WA NAKE SO CHAPTER 5
Tin daga ranar kullum major AK na dawowa daga gidan gwamnati yake tafiya gidan su Aisha Wanda wani lokacin ma a hanya suke haduwa su karasa tare.+
Sosai suka shaku da juna, Dan kullum zai zo ya koya Mata karatu Wanda In har kana son Aisha ta so ka ko tana kula ka to kana kawo mata zancen makaranta.
Wata Ranar alhamis Mamah ta manta Bata bawa yayen Aisha su yo nika ba. Dan har sai da ta daura ruwan tuwon sannan taje Dan ta debo gari tayi talge amma Sai taga Babu wannan yasa ta bawa Aisha taje tayo nika.
Amsa tayi tana fita Major AK na karasowa. Murmushi yayi tace
“Ina yini?”
“Lafiya Lou. Ina zuwa?”
Baki ta Dan turo tace
“Nika Zan Kai baka ga layi ba Kuma.”
Murmushi yayi yace
“Shine zakiyi kuka Kuma? Muje na rakaki.”
Nan suka fara tafiya suna Hira jifa jifa. Can Aliyu ya kalli Aisha yace
“Kanwata ina son ki fada min dalilin ki na son ganin gwamna.
Kallon sa ta tsaya Yi sai Kuma ta cigaba da tafiya tana fadin
“Baka manta ba Ashe!”
“Tayaya zan manta bayan shine dalilin haduwar mu.”
“Haka ne!”
Suka cigaba da tafiya can Kuma tace
“Hakika nin gaskiya shugabanci bala’i ne, Wanda ba Zan so wani nawa yayi ba Amman Kuma in har hakan zai zama hanyar da za a kubutar da wasu daga wani Hali Abu ne Mai kyau.”
“Uhmm!”
“A gaskiya abinda gwamna yayi wa mahaifina ya tsaya min a Rai…..”
“Wane gwamnan?”
Ya katse Mata maganar ta.
“Dan uwanka!”
“Nasan mahaifin ki ne?”
Yai Mata maganar dan shi bai san ma yayi ba kuma shi ba wanda ya sani a garin ba.
Kallon sa Aisha take da Mamaki sai kuma tace
“Gwamna nace!”
Dan basar wa yayi yace
“Ina nufin yasan mahaifin ki ne?”
Kallon sa ta danyi sai kuma ta dauke kai tace
“Mahaifina yana daya daga cikin masu masa aiki a gidan da kake. Wanda Ranar da ya nemi ganin ma’aikantan a lokacin mahaifina yana Jin zazzabi ya taho gida wannan yasa a washe gari da yaje ya je Dan ya bashi hakuri Amman kasan bai saurare shi ba sai ya kore shi”
Ta dago tana kallon Aliyu Ido cikin Ido tace
“Shin haka shugaba ya Dace suyi a matsayin sa na shugansu da suke aiki a gidan su ai ya kamata yaji uzurin sa akan ya zartar da hukunci. Shin yasan ladan da yake samu na daukar mahaifina aiki da yayi. Hmmm! Kasan me zai ciyar da marainiyya ya tufatar da ita ya ilimantar da ita bayan haka iyalan sq suma duk zai musu haka. Baka zaton duk da Mahaifina aiki yake. Aba Biyan sa Amman shima zau samu lada Dan ya taimaka masw ya ciyar da iyalan sa.”
STORY CONTINUES BELOW
Wajen nikan suka karasa ta ajiye a layi sannan suka matsa gefe tana fadin
“Wannan shine dalilin son ganin gwamna da nake Yi ina son in masa nasiha akan duniya da mulki Amman tin da gaka zan maka Kai Kuma kaji tsoron Allah tin da kana tare dashi. Ka fada Masa gaskiya ya kula ko ta wannan sanadin ya tsira.”
Aliyu Sam ya Manta da ya kori wani bare har ya tuna wanene ma. In ya kalli Aisha yaga yadda take magana with full of confidence ba tsoro tana burge shi. Dan da yawa mutane na da sanin gaskiya amman tsoro da son abin duniya Sai ya hana su fadin gaskiyar. Lallai Aisha ta wuce tunanin sa da sanin sa. Zama da ita zai Ankara da Kai abubuwa da dama.
Duk Yana wannan tunanin ne a lokacin da ya zuba Mata Ido.
“Kallon fa?”
Ta fada tana fadin
“In har mutun na son mulki na gaskiya Sai ya cire son zuciyar sa daga neman azurta Kansa daga dokiyar talakawa Dan dukiyar dake hannun sa ba tashi bace ta talakawa ce. Sai ya sa wa zuciyar sa cewar aljannar Sai zai nema daga wannan mulkin in ba haka ba kuwa son duniya zai rude shi Amman in har ya San aljannar sa zai neman zai cire son zuciya ya bautawa ubangiji.
Akwai hadisin da Annabi yake cewa
“Shugaba makiyayi ne, Kuma za a tambayar shi Akan kiwon sa.”
Kasan me hakan yake nufi kuwa? Dole ne ko wanne shugaba ya kula da mutanen da yake jagorantaka saboda a gobe kiyama Allah zai tambaye shi tayaya ya mulki Al ummar sa.
Yanzu da aka ce shugaba bawan Al umma ne, hakan Yana nufin Sai yayi aiki tukuru dan ganin ya kula da ko wacce Al umma dake karkashin sa.
Yana da kyau shugabanin mu su San cewa akwai gobe kiyama Ranar da Allah zai tsaida ka Dan Jin yadda ka kula da Al ummar ka.
Meyasa idon mu ke rufewa in Jin dadi ko mulki ya same mu ne? Mu manta komai sai duniyar bayan duniyar ba matabbaciyya bace.”
hawayen idon ta ta goge tana fadin
“Bayan lahira ita ce gidan mu tabbatace wanda ya kamata muyi iya yin mu Dan samun shi Amman ina Sam bama ta shi ta duniyar Muke kawai. Bayan duniyar gidan banza da wofi gidan da ba zamu taba dauwama a cikin sa ba. In kuka Tina ciwo zamu gane Lallai duniya abar banza ce mu nemi lahira ingantaciyya. Sai kana da lafiya lokaci daya ciwo ya same ka a lokacin zaka ji tsoron Allah domin in Allah yayi duk maganin da zakayi ba za a taba warkewa ba sai mutuwa. Mutuwa kadai Aya ce wacce zata tsorata duk wani Mai hankali da tunanin. Bayan mun mutu anan wata ayar take. A da Kai kake wanka Kai tafiya amman a lokacin sai dai ai maka. Abinda yafi wannan Kuma kwanciyyar kabari in da za akai ka a baro ka daga Kai sai halin ka. Ya salam acan fa abin yake acan danasani take ga wanda ya aikata ba dai dai ba kenan. to kada mu kuskura mu kasance cikin masu danasani a cikin kabarin mu muyi aikin da zai raba mu da yin danasani.
Sai Kuma final stage inda in a nan zamu tafi gidan tabbatace wanda in munyi aikin dai dai mu shiga aljanna in Kuma munyi aikin ba dai dai ba mu shiga wuta Wanda ba Wanda zai so shigar ta ko kafiri bare mu musulmai da ake kwadaita mana aljanna da tsoratar da mu da wuta.
Yana da kyau shugabanin mu su kasance suna koyi da kalifofin mu kamar Umar, Usman, Aliyu da Abubakar. Ba irin mulkin wadan nan shugabanin ba da kansu kadai suka sani ba.”
Tin da ta fara magana yake kallon ta. Lalai Allah yai baiwa a gun Aisha. Wani matsayi yake ji ya Bata na daban Wanda bai taba bawa wata irin da ba.
Hakika abinda yake so ana tunasar dashi Kenan Amman ba Mai masa haka Sai iyayen su. Matar sa da tafi kusa dashi a yanzu Bata tabai masa nasiha akan yaji tsoron Allah ba haka mabiyan sa.
Hakika ba zai taba barin Aisha tai masa nesa ba domin kuwa Aisha abar so ce da son kasancewa da ita ce.
Sosai jikin sa yai sanyi da Wanda Nan kalaman Aisha. Aishan ma tsoron duniya duk ya Kara kamata. Ganin an nika Mata yasa ta dauko shi ya amsa suka tafi sai dai. Yanzu tafiyar kurame ake ba me cewa uhm bare uhm uhm kowa magana yake da zuciyar sa.
A haka suka karasa gida lokacin har shida saura. Kallon sa tayi tace
“Yau dai ba karatu Dan da alama zamuyi dare a abinci zan je na taya Mamah. Nagode Alah saka da alheri Sai da safe!”
STORY CONTINUES BELOW
Kai ya gyada tayi cikin gida. Kasa tafiya yayi Sai zama yayi Akan dakalin gidan Yana zaune yana tunanin a zuciyar sa na kalaman Aisha da duk ba karya a cikin su Sai ya Kara Jin tsoron Allah da duniyar.
A haka akai sallah yaje yai sallah har akai isha’i sannan ya tafi gida jiki a matukar sanyaye. Yana zuwa ya fada saman kujera Yana bin gidan da kallo wayar sa ce tai Kara Yana dubawa yaga Maman sa ce wannan yasa ya dauka murya a matukar sanyaye.
“Ina yini Mama?”
“Lafiya Lou Baba na ya kake? Me yake damun ka?”
“Mamah tsoron duniya shi yake damu na.”
Dan murmushi tayi tace
“Yana da kyau ko da yaushe kana tsoron duniya domin duniya abar tsoro ce. Kuma Jin tsoron duniya shi zai sa ka kasa aikata aiyuka na gari bama da Allah ya baka wannan mu’kamin dole kayi taka tsantsar da wadan da ke gefen ka sannan ka samu amintacce a cikin wanda kuke tare da zai na nusar dakai. Ina Fatan sirika ta tana baka kulawa tare da kwarin gwiwa ko?”
“Uhmm Mamah ina Maryama da Abbah?”
“Suna nan lafiya. Abban ka yana bangaren Mamin ku.”
“Alright zan kwanta Mamah a cigaba da samu addu’a Allah ya bamu ikon yin adalci “
“Insha Allahu Baba na. Allah ya taimaka ya taya riko kaje ka kwanta sai da safe!”
Wayar yakashe ya lumshe ido Aisha kawai yake gani tana goge hawayen idon ta. Kai ya girgiza yana mai jin wani abu na ratsawa tin daga kasan zuciyar sa. Lallai dole ya rike Aisha domin kuwa ta silar ta ya kara shiga hankalin sa da tunanin lahirarsa duk da yana yi amman ta kara zaburar dashi dole ya mike yai taka tsantsan da mulkin nan nasa duk da bai so amman yana addu’a Allah yasa ya zama silar kubutarsa.
Ranar bai bacci ba tunanin sa mulkin sa shin yana yin adalci kuwa shi dai a yadda ya sani ana yawan yin aiyuka dan ana kawo masa takardun amsar kudi za’ai kaza za’ai kaza kenan anayi din.
Washe gari da ya shiga gidan gwamnati PAn sa ya sama akan aje gidan su Aisha a bawa mahaifin ta rumfa a kasuwa sannan a bashi jari masu yawa.
Baba yana gida yana shirin fita aka aiko ana sallama dashi yana fitowa PAn Aliyu ya mika masa hannu suka gaisa. Bayan sun gaisa ne yake fada masa aiken daga mai girma gwamna ne sannan yazo suje yaga shagon da aka bashi.
Ba musu suka tafi a take aka bashi takardun shagon da kudaden. Murna wajen Abbah kamar me a lokacin ya koma gida lokacn da Aisha a dawo daga makaranta kenan ta samu wannan labarin hakikanin gaskya taji dadi sosai. Sai ta fara tunanin keman magabar ta taje wajen Gwamna lallai in har taje gwamnan nan yana da daukar shawara lallai ba yadda ta dauke shi ba
Ranar wani nishadi ta jinga ji tare da farin ciki duk wanda ya ganta a take zai gane hakan. Karfe biyu da kwata tatafi isilamiyya.
Aliyu kuwa yana can office yana ta aiki yana gano aiyikan da ake gudanar wa kamar yadda takadu ke nuna masa shi kuma yasa hannu aje a amshi kudi. In yai duba da hakan yana ganin ai bashi da matsalar komai dan haka sai yaji damuwar sa ta ragu amman a ransa akwai wani target da yake dashi wanda da kan sa da kuma dukiyar sa yake son yanayi.
Hudu nayi ya bar gidan bayan yai sallah la’asar garin ya hau zagayawa sai dai a yadda yake jin ana aiki sam sai yaga kamar ba abinda ake ba titi ka bayan hawan sa an ce anyi titika sunfi hamsin amman tin da ya hau zagaya gqrin bai ga wani sabon titi ba. Har biyar da ashirin tayi sannan yayo hanyar gidan su Aisha dan ko gida ranar bai da niyyar komawa.
Yana daga cikin motar tasa ya hango ta tana tafe cikin uniform din ta tai kyau ga annurin fuskata duk dadu. Kallon ta ya tsaya yi yana jin wani sanyi da nishadi har ta gota motar zata shiga gida yai saurin bude murfin kofar ya fito.
Tana ganin sa ta kara fadada fara’ar kan fuskar ta tace
“Ina yini?”
“Lafiya lou Aisha ya gida da makaranta?!
“Alhamdulillah! To je kicire uniform kizo muyi watacmagana yau ba lesson.”
Baki ta washe tana fadin
“To ina zuwa!”
Tafiya tai cikin gida bin ta yayi da kallon yana mai girgiza kai hadi da shafa sumar kan tashi sai kuma ya lumshe ido. Shin me yake ji game da Aisha ne? Yana jin abubuwa masu yawa wanda ba zai iya misaltasu ba.
Bata jima ba ta fito fuskar ta dauke da murmushi wanda yasa kumatunta lotsawa. Kallon ta ya tsaya yi. Hannu ta tafa masa tace
“Kallon fa?”
Murmushi ya saki. Shi kan sa Aliyu yana mamakin kansa. A baya ba ruwan sa da shiga abinda ba ruwan sa dashi amman daga kan Aisha komai ya canja masa. Shine zai zauna yai ta magana ko Aishan ta cika shi da surutu amman bai ji ta gudure shi bare ta saka masa ciwon kai.
Shi da bai kallon mace amman yanzu idanun sa ba abinda suke so da muradin kalla kamar Aisha. Jin matsayin Aisha yake a jikin sa kamar yar uwar sa. Haka na matsayin ta azuciyar sa ya kasa ganewa.
Ido ya lumshe sannan ya bude ya sauke akan ta tare da sakin wata ajiyar zuciya. Itama kallon nasa take da murmushi akan fuskar ta
“Ya dai?”
Ta fada tana dage girar ta Murnushi yayi yace
“Normal!”
“Kace za muyi wata magana!”
Shi har ga Allah ya ma manta da ya fada mata.
“Zauna mana.”
Zama tayi tana kallon sa. shima ita yake kalla. Ita tai karfin halin janye idon ta.
Murmushi ya saki yace
“Tambayar ki zanyi Ayshh!”
Juyowa tayi jin yadda ya ambaci sunan ta. Kai ya gyada mata. Kai ta dauke dan wani abu ta gani a idon sa wanda ta rasa gane menene shi.
Murmushi yayi yace
“Ya kike ganin mulkin dan uwa na? Shin yana aiki ko kuwa?”
“Ba zance ba a aiki ba Yaa AK amman a gaskiya in ma anayi wani wajen basu san da anayi ba. Ilimi yana daga cikin manyan abubuwan da ya kamata gwamnati tana taimakawa amman abin sam ba haka yake ba. Zan so kazo makarantar mu kaga babu cikakun malamai, ba wajen daukar karatu mai kyau ba kayan daukar karatu duk abin sai a hankali bayan ana son kan a dau darasi ya zamaba environment din is well established with all teaching and learning material wanda zasu taimakawa yaran su gane abinda ya dace su gane, hmmmm did u know wai nan mu yan secondary ne, ina ga primary school student su tayaya kake ganin zasu samu abinda ake so for god sake. Tayaya ake ganin zamu zama wasu ko mu taimakawa al umma bayan muma ba atsaya mana akan mu zama hakan ba. Yaa AK their is problm on education in our state.”
Ajiyar zuciya ta sauke tana kallon sa tace
“Ilimi ya zama koma baya bayan shi ya kamata ya zama abu na farko da za a taimaka mana dashi…………