WANI AURE.
CHAPTER 19
Rungume take a faffadan kirjinsa har lokacin ” yayinda hawayen tausayin kanta ke cigaba da bin kuncinta” danasani tattare da nadamar abinda ta aikatawa kanta a can baya ne ke damun zuciya .
‘hakika rayuwa bata da tabbas gashi komai yana neman tsaya mata ” zuciyarta kemata wani irin zafi yau tazo mata tazo mata abu mafi muni ,kishiya …fa.
yau ita zeenat da kanta ake kokarin son sanya mijin yi karo mata kishiya… Kishirya.. ta sake maimaita hakan akasan ranta abinda tafi mugun tsana a rayuwarta kennan ,wai aba kishiya .. +
kirjinta ke mata radadi da nauyi tamkar an dora mata dutse ita kadai tasan yadda take jin zuciyarta da gangar jikinta… wani irin maseefaffen kishin mijinta ne ke sake tasomata fiyye da yadda take ji a da.
tsanar sauran matan dake duniya zaune bbu aure ne ya dirar mata lokacin.
Kukanta yasoma damun tunani ,kasancewarsa mutun marason damuwa da yawan hayaniya. hakan yasa yasoma sausauta rungumar da yayi mata daga qarshe ya ma rabata da sansar jikinshi gabadaya.,
Tare da zuba mata rikitattun idanushi kawai Dan shi sam kwata kwata bai iya wani abu wai rarrashi ba . ballanantana har ya tsaya wani bata lokacinsa gurin rarrashinta . +
,a dake taji sautin muryasa ‘,malama kiyiwa mutane shr duk kinbi kin cika min kunne da wannan bazan kukan naki mara ma’ana ..
ko uban wani ne ya aikeki wulakanta cikin da Allah yabaki tun farko .
Wlh idan kikasa damuwarki tashafi lafiyar mahaifiyata akan maganar kishiya ..nan zan baki mamaki ..
kishiya …bama daya zanyi ba har biyu idan nagama sai nayi .
“inyaso ki mutu sai ki kashe kanki kmr yadda kika ce ,sha sha kawai ya fadi hakan yana may da jan mugun tsaki… mtssss .
take jikinta ya dauki rawa kirrrrrrma jin maganar bama kishiya daya ba har idan yaso zaiyi ..
“ai …batasan sanda ta zube kasa ba.
Tana kuka Tana girgiza masa kai dan gabadaya kasa magana tayi sai jujjuya kai kawai take tana zubda kwalla.
Wata uwar ,harara ya watsa mata hade da binta da wani irin bazan kallo wanda yasan hantar cikinta kadawa wayyo hrt karka min haka dan girman Allah karka min kishi….sai km Tayi shr Tana cigaba da kuka…. bakinsa Ya tabi tare da cewa meyya haka oya Mike .. Mike ni kibar min dakin kinsa fa ni bana son damuwa .
Yana gama fadar haka ya haura saman gadonsa ya dau towel daman km abinda ya fito dauka kennan . +
bathroom ya sake koma ya sakarwa kansa ruwa tare da dauro alwala sannan ya fito kugunsa daure da towel .
mamaki ganinta yayi har lokacin bata bar dakin ba Tana nan durkushe tamkar yadda yabarta ,ganin yanayinsa da km yadda yake kallonta da rikitattun idanushi masu matukar birkita mata kwalkwaluwa ,da hana zuciyarta sukuni .
yasa ta mike tsaye da sauri jiki har rawa rawa yake tsabar tashin hankali ,a sukwane ta tabar masa dakinsa Dan tasan halinsa maseefar sa, bakaramin aikinsa bane ya shuka mata rashin mutunci idan ma taci sa’a Bai hada mata da mugun duka ba tunda daman ya mata gargadi kar sake ganinta bedroom ba .
Fitarta daga dakin yayi daidai da sauke naunauyen ajiyar zuciyar da yayi..
, yayinda wani gefe na zucitarsa na Dan tausayawa mata game da halin rayuwar data jefe kanta ciki.
hakika shi yasan tana wahalar da zuciyarta ne kawai akan batun kishiya .
Dan kishiya ba fashi sai ta zauna daita.
‘ahankali ya sake sauke wani naunauyen ajiyar zuciya tare laso lip’s dinshi na kasa …
” cikin sauri ya shiga shirya kansa cikin wasu hadaddun kananan kaya masu matukar kyau da daukar hankali shirt ce ashi colour mai gajeren hannu sanye a jikinsa sai wando blue jeans wanda suka yi matukar karbar surar jikinsa.
‘ koda yake shi din may matukar kyau ne km kowani irin kaya ya sanyawa jikinsa sai sun amshi karbi shi.
cikin sanyin nan nasa da takunsa na kasaita yakarasa gaban mirrow ya dauki turarensa mai matukar kamshi ya feshe ilahirin jikinsa dashi.
‘ sannan ya gabatar da sallah byn ya idar sallah ne ya sauko parlour kasa cike da isa .
Anan ya iske ,Ummi tare da zeenat zaune sunyi jugun jugun abin duniya ya damesu.
Ummi ta rafka uban tagumi tana tunani duk da yasan zance dai bazai wuce akan maganar aunty shi bane .
Yana tsaye yana kallonsu yaga zeenat ta kwanta akan cinyar ummi tana kuka ‘ tana goge Hawayen idanunta da bayan hannuta kukan ya isa haka mamana kada wani ciwon yakamaki fa.. . Ummi bazan iya zama da kishiya ba wlh taba kirjina kiji ta fadi haka tare da janyo hannun Ummi zuwa saman kirjinata .
Kallo daya yayi musu tare da dauke idanunshi daga kansu..
ya tabe baki kai tsaye dinning area ya nufa yaci abincinsa hankali kwance . Sannan yacigaba da zamansa yaciro wayarsa yana operating ..
Km duk yana jin abinda zeenat kecewa da yadda Ummi ke rarrashinta da kwantar mata da hankali akan bbu wata kishiya da za’a yo mata ita kadai ce bbu kari …
, Jin haka Yasa Daga can inda yake zaune yayi gyaran murya.
,Ummi ce ta juyo ‘ahankali Tana dubansa ,yatsansa daya ,ya karkada mata alamun a,a harara Ummi ta sakar masa yayinda shi km ya girgiza mata kai kawai yana tabe baki.
Ahankali Ya Mike tsaye ya dawo kusa da Ummi Ya zauna fuskarsa a hade yace ke…..yi excuse dinmu please zata Mike kennan ummin ta maidaita Dan me zaka korar min yarinya tana cikin halin damuwa ?
idan har baka shirya yin magana dani bane tana nan kana iya barin maganar har zuwa wani lokaci dan bbu inda zata ke koma kiyi kwanciyar kinji..
,koma kuwa tayi kwanciyarta kmr yadda Ummi tace amman har lokacin Hawaye bai daina bin kuncinta ba .
Kafadarsa ya sake dagawa alamun bai damu ba da abinda Ummi tace ba ..
Wayarsa ce ta dauki kara sauti mai dadi Mikewa tsaye tare da pic din call din ya manna a kunnenshi tana tafiya . +
Hello ..Yaya ganin nan zuwa yanzu sannan yakashe wayar yabar musu gidan gabadaya .
Yana fita Ummi ta dauki wayarta takira hajiya turai bagun farko hjy turai ta dauki wayar da sallamarta ” bbu abinda Ummi tasoma tmbyrta sai an km samu kuwa ?
Ummi tayi hakan ne Dan kada zeenat din tadago wani abu dangane da shirinta.
bangaren hjy turai kuwa cewa Tayi eh ansamu amman sai dai guda daya ce km Tanada dan shekara ,Ummi tace kmr shekara nawa gareta ?
eh zata kai kmr 23 haka inji cewar hjy turai ok ki kawota naganta hjy turai tace sai dai kibari zuwa gobe idan Allah Ya kai mu ‘ latifa zata zo gurina idan zata wuce gida zan bari takaraso miki da yarinya ,Ummi tace ok shikennan sai sun zo din takashe wayarta tare yiwa hjy turai godiya .
Washegari da misalin karfe hudu daidai latifa takawowa Ummi shafa. kallo daya Ummi tayiwa yarinyar taji kwata kwata bata kwanta mata arai ba a ranta tace itama kennan Ina Ga oga DEENI.
tasan ma bazai wank mu,ammultu da yarinyar ba , girgiza kai kawai Tayi byn tasa an kawowa latifa abin motsa baki .
,’ahankali Ummi ta Mike tsaye ta nufi wani kofa tayi warning din glass tare da cewa latifa ta biyo bayanta , latifa ta Mike ‘ahankali tabi bayan Ummi .
Wani madaidaici parlour Ummi takai latifa byn sun zauna ne Ummi tace Kira sunan lafita ta amsa kina jina latifa ..yarinyar nan bata min ba km nasan tunda bata min ba da wuya tawa mai gidan Shima kinsa shi da kyankyami tsiya .
dan haka asamo wata kota gurinki ne amman dai zan bar Ita wannan din kafin asamu wata ,dan aikin gida sbd aikin nayiwa laraba yawa ,latifa tace ok babu damuwa ,daman kuwa akwai wata yarinya dake neman aikin gida irin wannan amman kibari zan miki kokari inshallahu .
Ummi tace shikennan latifa Nagode sosai suka yiwa juna sallama sannan latifa ta wuce .
Byn fitar DEENI daga gida kai tsaye gidan yayansa mahamud dake cikin estate din yayi . +
zaune suke shida da Yaya Muhamud din babban parlour baki na gidansa .
Shr yabiya baya kafin Yaya Muhamud ya numfasa tukun yasoma magana kmr haka DEENI abinda yasa nace kazo nan ina nemanka ,akwai magana may mahimmanci da nake son muyi akan company,s dinmu.
,kaga dai yanayin danake ciki halin yanzu nima girma ne yake zuwa min yayinda abubuwa ke sake min yawa ni kadai raina nake kokari akan lamuran company,s dinmu na cikin gida da sauran kasashen duniya shine naga yakamata ace kaima , ka’ajiye wannan aikin naka kazo mutaru mu kula da komai Tare.
,kasan mutane wasu basu da amana , amman yaka Gani akan lamarin .. DEENI yayi shr kawai yana sauraransa har yakai karshen zance ,sannan ya dan yi murmushi karfin hali har dimple dinsa ya lotsa ,rasa mezai cewa yayansa yayi dan haka yace shikennan Yaya zan duba nagani idan hakan zai yiwu dan gsky Ina matukar son aikina km banason abinda zai rabani dashi .
,DEENI..yaya Muhamud ya sake kiran sunanshi DEENI ya dago da idanushin yana dubansa dasu , wannan aikin naka yana mahimmanci a rayuwa Shima km talafawa company,s dinmu haka ,amman abinda nake so dakai kaduba din kmr yadda kace ,nan suka bar zance suka shiga hirar duniya har DEENI yake sanar masa da abinda mama ta abuja, tayiwa Ummi akan zeenat , Shima Yaya Muhamud din baiji dadin abinda Tayi ba .
Bayan wata biyu
Al’amarin duniya fa yasoma damun Zeenat tayi mugun tada hankali kan maganar aunty,n su Ita DEENI gabadaya afrigice take da komai , kawai burinta ahalin yanzu bai wuce kawai ta ganta dauke da ciki ba . +
amman kwata kwata hakan yaki samuwa gareta ga lokacin na tafiya , gabadaya hankalinta a tashe yake matuka.
haka ma ta bangaren Ummi itama hankalinta a tashe yake da yadda take ganin yanayin diyar tata.
,shi kuwa gogan sam bbu ruwanshi da wani tashin hankali da suke cikin .
‘ hakar gabansa kawai yake domin komai yana tafiyar masa yadda yake so daga office har gida .
Sakamakon damuwar da zeenat tasawa ranta ne har hakan yajawo ta Dan rame kadan kallo daya mutun zai mata yagane tana cikin tension .
” Ko school ma sai da wata friend dinta may suna halima ta gane Tana cikin damuwa dan haka tmbyeta ,zeenat bata wani boye mata komai dangane da halin datake ciki ba .
,nan fa halima tace Ina ai baki Ga ta zama ba zeenat kishiya fa ….Ai ni ko sunanta ban kaunar ji ballanantana tashigo min gida gaskiya kitashi tsaye tun wuri , zeenat marairaice murya hali bansa yadda zanyi ba ,bansan koina ba , hospital kawai nasa km muje ,hali tace ok kada ki damu akwai wani mutun danasan yana bada maganin haihuwa ,kibari zan rakaki gurinsa amman a sango ota dake hanyar abe okuta yake ,idai zaki zan rakaki ,zeenat najin haka ta kamo hannunwan halima duka cikin hannuta Tana murna dan Allah hali kitaima min koma Ina ne zani indai zan samu cikin haihuwa nidai banason mijina yayi min kishiya dan bana kaunar zama daita a rayuwata ta duniya km nasan rashin haihuwar nan zai iya bawata shigo min gida .
gara mutuwata danaga zuwan wannan rana.
,hali tace haba kada ki damu zan taimakamiki ai murigada mun zama daya .
Nan fa suka bar zance da zumar gobe zasu tafi songo ota .
Washegari kuwa da wuri zeenat tashirya har Ummi tacewa yana Ga yau kinashiri cikin sauri haka.
Murmushi Tayi kawai Tayi wlh , Ummi lecture gareni da wuri shiyasa kika ganni haka.
Ummi tace ok , koke fa haka nake son ganinki cikin walwala da kazarkazar tattare kwanciyar hankali .
,banason ganinki cikin damuwa zeenat ta sake yin murmushi tare da cewa Ummi sai ta dawo Ummi tayi mata addu’a .
+
Haka suka je gurin may bada maganin Ita da hali batare da sanin kowa ba .
Bawani abu mutumin yabata ba, baya Ga garin magani baki yace ta da lemun tsami ta dinga da sha da zarar sun gama sex da mijinta har sai maganin yakare har yana sake tabbatar mata maganin bazai kai Ga karewa ba zata samu ciki . Uhmmmm
da murnarta dawo gida km Tayi kmr yadda mutumin yace Tayi.
,tare da zaman jira tsammani , har zuwa lokacin zuwan period dinta, bata Ga jini ba , .
Tacigaba da shan magani ,murna kuwa kmr ta Yaya ,dan duka tunanin ciki gareta amman byn kmr sati daya da shanye maganin sai Ga jini ..
ranar kuwa data Ga jinin zaman dirshan Tayi a bayi “tare da daura hannuta duka bisa kai ta saka kuka a gurin .
,wunin ranar bbu inda taje ko parlour kasa bata keko ba , , Ummi zaune ita da DEENI wanda Bai dade da dawo ba zaune yake kusa da ummi suna hira ,ganin shr shr bata zeenat ba yasata zuwa dakinta , da fari ta dauka ko bacci take ,ganinta kwance tana sheshekar kuka ne yasa gaban Ummi faduwa da sauri takaraso inda take kwance Tana kiran sunanta ke zeenat.. lfy ki kuwa ,kukan me kike haka ?
Aiko zeenat naganin Ummi ta sake rushewa da wani sabon kuka km tashiga gayawa Ummi abinda ya faru amman sai dai ta boye bata gayawa Ummi zance zuwa gurin amso magani ba .
Allah sarki Ummi baiwar Allah haka ta dinga rararshinta Tana kuka itama. jin shr yayi yawa ne yasa DEENI biyo bayan Ummi yaga ko lfy aiko yaga abin mamaki dan zaune ya tadda ummi yayinda zeenat din ke rungume ajikinta suna aikin kuka tamkar wayan,da akayiwa mutuwa mai zafi.
Yana ganin haka yasan iskancin zeenat din ne ya motsa ,dan haka bai wani damu ba ko tada hankalinsa.
dan yasan zance gizo baya wuce na koki ,sai ma tsawar daya dakawa zeenat din ..Tare da nunata da yatsansa daya ke……. banson wulakancin da rainin hankali fa yazaki zo ki tasa min uwa gaba da kuka?
Ke…duk matsalar ki sai sanya mutane ciki.
” kinsa Allah idan baki daidaita kanki da kyau ba zan iya ra…..
Ummi ta katseshi ta hanyar taga masa hannu ,ya isa haka bana son jin komai .
km ni ai baita ce tasani kuka ba, Tayi missing din kwanakin period dinta ne so shine da shirmenta ta dauka ko ciki ne da Ita ,sai km Ga period din Ta yazo .
” kasanta da shririta shine ta zauna Tana kuka ,ni km tausayi tabani ,Ummi na kaiwa karshen maganarta , DEENI ya watsawa zeenat din harara ,yanzu ne kika damu da haihuwa ko da kika ji zance abinda kika fi tsana a rayuwarki ?
Kinsa Allah zeenat ki fita daga idona kada ki kashe min uwa da matsalarki .
,kikasa wasa ma wlh me gabadaya zanyi in yaso ki mutu gabadaya na huta da matsalarki , km bbu abinda zai faru Dan duniyata zan cigaba da ci hankali kwance byn baki raye .
kinga karshen kishi kennan…. zeenat najin haka ta fashe da wanj sabon kukan Ummi kina jinsa ko …..so yake na mutu yakara aure sbd ya daina sona …sai km Hawaye sharrrrrr . +
Dakuwa Ummi Tayi masa da hannuta ungo nan DEENI wani irin rashin imani ne haka ,kake nuna mata , rashin son nata har yakai ka dinga yi mata fatar mutuwa km a gabana DEENI… ko kunya idanuna bakaji ba .
To inshallahu ta Allah bataka ba km bbu wata mutuwa a fuskar diyata km haihuwa zatayi shi da yarda Allah .
Zeenat fa tashiga neman haihuwa zanga zabga tamkar zatayi hauka duk inda taji ana bada maganin haihuwa sai karfa taje ba .
har gurin wata sabuwar malama datazo Lagos wacce ake Kira da malama shema,u taje neman magani haihuwa.
wanda mutune sukayi ittifaki akanta muguwar Yar damfara ce daga Yola take ,da farko Kano ta fara zuwa tana Dan farar mutane mlm aminu Ibrahim daurawa ya fatattakota ,shine tayo garin Lagos . Nan ma dai zeenat taje bbu wata nasara data samu sai kudinta data kashe .
Cikin haka maganar da mama ta abuja Tayi akan kara auren DEENI taje Ga kunne big Dady , musamman yasa tazo daga abuja km ya nuna mata sam Bai ji dadin abinda Tayi ba.
,inda ma shi DEENI din ne da kansa yaso kara aure wannan dadan bbu may hanashi amman tace lallai sai ya kara aure akan wata lalura ta matasa ko wani dalili na dabam , hakan baiyi ba dan haka bayason a km tadda zance .
Wannan batu da big Dady yayi da km daurin gidin Ummi da take dashi yasa hankalin zeenat din kwanciya .
Cikin dan kankani lokacin ta maida kibarta Tayi fes daita ta dawo da gayunta kmr da.
A cikin wannan lokacin ne latifa takira Ummi tasanar daita cewa an samu mai aiki karama Yar shekara gamo shabakwai … yanzu haka jakar kayanta a gidanta ya kwana Amma ita bazata samu damar zuwa ba ,sai dai zata turo mata da number yayar yarinyar takira ta ,tabata address din estate din murna fall cike da zuciyar ummi tace badamuwa turo min yanzu yanzu ,kinji diyarta….ummi na sauke wayar sako yashigo tana dubawa taga suna kmr salmah Tare da number .
Al’amarin gidan kuwa gabadaya ya sake canzawa tun daga kan mutane dake rayuwa a cikin gidan har zuwa Ga gidan karan kansa .
Dan gabadaya DEENI ya gyara kowa Ina a gidan inda ya sake fadada girman dakunan dake kasa tare da kawatasu da ado .
Wanda ,a halin yanzu yakoma amfani da dakin sama da kasa .kallo daya zakawa gidan ya birgeka km kasan ya fita daban da sauran gidanjen dake cikin estate din.
+
Ummi bata Kira number Salmah ba sai byn data sallami shafa da kwana biyu sannan takirata
Ranar da shafa ta tarkata tabar gidan ranar itama Zeenat tashi da zumar dawowa dakinta na kasa wanda DEENI ya cire mata ,dan haka bata tsaya wani bata lokaci ba tasa laraba tayi mata komai ,tare da abubuwan ta masu mahimmanci sai abinda baza’a rasa ba tabari a dakin sama .itama takoma amfani da daki biyu a cikin gidan.
Matashiyar budurwa ce Tare da yayarta tsaye abakin titi .
suna jiran mota ‘ sun dauki sama da rabin awa tsaye a haka suna jiran abin hawa amman kowace mota tazo wucewa” cike take tap da mutane .
,sakamakon cunkoson ababen hawa da aka tashi dashi a garin Lagos.
, aunty me zai hana muhau machine ne , kinsa fa inda zamu da Nisa sosai .
, saboda ke da zaki dawo .
Dan naga yanayin garin yau sai a slow inji cewar nablah…..
, aunty Salmah ta dan juyo ta kalli gefen inda sisinta ke tsaye tare da cewa ‘shikenan nablah muhau machine din kawai Dan nima bana son dadewa .
gaba kadan suka karasa wajen yan machina,
malam dan Allah lawansi bustop zaka kai mu, inji cewar aunty Salmah.
mai okada ya gyara tsayuwar machine dinsa ta yadda za su samu damar hawa ..
Kin hawa aunty salma tayi sai ma tmbyr mai okada take da nawa zamu bayar tukun.
, Atakaice dai muna kai mutun daya a naira dari mutun biyu dari da hamsi aunty Salma tace Shikenan ke nablah fara hawa.
” dayake kaidar Aunty salmah kennan.
muddin da kanneta zata hau machine bata yarda tafara zama a farko, sai dai tace su hau gaba ita km ta zauna a baya.
‘Ahankali Suka dane machine”
dai dai bakin filling station din dake lawansi, suka sauka aunty Salmah ta bude jakarta tabawa Dan okada kudinsa . +
tafiya suka soma yi zuwa inda zasu shiga motar da zata kai su surelere .
Suna tafi suna hirarsu abin sha’awa har suka isa wajen shiga motar Masha.
, daidai Bakin get din da zai kai ka ilori Street suka sauka , tafiya kadan sukayi suka isa inda zasu .
aunty Salma tasa hannu ta tura get din gidan wanda koda yaushe haka yake a bude, .
Da sallamarsu suka karasa bakin net din latifa . Aunty Salmah na kwalara mata Kira latifa latifa.. Amman shiru ba amsa yayinda kofar ma take a kulle .
Tsayuwar Minti goma sukayi kafin daga baya suka jiyo sautin muryar latifa .
ku biyo ta nan kofar kitchen,an kulle nan ne sbd yara .
” zagayawa sukayi ta kofar kitchen suka shiga.
Latifa naganin su tasaki murmushi ,kai kai gsky dai Salmah kunyi latti wlh kin kuwa san nisan unguwar da zaku kuwa ?
aunty Salma tayi dariya wlh kinsa halin mutumin naki hukuma ne sai da rarrashi .
duk shi ya bata mana lokaci , gashi Bai fita da wuri ba.
, to shikenan sai kuxo Ku tafi tun rana batayi ba . “ai ma hajiyar takirani tun sassafe tamin kwantance yadda zamuje can din ” da ,na so mu wuce ta mushi ne saboda akwai mota mai zuwa can direct sai dai kinsa jakar nablah na nan shiyasa dole sai munbiyo tanan din .
Latifa tace ok ina zuwa ku shiga daga ciki bari na amso sako dana aika .
dan Allah kiyi sauri ba sai munshiga ba . +
ina jakar take saboda kar lokaci ya wuce ?latifa ta kwallawa mai aikinta kira… ke uzaima …
“uzaima ta amsa tare da karasowa ,Gani aunty jeki dauko jakar nablah a karkashin step yanzu .
Sannan taje tasamu yaron mijinta da ta aika tun dazu ATM tace ibrahim ya’akayi ne ,ya tura hannu ciki aljihun wandonsa ya ciro kudi masu yawa ya mikawa latifa Tare da ATM a saman kudin tace yauwa na gode.
har ya juya ta kiransa ya dawo , akwai wa’yanda nike son ka dan kai mun su inda zasu samu motar zuwa obalende .
, yace to badamuwa ,ta koma ciki inda ta tarar har an dauko jakar nablah ,latifa taciro dubu biyar ta mikawa Aunty salmah gashi kikara kuyi kudin mota dashi ,saboda yanayin hanya .
aunty Salma ta amsa tayi godiya, hade da yi mata sallama .
bakomai sai kin dawo mayi waya duk abinda ake ciki Kya sanar min ni dai addu’ata Allah Yasa tayi musu ..
Kai tsaye inda zusu samu motar da zata kai su obalende ya, ajiye su .
, Suna tsaye cikin mota BRT dayake standing suka samu , Aunty salmah tace nablah ajiye jakar kayanki ki zauna akai .
Sannan kiciromin wayata a jaka ki duba dealing zakiga wata number MTN karshenta 12 kikiramin ,ki mikomin.
,haka kuwa nablah tayi tare da Mikowa Aunty salmah wayar .
ta manna wayar a kunneta tare dayin sallama. hello hjy gamu cikin motar obalende daga nan wace motar zamu shiga” daga can bangare ummi kuwa cewa tayi yauwa inkunzo ku hau motar mai zuwa aja sai ku sauka (a jakonde first get).
ai kinsa lekki ko?
” aunty Salmah tace A,a bansan side din ba , ina dai jin sunan waje.
Ok .. inda kun sauka a first get din kiyi flashing dina.
Aunty salam ta, ajiye wayar..
Bayan kmr awa daya da rabi sai gasu jakonde first get…
Kiran ummi suka sake yi kmr yadda tace .
ok kuyi crossing main road ta hannuku na daman zakuga sambord an rubuta lekki road hanyar zaku biyo layi na uku .
daga hannun hagunku in kun kai kikirani
,nan dai suka sakeyin tafiya minti goma suka sake kiranta byn ta dauka ne tace kuna kan layin ne?
Aunty salmah tace Eh to zakuga cona ta hannun hagunku zakuga wani babban church ,dan suna tafiya ne suna waya da ummi tana basu direction .
Aunty tace ga church din nan ma mungani to ku tsaya a wajen zaki ga get opposite din shi .aunty Salmah tayi saurin cewa shine.
PLASNUW ROWS FAMILY ESTATE ?
Ummi tace yauwa shine kin iya rubuto?
Sai da Aunty salam tayi murmushi sannan tace ba laifi .
ok bani minti biyu na kira securities din get din.
” za su tambayi sunanki aunty salam tace to ….
+
Nablah ta zubawa hadadden get din gidan idanunta kawai wanda basan yadda zata iya kwatanta girman sa ba ballanantana tsawonsa .
sai dai zata iya kiran get din da JAMA GET ..wato na gidan bursunan dake garin Lagos KIRIKIRI .
daya daga cikin securities din get din ne ya dan leko ganinsu tsaye ne yasa shi cewa madam can i help you?
who are you, looking 4 duk a tare ya jehowa auty Salmah tamyr dayake itace kusa dashi.
,
the person we are lokin 4 said we should Wait 4 her “inji cewar aunty Salmah mutumin yace or rigth sannan yakoma mazauninsa “
can ya sake lekowa yace are you salmah ?
“auty Salmah ta daga masa kai .
‘yace ok you can come in.
tare da bude musu Dan karamin get suka shiga ya nuna masu ,wani gurin yace inter and rigth ur ful name down
,Can u write ya sake tmbyr Aunty Salmah.
tace Eh.
byn sunyi komai har da sign sannan ya sake bude wata kofar yayi gaba yace su biyo shi a baya.
‘Ahankali ta sunkuyar da kanta kasa tana wasa da yatsun hannunta wanda kusan rashin abinyi ne kesata yin haka. +
,haske taga ya garwaye parlour gabadaya ‘koina ya dauki haske tamkar rana ce ba dare ba.
wani irin kamshi ne mai azababen dadi yake kusantota ,har inda take zaune ,yayinda mamallakin turaren ke tukarowa parlour zuwa indasuke haka shima kamshin ke kai kawo acikin hancin nablah .
har zuwa sanda mamallakin kamshin ya karasa yashigowa, gabadaya parlour ya canza wani irin cent na daban”, take gabanta yashiga dukan uku uku gashi tana san dagowa ta kalli kowaye mamallakin wannan azababen kamshi Amman takasa dago idanunta,dan ko kwakkwaran motse kasawa tayi ballanantana tasan kowaye mamallakin wannan turaren mace ko namiji ne sakamakon kanta dake Duke akasa har lokacin.
Ta kafe teas din parlour da ido “.
Ta kasan idanunta ta hango wando jeans. wanda hakan ya tabbatar mata da mammallakin kamshi turaren nan namiji ne .
“duk da bataga komai nashi , baya ga Zara zaran yatsun kafafuwansa da kowani ke kwance da gargasan gashi.
‘ahankali yake takowa zuwa inda ummi take zaune .
Muryar ummi taji tana cewa ka fito son ?
tun da zu muke Jira … matarka tace wanka kake yi ,’ahankali ya juyo ga mahaifiyarsa yana kallonta sannan yadanyi murmushi gefen baki .
hannunsa yasa ya dauki remut ya canza channel zuwa ta kallon Ball sannan ya Mike kwance kan three site hade da cewa gani first lov anything for you my beautiful mum…
Ummi ta saki murmushi sakamakon jin dadi abinda yace sannan tace kai ko Allah ya shirya min kai …tare da kai hannuta kai kan tilon dan nata ta shafa tautausar sumar kansa tana jin wani irin sanyi a ranta .
Muryata A dake takira sunansa ‘ deeni…..
Ya dago rikitattun idanushi yana kallon ummi batare da yace komai ba …
“maganar mai aiki da mukayi dakai za’a kawo ,to orready ma she’s here.. ta iso sauran muji meyye ra:ayinka nidai na amince daita hundred percent .. +
kasa kasa yayi da muryasa wanda daman can haka yanayin maganarsa take ..
Kuma yadda yayi magana ummi ce kawai zata iya jin meyace ..
tana ina …….?
abinda kunne nablah ya ji kennan.
gata can ummi ta fada tare da nuna inda nablah take zaune …
‘ahankali ya juyo tare da kallon inda ummi tayi mishi nuni da hannuta. idanunshi ya runtse gam sannan cikin sanyayyayiyar muryasa mai kashi jikin duk wanda tsautsayi yasa ya fada kunne shi ” yace first lov… kice ta Mike naganta ..
tsoro da fargaba tare da frigice ne suka taru suka kaiwa zuciyar nablah farmaki” tashi daya taji jikinta yakama rawa gabanta yashiga faduwa da sauri, tasoma tunanin abinda ya kawota wannan gida mai cike da abun tsoro da abubuwan ban mamaki …
sai kawai ta tsinci kanta da ambato sunnan Allah a kasan ranta da karanto duk addu’ar datazo bakinta Dan rage jin tsoro ” take taji wata natsuwa tazota mata aboye ta dinga sauke ajiyar zuciya .
‘Ahankali ummi takira sunata nablah Mike tsaye man ya ganki , batare da wata gardama ba,ko bata lokaci ta Mike tsaye kmr yadda ummi tace .Amman still jikinta Bai bar kirma ba haka ma hannuwata suna sarkafe da juna tana cigaba da wasa dasu ” yayinda ta cikin hijab dinta kuwa uhmmmm tashin hankali kennan ‘dan kuwa jikinta sharkaf yake da gumi tsabar frigici datake ciki ,duk da tsanyi AC dake aiki a parlour hakan bai hana gumi tsassafowa ilahirin jikinta ba .
idanunshi da Suke a runtse ya kafeta dasu yana kallonta ,jin shr,n da yayi yawa ne yasa nablah dago fararen idanunta dan satar kallon mutumin dataji an Kira da suna DEENI . take zuciyoyinsu suka buga a lokaci daya …….
Yayinda jikin nablah ya dauki kirma… zuciyarta ta sake amsawa daf..daf..daf.. ‘da sauri tayi kasa da idanunta ahankali ta furta wayyo Allah na.. a kasan ranta.. mutun ko aljani nake Gani yau .
, tsabar kyauwu halitta da Allah yayi masa .tunda take a rayuwarta bata taba ganin mai tsananin kyau halitta da kwar jinin irin mutumin da take gabansa tsaye a halin yanzu haka ba .
kusan tsawon minti 5 ya dauka yana kallonta batare daya bude Idanunshi ba” sannan ‘ahankali ya dauke idanunsa daga gareta yakoma ya kwanta sosai acikin kujerar dayake “ummi tace ya’akayi ne DEENI naji kayi shr… ….
Tayi…..
abinda kawai nablah ta iya ji kennan daga bakinsa , Dan gabadaya ma jitayi kunneta ya daina jin magana tsabar tsoro da rikici hakan km sai lokacin hankalinta ya dawo gangar jikinta daga mummunar damuwar data tsinci kai ciki …
Amman fa duk da Haka a tsorace take da mutumin dake kwance a gabanta . +
,ummi kuwa ta furta kalmar alhamdulilllahi yafi Sau dari kafin daga baya ta kalli nablah a tsanake sannan tace jeki nabla ma hadu gobe kinji ..
,muryarta nablah a sarke tace to … sai da safenku sannan ta juya cikin tsanyi jiki ahankali take tafiya yayinda itama ummi ta juyo tana sake bin bayan nablah din da kallo har tabar parlour zuciyarta na karanto mata abubuwa dayawa game da yarinyar ga wani irin tausayin yarinyar daya mamaye zuciya …
Bangaren deeni kuwa gabadaya ji yayi tamkar am masa wanka ne da ruwan sanyi , jikinsa ya mutu murus tamkar mara lfy haka ya dinga ji ajikinsa tun sanda yabi hannu ummi da ido .
kwarai yaso ya bude idanunshi yakarewa yanayinta kallo Amman sam yakasa aitawatar da hakan , sai ma tsintar kansa da yayi da mummunar faduwar gaba a lokacin da yake kallonta .
, wanda har yanzu dayake kwance a wajen bai daina jin yadda zuciyarsa ke bugawa da sauri ba ..
‘ahankali yasake runtse idanunshi gam ko zai daina jin abinda yake ji ajikinsa ,amman kwata kwata sabanin haka Ya dinga ji .
Sai ma zuciyarsa da tacigaba da harbawa da sauri da sauri .
abinda bai taba ji atare dashi ba kennan tun iya tsawon rayuwarsa wai faduwar gaba akan mace ….
Macce ma , mai matsayin mai aiki …
ahankali ya furta sunan da yaji umminsa takira yarinyar dashi nab….lah… Yadda ba mai jinsa ….
muryar matarsa yaji tana cewa ummi ai wannan yarinyar bakaramin daga tuta tayi ba , tunda har my hrt yace tayi.
ummi tace al,amarin Allah kennan nima gsky naji dadi matuka da tamasa saboda daganin yanayin yarinyar ba tmby akwai natsuwa atare daita .
kema kiyi kokarin ki sota a ranki ” ba mamaki wata rana tayi miki amfani .
dagani bazamu samu matsalar daita ba “, zeenat tayi murmushin karfin hali tare da kwabe baki Dan ita kwata kwata bata ji son yarinyar aranta ba . tanaji a zuciyarta tamkar ta sallameta daga gidan ne yanzu yanzu ….
+
Muryata Cike da takaici tace wani amfani km ummi .Allah yakiyaye wannan yarinyar tayi min amfani .
ni wlh Dan bani da iko ne.
tunda kince ta kwanta miki a rai .
wlh da tuni korarta zanyi. Dan Haka kawai nake jin tsanar yarinyar har cikin raina .
deeni dake kwance ya ja tsaki mai tsawo..Dan takaicin maganar Zeenat din sannan ya Dan juyo ya tsareta da rikitattun idanunshi masu sata natsuwa a duk lokacin daya watsa mata su.
take tayi shr ta hadiye maganar ta ,sannan yace I don’t want to hear anything stupid here.
A Zafafe yacigaba magana haba kin cikamin kunne da shirme banzan ki .
sannan ya dan sausauta murya tunowa da yayi ummi natare dasu ,cikin sanyi jiki ya juyo suka hada Ido da ummi . itama shi ta zubawa idanunta kawai .
Cikin sanyi ya kamo hannun ummi cikin nasa yana mai karkada mata kai ‘ahankali yace am sorry…my first lov .
take ummi taji wani irin sanyi a ranta , gashi bata iya fushi da tilon dan nata, Kuma bata son damuwarsa ,gara ace duk abinda zai same shi ya tsaya a kanta.
” hannuta tasa ta dungure masa kai dashi ” tace kai dai kacika maseefa wlh ai barewa batayi gudu ba danta yakasa rarrafe like father like son ai lokacin aliy ….. ganin ummi zata soma tabo labarin dad dinsa yasa yakatseta da hanzari muryarsa cike da shagwaba yace please first lov ya nuna mata yatsansa alamu tabashi 1 minti sannan ya juya inda zeenat ke zaune ta kasa kunne, kallo daya yayi mata wanda yasa ta gane abinda yake nufi tun kafin yayi magana ta Mike tsaye ‘ahankali tabar gun.
hade da cewa maseefafe banza kawai akasan ranta in maseefarka ta motso kowa yashiga uku acikin gida.
sai da ya tabbatar da Zeenat tabar part din gabadaya sannan yace ok continue first lov ummi ta tabe bakinta sannan tace anki ayi continue din.
dan saboda za’a yi maganar dad dinka shine ka koranmu yarinya.
A shagwabe yace haba first lov a gabanta zakirinka jistin din abinda dad dina yayi ya girgiza kai impossible…. Ai zaki sa ta raina ni .
Ummi Tasaki murmushi ganin yadda ya hade rai kmr mai shirin kai gumurzu sannun gyenbo sarkin son girma aiki DEENI ya yamutsa fuska jin abinda ummi tace murmushi tayi nan dai suka cigaba da hira su ta tsakanin uwa da “da” …..
+
Koda nablah ta koma dakin daaka sauketa ciki ,key tayiwa kofar saboda tsaro ,sannan ta cire hijab din jikinta ta tsaya tana bin jikinta da kallo yadda take ajike jagab da gumi tana tsiyaya ,dariya ce ta kufce mata, ai kuwa tashiga yiwa kanta dariya ,sosai tayi dariya har da rike ciki saboda tuno yadda ta koma kallar tausayi dazu a parlour.
,a hankali ta zare kayan jikinta dayake doguwar riga ce “ta daura zaninta data zo dashi tashiga bathroom..
Byn tayi wanka hade da dauro alwala ta fito , duk wani abu da yazama na aladarta kafin tayi bacci sai datayi , tare da yin addu’oi tsari ta shafe jikinta dashi ta nemi waje akan gado tayi kwanciyata cike da kewar iyayeta da yan’uwanta ‘ahankali ta runtse idanunta tayi lamo akan gado wani tunanin ne yazomata take taji gabanta yashiga faduwa. anya kuwa … banyi kuskuren cewa bazan koma gida ba kuwa? duk da lokacin dana fadi hakan ummamu kin amincewa tayi da hakan.
‘ahankali” ta sauke naunauyen ajiyar zuciya a filli ta furta kai bazai yiwa ba wlh na canza shawara gwara narinka zuwa gida time to time ina ganin yangidamu .
jin wannan shawara data bawa kanta ne yasa taji wata natsuwa nasake bin jikinta ta kudindine jikinta waje daya a haka har barci mai nauyi yayi awon gaba da ni….
Can kuwa bangaren uwa da “da” ummi ce ke kokarin mikewa tsaye tace kai ni tashi kaje gun matarka Lada ya isa haka bacci nake ji .
DEENI ya karyar da wuya yana duban agogon dake manne a bangon parlour sannan yace look at the Time first lov. fast ten fa yanzu muna hirarmu mai dadi shine zaki koreni ko… Cike da tsokanarsa ummi tace .. ni na isa na kor i farincikin rayuwata hasken duniyata hade ta karasa fadar haka tana kama bakinta. +
DEENI ya tabe baki kawai batare da yace komai.. ok baka yarda Kaine duniya ta ba.. murmushi gafen baki yayi tare da kashe mata idonsa daya” ai na dade da sanin wannan .
Kmr yadda nima kece duniya first lov ….. sannan suka Mike atare yace muje naraki .
har dakinta yakaita ,ta juyo tana sake kallon dan nata Allah ya maka albarka yadda kakemin biyayya kaima Ina rokon Allah yabaka masuyi maka fiyye da abinda kamin ina addu’a Allah yabani aron rai da lafiya naga jikokina wato yayanka….
jikin deeni na maseefa daukar sanyi ” a duk sanda mahaifiyarsa taimasa wannan addu’ar yakan tsinci kansa cikin tashin hankali.
,da yanada yadda zaiyi yasamu yaran dazasu yasamarwa mahaifiyarsa farinciki da tuni an wuce wajen .
batare da ya bari tayi nasa auren datake kokarin yi masa ba.
yana son kullun yaganta cikin farinciki fiyye da wanda take ciki a yanzu tana tagama fadar haka, ta juya masa baya dan bata san ganin damuwarsa.
, cikin sarkewar murya tace kaje abunka ai burina ya kusan cika ” Allah yatashe mu lfy da kyar ya iya amsawa da Ameen sannan, ahankali ya juya ya bar dakin direct dakinsa ya wuce ya zauna akan kujerar da yake zama idan zai yi aiki a system dinshi tare da sa hannushi duka ya dafe goshinsa dasu .
yana matukar jajantawa kansa ” hakika Allah yabashi komai tare da wadatashi da abubuwan more rayuwar duniya sai dai yarage shi da abu daya Wanda yakasa daurewa wato zubar masa da ya’ya da Zeenat ta dinga yi arariya …..
‘Ahankali yasoma lumshe rikitattun idanunshi Yana budesu sunnu Ahankali har ya rufesu luf… Sosai yayi zurfi cikin wata duniya ta daban .yayinda zuciyarsa ke bugawa ,da sauri Wanda yarasa dalilin jin hakan.
yana cikin wannan tunani ne bacci mai nauyi yayi awon gaba dashi .
+
Sapanin bangaren Zeenat da” tunda ta kwanta akan makeken gadonta bacci ya kaurace daga idanunta” bbu abinda take tunani Sai mijinta.wanda tun tahowarta da tunaninsa take bacci take tashi
” taso a daidai wannan lokacin tana tare dashi rungume a saman fadadden kirjinsa mai cike da yalwan gashi amman kashiii… ..
son zuciyarta da km kaddara data gitto tasanyata zama cikin kadaici da kewar mijinta.
‘Ahankali tasa hannu ta rarumo pillow dake kusa daita “ta rungume tsam akirjinta,tare da fatan samun saukin abinda take ji ,a tunaninta ko hakan datayi zai ragewa zuciyarta damuwa akan rashin mijinta kusa daita. amman sam hakan yaki samuwa gareta.
‘ domin pillow kadai bazai taba . maye mata gurbin dumin jikin mijinta datayi missing ba.
Dan yarigada yayiwa jikinta “mugun sabo da zazzafar soyayyarsa mai cike dadi da kashe tsansar jiki.
Uhm DEENI kennan daban yake acikin maza Haka ma soyayyarsa .
ganin bacci ya kauracewa idanunta ne yasa, ta Mike da kyar tashiga bathroom ta dauro alwala, nafilar dare ta fara ‘da zumar samun sausauci a gurin ubgj tare da rokon Allah Ya sake mallaka mata mijinta a tafin hannuta. ,
Hankalisa kwance yake shakar baccinsa tamkar Yana sama jannati.
Kyakkyawar budurwar ce take kusantoshi har inda yake kwance flat akan bed dinshi tare da sa hannuta,ta shafo kyakkyawar fuskarsa mai cike da suma da annuri.
‘ahankali yasoma bude Idanunshi tare sauke kwaryar idanushi acikin nata , tsaye take kyam . tana sakar masa kayataccen murmushin daya bayyana wushiryarta.
‘ahankali ta Miko masa zarara yatsun hannuta masu matukar kyau da daukar hankali. tamkar jira yake ya damki hannunta tare da fizgota saman daddaden kirjinsa mai cike da yalwar gashi ya rungumeta tsam tsam ajikinsa yana sakin numfashi shima Ahankali yakai bakinsa tsaitin wuyanta Yana shinshina kamshin jikinta .
cikin wani irin salo yasoma cire mata kayan jikinta, bata hanashi ba har yagama cire mata kayan jikinta tsab .
ta saura daga ita sai pent da bra Shima ‘ahankali ya zaresu yayi flinging dasu gefe , breast dinta masu matukar kyau “da daukar hankali suka bayyana sai sheki suke tsabar baiwar da Allah yayi musu .
tamkar wani mayyunwacin zaki a gigice yasa hannuwansa duka ya damki dukiyar fulaninta yasoma murzawa Ahankali Yana lumlumshe idanu, itama kmr Jira take ta dinga narke masa ajiki tana cire masa kayan jikinsa, habawa Ai gabadaya deeni ya susuce ya fara romancing dinta cikin zafi zafi tare da hade bakinsu waje daya Yana tsotsa tamkar yasamu loly pop +
Cike da shauki ya birkito daita takoma kasa tare da zare mata pent din dayayi saura ajikinta , sannan yahaye saman ruwan cikinta ” yasoma kokarin ware kafafuwanta kana ya tsaita kan joystick dinsa cikin kofarta, Ahankali cikin wani irin salo ya zira jijiyarsa ciki.
hankali kwance yasoma saduwa daita Yana cikin kokarin yin realize ne sautin . allahu Akbar lahu akbar …. kiran sallah da’ake kwallarawa daga masallaci dake cikin estate din ne ya farkawa dashi a , afrigice ya farka tare da wata mummunar faduwar gaba ya Mike zaune hannushi dafe da kirjinsa Yana waige waige acikin dakinsa.
Numfashi sama sama kawai ya dinga saki ” Tare da kallon ilahirin jikinsa dake kirma… duk abinda ya farkar dashi daga baccinsa bai bashi mamaki ba facce ganin jijiyarsa’ da yayi a mike sambal… da km yadda take harbawa da sauri yasa hankalinsa mugun tashi.
Gabadaya gangar jikinsa rawa yake zuciyarsa ce ke harbawar da sauri ,take ya Daura hannuwanshi duka kan joystick dinsa ya dafe .
wani irin azababen shock yaji ajikinsa Wanda yasa jikinsa sake cigaba da kirma…
.
, ‘ahankali ya dinga furta kalmar inna lillahi wa inna lillahi rajiun akasan ranshi, ya jima zaune yana maimaitawa sannan ya samu sauki da natsuwa zuciya iya tunaninsa Bai san meyasa yin irin wannan mafarkin ba” haka nan km Bai kwanta da Sha,awar wata diya macce a ranshi ba ,hasali ma zuciyarsa cunkushe take da abubuwa da yawa kafin ya kwanta ,Sai dai ko daga Allah ne .
Mike yayi Ahankali yashige bathroom domin tsarkake kansa.
Byn yayi wanka tsarki ne ya fito tare da dauro alwala yazo ya gabatar da raka’a taini fajir sannan ya wuce masjid . +
koda ya idar da sallah ma ya dade zaune Yana jimami da mamakin mafarkin da yayi har ya dawo gida ,ya kwanta rigingine akan royal bed dinshi Bai daina jin sa some how ba .
8:00
Daidai Ya tashi .
duk ilahirin jikinsa a sanyaye yashiga bathroom “wanka yayi ya fito yasoma shirin zuwa aiki .
Yana gama shirinsa tsam cikin uniform din su na soldier .
, ya nufi part din first lov domin yaga yadda ta tashi dan ka,ida ne muddin gari ya waye sai yasanya mahaifiyasa a idanunshi sannan yake fita .
da sallmar sa yashiga dakin zaune yasameta akan gado, tana ganinsa ta fadada fuskarta da murmushi ” tasoma masa kirari kmr yadda tasaba” kaga namijin uban mazaje namijin duniya yaro in bakayi bani guri” sannu zaki maza,km jarumina matashi magidanci son kowa kin wanda yarasa.
“da” daya tilo ” da” daya .
kafi Yaya dubu agurina ,sadauki ranka yadade ta dunkuleta hannuta tare da jinjina masa “
DEENI ya karkace kai kawai yana kallon mahaifiyasa “yana sake jin yadda soyayyarta ke sake ratsa kowani part na jikinsa.
duk duniya bashi da sama daita. itace duniyarsa ,shiyake daita ,ita take da shi cikin takunsa na kasaita yakaraso har inda take ya zauna kusa daita yana murmushin ,duk wannan kiraki nawa ne ni kadai first lov sannan yace mun tashi lafiya .
,tana murmushi tace lafiya lau dana , yakata shi kaima ?
,ya shagwabe fuska kmr wani karamin yaro yace lafiya Amman ba lau ba .
Ummi ta zaro idanu tunaninta ko wani abu ne yana shi yin bacci .
,meyasa Meka ya kai dana ummi ta fadi hakan tana mai nazarinsa ” Ahankali ya shagwabe fuska byn tunaninki ne ya saka gaba ya hanani yin bacci ummi ta sake zaro idanu tare da sakin murmushi irin na manya.
Aiko ” tunanina bai kyauta min ba wlh .
” Har daya hanawa tilon dana samun natsuwa”
Deeni yasake narke fuska yana duban umminsa , Allah first lov ki nemo shi tunanin ki hukunta shi da kanki .
ta sake yin murmushi kusan koda yaushe agaban mahaifiyasa haka yake zama tamkar wani jinjiri , ummi numfasa sannanAuntyna tace maza tashi kaje nasan yanzu haka ko breakfast bakiyi ba kike shirin fita ?
A sukwane ya Mike tsaye yana duban ummi .
“mkr kinsani wlh amman daga wajen yin break zan wuce office , ganin yana tsaye bashi da alamun tafiya ne yasa tasan abinda yake Jira ,dan haka tashiga yimasa addu’a tare da sake nuna masa mahimmanci Zeenat a gurinsa .
sannan ya fice daga dakin hade yi mata sallama ..
+
Koda ya bar part din first lov part din zeenat yashiga kwance ya tadda ita Tayi zurfi cikin duniyar tunani sannan idanunta na kallon celling dakin da dukkannin alamun ma bata samu runtsawa ba .
‘Ahankali Yasa hannunshi ya ja yatsun kafarta dashi ‘ a sanyaye ta kallosa da idanunta tana may sauke naunauyen ajiye zuciya sannan ta zuba masa kwayar idanunta cikin nasa hk shima yake kallon tare da dan matsowa kusa da ita sosai yana son sake karantar yanayin da take ciki .
haka kawai wani lokacin yake tsintar kanshi da tausayawa mata ,sbd yadda take maseefar sonshi da kishinsa.
daidai kunneta yakai bakinsa, kana yayi kasa kasa da muryarsa yace meke damunki haka Zeenat …….? ‘Ahankali ta girgiza masa kanta ,alamun bbu komai, ya furzar da iska mai zafi daga bakinsa .
saannan yace ok..to meyya hanaki bacci?
Ahankali ta juyo ta zuba masa kananun idanunta tana kallonsa dasu sosai take jin yadda kaunarsa ke sake taso mata tamkar zata huda mata zuciya , tare da mamaye mata dukkan sansanr jiki .
Sai data kalleshi son ranta sannan ta sauke numfashi ‘ahankali muryata a shagwaba tace kai ne da tunaninka ya hanani runtsawa.
ya runtse Idanunshi sannan Ya bude su Dan sake dubanta suka hada Ido dashi ta lumshe masa idanunta tana sake tabbatar masa da iya gskyrta ta fada . +
yes …. tunaninka ke damuwana yayinda kewarka ke hanani ke hanani sukuni ballanantana na samu sararin ishashen bacci .
, ajiye zuciya ya sauke tare da zama gefen bed side dinta ,yakamo tafin hannuta cikinsa yana murzawa ahankali ‘ahankali .
tsareta yayi da rikitattun idanunshi yana kallon cikin kwayar idanunta .
‘ itama shi take kallo still take ta dinga jin wani iri iri ajikinta . gabadaya tsigar jikinta suka Mike tsaye yrrrrrrrrrrrrr……
Bazato ba tsammani taji sautin muryarsa meyasa kike son halaka kanki da tunani na Zeenat ?
cike da damuwa yake magana , alhalin duk maseefar da tasameki kece silar jefa kanki ciki.
kau da kanta tayi gefe window ta zubawa wajen idanu kuri batare da tasan abinda yakama tace ba .
” ganin da yayi hawaye ne keson zubo mata , yasa hannusa Yana juyo da fuskarta garesa suna sake fuskarta juna.
yace karki soma barin hawayen nan su zubo daga idanunki sbd bana bukatar ganinsu km basu na tmyeki ba .
D karfin tsiya ta ciza lip’s dinta tasoma kokarin mai da kukanta.
inason kin manta komai dangane da abinda ya faru baya kicanza new life banason ganinki cikin wannan moon din “ko kinason first lov ta fuskanci wani abu na damunki byn damuwar rashin haihuwa da tasan itace matsalar mu , ta girgiza kai yace kiyi fatan samun wasu ya’ya masu albarka .
maganar dayayi mata kadai Ya taba tsantsar jikinta tare kwantar mata da hankali.
Hannuwata dake cikin nashi tasa ta matse tafin hannushi cikin tare da danne hawayenta , muryata a sarke tace Ina sonka dayawa my heart….. ,meyasa kaima bazaka soni tamkar yadda nake maka ba Ina son kasancewa tare da kai bana son yin nisa daika .
Uhmmmm Zeenat kennan Ina sonki man abinda kika aikata gareni ne yasa soyayyarki takasa yin tasiri a zuciyarta sannan kece kika hana wannan soyayya samu gurbi may mahimmanci,Amman dai… Sai km yayi shr tare da mikar da ita tsaye ya mannata da gafen jikinsa yana shafa bayanta ‘ahankali , .
dan yasan duk randa basu kwana tare ba “bata samun ishashin bacci ga tarin tunanin rashin haihuwa da take kwana yi wanda duk ita tajefa kanta cikin .
Ahankali Ya juyo daita suna facing juna tare dadago habarta ya zubawa fuskarta eyes dinshi sannan ya kai bakinsa kan nata ya tsotsan lip’s dinta yace I still care about you. +
murmushin tasakar masa Wanda ta jima batayi irinsa ba ,cikin jin dadi ta kamo tafin hannushi muje kayi breakfast .
am orready late Zeenat anajirana a office nebazan iya tsayawa cikin komai ba . uhmmmm nidai please muje kaban ko 5 minutes na hada maka ko tea ne kaji.
ya karyar da kai kawai yana dubanta , atare suka jiro hannunsu sarkafe da juna har darning wanda daman komai a kammale yake ta zaunar da shi cikin sauri sauri ta hada mishi tea kurba uku yayi ya Mike tsaye , tasan yanzu tana sake yin wani complain .
sunanta sorry a gurinsa Dan wannan kulawar dataga daga gareshi tasan darajar addu’ar data kwana tana yi ne da km ummi dake tsaye a tsakaninsu har Bakin kofar main falon din su takai shi ta Mika masa briefcase dinsa Dan bayarda da hakan sannan ta koma dakinta …
Direban sa wanda shima soldier ne yataso da sauri yakarbi briefcase din hannunsa hade da Sara masa sannan ya bude masa murfin kofar.
,tun kafin karosowarsa Bakin get din gidan securities ke Sara masa har aka bude get suka bar gidan ..
Tunda ta tashi tayi sallar asuba take kwance takasa fita ko nan dacan tana jiran kira daga masu gidan Amman shr ga yuwa tasoma kmr me .
Mikewa tayi jiki a sabule tashiga bayi wanka tazo ta canza kaya tare da zubawa sarautar Allah Ido can taji ana nouking dakin ahankali ta Mike ta bude kofar ummi tagani tsaye ta dan matsa taba hanya tashigo dakin sannan ta gasheta cikin sakin fuska ummi ta amsa tace nablah ya kwanan bakunta ?
Ta Dan yi murmushi tare da cewa alhmd ummi tace Masha Allah yanzu dai muje kiyi breakfast daga nan sai mamana ta nuna miki aikin da zaki rinkayi ummi nagama fadar haka ta juya itama nablah tabi bayanta …
Falo uku sama uku kasa uku banda dakuna wanda sunkusan goma acikin gidan , madam kmr yadda taji laraba nakiranta da shi ita ke nuna mata komai.
A yatsine tace ki dauki gyaran sama kibarwa laraba kasa nablah tace mata to dan batada zabi sai abinda tace ..
har falon magidan da dakin sa komai dai ataikaice sai da aka nunamata Kuma tun a rana tasoma aikita hade da tattaro kayanta tadawo sama kmr yadda ummi tabata umarni .
Misalin karfe takwas dai dai na dare nablah ta kammala da komai na aikin gidan har part din abinci wanda tare da madam muzeenat sukayi komai wai tana son ta kware fannin abinci mai gida dan haka gabadaya agajiye take likis.
Tana shiga dakinta kwanciya tayi bata dade ba bacci yayi gaba daita.