WA NAKE SO CHAPTER 6
Bashi ya dawo ba sai gab da magariba Dan Yana dawowa ya shiga ya dauro alwala ya tafi masallaci. Acan suka hadu da Abba wanda basu fito ba sai da akai sallah isha’i sannan suka fito a tare sukai bangaren Mai martaba tare da fadawan dake takewa Abbah baya.+
Suna shiga Momy dake da girki na bangaren tana ganin Aliyu ta Bata Rai Sai Kuma ta saki fara’a tana fadin
“Barka da zuwa ranka shi Dade!”
“Yauwah Fulani. Ya gidan?”
“Alhamdulillah!”
Waje Aliyu ya samu ya zauna. Sannan ya kalli Abbh yace
“Gobe nake son na koma da gudanar da abubuwan da suka Dace.”
“To madallah. Allah ya kaimu.”
“Amin!”
Ya Mike Tare da Dan rusunawa yace
“Na barka lafiya. Sai da safe.”
“Allah bamu alheri.”
Ya juya zai fita sai ga Momy Nan da kuganyu sun shigo rike da tray.
“A’ah ina Kuma zaka baka ci abinci ba?”
“Alhamdulillah!”
Ya fada Yana yin gaba abinsa. ciki suka karasa. Shi Kuma yayi bangaren Mamah Yana shiga suka gaisa sannan ta saka Maryama ta kawo Masa abinci.
Zama yayi yaci ya koshi sannan ya kalli Mamah yace
“Gobe da safe Zan koma fa.”
“Tin gobe!”
“Mamah Ina son naje na gudanar da aiyukan dake gaba nane.”
“To amman wannan sallar zaka zo kayi a gida ko?”
“Sai yadda Naga yanayin aikin.”
“Toh Allah taimaka.”
“Amin.”
Ya Mike Yana fadin
“Sai da safe.”
“Allah tashe mu lafiya “
“Amin!”
Ya fice ta bishi da kallo so da kaunar sa hadi a tausayin yaron take ji. Tana son Aliyu tana son wannan dabi’ar tasa ta ragu ta miskilanci. Ta zata in yai aure zai rage amman Ina abun kamar daduwa take gwara kwanan ma taga ya dan rage ko me yasa oho? To Allah dai yasa Aliyu ya rage wannan miskilanci.
*
Aisha kuwa yau da ta taso tazo taga Aliyu bai zo ba sai ta shige gida. Kaya ta canja ta saka wata doguwar rigar atamfa wacce take blue kala an mata ado da yellow da fari. Tayi mata kyau. Farin Hijab ta saka ta fito tacewa Umma zata je ta dawo tana fita tayi gidan Aliyu.
Mai gadi yana zaune ta karasa. Yana ganin ta ya saki fara’a Yana fadin
“Ranki ya Dade yau a garin.”
Murmushi tayi tace
“Ina yini?”
STORY CONTINUES BELOW
“Lafiya Lou! Ya kwana biyu?”
“Alhamdulillah!”
Kallon gidan tayi yace
“Yaa AK kuwa Yana Nan?”
“Waye haka?”
Ya tambaye ta.
“Mai gidan Nan!”
“Oh wallahi dazu da safe suka fita shi da Yan gidan su daga gani Kuma nisa yayi gaskiya.”
“Oh shikenan sai anjima.”
Ta juya ta tafi ranta ba Dadi kamar zatai kuka. Yanzu Ina Yaa AK ya tafi ya manta da ita Kuma shine bai fada Mata ba.
Tana komawa gida dakinta ta shige ta kwanta. Mama da tana ban daki ta shigo gidan yasa Bata San ta dawo ba. Sai da zata shiga daki taga takalman ta. Lekawa tayi gnin Aisha kwance abin ya bata mamaki.
“Lafiya Aisha?”
Ummah ta tambaya. Tashi zaune tayi tace
“Lafiya Lou Ummah”
“Shikenan.”
Ta fita. Aisha kuwa kwanciyya ta gyara tana Jin wata kewar Aliyu. Ji take kamar Bata da lafiya ma garin duk yai Mata ba Dadi sanna ta saka Rai da zuwan shi Amman Kuma bai zo ba dan haka duk sai zuciyar ta ta baci komai ya dagule mata.
Ko magariba a daki tayi haka nan sallah isha’i da Abba ya dawo ma suna cin abinci ta koma daki abun ta.
Abba ma mamaki ya kamashi kasa yin shiru yyi yace
“Uwa ta kuwa lafiya take?”
“Lafiya take Malam. Nima dazu sai da na tambaye ta.”
Mikewa yayi ya shiga har dakin nata tana kwance tana juye juye yai sallama. Mikewa tayi zama yayi yace
“Uwa ta lafiya kuwa?”
Kai tayi kasa dashi tana wasa da yatsun ta tace
“Lafiya Lou Abba.”
“Kin tabbatar.”
Kai ta gyada. Yace
“To madallah.”
Sannan ya fice. Ta koma ta kwanta tana rasa me ke Mata dadi. A da in Yayan ta ya tafi take Jin irin wannan Amman yanzu me yasa take Jin yanayin. Ga haushin Yaa Aliyun ta da take ji akan ya tafi bai fada Mata ba. Da kyar tayi bacci a Ranar.
*
Aliyu ma Sai da yaje kwanciyya yaji shi incomplete Sam ya rasaa menene bai yi ba da ya tsaya Masa a Rai. Yana kwanciyya ya lumshe Ido. Fuskar Aisha ya gani da sauri ya Mike Yana dafe kan sa.
Wata kewar ta yaji Yana yi. Kwana biyu da bai ganta ba Amman duk ji yake kamar ya shekara biyu. Shin Wai har yaushe suka shaku da Aisha har take son zama jinin sa da tunanin sa.
A lokacin ba abinda yake son gani inba Aisha ba. Da kyar yai bacci. Da asuba kuwa Yana tashi yai shirya tafiyar sa gaba daya.
Da sassafe ya bar garin su Dan Yana so yaje ya gudanar da aiyukan sa sannan yaga Aishan sa. Dan baya Jin zai iya Kara kwana bai saka ta a idon sa ba.
Daga Nan ba inda aka wuce dashi sai gidan gwamnati. Yana zuwa ya shiga office yayi abinda zaiyi karfe Sha biyu ya fito ya shigan wajen da ya saka a kulle Masa mutanen sa.
Cikin kwana daya sun canja kama sunji Baki sun ji jiki. Yana shiga yace a sake su Amman ya Basu kwana biyu su dawo Masa da kudaden da suka amsa.
Nan ya fice ya wuce cikin gidan. Matar gidan na falo dakin cike da kawayen ta Sai shewa ake.
Yana shiga bai ni ta kansu ba yayi ciki. Da Ido suka bishi. Nan ta kike tace
“Ina zuwa.”
A falo ta same shi Yana danne danne a wayar sa. Zama tayi tana fadin
“Ranka ya Dade kwana biyu?”
Murmushi yayi Mai ciwo yace
“Oh kina nema na Daman?”
“Ni fa matar kace.”
Dagowa yayi Yana kallan ta kafin yace
“Au haban Ashe fa ke matata ce ko?”
Kallon sa ta tsaya Yi na mamaki. Sannan yace
“Alhamdulillah ni Ina sauke nauyin dake Kai na. Na fada Miki ki biyoni gida na Dan Nan ba gida na bane Amman kin ki. To Kinga ai ban Isa dake ba kenan ko? Ni ba Zan takura Miki ba amman ki sani duniya ba mattabata bace “
STORY CONTINUES BELOW
Yana gama fadin haka ya Mike ya fice a dakin. Da ido ta bishi.
Sallah yayi ya koma office. Bai Jima da zama ba aka zo aka fada Masa yayi Baki. Bada izinin shigowar su yayi Dan shi ya neme su. Yan kwangila ne Nan ya Basu duk abinda ya Dace ya Basu time din da uake so yaga kammaluwar aikin. Sun Jima Dan har akai kiran sallah sannan suka fita Dan yin ta. Suna idarwa suka koma ya Basu location da komai sukai handling sannan ya fito Dan ya tafi gida.
Karfe biyar da rabi ya koma gida a gajiye. Wanka kawai yayi ya shirya cikin bakin wando da Ash din Riga yai kyau sai tashin Kamshi take. Da hanzari ya fito ya nufi gidan su Aisha.
******************************************************************************************************************
Ranar da Dady zai dawo a Ranar tin safe bamu koma ba mune gyara gidan da girke girke kala kala. Sai karfe biyu duk muka shigar mukai wanka muka shirya cikin kaya masu kyau.
Sai dai daga kallo daya zaka game sam bama cikin kuzari Wanda tin safe Momy take ce min tana fama da faduwar gaba Nima hakan nake ji Amman na danne nace
“Kila duk murnar dawowar Dady ne.”
Murmushi Momy kawai tayi muka cigaba da aiki. To yanzun ma abinda nake ji a zuciya ta kenan. Muna zaune Muna jiran isowar su Dan munyi waya a lokacin da suka wuce kaduna yace gasu Nan karasowa.
Muna zaune gaba dayan mu a falo mukaji an bude gate ni da Basma muka fita a guje bama da taji karar Motar Dady. Kan mu fito har anyi parking wannan yasa a guje mukai wajen motar sai dai ana budewa muka ga ba Dady bane.
Turus mukayi Muna bin sa da kallo.
“Ina Momyn taku?”
Ya tambaye mu.
Jiki na, na rawa nai Masa nuni da cikin gida. Motar kwana kwana ce ta shigo gidan abinda ya Kara kada hanjin ciki na. Na juyo da sauri ina kallon motar. Momy ma dake ciki ta fito a guje Sai tayi turus a bakin kofar falo.
Muna tsaye kowa ya kasa motsawa aka bude motar aka fito da mutum kwance Akan gadon asibiti. Ido na zaro. Kirjin na na dukan bakwai bakwai. Da gudu nayi wajen gadon ina zuwa na bude abinda aka rufe masa fuska dashi. Dady ne kwance fuskar nan tasa tai fayau da ita tayi haske kamar Yana murmushi.
Ido na zaro ina nuna shi tare dayin baya. Daga Nan ban Kara sanin a inakai Na yake ba.
Momy baiwar Allah kuwa tana tsaye har nurse din da aka zo da ita ta karaso tana fadin
“Hajiya sai hakuri Allah yayiwa Alhaji rasuwa.”
Zabura Momy tayi sai Kuma ta hau girgiza Kai tare da yin wajen gawar. Tana ganin Dady ta fada kan sa tana fadin
“Alhaji Dan Allah ka tashi kar ka tafi ka barmu. Innalillahi wainna illahir rajiun. Shikenan gatan munya Kare Dan Allah ku tashe shi bai mutu ba dazu yai min waya ya fadi na girka Masa tuwo wallahi Alhaji na girka maka ka tashi kaci dan Allah kada ka tafi ka barmu Dan Allah.”
Nurse din da aka zo da ita ce ta janye Momy Tana lallashin ta tare da shiga da ita ciki. Nan aka dauki gawar Dady aka shiga da ita ciki.
Ni Kuma da Abokin Dady ya kamani da zan fadi Yai cikin gida dani Yana yiwa Nurse din dake tare da Momy maganar cewar ta kula Dani.
Kan kace me an fadawa Yan uwa da abokan arziki Nan da Nan gdan mu ya cika da mutane daga Yan uwan Dady da Yan uwan Momy na da makwabtan mu.
A take akai wa Dady sutura aka Mika shi gidan gaskiya. Sam Momy ta kasa kuka sai sunbatu da take da ka kalle ta kasan bata cikin hayyacin ta. Kaka ta Baba Uwani da tazo sai rubutu ta saka akai Mata Amman ina Sam in anzo Mata gaisuwa ma bata gane mutanee. Batai kuka ba amman idon ta yai micin micin kamar wacce ta Sha kuka. Muryar ta ma ta makale.
Abin tausayi. Ni kuwa da na farfado ina kuka da surutan wannan yasa akai min allurar bacci.
Bani na farka ba sai wajen isha’i Anty Huwaila Yayar Momy na mahaifiyar Yaa Fauwaz na gani a dakin zaune akan sallaya. Ido na mutsuke na Mike Sai na ji jiri da sauri ta dago tana fadin
“Ah kin tashi kiyi a hankali fa.”
Ta mike tana kamani tace
“Ina Zaki?”
“Bandaki!
Na Bata amsa. Ita ta taimaka min na shiga. Ina shiga na saki wani irin kuka Mai taba zuciya. Na jima a ciki sannan nayi alwala na fito. Hijab Mami ta bani na tada sallah. Sai da nayi magariba sannan nayi isha’i na Jima ina addu’a, Kai na na tusa cikin cinyoyi na ina sakin wani kuka a hankali.
A Raina fad nake
“Shikenan gatan mu ya Kare.”
Dagowa nayi na kalli Mami da idanu na da suka rine dan kuka da tashin hankali. nace
“Ina Momy?”
“Taso muje kin idar!”
Na mike muka Fita, falon gidan cike da mutane duk da dare ne. Momy na hanga zaune a kan sallaya kan ta a kasa bqn San lokacin da na saki wani kuka nayi kan ta ba. Tana Dagowa taga nice sai ta rumgume ni Yana bubbuga min baya na.
Baba Uwani ce ta dago ni tana fadin
“Menene nq kukan to Fateema ai addu’a ita ce gatan sa ita yake neman ba kukan ku ba. Ki daina kuka kinji ko?”
Kai na gyada na lafe a jikin Baba Uwani. Muna zaune mahaifiyata Fu’ad da kishiyar ta suka shigo wasu yara biye dasu da kulolin abinci.
Da mutanen dakin suka gaisa sannan suka gaisa da Baba Uwani sun karai Mata gaisuwa duk da dazu suna Nan aka Kai Dady.
Hajiyar Fu’ad ce ta matso kusa damu tana fadin
“Fateema kin farka kenan. Ya Karin hakuri?”
“Alhamdulillah!”
Ta na fada ina da fadin
“Ina yini?”
Ta amsa na gaisar da kishiyar ta suna min ya Karin hakuri. Sun Jima Dan har wajen Tara sannan suka tafi.
Fu’ad kuwa sai kace mahaifina sa ne ya rasu Dan yashiga tashin hankali sosai Dan ya San nima duk inda nake ina cikin sa. Sam ya kasa cin abinci kwata kwata.
A compound suka same shi Yana jiran su. Suna fitowa yayi wajen Hajiyar sa Yana fadin
“Hajiya ta farka kuwa?
“Ta tashi tana jikin Baba Uwani ma.”
“Alhamdulillah!”
“Muje ko?”
“To Hajiya taci Abinci.”
“Anya kuwa.”
“Hajiya ina son naga Fateema.”
“Fu’ad ka Bari zuwa gobe kawai.”
Kai ya gyada suka tafi.
Washe gari ma daga gidan su Fu’ad Sai da aka Aiko da Kunu da kosai da fanke har da bread da tea.
Sam tin jiya da safe rabo na da abinci domin kuwa jiran dawowar Dady Muke muci tare Sai zuwan gawar Dady muka gani.
Ina kwance a falo su Suraiyya sa’anina da wasu class mate dina sunzo. Dakin kowa jigum jigum abin tausayi cikin Kwana daya na rame sosai.
Mami ce ta shigo hannun ta rike da cup kunun gyada ne da yaji madara ta mikon tace
“Amshi maza Kisha ko cikin ki ya sake ace tin jiya rabon ki da abinci.”
Amsa nayi na rike a hannu na tana fita na ajiye a gefen kujera. Ina zaune ana ta zuwa gaisuwa wanda ni duk hankali na baya jiki na ji nake kawai kamar Dady bai mutu ba wasa ake Mana zai dawo Amman ina har lokacin shiru.
Zuciya ta ta gama karyewa na kasa gane me nake ciki. Ina zaune aka shigo Yan matan me kyawawa tin da suka shigo daya a cikin ta zuba min Ido tana kallo na. Sauran ne suka ce
“Anty Fateema ya Karin hakuri?”
“Alhamdulillah!”
Na fada ban gane su ba. Muna zaune Mami ta shigo tace
“Fateema kinsha kunun kuwa?”
Kallon sa nayi nace
“Mami na kasa Sha.”
“Toh yanzu haka Zaki zauna Baki Sha komai ba.”
Fuska na marairaice.
Mami tace
” ‘yan gidansu Fu’ad ne fa suka zo “
“Allah sarki Ina Hajiyar?”
“Suna Falo!”
Kallan Yan dakin tayi tace
“Ai tare suka zo da wadan Nan ko?”
Yan matan suka ce
“Eh!”
Haba sai lokacin Naga Ashe da Fu’ad suke kama. Mikewa nayi muka fita tare da Mami. A falo Yan uwan su Fu’ad ne da yawa suka zo gaisuwa yanzu ma har da abincin shinkafa da Miya.
Bayan mun gaisa Mami tace muje waje. A can na ga Ashe Fu’ad ne yazo min gaisuwa. Ina Ganin shi zuciya ta ta karye sai hawaye. Sitting room muka nufa ina shiga na zauna na hade Kai na da gwiwa ina kuka.
Matsowa yayi ya durkusa a gabana Yana fadin