwarmaya da ake fama.

Bayan an gama aka mikawa sarkin garin Allon yan sauka dan ya bawa maza. Bayan ya gama aka mikawa Gwamna dan ya bawa Mata.

Tin da aka kira Aisha Isah kirjin sa ya buga haka tazo ya mika mata ba tare da ya kalli ko wacce ba.

Bayan an gama aka kira dalibar da tafi kowa kokari aka bata kyauta ba kowa bace face Aisha Isah.

Haka a dalibar da tafi kowa zuwa da wuri ma ita ce. Aliyu jin sunan Aisha yana ta yawo akan sa ya dago kai sai kuma akai rashin sa’a bayan tabya gani domin ta koma ta zauna ne.

Suna zaune ana ta gudanar da abubuwa nan aka kira Aisha dan ta kara karatun alku’ani mai girma.

Tin da ta fara Aliyu ya lumshe idon sa yana jiyo muryar har tsakar kan sa da tafin kafar sa. A zuciyar sa kuwa fassara surar da take karantawa yake jikin sa ya kara sanyi da jin tsoron Allah.

“Anya ita ce?”

Zuciyar sa ta fada masa.

Sai da ta kai aya zata koma sannan ya bude idon sa. Fes akan ta.

Ido ya zaro kirjin sa na dukan uku uku.

“Ita ce kuwa?”

Ya fada dan ta canja tayi kyau ta kara tsayi ba laifi binta da kallo yai har ta koma gun zaman sa. Tin daga lokacin bai kara sanin me ake fada agun ba saboda gaba daya hankalin sa ya koma ga Aisha.

Kyautar da ya tanada sai PA sa ne ya gabatar kudi ne sai atampopi da shadodi har da fili da ya bayar dan a kara girman makarantar.

Ana cikin raba musu Aisha ta dago kai wa zata gani. Tabbas wannan shine wanda ya ce zai hada ta da gwamna.

Murmushi ta sakar masa wanda shima bai san lokacin da ya mayar Mata ba.

Yana can kallon Aisha sai ji yai PA sa ya ce,

“Yallabai zamu iya tafiya?”+

Kamar ya ce,

“A’ah!”

Sai kuma ya gyada masa kai, haka ya mike, suka rufa masa baya. A ransa kuma bai so tafiya ba. Dan zuciyar sa da tai masa arba da Aisha tini ya ji wani farin ciki annushuwa sun cika masa zuciya.

Haka har suka shige mota yana hango ta kafin daga bisani motar ta tashi.

Aisha bata lura da tafiyar sa ba sai waiwayo wa da tai taga babu shi, ido ta murza taga ba shi a ranta ta ce,

“Ko gizo yake min?”

Haka dai har aka tashi tana tunane tunanen, ta har suka koma gida nan ma, biki walimar ake tayi.

An basu hutun sati biyu dan su koma su cigaba da daukar wasu littafan a makaranta tare da taimakawa makaranta wajen koyar da wasu ajijiwan.

Bayan sauka kuma ta cigaba da zuwa makaranta da kan ta.

AK na komawa gida yaji son ganin yarinyar na kara tunzura shi. Haka ya kwana juyi washe gari ma. Duk ya rasa tunanin sa.

Karfe biyu saura ta dawo gida abinci taci tai wanka tai sallah sannan ta kwanta dan ta huta.

Ba ita ta tashi ba sai gab da sallah la’asar sallah tayi sannan ta fito ta kara share compound din su.

Har ta mike zata fita sai ta jiyo muryar Yaa Muhammad da sauri ta kara sa jikin sa tana fadin.

“Oyoyo Yaya nah!”

Ta amshi jakar sa ta kai daki sannan ta dawo ta kai masa ruwa duk Ummah na ganin su.

Haka suka zauna suna ta hira ta yaushe rabo sai kallon Aisha yake dan ta kara girma dan wata ukun da yaje yayo.

Wannan zuwan ma bata da matsalar komai dan Yayan ta kan mata duk abinda take so. Wanki shara har wanke wanke yakan mata in Ummah ta bata ta yi.

Ya zama daga makaranta sai zaman gida ko ta ci abinci kawai. Aikin makaranta kuwa ta samu mai daura ta akan hanya.

Haka suka kare sati biyu sannan Yaa Muhammad ya fara shirin komawa wanda yace in ya tafi zai dade bai dawo ba.

STORY CONTINUES BELOW

Har da kukan Aisha da zai tafi duk ta daga masa hankali a haka sukai sallama. Ranar da ya tafi ranar ta koma makarantar isilamiyya..

Tana fita da niyyar tafiya sai ta tino da abinda ta. Sa a gaba tin kan ta kwanta ciwo.

Murmushi tayi dan tasan yau zata je taji bayani daga wajen dan uwan gwamna kamar yadda AK ya fada mata.

Bayan an tashi daga makaranta sai ta Zarce gidan nasa. tana zuwa mai gadi ya ganta ya ce,

“Kece?”

Ta ce,

“Eh nice, please yana nan?”

“Bai dawo ba amman ki zauna yanzu zaki ganshi.”

Ta shiga ta zauna a gefen bencin sa suna ta hira har da dariya.

Mai gadi ya ce,

“Wai yan mata ya sunan ki ne?”

Dariya tayi ta ce,

“Sunana Aisha Humairah”

“Masha Allah!”

Ya mike ya fara alwala, yana cikin wanke hannun sa ya jiyo horn da sauri ya mike inda Aisha ta bishi da kallo yana alwala ya tashi daga jin horn ta jinjina kai.

Major AK na shigowa yayi gun parking  ya ajiye motar ya jima kafin ya fito daga motar.

Kamar ance ya kalli gate ya hange ta tana wa Mai gadi magana. Da sauri ya bude murfin motar ya fito har yana tuntube. Bai damu ba ya cigaba da tafiya Karasawa wajen yayi yaji tana cewa,

“Haba Baba kana alwala dan an yi horn sai ka katse haka akeyi.”

Zai yi magana taga karasowar Major AK. Kallon sa tayi ta ce,

“Ga shi nan kai masa magana yana alwala daga yaji karar motar ka ya tashi, na tabbata da sallah yake ma haka zai katse ta dan haka ka hana shi watakila wannan gwamna shi ya sabar masa da haka ko?”

Shi dai Major AK kallon ta kawai yake. Ta ce,

“Wai ba da kai nake magana ba ka zuba min ido kana kallo na.”

Mai gadi dai jikin sa har rawa yake. Major AK ya ce,

“Ka kiyaye ka daina kaji.”

Kai ya gyada ya ce,

“Yau kuma ke ce kika zo?”

Ya fara yin ciki. Bayan sata bi ta ce,

“Eh sai yau Allah ya kawo ni. A gaskiya ina son ganin gwamna a yau din nan.”

Dariya Major AK yayi ya ce,

“Akan me?”

“Ina da abubuwa da yawa dazan fada mishi. Dan naga shi bai da mai fada masa yaji ko mai bashi shawara ne bai da shi. Nasan dai yana da aure kuma yana da iyaye bayan nan yana da mataimaka amman ace duk cikin su basa bashi shawara ta gari dan yana shugaba sai abinda yayi shine dai dai fai!”

Kallon ta ya tsaya yi yadda take magana ba tsoro sai yaji wani sanyi yau yaga sanyin idaniyar sa.

“Na fada miki ganin gwamna ba sauki bane!”

“To ya za ayi kenan!”

“Yadda kika ce!”

Shiru tayi. Can idea ta fado masa ya ce,

“In kina son sakon da kike so ki bashi ya isa gare shi ki bani na bashi.”

Wani kalli tai masa ta ce,

“A’ah ina son ni da shi ne. Dan yasan mahinmancin abun!”

“Shikenan yanzu ya makaranta?”

Wani murmushi ta saki wanda yasa Major AK tsayawa kallon ta. Tare da manta a ina yake.

Ta ce,

“Makaranta Alhamdulilah! A duniya ban da abunda nafi so a tambaye irin karatu na.”

A rans ya c,e

“Ai naga alama!!

A fili kuma ya ce,

“Ai ilimi shine hasken rayuwa.”

“Kai ma kana son ilimin?”

“Sosai ma!”

“Yau Yayanah ya koma makaranta yanzu ban da mai koyan karatu ko ina kawo maka kana koya min.”

Murmushi yayi ya ce,

“Ko dai ni nazo ina koya miki?”

“Dan Allah da gaske zaka zo?”

“In dai kina so zan zo!”

“Wallahi Allah ina so!”

“To shikenan zan na zuwa. Amman a gida fa?”

STORY CONTINUES BELOW

“Kar ka damu Baba yasan indai a kan karatu ne to kowa ma zan kula!”

Yai murmushi ya ce,

“Me kike so ki zama nne?”

Kallon sa tayi ta ce,

“Buri na na da yawa in nace zan fada maka sai mu kwana ga yamma tayi ni zan tafi sai gobe! Yaushe zaka na zuwa kana koya min karatun?”

“Duk lokacin da kike so!”

“Allah ni ko yanzu ne bismillah!”

Dariya yayi ya ce,

“Muje naga gidan ku!”

A haka suke tafiya sai surutu take masa. Shi dai ba abinda yake sai murmushi. Ko ya buta da kallo a haka har suka karasa ya tsaya daga kofar gida sannan sukai sallama kan gobe zai zo.

Godiya tai masa sannan. Ta shige gida. Haka ya koma cike da nutsuwa da nishadi.

Wanka kawai yai akayi alwala ya fito sallah har akai isha’i sannan. Ya koma gida. Yau sai gashi ya kira Abbah da Mamah sun dan taba hira ya sake kadan.

Haka ya kwana murna da fatin ciki wanda ya rasa na menene.

**************************************************************************************

Fateema ce zaune ita da Fu’ad da yazo suna hira abin su gwanin sha’awa domin kuwa kowa yaga Fateema da Fu’ad yasan sun dace da juna.

Ido ya kure ta dashi dagowa tayi tace

“Wai kai meyasa baka gajiya da kallo nane!”

Ajiyar zuciya ya sauke yace

“Fateema Allah shi ya dauran son ki wanda ban san tayaya zan iya cire shi ba komai naki kyau yake min da burgeni. Ina son ki har cikin zuciya a domin kece farin ciki na burin rai na kwanciyyar hankali na. In har na rasa ki zan rasa rayuwa ta da jin dadi na. Ina son ki Fateema har ban san adadin da yasa nake son ki.”

Kallon sa nayi domin Fu’ad karshe ne wajen iya kalamai da mantar dani a ina nake. In ina tare dashi ina samun farin ciki sosai fiye da tunanin me karatu. Kuma na yadda da son da yake min tabbas babu algus a ciki.

Agogon hannun sa ya kalla yaga karfe goma saura. Wannan yasa ya mike yana aikon da murmushi, kyan sa ya kara fitowa kasa nayi da kai na. Yace

“Tashi mu tafi mana!”

Kasa tashi nayi, yace

“Ko na kwana ne?”

Kai na gyada mishi murmushi yayi yace

“Soon zamu kasance a karkashin inuwa daya.”

Murmushi na saki na mike nabi bayan sa. A jikin motar sa ya tsaya yana kallo na. Kasa nayi da kaina Yace

“Zan tafi I miss u!”

Murmushi kawai nayi yace

“Sai yaushe?”

“Ko yaushe ma.”

Na fada.

“Shikenan kila Friday na shigo.”

“Allah kaimu!”

Ya shiga mota naja baya ina tsaye yazo ya fice yana daga min hannu. Cikin gida nayi kan na karasa falo wayata ta hau kara. Dubawa nayi jaga Yaa Fauwaz ne.

Murmushi kan fuskata ne yaya fadadada na dauka ina fadin

“Yaya nah!”

“Na’am my beauty ya gidan?”

“Lafiya!”

“Wallahi I miss u so much!”

Kan kujera na fada ina fadin

“Miss u more!”

Murmushi yayi yace

“Na kusan zuwa ki zama cikin shiri!”

“U re always welcome.”

“Am eager to come and see ur beautiful face Baby. Wallahi am feeling kamar nai tsuntsuwa nazo na ganki. I really really miss u Baby me.”

Murmushi nayi dan nima ji nake kamar nai tsuntsuwa naje na ganshi.

“Bakya kewa ta ko Baby?”

“Haba Yaa Fauwaz! Kar kace haka man. Kai ma kasan nayi kewar ka.”

Nafada a shagwabe.

“Da gaske?”

“Kana so nazo nai kuka ne?”

Nan na fara kuka kamar ance nayi dan wallahi ji nayi kamar nayi dan yadda nake son na ganshi. Kewar sa duk ta dame ni.

“Haba Baby please kiyi hakuri please am sorry ina nan zuwa gareki with all my love and care in nazo sai kin gaji dani.”

“Ba wata gajiya da zanyi da kai. Yaa Fauwaz zan so na kare rayuwa ta da kai. Ina son ka ina sonka.”

“I know My sis. Tnc for ur love I love u more!”

Ya mata kiss yace

“Kinga dare yayi kije ki kwanta mayi magana gobe kinji.”

Ina kashewa naga missed call din Fu’ad har da text din sa. Wanka na fara yi sannan na shirya cikin kayan baccin na na haye gado. Waya ta na janyo nai masa reply sannan nai addu’a na kwanta bacci.

*

Kamar yadda ya fada min Friday da yamma sai gashi yazo, nayi kwalliyar ta kamar yadda na saba dan duk Friday mun dauke ta kamar sallah dan muna yin komai special kamar su girki da kwalliyya.

Ina zaune ina ta trying Number Yaa Fauwaz dan yau tin safe na ke neman sa ban samu ba kiran Fu’ad ya shigo akan cewa ya karaso.

Mikewa nayi na shiga bedroom dina orange kalar shadda ce a jiki na an min aiki da brown kala dan haka na dauko wani medium brown mayafi na da flat shoe shima brown sai waya ta a hannu na fadawa Momy Fu’ad yaxo na nufi can inda muke zama.

Ina shiga ya mike sanye yake da milk din shada an mata aiki da brown din zare ya saka hula da brown din takalmi da agogo sai tashin kamshi yake. Tinda na shiga yake sakar min murmushin sa mai kyau. Nima murmushin na sakar masa duk da bai kai zuci ba dan duktunani na yana ga Yaa Fauwaz.

Zama nayi sannan shima ya zaune yana bina da kallo ‘kin yadda nayi mu hada ido dan nasan Halin F-u’ad yanzu zai gane a halin da nake ai kam illai sai jin tambayar sa nayi

“Me yake damun ki Fateema?”

Murmushi na kara saki nace

“No ba komai!

Dan murmushi ya saki yace

“Kinsan in zaki boyen damuwar ki dole na gane ko? please ki dauken yadda na dauke ki wallahi Fateema nafi son ki akan kai na. Wallahi ba da wasa ba nafi jin ki da son ki akan kai na. Ina miki son da ban san adadin sa ba. Kallon ki kadai nayi ina gane halin da kike ciki, dan haka please ki daina boyen damuwar ki zan yi kome menene dan ganin farincikin ki. Ki yadda dani I mean it wallahi har cikin zuciya ta.”

So da tausayin Fu’ad ne ya cikan zuciya ta hakikanin gaskiya Fu’ad ya iya soyayya in kana tare dashi zai cire maka duk damuwar ka sannan zai nuna maka babu kamar kai. Ido na lumshe na bude ina sakar masa murmushi na nace

“Na yadda da kai Fu’ad. Ka yadda nima ba wani abu bane ya wuce!”

Murmushi yayi yace

“Gud ya Friday din? Kinga yadda kikai kyau kuwa sai kace ranar abin!”

Dan hararar sa nayi nace

“Kaji ka da tsokana ko? Ni ba wani kyau da nayi kai ne kayi kyau kamar ango!”

Murmushi yayi yace

“Soon insha Allah! Waya gannin na zama angon Fateema!”

Murmushi nayi nai kasa da kai na. A haka muka dinga hirar mu har na cire duk abinda ke damu na a rai na.

Karfe shida saura aka kira Fu’ad akan zai ba da sako abinda yasa ya mike zai tafi ba dan lokacin tafiyar tasa tayi ba.

Mikewa nayi muka fito compound din gidan mu a jere da juna duk wanda ya ganmu yasan mun dace da Fu’ad jikin motar sa na tsaya yace

“Beauty zanyi missing naki kisan Allah tin kan mu rabu nake fara jin kewar ki.”

Dariya nayi ina girgiza kai na yace

“Shiyasa na matso ayi abin ya kasance ko da yaushe muna tre!”

Fuska na rufe da tafin hannu na ina mai sakin murmushi. dai dai lokacin da wata mota ta shigo gidan mu. Da kallo muka bi motar. Take naji kirjina ya buga duk da ban san wake cikin motar ba.

Fu’ad ne yace

“Bari na tafi sai munyi waya!”

Dai dai lokacin da Yaa Kamal ya fito daga gefen mai tukin mota gun mu yayo suka gaisa da Fu’ad da shima ya bude mota zai shiga.

Dai dai lokacon aka fara kokarin bude motar Yaa Kamal daya shigo da ita cikin gidan. Ana budewa ya zuro kafar sa wanda take cikin wani black sandal tayi kyau ta kara haske. Yasun nan nasa zarara zarara acikin takalmin nasa.

Gaba na naji ya fadi wanda har sai da na dafe kirji na dagowa nayi ina son ya fito naga ko wanene?

Dai dai lokacon aka fara kokarin bude motar Yaa Kamal daya shigo da ita cikin gidan. Ana budewa ya zuro kafar sa wanda take cikin wani black sandal tayi kyau ta kara haske. Yasun nan nasa zarara zarara acikin takalmin nasa.+
Gaba na naji ya fadi wanda har sai da na dafe kirji na dagowa nayi ina son ya fito naga ko wanene?
Kafar sa ya kara sa zurowa sannan ya fito daga cikin motar gaba dayan sa. Sanye yake da bakin wando da orange kalar riga mai dogon hannu. Idon sa sanye da farin glass, sai tashin kamshi yake ya kara haske da kyau dashi.
Dagowa nayi ina kallon sa bugin kirji na,  na dada yawa saboda tsoro da fargaba ya kamani red handed da Fu’ad. Kallo daya nai masa na dauke kai na idon sa yayi jajir haka nan fuskar sa ta yi ja.
Da yake yana ta gefen Fu’ad da ya bude mota zai shiga wannan yasa ya miko masa hannu amman sai yai gaba abin sa ko kallon mu bai ba. Yaa Kamal da tini yai ciki daman. Ajiyar zuciya na sauke na kalli Fu’ad ina sakin murmushin da bai kai ciki ba nace
“Nagode bye!”
Nayi cikin gida da sauri zuciya ta na zafi da bugawa. A falo na samu Momy da Yaa Fauwaz da Yaa Kamal suna gaisawa. Ban kula su ba nayi cikin daki na dan ban san me ma zance musu ba. In shiga na fada saman kujera ina sakin numfashi kirji na na bugawa da sauri da sauri haka nan zuciya ta na zafi da radadi. Duk da na rasa abinyi ban an kara ba naji hawaye na zubo min. Kifa kai nayi akan kujera ina kuka. Na jima ina hawaye har akai idar da sallah magariba da kyar na mike nayi cikin bedroom din na bathroom na shige nayi alwala na fito na hau kan sallaya. Na jima ina addu’a.
Ina zaune akan sallaya har akai sallah isha’i na mike nayi. Wayata naji tana kara janyowa nayi naga Fu’ad ne. Wasu sabbin hawaye ne suka zubo min hannu na saka na goge. Sannan dauka. Cikin sanyin murya nayi sallama.
Amsawa yayi yana tambaya ta lafiya. Shiru nayi yace
“Fada min me yake damun ki muryar ki ba dai dai take ba.”
“Uhmm ba komai Fu’ad ka koma gida lafiya?”
“Lafiya,  But ni ki fadan what’s wrong with u please!”
“Ba komai fa nace!”
“Baza ki fada min ba ko?”
Shiru nayi yace
“Shikenan amman dan Allah ki cire damuwar kinji. Wallahi in har kina cikin damuwa ina fin ki shiga damuwa.”
“Nagode da kulawar ka sai anjima”
Na kashe wayar na jingina kai na da jinin gado ina mai lumshe ido.
Ba komai yake yawo a raina ba sai irin son da Fu’ad ke min. Wannan yasa na fara tino asalin soyayyar mu.
STORY CONTINUES BELOW
*
Kamar yadda na fada muku tin ina shekara tara zuwa goma nake tare da Fu’ad. Asalin soyayyar tamu.
Lokacin da muka dawo unguwar mune, aka kai ni Makarantar su Sani. (Kamar yadda fada Sani dan Yar Momy nane kani be ga Yaa Kamal). A lokacin sun bani aji biyu tazara amman a ko da yaushe in an tashe mu zan tsaya a tashe su sannan ya rako ni gida.
Ni da Sani mun shaku matuka dan kusan sa’ani ne. Yaye na Maman shi ita ta yaye ni dan haka kusan tare muka taso sai daga baya na dawo gida shi yasa na shaku da yan gidan fiye da sauran yan uwa na.
Watarana ina tsaye ina jiran a taso su Sani wanda daman ana riga tashin mu da mintuna sannan a tashe su. Ina tsaye aka fara fitowa yan ajin su.
Shi ya fara fitowa wanda ina daga ido muka hada ido. Murmushi ya sakar min nima na sakar masa, duk da ba sanin sa nayi ba. Waje na yayo yace
“Wa kike jira?”
“Sani nake jira!”
Zai magana kenan Sani ya fito daga ajin su. Kallon sa yayi yace
“Ah Fu’ad baka tafi ba.”
Kai ya gyada. Ya kalli sanin yace
“Eh kanwar kace?”
Kallo na yayi yace
“Eh!”
Hararar sa nayi nace
“Kaji ka kwana nawa ka bani?”
Da Fu’ad da Sani suka fashe da dariya, Fu’ad yace
“Kwana nawa ya baki?”
Baki na turo nace
“Momy tace Yana yaro dai aka haifen bai ban shekara ba fa!”
Dariya suka karayi yace
“Fateema uwar son girma!”
Fu’ad yace
“Sunan ta Fateema?”
Y fada yana kallo na.
“Eh!”
Sani ya bashi amsa yana amsar jaka ta yace
“Mu tafi ko?”
Ya kalli Fu’ad yace
“Mu zamu tafi!”
“Oh sai gobe!”
“Allah ya kaimu.”
Sai da mukai gaba nace
“Waye wanan ne?”
“Sabon zuwa ne. Tin da yazo ajin tamu tazo daya, a kusa dani ma yake zama yana da kokari sosai.”
Kai na jinjina haka muka karaso bakin gate tsayawa yayi na kalle shi nace
“Muje mana!”
“Tafiya zan!”
“Wallahi na taho maka da sweet daga ckul!”
“Ah haba muje!”
Nan mukai cikin gidan.
Sani bai samu damar tahowa ba har sai da aka kusan kiran magariba ya tafi gidan su. A hanya zai karasa gida ya hadu da Fu’ad har ya cire kayan makarantar sa.
Fu’ad na ganin sa yace
“Na ganka da uniform baka koma gida bane?”
“Walahi na raka Fateema gida ne!”
“Ok!”
Nan suka jera suna tafe suna hira har aka zo kofar gidan su Sani ya kalli Fu’ad yace
“To ni na karaso sai gobe!”
“Oh wai nan ne gidan ku daman?”
“Eh!”
“Ni gidan mu yana gaban layin ku. Nagode sai anjima!”
Sukai sallama suka tafi.
*
Washe gari Fu’ad shi ya biyawa Sani daga nan sukayo gidan mu. Lokacin ina compound dan haka ina ganin su muka tafi. Abun da na sani kawai ina matukar jin kunyar Fu’ad wanda ni ban san dalii ba.
Tin daga ranar kuma suka kulla aminta da Fu’ad da Sani ta inda har ta kai tare suke rakoni gida in zamu ckul ma tare muke dawowa dasu.
A haka har girma ya fara zuwan min wanda inada shekata goma sha biyu. Wanda har lokacin Sani da Fu’ad basu fasa rakoni da dauka ta mu tafi makaranta ba. Kuma har lokacin nima ban daina jin nauyin Fu’ad ba dan mun zama kamar surukai.
Shi Fu’ad tin da ya fara gani na yaji kawai yana so na duk da shima a lokacin ba wani sanin menene so yayi ba. Dan shima lokacin bai fi shekata goma sha hudu zuwa biyar ba dan haka ba zai iya dorar da meke going ba. Sai a yanzu da nake tunanin nan nagane hadin Allah ne. Domin nima tin lokacin naji Fu’ad na burge ni ga kyau tsabta da kokari.
STORY CONTINUES BELOW
Sai a hankali da muke kara girma Fu’ad ya gane kuma ya yadda wa kansa yana son Fateema. Wannan yasa yake kara saka ido akan ta da kaf kaf da ita. Yarinyar na burge shi nutsuwar ta da hankalin ta da kyan ta ga kokari gata shiru shiru.
A lokacn ta kai ta kawo har in ya kwanta bacci zai yi mafarkin Fateema wao sunyi aure har ma mun haihu. Ya yadda Allah shi ya daura masa so na dan daga kallo daya ya kamu dashi a lokacin da bai san menene so ba da dan me ake son mutum ba dan sai daga baya ya kara ganin dacen ya so nin dan ina da qualities din da na cancanci a so nin.
Me ke sa a so mace kyan ta nasaba dukiyar ta da ilimin ta. To lokacin da ya fara so na duk bai san da wadan nan ba sai da yai nisa a so na sannan yasan dasu kuma da ya duba ya hanga ya hango duk ina dasu wannan ya kara kwadaitawa Fu’ad soyayya ta. Amman soyayyar mu hadin Allah ce. Kamar yadda nima son nasa ya kamani tin daga yarinta a lokaci da ban san menene son ba.
Wani yaro ne dan ajin mu wai yace yana sona shine nake fadawa sani dan yai masa kashedi.
Ana haka wata rana muna hanyar mu ta dawowa daga ckul na kalli Sani nace
“Kai wa yaron nan magana kar ya kara cewa yana so na!”
Dariya Sani yayi yace
“Menene da Yaron to?”
Harara sa nayi ina turo baki har da hawaye. Fu’ad da ya karaso wajen yace
“Me ya faru ne? Wa ya taba min yar gida na?”
“Yar gidan ka ko daru gata nan dai!”
“Ai bata daru sai an tabo ta.”
Dariya Sani yayi yana fada masa abinda ke faruwa. Fu’ad naji Hankalin sa ya tashi yace
“Wane yaro ne?”
Nan Sani ya fada masa komai wanda karshen labarin yai dai dai da karasowar mu kofar gida dan haka nai musu sallama na shige gida.
A hanya ne Sani ya kalli Fu’ad yace
“Fu’ad Yanaga hankalin ka ya tashi ne?”
Kallon Sani yayi yace
“Sani ba zan boye maka ba a gaskiya ina son Fateema!”
Kallon sa Sani yayi yana dariya yace
“Wai da gaske kake?”
Kai ya gyada yace
“Da gaske nake ina son Fateema.”
“Ai shikenan zan fada mata. Allah tabbatar da alheri.”
“Amin!!”
Ya fada yana murmushi.
*
Washe gari bayan an tashi daga isilamiyya ne bayan sun rakani gida Sani yace yana son magana dani. Gefe Fu’ad yayi.
“Daman Fu’ad ne ya aiko ni.”
Sani ya fada.
Kallon inda Fu’ad din yake nayi ina murmushi nace.
“Me yace? Shi da ba zai fada min ba.”
“Fateema son ki Fu’ad yake!”
Kai na dago ina kallon Sani sai kuma na kalli Fu’ad da ya zubo mana idanu. A guje na kwasa nayi cikin gida. Daga Fu’ad har Sani sai da sukai dariya sannan Fu’ad ya matso yana tambayar Sani Lafiya.
Sani na dariya ya bashi labarin komai. Kai ya girgiza suka tafi suna mai da maganar.
Da gudu a shigo har falo Momy tace
“Lafiya?”
Haki nake saukewa na amsa mata da lafiya na shige daki na. akan gado na kwanta a gaskiya a lokacin ban san a wane hali ko yanayi nake ba amman naji a raina nima ina son Fu’ad kawai.
Ai washe gari kan su zo har na tafi makaranta ana tashi kuma nake gudowa daga Sani har Fu’ad sai suka daina gani na.
Tin daga lokacin na daina bin su da kai na nake tafiya makaranta na dawo da kai na. Letter Fu’ad ya rubuta ya bawa Sani ya kawon wannan yasa bayan an tashi na koma gida ina falo ina homework dina naga Sani ya shigo dan ko gida bai koma ba.
Kallon sa nayi na mike zan gudu yace
“Dallah tsaya kiji”
Tsayawa nayi yace
“Fu’ad ne ya aiko ni.”
Ya mikon letter amsa nayi nace
“Sai anjima to!”
STORY CONTINUES BELOW
Ya juya ya fice. Komawa nayi na zauna na gama homework. Sai da dare har na kwanta na tuna da letter na dauko na fara karantawa. Sakon soyayyar sa ne yace kuma in na yadda da soyayyar sa in rubuto masa da reply a daren na mike na rubuta reply na saka a jakar isilamiyya ta.
Lokacin ina Jss 3 wanda Fu’ad a shekarar ya fara zuwa university shi kuma.
A bangaren Fu’ad Allah Allah yake gari ya waye aje isilamiyya ya samu reply daga gareni wanda a ranar gani yayi kamar lokaci baya tafiya.
Lokacin da mukaje Isilamiyya har leke na yake ni kam sum sum nake shigewa aji dan kunyar sa nake ji kamar me kasa hakura yayi sai da aka fito sallah yasa Sani ya amsar masa sakon. Nan na bashi.
Ana tashi nayi gida. Fu’ad kuwa rasa inda zai saka wasikar nan yayi dan farin ciki duk da bai karanta yaji me na saka a ciki ba. Bai samu damar karantawa ba sai da dare bayan ya shiga dakin su.
Reply ne daga gareni da nake nuna masa na amshi soyayyar sa. Dadi kashe Fu’ad haka ya dinga ji.
Tindaga lokacin ya zamana kullum zai min wasika ni kuma washe gari na rubuto amsa na bawa Sani. Amman fa ban yadda mun hadu ba duk abinda muke ta wasika ne. Dan soyayya muke sosai duk da a lokacin ina da karancin shekaru.
Ban fara tsayawa da Fu’ad ba sai da na shiga SS 2 shima gida suka zo da Sani kuma ranar suka kama ni a Falo wannan yasa muka gaisa na mike zan tafi daki Sani yace
“Wajen ki yazo fa.”
Komawa nayi na zauna kai na a kasa. Amman dagani har shi aka rasa wanda zai magana dan shima kunyar tawa yake ji. Haka muka gama zaman namu ya tafi.
Tin daga lokacin ya zamana suna yawan zuwa gida tin ban sakewa ina kasa magana har na fara sakewa muna dan taba hira a haka kuma muka saba soyayya mai karfi ta shiga cikn zuciyoyin mu.
Wata hirar mu ce ta fado min wacce bamu dade da yin ta ba da nake cewa
“Me yasa kake sona Fu’ad?”
Kallo na yayi yai murmushi yace
“Fateema sonki daga Allah yake, Allah shi ya sakan sonki dan a lokacin da na fara ganin ki a lokacin son ki ya shige bayan a lokacin bansan ke wacece ba ke ba zance ga abinda ya rude ni ba domin baki da abinda zai ruden a lokacin son ki daga Allah ne sai daga baya na gane kin cancanci a so ki da nayi rayuwa dake na kuma fahimce ki. Dabi’un ki kyan ki nasabar ki hankali da nutsuwa su suka karan sonki amman ada na so ki ne babu dalili.”
Wallahi soyayyar Fu’ad gareni gaskiya ce dan zai iya sadaukar da farin cikin shi da rayuwar sa gareni. Na yadda na aminta na aure Fu’ad na gama dace da samun soyayyar gaskiya.
Tin daga kan Fu’ad ban kara son wani ba dan ko ance ana so na da na hada wanda yazo min da Fu’ad zan ga bai kai ba. Ba wai dan son Fu’ad ko kyan sa ba a’ah.
Fu’ad mutum ne mai hankali da j
Nutsuwa dan ko a gidan su ya fita ya zakka. Kowa yana yabon sa haka nan yan unguwar su. Yana da ilimi da addini ga tarbiyya hakuri duk ya hada.
Wallahi ina rantsuwa da Allah duk wanda ya samu Fu’ad ya gama dace a duniya lahira ma ina da tabbaci zai taimaka wa matar sa dan ta shige shi. Fu’ad ya gama yi a rayuwa.
Muna cikin rayuwar mu kwasam sai muka fara waya da Yaa Fauwaz wanda zuwan sa ya dagula min tarayyar mu da Fu’ad. Abinda na kawo shine meyasa na cewa Yaa Fauwaz ban da wanda nake so ban san dalili ba amman nasan saboda ina son kasancewa dashi ne.
Bama wannan ba da farko ji nayi ba zan so shi ba just muyi dating kowa ya kama gaban sa wanda banyi tunanin me Allah ya hukunta ba. Ai kam gashi nan Allah ya jarabce ni da son sa bayan son da nakewa Fu’ad da alkawarurukan da muka daukar wa junan mu na bazamu tana rabuwa shin ni yanzu ya zanyi *Wa nake so?*
Wallahi dukkan su ina son su inda za ace mace na auren maza biyu dukkan su zan aura. Amman yanzu dole na zabi *wanda nake so!* al halin a halin yanzu ban zan ce ga *wanda nake so* please ku tayani zabar da sanin *wa nake so?*
Ajiyar zuciya na sauke ina gyara kwanciyya rayuwa ta da Yaa Fauwaz ta fado min wato zuwan sa. Yadda muke taraiya da yadda muka shaku.
Na kasance mace mai kunya wacce magana ke min wuya amman in har ina tare sa Yaa Fauwaz zai kawar min da wannan matsalar ta.
Ina muna hira na kanji dama mu dauwama. Ina son Yaa Fauwaz ban sani ba ko dan jini nane. Ba zai nunawa Fu’ad komai ba sai dai Fu’ad ya nuna masa abubuwa da yawa abu daya nasan zai iya nunawa fu’ad shine irin tashi wayewar da bai tashi a kasar hausawa ba daga kasar turawa sai ta iya mure.
Dan Yaa Fauwaz a gaban Momy bai ki ya nuna min soyayyar sa ba mutum ne dan in yana son abu yana son sa. Dan bai taba son mace kamar yadda yake min ba. Ya gama sawa a ransa ni ce zabin sa kuma ni zai aura. Addu’ar sa a kulla Allah ya malaka mai ni.
Ranan da muna waya na tuna lokacin da mukai waya yace
“Teemah all my life yanzu dake nake tsara ta. Fatana da addu’a ta Allah ya mallaka min ke ina addu’a Allah yasa ke alheri ce a gareni ke ina addu’a ko ke ba alheri bace Allah ya juyar ya sa ki zama alheri a gare ni. Fateema ban san irin son da nake miki ba ina miki son da zuciya ta zata iya tarwatse wa dan tsanin son da nake miki. Ni kadai zuciya ta kan zafi dan son kasancewa dake. I love Fateema I love u wit all my heart I can’t do without u ki riken amana da alkawari koman daren dadewa ke tawace.”
Ido na lumshe tuna wannan hirar tamu. Nasan Yaa Fauwaz mutun ne mai tsananin kishi. Fu’ad yafishi amman shi Yaa Fauwaz kishin sa a bayyane yake.
Hawaye ne ya fara zubo min na rasa ina zan saka kai na da soyayyar wadan nan mutane biyun da na rasa wanda yafi sona a cikin su ko da yake Momy tace min na zabi *wanda nafi so* to ni *wa nake so?*
Kuka na fashe dashi saboda na rasa ina zan saka zuciya ta da rai na. Na jima ina abu daya wannan yasa na mike dan na dauro alwala tin da baccin yaki yazo sai da namike na kalli agogo naga karfe uku saura na dare.
Nayi mamakin lokacin da na kwashe ina zaune. Alwala na shiga na dauro nai ina kai kuka na ga Allah akan ya yafe min ya kawon dauki da sauki ya kuma zaba min abunda yafi alheri. Ranar banyi bacci ba har asuba sai da nai sallah asuba sannan bacci ya dauke ni akan sallaya.

*

Washe gari.

Momy da tasan zan fita tajini shiru ta leko taga ina bacci sai ta koma dan tasan kila na fasa fitar ne. Ban farka ba sai karfe goma na safe da wani ciwon kai da zazzabi na tashi wanda da kyar na shiga nai wanka ina fitowa na shige cikin bargo dan sanyin da nake ji.

Momy ganin shiru shiru har sha daya yasa ta shigo daki gano ni cikin bargo yasa tayo guna tana fadin

“Wai baccin me kike yi haka?”

Dagowa nayi ina kallonta da idanu na wanda sukai jajir saboda azabar ciwon kai. Ido ta zaro tace

“Me yake damun ki?”

Tana taba jiki tace

“Zazzabi bari na fadawa Dadyn ku ya jira muje asibiti.”

Nan Momy ta fita ni kuma na koma na kwanta bata jima da fita ba suka dawo tare da Dady da ya shirya dan ya fita. Waje na yayo yana fadin

“Sannu Fateema!”

Kai na gyada masa, Momy kuma tayi gun wardrobe dina ta daukon wata bakar doguwar riga da mayafinta. Guna tayo tazo ta daga ni fita Dady yai Momy ta sakan kayan sannan ta dauran mayafin ta kamoni muka fita. A falo na muka samu Dady dan haka ya kamani muka fice ya saka ni a mota sannan shima ya shiga Momy ma haka.

Muna zuwa aka wuce emergency dani yadda jiki na yai zafi da zazzabi Likitana gani yace a kara min ruwa nan aka bamu gado dan asaka min ruwan. Ana fara saka min ruwa bacci ya dauke ni.

Bani na farka ba sai karfe biyu da na tashi ba zazzabin sai ciwon kan. Momy na hanga zaune akan sallaya tana lazumi tana ganin na tashi ta mike tana fadin

“Sannu Fateema kin tashi?”

Kai na gyada mata tace

“Bari na fadawa doctor.”

Zata fita kenan sai ga Yaa Fauwaz da Yaa Kamal dan haka sai Yaa kamal ya tafi kiran sa Momy da Yaa Fauwaz suka shigo dakin. Ido na a lumahe amman ina jin kamshin turaren sa na bude ido ina kallon dakin. Yana zaune a gaban gadon da nake akan kujera ya kura min ido.

Shi kadai yasan me yake ji akan son Fateema domin jiya bai bacci ba ganina da yayi da Fu’ad. Yau ma da ciwon kai da kirji ya tashi dan yadda ya saka abun a ransa sosai.

“Sannu Teemah ya jikin?”

Ya fada cike da kulawa.

“Da sauki.”

Na fada muryata a sanyaye kamar zan yi kuka dan ganin Yaa Fauwaz kadai ya tada min da wani miki a zuciya ta.

Kirji na dafe dan yadda yake min zafi, dagowa yayi yacgannin dafe da kirji wannan yasa yace

“Samnu yana miki ciwo ne?”

Kai na girgiza kawai dan in nace zan magana nasa kuka zai zubo min. Momy ce ta fito daga toilet da wani dan bowl ta karaso ta dauko ruwan Sona ta dauko toothpaste da toothbrush din nan ta kawon na wanke baki na nace

“Momy zan yi sallah amman jiri nake ji.”

STORY CONTINUES BELOW

Dai dai lokacin da doctor ya shigo kenan. Kallo na yayi yace

“ya jikin?”

“Alhamdulillah!”

Na bashi amsa a sanyaye.

“Sannu!”

Kai na gyada. Kallon su Momy yayi yace

“Zaku iya bamu waje!”

Fita sukai suka barni daga Doctor sai ni. Kai na a kasa yace

“Yanzu me yake damun ki?”

Kai na ke ciwo sai jiri da nake ji.”

“Sannu bakya jin zazzabin?”

Kai na gyada. Bp na ya gwada sannan ya kallen yace

“Wacce damuwa kika saka a ranki da ta haifar miki da wannan ciwon?”

“Ni ba damuwar da na saka?”

Murmushi yayi yace

“Jinin ki ya hau fa!”

Dagowa nayi da sauri ina kalon sa. Kai ya gyada min. Kasa nayi da ido na ya ce

“Ya kamata koma menene ki kula dan at ur age bai kamta ace jinin ki ya hau haka ba.”

Kai na gyada sai na kalle shi nace

“Please kada ka fadawa su Momy nah!”

“Why?”

“Wallahi zasu shiga damuwa sosai!”

“In bakya son ganin damuwar su kema ki cire damuwar dake ran ki.”

“Insha Allah!”

“Zan rubuta magani sai ki kula da sha kuma ki kiyaye saka damuwa a ranki Allah baki lafiya.”

“Amin nagode!”

Ya mike ya fita nan su Mony suka shigo tare da Yaa Fauwaz kama ni tayi ta kaini bandaki nayo alwala sannan na fito ina bin bango a zaune nai sallah. Ina kan sallaya Dady ya shigo dan an kira ance na farka.

“Ya jikin?”

Ya tambaye ni cike da kulawa

Kai na a kasa na bashi amsa da

“Da sauki!”

“Allah kara sauki ina Kamal din?”

“Yaje siyo magani!

“Alright bari naje gun doctor na dawo!”

Tea Momy ta hada min ta mikon ina cikin sha Dady ya shigo tare da Yaa kamal ya kalli Momy yace

“Ku shirya dan an sallame mu.”

“Toh!”

Momy ta fada tana hada kayan dakin. Yaa Fauwaz na taya ta tana gamawa suka fitar da kayan ni kuma Dady ya kamani muka fice Momy na bin bayan mu.

*

Muna zuwa daki na aka wuce dani ruwan wanka Momy ta hada min sannan na shiga nayi ina fitowa na saka riga da siket yan kanti. Sallah La’asar na tayar dan naji an tayar a masallaci. Ina kan sallaya Momy ta shigo da plate din abinci da ruwa da lemo.

Ajiyewa tayi. Dai dai lokacin da yaa Fauwaz yai sallama ya shigo kenan.Fita Momy tayi. Matsowa yayi yana kallo na yace

“Samnu!”

Kai na gyada. Abincin yaja ya fara bani a hankali a hankali kadan naci nace na koshi. magani ya dauka yana dubawa. Sai da ya gama dubawa sannan ya ban nasha. Komawa nayi kan gado na kwanta ido na yana zubar da ruwan hawaye. Kallon na yayi yace

“Haba Teema stop crying man. Kinga condition din da kike ciki dai. Nayi magana da doctor ya fadan me yake damun ki. To menene na kukan zaki kara saka wani damuwar ko?”

Momy ce ta shigo tace

“Ai ka gaji indai Fateema ce in dai bata da lafiya tai ta kukan nan kenan!”

Kallon mu tayi tace

“Taci abincin ne?”

“Taci kadan!”

“Ok!”

Ta dauki plate din fice.

Hamnu na ya kamo yana kallo na yace

“Me kiike so?”

A rai na nace

“Kai!”

A fili kuma ta girgiiza kai nayi. yace

“To is alright sannu kinji.”

Yadda Yaa Fauwa ya dinga kula dani shi ya kara narkar min da zuviya.

Fu’ad kuwa yana can cikin tashin hankali dan tin jiya yake kira wayar a kashe duk ya shiga damuwa ya rasa sukuni.

*********************************************************************************************************************************

Washe gari kuwa Allah Allah yake ya dawo daga gidan gwamnati Dan yaje yaga Aisha ya rasa dalilin da yasa zuciyar sa ke azalzala shi akan Al amarin Aisha.

STORY CONTINUES BELOW

Duk kasa yin aikin yayi in Banda kwanciyya gashi Sai yaga time din Sam baya gudu a haka akai la’asar yai sallah. Ya Jima a masallaci Yana azkar da karatun alkur’ani dai biyar ya fito daga masallacin ko ciki bai shiga ba ya shige cikin motar sa ya bar gidan.

Yana komawa gida a gaggauce yai wanka ya canja Kaya sannan ya fito Dan tafiya gidan su Aisha. Lokacin karfe biyar da rabi. Tafiya yake cikin nutsuwa iskar garin na kada shi wani nishadi da annushuwa na shigar sa. Yana tafiya Yana kallon yanayin garin Mai ban sha’awa da ni’ima Daman damina ta fara sauka.

A haka cikin tafiyar sa kamar ba zai taka kasa ba ya karasa kofar gidan su. Sai da ya Isa Sai ya dinga mamakin tayaya yazo yazu ya zai Yi ya aika ta fito.

Aisha da ta dawo daga makaranta tin daga nesa ta hange shi wani Dadi da farin ciki taji da sauri ta take tafiya dan ta karasa wajen sa.

Yana tsaye a gun kusan minti biyar ya rasa yadda zai Yi yayi nisa a cikin tunanin sa. Yaji muryar ta dake saukar masa da nishadi tana Masa sallama.

Bai San lokacin da ya saki wata ajiyar zuciya ba ya juyo Yana kallon kyakyawar fuskar ta. Wacce Bata rabuwa da fara’a a Koda yaushe.

Kallon ta yake baya ko kiftawa wannan yasa ta tafa hannayen ta a fuskar ta tana fadin

“Kallon fa?”

Ta tambaya hade da dage kanta. Murmushi ya saki Yana kawar da maganar ta yace

“Yan makaranta an dawo me?”

“Eh! Allah yasa baka Dade da zuwa ba dai.”

“Ban Jima ba.”

“To Bari naje na canja Kaya na fadawa Ummah.”

Kai ya gyada tayi ciki da sauri. Da Ido ya bita Yana murmushi da bai san dashi ba.

Ummah ta sama a bakin murhu tana tuka tuwo ta durkusa tan fadin

“Sannu da gida Ummah”

“Yauwah Aisha kin dawo?”

“Eh!”

Ta mike ta shiga dakin ta canja Kaya ta dauko jakar makarantar bokon ta. Ummah tace

“Ina Kuma Zaki?”

“Ummah Wanda zai na koyan karatun ne yazo.”

“Oh to shikenan Allah bada sa’a.”

“Amin!”

Akan dandamalin kofar gidan ya zauna. Dan haka itama ta zaune daga dayan gefen. jakar ta ta bude ta dauko Masa English note and text book din ta. Amsa yayi yaga abinda akai mu.

Tambayoyi ya farai Mata akan last topics din su dukka ta amsa Masa wannan yasa ya gane tana da kokari Dan haka batare da ya bata lokacin ba ya fara koya Mata karatun Kuma sosai take ganewa tana cooperating wannan yasa yake Jin dadin koya matan.

Yadda yake speech din sa ta Kura Masa Ido Dan kamar bature haka yake pronouncing ko wacce word abin da ya Kara burge ta dashi kenan. Ganin ta tsaya tana kallon sa shi Kuma Yana tambayar ta tai shiru sai murmushi take wannan yasa yace

“Hey u kallon fa?”

Kai tai kasa dashi cikin Jin kunya tace

“Kawai ka burge ni yadda kake magana kamar wani bature.”

Murmushi yayi yace

“Kema in Kika Mai da hankali Zaki fi haka ma iyawa.”

“Aikam Zan Mai da hankali.”

“Gud!”

Haka suka cigaba da karatun tana ta bashi amsar da duk yake mata.

Har Basu an Kara ba Sai Kiran magariba suka ji. Wannan yasa ta Mike tayi ciki ta kawo Masa ruwan alwala Ya amsa yai alwalar ta dauki butar tana Mai fadin

“Nagode Allah saka da alheri. Sai gobe!”

Kai ya gyada Mata yai gaba Dan har an shiga masallaci. Ciki ta koma ta ajiye jakar ta, ta daura alwala sannan ta tada sallah dan Ummah ma sallar take.

Tana idar wa ta janyo jakar ta tana duba karatun da yai Mata. Tana Yi tana murmushi tare da kwaikwayon yadda yake koya Mata itama a lallai Sai tayi irin yadda yake karya harshen sa.

Tana zaune akai isha’i wannan yasa ta mike ta tada sallah tana idar wa Abbah ya dawo Dan haka sukai Masa sannu da zuwa suka ci abinci. Suna idarwa suka zaune karatu kamar yadda suke ako da yaushe.

Major AK kuwa anan masallacin unguwar yai sallah magariba yayi isha’i sannan ya koma gida. Yana tafe a hanya Yana tunanin ya akayi ba wuta a masallacin da yai sallah. Bayan kullum ana kawo Masa burget Akan kudaden da ake amsa na gyara masallace da siyan musu generator Kar har da solar ma Amman sam bai ga alama a masallacin da yai sallah ba shin me kenan?

Haka ya karasa gida. Mai gadin da kuwa tin da akai magariba bai gansa a masallaci ba ya shiga cikin damuwa dan yasan magariba batai wa uban gidan nasu a waje. Amman har akai isha’i bai dawo ba duk Sai ya kasa tsaye ya kasa zaune.

Yana bakin gate yana kallon hanya ya hango shi Yana tahowa ajiyar zuwa ya sauke. Yana Karasowa ya zube yana fadib

“Barka da dawo wa.”

Hannu kadai ya daga masa ya sa Kai yai cikin gidan. Yana shiga ya zarce dakiin sa ya cire Kaya ya wuce bandaki ya watsa ruwa. Bai saka komai ba daga shi sai boxer ya fito falo ya dauki fura. Dakin sa ya koma ya zauna akan sofar sake dakin ya fara Shan furar, sai da ya gama ya shiga ya wanke bakin sa sannan ya koma dakin.

Kan gado ya hau kwanta Yana Mai lumshe Ido. Aisha yake gani kawai ta tsura Masa Ido tana ta murmushi. Shima bai san lokacin da murmushi ya sauka Akan fuskar sa. Wanda in dai zai tunanin Aisha to tabbas zai tsinci kan sa a cikin fara’a da nishadi mara misltuwa.

Aisha na saka shi yaji ya manta da komai sai ita kawai. Baya zama waje bai tunanin ta ba shin me kenan?

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *