WANENE SHI CHAPTER 3

WANENE SHI





CHAPTER 3








Wai ya na gansu ne kala-kala?” +

Amina ta tambaya tana warwara katunan dake kan bencinsu. Nanne ta tsotse kwallon agwalumar bakinta tace

“Wai fa bayan events ukun da za’ayi kowacce sun had’a nasu daban zasu yi da yan’uwansu, shine baffa yace shi ‘yanuwansa kala d’aya ne kuma dole zasu je na kowa don haka suyi a rana daban-daban.”

“Toh ai dates din sun hargitse min, kati wajen bakwai wanne za’a fara?”

“Kinga fa, event din farko shine wankan amare ranar litinin, shi inna ce ta hada da daddare za’ayi, sai kamu washegari talata shima a gida za’ayi, laraba mother’s eve na kowa da kowa a wannan event center din, Alhamis shine bikinsu hajiya Babba suma ga inda zasu yi, juma’a na mama rabi itama da wajenta, Asabar kuma nasu mama halime, sai lahadi a d’aura aure kowacce ta kama gabanta.”

“Tabdijam! Wannan ai gajiya zaku yi, bikin ba zai taba dadi ba.”

“Ko dai su gaji, an gaya miki kowanne zanje, ni kawai bak’in cikina za’a hana ni baccin safe weekend.”

“Toh ba kowanne zaki ba ni kika tattaro ki kawo min gabadaya?”

“Ai wai ki zab’a ki darje, wad’ancan guda biyun fa na mama rabi da mama halime duk card admits ne, inda zaki san abin k’aranta ne, ita hajiya babba data isa babu wani sai da kati, kowa shiga zaiyi kuma yaci ya koshi.”

“Toh wanne zaki a ciki?”

“Duk wad’anda za’ayi a gida ina nan, sai mother’s eve da kuma na hajiya babba.”

“Biyun nan ne baza ki ba kenan?”

“Gaskiya dai, kuma fa mama halime harda wani aiko min da anko.”

“Ke dai kawai ba kya son matar nan ne amma wallahi tafi mama rabi kirki. Bar ma zancen bikin nan, baki ban labarin ba.”

Nanne ta tsotse wani kwallon, tana tand’e baki.

“In gaya miki sai ga sallama wai malam mukhtar ne yazo, inna har tana washe baki da taga zan fita ta zata na fara sauraren irin mayun nan ne masu nacin aike, na fita na gaishe da bawan Allah nan…ya kuwa hau bayani tiryan-tiryan wai wallahi akwai abinda ya same ni da ban sani ba, malam murtala har wace k’asa ce yaje akan sannin sirrin aljanu kuma wai wallahi ya ga aljani a jikina sanda na shake shi.”

Amina ta kyalkyale da dariya harda buga benci.

“Na yarda dake wallahi sa’adha, nina san zaki iya shi yasa nace miki kawai ki zare idonki ki mari mutum!”

“…mhmmm ina kaiki ke dai, ya gama bayanansa ya kawo wani k’ullin leda, wai ingattattun magunguna ne da aka kawo daga madina, dana wanka, na sha da madara ko nono, na shafawa a kai, na wace tsiya-wace tsiya, ni dai na karba nayi godiya, ina shigowa gida kuwa na jefa a sharar compound kar ma wani ya ganni dashi.”

“Ke amma fa sunyi kokari, magungunan aljanu fa ance da tsada.”

Nanne ta galla mata harara. “Toh in gaya miki a satin dana koma na bada kudin makaranta, na tabbata dashi suka siyo tunda sun san ba dawowa zanyi ba.”

Amina ta sake kyalkyalewa da wata dariyar.

“wallahi ko hakane sunyi kokari, tunda zasu iya cinyewa.”

“Can musu da iyayi, ni yanzu abinda ke gabana daban.”

“Allah koh? meye a gaban naki?”

A lokaci d’aya bugun zuciyarta ya k’aru, don duk duniya abinda ke d’an damunta guda d’aya ne, ji take yi kawai tana son sake ganin IMRAN, a kwanakin baya da bata ganinsa bata damu kanta haka ba, amma tun daga wannan ‘yar maganar da suka yi shikenan kuma take jin wani abu kamar damuwa a ranta na rashin ganinsa kusan sati biyu.

STORY CONTINUES BELOW

Gashi ba wanda ta sani da zata tambaya, k’anwarsa ma da take gani tare da safiya yanzu basa haduwa tunda ta bar islamiyyar, ba sau daya ba, ba sau biyu ba tasha leka bakin gate da zummar ko zata ganshi, har ta gaji ta yardarwa kanta cewa da gaske baya nan, ya sake irin tafiyar da yayi kwanaki.

Wai meye had’ina dashi ne ma da zan damu kaina da son ganinsa.

Ta ayyana hakan a wani gefen zuciyarta lokacin da yatsunta suka matse agwalumar har saida wani kwallon ya bullutso

*****

Ya jingina da kujerar bayansa yana juyawa a hankali, idanunsa a rufe yana sauraren assistant dinsa dake gefe yana karanto report din karshen wata shida na ma’aikatarsu. Kwakwalwarsa na jin komai daki-daki yana saving d’insa, daga yanayinsa kad’ai wani za daga yanayinsa kad’ai wani zai zata shine shugaban kamfanin gabadaya. Kamfanin nasu na ‘ORZ’ dake kula da duk wasu harkokin talla da ake gudanarwa a media platforms da kuma billboards na kan titi. +

Ya bude idonsa da sauri sanda yaji wani abu daya dau hankalinsa.

“Kaji koh? Kaji abinda nake fad’a masa exactly last six months?”

Mr. Marvin ya rufe file din.

“Shima ana kai masa result din abinda ya fara cewa kenan, yace abinda imran yake fad’a ya tabbata.”

“Ba irin bayanin da banyi masa ba a lokacin amma ya kasa fahimta ta, na fada masa ‘G&M’ ba kamfani bane da za’ayi trusting d’insu da makudan kudi haka, amma ya samu wannan yaron yana gaya masa kawai adadin hundreds din da suke biya per week, gashi nan yanzu just in a half year budget d’inmu yayi kasa da 20%, who knows me zai faru nan gaba?”

“Ni naji fa ana cewa zai janye ne, kawai a maida contract d’in ya zama iya rabin shekara.

Imran ya girgiza kansa.

“Wallahi ba zasu yarda ba, ai yau ko karamin kamfani ne akayi wannan yarjejeniyar dasu baza su taba yarda da haka ba, kuma we can’t force them tunda an riga an rubuta komai da sa hannu.”

Sunyi kamar minti goma suna tattaunawa kafin mr. Marvin ya mik’e.

“Akwai wasu files da zanyi compling, sai na ganka anjima.”

Bayan fitarsa, Imran ya cigaba da ayyukansa, sai da yayi nisa sannan wata mak’ociyar office d’insa maryam ta shigo, ya d’an ja tsaki a k’asan numfashinsa, ko kad’an baya bukatar surutun ta a lokacin. Don a cikin mutane masu irin zuciyarta ma daban ne, yayi tunanin zata daina shiga hanyarsa tun lokacin da ya gaya mata kiri-kiri cewa abinda take tunani tsakaninsu ba zai taba faruwa ba. Amma sai ya zama kamar ba’ayi ba.

“Good afternoon dear, aiki ne da kai yau haka?”

Muryarta mai sanyi ta shiga kunnensa.

“Afternoon.” ya amsa a gajarce ba tare daya kalleta ba.

Ta tsaya daga karshen bencin ta dafa hannayenta da suka sha kunshi akai.

“Akwai wani project na oil company da shamsu yace min zamu yi aikinsa tare, an kawo maka ne?”

“No, banyi signing akai ba, so yanzu ke dashi ne kawai zaku yi handling.”

“Amma saboda me? Zaka bamu guidance fa.” ta marairaice murya.

“kinga maryam…” ya d’ago da kansa.

“In the next 3 months ma bani da aiki dake, kuma kina iya gani yanzu wani abin nake yi, so if you will excuse me.”

Ya nuna bayanta hanyar kofa. Da yake ‘yar duniya ce ko a jikinta, sai kawai ta gyara zaman d’an mayafinta tace.

“Okay, lets discuss something then…nayi zaton baka da relation a kusa kamar yadda yake a file dinka da komai, amma yau sai Allah ya had’a ni da brothernka.”

Ya had’e kakkaurar girarsa waje daya yana kallonta, itama ta nutsar da idanunta cikin nasa sannan ta kiftasu a hankali.

“I’m serious Imran har kama kuke.”

Jin haka yasa gabansa ya fadi, don daga yanayin muryarta ya tsinci k’anshin gaskiya a ciki. Sai dai ya riga ya san halinta, sai ta gama juyashi kafin ta gaya masa gaskiya, kuma bashi da wannan lokacin da zai iya jiranta saboda haka a lokaci d’aya ya tsaida duk wani abu dake motsi a cikin office d’in sannan ya mik’e ya isa wajenta, jikinta ya sandare kamar a k’ank’ara ga hannayenta a iska, sannan bakinta slightly a bud’e alamun tana shirin yin magana ne, bugun zuciyarta ne kadai abinda ya rage mai motsi a tare da ita.

Imran ya tsaya cak ya kalli cikin idanunta, nan take ya shiga ganin abinda ya faru da ita tun daga tashinta a yau har zuwanta office, ya dinga wuce mutanen data hadu dasu kala-kala da abubuwan data yi har zuwa sanda ta koma wajen motarta dauko wani flash, yaga sanda ta juya ta kalli wani kyakkyawan matashi dake mata murmushi daga gefen mota a dai parking lot na office dinsu, bai tsaya yaji maganar da suka yi ba yayi sauri ya nufi kofa, har zai bud’e ya tuna ya murza hannunsa, take komai ya dawo daidai.

“Ko kana tunanin karya nake…”

Maryam ta zarce da maganar data makale a bakinta

“Idan kin gama ki rufe min office din.”

Yana fada yayi ficewarsa. Ta juyo a kid’ime ta kalli kofar da tsananin mamaki sannan kuma kujerarsa.

Yana isa parking lot d’in ya hango wannan matashin dai tsaye jikin motar nan kamar yadda ya gani a idanun maryam. +

“Wallahi na raina haukan yarinyar akanka, na zata tun sanda ta ganni zata je ta fada maka amma kusan mintuna talatin ina tsaye.”

Imran ya bashi amsa yana k’arasawa wajensa.

“Waya sani ko tana tunanin canja shek’a ne tunda ta ganka.”

“Kuma ka san har number wayarta ta bani.”

“A ina ka samu waya?”

Ya d’ago masa tsinken dake hannunsa.

“Shi ta gani a matsayin waya.”

Ya girgiza kansa yana k’are masa kallo.

“Wallahi daka san yadda kayi kyau, da kayi sujjada a wajen nan ka ta rokon Allah ya maida kai haka.”

“Bana son wannan zancen, kaima ka san ba don abu mai muhimmanci ba, babu abinda zaisa inzo nan.”

“Meya faru?”

“Tafiya ce ta dole ta kama ni zuwa k’asar Nepal, kuma zan d’auki kusan wata guda don maganin da zanje karb’owa sai an hada shi tukunna.”

“Maganin waye?”

“Bwama ce ke fama da ciwon b’arin kai.”

Imran ya girgiza kansa.

“Ya salam, Allah ya bata lafiya…amma da kun gwada panadol yana aiki sosai.” jaamil yaja tsaki.

“Bani da lokacin rainin hankalinka yarima, abu d’aya ne ya kawo ni nan…”

“Na sanshi…”

Bai saurareshi ba ya cigaba.

“Naani bata san da tafiyata ba, ka dubi girman Allah, ka tafi da komai daidai har na dawo, zuwa sannan na san baifi wata biyu ba mu huta da duk wannan wahalar.”

Imran ya cigaba da kallonsa gira d’aya a d’age, kamar akwai wani abu da bai fada ba yake jira. Jaamil yayi ajiyar zuciya sannan yace.

“Kar kaje wajenta.”

****

Ranar Asabar tunda ya tashi yake gida yana ta harkokinsa, kwana biyu kenan yana rayuwar ‘yanci tun tafiyar jaamil ranar alhamis, a yanzu bashi da wani mai takura masa ya san yayi nesa daga duk wani idon sani, jinsa yake kamar a farkon watanni hud’un da suka wuce, watannin da ya canja rayuwarsa gabadaya zuwa wata siffar da har yanzu ya kasa yardarwa kansa cewa hakan ba zai d’ore ba

Wajen karfe uku yana kitchen, ya gama cin abincin daya dafa, ya wanke kayan da yayi amfani dasu ya kife a dryer, sannan ya wanke sink din, yana aikinsa ya sauraren cool wakokin da yake so daga cikin bluethoot a gefe.

Sai da ya kimtsa komai sannan yayi wanka ya shirya cikin wani light blue yadi mai kyau, d’an fitted dinkin kuwa ya zauna daidai a jikinsa, ya gyara sumar kansa sannan ya feshe jikinsa da turare, wanda ko bai sa ba kanshinsa baya taba barin kayansa. Kafin ya gama shiryawa ya kunna wayarsa tare da data, messages suka dinga kokawar shigowa kota’ina harda voicemail, yana danna na farko muryar maryam ta karad’e dakin.

“Imran na kira ka several times wayarka bata shiga, please if you got this message call me, na kasa nutsuwa da abinda ya faru ranar thursday…”

Ba bari ta k’arasa ba ya danna na biyu, muryar wani ta maye tata, ya cigaba da saurarensu d’aya bayan d’aya kafin ya fito falo, ya kashe Tvn dake nuna tashar football da duk wasu switches na gidan sannan ya fita. Bai d’auki mota ba don strolling kawai yake son yi yaga unguwar sosai.

A wani masallaci dake can gaba da gidansa yabi jam’in sallar la’asar, ya dad’e ma a ciki yana addu’oinsa kafin ya fito ya nufi hanyar gida ta cikin wani layi mai yawan bishiyu. Sai dai me? yana shan kan kwanar yaji gabadaya duk wata jijiya ta jikinsa ta shiga aiki da sauri.

Tar! idanunsa suka hango masa sa’adha ta fito daga wani k’aramin gida, fararen hannayenta sun sha jan k’unshi mai kyau, sannan ga bak’i a sama tana ta hura shi da iskar bakinta, tana yi tana wa k’awarta mitar zaman bin layin da suka yi, wanda duk da tazarar su yana jiyo komai.

Saura kad’an yayi wani abu daya kusan manta shi a rayuwarsa, saura kad’an ya sulale yabi jikin bishiyar bayansa sanda idanunta suka d’ago suka kalle shi.Da sauri ya janye idanunsa daga cikin nata sannan ya d’auke kansa yayi kwanar dake damansa, ya zaro wayarsa ba tare da ya ko juyo ba ya b’acewa ganinta.

A lokaci daya nanne taji guntun murmushin da take shirin yi yabi iska, wani abu mai kama da mamaki ya maye gurbinsa, ta rufe idonta ta sake bud’awa ta kalli inda ya tsaya sannan kwanar da yayi, tabbas ba karya idanunta suka mata ba ya ganta, ya ganta ya kalleta sannan ya d’auke kansa yayi gaba.

“Me kike kallo ne wai? Kizo muyi gaba baza mu sami abin hawa ba anan.”

Ta tsince muryar rahma daga nesa kamar ba’a kusa da ita take ba, ta juyo da sauri tace.

“Rahma kinga mutumin daya wuce yanzu?”

“A ina?”

“Anan wajen, wanda yayi can kwanar da light blue kaya.”

“Anya? kin san na sunkuya d’auko kudin mota….waye shi?

“Wani ne.” Ta fada a hankali idonta na kallon hanyar, kamar tana jira ya dawo ya fada mata dalilinsa na kin mata magana, Toh amma saboda me? Ta tambayi kanta, bata da wata alak’a dashi, me yasa in ya ganta zai mata magana? Don kawai ya taimaketa sau d’aya kuma ya tambayi sunanta a ranar?

“Nanne muje mana la’asar fa ta wuce, ko sallah bamu yi ba.”

Ba yadda ta iya haka tabi Rahma da hannayenta a d’age suka yi titi.

Har bayan magriba wani iri take ji a jikinta, ta rasa kuma dalilin hakan, ko don zuciyarta ta damu da son sake ganinsa ne a baya, yanzu kuma ta ganshi ya d’auke kansa.

Ta dafe kanta sanda take zaune a kan kujera tana hango tarin ‘yan aikin da suka baje a tsakar gida anata packaging sabulun salo dana magarya a roba wanda za’a rabawa mutane jibi ranar wankan amare. Tayi tunanin tashi daga wajen amma bata san inda zata ba, don koina a gidan cike yake da mutane, hatta dakinsu yanzu tarin ‘yan niger ne fal, ‘yan uwan inna tsofaffi sun had’u anata hirar yaushe gamo, inna ta basu labarin abubuwan da suka faru da ita, suma su bata nasu na can.

Rahma ta d’ago mata hannu daga tsakiyar matan wai tazo ta zauna amma ta girgiza kanta. Abu na karshe da zata so yanzu shine ta shiga cikinsu duk da cewa anata irin hirar da take so ana dariya, don sun samu taimakon wasu ‘yan niger masu barkwanci, amma zuciyarta ba dadi a lokacin.

“Ko zaki taimaka mana da kujerar nan dan Allah kitso zamu yi.”

Ta juya taga wata mata tsaye akanta da kibiya a hannu. Ta san ta sarai daga cikin ‘yanuwan mama halime take, su da suka fara zuwa tun cikin sati masu aurar da ‘ya’ya biyu.

“Gaskiya ba yanzu zan tashi ba.”

“A’ah uwata…” mama Azumi da zata wuce ta katseta.

“…Taimaka ki basu mana, gidan ne yayi albarka duk kujerun an zaune.”

Kamar baza ta tashi ba, don dai kawai mama azumin ce yasa ta mike.

“Ko kefa, zo muje ta kicin akwai abinda na ajiye miki.”

Dama yunwa take ji, don sun dawo daga kunshin ta tarar jollof akayi tun rana tayi shape din flask, ita kuma taki ci don babu ko zob’o tunda yanzu yawan gidan ya kai intiha.

Ta tarar cake ne k’anana wajen guda takwas, ta karb’a da murna ta dauki ruwa sannan tayi wajen compound, ta samu k’arshen barandar d’akunan mazan ta zauna, ta zame dankwalinta saboda zafi da ake d’anyi a lokacin.

Bata ci ya kai uku ba sanda taji Alamar an turo gate din gidan, wannan k’iii! din k’ofar ya shiga kunnuwanta, ta rufe idonta gami da d’an jan tsaki, don ta san in d’aya daga cikin su ya sulaiman ne yanzu za’ace ta shiga gida, musamman ace da wani abokinsu suka shigo.

“Sa’adha..!”

Wannan muryar mai zurfi da taushi ta shiga kunnenta, tana juyowa taci karo dashi tsaye daga d’an gaba da ita. Bakinta ya bud’e saboda mamaki, a lokaci daya taji zuciyarta da tayi sanyi ta shiga bugawa da karfi.Tayi saurin jawo mayafinta ta rufe gashinta.

“Yaushe ka shigo? ta ina?” +

Ganin gashinta da yasha gyara dakuma hanbayenta masu kunshin nan yaso dauke hankalinsa, don sai da yayi shiru sannan ya amsa a hankali.

“Yanzu na shigo ta gate.”

“Dama kana shigowa gidan nan?”

“Wani lokacin ina zuwa wajen umar.” ya nuna kofar d’akin dake gefenta.

Ta mike da sauri kafin tace.

“Ina ga baya nan yanzu.” Bata jira komai ba ta juya tayi hanyar komawa ciki.

“Sa’adha..!”

“Ba wajensa nazo ba, ke nake son gani.”

Bata juyo ba ta girgiza kanta.

“Ba zan iya tsayawa ba, in wani ya ganka za’a min magana.”

“I’m sorry, d’azu na ganki bamu gaisa ba ina sauri ne.”

Kanta yayi duumm! Ta kasa gasgata abinda kunnuwanta suka ji, da gaske shi din ne? Ya shigo har compound d’insu don kawai ya bata hakuri? ta juya a hankali rik’e da plate d’in cake d’in. Yana tsaye kuwa, ya d’an biyo bayanta kad’an.

Dogo ne sosai, ba fari ba sai dai yana da hasken fata irin ta murjewa, sumar kansa a dunk’ule take kamar ta jinsin larabawa, ta taho tun daga saje ta zagaye bakinsa, Ga wani irin k’anshi dake tashi mai dadi wanda tabbas daga shi din ne, Taji bugun zuciyartu ya karu akan da, kamar yana barazanar tarwatsa kirjinta.

“Ba komai, sai da safe.” muryarta da kadan tafi rada.

Imran yayi ajiyar zuciya sanda ta b’acewa ganinsa, bai san me yake shirin faruwa ba dashi ba, amma zai daurewa koma menene tunda yanzu ya sauke wannan nauyin, nauyin daya dame shi tun lokacin da ya ganta d’azu yayi tafiyarsa.

A lokacin ya dake zuciyarsa ne cewa zai cika alk’awarin daya d’aukarwa Jaamil da Naani, na cewa ba zai bari wani abu ya shiga gabansa ba, zai tafi da tsarinsu kamar yadda suka shirya komai a farko, amma tunda ya koma gida ya kasa wannan dauriyar, ya kasa cire fararen idanunta daga ransa, yadda ta bishi da kallon mamaki sanda ya juya, da yadda take ta kallon hanyar da yabi, yana iya ganin zafin dake cikin idonta tunda daga nesa.

Rauninsa kenan a duniya, baya taba son ya zama sillar bacin ran wani, ya shigo cikin rayuwarta da salama ba zai so ace hakan ya zama rabuwarsu ba.

Da wannan tunanin ya samu kwarin gwiwar zuwa wajenta. Ya gayawa kansa cewar abinda Naani da jaamil ke tunani ba zai taba faruwa ba don yazo wajenta sau d’aya, yana da enough focus d’in da ba zai taba zama distracted ba, sai dai ma ya zama distracted in wani abu na damunsa.

Yayi saurin yin baya sanda wasu mata suka fito daga cikin gidan rike da kaya niki-niki, ya matsa wajen duhun rumfar adana motocin dake gefe, sannan ya bar wajen, a tunaninsa ya barshi kenan har abada.

Sai dai kuma wata kaddarar bata ma soma ba! A daidai ina muka tsaya wancan karon?”

Muryar da kaushi ta fita, cikin wani irin amo mai girgizawa, don yana iya ganin yadda ‘yan k’ananan decor’s d’in dake kan center table na gabansa ke jijjigawa.

Imran ya d’ago da idonsa ya kalli manyan-manyan hallitun dake tsaye a bayan kujerar falonsa, basa bada ko karamin motsin da zai nuna cewa suna raye.

A tsakiyarsu akwai wani dunkulallen haske dake lilo a iska, haskensa ya tarwatse ya baje ko’ina a cikin d’akin, daga kasa kuma jikin inuwarsa, wani tambari ne ya fito, tambari irin na adon sarautarta.

“A ina muka tsaya yarima…?”

Muryar tasa kowacce tsigar jikinsa mik’ewa, A kullum girmanta da matsayinta karuwa suke a wajensa.

“Ki min gafara Naani, abinda kike tunani ko kadan ba haka bane, a wancan lokacin kinyi fushi ne dani sosai shi yasa na kasa miki bayani, amma an samu sab’anin fahimta ne tsakanina da jaamil, don kinfi kowa sani na a duniya, kinfi kowa sanin cewa ba zan taba yin abinda zai bata ranki ba.”

Maganarta ta fito a gajarce.

“Ina saurarenka.”

Ya gyara Gwiwoyinsa dake zube akan tattausan carpet d’in sannan yace.

“Farkon zuwana garin nan, na had’u da ita ne a layin da nake tunanin zama, daga baya na fahimci wajen yana da yawan jama’a sai na barshi, kuskurena na farko shine ban rabu da ita ba, na cigaba da bibiyarta bayan nan, kuskurena na biyu shine a lokacin da jaamil ya gane, sai na maida abin kamar sigar tsokanarsa, har nayi mata magana don ya gani, amma babu komai a raina game da ita, kuma tun a huduwarmu a baya nayi miki rantsuwa cewa ba zan kara zuwa kusa da ita ba.” 1

Shiru mai yawa ya biyo kafin murya ta sake fitowa.

“Me ake ciki game da tsarinmu?”

Ya lumshe kyawawan idonsa sannan ya amsa.

“komai yana tafiya daidai, bana tunanin zamu kai watannin da aka d’iba don YA RIGA YA FARA YARDA DANI YANZU!”

****

~_~ Ta zama tazama…ta zama d’auko riga, tazama d’auko wando, ta zama tazama…ta zama dama furar nan…! ~_~

Wak’ar ta karade katon filin farfajiyar gidan su Nanne, wajen ya tsaru sosai kamar bashi ba, yasha ado da kayan al’ada na gargajiya kala-kala. Rumfar da amaren ke zaune a tsakiya akayi ta kuma ba’a shimfida komai a k’asa ba saboda ‘yan kujeru ne irin na tsakar gida guda hud’u inda kowacce amara ke zaune akan d’aya, a gefenta da katuwar roba da aka cika da ruwan d’umi, duk wanda yazo gaban amarya zai d’ebi ruwan ya watsa a jikinta, sannan ya ajiye gudunmawarsa a k’asan k’afarta wanda ake kira da ‘kudin sabulu.’

Amaren gabadaya farin zanin da inna ta sak’a sukayi d’aurin k’irji dashi sai da kowacce tasa farar t-shirt daga ciki kuma sunyi yafen farin mayafi. Sannan gabad’aya ‘yanmatan da suka sa anko daga kowanne b’angare na amaren, ankon plane zani suka yi suma da riga buba.

Nanne na zaune ita da Amina daga can kujerun baya suna cin gasasshiyar awarar nono wadda aka raba a wajen da kuma fura. Itama irin ankon ‘yanmatan ne a jikinta, sai dai ba ko hoda a fuskarta kuma ta cokala d’auri gaban goshi.

“Wallahi da kin fada min da nazo munje gidan kunshin nan tare, yaushe rabon hannuna da lalle.”

Nanne ta juyo daga kallon wasu ‘yanmata a gefensu tace.

“Nima rahama ce ta takura min, kwata-kwata banyi niyyar kunshin ba, kuma in gaya miki gidan d’an banzan layi kamar da sallah, tun wajen goma fa muka fita bamu muka dawo gidan nan ba sai bayan la’asar.””Ai baku yi jiran banza ba, ta iya wallahi.”

Nanne ta kalli hannunta sannan tace. +

“Kuma lallenta nada kyau, tunda fa tun ran asabar, gashi kamar yau akayi.”

“Ai gaskiya zanzo bayan bikin nan ki raka ni.”

Har Nanne zata ce wani abu wata murya ta tsaida ta.

“Kinga dan Allah tambaya muke.”

Ta juya taga d’aya daga cikin ‘yanmatan dake gefensu ce ta d’an juyo da kujerarta saitinsu.

“Naga kamar kin san ‘yan gidan nan ne?”

Nanne ta d’aga kai tana kallonta.

“Dan Allah kin san wannan?”

Ta miko mata hadaddiyar wayar hannunta, Nanne na juyo da fuskar wayar taci karo da hoton Suraj tar! akan screen d’in. Wani hoto da salim ya dauke shi a jikin motar ya Ahmad, a ranar sati biyu kenan da bikinsa sunje gidansa gabad’ayansu ganin Amarya.

Amina ta sunkuyo da kanta kad’an tace.

“Ba suraj bane wannan?” Nanne ta mika wa yarinyar wayarta.

“Eh na sanshi anan gidan yake.”

Da jin haka ta juya ta kalli sauran k’awayen nata biyu.

“Kun ji koh? Na gaya muku wallahi shine….” ta dawo kan nanne.

“Dan Allah yaushe ya dawo daga cyprus d’in?”

“Wace cyprus?”

“Inda yake karatu..”

Nanne ta kalli Amina suka kyalkyale da dariya.

“Shi yace miki a cyprus yake?”

“Eh mana ba’a can yake karatu ba?” d’aya kawar ta tambaya.

Nanne tayi k’okarin danne dariyarta.

“Tsaya ma tukunna wane karatun?”

“Degree mana…” Aiko bata k’arasa ba suka sake fashewa da dariya.

“Dan Allah tambayarku fa muke…”

Basu ko kulasu ba saida suka kyakyata mai isarsu sannan da kyar Aminah tace.

“Yi hakuri, wallahi k’arya yake muku, kwanan nan suka gama waec da neco a makarantar mu.”

“Ke toh anya kuwa shine, shi fa har facebook account dinsa gabad’aya komai na can ne.”

“Ai shine…” d’ayar ta karba.

“…Ba kince mana harda outside number yake kiranki ba?”

Nanne ta kalle su tace.

“Wallahi duk karya ce, in gaya muku nan ne gidansu kuma ni k’anwarsa ce, in baku yarda bama kuzo in kaiku ku gaishe da Babarsa.”

“Dan Allah da gaske kike?”

Ta sake kyalkyalewa da dariya kafin tace.

“Wallahi da gaske nake muku, d’azun nan ma ya gama fito da kayan wankinsa akan barandar can, ga d’akinsu can a kulle.”

Ba shiri kuwa suka matso da kujerunsu kusa dasu. Yarinyar tace.

“Shifa ce min yayi a Abuja gidansu yake, toh d’azu da muka je sallah a cikin gidan sai naga wani family hoto a d’akin da muka shiga, harda wani a ciki kamar shi, muka yi ta doubting, shine fa na tambaye ku.”

Tana maganar kamar zata yi kuka, Nanne na k’ok’arin matse dariyarta amma ta kasa saboda Amina data sunkuyar da kai tana ta kyalkyalawa tana mintsininta.Dan Allah ku bar dariyar nan, kuyi magana mana…” +

“Yo me zamu ce? Karya ce dai ya riga ya tafka muku, don wallahi makarantar daya gama ma a tsakiyar garin nan take ba wani waje ba, kuma ko result d’in waec d’insu bai fito ba balle ya tafi wata jami’a, kullum suna gidan nan shi da twin brother dinsa, in banda bacci ba abinda suke sai yawo…”

Tun suna dariyar su biyu, har k’awayen yarinyar ma mai suna Ameerah suka bi sahun su, aikuwa basu rabu dasu ba sai da nanne ta sauke musu duk wani in and out na Suraj data sani, harda kuwa abinda yayi tun yana k’arami data ji labari.

Bayan sun rabu dasu, suka matsa wajen rumfar amaren Aminah tace zata dauke su a hoto, suka yi hotuna kuwa masu kyu abin mamaki jamila sai washe musu baki take, lalle buri ya cika an samu abinda ake so, Nanne ta ayyana a ranta. 1

Suna fitowa daga wajen, wayar Aminah tayi kara.

“Anzo d’auko ta, sa’adha ba zanzo kamu gobe ba sai jibi ranar mother’s eve.”

“Toh shikenan, bari in d’auko miki dankwalina ki taho min da mayafi kalarsa a wajen Aunty maimunah (yayar Aminan).”

“D’an 3 thousand ko 5?”

“Three d’in dai, an gaya miki kudi ne dani.”

“Toh yi sauri don Allah hashim azalzala ce dashi wallahi.”

“Kije wajen motar, zan same ki acan.”

Ta cikin tarin jama’a da kuma kujeru nanne tayi ta kutsawa har taje can k’arshe wajen fulawoyi inda inna ke zube akan carpet da jama’arta ‘yan tsofaffi wanda basa iya hawan kujera.

Da kyar ta samu innar ta saurareta saboda jama’ar da suka yanyanmeta anata gaisuwa da Allah sanya alkhairi.

“Inna muk’ullin wardrobe zaki bani.”

“Me kika ce?”

“Mukullin wardrobe wanda nasa a jakarki d’azu.”

“Yana ina?”

“A cikin jakarki, na saka d’azu.”

Ta miko mata ‘yar purse d’in hannunta gabadaya, ta d’auka sannan ta mika mata. Da kyar ta iya tsallake su ta wuce, saboda kowa duk’awa kawai yake ana gaida ‘yan tsofaffin.

Daga cikin gidan, sautin kid’an kad’an ake ji sannan ba mutane sosai, daga wajen kicin ne kawai da mutane suma kad’an. Har zata hau benen ta gano rahama da wata sun jawo buhun takeaway d’in sabulun salo,magarya da kuma turaren wuta wanda za’a rabawa mutane. Tausayinta ya kamata don wallahi tun yanzu ta san rahma ta gaji, sun aikatu sosai, ga kuma biki yanzu aka fara. Ta hango ta itama.

“Nanne akwai na k’awayenki dana ajiye a kicin, bari mu kai wannan in d’auko miki.”

“Kinga ni mutum daya fa na gaiyata, kuma yanzu zata tafi ma, miko min d’aya kawai.”

Ta jikin hannun benen ta miko mata sannan suka yi gaba.

Tun daga k’ofar d’akin nasu ta jiyo karar tv na tashi, mamaki ya kamata don ta san tunda satin bikin nan ya kama ba wanda yake kunna tvn. Ta d’an ja tsaki.

Watakila ma yara ne, tunda kowacce ta jajibo ‘ya’ya anzo an cika musu gida.

Ta k’arasa ta kashe ta sannan tayi cikin d’aki. Ta bud’eshi da mukulli don shi a k’ulle yake saboda sha’anin biki, ta kunna fitila sanna ta bud’e wardrobe d’in ta shiga laluben d’ankwalin a wajen sababbin kayanta.

Kawai sai jikinta ya bata alamun wani ya shigo cikin d’akin yana tahowa wajen wardrobe din. Ta rufe murfin ta juyo, sai dai me? Babu kowa.

Ta d’an tsaya da mamaki sannan ta sake bud’e wardrobe din. Sai dai hannuta na kaiwa kan d’ankwalin ta sake jin alamun mutum na tahowa, ta tsaya tayi shiru tana saurare, sai da taji motsin ya karaso dab! da ita sannan ta sake rufe wardrobe d’in da wani irin sauri ta kalla…..

Irin dai d’azu babu kowa ba alamun mutum, sai dai kuma idonta ya kula da kofar d’akin tana lilo a hankali. Ta janyo mayafin da sauri kawai ta fito, ta kulle d’akin sannan ta juyo, abinda ta gani ya razana ‘yan hanjin cikinta. Tvn data kashe yanzu an sake kunnata, amma yanzu ba sound ko kad’an sabanin d’azu da yake kusan a k’ure.Waye a d’akin nan?” Ta fad’a a fili tana kallon kowacce kusurwa. +

Shiru ya biyo bayan maganarta, babu motsi a ko’ina sai tvn dai dake ta aikinta tana nuna tashar cartoon. Tayi ajiyar zuciya sannan ta k’arasa ta sake kashe ta.

Sai dai kuma me? Tana juyowa taci karo da kofar falon a rufe. Wani abu da rabon data ga anyi baza ta iya tunawa ba, don ko da daddare cikin d’aki kawai suke rufewa ita da inna. Sannan labulen ma da ya rufe k’ofar an d’age shi an mak’ale a gefe.

Ta k’arasa da sauri ta murd’a handle d’in.

A rufe take gam! Alamun da muk’ulli aka k’ulle!

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *