WA NAKE SO CHAPTER 9
Alhamdulilah. Sosai na samu kulawa daga gun Momy da likitoci har da nurses da yan uwa na domin kuwa sun yiwa su Momy magana kan kada ana bari na ni kadai dan zan na saka abu a rai na wanda zai kara dagula lafiya ta.+
Wannan yasa ma suka ce a karo mai kula dani dan haka da Momy da Suraiyya muke kwana. Sam basa bari na a kadaici da zanyi wan tunani kuma da safe haka Baba Uwani zata zo da yan gida. bayan sun gamai min allurai sukai sallameni bayan sun kara jawa su Momy kunne akan kulawa dani.
Gidan mu Suraiyya ta dawo haka Yaa Kamal ma dan haka sam basa bari na ni kadai. Kullum tare muke yini suyi ta saka ni dariya da labarai. Dan haka sam ban kawo Fu’ad sai naje bacci ko na kwanta nai ta mafarkan sa. Bana kuka a gaban kowa dan da sun ga mood dina ya canja a lokacin duk hankalin su zai tashi suyi ta tambaya ta menene.
Kwana na biyar da sallama wanda a lokacin satin Fu’ad biyu da tafiya kenan. Bayan na fito a wanka Momy ta shigo dakin. Mai na dauko ina shafawa tana kallo na tace
“Ashe wanka kike naji ki kin jima.”
“Eh wanka nayi.”
Kallo na ta tsaya yi dan duk ido na yayi jajir alamar naji kuka haka nan murya ta har ta dashe dan haka ta zauna a gefen gado tana kallo na har na gama na saka riga da siket na atamfa na saka hula.
Kallon ta nayi ganin yadda ta zuba min idanu. Zama nayi nace
“Lafiya Momy?”
“Fateema wai kwana nawa Fu’ad yace zai yi ne?”
Take naji zuciya ta ta buga dan har sai da tari ya kubce min nai shiru tace
“Kuna ma waya kuwa? Ko akwai wata matsala ne?”
Kuka na fashe dashi na fada jikin ta ina girgiza kai na. Baya na ta hau bubbugawa tana fadin
“To ai ba kuka nace ki min ba. Akwai wata matsala ne.”
Kirji nane ya kulle wanna yasa na dafe da hannu na ido na na zubar da hawaye ga tari da nake duk abin sai ya zamar min goma da ashirin nan Momy ta daukon ruwa amman tarin yaki tsayawa sai da kyar ya tsaya wannan yasa ta mikon na amsa na sha sannan na koma na kwanta ina lumshe ido hannu na daya dafe da kirji na.
Munyi minti talatin sannan na mike zaune kirji na yai min nauyi sosai. Kallon Momy nayi da take kallo na cike da tausayawa tace
“Kinsha magani kuwa?”
Kai na gyada mata. Hannuna takama tana fadin
“Sannu!”
Kai na gyada nace
“Momy Fu’ad fa ya sauwaken auren sa gaba daya”
Da sauri momy ta saki hannu na tana zaro ido hannu ta dafe da kirji tace
“Innalillahi wainna illahir rajiun. Yaushe?”
“Da zai tafi ya ban takadar sai da na kwana biyu sannan na karanta shine abinda yasa na shiga halin da na shiga.”
Na karasa maganar hawaye na zubo min.
“Naga takardar?”
Momy ta fada. Jaka ta na dauko dan bayan na dawo gida naga takardar a ciki abinda ya hanani taba jakar ma kenan na ajiye ta.
Momy na mikawa na koma na kwanta. Karantawa Momy ta fara tana matsar hawaye tana kai inda ya saken ta saki takardar tana aika min da wani irin kallo. Mikewa nayi ina kallon ta a tsorace kan nace wani abu ta mike ta fice min a dakin
STORY CONTINUES BELOW
“Me kenan?”
Na tambayi kai na. Ko da yake nasan dakyar Momy taga laifin Fu’ad nawa zata gani shin to ni me nayi? Kuka na fashe dashi wanda yasa numfashi na daukewa cak dai dai shigowar Suraiyya kenan ta ganni ina dafe da zuciya ta ga numfashi da nake kokarin jan sa.
Falo ta fita a tana fadin
“Momy jikin Fateema ne ya tashi.”
Momy tace
“Me zan mata to?”
Ta mike tayi sama. Yaa Kamal da suraiyya suka kalli juna sai kuma ya mike a guje yayi dakin Suraiyya ce tabi bayan sa a guje. A yadda Suraiyya ta barni a haka ta dawo ta same ni dan haka Yaa Kamal ya dauken muka fice a mota sai asibiti muna zuwa likita ya amshe ni.
Allura yai min sannan ya sakan oxygen sai a lokacin numfashi na ya dai dai ta. Nan likita ya fito ya tafi office. Yaa Kamal da Suraiyya suka bi bayan sa dan ya barni da nurses.
Suna shiga office din ya zauna yai rubuce rubuce a file dina sannan ya ajiye ya dago yana kallon Yaa kamal yace
“Garin ya haka ta faru?”
.
“Me fa?”
Yaa Kamal ya tambaya.
“Jinin ta yai mugun hawa. sannan as sign din ta ya nuna kamar zuciyar ta ta kamu da ciwo. Daman har kwana kin nan da kukai bata cire damuwa bakwa debe mata kewa kamar yadda muka ce.”
Shiru Kamal yayi dan shi ya rasa mema zai ce.
Doctor yace
“To gaskiya sai mun rike ta dan conditon din da take ciki tana cikin hatsari.”
Nan ya rubuata abubuwan da ake bukata ya bawa Kamal sannan suka mike suka fito.
Dakin da nake suka shigo suka zuba min ido suna mai tausayi na ganin duk yadda na kare kamar bani ba. Sun jima a haka sannan Yaa Kamal yq kalli Suraiyya yace
“Bari naje na siyo na dawo.”
“Toh!”
Ta fada tana zama a kan kujera ta zuba tagumi
Da sauri ya fita ya tafi ya siyo komai ya dawo ya ajiye yace
“Bari yaje ya sanar da Momy.”
Gida Yaa Kamal ya koma gida. A kitchen ya samu Momy tana irrkin dare dan haka ya karasa jiki a sanyaye. Kallon sa tayi tace
“Ya akai Kamal?”
“Momy jikin Fateema ne ya tashi.”
“Allah sauwake.”
Ta fada tana cigaba da aikin ta.
“Momy an basu gado ne fa.”
“To ai shine nace Allah bata lafiya.”
Kallon Momy ya tsaya yace
“To anjima in kin gama abinci na kai ki ne?”
“Ka kai ni ina Kamalu? Ba inda zani Allah ya sauwake ai ita ta daurawa kanta.”
“Anya kuwa Momy me yake faruwa ne. Fateema fa nace miki bata da lafiya har an bata gado.”
“Kamal na jika sarai amman ba inda zani Allah sauwake.”
Kallon Momy ya tsaya can yace
“Doctor yace jinin ta yafi wancan hawa sannan zuciyar ta ta kamu da ciwo Momy wai me yake damun tane?”
Duk da Momy hankalin ta ya tashi ta shiga firgici jin halin da nake ciki amman sai cewa tayi
“Allah sauwake.”
Yaa Kamal yace
“Momy wai me yakre faruwa ne?”
“Ka tambaye ta ta fada maka.”
Shiru yayi can yace
“Bari na koma amman gaskiya Momy anjima zan dawo na dauke ki.”
“Kamal kasan Allah ba inda zani.”
Kallon mamaki ya tsaya yanawa Momy ta juya ta bar shi ta cigaba da aikin ta. Ya jiima a kitchen din sannan ya juya ya fita jiki a sanyaye.
Asibitin ya dawo har lokacin ina bacci Suraiyya tace
“Ina Momyn?”
“Momy bata jin dadi itama gaskiya ba zata samu zuwa yau ba.”
“Allah sauwake.”
“Amin!”
Ya fada yana kallo na cikin tausayawa. Can yace
“Wai ina mijin ta ne?”
“Yayi tafiya ne.”
Suraiyya ta bashi amsa tana kallo na.
STORY CONTINUES BELOW
“Amman ya kamata dagin mijin ta su san a halin da take ciki ko?”
“Gaskiya dai.”
Mikewa yayi yana kallon Suraiyya yace
“An kira sallah bari naje nayi daga can zan amso muku kayan ku ko?”
“Toh angode.”
Ya fita. Bayan yai sallah yaje ya debo musi kayan su sannan ya biya ta gida ya amso musu abinci ya dawo asibitin.
Nan suka zauna bai tafi ba sai karfe sha daya sannan ya tafi.
*
Da dare haka na tashi nai ta kuka da kyar Suraiyya ta lalashe ni na kwanta. Nayi mamakin rashin zuwan Momy amman nai shiru.
Washe gari da sassafe Yaa Kamal yazo ya taho mana da abinci. Tea kadai nasha nurses suka shigo suka ban magani sannan sukai min allurai na koma bacci.
Wannan jinyar daga Yaa Kamal sai Suraiyya su ke yini a kai na. Yaa Kamal sai wajen sha daya yake tafiya gida. Baba Uwnai kuwa kullim zata zo da Maman Suraiyya suna kawo mana abinci.
Kwana na uku likita ya sallame bayan ya kara bani dokoki ya bawa su Yaa Kamal ma.
Muna komawa gida na shige falo sai dai naga Momy bata nan dan haka da sauri na na karasa dakin ta.
Tana zaune ta zuba tagumi tana jin sallamata ta dago tana kallo na. Tausayi na ne ya kamata dan na rame sosai wannan yasa tai saurin dauke idonta daga kallona.
Karasowa nayi na zube a kasa ina fadin
“Momy dan Allah ki yafe min tayaya zan ji dadin rayuwa bake ba Yaa Fauwaz ba Fu’ad. Dan Allah Momy ki yafe min.”
Na fada ina mai sakin kuka. Bata kallen ba tace
“Me kika yiwa Fu’ad har ya sauwake miki?”
“Wallahi Momy ba abinda nai masa ni ban san…..”
“Rufe min baki. Tayaya zakice baki san me kikai masa ehee?”
Kuka nake ina girgiza kai nace
“Wallahi Momy ban san me nayi masa ba.”
“Zaki daina fadan baki san me kikai masa ba ko sai na dauke ki da mari shahsahar banza da wofi. Kinje kina masa rashin hankali ko? Maganar Fauwaz kike masa ko?”
Kai nake girgiza ina hawaye nace
“A’ah Momy.”
“Ba zaki fada min me kike masa ba. Shin daman Fateema bakya son Fu’ad kika bari kika aure shi? Wannan ai cuta ce.”
Kai nake girgiza ina mai cigaba da kuka.
Momy tace
“Allah ba zai barki ba tinda kika cuce shi. Meyasa kika bari kika aure shi bakya son sa? Tin farko ban fada miki ki auri wanda kike so ba domin anan ne zaki samun zaman lafiya da kwanciyyar hankalim Shin na nuna miki wanda nake so a cikin mane man ki?”
Kai nake girgiza wa kai na na sara min ga kukan da nake ga kirji na da yai min zafi da nauyi.
“Ban nuna miki wanda nake so ba dan kar ki je ki min biyayya ke kuma bakya son sa. Amman dan me kika yaudari Fu’ad din. To wallahi Fateema duk da Fauwaz ‘da nane na fison Fu’ad domin Fu’ad masoyin kine amman dan uban ki ki fadan dan me kika aure sa dan ki broken heart 💔 nashi ehee?”
Kai na girgiza nace
“Wallahi A’ah ina son Fu’ad son sa a jini na yake. Ana fada in dai da shakuwa sam ba a rabuwa sai dai a kara jituwa. Wallahi Momy ban taba son wani kamar Fu’ad ba. Dan Allah Momy ki yafen ki kira Fu’ad ki fada masa ina son sa dan Allah wallaho mutuwa zanyi in ba Fu’ad zuciya ta zata tarwatse ni ina son sa.”
Wani kallo Momy ke jefa min tace
“Basai naje na nemo mikin shi ba shasha kada ki manta ko da Fu’ad zai dawo a yanzu ba aure tsakanin ku. Kuma kin cuci yaron nan wallahi ni kai na kunya nake. Nasan Fu’ad nasan hakurin sa tin da yai haka kin kai shi bango. Kuma daga jin statement din sa akan farin cikin ki ya sake ki. Dan uban ki menene farin cikin naki da yasa ya sake ki dan kije gare shi. Kada kice min Fauwaz ne?”
Kai na ke girgizawa dan na kasa magana ma na kama kafar ta ina jijjiga wa da kyar na iya cewa
“Momy ki yafe min. Ki nemon Fu’ad ya yafen. Momy dan Allah ki yafen ko naji wani sanyi a rai na.”
“Fateema zan yafe miki amman sai kin fada min yadda zaman ku ya kasance da Fu’ad in kika boyen wani abu ke da Allahn ki.”
Kuka nake ina gyada kai.
Tace
“Ina sauraron ki.”
Cikin kuka na labarta mata komai. Ina kai aya tace
“Wato ke tunanin ki ina Fauwaz yake ko kinyi aure kin barshi ko? Da yake shi cewa yayi ba zai aure ba ke zai zauna jira ko? Fateema wai me yake damun ki da zuciyar ki ne? Yanzu akan Fauwaz kika kashe auren ki?”
Kai na girgiza nace
“Wallahi A’ah Momy.”
“Gashi nan kuwa duk wanda aka bawa labarin nan ai yasan dan me Fu’ad ya sake ki. Shima ya fada ba zai tauye miki farin cikin ki ba zai baki farin cikin ki. To ciwon uban kike dan ya sake ki.”
“Momy wallahi ina son Fu’ad wallahi nafi son sa akan Yaa Fauwaz. Halin da nake ciki na rashin sa ban shiga a lokacin da na rasa Yaa Fauwaz ba. Dan Allah Momy ki yafen ki daina fushi dani.”
Kai Momy ta dafe can ta dago tace
“Da auren ki kike tunanin wani can.”
Ji take kamar ta rufe ni da duka dan dai ban da lafiya ne amman nasan da tini na sha duka a gun Momf. Tagumi ta zuva nace
“Momy ii yafen dan Allah.”
“Ki nemi tuba a gun Allah da wanda kika zalunta bahan kinsan bakya son sa kika aure shi.”
“Wallahi Momy ina son sa.”
Na fada ina kuka. Momy ta dauke tagumi hadi da sauke ajiyar zuciya tace
“Wallahi kinyi babban rashi. Allah ya kyauta.”
“Momy dan Allah ki yafe min ki daina fushi dani.”
“Fateema ya zan miki ehee? Ya zanyi dake amman a gaskiya kin batan rai baki taba batan rai kamar wannan ba.”
Kuka nake ina dafe kirji wannan yasa tace
” tashi kije. Allah ya yafe mana gaba daya.”
Kin mikewa nayi haka xauna dafe da kirji har akai kira magariba Momy ta mike ta shiga bandaki tayo alwala ta zo zata tada sallah gani na a zuane a wajen har lokacin tace
“Tashi kije kiyi sallah!”
Mikewa nayi duk da bana yi na nufi kofar fita adakin. Da kallo ta bini.
Aliyu kuwa lokacin da yaga sakon Aisha murmushi kawai yayi a ransa yace
“Da sannu zaki gane manufata Aysher.”
Sai kuma ya dago yana kallon agogo dan ya kosa ya tafi gida yaje yaga Aishan sa. Abinda ya fada har ya sa yayi murmushi ya maimaita kalmar a fili
“Aysher ta!”
Gashin kansa mai taushi ya shafa yace
“Allah ya bani ke Aysher nah.”
Wani murmushin ya kara yana fadin
“Yau ace gani an daura aure na da Aysher shin ya zanji a zuciya ta?”
Baki ya dan cije yana murmushi yace
“I will show u my love and care u will never cry i will do all u want. Zan mai dake sarauniyyar zuciya ta. Sai ko wacce mace tayi sha’awar ki tace ina ma ita ce ke.”
Ido ya lumshe yana fadin
“Yaa Allah see me through”
“Shin in kuma halaiyar ta irin ta Hajara ce fa.”
Zuciyar sa ta tambaye sa. Kai ya girgiza yace
“Yaa Allah nima ka bani wacce zan ji dadi da ita nasan nayi aure. Sam yaye na ba haka matam suke ba. Even my junior brother’s wife are so care and love to their husband why my wife is different from their own. Why?”
Ya fada yana fada ya mike ya shiga ya dauro alwala. Sallah yazo yayi nafila sannan yai addu’a sosai akan lamarin. Dan har ga Allah yana cikin matsala yana bukatar kulawa amman sam matar sa bata iya ba.
Zai ce tinda yai aure bai taba cin girkin Hajara ba bai taba ganin Hajara ta gyara masa daki ba duk da yasan gidan su gidan sarauta ne suna da masu kula amman duk da haka Momy bata fasa gyarawa Mai martaba bangaren sa ba. To shi meyasa matar sa take haka. Kenan ita a gidan su bata san duk wadan nan abubuwan ba kome.
Yai mata shiru tana ganin kamar bai damu ba itama kuma bata damun ba. Kwafa yayi ya mike dan yaji ana kiran sallah ya fice ya tafi masallaci.
*
*
*
Da yamma kamar yadda ya saba bayan ya wanka ya sauya kaya zuwa kanannun kaya dan yawanci su yake sakawa in ba yana gida ko ranar jumma’a ba zai yi wuya ka ganshi da manyan kaya. Yana tafe yana tunanin abinda zai soma a wajen Aisha.
Bayan yaje ya zauna a inda suke zama. Bai jima da zama ba ta dawo daga isilamiyya. Fuskar ta dauke da murmushi ta karaso wajen sa. Shima haka. Sallama tai masa ya amsa sannan yace
“Kanwa ta?”
“Na’am Yaa AK ina yini?”
Ta dan durkusa. Murmushi dauke akan fuskar sa ya amsa. Tace
“Bari na shiga na fito.”
Kai ya gyada ya bita da kallo yana lumshe ido hade da shafa sumar kan sa. Bata jima ba ta fito cikin wata doguwar riga wacce take yar kanti multi colour ce tai mata kyau ta daura hijab din ta akan wanda yai mata kyau.
Hannun ta rike da littafin ta. Dan akwai wani aiki da take son zasuyi. Zama tayi ta mika masa littafin. Amsa yayi ya duba yai murmushi ya mika mata yace
“Ai zaki iya!”
Kai ta gyada yace
“Yi in da gyara sai nayi miki.”
Suna zaune ta fara aikin yana kallon ta yadda take rubutun ta hankali kwance bata dago ba har sai da ta gama tana dagowa suka hada ido. Murmushi ya sakar mata tai saurin dauke kan ta tana miko masa littafin. Amsa yayi yana dubawa yana gyada kai har ya gama ya rufe yace
“Da kyau Indo na.”
STORY CONTINUES BELOW
“Baki ta turo tace
“Ni bana son wannan sunan!”
Dariya yayi yace
“Ni kuma ina so.”
Baki taka turowa tace
“Nima Yaa Ali zan na fada.”
Murmushi yayi yace
“To me zance miki Sweety ko Honey!”
Ido ta zaro tana bin sa da wani kallo da ya kashe masa jiki. Murmushi yayi yace
“Wanne a ciki?”
“Uhmm!”
Kawai ta fada tana dauke kanta.
“Kanwata in tambaye ki mana?”
Kai ta gyada alamar tana jin sa. Yace
“Waye saurayin ki?”
Dagowa tayi a tsorace tana kallon sa sai kuma ta dauke kai tana mai girgiza kai tace
“Ni yar karamar nan dani?”
Murmushi yayi yace
“Ai yanzu kin tashi a karama Baby dane kike karama amman yanzu kin girma graduation fa zakiyi.”
“Uhmmm!”
“To in aka ce miki a cikin mutanen da kike rayuwa dasu ki zabi daya ki aura wa zaki aura.”
Shiru tayi tana wasa da yatsun hannun ta dogaye. Kallon ta yake yana murmushi can yace
“Me kika fi so a rayuwa Aysher?”
Ido ta lumshe tana mai budewa tace
“Naga ina taimakon mara sa shi naga na zama mai kwatar wa talakawa yanci domin a yanzu talaka bashi da yanci danne masa ake yi.”
Kai ya gyada yace
“In zaki tafi university wane course zaki yi.”
“Na fison na zama likita but ance karatun bana talakawa bane irin mu. In ban samu na zama likita ba zan so na zama lecturer.”
Murmushi yayi yace
“Ki zabi duk kasar da kike so ni nai miki alkawarin kai ki kiyi karatun likitancin ki.”
Kallon sa ta tsaya yi sai kuma ta girgiza kai tace
“Ba zan daura maka nauyi na ba ga gidan ka da iyalan ka.”
“Kina son ki zama likitan?”
Ya fada yana zuba mata ido. Kan ta a kasa ta dago tana kallon sa.
Gira ya dage mata da sauri ta dauke kanta dan in tana kallon idon sa wani irin abu take ji. Shi kansa yana mamakin kan sa na yadda baya gajiya da kallon Aisha bayan a da bai tsayawa kallon ko wacce mace.
Aisha ma mamakin kan ta take ada sai ta kure shi da ido amman kalli a yanzu wai kallon sa ma sai a sace take yi.
“Kina so?”
Ya katse mata tunanin da take. Kai kadai ta gyada masa yace
“Me kike ganin zai hanaki karatun a yanzu in na dau nauyin ki.”
“Baba zai iya cewa zai min aure.”
Kallon ta yake yace
“Da gaske?”
Kai ta gyada yace
“In ya barki fa.”
“Zan fi kowa farin ciki da jin dadi.”
“Insha Allah Aysher zaki zama likita da izinin manzon Allah abinda nake so dake kawai ki tsaya kiyi karatu kinji?”
Kai ta gyada yace
“Dat gud Baby.”
Dagowa tayi tana kallon sa dai dai lokacin da shima yake kallon ta wannan yasa idanun su suka sarke cikin na juna.
Ita ta fara karfin halin janye nata tana wasa da yatsun hannayen nata. Kallon ta yake yana murmushi farin ciki kwance a cikin ransa da kasan zuciyar sa.
Itama wata nutsuwa da farin ciki take ji wanda bata ta jin su ba irin haka. Kiran sallah da taji anayi yasa ta mike ta kawo masa ruwa. Alwala yayi tana nan a tsaye ya kanasa. Tana kallon sa dan komai yake burge ta yake yi har ya gama ya dago sannan tai saurin dauke kan ta. Murnushi yayi yace
“Wannan kunyar kuma wai yaushe aka samota.”
Baya ta juya masa ya karaso inda take yana leken fuskar ta sannan yace
“To ni dai sai munyi waya ko?”
Kai ta gyada ta yi ciki yace
“Butar fa”
STORY CONTINUES BELOW
Juyowa tayi kanta a kasa ta zo ta dauka yace
“Aysher kenan.”
Tana dauka tayi ciki da sauri kamar wacce ake hankadata ta shige. Kai ya girgiza ya juya ya nufi masallaci yana mai sakin fara’a.
*
**
***
****
*****
******
*******
Washe gari da safe bayan nai wanka na fito. Anan falo na samu Momy. Har kasa na durkusa na ce
“Ina kwana?”
“Lafiya ya jikin?”
Ta fada tana mikewa ta bar wajen.
Suraiyya ce ta fito a kitchen hannun ta rike da warmer ta nufi dining gani na durkushe a kasa tayo guna tana fadin
“Ya jikin?”
Dan murmushi na saki nace
“Da sauki.”
“Allah kara sauki. Taso kici abinci kisha magani.”
Mikewa nayi na nufi dining din dai dai lokacin da Baba Uwani ta fito kenan.
Momy ce ta karaso tayi serving Baba Uwani sannan ta bar wajen. Farkon ciwo na da aka sallamo mu ita ke min komai amman yanzu ko kallo na bata yi. Da ido na bita.
Suraiyya ta matso ta dibar min tace
“Maza kici kizo kisha magani zan je rabon kati ko zaki rakani?”
Kai na girgiza kawai. Abinci kadan naci ta ban magani nasha sannan na koma daki na. Kwanciyya nayi ina zubar da hawaye domin wata irin kewar Fu’ad nake ji.
Ina kwance tazo ta fita bayan tace
“Me zan taho miki dashi?”
“Komai ma.”
“Ro shikenan sai na dawo.”
“Nagode”
Na fada ta fice.
Ina kwance ina tunanin Fu’ad Ba lokacin da na tuna sai satin farko na auren mu lokacin da safe ina ta bacci na cikin kwanciyyar hankali har karfe tara ban farka ba. Shi yai mana koma na gidan shara wanke wanke sannan ya hada mana break. Bayan ya gama ya shiga yai wanka ya fito cikin wata shadda ash kala wacce dinkin yai masa kyau ya amshi jikin sa. Yai wanka da ruwan turare.
Dakin da nake ya taho gani na har lokacin ina bacci yasa ya dagoni a hankali ya daura a jikin sa. Hannun sa ya zura cikin gashin kai na yana susa min a hankali. Cikin bacci nake jin abinda yake min dan haka a hankali na bude ido na. Fuskar na gani mai kyau da ita. Tai kyau tana sheki. Gashin kan sa akwance luf luf dashi. Sai girar sa da take cire da gashi mai yawa kuma a tsari kamar dasa shi akai. Idanun sa manya wadan da suke a dan lungu kadan masu dauke da gashin ido gazar gazar. Sai hancin sa dogo mai kyau siriri bakin sa madaidaici mai dauke da gashin saman baki da gemu madaidaici.
Gaskiya ba karya ba Fu’ad yayi duk wacce ta samu Fu’ad ta godewa Allah domin kuwa ta gama dace a kyau ma kenan bare halaiya da dabi’un sa. Idon sa na kara kalla wanda ya kafe su saman fuskata yana kallo na cike da so da kauna.
Bakin sa ya matso dasu kan idanu na yai kissing dayan sannan yayiwa dayan. Bakin sa ya bude a hankali yace
“Amarya ta bacci ya isa haka ko?”
Murmushi na sakar masa na dauki hannu na na shafa masa fuskar sa dan yai min kyau sosai. A hankali nace
“Kayi Kyau My. Allah ya bani ya’ya masu kyan ka.”
Fuska ta ya shafa yana murmushin da bai barin fuskar sa yace
“My ai kin fini kyau. Ni na fison ya’ya na suyo kamar ki.”
Ciki na ya shafa wanda ya sa tsigar jiki na ta tashi. Ido daya ya kanne min sannan yace
“I can’t wait to see u carrying my…..”
Ture masa hannun sa nayi saboda wani irin yanayi da yake min a cikin nawa. Abinda yasa bai karasa maganar tasa ba kenan. Kan gadon ya kwanta na mike na juya masa baya ina tafiya.
Kallo na ya tsaya yi nace
“Ka tashi ka fita xanyi wanka!”
Ido ya zaro yace
“In je ina? Dan bance zan miki ba ko?”
Ido nima na zaro na make kafada ban magana ba na dauki wani zumbulelen hijab dina na wuce toilet.
Dariya yayi ya mike ya hau gyara dakin kan na fito har ya share ya saka turaren wuta ina fitowa bangansa adakin ba wannan yasa na cire Hijab din nawa ya rage daga ni sai karamin towel dauri a kirjina iya kar sa cinya. Mai na fara shafawa ban aune ba sai jin hannun mutum nayi a saman kafada ta.
Sosai na tsorata har ban san lokacin da na mike a firgice ba towel din jiki na kuwa ya subce ya fadi. Da sauri na durkushe ina kuka.
Towel din ya dauko ya dago ni ina nonnokewa. Muna hada ido na harare shi shi kuma yai murmushi yace
“Ki tsaya na kalle ki mana u re now my property fa.”
Ido na zaro naji wani iri. Ganin yana kallo na yasa na kalli jiki na ina ganin jiki naga ashe ba towel din wannan yasa na fada jikin sa na rumgume shi. Hannun sa ya daura a kan kugu na. Wani irin abu naji yana taso min wannan yasa na kamkame shi ina runtsa ido na. Kuka na farai masa nan ya saken yana juyan baya yace
“Am sorry My shirya bari na fita.”
Ina ganin ya juya baya nayi kofar towel da gudu juyowa yayi yana kallo na yana dariya.
*
Dariya na fashe da ita hawaye na bin ido na. Dan tina abinda nayi wato haka na shige ba komai fa a jiki na maimako na mai da towel dina Dakin da nake na kalla sai naji ina ma ina tare da Fu’ad. Hakika zama na dashi bai cutar dani ba sai dai ko ni na cutar dashi domin kuwa sai abinda nake so yake min. Kullum cikin faranta min da sani farin ciki yake.
Yau ina Fu’ad ya shiga ya barni. Maganar sa ce ta fado min da yake fadin
“My ina son naga kin cika min gidan na da yara masu kama dake.”
Tayaya burin Fu’ad zai cika tayaya kenan bayan ya yanke dukka igiyoyin dake kai na nasa. Shin yasan cewa shine farin ciki na. Waya ta na dauka ina kara dailing number sa wacce na kira yafi sau dubu daga lokacin da na dawo gida daga asibiti zuwa yanzu.
“Ina ka tafi ka barni My ina ka tafi dan Allah kadawo wallahi ina son ka ba zan iya rayuwa ba kai ba kaine farin ciki na ka yafen My ka dawo muyi zaman mu lafiya dan Allah My.”
Abinda nake fada kenan ina kuka da juyi akan gado na.
Na jima ina kuka dan kiran sallah azhar shiyasa na mike na shiga na dauro alwala sannan na dawo na tada sallah. Na jima ina addu’a akan Allah ya zama gata na ya dawon da Fu’ad dina.Ina xaune aka bude kofar dakin a hankali na dago Yaa Kamal ne ya shigo hannun sa dauke da leda guda biyu. Zama yayi a gefen gadon ya ajiyen ledojin a gaba na yana fadin
“Ya jikin?”
“Da sauki!”
Na amsa masa ina jan ledojin na bude daya fruit ne a ciki dayar kuma Rufaidah fura da Nono ce mai sanyi. Yaa Kamal kenan kullum ya fita da abinda zai kawo min. Bama da yasan abubuwan da nake so.
Dagowa nayi ina murmushi hawaye cike a ido na. Kai ya hau girgiza min yana fadin
“Dan Allah kada kiyi kuka.”
Kai na gyada na saka hannu na na goge ido na nace
“Nagode Yaa Kamal!”
Murmushi kawai yayi. Nan na dauki daya na fara sha sannan na mika masa ledar nace
“Ka dauka!”
“No ni ke na kawowa.”
Nayi murmushi nace nagode. Naci gaba dasha.
*
Ba wanda na tuno ina shan furar nan sai Fu’ad lokacin da ya siyo min ya zauna ina sha ya zuba min ido. Dagowa nayi ina kallon sa fuskar sa dauke da murmushi na mika masa spoon din na diba na kai masa wajen bakin sa.
Kai ya dauke na dan bata fuska nima na ajiye robar. Kallo na yayi ya dagen gira alamar menene? Baki na turo nace
“Nima ba zan sha ba in ba zaka sha.”
“Haba My ni na koshi ne gasu nan duk naki ne.”
Ya fada yana turon ledar dake ajiye a kasa. Nace
“Uhmm ni naji. In ba zaka sha ba nima am ok!”
“Am sorry bani.”
Ya fada yana bude baki. da sauri na dauki spoon din na diba na kai bakin sa. Amsa yayi ya lumshe ido yana gyada kai yace
“Kai ashe haka take da dadi.”
Murmushi nayi na ce
“Ko?”
Kai ya gyada yace
“Eh!”
Sannan ya amsa yana bani nima ina na bashi a haka muka shanye roba daya amman duk ya batan saman baki na. wannan yasa ya janyo ni ya sa harshen sa yana lashen baki na. Wani abu naji yana taso min abinda yasa nai saurin lumshe ido na kenan.
*
Ido na, na bude naga Yaa Kamal zaune yana danne dannen wayar sa. Dagowa yayi yana kallo na sai ya zare ido yana fadin
“Kuka kuma!”
Ban san kukan nake ba sai da ya fada na shafa fuska ta ai kam na shafo hawaye wannan yasa na hade kai na da gwiwa ina sakin kuka mai sauti. Kallo na Yaa Kamal yake jiki a sanyaye yace
“Fateema wai me yake faruwa ne ki fada min dan Allah kinji. Menene na kukan ehee? Ko wani abu kike bukata ne?”
Kai na hau girgiza masa. Yace
“Is Alright daina kukan dan Allah kinga doctor yace ki daina saka damuwa ko?”
Kaina gyada. Yace
“To daina kukan kinji.”
Fuskata na hau gogewa. Sai da na gama yace
“Yauwah ko ke fa. Maza shanye a barki. Yanzu zanje na dawo me kike son na taho miki dashi.”
Kai na girgiza nace
“Nagode.”
Mikewa yayi yace
“Alright zan taho da Suraiyya daga nan.”
Nai murmushi nace
“Kundai kusa ku amarce ai a huta.”
Yai dariya ya fice. Ido na lumshe tuna in Fu’ad zai fita ya ta tambayata da me zai kawon kenan duk fitar da zai bai fita haka sai ya kawon abun matsa baki.
STORY CONTINUES BELOW
Hawayen da ya biyon fuska na goge ina mikewa na koma kan gado na zauna ina zuba tagumi.
“Why will u leave me My? After all u know i love u. I can’t do without u. U re my heartbeat my love, my happiness. Nafi son ka akan Yaa Fauwaz meyasa ka tafi ka barni? Meyasa ka yanke hukunci ba tare da ka tambayen ba? Why Fu’ad? Why?”
Na fada ina kifewa akan gado ina kuka mai taban zuciya. Wanda ina kukan naji zuciya ta na zafi. Na jima ina kwance zuciya ta in banda zafi ba abinda take min. Na jima a haka sannan na mike dan ana kiran sallah la’asar nayi cikin bandaki na dauro alwala.
*
Yaa Kamal na fita ya nufi gidan su Fu’ad. A Compound ya tsaya yasa a fadawa Hajiyar sa. Hajiyar sa na fitowa taga Yayan Fateema tace
“Au kaine kuma aka barka a waje taho mu shiga.”
Tayi ciki yabi bayan ta. A falo ta zauna ya zauna a kasa kan sa a kasa yace
“Ina yini?”
“Lafiya lou ya kuke ya gida?”
Ta amsa cikin sakin fuska sannan ta kawo masa ruwa da lemo. Kan sa a kasa bayan sun gama gaishe gaishen yace
“Hajiya daman Fateema ce bata da lafiya tin tafiyar Fu’ad. Sau biyu muna kwanciyya a asibiti naga ba Fu’ad ba ku ko baku sani bane? Abinda da ya fi damuna yawan damuwar da take ciki Hajiya shine nace ko lafiya?”
Shiru Hajiya tayi can tace
“Ikon Allah amman baka tambayi Hajiyar Fateeman ba ko?”
“Ko na tambaya ba fadan zatai ba?”
Kai Hajiya ta gyada tace
“Haka ne. Jiya da dare tazo gidan nan tazo min da wani alamari mai girma wanda har yanzu yake tsaya min a rai na. Wai Fu’ad ya saki Fateema!”
A razane Kamal ya dago yana kallon Hajiya yace
“Ya sake ta Hajiya?”
“Wallahi nima jiya Hajiyar taku take fada min yanzu haka so muke ayi la’asar mu zo can gidan naku.”
“Ikon Allah!”
Kamal ya fada yana girgiza kai.
Yai shiru Hajiyar ma tai shiru. Hajiya tace
“Me yake damun Fateema? Ko ciki ne da ita?”
Ajiyar zuciya Kamal ya sauke yace
“A’ah na farko a sume muka kai ta asibiti mun zata ma ta mutu. A lokacin Iikitoci suka rufe akan sai daga baya da kyar suka ceto ranta. Bayan nan kuma ta shiga comma dan sai da ta kwana wajen bakwai ta dawo. Anan ya fada mana taga abinda ya razana ta ne har yaso ya taba zuciyar ta. Munyi jinyar sati biyu aka sallamo mu. Kwana mu uku a gida ciwon ya kara tashi inda mukai asibiti likita ya dinga fada dan jinin ta yai mugun hawa ga zuciyar ta da ta kamu da ciwo. Wallahi tin lokacin Fateema bata da sukuni kullum cikin kuka da damuwa ni ban matsa mata da tambaya ba amman dai abun na raina nace zan zo na sanar daku.”
“Allah sarki kila duk sakin ke damun ta. Fu’ad bai kyauta min ba bai kuma kyautawa Fateema ba. sai dai nace Allah ya shirya.”
Kiran sallah da taji anayi yasa tace
“To ga sallah ana yi ko zaka yi sai mu tafi gaba daya can gidan.”
“To Hajiya “
Ya mike ya fita. Yai alwala anan famfo dake a compond gidan sannan ya tafi masallaci. Sai da ya idar sannan ya dawo ya shiga gidan.
Hajiya taje ta kira Hajiyar cikin gida sannan suka fito suka shiga bayan mota ya jasu. Duk da zai je daukar Suraiyya ya fasa sai text da yai mata yace in ta gama ta taho kawai.
Suna zuwa yai parking suka fito. Shima ya fito wayar sa ce ta hau kara ya dauka ya kara a kunne yana answering call. Wannan yasa su Hajiya sukai cikin gida.
Ba kowa a falon dan haka suna ta sallama sai daga baya Momy dake sama ta jiyo ta sauko bayan ta amsa. Tana ganin su Hajiyar Fu’ad ta saki fara’a ta karaso falon tana fadin
“Lalle marhabun sannun ku da zuwa. Bismillah!”
Zama sukai sannan aka fara gaisawa sai da suka gama gaisawa Hajiyar cikin gida tace
“Ashe haka abu ya faru?”
Momy tace
“Wallahi Hajiya!”
STORY CONTINUES BELOW
“To Allah kiyaye gaba ya bada hakuri.”
“Amin mun gode.”
Kamal ne ya shigo yace
“Ah ina Fateema?”
Momy tace
“Bama tasan sun zo ba.”
“Bari na kira ta.”
Ya fada yana nufar kofar dakin Fateema.
Mikewa Momy tayi ta kawo musu ruwa da lemo sannan ta zauna suna taba hira.
A kwance ya same ni idon na a lumshe kamar me bacci.
“Fateema;”
Ya kira sunan ma. A hankali na bude ido ina bin sa da kallo. Tausayin na yaji yana shigar sa.
“Hajiyar Fu’ad ce tazo!”
Da sauri na mike zaune nace
“Sunyi waya dashi.”
Sai kuma na koma na zauna hawaye na zubowa daga ido na. Shin in Fu’ad ya dawo a yanzu me zan masa bayan ba aure tsakanin mu. Abinda yasa naji zuciya ta ta tsinke kenan na fara kuka.
“Menene na kukan wai? Ke kenan kullum kuka haka ake yi shin ba zaki godewa Allah da ya jarabce ki a rayuwa ba. Ina kinsan duk bawa tin daga lokacin da aka haife Allah ke tsara masa duk ‘kaddarar sa da zata same shi a ciki har da ranar mutuwar ka. To ke Allah ya ‘kaddar ta hakan a rayuwar ki kenan baki gode masa ba butulci zaki masa kome? Dan Allah Fateema ki amshi jarabawar ki insha Allah komai zai yi sauki. Amman wannan yawan kukan me zai kara miki in ba ta dada kwantar dake ba ko kin fiso ke kenan kullum a asibiti hankalin Momy da namu a tashe shi yana can bai san kina yi ba. Dan Allah ki daure ki cire damuwa Allah ya riga ya ‘kaddar ta karshen zaman naku kenan a yanzu bamu sani ba ko nan gaba amman ayanzu ya kare to me kuma zaki tsaya yi. Kiyi ta addu’a Allah yasa haka shine mafi alheri sannan Allah ya baki hakuri da dangana ya kawo miki mai zama dake har karshen rayuwarki. Amman in kukan zaki tsaya yi me zai kawo miki zai dawo miki da Fu’ad din ne ko zai sa auren ku ya zauna. Bai zai yiyu ba sai dai kullum ki kasance a wahale. Dan Allah Teemah kiyi hakuri ki mika komai ga Allah. Insha Allahu Allah zai iya miki da sannu komai zai zama tarihi a rayuwar ki kinji?”
Ya fada cikin lallashi. Kai na gyada ina goge hawayen ido na. Ya mikon tissue yace
“Goge dukka ki taso muje ku gaisa kinji amman dan Allah ki daina wannan kukan!”
Kai ta gyada yace
“Promise!”
“Nayi”
Na fada a sanyaye. Yace
“Gud girl taso to.”
Na mike na dauki hijab na saka yai gaba ina bin sa a baya a haka muka karasa falo. A kan carpet na zauna kai na a kasa na fara gaishe da Hajiyar Fu’ad
“Ina yini Hajiya?”
“Lafiya lou Fateema ya jikin?”
“Alhamdulillah!”
“Allah kara sauki.”
“Amin.”
Kai na a kasa na dan kalli gefen da Hajiyar cikin gida take nace
“Ina yini Hajiya?”
“Lafiya lou Fateema. Ya karfin jikin?”
“Alhamduliah!”
Na fada murya ta na rawa.
Tace
“To Allah kara sauki.”
Ban amsa ba saboda kukan ta ya tahon na tushe baki na kawai kai na a kasa. Mun jima zaune suna dan taba hira da Momy can Hajiyar cikin gida tace
“Ashe haka abu ya faru Fateema. Kiyi hakuri Allah yasa haka shine mafi alheri.”
Kai na a kasa na amsa da amin a hankali. Hajiyar Fu’ad tace
“Kiyi hakuri kinji. Kada ki saka wata damuwa Allah yana tare dake kuma zai kawo miki dauki”
Kai na gyada kawai so nake na tamvaye su sunyi waya da Fu’ad amman na kasa saboda nauyin Hajiya da nake ji. A haka suka mike suna fadin
“To Hajiya mu zamu tafi sai anjima!”
Momy ta mike tana fadin
“Nagode sosai Allah ya saka ya bar zumunci “
“Amin!”
Hajiyar cikin gida ta fada. Hajiyar Fu’ad ta kallen tace
“Amman dai zamu cigaba da zumunci ko Fateema.”
Kai na gyada tace
“Yauwah nagode Allah yayi albarka.”
“Amin!”
Hajiyar cikin gida ta fada. Kai na a kasa nace
“Nagode ku gaida gida.”
Suka amsa da
“Gida zai ji.”
Suka fice har da Momy tana mai musu rakiya. A compound suka tadda Yaa Kamal yana ganin su ya shiga ya dauko mota ya fito da ita.
Hajiyar Fu’ad ta kalli Momy tace
“To dan Allah kada a yada zumunci mu cigaba daga inda aka tsaya. Dan ni dai ina son Fateema wallahi.”
Momy tace
“Insha Allahu Hajiya za anayi.”
“Yauwah nagode.”
Suka karasa wajen mota. Momy tace
“Toh ku gaida gida na gode.”
Suka shiga ta koma ciki. A falo ta tadda ni na hade kai da gwiwa. Kai ta dauke tayi sama. Dagowa nayi ina bin Momy da kallo. Hawaye ne ya zubon nasa hannu na na goge shi.
“Shin Momy tafi son Fu’ad ne akai na?”
Tambayar da nayiwa kaina kenan. Sam bata damu dani ba duk dan Fu’ad ya saken.
“Shin ni nace Fu’ad ya sake ni ne? Dukka su basu san irin son da nakewa Fu’ad ba. A satitikan nan ni kadai nasan a halin da nake ciki ga kewar sa ga son sa dake addabar zuciya ta. Amman Momy gani take ni naja komai bayan nima ina son sa da nasan zai haka ba zan taba barin sa ba.”
Zuciya ta na dafe jin yadda take min zafi da radadi baki na na cije ina mikewa a hankali. Har nayi hanyar daki na. na komo nayi sama dakin Momy. Zaune na same ta tana waya. Tana gani na ta dauke kai ta cigaba da amsawa.
“Ke dai bari Yaya abin yana damuna dan Fu’ad yaro ne nutsatse!”
Shiru tayi can tace
“Ya zamuyi sai addu’ar daman.”
Ta karayin shiru sannan tace
“Insha Allahu. Nagode sai anjima!”
Da Mamin Yaa Fauwaz take wayar tin da naji tace Yaya. Wayar ta ajiye na karaso wajen ta a sanyaye na zube kafafuna a kasa ina kama kafaffun ta nace
“Momy dan Allah ki yafe min!”
“Fateema na riga na yafe miki.”
“Amman meyasa kike fushi dani?”
“Fateema dole nayi baki san yadda nake jin daci da radadin rasa Fu’ad da kikai ba. A gaskiya kin konan rai Fateema.”
“Dan Allah Momy ki yafen ki daina fushi dani Momy da wanne zanji da rashin Fu’ad ko da fushin ki. Wayoo Allah Dady nah dan Allah ka dawo ka jikai na.”
Jin na ambaci Dady sai jikin Momy yai sanyi. Kallo na take tana mai jin tausayi na. A shekara daya na rasa mutane masu mahimmanci na rasa Dady ga Yaa Fauwaz ga Fu’ad. Dole abun yai min yawa.
Kuka nake ina fadin
“Momy ki yafen dan Allah.”
Dagoni tayi tana fadin
“Na yafe miki Faeema.”
“Momy kin daina fushin dani.”
Na fada ina rike da hannu ta. Kai ta gyada min tana goge hawayen dake zubo min. Rumgume ta nayi ina sauke ajiyar zuciya.
Ina jikin ta ban san lokacin da bacci ya dauke ni ba har ta kwantar dani ta zuba tagumi tare da zuba min ido. Tausayi na na kamata dan yadda taga na rame sosai. Hawayen da ke son zubo mata ta goge sannan ta daukai daga kallo na dan zuciyar ta na karyewa.