WANI AURE
CHAPTER 17
deeni agabana zaka km dukan min yarinya wlh kafita idona dukiyar wannan dukan daka
mata Bai ishetaka ba Sai kazo gabana kakara mata. Yace wlh idan bata fidi abinda tayi da
bakinta ba Sai na tabbatar dana karyata kafin nabar gidan nan., atsorace zeenat tasoma
yiwa ummi bayanin abinda tayi da bakinta.
Kukan Ummi ya tsaya cak tayi sororo tana duban Zeenat jin abinda take fada tamkar a
mafarki ba gaske ba .can km Ummi ta sake rufe deeni da wani sabon fada dan ta zubar da
ciki zaka kashe min ita, haka Allah ya rubuto cikin ba masu rayuwa bane a doron kasa dan
haka hakuri kawai zakayi da yadda Allah ya kaddaro. Allah zai sake baku wasu.
deeni da ranshi yaga dagulewa ya baci da kalaman mahaifiyarsa. wacce yake ganin duk
duniya bashi da tamkarta ,shi yake daita ita take dashi km yasan duk son datake wa Zeenat
din bayansa yake yasan ta dai fadi haka ne kawai badan ranta yaso ba.
A sanyaye Yace yanzu first lov wannan kaddarace ko son zuciya?
ta biyewa ra’ayinta tayi abinda ranta ke so shine zakice “haka Allah ya kaddaro’ Ummi
tashiga girgiza masa kai
Kadai kayi hakuri nace bana son tashin tashina abar zance kawai .
Yace bbu wani zance da za’a dan Ga sakamakon abinda ta aikata min nan a hannuta na
bata,sai km tabi wani jirgin ba bana deeni ba.
ya juya fuuuuuu cikin tsammanin bacin rai ya bude kofar ya fita tare bugo kofar da karfi.
Ummi ta juyo ‘ahan kali tana kallon yadda diyarta ta dawo wata halita daban.
tace yanzu Zeenat wani laifi na aikata miki da na cancanci kiyi min irin wannan sakayar .
Yanzu kin kyauta abinda kike yi , gabadaya tsoro ya sake cika zuciyar Zeenat Tunaninta ko
dukanta Ummi zatayi dan haka tasoma ja da baya. Ummi tace Ina zaki Zeenat ni bbu
abinda zan miki , Zeenat ta durkushe gaban Ummi tare da kamo kafafunta ta rike gam Tana
kuka” Dan girman Allah Ummi kiyi hakuri wlh sharin sheidan ne Ummi kiyafe min wlh
bazan sake kibawa yaya hakuri shima ya yafe min Dan takaicin Ummi rasa me zata km
cewa Zeenat tayi dan haka ta rungumeta ajikinta suna kukansu tare.
Kafin kace me labari ya bazu acikin estate Zeenat ta zubar da ciki.
Inna lillahi wa inna ilaihi rajiun me naje ji kuke cewa wai Zeenat ta zubar ciki sau ba adadi ?
inji inna kakar Zeenat.
Data shigo parlour habibu danta dukkansu sukayi tsit shi da matansa da yayan Zeenat din
da suke uba guda “suna kallonta wai ba magana nake daku ba ,kum mayar dani tamkar
wata yar isaka kuna kallona.
“mahaifin Zeenat ne ya yi karfin halin sauke ajiyar zuciya Yace nima yanzu yasir yake gaya
min
inna ta fashe da wani irin matsanancin kuka tare da daura hannu bisa kanta tace wayyo
Allah nashiga uku ni patsima amman anyi gatalaliyar muguwar yarinya dan ubanta dan
nawa ta zubar tasan burin da naci akan cikin nan ,shegiya yarinyar ni da nake son naga
nafi kowa zuri’ar maza da mata acikin dagin nan shine dayake Yar iska ce ta zubar ciki.
Kai yasir maza muje ka saukeni a gidan inci uwarta har da kakarta ba indiya.
yasir ya girgiza kawai dan gabadaya maganarta dariya ta bashi gashi bbu damar yin
dariya dan ya hadiye dan yasan halin maseefarta Yace Ai Zeenat din ma tana gida tun jiya
Tace shine dan an raina mu shiyasa ita uwar rikon nata baza tazo tagamana “amman bbu
laifi ta kada kai tana kokarin barin dakin tace naje dakaina can naci mutuncin jairar yarinya
Dadaren deeni ya tafi gurin big Dady sakamakon turowa da yayi yazo yana son ganinsa.
Zaune yake agabansa shida fk da yayansa mahamud Sai wasu daga cikin family deeni
yasawa big dady kukan abinda Zeenat tayi masa kasa yarda big Dady yayi duk da yaji
dama. sai da faruk dake zaune a parlour,n ya sake tabbatar musu da haka ne jikinsu yayi
tsanyi big Dady Yace yanzu ita Zeenat din ce taiya aikata haka.
Inna lillahi wa inna ilaihi rajiun from no there suka ji suka ji muryar inna tana salati tashigo
parlour,n big Dady da gudu kmr an karota a rude tace kai zubairu kai zubairu kaga irin
dukan da wannan mugun yaron yayiwa jikata tamkar Bai san ciwonta ba.
big Dady dake alajabi abinda akace Zeenat tayi ya dago da fuskarsa yana duban inna tare
da nuna mata gurin zama. Zauna inna.
zaman may zanyi Dan wulakanci bazan zauna ba.
deeni dake zaune yaja tsaki wanda sai lokacin inna ta farga dashi.
ashe ma yana gurin.
ta fashe da kuka tana kallo tsaitin da deeni ke zaune tace Allah ya isa ban yafe ba yanzu ka
iya jikata irin wannan duka kmr zaka kashe min ita.
dan ta zubar da wannan wahalallan cikin naka may shirin kaita lahira .
a zafafe deeni Yace Ai abinda naso yi kennan na aikata lahira sannan na kawo muku
gawarta inyaso nima akasheni.
cikin kuka tace yanzu zubairu kana jin abinda wannan jairin may mugun kan yaron yake
gaya min ko.
To wlh duk shegen da Bai km dukanta ba Bai haifu cikin uwarsa da ubansa inji cewar inna
big dady ya kalli deeni Yace bana son ka sake cewa komai.
sannan Yace inna ki zauna amiki bayanin abinda ya faru.
taki zama sai maseefa take zabgawa akan andaki jikarta.
bayanin me zaka min zubairu byn nasan wahalallan cikin wannan jairin ta zubar ta
hutawa ranta.
da kyar big Dady yasamu ta ,zauna akamata bayani komai tundaga kan cikin farko da
Zeenat ta zubar har zuwa na yanzu.
tana gama jin ta mike tsaye Tana jan tsaki mtssss tare da tacigaba da zagin deeni .
Dan ta zubar da cikinka din baza shine zaka mata irin wannan duka , mara mutunci
kawai wlh bazan yarda ba,
Ran deeni ya sake mugun baci ” dan haka a hassale Yace da bazaki yarda ba sai kizo ki
rama mata tunda dukan dana mata yayi miki ,zafi.
, Zubairu kana jina da wanna gantalalan yaro ko.
Wlh koban rama mata ba,zamu barkar da Allah yayi mata bakar sakayar da bata da
magani
wlh ni karki dameni dan zan iya huce haushina akanki inji cewar deeni .
zaka dake ni nima ta matso gabansa tana zaka dakeni tantirin mara kunya kawai may dan
banzar mugun halin tsiya.
Sai da Big dady ya dakawa deeni tsawa sannan yayi shr ya rabu daita tana zuba maseefa iri
iri.
deeni ya mike da kyar yana kallon big dady miryasa can kasa Yace sai da safe ni zan wuce
ganin haka yasa shima fk ya mike yana mara masa baya.
Sai huci inna take maza ka dawo nan ka kawo min takardar sakin jikata dan wlh bazata km
cigaba da zama dakai ba mugu azalumi kawai.
Deeni dake shirin barin parlourYace tun yaushe aikin gama yagama Ai ko baki ce ba nima
bazan km,zama daita ba.
ta sake kurma kururuwa ihu yanzu kasar min jika byn kagama moremata jiki to Allah ya isa
wlh km sai kaga karshenka.
shi dai Bai km cemata komai ba ya karasa ficewa daga dakin.
Daidai kofar gidan fk suka ja suka tsaya faruk Yace gaskiya aboki banji dadin sakin dakawa
Zeenat ba.
dan kasan Ummi zatashiga damuwa,akan haka fk sakin Zeenat danayi shine yafi alkhari
da zaman Ify atsakaninmu ,dana dinga mata ciki Tana zubarwa a rariya gara nabarta kawai
fk Yaceto yanzu haka zaka cigaba da ?
deeni ya daga masa kafada tare cewa uhmmmm zaman haka zai fiyye da dai zama da
Zeenat.
nan dai fk yayita bashi shawara akan yayi hakuri ya maidaita tunda saki daya yayi mata,
Yace Nagode sosai aboki zan duba maganar idan hakan zai yiwu sai zuwa gobe kennan
tare da yiwa junanasu.sallama.
tare da yiwa junanasu.sallama.
Karfe tara daidai deeni yashiga gidansa ya haura sama,a sanyaye ya bude kofar dakinsa
yashiga yasoma cire shirt din jikinsa da dogon wando ya rage daga shi sai singlet da boxes.
yayi kwanciyasa kan bed dinshi tare da runtse idanushin yana jin zafin da radadin abinda
kakar Zeenat tayi masa.
Ga tashin hankali daya baro umminsa ciki yarasa meke masa dadi a rayuwarsa.
Gabadaya komai ya dagule masa waje daya mafuta kawai yake nema.
lokaci may tsawo ya dauka kwance yana tunani abinda yaka mata yayi batare da bacci ya
dauke bashi ba.
A ranar sam deeni kasa bacci yayi saboda tsantsar fargaba da tunanin da yake ciki akan
hukuncin da umminsa zata zarta akansa.
” dan Bai san abinda zai faru ba akan sakin da yayiwa Zeenat. farinciki ko akasin haka.
ganin kwata kwata bacci yaki samuwa agareshi ne Yasa ya mike ‘ahankali ya tashi tsaye
yashige bathroom, yayi alwala yazo yasoma jero nafiloli yana may kaiwa Allah kukansa.
koda ya idar sallah ma guri yasamu yayi kwanciyasa.
‘Sai daf da sallar asuba yasamu bacci ya daukeshi kwata kwata bacci daya samu baifi na
awa daya ba ya sake mikewa yayi alwalar sallar asuba yana zaune yana lazami har garin
Allah yawaye
Misalin karfe bakwai daidai yayi wanka sbd yana son fita da wuri sbd matsalar hoidop
din da ake fama dashi acikin garin Lagos sakamakon gyare gyaren titi da ake.
yana tsaye agaban mirrow yana shirin zuwa office amman gabadaya tunani umminsa
ya addabe zuciyarsa duk da ruhinsa.
“ranshi a dagule yake shirya jikinsa sbd yasan umminsa nacan na fushi dashi Yana
wannan tunanin haryagama shirinsa tsab.
Zaune yake a cikin tafkeken office dinsa may zagaye da makeken tablet cike da tarin file
files da takardu.
system din dake gabanshi yana aikin tura sakwanni ne” ya dan ture gefe tare da afkawa
cikin duniyar tunani abinda Zeenat tayi masa.
hakika Bai san yadda zaiyi da damuwar data kunsa masa ba.
, Sam yakasa hakura da abinda tayi masa Sosai yake jin zafinta har cikin zuciyarsa tsawon
lokaci Yana zaune yayi zurfi cikin tunanin .
STORY CONTINUES BELOow
Wani abokin aikinsa manir ne yayi kundin balar shigowa cikin office din” byn nouking din
da yayi tayi yaji shr ba respond.
Zaune manir ya samu deeni yayi shr yana duniyar tunani’ kusan Kira biyu yayi masa”
amman ko daya deeni bai san yana yi ba Sai ana uku ne yayi firgigib ya ankara”
da an shigo office din.
A wayance ya waske. Naunauyen ajiyar zuciya ya saki tare maida hankalisa sosai kan manir
Ahankali manir yasamu gurin ya zauna akan daya daga cikin kujeru guda 2 dake ajiye dan
zaman baki .
Shr shima Yayi ya zubawa deeni ido kawai yana kallonsa tare da nazarinsa “tsawon lokaci
suna kallon junansu batare da kowannesu Yayi tunanin yacewa dan’uwansa komai ba.
Har Sai da manir yayi karfin halin cewa .
wato har yanzu dai matsalar Zeenat din ce taki ci taki ciyenwa?
dayake yasan komai game da abinda ya faru.
a ganina zuwa yanzu yakamata ace kasawa ranka salama akan maganar yarinyar nan. kayi
hakuri kabarwa Allah komai.
deeni da Yayi shr kawai tare da kamo lip’s dinshi na kasa yana cizawa ‘ahankali’ahan kali
shi kadai yasan yadda yake jin zuciyarsa da gangar jikinsa ‘ahankali muryarsa a sanyaye
yace uhmmmm duk maganarta na damuna.
amman nafi tunanin halin da first lov zata shiga ne kasan yadda Zeenat din take a
gurinta.
Manir yayi shr ya jima yana jinjina girman alamarin sannan ya numfasa yace deeni Ina kan
hanyata yanzu ta zuwa llorin daman sallama nazo muyi .
bbu wani hanzari dazan iya maka akan maganar ka matarka daya wuce.
Sai km ya dan mike daga kan kujerar dayake zaune ya rankwafa gefen deeni tare da kai
bakinsa daidai tsaitin kunnen deeni, zo kaji wata magana.
,kusan minti biyu manir yayi Yana tsarawa deeni zance sannan ya dauke bakinsa yakoma
gurin zamansa.
” a razanane deeni yake bin manir din da wani irin matsanancin kallon tare da mamakin
abinda Yace.
manir yacigaba abinda kawai zakayi kennan karaba kanka da wannan damuwar dake
damunka kada zuciyarka ta samu matsala.
‘Ahankali deeni ya shiga girgiza kansa yana kallon manir batare da ya iya ce masa komai ba
haka kawai shine maganin matsalarka Amman ka zauna kayi tunanin shawarata da kyau
inji cewar manir.
Da kyar deeni ya iya bude bakinsa da Yayi masa nauyi Yace anya kuwa manir zan iya abinda
ka bukaceni da nayi kuwa?
‘manir Yace zaka iya mana Sai dai idan baka gadama ba.
deeni ya sake girgiza kansa,kai bazan iya ba wlh ..
Manir ya mike tsaye yana mikowa deeni hannunsa ‘ bbu dole fa cikin shawarata kaduba
kagani idan zaka iya kawai kayi “ni zan wuce Sai na dawo, jikin deeni a sanyaye shima ya
mikowa manir hannu sukayi musabaha.
manir ya wuce Yana cewa malam katashi tsaye kawai kayi abinda ya dace ba kullum tunani
ba.
Deeni ya jima zaune yana saka da warwara akan zance da manir yayi masa wanda gaf
maganar take da tarwatsa masa zuciya.
‘Ahankali cikin sanyi jiki ya, mike tsaye ya suke hannuwansa duka cikin aljihun wandonsa
yasoma zariya Yana zagaye cikin office din.
‘sannan’ ya dawo ya zauna a gefen tablet dinsa yana jinjina girman alamarin duk ilahirin
jikinsa sunyi masa mugun sanyi ‘ahankali ya sake mikewa ya koma kan kujerarsa ya
zauna yana son yacigaba da aikinsa idanushi suka sauka akan dan karamin fream din
dake ajiye akan table.
ya zubawa umminsa ido kawai yana kallonta shi kansa ya amince tun ba yanzu ba
umminsa na matukar son shi da kaunarsa fiyye da komai.
” shima km haka yake matukar sonta tamkar rayuwarsa.
duk duniya ita kadai gareshi ‘ahankali ya kai hannunshi ya dauki karamin fream din
yana cigaba da kallon umminsa” yayi matukar kewarta ” kusan kwana biyu Keenan
rabonshi da sanyata acikin idanunshi wanda km hakan ta faru ne a sanadiyyar Zeenat
,bancin haka yasan zuwa yanzu da tuni umminsa ta nemishi da kanta.
runtse idanushin yayi sosai Yana jin yadda kaunar mahaifiyarsa ke ratsa zuciya da gangar
jikinsa “tsawon lokaci idanunshi na runtse sannan ya budesu fes yana sake kallon
umminsa tare da sake jin haushi da takaicin Zeenat a ranshi.
Take yaji zuciyarsa tasoma amince masa daya dauki shawarar da maniryabashi Kodan
samun natsuwasa da km kuntatawa zuciyar Zeenat din.
sannu ‘ahankali ya maida hoton Umminsa ma,ajinsa yacigaba da abinda ke gabansa.
Gabadaya parlour,n big Dady cike yake da manya daga cikin en’uwa na family muhd bello
khaliyal.
Big Dady ya kalli gefen da Zeenat take zaune rakube tare da sunkuyar da kanta kasa tana
xubda hawaye.
” Yace yanzu Zeenat kin kyauta kennan da abinda kikayi ?
mezakicewa mahalincinki idan kin koma gareshi’ ashe daman karamin tunani gareki
bansani ba “Zeenat dai kanta na kasa tana cigaba da zubda hawayen nadama ta kasa
cewa komai big Dady ya girgiza kanshi kawai ‘sannan Ya maida kallonsa ga deeni
Kai km kuturu sarkin zuciya” Ai ba a yanke hukunci cikin fushi kwata kwata bamu ji dadin
hukuncin da , son ranka da kayi ba .
,domin kuwa har zuwa yanzu a karkashin ikonmu kake, yakamata ace ka kawo maganar
gabamu kafin kazarta da komai .
Dan haka muma zamu nuna maka har yanzu kai din a karkashin mu kake km abin ikonmu.
Big dady ya sake juyowa inda Zeenat take ” ke… saki nawa ya rubuta miki?
cikin kuka muryata na rawa tace nima ban sani ba.
Ina takardar sakin take ‘ahankali ta tura hannuta ta zaro farar takardar daga gefen zaninta
ta Mika masa.
Big Daddy ya karba ya bude Yana dubawa yaga ashema saki daya ne ,take yaji wata
natsuwa da kwanciyar hankali sun shige shi hamdala yayiwa Allah sannan ya sake duban
deeni.
yanzu me yakamata kayi tunda saki daya ne?
Bbu tsoro ko shakka ,deeni Yace bbu wani abu da zanyi da wuce kawai Allah ya hada
kowa da rabonsa.
Wh wih baka isa ba say kamayar daita sautin muryar inna ta karade dakin .
jikata ba zata zama bazawara ba’ byn kagama moremata jiki ba eheeeee.
kaji min yaro da muguwar mugunta da bakar zuciya kmr irin ta firauna.
To ,wlh baka isa ba ,ke km fadeela kina zaune kin yi shr kina jin abinda wannan gatalallen
“dan” naki yake fada.
Ita dai Ummi shr kawai tayi Tana kallon tsaitin da deeni ke zaune dan batasan abinda
zatace ba km koma tana da abin cewa bazata iya da jarabar inna ba .
Inna tacigaba ko baka maidaita jikata ba zata samu wanda yafi kyau da kudi da komai
“amman wlh tunda kagama morematajiki Sai ka maidaita gidanka.
ban da ma kaddarar aure mai jikata zatayi da kai tsami gaye da kai da tsayi awa bishiya.
abin dariya abin takaici a wulakanci deeni ya dinga kallon inna Yana jin wani irin zafi a
kirjinsa tamkar zuciyarsa zata buga.
a zafafe Yace to baza’a maidaita ba say kiyi duk abinda zakiyi.
,ni kake cewa bazaka maidaita ba, zubairu kana jinshi ko to wlh bada ni kake ba da
wannan ta zaune kake tashiga nuna Ummi da hannu ,mara kunya yaro kawai may dan
karan taurin kai awa na mutane farko.
Deeni ya bude baki big dady ya katse shi ta hanyar buga masa tsawa.
“mahaifiyar tamu kake kokarin yin sa,insa daita ,kar ka sake na sake jin bakin ka kaji dai
nagaya maka .
Dan Allah inna kiyi hakuri Ya isa haka”
Inna tace bai isa ba zubairu, nace bai isa ba kai ya kalli tsabar idanunka ya gayamaka haka
ko yagawa uwarsa haka ,say ni daya raina ko dan haka ko yamayar daita ko km wlh kotoce
zata rabamu dashi tare da fashewa da wani mugun kuka ,wlh Allah yaisa tsakaninmu
dakai deeni bamu taba yafe maka ba .fík yatashi ya mike dan takaici inna ya bar parlour,n.
Da kyar big Dady yasamu ya rarrashi inna. ranshi a bace Yace yanzu yanzu ka maida
matarka inji cewar big dady.
deeni Yayi shr Yana kallonsa Yana huci.
inna tace bakaji magana ake maka ba” kinbabbe kawai Sai faman huci kake kmr ,zaka
hadiye mutane.
” deeni ya tsareta da rikitattun idanushin kawai zafi zuciyarsa da kirjinsa suke masa
haushi da takaicin inna suka taru suka mamaye masa zuciya.
inna tace daina kallona da wayan nan mugayen idanun naka masu kama dana mage,
munafiki kawai.
Zeenat ce Sai Sai ta koma gidanka ko kaki ko kaso uhmmmm.
zeenat dai kanta na kasa Sai risgar kuka take tana addu’ar aranta kar Allah Yasa deeni
Yace ya maidata.
duk da tsananin son da take masa bazata iya juri zama dashi ba cikin wannan situation
din ba.
yayinda hawaye ke cigaba da bin kuncinta.
Wai wasa ake dakai ne ka tsai da mutane kana bata mana lokacin kowaye sa,an ka anan inji
wani kanin mahaifin deeni.
shi kuwa big dady tunda yayi maganar karshe bai sake cewa komai ba Sai idanu daya
zuwaba deeni Yana kallonsa ko kifta ido baiyi .
Ahankali deeni yake kallon duk ilahirin wayan dake zaune a parlour kaf dinsu iyayensa ne
idan aka dauke fk wanda shima sako yashigo kawowa ya iske ana maganar ahankali
yacigaba da kallonsu idanunshi suka fada cikin na umminsa wacce gabadaya tazamo kalar
tausayi, wasu abubuwa yake hangowa daga cikin idannun umminsa masu kama da
rarrashi da ban hakuri wanda suke nine a bukace take da son ya aikata abinda akace masa
Yayi.
ahakali ya mai da idanunshi kasa tare da sauke ajiyar zuciya. muryasa can kasa kasa Yace
na..mai daita…
Inna taja tsaki tare da Mikewa tsaye munafiki kawai’ daman can kana sonta iskanci ne
kawai irin na mai shayi ya tsaida uwarsa ya tsai fatan shayi, tsami gaye kawai.
Deeni ya dago rikitattun idanushin suka hada ido da Ummi tayi masa gargadi da idanunta
alamun karya sake Yace Komai
Ahankali Deeni ya dauke rikitattun idanushin daga cikin idanun umminsa ya maidasu
kan inna dake tsaye tana fama, babatu da sambatu iri iri “km duk cikin taron mutane dake
zaune a parlour bbu wanda yayi yunkurin dakatar daita daga maganganu da take.
zuciyar Deeni cinkushe da haushi hade da takaicin inna” bakinciki ganinta ke sake
nunkuwa a kasan ransa yayinda yashiga da zuciyarsa wani irin zafi da suya zuciyarsa ke yi.
” so yake ya murje idanunshi Tare da cire kunyar jamar dake zaune a gurin, sannan ya
zage kunjinsa ya zabga mata rashin mutunci fiyye da irin wanda ta iya.
,amman Ina..tuni idanun umminsa dake yawo a kansa” yasa ya kasa aiwatar da komai
sakamakon gargadin dinsa datake ta hanyar kwayar idanunta.
dan haka daya rasa yadda zaiyi ya fanshe tarin wulakancin inna gareshi,sai kawai ya
shiga aikawa inna da wani irin mugun Kallo may hade da harara.
Wanda yasa ,ita kanta inna dake tsaye har lokacin sake jin haushin DEENI da takaicin irin
kallon kaskancin da wulakancin dayake aiko mata dashi.
“Km hakan yayi sanadiyyar kara hassalata, dan haka a tsawace Tace ni daina kallona
ka wani tsareni da wa’yan nan mugayen idanun naka masu kama dana mage , kana
aikomin da kallon wulakancin to bada ni kake da wannan uwartaka ta zaune kake.. ehee.
takarasa fadar haka tana may jan mugun tsaki a fili tare da soma kokari kamo hannun
Zeenat.
Ke tashi mu tafi, can sashina ko kya samu ki maida jikinki ki murmure daga wannan bakar
ramar da kikayi ” inna tasoma kokarin mikar daita Zeenat tsaye.
Yayinda Zeenat din km taki mikewa Sai ma sake cure jikinta da tayi gurin guda alamun
babu inda zata.
au bazaki mike mu tafi can gurina ba ,kinfi son ki zauna inda za’a dinga miki izaya da
tsotse miki jinin jiki.
Dan zama da wannan mugun azalumin kadai ya,isa yasa jinin jikinki ya kafe batare kowa
yasani ba “ni tashi mutafi.
juyin duniya nan inna tayi da Zeenat kan ta tashi su tafi can part dinta ” amman kememe
Zeenat taki tashi.
ganin haka yasa inna sake tunzura, ta cigaba da tsayuwarta tare da surfa masu maseefa iri
iri km har lokacin bbu wanda yaiya cewa komai
big dady ne “ya dan dago idanushi yana duban sashin da inna ke tsaye Tana surfa
maseefa ya xuba mata kawai domin shi kansa big Dady rasa me zai cewa inna yayi..
kusan minti goma ya dauka Yana kallonta batare da yayi yunkurin dakatar daita ko ce
mata wani abu ba ‘ kafin daga baya ‘”ya gyara zamansa Tare da numfasawa. cikin tsantsar
ladabi da laushin murya yasoma magana, Dan Allah inna kiyi hakuri ki tafiyarki abinki
“tunda yarinyar nan Ta nuna bazata biki ba.
, Say da inna ta tabe bakinta tukun sannan tace “yo Ai ka kace min nayi tafiyata man”
tunda fadeela da danta sunfini daraja da kima a idanunku” duk irin wulakanta min jika da
wannan banza yaron nata yayi baku Gani ba Sai na laifin zakugani .
,big dady sam Bai damu ko jin mamakin abinda inna tace ba, dan yasan kadan daga cikin
aikinta. domin zata iya fadar fiyye da abinda yafi haka ma.
Dan haka big Dady Bai damu da abinda tace ba ya kara kwantar da murya cike da
girmamawa ya sake cewa, Dan girma Allah inna kiyi hakuri kiyi tafliyarki tare da yiwa
yaran nan fatar alkhari a rayuwar aurensu tunda komai yazo da sauki saki daya ne yayi
mata. Km ya maidaita.
Duk ma da abinda Deeni yayi mata Ai bai laifi bane tunda ita tajawa kanta .
inna ta katse big Dady Ta hanyar daga masa hannuta,dakata… ya isa haka karka cika min
kunne” naji zan tafi amman wlh wlh kaji na rantse to kagayawa wannan gantalallan “dan
‘naka yakiyaye ni” kar ya km yin gigin kai hannushi da sunan sake taba min lafiyar jikata.
Domin ita ba jakar gidan ubansa bace
Big Dady yace shikennan kiyi hakuri ki yi tafiyarki zan gaya masa.
Inna Tace da dai yafi dan wlh idan ya km yunkurin kai hannushi jikinta ba yarda zanyi ba.
,da kyar da Allah da rarrashi, big Dady da sauran mutane dake zaune a parlour aka samu
inna ta fice daga parlour tana zage zage.
‘ahankali big Dady Ya sake numfasawa tare da duban inda Deeni ke zaune ya hade fuska
tamkar hadari suna fuskartar juna ,tsawon lokaci big Dady ya dauka Yana dubansa ,kafin
daga baya yayi masa fada sosai akan irin hukuncin daya dauka akan Zeenat din sannan
daga karshe ya bige dayi masu nasiha mai shiga jiki shi da Zeenat ,akan su taru su zauna
Ify.
Yace deeni Kayi hakuri akan laifin da Zeenat ta aikata a gareka, hakika munsa bata kyauta
ba amman ka dauka daman can haka Allah ya rubuto cikin data zubar maka ba masu
rayuwa bane a doron kasa.
Dan haka kayi hakuri ku zauna lfy hakan kadai shine muradinmu da km kwanciyar
hankalinmu dana umminku gabadayan.
Sauran en’uwa ma kowa ya tofa albarka bakinsa sannan
Jiki a sanyaye Deeni yace yaji tare da yin musu godeya, duk da ran nan nashi, in yayi
dubu to a jagule yake .
da kyar ya samu ya kokarta ya mike tsaye dan kokarin barin parlour har yakai daidai bakin
kofar fita .
“cak yaja ya tsaya jikinsa har wani shake yayi sakamakon jin sautin muryar umminsa
mafi soyuwa a zuciyarsa.
‘,kaje gida kajirani gani nan zuwa yanzu, abubuwa dayawa suka zo masa tare da tsaya
masa a rai.
jin yadda ummi tayi maganar kadai yaisa yasan yadda ranta yayi kololuwar bace .
dan gane da abubuwan dake faruwa a atsakaninsa da Zeenat kasa cewa komai yayi sai,
kansa kawai daya iya daga mata alamun yaji ‘sannan Yakarasa barin parlour.
Byn kmr minti ashirin Zaune Ummi da Zeenat suka taddashi kan kujerar one siter
hannushi rike da waya yana daddannawa “a yadda yake operating din phone dinsa zaka
dauka kwata kwata baya tattare da wata matsala ne” ballanantana wani abu makamanci
damuwa, amman a hakikanin gsky kallo daya zaka yi masa kasan cewa yana tattare da
kunci may tarin yawa.
,a fusace Ummi take kallonsa ganin yadda Ya hakince tamkar Bai san da tsatuwar wasu
halitu a gurin ba.
yayinda gabadaya ranta a dagule yake da abubuwan da ya dinga yiwa inna a gaban
dangi.
wanda inda wani ne yasanar daita zai iya yin abinda yayi” zata iya ransuwa da Allah akan
sharri aka,a masa ,amman Sai gashi a gabanta komai ya faru.
ahankali DEENI ya dago rikitattun idanushin dasuka gama canza kala tsabar tashin
hankali dayake ciki ” ya zubawa ummi yana kallonnta..
Ganin haka tasa , ummi sake hade ranta tamau dan batason yakawo mata rainin wayonsa
dayasa ba “sannan ta cigaba dubansa
, tare da cewa yayi maka kyau… Deeni, da duk ma abinda kayi min, na gode matuka “tun
daga kan dukar min yarinya dakayi tamkar kasamu baiwa tare da hado min ita da takarda
saki har kawo abubuwan da suka faru a yau
Dan wulakanci ma yau kusan tsawon kwanaka uku kennan rabon daka Tako kafafunka
cikin gidan nan .tsabar kagama rainani
Deeni dake zaune yayi shr tare da cigaba da duban ummi kawai batare da yace mata komai
“dan ma rasa abinda zaice mata yayi km yana son ta fahimce shi tasan duk abinda take
tunani akansa ba haka bane amman Sam yakasa magana .
Ummi ta sake juyowa inda Deeni ke zaune suna fuskantar juna dashi.
“Tambayar da zan maka yanzu nake son ka amsa min d eh ko A’a.
daman can ba kai ne da kanka ,ka nemi auren Zeenat din a gurina ba?
ahankali Deeni ya dagawa Ummi kansa.alamun shine ya furta Yana son ta aura masa
Zeenat din.
Ummi Tacigaba To yanzu dan ta zubar da ciki ne yasa har ka iya mata irin wannan dukan
mutuwar ?
Km har da ikirarin zaka kashe min Ita dan baka san ciwonta ba.
Ko kana tunanin idan ka mata illa zan barka ne kaima.
Kai gaka sarkin en zuciya madadin ka kawo maganar gabana nasan yadda zanyi solving
din matsalar batare da kowa yasani ba, shine ka tuzartata Tare da zartar da hukunci ta
hanyar azabtar min da yarinya tamkar kasamu baiwa.
Sai lokacin deeni yaji wani kuzarin yazo masa Dan haka cikin , tsanyin murya tamkar may
shirin zubda kwalla Deeni soma magana ” kwarai first lov nayi kuskure guda daya
narashin sanar min ki kafin zartar da komai amman na rokike kiyi hakuri.
Amman ta ya zuciyata zatayi sanadiyyar barinta cikin kunci da cuta alhalin nasan amanarta
kika damka min acikin tafin hannuna’ ya fadi haka tare duban tafin hannun nashi da
kwayar idanushi
, indai akwai wanda na cuta to kece da bansanar miki da abinda tamin ba ,kafin na zartar
da hukuncina akanta. amman ki gaya min me yakamata nayi byn na kamata dumu dumu
da laifin zubar min da ciki har Sau biyu tare da shan maganin hana daukar ciki Sau ba
iyaka.
Cikin zafin rai ya Kamo lips dinsa na kasa yasoma cizawa da karfi sakamakon hawayen
dayaji yana kokarin son zubo masa.
“wani irin nauyin zuciyarsa tayi “yana ji yadda kirjinsa ke masa zafi da ciwo tamkar an
daura masa dutse may shege nauyi a sama kirjinsa,
,Da kyar yasamu yacigaba da magana. mutane na gudun tsautsayi amman ni na zauna da
nawa tsautsayin batare dana sani ba ‘bana da miradin danayi gida biyu amman nayi
tunani indai tsautsayi ne ya hau kaina “to itama dole tsautsayi ya hau kanta.
ni muradina gida daya ne kawai nake da bukata amman tunda itama ta cin nawa zuciya
gobarar datayi sanadiyyar tarwatsa min zuciyarta tarabani da abinda nafi so a rayuwata
to tabbas nima say na nemo may kashe min wannan wutar.
ta hanyar musguna mata
Kada ka taba karya zuciyar mace kada ka taba ruguza iyali domin cika muradinki first lov
NASURULDEENI dinki babu abinda bayawa Zeenat na jin dadin rayuwar aure “tare da
sanyata cikin farinciki mara misaltuwa.
burina na kyautata mata.
‘ta yadda zan samar da murmurshi da farinciki a fuskarta amman firt lov ki duba kiga da
irin abinda ta saka min dashi.
gata nan tsaye ki tmbyeta ban kasance may adalci agareta ba A dan ,zaman da mukayi
daita
ahankali ya mike tsaye hawaye dake makale a idanushi sukayi nasara zubowa batare daya
shiryawa hakan ba.
shin na zalinceta ko daidai da rana daya ne.
ki tmbyeta first lov amman duk da haka idan kina ganin banyi daidai ba akan dukan danayi
mata to zaki iya rama mata ki hukunta ni ta duk yadda kike so.
kece kikayi sanadiyyar kawo ni duniyar nan…
ko mayar dani lahira kike son yi “ahalin yanzu ba zance miki komai ba.
wlh Deeni dinki bazai taba cewa komai ba. Hawaye yacigaba da bin fuskarta.
km ba,zan miki wata jayayya ba abisa Ga hukunta ni da zakiyi.
jikin Ummi yayi maseefar sanyi dangane da jin Dukabinda dan nata ya zaiyana.
jikinta a sanyaye takaraso kusa da tillon “Dan” nata tana kuka itama tare da dora
hannuwanta duka ta riko fuskarsa dashi tana kallonsa.
wani irin matsanancin tausayi tattare da kaunar “Dan’ nata ne taji Ya sake nunkuwa
acikin zuciyata.
Yayinda kuka mai karfi ya kufce mata” from no where kawai ta rungumeshi ajikinta tana
cigaba da kuka shima kukan yake yarona kayi hakuri.
“kukan ya isa haka kabar kuka kayiwa umminka uziri bisa Ga zarginta gareka.
amman duk da haka umminka na neman alfarma gareka ,na rokeka Dan Allah kada ka
juyawa Zeenat baya ,ita din diyata ce halak malak duk duniya nan batada wata uwar data
fini.
, ka cigaba da hakuri daita “inshallahu zata canza ,zata canza ,zan sata ta canza kaji
yarona.
“Allah yayi maka albarka yadda kake faranta min ,kaima Ina maka addu’ar Allah yabaka
ya ya wayanda zasu maka fiyye da haka.
Zeenat ,dake tsaye taji hawayen tausayin su gabadata, nabin kuncinta, tasan hakika ta
tafka babban kuskure a rayuwarta
tare da aikatawa kanta mugunta mafi muni da radadi wanda batasan tsawon lokacin
dazata daina jin zafi da ciwon abinda ta aikatawa kanta. Da
wa yan nan bayin Allah ba.
Hakika ummi uwace guda a gurinta har da rabi.
kodan ummi yaci ace tayi hakuri da juriya tabar cikin jikinta .
gabadaya tausayinsu ne ya taru ya mamaye mata zuciyarta yayinda hawayen idanunta
suka cigaba da zuba shaaaaaaa… * *******
kuka ne mai karfi yaci karfinta tasa hannuta duka ta toshe bakinta dashi tare da rugawa
da gudu ta haye saman up stairs din ummin tana gunjin kuka
Kiyi hakuri first love da abinda zance inji cewar Deeni dan girman Allah first love kimin
uziri na kara aure domin zama daga ni say Zeenat, zai haifar da mummunar damuwa
wanda zaisa mudinga samun matsala daita a yadda nake jin zuciyata.
, uhmmmm Deeni bbu wani matsala ko damuwa daza’a km samu a tsakaninku muddin Ina
raye ni kaina zan koma can gidan naku” nacigable da zama tare daku har sai Sanda naga
zaman naku ya daidaita.
maganar kara aure km bazan hannaka ba domin hanaka daidai yake. Dana shiga
hakinka tunda kayi Niyya, say day kasani bazan taba barinka ka aure matar da nasan
cewa zata fi Zeenat dina da komai ba arayuwa.
, say day idan ka amince zaka aure kasa Zeenat din.
Tukun zan amince da kara aurenka .
Km abisa sharadi duk yayan da matar za’ta haifa maka ,zasu zauna matsayin na Zeenat ne
muddin rai matsawar ba nata tasamu ba.
dan haka Sai km tayi kasa kasa da muryata ta yadda bbu mai jinsu tayi masa magana.
Wanda yasa Deeni yin sororo kawai yana duban umminsa t
e da nazarin maganarta tsab
“exactly irin dai abinda abokinsa manir ya fada masa ne
,say gashi itama umminsa tazo masa da irin maganar wanda shi sam a ranshi yake jin
rashin yuwar yin haka.
ahankali ya samu guri ya koma ya zauna jagwab.. akan kujera yana may fidda numfashi
sama sama.. domin maganar tayi maseefa girgizasa tare da daga masa hankali “har ma
tana barazanar tarwatse masa zuciya.
,da kyar yasamu Ya daidaita’ numfashinsa ya dawo normal.
,itama Ummi guri tasamu nan kusa dashi ta zauna tare da kamo tafin hannushi cikin nata
Tana may nazarin yanayin daya shiga ,ka natsu ka kwantar min da hankalinka Deeni kada
kasawa zuciyarka damuwa.
kasani a tashin hankali. wannan bawani abu bane so big kmr yadda ka dauka ,kusan
anayin irin hakan Sosai a wannan duniyarta tamu.
Sake, dago rikitattun idanushi yayi yana kallon umminsa dasu take yaji wani ya tsigar
masa a kanta kirjinsa ya rike gam Tare jin wani abu ya tsaya nasa a wuya yakasa
kwakwarar motse ballanantana yace mata wani abu.
‘Ahankali”‘ummi ta numfasa sannan tacigaba maganarta irin wannan auren kawai zan
iya yarje maka kayi.
,dan bazan taba yarde maka ka auro matar danasan zatafi Zeenat da komai ba, baya Ga
kaskantacciya mara galihu ..
da kyar deeni yasamu ya hadiye abinda yaji ya tsaya matsa makoshinsa sannan ‘ahankali
ya iya bude bakinsa tare da kiran sunan umminsa haba first lov…. ta yaya da matsayina
da girma zan bige da auran kaskantacciya km mara galihu?.
Ummi ta katse shi ta hanyar daga masa hannuta, sanin halinka da nayi ne yasa haka.
da km sanin burin kalar mace dakake muradi tun farko yasa nace haka ,ko kamanta
kataba gaya min irin kalar mace dakafi son ka aura kafin daga baya kadawo ,kace min
Zeenat kake so.. wanda ni bansan dalilin dayasa kacanza ra,ayinka ba.
Dan haka, bana son sake jin komai daga bakinka ,muddin kana bukace da kara aure kmr
yadda ka bukata” to say dai ka auri irin kalar yarinyar danake so…
idan km kaga bazaka iya ba, kana iya cigaba da zama tare da matar har sanda Allah zai km
azurtaku da samun wani cikin.
“cikin sanyi jiki ya dinga girgiza kanshi kawai yana jin tamkar mafarki yake ba gaske bane
wai yau shi umminsa ke shirin shiryawa irin wannan auren sbd farinciki Zeenat..
shin wani irin KAUNACE a tsakanin Zeenat da ummi,ai Bai sani ba a fali yayi maganar Sai
ji yayi ta bashi amsa ,da kauna irin ta “da” da uwa numfashi ya sauke yashiga sauke
‘ahankali’ahankali yayi shr tare da sake lulawa duniyar tunani.
Tsawon lokaci sannan ummi tace kayi shr batare da kace min komai. amincewa da auren
irin yarinyar danake so “ko km ka fasa auren gabadaya.
Xuru yayi kawai yana kallon mahaifiyarsa.
abu na farko dai bayajin zai iya duka abinda umminsa ke so .
hakura da auren dayakeyi . tamkar Bai ruguza zuciyar Zeenat bane ,sannan km auren irin
kalar yarinyar da umminsa ke so tamkar zubar da kimarsa da ajinsa ne .
shi da yafi bukatar auren maccen data amsa sunanta mace ta yadda Zeenat din karan kanta
zata raina kanta Amman Sai gashi ummi takasa ta tsare ta neman kwafsa masa.
Amadadin ya hakura duka gara ya auri koma wace irice mace ce kodan kuntatawa zuciya
Zeenat.
l.
8:27 PM .
Xuru yayi kawai yana kallon mahaifiyarsa.
abu na farko dai baya jin zai iya duka abinda umminsa ke so …
hakura da auren dayakeyi . tamkar Bai ruguza zuciyar Zeenat bane ,sannan km auren irin
kalar yarinyar da umminsa ke so tamkar zubar da kimarsa da ajinsa ne .
shi da yafi bukatar auren maccen data amsa sunanta mace ta yadda Zeenat din karan kanta
zata raina kanta Amman Sai gashi ummi takasa ta tsare ta neman kwafsa masa.
Amadadin ya hakura duka gara ya auri koma wace irice mace ce kodan kuntatawa zuciya
Zeenat.
Domin shi karan kansa yasan irin yadda Zeenat ke tsantsar kaunar shi da kishinsa, bubu
abinda zai haukatata a tashin farko daya wuce taji zai kara aure.
wani tsanyi da farinciki ne suka ziyarci zuciyarsa a lokaci daya, tamkar wanda akawa
albarshir da gidan aljanna.
take yaji Ya amince da hukuncin umminsa.
Dan haka ya dago da rikitattun idanushin suka hada ido da umminsa ‘ahankali ya bude
bakinsa Tare da cewa shikennan first lov ,badamuwa na amince kiyi komai kawai kmr
yadda kike so ,kawai.
Ummi tace very gud Sai day km zanso maganar ta tsaya iya nida kai ne kawai bance
kasanarwa da kowa ba ” koda kuwa faruk ne.
,Zeenat kuwa idan lokacin daya kamata tasani yayi ni da kaina zan sanar mata.sai abu
nagaba wanda umarni ne zan baka ba shawara Ina son Zeenat tacigaba’da karatunta
sannan km ka canza mata motar hawa shi deeni zugun tayi yana kallon ummi abubuwan
nata sun daina bashi mamaki sun koma bashi tsoro ,runtse idanushin yayi Tare da cewa
yaji ummi ta Dan murmusa jin ya amince tace Allah yayi maka albarka ya albarkaci auren
dazakiyi da kyar deeni ya iya bude baki ya amsa da Ameen .