WANENE SHI
CHAPTER 2
An kawo lefe kamar yadda kowa ya zata, akwati goma sha shida da kuma bayanin cewa bayan auren a can nijar jamilan zata zauna, anci an sha a gidan kamar gidan biki sannan kuma an tarbi mutanen nijar cikin girmamawa kafin su tattara su tafi wani guest inn dake bakin titin unguwarsu inda baffa ya kama musu d’akunan kwana. Su mama rabi an samu abinda ake so, wato lefen ‘yarta yafi na kowa, don na Aisha guda goma sha biyu ne, nasu maryam da nafisa kuma takwas-takwas. Saboda haka sai washe baki take yi anata hidima.
Duk wannan abin ya faru ne bayan an gama tashin hankali da bala’i a gidansu hafsa, inda nanne ta rufe idonta ta zage ta tas! a gaban ‘yan gidansu, ba don rahma bama da abin ya kaisu harda kokawa don sun tarar maman su hafsar da kishiyarta basa nan sai ‘yan matan gidan kawai, amma duk da yawansu ba wanda nanne ta kyale a cikinsu, sai da rahma taga abin zai koma kokawa sannan ta jata da kyar suka bar gidan.
Suna zaune bayan sallar isha a barandar dake kofar kicin itada Rahman dake b’arar maggi, ta sake yin kwafa tace.
“Na rantse da Allah rahma don dai ba zan iya kula wannan jagwal din yaron bane, amma wallahi da sai yarinyar nan ta zama ‘yar kallo tsakanina dashi sai na mayar mata da tunaninta ya koma gaske.”
“Dan Allah ki bar maganar nan, tunda dai kinje kin ja mata kunne ai komai ya wuce.”
“Ba abinda ya wuce, in dai bala’i ne yanzu aka fara, saboda da sai wani satin nake tunanin komawa makarantar, amma wallahi ranar asabar d’in nan zanje muyi ta da sauran ‘yan iskan k’awayen nata da suke biye mata, sai naci mutuncinsu d’aya bayan d’aya.”
“Kin san fa malam murtala ya dawo, wallahi aka kai masa ku kuna fad’a ba zai muku da sauki ba, don ranar litinin d’in nan kusan bulala talatin yayi wa su Anisa.”
“Ko d’ari zaiyi min wallahi sai nayi musu kacakaca a ajin nan…”
Ganin bata da niyyar sauka yasa ta karkato da farantin kan cinyarta tace.
“Allah ya kaimu asabar d’in toh….yanzu dai d’an taya ni b’arar maggin nan.”
Suna cikin yi, rahma ta sako mata zancen saurayinta daya nace akan zai turo iyayensa, ita kuma ta dage sai ta gama makaranta tukunna tunda dama ss3 zata shiga yanzu, tare dasu nannen.
“Toh wai meye? Tunda dai mamanki ta yarda dashi ki bari ya turo mana.”
Rahma ta kalleta da murmushi.
“Kalli wadda take cewa ba wani abu bane, ke da har yanzu ba wanda kika taba saurara…kuma kin san in dai za’ayi auren zainab baffa dake zai hada tunda ba dole sai kun fara jami’a ba, gashi ita tana da wani.”
Nanne ta tabe baki.
“Nifa na gaya miki harkar samarin nan duk wahala ce, ni in zanyi auren ma cewa baffa zanyi kawai ya zabo min babban mutum mai hankali, don duk samarin nan ‘yan duniya ne.”
“Haka dai kike gani don baki taba tsayawa kin saurari wani ba, ga masu son miki magana da yawa.
Da jin haka, idonta ya hango mata fuskarsa, wani mutum guda daya da ta kasa cire shi daga tunaninta, tun ranar data fara ganinsa har yanzu da baya nan, yanzu da take jin kamar tana kewarsa, kewar yadda take ganinsa tsaye a kofar gidansu duk sanda ta dawo daga islamiyya, a saman mota yana danna waya ko tare da abokansa.Yawanci iya haduwarsu kenan, sai ko da safe wani lokacin in zasu makaranta ta hango shi ya dawo daga morning training, ita ko sanin gabadaya ‘yan gidansu ma bata yi ba don bata taba shiga ba, duk da cewa yanzu zasu yi kusan wata hudu da dawowa, kuma wata k’anwarsa ma sun saba da safiya don ta shiga islamiyarsu. +
“Wai tunanin me kike?” Rahma ta katse ta.
“Ba komai, me kike cewa?”
“Wannan purple jakar ta lefen aunty jamila tayi kyau sosai, kinga d’an flat takalminta kuwa?”
Daga nan ta shiga santin abubuwan ciki, wanda a lokacin da ake d’agawa ita nanne hankalinta ya tafi wajen zirawa Aunty nanah (k’anwar mama rabi) fara cikin rigarta, don sun kusa yin karo da ita a hanyar bene ta zageta har tana fad’in tayo halin rashin mutunci irin na Nuratu mahaifiyarta.
Ai kuwa ba’a gama ganin kayan ba, ta hau make-make a jikinta, kafin ta tashi da gudu tayi d’aki. 1
***** *****
Sati d’aya bayan haka rayuwar gidan ta cigaba da tafiya tare kuma shirye-shiryen biki daga kowanne b’angare, don kuwa kowa ya dage wajen ganin bajintarsa tafi ta sauran saboda wata guda ne kawai ya rage ayi bikin, baffa ya saiwa kowacce amarya dank’ara-dank’aran gadaje guda biyu da kuma furniture saitin kujeru suma guda biyu, sai manyan-manyan tvn plasma da sauran kayan saitinsu.
Sauran abubuwa irin na kitchen da kuma k’arin wasu abu na ado wannan duk na iyayensu mata ne, sannan ya bawa kowacce a cikin matan nasa dubu d’ari tasa gudunmawar don yaga take-takensu na cewar bayan events d’in daya had’a za’a yi gabad’aya, kowacce na shirin kama waje tayi wani bikin da ‘yan uwanta. Hatta Aunty amarya saida ya bata dubu hamsin yace tayi d’inki itama da ‘ya’yanta. Don haka a kowacce rana gidan cike yake da mutane na ‘yan uwa dake zuwa anata faman hada-hada tsakanin gidan da kasuwa.
A lokacin an koma makarantar boko daga dogon hutun da akayi na sabon zango, wanda su nanne suka shiga aji shida itada sadiq da zainab, safiya kuma na aji uku, surrayya ce kad’ai a ajin na k’arshe a primary. ‘yan biyu kuma sun sami abinda suke so sunyi candy, sai aikin baccin safe kamar baza su tashi ba, da yamma kuma su tafi ball ko yawon eatery da abokai.
Da safe nanne na zaune a falo ta hard’e k’afa d’aya kan daya tana shan tea, uniform d’in makarantarsu ne a jikinta na farar riga da bak’in wando, ba d’ankwali a kanta sai jelar manyan kalbar da rahma tayi mata sun zubo har k’asan kafad’arta.
Inna ta juyo ta kalleta daga kan sallayarta data gama lazumi.
“Yanzu nanne baza ki dubi girman Allah da magiyar da nake miki ki tsefe kalbar nan ba? Tafi sati biyu fa akanki.”
Ta yamutsa fuska.
“Inna na fad’a miki sai na wanke kan ne kafin in sake kitson kuma wankin wahala yake bani, so nake in samu lokaci inje saloon tukunna.”
“Ai shikenan. sai kiyi ki gama kafin su fara jelan kiranki.”
Tana rufe baki kuwa safiya ta shigo falon, ta durkusa har k’asa ta gaishe da innan sannan tace.
“Nanne tun d’azu fa muke jiranki, kowa ya fito kuma yaya umar ne zai kaimu yau.”
“Yaya umar?…ina idris d’in?”
“Wai ya aiko bashi da lafiya.”
“Toh maza tashi, don kin san halinsa.” inna ta fad’a da sauri.
Ta zura hijabi sannan ta dauki jakarta tare da safa da dankwali tabi bayan safiya, tun daga waje sadiq dake zaune a gaban sienna da ake kaisu ya langwab’e kai yana mata murmushi, hakan ya tabbatar mata sun dad’e suna jiranta kenan.
Suna isa safiya ta shige baya sannan ta zauna a kujerar gefen surrayya ta rufe kofar motar, umar ya ajiye tab d’in da yake dannawa a gefe sannan yayi magana ba tare daya juyo ba.
“Ke kina jina?”
“Eh.” Ta fada kanta tsaye.”Idan kin dawo kije wajen mama Azumi ki karbi key din d’akina, ki gyara shi tas! Ki wanke band’akin, sannan kuma for the whole week ni zan dinga kaiku makaranta, idan kin ga dama ki bari kullum in dinga riga ki shigowa motar nan.”
Yana gama fad’in haka yaja motar suka yi gate, ta had’a ido da sadiq ta cikin mudubi ya sake sakar mata murmushi motsin fatar bakinsa na fad’in ‘yan mata! Ta gallara masa harara kafin ta sunkuya saka safarta.
Suna isa makarantar ta tarar har malami na farko ya shiga, wata malamar biology mai tsanani rashin son surutu ta juya kan allo tana rubutu, bata bari ta ganta ba ta shigo a hankali ta wuce bencinsu ita da Amina, dukkan ‘yan ajin na kallonta ba wanda yayi magana, don duk da cewa ba tsoronta suke ji ba kowa yana d’an shakkar surutun ta, irin dai karar da akewa mutum mai baki.
Tana zama Amina tasa hannu ta cusa mata jelar gashinta da ta fito ta gefe. In da akwai abinda ya banbanta halin nanne da Amina to rashin kunya ce, saboda ita magana ce kawai da ita amma bata da rashin kunya irinta nanne
“Ya akayi yau kika zo da wuri?” ta tambayeta a hankali.
“Azababben yaya umar ne ya kawo mu wallahi.”
“Ina idris d’in?”
“Wai bashi da lafiya.”
“Kice kin daina missing first period.”
Taja guntun tsaki.
“Wai a tunaninsa ma fa haka na makara ban fito ba.”
Amina ta d’anyi dariya kafin tace.
“Zaki saka mai wani sabon tunanin ne.”
“Ke bari a fita break, akwai maganar ma daza muyi.”
“Haba? Ko munyi first catch ne?”
Ta juyo daga kokarin d’auko littafin da take, ta gallara mata harara.
“Ke dai ‘yar iska ce, baza a taba wani abu a duniya ba sai saurayi.”
A daidai nan malamar ta juyo ta kalle su.
“Surutun me kuke yi?” Ta tambaya da turanci.
Kai tsaye Amina ta d’ago tace.
“Malama rasuwa aka mata ne shine nake mata gaisuwa.”
“Ajin nawa ne gidan gaisuwa?”
Ta sake gyara murya tace.
“Ma, ai yadda mutuwa take zuwa ko’ina haka gaisuwarta ma ana iya yi a koina.”
Ta kalle ta da mamaki kafin ta nuna musu hanyar kofa.
“Toh ku fita waje kuyi zaman makokin.” 1
Inda sabo dama hakan yasha jawo musu fitowar bakin aji, don Amina irin mutanen nan ne da basa taba rasa amsar fad’a, ko waye mai tambayar kuwa.
Har sun kai k’ofa ta tsaida su da tambayar waye ya rasu, Nanne tayi rau! da ido kafin ta amsa da kazar da take kiwo ce, abinda ya jawo dariyar gabadaya ajin kenan wanda ya jawo musu kneel-down a gaban aji, next period ma english ba suka shiga aji ba, tunda malaman k’awaye ne haka suka zauna har aka fita break. 2
Da break d’in ma basu samu damar maganar ba saboda haduwa suka yi da ‘yan click dinsu akayi ta hira kala-kala, wata maryam tayo musu dan malele ana sha ana cafta. Bayan an kada kuma suka tafi wanko farantan da suka aro a kicin din makarantar, suna dawowa kuma aka tafi physics lab, suka ci uban note sannan aka fara practical, last period ya kasance geography ne, wani malami mai azabar dictation shima. 1
Sai da aka tashi sannan suka tsaya daga k’asan wata bishiya a harabar parking lot din inda ake d’aukarsu. Nanne ta kalli Amina sosai tace.
“Ta yaya aljanu suke shiga jikin mutum?”
Amina ta d’an had’e girarta.
“Ban gane ba, nifa ba malama bace.”
“Dalla ina nufin kamar yanzu ni in inaso aljanu su shiga jikina me zanyi?”
“Sa’adha aljanu? Me zaki yi dasu?”
“Wani malami nake so na waskawa mari a islamiyarmu.”
“Me yayi miki?”
STORY CONTINUES BELOW
“wai kawai daga cacar baki ta had’a mu da wasu mahaukatan yara a aji, ya kama ya mana bulala ashirin-ashirin.”
“Toh kiyi na k’arya mana, me zai sa ki jawo wa kanki bala’i?”
“Malamin ne mugun d’an izala ne, yanzu sai ya iya ganewa.”
“Wallahi ba ta yadda za’ayi ya gane tunda aljanu dai ba ganinsu ake ba, kuma a yadda na sanki zaki iya, kawai abu d’aya ne kar ki tab’a bari ya dake ki da sunan ruk’iya tunda kin san ke za’a jibga.”
Ta d’anyi shiru tana tunani.
“Kuma fa hakane, ba dai ihu ake ba da zare ido?”
“Sannan ki cire d’ankwalinki ki tsaida idonki tar! ko waye yazo kar ki nuna kin sanshi ma balle wani tsoronsa, ki zagi duk wanda kike so kuma.” 2
Nanne ta tsaida idonta waje d’aya, tunaninta na hasko mata ita a hoton da Amina ke zanawa. 1
**** ****
BAYAN SATI BIYU.
Da maghriba ta dawo daga bayan layinsu gidan wata hajiya talatu, ta karbowa inna tarin adduwa a cikin bakar leda wai ta gaji da cin goro. Tana tafe tana cilla ledar a hannunta, layin ko’ina da haske saboda wuta da aka kawo a lokacin kuma babu mutane da yawa, daga tsillin masu wucewa sai masu gadin gidaje da suka fito waje da ‘yar rediyonsu.
Cilla ledar da zata sake yi sama sai kawai ta yage a daidai sanda ta karyo kwanar layinsu, gabadaya adduwar ta tarwatse wasu ma suka shiga gangarawa cikin kwalbatin dake gefenta, taja karamin tsaki.
“Ai wallahi dama na san sai ledar nan ta yage, matar nan tana tab’a bada wani abin arziki ne?”
Ta tsaya tana kallonsu kamar su zasu kwashe kansu kafin ta tsugunna ta shiga bin wadda bata fada kwalbatin ba tana sakawa a hijabinta.
“ledar bata da kwari ne?”
Kamar a irin tunanikan da take yi kunnenta ya jiyo mata wannan muryar, wannan muryar mai taushi daga bayanta, ta juya da sauri daidai sanda yake kokarin tsugunnawa. Yana sanye da farar t-shirt da kuma farin wando, ya kara wani fresh akan yadda ta sanshi a baya.
Bata san lokacin da ta d’aga kanta ba.
“Ina jin dama ta fara yagewa.”
“Ko kuma kin cilla ta sama da yawa.”
“Cillawa sama ba zai sa ta yage ba.”
“Inji wa? Bayan da nauyi a cikinta.”
Ta mike tsaye rike da karshen hijabinta.
“Watakila baka san adduwa bane, amma bata da nauyi.”
Ya karaso gabanta hannayensa cike da wandanda ya tsinto.
“Na san adduwa mana harda sauran ‘yan uwanta, su taura, magarya, d’inya da kuma d’ayan mai kwallo da yawa a ciki.”
Ta daga siririyar girarta d’aya.
“Kad’anya…?”
“Right! Kad’anya.”
Ta girgiza kanta alamun ta gane sannan ta kalli hannayensa tace.
“Nagode.”
Maimakon ya zube mata a ciki, sai ya zaro handkerchief daga aljihunsa ya zuba a kai, sannan ya kwashe na hijabinta ma sannan ya fara tafiya, ta kalli bayansa kafin ta bishi.
“Sunana Imran, baki taba gaya min naki ba.”
Tayi shiru kamar baza ta amsa ba.
“Baka taba tambaya ba.”
“Baki taba bani damar tambaya bane.”
Ta kalle shi da gefen ido.
“A ina kake ganina?”
“In dai ina garin nan kullum ina ganinki, da safe in zaku tafi makaranta, da rana in zaki je islamiyya, da yamma in kin dawo…ko kuma sau da yawa in kin fito keda k’awarki.”
“Ta yaya kasan duk wannan abubuwan?”
“Abubuwan da na sani naki sun fi cikin kirga, d’azu ma kin raka inna asibiti wajen gashin k’ashi.”
Daidai sannan suka iso kofar gidansu, ya mika mata handkerchief din ta karba.
“Zaki fada min sunan…?”
Ta sauke gashin idonta kan hannayenta dake rike da adduwar.
“…Don Allah” muryarsa a hankali ta fito.
“Idan ka san duk wadannan abubuwan, sunana ba zai maka wahala ba, sai da safe.”
Tana fadin haka ta tura gate d’in ta shige gida. A ranar ko inna ta shaida cewa cikin farin ciki take.
Sai dai kuma me? Ta kwana da wani matsanancin ciwon kai!”Inna wai ina cokulan, nifa bangansu akan tray d’in ba.” +
Nanne ta tambaya daga falo bayan ta dawo daga makarantar boko ta saka kayan islamiyya. Inna ta amsa daga cikin d’aki.
“Toh watakila basu sako ba, don yau ance ba azumi bace akan rabon, iyami ce.”
“kuma a rashin hankalinta haka zamu ci abincin da hannu?”
Don a yadda tsarin abincin gidan yake, duk matar da ranar girkinta ce, ita zata bada odar abincin da za’ayi ta kuma tsaya a kicin d’in har sai an gama an rarrabawa kowanne d’aki, har da ‘yan mazan kowa tray d’insa daban mai d’auke da flask, plate da cokula harda jug saboda ba’a taba yin abinci a gidan ba babu abin sha, musamman zob’o kusan kullum akwai shi a gidan nan.
Sannan ba wanda zaici abincin yace na gidan yawa ne don ma’aikatan gidan gabad’aya an bi musu da tsari akan tsafta, sannan ma girkin kamar gasa ya zama tsakanin matan, kowacce na son ace ranar girkinta abinci na dad’i saboda hatta baffa shi yake ci, bai taba son a banbanta nasa ba.
“Kije ki karbo mana.”
“A wannan yunwar da nake ji yaushe zan iya sauka k’asa.”
“Toh ai sai kisa hannunki tunda daga wanka kika fito.”
Ta zuba abincin, ta koma kan kujera ta fara ci, idonta na kan agogo tana lura da lokaci. Bata san me yasa jikinta yayi sanyi ba duk da sun gama tsara komai ita da Amina, kuma ta dake ranta cewa zata yin, amma jikinta kwata-kwata ba kwari.
Ta rufe idonta tana tauna abincin, haka kawai taji ko dadi ma baya mata, saboda haka ta rufe shi ta zura dogon hijabinta.
“Ina zaki da tsakar ranar nan.”
“Islamiyya mana, kin manta tun wancan satin na koma.”
“Yaushe naji kina cewa canja ta zaki yi?”
“Na fasa ai.”
“Ai miki wannan dukan kuma ki cigaba da zuwa?”
Ta hadiye yawu cikin makogwaronta.
“Inna ba lallai bane ma malamin ya kara shigo mana, bari inyi sauri kar su safiyya su tafi.”
Tunda ta isa cikin ajin nasu ba wanda ta yiwa magana, da yake ma kusan rabin ajin na jin haushinta akan dukan data jawo aka musu sai ba wanda ya kulata, iyaka kad’an dake binta da sannu kawai. Ko da rahama ta iso ma da ka kawai ta amsa tambayar data mata.
Malamin fiqhu ya shigo ya biya karatunsa yayi bayani sannan aka fita sallah, ana dawowa malam murtala ya shigo aka fara bita, tunda aka fara kuwa nanne bata ko d’ago da kanta ba balle tayi karatun, har akayi izu biyar, sannan ya biya k’ari yace suma su biya. A nan ma ta k’ara dankwafar da kanta ta, tun yana kyalewa har zuciya ta kawo shi yace kowa yayi shiru.
“Sa’adha tashi ki biya karin da aka yi!”
Bata ko motsa ba balle ta nuna taji me yace. Ya sake maimatawa ba wani canji, Rahma dake gefenta ta tabo cinyarta bata d’ago ba, gabadaya ‘yan ajin sun juyo kowa na kallonta, ai kuwa bai k’ara magana ba ya janyo bulala yayo kanta, Rahma tayi saurin matsawa sanda ya k’araso ya sauke mata guda d’aya a tsakiyar bayanta.
Ai kuwa tana jin vibration d’in bulalar a jikinta taji wani irin karfi da bata san tana dashi ba ya shige ta, kafin kwakwalwarta ta iya wani tunanin taji wata bulalar a jikinta ba shiri kuwa ta mike tsaye, ta fito bakin bencin ta tsaya daf dashi idanunta a tsaye kyam!
“Keh baki da hankali? ni kika tsayawa a kai haka, koma ki zauna…nace koma ki zauna!”
Tak’i zaman, ta tsare shi da dara-daran idanunta da bata san sunyi jawur ba, ya d’aga hannunsa ya k’ara mata wata bulalar, ba tare da tunanin komai ba kuwa nanne ta waska masa mari, mai kauri sannan ta cakumi wuyan rigarsa, ta d’aga shi sama har sai da kafarsa ta rabu da k’asa. 1
Ajin gaba d’aya ya rude da ihu wasu kuma suka yi waje, malam murtala yayi-yayi ya raba hannun nanne da rigarsa amma ya kasa gashi bata ko ihu balle magana, sai zazzare jajayen idonta take yi ga kuma radadin marin na shigarsa. 2
A haka wasu malaman biyu suka shigo suka ratsa ta cikin cincirindon daliban suka raba su da kyar. Tana sakinsa kuwa ta sulale ta fadi kasa kamar an zare wani abu daga jikinta.
Aka fita da malam murtala, d’aya malamin kuma ya shiga bada umarnin a daga ta, rahama ce ta fara zuwa kanta tare da wasu mutum biyu, suka maida ita kan bencin. Nan fa makara makaranta ta rude daliban wasu ajujuwan suka dinga shigowa, malaman sukayi-sukayi kowa ya koma aji amma suka kasa, sai tururwar ganin nanne suke da kuma malam murtala da aka kai staffroom. +
Har aka tashi, Rahma da sadiya suka raka nanne gida bata san inda kanta yake ba, don wani irin ciwo yake mata da kuma juyawa. Saboda haka koda rahama ta cewa inna bata da lafiya ne, bata d’aga hankalinta ba ta barta ta kwanta.
Tana yin sallar isha kuwa ta nemi kan gado, a lokacin tasha panadol ya kai hudu amma ba abinda ya ragu, da kyar ta samu bacci ya dauketa.
A cikin baccin, tayi mafarki da fuskarsa, fuskar IMRAN, muryarsa mai taushi ta cika kunnuwanta, a hankali kamar sanda yake mata magiyar sunanta. Sai dai wannan karon sunan ya fad’a, sunanta kad’ai.
“Sa’adha!.”
**** ****
“Wai don Allah meya same ki?”
“Rahama nace miki ki daina zancen nan koh? Wai sai inna taji ne?”
“Nanne abin ne ya bani mamaki, na san baki da aljanu, amma d’aga malam murtala fa kika yi har sama, ta yaya kika iya?”
Nanne ta had’iye yawu, itama tun tashinta take wannan tunanin, ta rasa ya akayi taji wani irin karfi a daidai wannan lokacin, karfin da har ta iya daga mutum.
“Nifa ban sani ba, watakila kawai don na sa kaina zanyi ne, saboda haka ni kawai kiyi shiru kar wani ma ya jiki.”
Tana fad’in hakan ta cigaba da cillo kayan wankinta daga cikin wardrobe.
“Bari in gama hadawa ki tayani sauka k’asa dasu bello zan bawa wankin, na nasiru baya fita wallahi.”
“Nanne…” Rahma ta kira sunanta a hankali.
“Su malam murtala fa sunce zasu zo gidan nan yau, d’azu na hadu da malam mukhtar yake ce min anjima zasu zo.”
Ta juyo a hankali rike da wata riga.
“Zasu zo? Me zasu zo suyi?”
“Wai hankalinsu ya tashi aljanin da ya shige ki mai karfi ne, malam murtala yace yaga alamunsa a cikin idonki.”
Sakan daya-biyu tana kallonta kamar abinda ta fada ya tsorata ta, kafin kuma ta kyalkyale da dariya harda rik’e murfin wardrobe din.
“Kice malam yaji shak’a, wato a aljanun ma nawa mai karfi ne, aiko zan nuna masa wasu k’arin moves din da aljanin ya iya ne ma duk sanda ya sake dukana wallahi.”
Rahma ta girgiza kanta.
“Yanzu toh ya zaki yi in sun zo?”
“Yafi ince karya suke min, ba dai baffa zasu gayawa ba…kar su fasa Allah ya kawo su.”
****
Ya lumshe ido yana lokacin da muryar gefensa ke fita cike da bacin rai.
“…me yasa kake tunanin yin abinda ba zai tab’a yiwuwa ba? Me yasa zaka fara abinda ba zai d’ore ba?”
Ya ciza gefen lebb’ensa yana sauraren yadda iskar saharar ke kad’awa da karfi.
“Tana da kyau jamil, idan tana fad’a zaka ga kamar lebbenta zai koma ciki ne.”
Jaamil yaja tsaki kafin ya sulale yabi cikin iskar saharar.A daidai kofar shiga falon baffa nanne ta tsinci muryar ya sulaiman cike da bacin rai yana fadin.
“A tunani na baffa gwara a takawa yarinyar nan birki wallahi tun yanzu, abubuwan nata sun fara yawa.”
Bata bari baffa ya bashi amsa ba ta murda handle din kofar ta shiga, sulaiman din ne kuwa zaune a katon falon yayin da baffa ke daga can karshe kasan kujerarsa, jaridu kusan uku a gefensa da kofin coffee dinsa.
Ta zube daga tsakiya tana gaishe shi, fuskarsa ba yabo ba fallasa ya nuna mata gefen hagunsa, ta mike ta koma can. Ba yadda sulaiman ya iya dole ya fita don ya san baffan baya bukatarsa a lokacin.
“Sa’adha me ya faru a makarantarku jiya?”
Muryarsa taso ta yanke karfin gwiwar da ta shigo dashi, ta hadiye yawu a hankali kanta na kasa tace.
“Wace makarantar? Islamiyya ko boko?”
“Islamiyyarku ta bayan layin nan.”
“Babu komai, jiya ma da wuri aka tashi.”
“Ya akayi akace kin mari malami jiya?”
Da saurinta tace.
“Duk wanda ya gaya maka karyane baffa, ni ba abinda nayi.”
Ya gyara zamansa yana kallonta sosai.
“Baki san kin mare shi ba?” Ta d’aga kai.
“Kenan in yarda da abinda malamanki suka fada?” Tayi shiru.
“Nan wajen yayanki ya rako su suka zauna suna fada min wai ba’a hankalinki kika yi komai ba, aljanu ne suka shige ki kuma suna tunanin masu k’arfi ne.”
Ta bata rai, ta kirkiro hawaye. “Wallahi baffa karya ake min ni babu aljanin daya shiga jikina, kullum sai nayi addu’a kafin na kwanta.”
“idan haka ne sa’adha, toh me zaisa ki daga hannu akan malaminki, ni dai na san har ga Allah ba’ayi miki wannan tarbiyar a gidan nan ba. Wadda ta raineki ita ta raine ni, kuma na tabbata inna baza ta taba cewa kije ki mari malamin ki ba.”
Ta shiga rera kuka tsakaninta da Allah tana bashi hakuri, yayi ta nasiharsa akan girman malami da kuma girman laifinta kafin ya sallameta, sai dai har ta gama bashi hakurin ta fita, ransa bai dawo daidai ba.
Tana zuwa daki ta tarar inna ta fara gyangyadinta na maghriba, ta shiga toilet ta wanke fuskarta tana fadin.
Ta Allah ba taku ba, wato a tunaninku baffa yace ku tafi dani ayi min ruk’iya, a sami abin jibga…ba sai kun sake ganina ma a islamiyyar ba.
Ta fito falo ta zuba abincinta sannan ta kunna tv. Abinda ya tashi inna kenan ta mike da salati.
“Me ya sami idanunki suka kumbura?” ta tambaya tana kare mata kallo.
Nanne ta dan ja tsaki, matsalar fuskarta kenan, ko hawaye tayi sai idanunta sun kada.
“Ba komai, kaina ne kawai ke ciwo.”
“Ke anya lafiyar ki kalau kuwa? A satin nan sau nawa kika yi wannan ciwon kan?”
Ta d’anyi shiru, duk da ba ciwon kan take ba amma abinda inna ta fada haka ne. Bata fiye ciwon kai ba amma kusan a satin nan sau uku tana yinsa. Anya lafiyar tata kalau kuwa? Sai kuma tayi saurin kawar da zancen kar inna ta shiga damuwa.
“Watakila wahalar komawa makarantar nan ce, in zubo miki abincin ko sai kinyi isha?”
Lokacin da taje jera kayan da aka kawo mata daga wanki, handkerchief din daya bata ya fado, ta sunkuya a hankali ta dauka, tun a wancan daren data ninke shi ta ajiye bata kara bi ta kansa ba, babu ko kanshin turare a jikinsa amma sai taji gabanta ya fadi sanda ta kaishi kan hancinta, wani irin faduwar gaba mai nauyi, kamar an cilla katon dutse cikin ruwa.Ta ware shi gabadayansa, anan wani mamakin ya tsaida numfashinta, d’an karami ne da baifi a dunkule shi ba. Toh amma yaya akayi a wancan lokacin ya d’auki tarin adduwar data yi kusan rabin leda?
Adduwar da kusan sati d’aya kenan har yanzu bata kare ba?
*****
Gari ya waye, rana ta bude a sararin sama. Yana bud’e idonsa yaci karo dana jaamil zaune akan stool d’in mudubin dake dakin.
“Barka da tashi, ashe ka canja gida?”
Ya mutsika idonsa.
“Wallahi, kwana waje tara kenan da dawowa ta.”
“Allah ya sanya alkairi, bamu sani ba ai da munzo mun taya ka d’iban kaya.”
“Ai da yake abin ne yazo ba shiri, amma kar ka damu kanka ma ban debo komai na can ba, komai sabo na…”
Bai karasa ba jaamil ya dauki wata kwalbar turare dake kan mudubin ya jefo masa, amma maimakon ta same shi sai ta wuce ta cikin jikinsa ta daki bango ta tarwatse.
“Kwana na uku kenan ina faman nemanka yarima, ina tunanin ba gidan da ban shiga ba a garin nan.”
Imran ya mike zaune.
“Toh saboda me zaka shiga nemana? na san dai ba wani abu ne ya taso daga gida ba.”
“Idan a wajenka babu wani abu, ni dole ne inyi taka tsantsan da kai don duk abinda ya faru Naani zata ce laifina ne.”
“Me zai faru? Ba dai zancen zamana haka bane kuma ta sani?”
“Banda wannan, kaima ka san me nake nufi.”
“Baka yarda da rantsuwar da na maka bane?”
“Ina tsoron sha’aninka ne yarima, don tunaninka daban ne.”
Imran yayi gajeriyar hamma sannan ya lumshe kyawawan idonsa.
“Ka san me? Yunwa nake ji, bari in hada mana wani abun sai ka cigaba da gaya min maganganun daka saba, nima ina baka amsa da wadanda na saba…so, me zaka ci?”
Jaamil ya girgiza kansa yana masa kallon Ba inda zaka.
Mintuna goma bayan haka ya gaji da zaman d’akin ya bishi can kan dining d’in dake tsakiyar had’ad’d’en kicin d’insa (island).
“Ga ruwan zafi nan a kettle sannan akwai differents tea-bags a cikin cabinet din can ka zabi wanda kake so.”
A wannan lokacin jaamil ya san hanyar kawai da zai iya samun had’in kansa shine ya biye masa, saboda haka ba musu ya nufi jikin durowoyin ya d’auko wanda hannunsa ya fara kaiwa kai sannan ya dawo ya zauna a kujerar dake fuskantarsa.
Ya had’a tean kamar yadda yasha ganin imran na yi sannan ya shiga juyawa, idonsa na kan yadda yake ta cin kwan daya soya da fork yana kuma duba cikin wayarsa.
“Me yasa ka tashi daga wancan gidan?” ya tambaya kai tsaye.
Ba tare daya d’ago ba ya amsa.
“Na fada maka kwanaki nayi mistake wani mak’ocina ya ganni na shiga ta jikin katanga, bana son suspense!”
Jaamil ya gyada kansa.
“Toh me yasa ka dawo nan wajen?”
“Saboda ina son unguwar and yayi kusa da wajen aikina.”Kuma yayi kusa da gidansu.” +
Da jin haka imran ya tsaya da taunar da yake da kuma danna wayar. jaamil ya sake maimaitawa.
“Yayi kusa da gidansu yarima kuma ka sani.”
“Ka san me? lets get this straight…” ya dire wayar hannunsa da fork din.
“…Ka kai karata wajen Naani, ka fada mata duk abubuwan da nake tunanin sirri ne tsakanina da kai, and yes! na yarda cewa nayi kuskure, nayi kuskure dana bari ta sanni har kuma nayi mata magana, sannan nayi rantsuwa ba zan k’ara zuwa kusa da ita ba, toh me ya kawo wannan zancen yanzu?”
“Saboda ban yarda da rantsuwarka ba.”