WA NAKE SO CHAPTER 7
Fu’ad da yafi minti goma tsaye akai na ban san ya shigo ba har na fara hawaye sai ji nayi yana gogen hawayen ido na. Wannan yasa na dago a firgice ina kallon sa. Zama yayi a gefe na ya kamo hannu na yace
“Dazu muna magana mukai baki right?”
Ban amsa masa ba sai wani sabon hawayen dake, zubo min kai ya dafe yana fadin
“Fateema ba abinda na tsana na gani kina yi kamar kuka. Ina bawa kai na laifin na na kasa baki farin ciki. Dan Allah ki fada min me yake saki kuka?”
Kai ta girgiza masa. Kallon na yake cike da tausawa yace
“Ba zaki fadan ba.”
Shiru nayi. Janyo ni yayi jikin sa ya rungume ni kamshin turaren sa da nawa suka hadu wannan yasa na lumshe ido. Shima jikin sa sanyi yayi yace
“Dan Allah ki daina kukan nan. In kina kuka ina jin kamar ni nai miki laifi.”
“Ba kai min komai ba My.”
“Kin tabbata?”
Kai na gyada yace
“Yi baccin ki.”
Ya fada yana jijjiga ni a jikin sa kamar jaririya. Bacci ne ya dauke ni dan naji dadin kwanciyyar da nai a jikin sa. In ina tare da Fu’ad ina jin wata nutsuwa da kuma jina a cikin kariya.
Tunani ya fara dan ya kasa samun kwanciyyar hankali da kukan da Fatrema take. Ba zai ce Fateema bata son sa ba amman me yake sata kuka dole ya tuntuba ya gano me yake faruwa domin kuwa damuwar Fateema damuwar sa ce dole ya fita da ita daga damuwar da take ciki ko da shi zai dauwama a cikin bakin ciki. Yasha fada mata haka kuma yana jin a ransa ko rayuwar sa zai iya rasawa dan samuwar farin cikin Fateema.
A haka muka debe sati guda sam bani da walwala ko nutsuwa da na kebe kaina sai nai ta kuka wannan ba komai ke kara sani kuka ba sai mafarkan Yaa Fauwaz da nake kuma ba komai yake sani mafarkan sa ba sai yawan tunanin sa da a halin da yake ciki.
Duk kan mu daga Fu’ad har Ni mun rame bama Ni danke ciwo a daddafe amman naki ta nuna masa.
Da yamma ne wajen karfe biyar ina zaune wayar ta tayi kara na dubawa taga Suraiyya ce da sauri na dauka ina fadin
“Surry ina ta jiran kiran ki daga cewa zaki kira ni.”
“Abubuwa ne sukai mun yawa kinsan fa sauran wata daya biki ko?”
“Haka ne ya shirye shirye.”
“Alhamdulilah. Fateema ki fadan menene damuwar ki wallahi kullum da tunanin ki nake kwana nake tashi ina cikin damuwa ta dalilin damuwar ki. Tin kan biki nasan kina cikin damuwa amman na share ne ina ganin da anyi biki abin zai wuce sai gashi shiru har Fu’ad ya kawon karar ki fa. Yace baki da aiki sai kuka shin menene matsalar?”
Hawaye ne ya hau zubowa a idon Fateema.
STORY CONTINUES BELOW
“Kinyi shiru Fateema.”
“Uhmm Suraiyya ta ina zan fara ne?”
Fu’ad da ya shigo gidan ya baro motar sa a waje dan Hajiyar sa na son ganin sa ya biyo yaga ya Fateema take yaji ta fadi wannan kalmar wannan yasa ya tsaya a ta taga ta inda ta juya masa baya yana sauraron su.
“Ina sauraron ki. Ki fadan kome ke damun ki.”
“Hakika ina cikin matsala da tashin hankali. Na rasa yaya zanyi da rayuwa ta. Fu’ad shine masoyi na na farko kuma har yanzu ina son sa sai dai na kasa cire Yaa Fauwaz a raina Suraiyya kullum tunani na yana wane hali ya yake? Nasan ba kyau saboda ina da aure yanzu amman na kasa dainawa. Suraiyya kullum sai nayi mafarkin Yaa Fauwaz yana kara jajjada min son da yake min. Bazan boye miki ba a gaskiya ina son Yaa Fauwaz har yanzu.”
“Me kike Fadi Fateema? Fu’ad din fa?”
“Son sa a jini na yake shima ina son shi.”
“Ke me yake damun ki ne dole a kwai wanda kika fi so *wa kike so?* “
“Dukkan su.”
“Gaskiya Fateema dole da wanda kika fiso. Kuma ni a yadda kike fada min matsalar ki a yanzu Yaa Fauwaz kika fiso tinda gashi kina tare da Fu’ad hakan bai hanaki tunanin sa ba. Shin meyasa kika yadda da auren Fu’ad in bakya son sa.”
“Ki daina fadar haka Suraiyya wallahi ina son Fu’ad. Son sa a jini na yake.”
Tsaki Suraiyya tayi tace
“Ke wacce irin zuciya ce dake. Abinda zan fada miki wallahi ki rike Fu’ad dan bazaki taba samun kamar sa ba domin kuwa yana son ki in kika bari ya kubuce miku sai kiyi danasani nasan har da shaidan a kara tun zura ki akan soyayyar Yaa Fauwaz to wallahi kiyiwa kanki karatun ta nutsu ki zauna lafiya da Fu’ad.”
“Suraiyya ba zaki gane bane wallahi a halin da ake ciki nasan ina cutar Fu’ad kada Allah ya kamani da cutar da nake masa gashi da auren sa ina tunanin wani.”
“Gwara da kika gane hakan ba dai dai bane dan haka ki gyara.”
Hawaye idon ta ta goge tace
“Tayaya zuciya ta ce fa tayaya zan cire sa a zuciya ta ki fada min.”
Sai ta saki kuka mai taba zuciya. Ita kan ta Suraiyya tausayin yar uwar tata takeji. Dan zuciyar ta ta karye akan al amarin. Dan haka tai ta lallashin ta.
Fu’ad da ke tsaye jikin sa ne ya fara rawa shin daman har yanzu da son Yaa Fauwaz a zuciyar Fateema.
“Inna lillahin wainna illahir rajiun!”
Shine kadai abinda ya iya fada hawaye na zuba a idon sa da sauri ya bar tagar ya fita a gidan. Cikin motar sa ya koma ya kifa kan sa akan sitiyarin motar hawaye na zuba a idon sa.
Shin me zai yi yanzu. Son Fateema shine rayuwar sa rabuwa da ita kamar rasa farin ciki da walwalar sa ne. To ita in yana tare da ita ya tauye mata farin cikin ta. Yaya zai yi.
Yana tsaka da kuka wayar sa ta hau kara yana dubawa yaga hajiyar sa ce. Hawayen idon sa ya goge yace
“Hajiya wallahi aiki ne ya rike shiyasa amman gani nan zuwa.”
“A’ah ai kuma magariba tayi ka koma gida ka bar Fateema ita kadai tin safe gobe ka zo ka gaishe min da ita.”
“To zataji insha Allahu.”
Kiran sallah magariba shi yasa ya fita a mota a kofar gidan yai alwala ya shiga masallaci sukai sallah. Har aka idar bai tashi ba bare ya sa ran zai fito. Yana zaune aka kira isha’i tare sukai sannan ya kara zama sam ya kasa tashi har karfe tara yana zaune ya rasa tunanin da zai yi.
Fateema tin da akai isha’i Fu’ad bai dawo ba hankalin ta ya tashi dan haka ta kira sa amman ba a dauka ba. Sosai ta shiga tashin hankali har akai isha’i ta na falo ta kasa tsaye ta kasa ta zaune. Sai kiran layin take kuma ba a dauka.
Kuka na fara dan na tsorata ko wani hali yake ciki a lokacin. Ina zaune tara da kwata taji karar motar sa ta shigo gidan bam san lokacin da ta fita ba daman ban cire hijab din da nai sallah ba. Da gudu na karasa wajen sa yana bude mota na fada jikin sa ina sakin kuka ina fadin
“Ina ka tafi ka barmi?”
STORY CONTINUES BELOW
Rumgume ni yayi yana jijjiga ni yana kara jin son na da kaunar ta a zuciyar sa. Da kyar ya bude baki yace
“To mene na kukan ba gani na dawo ba.”
Kai na gyada masa nace
“To ai sai kiyi murna ko? Kinsan bana son kukan ki ko?”
Kai na kara gyada masa. Hannu yasa yana goge mata ido yana fadin
“To ya isa muje.”
Ina jikin sa muka shiga falo. Muna shiga ya zaunar da ni ya shafi fuskar ta yace
“Aiki ne yai min yawa shiyasa wayata kuma tana silent kiyi hakuri.”
Kai na gyada nace
“Kada ka kuma.”
Kai ya gyada yace
“Bari naje na watsa ruwa.”
“Muje na hada maka.”
“No yi zaman ki.”
Kai na make nace
“A’ah ka fa gaji.”
Murmushi yayi nai gaba yabi bayan na. Kaya ya hau cirewa yana mamakina ji wai dan bai dawo da wuri ba yadda na tada hankalina. Yasan ina son sa amman bai san meyasa nake tunanin wanin sa ba. Anya zai iya zama yana cut ta bayan yasan kuma da wanda nake so.
Towel ya daura ta fito ina ganin sa a haka nayi gaba da sauri. Kamo hannun na yayi yace
“Zo ki cudan baya mana.”
Ido na runtse ina girgiza kai na. Sakin na yayi yana kallon na na fice a guje shi kuma ya shiga yana wanka yana tunani. Zafi yake ji a zuciyar sa da radadi ya rasa na menene a haka ya gama ya fito sanye da three quater da riga mara nauyi.
Ina ganin sa na mike ya karaso ya kama hannun na mukai dining serving nasa nayi amman ya kasa cin ko da spoon uku ne sai juyawa yake. Ganin haka yasa na amshi spoon din ina fadin
“Ya dai ko bai dadi bane?”
“Ina fa yayi dadi har ya gaji da yin dadi.”
“Uhmm ko? To bude bakin in baka.”
Na diba ina bashi. Da kyar yake iya hadiyewa har na gama bashi abincin. muka koma falo karfe sha daya ya mike ya kalle yace
“Dare fa yayi kije ki kwanta.”
Kallon sa nayi dan nasan tun da mukai aure bamu taba raba wajen kwanciyya ba wannan yasa nace
“Kai a ina zaka kwana?”
“Daki na.”
“Saboda me?”
“Zan yi aiki ne.”
Jikin sa na kwanta nace
“Gaskiya ban yadda ba kayi dare a gun aiki sannan ka dawo ka kara kwana kana aiki ni gaskiya A’ah.”
Murmushi yayi yace
“To muje!”
Nayi gaba shi kuma ya kashe kayan wuta yabi bayan na. Bana daki dan haka ya zauna a gefen gadon ya zuba tagumi. Har na fito a wanka bai sani ba na gama shiryawa sannan nazo gaban sa na cire masa hannayen da ya zuba tagumi dashi. Nace
“Amman kasan ba kyau ko?”
Murmushi yayi min yace
“Zo ki kwanta dare yayi fa.”
Fuska na dan bata nace
“Bakace nayi kyau ba.”
Nayi juyi a gaban sa. Murmushi ya saki Allah ya sani yana son Fateema da halaiyar ta amman kuma a yanzu zuciyar sa yake tausayawa domin kuwa yanzu ya gane Fateema akwai soyayyar Yayanta a zuciyar ta.
“Fateema na kinyi kyau kinsan ke me kyau ce komai kika sa ke kike sashi ya yi kyau.”
Murmushi nayi nace
“Nagode amman ai kafini yin kyan.”
Kan gado na hau na kwanta ya mike ya kashe fitilar dakin sannan ya hau kan gado ya kwanta daga gefe. Jin sa a gefe yasa na matsa na kwanta a jikin sa. Yana jina na yai mata shiru kamar yai bacci.
Ranar bai bacci ba dan ya rasa wane irin tunani zai yi. Ya rasa yaya zai yi da son Fateema.
Har asuba idon sa biyu yana saka da warwara. Jin ana kira yasa ya mike ya tada ni. Fita yayi ya nufi dakin sa ya watsa ruwa yai alwala sannan ya wuce masallaci. Mikewa nayi ina mamakin sauyawar Fu’ad. Ban daki na shiga nayi wanka na dauro alwala. Raka’atanil fijir na kawo sanna na mike na tada sallah. Ina idar wa na hau gyara gidan kan Fu’ad ya dawo na gama hada break.
Wanka na shiga ina yi na fito nayi kwalliya cikin wata atamfa ta pink and black tai kin kyau nasha dauri na. A falo na same shi yana waya. Yana gani na ya zuba min ido can kuma saiya dauke kai yana mai cigaba da wayar da yake.
A hankali na karaso na zauna a kusa dashi. Hamnun sa dayan ya daura akan cinya ta ya na kama hannu na yana murzawa yana karasa wayar. Sai da ya gama ya juyo yana kallo na nace
“Ina kwana?”
“Lafiya lou My…”
Sai kuma yai shiru. Kallon sa nayi nace
“Menene?”
“Ba komai!”
Ya fada yana mikewa. Nima mikewa nayi na karasa dining break mukai amman kadan yaci ya mike har bakin kofa na rakashi sannan na koma.
A kan kujera na kwanta ina tunanin da na saba ko kuma nace wanda ya ya zame aiki kullum sai nayi. Ban san lokacin da bacci ya dauke ni ba bayan nasha kuka na na koshi.
Fu’ad kuwa yana fita a gidan ya tsaya a kofar gidan yana mai runtsa idon sa. Yana son Fateema yana son fari cikin ta yaya zai yi kenan. Yafi minti biyar a gun sannan yaja motar a hankali ya kama hanyar gun aiki yana zuwa ya shige office din za ya zauna.
Yana da aiki amman sam ya kasa sai zagaye office din yake yana tunanin tayaya zai bawa Fateema farin cikin ta. Shin me zai yi ya bawa Fateema farin cikin ta ya cire ta a damuwa. Yayi wa kansa alkawarin cewa duk abinda Fateema take so zai samar mata sai dai in ya kaucewa addini in kuwa ba haka ba komai zai bata ko da zai zama silar shigar sa bakin ciki da tashin hankali indai Fateema zatai Farin ciki to shi ya kasance cikin kunci.
_”Tab wannan lallai shine true love. Allah sarki Fu’ad reader me zakuce menene mafita ku bawa Fu’ad shawara_Ya kasa zaune ya kasa tsaye saboda da tunanin mafitar da zai yanke musu. Tunani yake kawai ya sauwakewa Fateema ko ta samu nutsuwa yaje ya nemo mata Fauwaz yazo ya aure ta, domin kuwa yasha fada mata tin kan ya aure ta indai Yaa Fauwaz zai aure ta to bai da haufi domin shima masoyin ta ne. Kuma ya sha fada mata zai iya sadaukar da farin cikin sa akan samuwar nata farin cikin.
Hakika yana kaunar Fateema kuma bai taba tunanin yau zai auri Fateema wata rana ya rabu da ita ba. Sam bai taba kawo haka ba ya saka a ransa shi da Fateema mutu ka raba.
Hakika in har ya bar Fateema to shi tashi rayuwar zata ruguje amman dole ya samarwa Fateema abunda take so. Yana son Fateema son da bai tabaiwa wani irin sa ba. Yana son Fateema fiye da kan sa.
Tabbas dole ya cikawa kansa alkawarin da ya sha daukar wa Fateema na cewar zai iya sadaukar da komai nasa dan samuwar farin cikin ta. Dole ya cika mata wannan alkawarin ko da shi hakan zai yi sanadin mutuwar sa.
Shin tayaya zai iya rayuwa ba Fateema daga jiya zuwa yau yadda ta dinga masa ya mugun tsaya masa a rai.
Waje ya sama ya zauna yana dafe kirjin sa da yaji yana barazanar tsagewa dan yadda yake tunani da saka damuwa har zafi yake masa.
Ido ya runtse yana mai yin salati a fili tare da cije bakin sa.
“Allah kai ka dauran son ta Allah Allah ya bani yadda zanyi. Allah ka bani ikon cika alkawarin da na dauka ka bani hakuri da juriya akan wannan al amarin da nake shirin aikatawa. Ya Allah ka bani dangana ka bani karfin gwiwa akan wannan alamarin.”
Ya fada yana rike kan sa da yaji yana barazanar tarwatsewa dan yadda yake masa ciwo. Hawaye ne ke zubowa a idon sa kamar famfo akan Fateema ba abinda ba zai iya ba.
Ya son ya zauna da Fateema ya bata gata da duk kulawar da zata bukata amman hakan ba mai yiyuwa bane. Wayar sa ya janyo dan zuciyar sa na fada masa ya kira Suraiyya ya kara tabbatar da abinda yake ji a gun ta.
Suraiyya na zaune taga kiran Fu’ad gaban tane ya fadi dan ita bata sa abinda zata fada masa ba ma. Sai da ta katse ta ya kuma kira sannan ta dauka da sallama a bakin ta.
“Assalamu Alaikum!”
“wa’alaikum salam. Suraiyya ya gida yasu Mama?”
Ya fada. Daga muryar sa kadai ta gane yana cikin tashin hankali dan haka tai karfin halin danne damuwar ta tace
“Alhamdulilah ya yar uwa ta?”
“Tana lafiya.”
“Baka da lafiya ne naji muryar ka haka?”
“A’ah ina son ki fadan me Fateema tace yana damun ta.”
“Uhmm tace ba komai fa kawai kewar gida ke sata kuka.”
STORY CONTINUES BELOW
Murmushi yayi me ciwo yace
“Ni kuma sai naga kamar bata so nane.”
“Haba dai ka bar fadar haka kaima shaida ne akan soyayyar da Fateema take maka wallahi Fateema na son ka ko akwai abinda BC ta fada maka ne?”
“No kawai karantar ta nayi ne “
“Ka kwantar da hankalin ka ba haka bane. Fateema na son ka.”
Murmushi yayi mai ciwo yace
“Shikenan nagode sai anjima.”
“Aha nagode.”
Ya kashe wayar yana mai zuba tagumi. Wato Suraiyya ba zata iya fada masa gaskiya ba kenan.
*
Mikewa yayi ya nufi office din manager dan daman suna son su tura shinyayi wani course a can kasar waje dama ya bari in yai aure ne su tafi da Fateema to tinda haka ne yanzu lokaci yayi da zai tafi bai sani ba ko in yai nisa da ita zai rage jin damuwa a ransa duk da yasan da wuya hakan.
Yana zuwa Manager ya tarbe shi nan ya fada masa bukatar sa ya amshe shi hannu bibbiyu yace kuma daman shi kawai ake jira dan haka ya jira su ya zama kuma cikin shiri a koda yaushe za a yi neman sa. Haka ya mike ya dawo Office ya kwanta dan ya kasa yin komai.
Ranar a kwance ya yini da tunanin mafita kala kala ba abinda ke fitar dashi daga office din sai sallah. Har akai la’asar sanna ya wuce gidan su.
Hajiyar su na falo ya shiga da sallama. Tin da ya shiga tabishi da kallo dan daga muryar sa ya nuna akwai damuwa a tare dashi.
Tana zaune akan kujera wanna yasa ya nemi kasa ya zauna ya tankwashe kafar sa. Sannan yai kasa da kansa. Da kallo take binsa. Domin Fu’ad ba dai hakuri da biyayya ba.
“Ina yini Hajiya?”
Ya fada kan sa a kasa.
“Lafiya Alhamdulilah! Kana lafiya ya Fateeman?”
“Tana lafiya.”
Wayar sa ce ta dau kara wannan yasa ya zaro a aljihun sa. *My* shine abinda ya bayyana akan scrreen din wayar wannan yasa ya gane Fateema ce ke kira.
“Hajiya zan dau waya.”
“Ba komai.”
Receiving ya danna ya kara a kunnen sa.
*Assalamu Alaikum My ya aikin”
“Wa’alaikum salam! Alhamdulillah gani a gun Hajiya.”
“Kai My amman kasan ina son naje na gaida Hajiya ko?”
“Kiyi hakuri zan kawo ki ai.”
“Uhmm bani ita mu gaisa.”
Da murmushi akan fuskar sa ya mikawa Hajiya wayar. Amsa tayi.
Nan suka gaisa daga nan Hajiya ta hau tambayar ta ya gida. Ganin hirar tasu bazata kare bane yasa ya mike yayi bangaren kishiyar Hajiyar sa.
Tana zaune a falo ya samevta. Nan suka zauna itama tambayar iyali tai masa. Sun jima suna hira dan kiran sallah magariba ne yasa yayi alwala ya tafi yin sallah.
A waje ma bayan yai sallah da yan unguwar suka tsaya suka gaisa sai bakwai da rabi ya koma gun Hajiyarsa. Yana zama tace
“A’ah ka tashi ka tafi ka barta ita kadai a gida.”
“To Hajiya amman ai bamuyi hira ba.”
“Wata rana mayi.”
Fuska ya marairaice. Tace
“Tashi kaje kaji Allah maka albarka. Ina fatan ba wata matsala dai ko?”
“Babu.”
“To a gaishe ta.”
Ta mika masa waya yai mata sallama ya fita yaiwa Hijayrar cikin gida itama sallama ya tafi.
************************************************************************************************************************************
Haka aka dinga hawan sallah har na kwana hudu a ciki anyi hutun kwanan biyu. Shi kan sa Alyu da yake ya jima baiyi sallah a gida ba yaji dadin sallah bama in suna zaune da yan uwan sa duk da bai fiya magana ba sai dai yana jn hirarrakin su.
Suma a gun su sunga dan canji daga wajen sa. Kuma sun ji dadi kasancewar sa a tare dasu dan da dane ko hawa bazai ba.
*
Bayan anyi hawan karshe sai kuma zaman fada na barka da sallah wanda Mai martaba da Iyalan sa zasu zauna a fada ana zuwa ana musu barka da sallah su kuma a lokacin zasu na alherai dan kudi da kayan sawa kala kala.
STORY CONTINUES BELOW
Wanda tin safe ake irin wannan zaman har magariba. Kowa yazo yaga Aliyu sai yai mamaki. Kuma Aliyu ba dai kyauta ba dan ba karamar kyauta in ya tashi bayar wa yake ba tare da yasan nawa a diba ba.
A irin wannan lokacin fadawa da bayin gidan sarki ba karamin alheri suke samuba dan kowa murna yake da sallah da azumi dan ko azumi kayan abncin da ake basu mai yawa.
*
Bayan sun yi magariba da isha”i ne kowa ya shga dan ya watsa ruwa sannan suja wuce gun mai martaba dan cin abincin dare. Daga nan kuma kowa ya koma makwancin sa.
A washe gari kuma mai martaba da iyalan sa ne suka hadh dan tare ake yini aci abincn rana da na dare a tare. Wanda kowa ka gani a matan Ya’yan yayo abinda yasan Mai martaba da Fulani suke so na kayan abinci da motsa baki.
Kowa da katon basket din sa yake zuwa, banda Hajara da ba ta zo da komai ba kuma su Mai martaba basu nuna komai ba amman sunji dadin abinda surukan nasu sukai msu.
Haka aka dnga hira a tare ma ake sallah. A wannan lokacin ne suke kara shakuwa da sada zumunci. Kuma da dadare bayan an gama cin abinci ma martaba kan yuwa kowa kyauta mai yawa da daraja dan a lokacin ne zai bawa ko wacce suruka kujerar makka guda biyar ko sama da haka ta dan iyeyen ta da wanda taga ya dace sannan ya basu kudi da kaya masu yawa
Haka Mamah ma take musu kyauta mai yawa kowa yai ta godiya hadi da murna. A haka zasu tafi.
*
Washe gari Aliyu shi ya fara shryawa dan Abuja zai wuce suna da meeting da gwamnoni kuma aranar yake son ya koma garin sa domin kuwa hakurin sa ya kare akan Aisha in ya dada kwana bai ganta ba zai iya shiga wani hali.
Domin kuwa shi kadai yasan a halin da yake ciki dauriyya da karfin hali kawai yake yi. Amman jin sa yake kamar bai da lafiya dan yadda zuciyar sa ke damun sa da son ganin ta ga kewarta da yake ji.
Lokacin da ya fito cikin shirin sa. Yayen sa da kakken sa duk ji suke kamar suyi kuka dan zasu yi kewar sa. Bayan yai wa iyayen sallama yazo ya rumgume duk yayyen nasa da kannen nasa. Maryama kuwa har da hawaye sannann ya shige mota suna dago masa hannu daga matan Yayen nasa har kannen sa. Ya’yan nasu kuwa suna kuka suna daga masa hannu. Duk sai sukanji ba dadi.
Bayan tafiyar sa suma komawa ciki sukai suka cigaba da shiryawa suma wajen karfe biyu kowa ua fito yayi sallama da Su mai martba sannan suka tafi gidan sai yai musu ba dadi.
Hajara kuwa saboda suna shirya abu ita da su sha’awa sai da ta kara kwana daya sannan ta koma gidan gwamnati. Komawar ta kuma taji wani mummuna labari akan wadan da Aliyu ya sauke da kuma kudin da yasaka su maida. A ciki akwai wani Lukman tare suke duk harkalar su da Hajara na kudi su aika da kwangila a basu su cinye kudi.
Ya rufawa Hajara asiri a lokacin ne don yana son ya cimma wani burin sa a gaba bata jima da komawa ba ya aika yana son ganinnta dan sai da ya san Aliyu baya nan sannan ya samu damar shigowa cikin gidan gwamnatin.
A falon ta na saukar baki ta sauke shi. Lokacin da ta ganshi tayi mamaki dan yai baki ba gayun sa na da. Zama tayi tana kallon sa da mamaki tace
“Alhaji Lukaman kai ne ka koma haka me ya faru?”
Wani murmushin mugunta ya saki yace
“Hajjiya ai labari ne mai tsawo.”
Zama ta gyara tace
“Ina jin ka.”
Komai da ya faru ya bata labari sannan ya daura da fafin
“A dalilin haka matata ta sa na sake dan ba zata iya zama dani ba aiki ba. Na rasa aiki na yanzu ban da komai.”
Jikin Hajara ne ya fara rawa. Hajara tace
“To yanzu me kake so in maka?”
“Kinsan dai na rufa miki asiri domin duk abinda aka kamani ina yi har dake a ciki in da na fadawa Mai girma gwamna na tabbata ba abinda ba zai hana kema ya hukunta ki ba ko?”
Kai ta gyada cikin tsoro.
Yace
“Dole ne yanzu kina ragen zafi na farko kenan sai na biyu dole ne duk lokacin da bani da kudi ke zaki bani ko kuma wallahi ina da detail na komai in nunawa Mai girma gwamna.”
Wayar sa ya xaro ya nuna mata duk wasu daga cikin harkalolin da suka dinga gudanarwa tare. Sosai Hajara ta kuma shiga tashin hankali dan tasan Aliyu zai iya cewa zai rabuwa da ita in kuwa ya rabu da ita wa ta kama. Tana samu tana rufawa kan ta da iyayen ta asiri.
Ana girmama ta ana son ta duk ta dalilin Auren Aliyu da take. Shin yau in ba Aliyu duk daina mata za ai lallai gwara ta yadda da abinda Alhaji Lukman yazo mata dashi dan ta cigaba da rufawa kan ta asiri tin da dai Aliyu ba sani zai ba. A boye komai xai faru.
Dagowa tayi ta kalli Alhaji Lukaman tace
“Na yadda amman kuma bana son ana wayan ganin gilmawar ka. In da hali ka fadan a inda zan na zuwa ina samun ka saura communication din manayi ta waya.”
Kallon Hajara yake da wani irin yanayi. Ba tin yau ba yake son Hajara. ashe dai da rabon samun Hajara. A farko ya so ya tona mata asiri amman sai yai tunanin rufa nata ko dan gaba ai kam aikin sa na kyau. A haka kuma sai samu damar da zai hukunta Aliyu tinda ya rabashi da aiki sa da matar sa to shi da rayuwar sa zai rabashi.