Washegari
karfe bakwai daidai ta fito daga dakin da’aka sauke ciki. shr koina babu motsen kowa ballanantana mutun ya saka ran ko akwai wani bil,adama acikin gidan kasancewar week end ce.
tafiya take ‘ahankali cikin tsanyi jiki , har ta iso part din ummi takutsa kai ta shiga da sallmarta … 1
nan ma shr ba motsin kowa ciki “can taji ” alamun motsen ruwa a bathroom dan Haka tabbatar da ummi tana.
” bata wani tsaya batawa kanta lokaci ba ta soma yin abinda yakaita, daidai nablah tagama gyara koina ummi tafito daga bathroom..
tana ganin nablah ta saki fuskarta sosai tare da yin murmushi . nablah ta gaishe da ummi cike da girmamawa .
Amman banda part din mai gida Dan so take sai ta gama da koina acikin gidan sannan tashiga part dinsa saboda tsaro ..
STORY CONTINUES BELOW
tsabar rikecewa batasan sanda ta kama handle din kofar bathroom ba ta afka ciki … Ai ko tana ganin ba kofar fita bace ta sake juyo da sauri ,bbu inda baya rawa ajikinta tare da tattara kayan moupystick dinta tabar dakin da saurin bala’i tana haki sama sama tare da fidda numfashi .
A can bakin corridor din dake tsakanin part din deeni da ummi taja ta tsaya ta sake fidda numfashi tare da addu’ar Allah yasota.. ..
tabe bakinsa yayi tare da jan tsaki sannan yacigaba da baccinsa .
Yana jinta Yayi banza daita tamkar bai jita ba Sai ma hankalinsa daya dauka kacokan yamayar kan ummi dake kallo, muryarsa a dake yace first lov ni zani masallaci ta juyo tana dubansa tare da ce wa To sai kadawo yarona , sa kai ya fice .
takasan idannu take kallon every step of him dab ..dab… kmr wani jinin sarauta yayinda duk takunsa daya ke daidai da bugun zuciyarta har ya bace wa ganinta idanunta nakansa km Sai lokacin tasamu natsuwar zuciyarta, dan gabadaya ilahirin jikinta bbu inda bayi sake ba .
Muryata Ummi ce tasa ta sake dawowa cikin natsuwarta . nablah ki dawo kan kujera man ki zauna kin wani je can kin rakube akasa… maza taso kidawo nan kusa dani kinji “ki saki jikinki damu nan ma tamkar gida ne , a sanyaye nablah ta Mike tayi kmr yadda ummi ta umarceta .
Ummi tacigaba da magana . kishirya zuwa anjima akwai doctor da zata zo ta miki test kinji nablah cikin sanyin muryarta tace to…..
Ummi tasa hannu ta dauki remut tana canza channel zuwa zeeword .
, zeenat ta dan juyo a wulakance tana kallon inda nablah ke zaune tare da watsa mata wata uwar harara .. bakinta ta tabe kawai cigaba da aikawa nablah da harara iri batare da tabari ummi taganta ba ita dai haka kawai take jin tsanar yarinyar har cikin ranta .
byn doctor din ta dibi jininta tashiga wani daki still dai acikin dakin da suke ciki tare da bawa nablah umarnin Wuce wa.
Ta Mike jikinta bbu kwari Sai dai bbu wata alamun damuwa ko fargaba atattare daita .
direct hanyar step tabi ” ta nufi dakinta” koda tashiga dakin ma rasa abinyi tayi domin kewar yan gidasu ne tattare da zuciyarta” tana ji kmr taje tasamu ummi ta roketa takirawo mata number auntyta su gaisa .
tunawa datayi Killa ma yanzu haka ummi na can tare da mutun da ko kafafunsa ta kalla zuciyata tamkar zata tarwatse takeji” yasa ta share kawai taki koma gurin ummi ..
Mikewa tsaye cikin hanzari da niyar zuwa tasamu ummi ta taimaka ta kiramata auntyta .
bude kofarta ke da wuya taga mutun tsaye abakin kofarsa yana kokarin yiwa kofar dakinsa da key .
Da sauri ta risinawa tana gaishe shi shiru yaki amsawa km bai da alamun zai amsa din sai ma dauke kansa dayayi yacigaba da abinda yake .
Jin yadda idanunshi ke yawo a tsantsar jikinta ne ” yasa Kirjinta ke wani irin harbawa da sauri tamkar wacce ake bugawa guduma a kahon zuwa .
Yanayin sanyita da tafiyarta yasake shagaltar dashi ba dan deeni yagaji da kallonta ba ,ya dauke idanunsa akan ba Sai Dan gudun juyowarta cikin sautsayi.
shr kusan two minutes sannan yazo ya wuce ta gefenta zuciyarsa na tacigaba da harbawa .duk da Bai bari jikinsu ya tabu da juna .
Tana nan tsaye har yazo ya wuceta tare da bude wata kofa ya shiga dan kusan har yanzu bata gama sanin kan dakun nan gidan ba.
,inda tasan zata samu ummi kai tsaye ta nufa zaune suke ita da Zeenat kmr koda yaushe suna kallo TV suna hira abunsu hankali kwance. Yayinda kayan fruit ke gabansu da sallmarta takarasa inda suke sannan tasamu guri kan Tia’s ta zauna tana wasa da Zara zaran yatsun hannuwanta. ummi ta juyo ahankali tana duban nablah byn ta amsa sallamarta kallonta kawai take Tare da nazarinta .
yayinda zeenat tunda ta juyo ta mata kallo daya ta dauke kanta tare da mai hankalinta kan film da,akeyi .
Sai da ummi tagama nazarinta tsab sannan ta takira sunan nablah ..
Ahankali ” tace Allah aunty bbu matsalar komai fa aunty Salmah tace to.to. shikenan ,ki kama kanki da kyau km ki dinga saka hijab dinki duk inda zaki shiga a gidan .
Nablah tace har baccima dashi nake aunty Salmah Tayi yauwa Yar gari nablah na murmushi tasake bude baki da niyar tambayar auntyta dip …maganar ta tsaya …… Tana zaro Idanu waje sakamakon hasken dataga ya gwaraye dakin gabadaya duk daman can akwai wuta a dakin dan koda tashigo fan na aiki ..
kwance yake akan kujera idanunshi a lumshe yana kallonta kmr ranar farko daya soma ganinta a rayuwasa .
murya aunty Salmah taji tana cigaba da cewa lfy na jiki shr kin dauke wuta kmr NEPA.
Itama shanyayun idanunta ta zuba masa kawai tana kallon kwakkywar fuskarsa dam …taji kirjinta da zuciyarta sun amsa a lokaci daya take ta soma jin tsoron yanayin irin kallon dayake mata.
,jikinta kuwa Banda kirma bbu abinda yake ,takoina gumi ya dinga tsatsafo mata ajikinta Jira kawai take taji yace arrrrrrr ta arce da gudun maseefa Amman Sai kawai taga sabanin haka, domin ko motsa bakinsa bai da alamun yi ballanantana akai gasamun fitowar kalma daya daga bakinsa Sai ma taga tabe bakinsa tare da dauke idanunshi akanta .
tayi shr sannan komai ta tuna ta dagamin kai …
Koda tashiga dakin ma bayi tashiga dan jin yadda cikinta ke murdawa ,tun sanda take tsaye gaban horo dan sunnan data bashi kennan take jin yadda cikinta ya cure guri daya .
toilet tayi sosai byn tagama tashiga cikin bathtub ta kunnawa kainta” shawa ta dade kwance tana jin dadin yadda ruwan ke rasa kowani part na jikinta .
,har wani lumshe shanyayun idanunta take sakamakon farinciki data tsinci kainta ciki.
ahankali nablah ta sauke idanunta fess. akan Zeenat dake tsaye kikam.. tana mazurai . take gaban nablah Yashiga faduwa da sauri a yatsine Zeenat ke watsawa nablah wani irin mugun kallon wanda ke hautsina kayan cikinta , ganin irin kallon rashin arzikin da Zeenat ke binta dashi ne . yasa nablah shan jinin jikinta.
tabe baki Zeenat tayi sannan tace Yar iskar baiwa… kawai abinda yakawo kennan , kin wani zo kin nemi waje a daki kin zauna kina tamkar boka dan tsabar munafurci , to kike so yayi miki sauran aiki da yayi saura uhm ?
Nablah tayi saurin girgiza kanta tare da cewa dan Allah aunty kiyi hakuri wlh na dauka ko mungama aikin ne.
Zeenat , ta sake watsamata wata uwar hararar hade da kallon banza.. wanda hakan ya suka sake frigita zuciyar nabla dake tsaye Amman ta dake batare da tabari Zeenat din ta gane yanayin data ciki ba .
“Nablah tayi zuru kawai tare da bin bayan Zeenat da wani irin kallon mamaki da alajabi abinda tayi mata.
dan ko kusa batayi tsammani zata fuskanci irin wannan babbar wulakancin ba mai cike da al,mara .
,’ahankali ta furzar da iska ta bakinta tana furta wlh da sake Dan zan iya daukar komai na kunci rayuwa Amman Banda zagar min iyaye .
,
, Mtssss taja tsaki itama tana harara kofar da Zeenat tabi .cikin sanyi jiki ta nufi kitchen .
Zeenat tace ,Yar iska yarinya kawai kina jin mutane suna kiranki Amman dan dakikanci irin naki kika yi shr..ko
nablah ta hadiye bacin ran dataji yana taso mata tun daga tsintsiyar kafafunta ,sannan tace kiyi hakuri basan dani kike ba” sbd ita kalmar ke.. din da kika ce bata daga cikinta sunan nablah….
cike da mamaki yarinyar Zeenat takarasa ta zauna ranta a abace wahake take fidda numfashi dan kwata kwata bata taba jin tsanar mai aikinta irin yadda take jin haushin nablah .
Gashin yarinyar kmr bata da wani alamun tsoro atare atare daita .
Cikin mintinan da basu wuce biyar ba ta sauke indomi ta yuye a plate sannan ta sake maida pot din abinci dare kan gas .
zaune ta sameta ta hankice a parlour sai faman cika take tana batsewa tare da hura hanci ‘tana kada kafa daya ..
ko meyasa ita takasance irin haka ba kmr ummi ba ,mai matsananin son mutane da kyautata musu” km tana lura da irin yadda ummi din ke matukar bawa duk wasu mutane dake shigowa cikin gidan, kulawa ta musamman ” sabanin ita wannan bazanr matar mai kama da mutane China .
, ‘Ahankali nablah tacigaba da aikinta na zagin Zeenat din aranta sai data gyara koina tsab .
sannan taje tambaye Zeenat din ko akwai wani sauran aikin da zatayi Dan gujewa cin mutuncinta .
,a yatsine Zeenat din ta dago fuskarta tamkar hadari sannan tayi mata nuni da hannuta alamun zata iya wucewa kawai .
jikinta a mace tabar gurin , da kyar ta dinga daga kafafuwanta tsabar gajiya datayi , yayinda idanunta suka ciciko da Hawayen batayi kokarin hana hawayen idanunta zubowa ba,sbd tashin hankali take ciki da wutar dake ruruwa a zuciyarta tana tafe tana kukan zuci yayinda hawayen idanunta ke sake cigaba da bin fuskarta…
STORY CONTINUES BELOW
A tsorace tasa tafin hannunta duka ta rufe fuskarta dashi.. kijinta na sake daukar kirrrrrrma .
‘Ahankali ya ja wani irin mugun tsaki mtsssssss wanda hakan ya sake jefe zuciyar nabla shiga cikin rudani .
,Karfe shadaya daidai deeni Yashiga dakin Zeenat byn ya gama shirin bacci cikin wasu ratsasun kayan bacci.m masu matukar kyau.
batasan shigowarsa ba tana can duniyar tunani “ahankali DEENI yakaraso har inda take tare da ya kamo tafin hannuta cikin nasa Yana murzawa sannan ta juyo ‘ahankali tana sauke naunauyen ajiyar zuciya.
Tana tsaye a kitchen din yayinda hannuta ke kai kawon gogen kayan kitchen din Wanda ya zame mata dole kullun garin Allah Ya waye sai tayi.
laraba ce tashigo kitchen din tana yimata sannu tare da sanya hannu tasoma kokarin taimakawa nabla da wasu ayyukan .
Nablah Tayi murmushi dama kinbarshi aunty yanzu zan gama ai”
,Dan har gara hjy da mai gidan akanta ” Dan shi maigidan kwata kwata baya shiga harkar mutune yayinda ita hjy wani lokacin takan tausayawa mutun.
nablah Tayi shr kawai tana sauraronta batare da tace mata ba , komai Sai ma maida hankalinta datayi kan aikinta.
laraba ta sake cigaba kinsa Allah ko abinci kika dafa wannan matar , muddin baiyi mata ba wlh dole ki sake yin wani .
Nablah dake tsaye ‘tana aikinta , tace nifa Ina ganin kmr mdm din nan taki , kwarkwar ce…….
“Haba aiko laraba ta kwashe da wata muguwar dariya , kai gsky nablah baki da kirki wlh madam din ce kwarkwar tana mai sake kwashewa da dariya .
nablah ta bar abinda take ta juyo Sosai tana duban inda laraba take .
,kinji ba , ai abinda yasa kikaji nace miki , Ina mata kallon kwarkwar ,Dan some time sai inga kmr tana hararata byn ban mata komai ba inji cewar nablah.
Laraba ta numfasa sannan tace shiyasa lamarin zaman gidan Sai kin kara da hakuri. nabla ta sauke naunauyen ajiye zuciya sannan tace indai hakan kike fama da matar nan Na jinjina miki dan gsky kinyi kokari wlh.
, ai a Haka ma bakiga komai ba indai mdm ce inji cewar laraba , Dan naga kmr ke kina da wani matsayi a gidan” tunda har an barki kina ganin mai gidan ,gashi km har special room aka baki a sama.
kai kawo nablah ta dinga yi tsakanin upstairs da downstairs , kallo daya zakamata ka gane tsansar yadda ta fita haiyacinta tsabar gajiyar dake tattare daita dole ma kaji ta baka tausayi .
tsaye take kusa da zeenat ta takure jikinta waje daya , byn ta gama waken kayan da Zeenat din tayi amfani dasu ,banda harara da kallon banza bbu abinda take jiho mata .
,A zafafe Zeenat din ta kallo inda nablah ke tsaye kinzo kin wani tsayamin a kai kmr zaki tsotsemin jinin jiki ki dauki plastic ki kawai my hrt.. takarasa fadar Haka tana watsawa nablah wanimugun harara .
Nablah tasa ‘hannu kennan zata dauka sai ga laraba tashigo kitchen wasu kayan wando jeans da Riga Tayi gurin frij .
zeenat ta kallite ta kalli kayan jikin laraba sannan ta watsa mata wata uwar harara ,har nablah ta ji hantar cikinta sun cure gurin daya .
Nablah ta dago ta dubi aunty laraba jens ne a jikinta sai riga iya gwiwa .
Domin bata ganin laifi Zeenat sai nata domin ita takawo kanta da kanta cikin wannan maseefa.
Ta Dan tsaya kafin takarasa parlour mai gidan Tasa ‘hijab dinta tana goge hawayen daya yasoma bin kuncinta dan iri irin abinda zeenat takeyi musu yana taba mata zuciya sosai .
‘cikin sanyin jiki tasoma tafiya har ta iso parlour da mai gidan yake tare da bakinsa da sallamarta tashigo. muryata fal cike da tsoro da fargaba.
kallo daya DEENI yayi mata ya dauke idanunsa sai abokansa guda biyu ne suka amsa mata sallamar.
, ahankali cikin tafiyarta mai daukar hankalin ga duk wanda ya kalleta , ta karaso ciki sosai , ta tsugunna ta ajiye plastic din da cup’s .
, duk yadda nablah taso hadiya damuwar dake zuciyarta hakan yakasa samuwa , domin kuwa sabon Hawayen dake makale a idanunta ne suka samu nasarar zubowa .
, uhmmmm daman Sai Dana gaya ummi tabari a sallemiki Dan nasan bazaki iya tabukawa mutane komai Amman tace Sam…
Yanzu kukan iskanci me kikeyiwa mutane nablah ta girgirza kai tare da cewa bbu .
Zeenat ta tasoma kada kai cewa zama ayi komai din sannan ta Miko nablah wani karamin jug mai dauke suga tace ungo Ni ki kaiwa mijinta baiwar banza kawai.
,jikinta a sanyaye km badan ranta yaso ba ta sake koma parlour …
byn ta fito ne ma abokinsa manir yace DEENI ina kasamo wannan fine bby din mai tsabar kyau gaskiya tamin kyau sosai …..
Take DEENI ya hade rai tamkar Wanda yaji wani mugun abu .. meye matsalarka daita ?
Manir yace yarinyar ce tamun kyau kawai , a fusace deeni yace bakowa bace facce house girl dina.
A zafafe DEENI yace bafa nason iskanci nan naku idan abinda yakawoku kennan natashi nakama gabana .
, ‘Ahankali ya ture document din dake zube gabansa ,Coffeen da nablah tasoma siyaya a cup, din yasa ‘hannu ya dauka yasoma kurba ahankali ahankali tare da lumshe ritattun idanunshi .
Manir da fahad suka bishi da wani irin kallo ganin abinda yayi . yayinda manir ya cika da mamakin deeni .
Fahad yace mekake nufi yanzu da haka sai da hadeye wanda ke bakinshi sannan yace ga abinda nake nufi nan kuwa , kowa ya yakama gabansa.
Zuwa yayi ya canza kayan jikinsa zuwa kanan kaya sai kamshi mat Hamilton 27 yake zubawa part din ummi yashiga yana kiran sunanta .. first lov.. were are you .
jin shiru bata amsa bane yasashi kutsa kansa cikin bedroom dinta kai tsaye batare da yayi tunanin wani abu .
Ita kuwa dake zaune tana jerawa ummi kayanta da mai wakin yakawo dazu a Waldrop ta zabura ta Mike tsaye da sauri, duk ilaihi jikinta bbu inda Bai dauki rawa ba saboda tsabar tsoron muryar data jiyo.
shima tsaye cak yana Kare mata kallo tsab wanda in ba lura mutun yayi da kyau ba.
ahankali yakaraso dakin sosai yana sake kiran sunna ummi . kainta a sunkuye a kasa yayinda zuciyata ke wani irin bugawa da sauri cikin siririyar muryata mai cike da in inna … tace ta.. tana.. bathroom …
Numfashi ta sauke tana may sa dukka ‘hannuna ta dafe kirjinta dashi tare da sauke ajiye zuciya.
fitar shi bai fi da minti uku ba ummi tafito tanawa nablah sannu da aiki sannan tasamu waje ta zauna, tana dan Jan nabla da hira , itama dai ba laifi takan dan saki jikinta ummi dan tafi zeenat sau dubu har aka kira sallah suna tare da ummi dan dakin tadawo yanxun saboda aikin da za’a yi Wanda ya hada har da dakin nablah.
Mikewa tayi nablah Tayi tare cewa ummi Ina son naje nayi sallah .
murmushin ummi Tayi haba nablah yanzu sallah ma sai kin tambaya ,ummi girgiza kawai tare da cewa ,jeki kawai kiyi sallahrki kinji ..