WANNAN RAYUWAR CHAPTER 11
Cikin gida suka dawo Hafsa ta shiga daki wayar ta tagani tana haske tana dubawa taga Ahmad ne dauka tayi tai sallama yace
“Ina kika shiga ne ina ta kira!”+
“Wallahi na fita naje gun Halima ne!”
“Ohk ya jikin nata?”
“Da sauki!”
“Allah kara sauki!”
“Amin”
“Daman zan fada miki gani nan karasowa! Zan zo naga my princess naga ita me takara sannan in amshi amsa ta.”
Murmushi tayi yace
“Toh Allah kawo ka lafiya.”
Yace
“Amin nagode! Kin shirya kenan”
“A’ah!”
“In nazo ma kya shirya ai.”
“Sai ka karaso.”
Ta fada yace
“Ok!”
Mai fruit ya sama ya siyawa Halima da yawan gaske sanna ya tada mota ya nufi gidan su Hafsa yana mai jin wani farinciki da dadi na ratsa dukkan jikinsa da zuciyar sa.
Yana kashe wayar ta mike ta canja kaya sannan ta zauna kirjin ta na dukan uku uku tunanin ta tayaya zata amshi soyayyar sa in taki kuma menene dalilin ta.
Tana zaune wayar tabta hau kara dauka tayi ta duba taga Ahmad ne dauka tayi yace
“Ina kofar gida!”
“Ok!”
Ta mike ta saka hijab sannan ta shafa turare ta fito. Umma ta sama tace
“Umma nayi bako bari naje mu gaisa.”
“To a kiyaye dai.”
“Insha Allah!”
Sannan ta fita. Yara ta gani suna shigo da bugun dankali da goya sai kayan marmari.
Kanin ta Lukman yace
“Yaya ke akace mu kawowa!”
“Ni kuma inji wa?”
“Yana waje!”
“Ok!”
Ta fada tana basu hanya sannan ta shimfida masa darduma ita kuma tayi waje. Tsaye ta ganshi jikin motar sa ya zubowa kofar gidan ido yana hango ta ya saki murmushi sannan ya fara takun sa mai kyau da nutsuwa yayo kofar gidan.
Sam bata san ya karaso ba, sai ganin sa tayi a gaban ta ba karamin kunya taji ba ta juya tayi ciki yabi bayan ta. Zama tayi a can karshen dardumar sannan shima ya cire takalmin sa ya zauna.
Kanta a kasa tace
“Ina yini?”
“Alhamdulillah ya kike?”
“Alhamdulillah!”
“Ya me jikin?”
“Da sauki!”
“Allah kara afuwa!”
“Amin!”
“Uhmm ina jin ki?”
Dagowa tayi ta dan kalle shi sai karaf suka hada ido. Kai ta dauke da sauri yai murmushi yace
“Ashe ke barauniya ce.”
Da sauri tana kallon sa. Yce
“You stole me heart!”
Waya ajiyar zuciya ta saki yace
“Haka ake kin dauke tawa amman kin ki bani taki biyu ta miki yawa ki taumaka ki ban taki zan kula miki da ita fiye da yadda zan kula da tawa.”
Bata san lokacin data sake wani murmushi ba tare da lumshe ido. Shima murnushin yake Yace
“Hafsa na fada miki ban taba soyayya ba kece the first girl dana taba cewa ina so kuma kece macen da na taba zama da fadawa ina so har nake bin ki kina gudu na. what I know is that your love makes love change me har nake abubuwa ba tare da na sani ba. Wanu lokacin cin naji sam in ban ganki ba kanar zan mutu ne. Hafsa i love you amson da ban san dashi ba da ban yadda da wani abu so kamar haka ba saib yanzu a yanzu ina jin I can do anything just to have you.”
STORY CONTINUES BELOW
Hafsa jin maganan Ahmad take har cikin ranta da duka gangan jikinta, takan rasa mai yasa take jin sonsa da kaunar sa a ko da yaushe tana ganin sa daban a cikin mutane domin tana ganin shi yafi sauran samarinta, ita dai tasan zuciyar ta ta riga ta kamu da sonshi ne, amma shine kadai yake magana da ita taji bata son ya Bari sannan takan sami nutsuwa Idan suna waya, takan rasa mai yasa ko wace kalma Indai ya fito daka bakinshi take jin dadinta ba, ta rasa dalilin hakan ga wani irin kwarjini da yake mata Sosai. Ba zata iya kin Ahmad ba domin yayi in ya tafi waye zai zo mata bata sani amman kuma in suka aure ya same ta ba a yadda yai tsammani bafa?…….
Katse mata tunani yayi da fad’in
“My love ya ake ciki da maganar mu?”
Gabanta taji ya fadi ta yi kasa da kanta. Yace
“Bakya sona kenan!”
Kai ta girgiza yace
“Uhmm say it out mana.”
“Ni ban san me zance ba!”
“Iyee Lalla ashe dai Ahmad bai da sa’a da farin jini ace the first girll da ya taba gani yace yana so taki amsar sa. Allah sarki Ahmad ba tausaya maka yanzu shkn mutuwa zai yi.”
Tinda ya fara magabar ta dago tana satar kallon sa tana murmushi dan dariya ya bata sosai. Yace
“Oh dariya ma kike min ko?”
“To ai ni bance bana son ka ba.”
“Uhmm me kika ce to?”
Shiru tayi ya matso kusa da ita yana kallon ta kanta a kasa yace
“Hafsa aure fa zamuyi dole kunyar nan ki ajiye ta yanzu just kice kina sona shine baxa ki iya ba.”
Sai ya koma ya zauna ya shagwabe fuska ya daga hannu ya kai wajen fuskar sayace
“Ni Allah kice kina sona!”
Dagowa tayi ta bishi da kallo ya hau buga kafa yace
“Uhmm uhmm ni ki fada.”
Dariya ta fashe da ita sai ya saki kamar karya yana fadin
“Au dariya ma kike min.”
“No no please sorry nifa ba dariya bake ba.”
“Me kike in ba dariya ba ni ki fada min.”
Tace
“To is ok naji ina son ka.”
Da sauri ya dago yana kallon ta yace
“Da gaske?”
Kai ta gyada sai kuma ta rufe fuskar ta. Ya saki murmushin sa mai kyau yace
“Alhamdulillah yanzu zan iya turowa kenan!”
“Not nowa Deedat!”
“Why?”
“Dududu yaushe kayi aure!”
“Shine me? Ni dai gaskiya ina so kwanan nan.”
“Gaskiya ka dada lokaci ya kamata ko shekara ne kuyi!”.
” shekara Hafsa wallahi ba zan iya shekara babu ke ba ke ko five month ba zan iya ba. Zan baki nan da wata daya zan turo gida ayi maganar auren mu.”
“Deedat!”
“Menene matsalar ?”
“Gashi nan na dada maka!”
“Wannan ba matsalar ki bace ai.”
“Amman ai….”
“A bar maganar nidai ga yadda nace nan in kina sona ki accepting a haka.”
“To Allah yasa haka ya zama.mafi alheri.”
“Amin Baby na amarya ta.”
Shiru tayi yaxe
“Sai mu fara shiri ko?”
“Shirin me?”
“Bikin mu.”
“Kai Deedat da saura ka bari mana.”
“Na bari shikenan!”
Ta gyada masa kan ta.
Haka yai ta janta da hira har ta sake dashi. Da zai tafi aka kira Halima yai mata sanni ya bata 20k da kyar ta amsa sannan sukai sallama da Hafsa yace gobe zai dawo.
*
Yaba shiga gidan su bangaren mahaifin ya ya nufa. A falo ya same shi yana waya zama Yayi yana jira ya gama bayan ya kashe wayan ya kalli Ahmad uace
“Yaushe ka shigo garin baka fada min ba.”
“Dazu Dady nazo ganin amarya tane!”
“Waxce fa?”
Fuaka ya bat kkamar zai kuka yace
“Wacce na fada maka mana Dady!”
“Oh na tuno ta. Wajen ta kazo kenan ka baro Hanna a can.”
“Dad na kasa zama.ne acan ita kawai bake son gani.”
“To yanzu ka ganta?”
“Yes Dad!”
“Sai ka koma gobe.”
“Sai monday Dad ya za ayi ina son a fara shirin bikin mu.”
“Amman Ahmad yaushe akai bikin ka ni nai maka alkawari zan maka auren wacce kake so amman ba yanzu ba sai ka kara zama da matar ka ka fuskance ta itama haka.”
“Har zuwa yaushe Dady!”
“Kuyi shekara.”
“Dady wallahi ba zan.iya shekara ba Hasa ba dan Allah ka taimaka min.”
“Shikenan nan da wata uku yayi!”
“Uhm wata uku Dady…”
“Eh! Bana son na dauko maganar Mum din ka ta ga lokacin yayi kusa.”
“Eh kuma fa haka ne.”
“Yauwah ka bari a yadda nace din amman ka cigaba da neman ta Allah tabbatar da alheri.”
Hugging Dadyn dinshi yayi tare da fad’in
“Godiya nake Allah kara gurma da nisan kwana. Allah jikan mahaifa.”
Dady ya amsa da
“Amin amin!”
Sannan ya mike zai fita Momy ta shigo.
“Damab yanzu ake ce min ka zo nace me.kazo ina ita Hannah”
“Tana Abuja.”
“Amman ka baro ta.”
“Haba Momy dan zan dan zo shine sai na tabo da ita. Yaushe dudud muka tafi.”
“Shiyasa nake mamakin zuwan naka ai.”
“Wani aiki nazo yi na kwana biyu.”
“Oh Allah bada sa’a “
“Amin Mony nah.”
Ya mike yace
“Bari naje na kwanta sai da safe.”
“Allah bamu alheru. Kaci abinci.”
“Na koshi.”
A ransa kusa fadi yake wane abinci zanci naga rabin raina
*
**
***
****
*****
******
*******
Yana tashi da safe ya hau hada jakar sa. Ya shiga yai wanka ya dauko jakar tasa ya fito falo ya ajiye. A dining ya samu Hajiyar da Dad din sa. Ya karasa ya gaishe da Dad ya amsa yana fadin
“Ya jikin Son!”
“Naji sauki dad!”
“Allah kara sauki.”
“Amin!”
Ya kalli Hajuyar yace
“Ina kwana Momy”
A share ta amsa ya zauna ya sha tea da bread kawai ya mike Dad yace
“Ba dai har ka fito ba?”
“Yes Dad gwara naje da wuri.”
“Shikenan zan turo maka da kudi ka kiyaye Mu’azam Allah ya tsare hanya.”
“Amin Dad!”
Ya kalli Hajiyar sa ta dauke kai yace
“Mom your prayer please!”
“Allah sauke ka lafiya.”
“Amin!”.
Ya fita driver yasa ya kaishi airport yana zuwa ya yanki ticket sannan ya zauna dan sai nan da awa byu jirgin zai. Duj ya matso dan ganin awa biyu yake kamar sati Biyu.
A haka da kyar yaga lokaci yayi suka tashi shi kansa gani yaui kanar jirgin baya tafiya. A haka dai suka sauka lafiya. Taxi ya samu ta dauke shi su suka isa hotel. Ya kama daki ya shiga yai wanka.ya dan ci abinci sannan ya shirya ya fito.
Wayar da ta tubuta a address ya dauko ga unguwa nan da layi amman ba number gida. Haka ya fita ya fadawa ma napep inda zashi ba bata lokaci suka isa imdai dai inda ta fada. Tsayawa yayi a titin yana tunanin ta ina zai fara dan dogon layi nr.
Yana tsaye wani yazo wucewa yace
” Assalam alikun bawan Allah.”
“Wa’alaikum salam”
“Dan Allah tambya nakr!”..
” Allah yasa na sani “
“Gidan su wata Sakina.”
“Ayyah wallahi ba a unguwar nake ba.,”
“Ok nagode!”
Wani yazo ya kara tambaya amman bai santa ba wani gub mai shago yaje ya tambaya yace
“Sakina anan unguwar gaskiya ban san ta ba gudan wa tace maka?”
“Bata fada min ha gaskiya.”
“To gaskiya ba nan unguwar bane kla wrong address ta baka.”
Ya tambayi fin mutum uku ba wanda ya sani tin yamma yake abu har magariba yai sallah ya koma hotel din da ya sauka jiki a sanyaye.
Sunyi wasa da Dady ya boye mada yace sun hadu tana gaishe shi amman sam.bai ganta ba dan kada ya tada masa da hankali ne.
*
A haka sai da yai kwana uku yana zuwa unguwar amman ba wanda yasan wata sakina domin yan gidn ba fita suka fiya ba bama Sakina da bata zama a garin. Gajiya yayi da hawa Napep kawia ya siyi nota.
*Dan Allah ku sani a addu’a akan Allah ya yayen abinda ke damuna ya biya min bukatu na na alheri.*
Abbah yace
“Ya zancen kafi Muhammad nace za aje a yi a gidan da na baka kace a dakata.”+
Kai yayi kasa dashi yace
“Haka ne Abba daman ina can nake aiko da kudi ana min gini anan to shine yanzu ma daga can nake an gama komai a jiya shiyasa nace a dakata. Kuma Abbah ina neman wata alfarma dan Allah.”
“To masha Allah hakan ma yana da kyau ai. Allah sanya alheri.”
“Amin!”
“To wacce alfarma kenan?”
“Abba daman so nake a bani dama na zuba kayan cikin gidan ba sai anje wani kafi ba ni zanyi.”
“A’ah A’ah Muhammad haka ma ya isa, kaya an riga an siyo dan haka kayi hakuri kawai Allah yayi albarka.”
“Amin to Abba na gode yaushe zan kai ka, ka gano gidan?”
“Sai wani lokacin Muhammad!”
Hannu ya zura a aljihu ya ajiye keys din yace
“To ga makullin gidan nan sai a fadi lokacin da za aje kafin zan aiko motoci.”
“Haba Muhammad ai wahalar sai taimaka yawa.”
“Dan Allah Abba kada kace A’ah ka bari kawai azo a akai su.”
“To shikenan Allah ya kaimu gobe ne da safe tinda kaga a gobe zata tare kamar karfe tara sai su tafi ayo kafin.”
“To Allah kaimu.”
“Amin! Su Umma na ciki zan shiga na gaishe su.”
“Suna nan muje na rakaka.”
Suka mike Abba na gaba Muhammad na bin sa a baya har falon Umma dake zaune suna ta lissafi. Tana ganin sa ta mike tana fadin
“Ah Muhammad an dawo ashe.”
Ya durkusa yace
“Eh Umma ina yini mun sameku lafiya?”
“Alhamdulullah!”
“Masha Allah! Yasu Hajiyar taka?
” Tana lafiya. Tace agaishe ku”
“Masha Allah muna amsawa.”
Sannan yace
“To sai anjima.”
“To ka gaishe ta da yaran!”
“Zasuji nagode!”
Suka nufi dakin Mama dake zaune tana waya. suna shiga ta dinga binsu da kallo dan ita ta kasa gane Muhammad ma. Sai da ya gaishe ta sannan Abba yace
“Muhammad ne mijin Ummu fa.”
Fuska ta bata tace
“Oh ashe ya dawo!”
“Ya dawo dazu!”
“To madallah!”
Ya mike yace
“To sai anjima.”
“Mujima da yawa!”
Suka fito. Ya dan rissina yace
“To Abba ni zan koma.”
“To Muhammad ka gaishe da Babar taka.”
“Zata ji.”
Har ya juya Abbah yace
“Zo!”
Ya dawo yace
“Baka ga Ummu ba ko?”
Yai kasa da kansa ya kasa magana. Abbah yai murmushi yace
“Tana gidan Zainab nasan gobe zata dawo nima tinda ta dawo sau daya na ganta Zainab ta kwance min ‘ya.”
Muhammad yace
“Ba komai Abbah nagode.”
“To ka gaisa gida!”
“Insha Allah.”
Ya fice. Gidan Anty Zainab ya wuce kai tsaye bayan yai parking yaran suka taho suna ganin sa suka hau fadin
“Oyoyo Uncle!”
STORY CONTINUES BELOW
Ya dauki karami yana fadin
“Ya kuke?”
Baban yace
“ina yini Uncle!”
“Lafiya ya kake?”
Mai binsa ma ya gaishe shi. Karamin dake hannun sa shima yana gwaranci ya gaishe shi ya amsa yana murmushi. Sannan ya kalli Baban yace
“Kaje kacewa Umman ka Uncle yazo.”
Nan yai ciki da gudu. Bai jima ba ya dawo yace.
“Momy tace ka shigo.”
Shiga sukai tare ya basu sweet duk sukai godiya sannan suka koma can compound suna wasan su. Gaisawa sukai da Anty Zainab tana fadin
“Ya Hanya?”
“Alhamdulillah Anty ya gida?”
“Alhamdulillah.”
Sanna ta mike dan ta kawo masa ruwa da lemo. Tana mikewa ya dauki wayar sa ya fara neman layin Ummu!
*
Ummu kuwa tana can wajen gyaran kai da lalle dan tin safe wajen goma ta fita sai daya aka gama mata jan lalle sai da tayi sallah tasha maltina karfe biyu aka farai mata baki yadda ake zanawa kamar dashi aka hallice ta domin yai kyau ya hau kan kafa da hannun nata. Sai uku aka gama ta zauna dan ya bushe. Karfe hudu aka kankare sannan tayi sallah aka hau gyara mata kanta.
*
Tana cikin dryer taji wayar ta dake cinya tavfara vibrating dauka tayi taga Muhammad ne. Murmushi tayi ta dannan received sannan ta fito da kan ta dan answering call din.
“Amarya ta tana ina? Nazo gida ina ta zuba ido ban ganki ba.”
“Haba dai ka sauka kenan!”
“Na sauka Ummu tin dazu na kira ki baki dauka ba ai.”
“Ayyah wallahi ban gani ba wayar na jaka. Ka dawo lafiya ya hanya da gajiya.”
“Ban amsawa ta waya ki fito ina falon Anty Zainab kimin barka da zuwan.”
Tai murmushi tace
“Nifa bana gida!”
“Kina ina to?”
“Ina wajen gyaran kai fa.”
“A ina ne?”
Dai dai fitowar Anty Zainab. Tace
“Zoo road!”
“Ok gani nan.”
Ya mike. Anty Zainab tace
“Ina zaka kuma na kawo maka lemo da ruwa.”
“Anty Zanje wajen Ummu ne yanzu zamu dawo.”
“Ok! Sai kun dawo.”
Ya fice da sauri. Yana zuwa inda take yai mata waya yace
“An gama ne?”
Ta ce
“A’ah ana dai yi.”
“Ok!”
Ya fada ya fito daga mota. Babban waje ne dan haka ya shiga ya tambaya wajen manager can yaje ya fada masa yana son yaga matar sa ana gyara mata kai. Sunan ta ya fada nan ya sa aka duba room nawa take sannan yasa ai masa jagorancu.
Lokacin da suka shiga har an fito da ita daga dryer ana gyara mata kai. Ta runtsa ido saboda yadda taje jin zafin ana ja mata kai. Sam bata san ya shigo ba ta dai ji Mai gyara mata kan tace
“Welcome Sir!”
Bata ji mai ya yada ba dan hannu kadai ya daga ma matar. Sai da ta gama gyara mata sannan tace
“An gama Hajiya!”
Ido ta bude ta kalli kan ta da sai sheki yake ya sauka har gadon bayan ta. sannan ta kalli matar ta sakar mata murmusji tana fadin
“Thank you!”
Ta mike tana kade jikin ta za ta tafi zata dauki hijab din ta kenan ta ganshi zaune ya zuba mata ido. Da mamaki ta bude ido tana nuna shi. Mikewa yayi ya bude mata hannu a hankali ta karasa wajen sa tana zuwa ya rumgume ta yana fadin
“Uhmm Alhamdulillah finally am with my wife!”
Kokarin janye jikin ta take dan tasan basu kadai bane a dakin dame gyaran kai amman ya ki barin ta. Sai ajiyar zuciya da yake ta saukewa sai da ya nutsu sannan ya dawo yana kallon ta yace
“Sweetheart haka kika koma kinganki kuwa?”
Kunya ya bata tai saurin juya nasa baya. Ya juyo da ita yana shafa gashin kanta yace
“Kai amman gyaran nan yai kyau Sweetheart!”
Ya kamo hannu ta yana kallon zannen bakin lallan yace
“Tubarkallah masha Allah.”
STORY CONTINUES BELOW
Ya juyo tafin hannun nata da ya sha jan lalle bai san lokacin da ya sumbaci hannun ba dan Muhammad yana son lalle sosai. Duk wani iri take ji ya jata jikin sa yana fadin
“Da me lallen nan dame gyaran kan na sai na kara musu kudi kuma su zasu cigaba da miki domin yai min kyau sosai Ummu!”
“Kai Yaa Muhammad ai na biya su.”
“Wannan reward ne from ur husband saboda yadda yai kyau.”
“Uhmm ya kake ya hanya? Kai ko hutawa bakai ba kake yawo ko?”
“Zuwa ganin Gimbiyar tawa ne yawo.”
Murmushi tayi yace
“Kinsan da na ganki duk gajiya da abinda nake ji sun gudu!”
“Uhmm!”
“Kinyi kyau Ummu!”
Ya latsa jikin ta ya lumshe ido dan yadda yaji taushin jikin ta zama yayi ya daura ta akan cinyar sa ta fara mutsu mustun tashi yace
“A’ah Ummu mijin kine fa.”
Daina motsin tayi tai kasa da kanta kawai. Hannu yasa ya dago kanta yana kallon idon ta da sauri tai kasa da idon nata yai murmushi yace
“Haba Amarya ta ki barni naga kwayar idon naki mana.”
Mikewa tayi da sauri tace
“Dan Allah tashi mu tafi.”
Kallon ta ya tsaya yi tin daga sama har kasa. Doguwar riga ce a jikin ta mai A Shape ta kamata daga dama ta baje daga kugunta. Ganin kallon da yake mata yasa tai saurin janyo Hijab din ta tana kokarin sawa ya amshe.
“Dan ina kallon ki shine zaki rufe jikin ki Ummu mijin kine fa ni.”
Kai tayi kasa dashi, ya matso yana rumgune ta ya saka kan sa a kaffadar ta yana shinshinar wuyan ta dake fitar da wani kamshi na daban dagowa yayi ya kissing forehead nata sannan yayi mata a kumatun ta, ido ta runtse yai wa idon ta sannan yai wa dogon hancin ta batai aune ba sai jin bakin sa tayi a cikin nata.
*
**
***
****
*****
******
*******
Zaman Fauziyya da Muhammad zaman lafiya suka tana faranta Masa Shima haka sai dai har yanzu ba wani Abu da ya shiga tsakanin su domin Fauziyya tana tsoro da kunyar in haka ta faru kada Muhammad ya juya Mata baya. Wannan yasa Shima ya share a haka suke Shan soyayyar su Yana kulawa da ita sosai baya son yaga bacin ranta ko Kadan.
Zaune suke a falo tana gaban flask shi kuma Yana zaune yace
“Baby jibi tafiyar mu ya kamata muje gida ki fadawa Hafsa Dan tare zamu tafi!”
Dagowa tayi da zuba Masa abinci tayi tana fadin
“Oh da gaske?”
Kai ya gyada Mata, tace
“Amman naji Dadi sosai. Kenan gobe zamu gida?”
“Haka ne Amman me za a kaiwa su Baba?”
“No Ummah dai Baba me zai bukatar?”
Ta fada duk Dan kada yai Mata fada.
Yace
“Duk da haka. Ga kudin da nake Tarawa Dan in zamu gida dubu dari ne Sai muje a siya musu kayan abinci da wasu abun ko?”
“A’ah Kaga Ina da kudi ayi amfani dasu kawai. Naka ka ajiye Kai da zamuyi tafiya Kuma zaka cikin Yan uwa Suma zasu so Kai musu dawainiyya ka ajiye na gunka na guna Sai ayi abinda za ayi dasu yayi?”
“Baby!”
Ya fada Yana kamo hannun ta. Dagowa tayi tana kallon sa. Yace
“Meyasa kike son kina hanani kyautata Miki!”
“Ba haka bane baka dashi ne tinda Ina dashi sai mu rufawa juna asiri naka ka ajiye can ai amfani dasu nawa ayi Anan in sun yi saura sai mu hada mu tafi dasu haka yayi?”
“Allah Miki albarka.”
“Amin!”
“Amman da nawa za ayi kiyi shiru kawai.”
“Angode Allah Kara budi ya saka da alheri.”
“Amin Baby na. Addu’ar budin kawai Zaki min Amman ban son godiya.”
Tai murmushi ta dauki spoon tace
“Ni zanyi feeding naka yau sai cikin ka ya fashe Zan barka.”
“In mutu kenan!”
Fuska ta Bata tace
“Please ka daina fada ka mutu in ka mutu Ina zani?”
Hannun ta ya kamo yace
“Shikenan kada kiyi kuka ba yanzu Zan mutu ba sai min haifawa Ummi Ya’ya guda ashirin!”
Ido ta zaro tana fadin
“What? Asihirin? Da Mata nawa?”
“Ke kadai!”
Kai ta hau girgizawa tace
“Ba zan iya ba so kake na zama tsoho kawai.”
“No ai Zan Taya ki ki haifi goma na haifi goma.”
Kai ta make tace
“Naki wayon wannan kawai salon wayo ne.”
Janyo ta yayi yace
“Da gaske kinga sai kina haifa man biyu biyu uku uku baifi sau biyar zuwa bakwai kin gama ba.”
Dariya tai tace
“Eh lallai sannu!”
“Da gaske?”
“Ni am not twins bare na haifa!”
“Kar ki damu Ummi na Twins ne kinga zamu iya samu Ina da kanne Mata twins too Kinga kila dai mu samu.”
“Kasan kuwa I like twins!”
“Sai kin gaji da haihuwar su.”
Hancin shi taja tace
“I will not indai jinin ka ne!”
Rumgume ta yayi tace
“Kaga muci abinci in ba haka ba zai sanyi na Sanka.”
Yai Dariya yace
“Kin samu dai.”
“Ni ba ruwa ba.”
Murmushi kawai yayi. Haka suka dinga cin abincin tana bashi a Baki Yana Bata a Baki har suka koshi Nan suka zube suna zuba soyayyar su.
Sai goma suka tashi suka cire Kaya wanka suka shiga sukai a can ma Sai da suka gama soyayyar tasu suka koma daki abinsu. Suka shafa Mai suka saka kayan Bacci suka shige bargo. Kanta ya haye ta fara kuka tana fadin
“Wannan kayi nauyi yanzu fa gaskiya dagani nice zan hau kan na.”
Sauka yayi ta haye kan da ta zagaye hannayen ta a jikin sa. Yai kissing goshin ta tace
“Bacci fa zamuyi not dis!”
“Ni wallahi am not satisfied!”
Ido ta zaro tace
“Kana so ka gama tsotse ni!”
“To ki bani the other things please.”
Take yanayin ta ya sauya nan ya hau lallashi.
Ai sai ta saka Masa kuka. Yace
“Haba Baby menene na kukan to?”
“Ina cutar da Kai Dan Allah kayi hakuri Kar kayi fushi Dani mala’iku su tsinre min!”
“Haba Baby ba haka bane kiyi hakuri Dan Allah ba zan sake ba I love you kinji.”
Da kyar tayi shiru ya lallabata tayi Bacci.
Mikewa yayi ya dauro Alwala ya dawo ya tada sallah. Har karfe biyu Yana kan sallaya.
*
Firgigit ta tashi tana kallon dakin da take tana kallon Muhammad ta sauko ta fada jikin.
“Lafiya?”
Ya fada Yana shafa bayan ta.
Kai ta hau girgizawa tana fadin
“Akwai abinda yake faruwa a gida!”
Ta mike ta dauki waya zata Kira number wayar Hafsat. Wayar ya amsa Yana fadin
“Da Daren nan Baby me ya faru?”
“Ni dai ka bani na Kira naji ya suke?”
“A’ah! Fada min!”
*Alhamdulillah. Nagodewa Allah nagode da addu’o’in ku. Alhamdulillah jiki yayi sauki ina mai godiya Allah ya saka ya bar zumunci. Hakika naga kauna sosai. Wanda suka kira da wanda sukai min text ta waya da whatsapp, groups duk na gani kuma nagode. Allah saka da alheri naji sauki kuma ina dai mai kara barar addu’ar ku.*”Ni dai nayi mafarki da Yan gida Kuma abun ba Dadi!”
Tana fada ta fashe da kuka.
“Ya Isa haka?”
Ya rumgume ta Yana shafa bayan ta a hankali kukan ta ya dinga tsayawa har tayi shiru gaba daya. Ya dauke ta suka hau saman gado ya kwantar da ita.
Mikewa tayi da sauri tana Fadi
“Dan Allah Muhammad kada ka barni Ina son ka Dan Allah kada ka juyan baya.”
“Ki daina fadar haka Baby. Insha Allahu mutuwa ce kadai zata raba mu Ina son ki ba Zan taba barin ki ba.”
Kai ta gyada tace
“Mu kwanta to.”
Kwanciyya yayi ta shige jikin sa. Ya tofa Mata addu’a. Take Bacci ya dauke ta.
Karfe 5:10am suka farka Dan sun Saba a tare suke tashi. Wanka sukai ya tafi masallaci ita Kuma tayi a daki. Tana idar wa tayi addu’a sannan ta tashi ta hau gyara gidan.
Ta gyarra daki ta share ta saka turaren wuta sannan ta share tsakar gida ta wanke bandaki. Kitchen ta shiga tai shara sannan ta fara wanke wanke ta gama ta daura tea.
Sannan ta shiga ta fara wanka tana fitowa ta zuba tea a flask sannan ta soya kwai ta shige daki.
Daki ta shiga ta shafa Mai tai kwalliya ta saka wani bakin less Mai adon ja dinkin riga da siket yai Mata kyau ta daura dauri.
Sam Bata ji bude kofar sa ba sai ji tayi an daga ta ta baya a tsorace ta juyo tana ganin shine ta fada jikin sa tana sakin ajiyar zuciya.
Yace
“Wai tsoron menene haka?”
Kai ta girgiza tace
“Ina ka shiga.”
“Yawo.”
“Katafi ka barni.”
“To ba gashi na dawo ba.”
“Ba ruwa a dakai.”
Ta tashi a jikin sata fita. Ruwa ta hada Masa ta dawo tace
“Na Kai maka ruwan wanka.”
Janyo ta yayi yace
“Ke Yar Nan da ni kike fushi to tuba nake naje maganar shagon Nan ne.”
“Amman kace yawo.”
“Tsokanar ki naje. Kinga Naga kosai na siyo Mana.”
Amsa tayi tace
“Kaje Kai wanka sai mu karya.”
Daki ya shiga ya cike kayan sannan yai wanka ya shirya yazo suka karya. Shi ya wanke cups din da plate sannan ya dawo daki. Tace
“Yaushe xamu tafi ne?”
“Ai ma Bari Sha biyu tayi ko?”
“Kai ai Rana tayi Nan da goma dai!”
“Sha daya dai Baby goma yai safiyya.”
“Shikenan Allah kaimu “
Tin goma ta dauki mayafi da jaka da takalmi Yana zaune Yana Tai Mata Dariya Basu fita ba sai Sha daya d arabi.
Wani supermarket suka shiga ya siya buhun shinkafa da tafiya Mai Maggi sabulun wanki da wanka sai biskit da alawa na yara. Sannan aka saka musu a napep suka fito suka dau hanyar gida.
Sha biyu da arbain da biyar suka Shiga unguwar ana tsayawa a kofar gida ya fito ai da gudu ta fito ta fada gida ya bita da kallo Yana girgiza Kai.
STORY CONTINUES BELOW
Yara ya sama ya suka shiga da kayan.
Tana shiga ta fara kwadawa Hafsa Kira. Hafsa na daki ta juyo kamar an Kiran ta tana fitowa taga Fauziyya da gudu ta Karasa ta rumgume ta Yana fadin
“Anty na oyoyo!”
Da kyar suka saki juna sai sukai dakin Ummah. Nan ta fada kan Umma tana Fadi
“Umma Ina yini?”
Ummah na kallon ta yadda Tai kyau tai fresh da gaske tace
“Masha Allah.”
Nan suka gaisa. Sakina ta fito tace
“Wow Anty kinyi kyau!”
Ta rumgume ta duk yaran gidan suka bai baye ta ana ta murnar zuwan ta.
Yara da suka fara shigo da Kaya ne ta Tina da Muhammad a wajen.
Umma tace
“Ba dai tare kuke ba?”
Kai ta gyada tace
“Kinji Fauziyya! Hafsa je ki shigo dashi ai Alhaji ma Yana Nan bai fita ba.”
Nan ta mike Dan fadawa Alhaji zuwan su. A falo ta same shi ya fito zai fita yace
“Alhaji Fauziyya da Mai gidan ne suka zo!”
“To ba dai wani Abu suke so ba ko?”
“Gaishe ka suka zo Yi kawai.”
Komawa yayi ya zauna, yace
“Turo su.”
“Tana fitowa Muhammad na shigowa. Tace
“Kuje ku gaishe da Baban fita zai Yi.”
Gaba Fauziyya tayi Muhammad yabi bayan ta. A kasa ta zauna shima ya zauna a kasa. Tace
“Ina yini Baba?”
“Lafiya ya gida?”
“Alhamdulillah!”
Yaa Muhammad yace
“Ina yini Baba?”
Yace
“Lafiya ya gida Yaa aiki?”
“Alhamdulillah!”
“Ba dai wata matsala ko?”
“Babu.”
“Haka ake so!”
Fauziyya ta mike tayi Waje Muhammad ya saka hannu a aljihu ya Mika Masa bndir din 1k
Baba yace
“Ah har da wahala.”
“Baba ba yawa Daman gobe zamu tafi gida na kawo ta tayi sallama.”
“Toh madallah. Allah saka ana hakuri da ita.”
“Ba komai nagode!”
Ya mike ya shiga dakin Umma akan sallaya ya zuna suka gaisa da Umma Nan ma ya dauki bandir din 500 ya ajiye Mata yace
“Gashi ba yawa. Gobe zamu tafi gida na kawo ta kuyi sallama.”
“To Muhammad angode Allah kra budi.”
“Amin!”
Ya mike yace
“Zan tafi.”
Yana fitowa Baba ya fito ganin an jibge kayan abinci yace
“Wannan ba dai Kai ka kawo ba.”
Kan Muhammad a kasa yace
“Baba ba yawa ayi manage!”
“Ai Mai yawan kenan angode fa Allah saka. Madallah Kai Alhamdulillah!”
Muhammad yace
“Zan tafi so anjima Zan zo mu tafi da ita.”
“To to ba matsala.”
Muhammad ya fita shinkafar ya duba yace
“Ikon Allah Yar gwamnati a marar Nan. Azo aje a canjo a kawo Yar hausa.”
Sakina da ta fito tace
“Akan me Baba Kai da ba da kudin ka aka siya ba ko Kai akace ya kawo wa. To Umma ya kawo wa ai yasan yadda gidan yake shiyasa!”
Kallon ta kawai yayi ya fice Dan da yaran ko kallon sa basa Yi Amman yau har ana maida Masa magana.
Daki tashiga tana fadin
“Kinji Umma Wai Baba aje a canjo shinkafa zuwa Yar hauaa.”
Hafsa tashi muje mu shigo da kayan Nan.”
Suka shigo dashi. Fauziya ta mike tayi dakin su.
Hafsa tabi bayan ta tace
“Anty ya gidan kuwa?”
“Alhamdulillah ya gida Nan jiya nayi mafarki me yake faruwa?”
“Anty abubuwan da yawa bakiga Anty Sakina ta dawo ba.”
“Na gani.”
“Uhmm ita ma da alama dai ta tuba.”
“Masha Allah.”
“Anty farisa ta dawo yau da safe ta koma ma Amman ita sai a hankali.”
“Muyi ta mata addu’a Allah ya shirya.”
“Amin!”
“Mamah har yanzu shiru ko?”
“Wallahi kuwa?”
“Anty fa!”
“Uhmm sai abinda yayi gaba.”
Kai ta girgiza tace
“Yaran fa ba matsala ko?”
“Kai Anty an samu matsala last week bana fada miki Halima ba lafiya ba Anty Ashe ciki me da ita!”
“Ci me?”
“Ciki!”
“Ikon Allah waye Mata cikin!”
“Wani saurayin ta.”
“Yanzu ya ake ciki?”
“Ai sai da ya bare muka sani. Baba ya Bata wani magani ta Sha yasa ta fara bleeding cikin dare muka tafi asibiti wani abokin saurayin shi ya taimaka Mana kwana mu biyu zuwa uku aka sallamo mu Tasha wahala Amman yanzu taji sauki.”
Tagumi Fauziyya ta zuba tace
“Oh mu Kuma tamu kalar kaddarar kenan. Shin laifin mune ko n iyayen mu?”
“Anty ke lafin Mama ne mu kuwa laifin mu ne. Kece kadai Baki shiga abun Nan ta dadin Rai ba Amman mu fa gashi Allah ya Baki miji na gari kina zaune lafiya abun ki nasan da wuya mu samu rayuwa irin Taki domin ke daban ce a cikin mu.”
Ta fashe da kuka.
Fauziyya tace
“Menene na kukan to Ai akwai Allah. Allah Yana gani zai turo kema me share Miki hawaye ina Ahmad?”
“Yana Nan dogon labari ne.”
“Kada ki damu dake zamu tafi ai.”
“Da gaske?”
Kai ta gyada ta rumgume ta tace
“Naji Dadi.”
“Kada ki damu zamuyi magana a tsanake!”
“To!”
“Kince Farisa tazo?”
“Tazo tana ta fada Wai kinyi aure!”
“To uwa ta zan a zaune jiran ta kada nayi aure ko?”
“Nima Wai kada na biye Miki kaza da kaza dai.”
“Ikon Allah Allah ka shiryi Farisa!”
“Amin!”
“Yanzu ki tashi ki hada kayan naki bari naje wajen Ummah naji me take da bukata sai naga Halima daga nan!”
“Toh!”
Ta mike ta fita. A falon Ummah ta zauna tace
“Umma dama da Hafsa zamu tafi can dagin shi.”
‘To Allah ya tsare Fauziyya ya gidan badai matsala ko?”
“Babu Ummah.”
“Masha Allah.”
“Ku nan ba wata matsala.”
“Hmm kema kinsa halin Baban ku dai. Sai dai hakuri amman yanzu kinga kudin da ya ban na juya kuma ga kayan abinci ko?”
“Haka ne. Allah ya ganar da Baba.”
“Amin!”
“Ba labarin Mamah har yanzu ko?”
“Babu wallahi Fauziyya nima na shiga damuwa rashin abokiyar zamana ina addu’a Allah yasa tana lafiya ya dawo da ita lafiya.”
“Amin!”
Sakina ce ta shigo tabi Fauziyya da kallo tace
“Sis wai ya akai Baba ya yadda da auren ki.”
“Hmmm nima ban sani ba kawai fa ce min yayi an dauran aure miji na zai zo ya dauke ni.”
“Ikon Allah. Allah ya kyauta!”
“Amin!”
“Nima Allah ya kawon miji Baba ya yadda.”
“Amin Sakina. Ai auren shine rufin asirin mu.”
“Haka ne.”
Halima ce ta shigo Fauziyya ta bita da kallo, kallo Halima tayi halima tai kasa kai tace
“Ina yini Anty Fauziyya?”
“Lafiya lou ya kike?”
“Alhamdulillah!”
“Kije dakin Mamah gani nan ina son ganin ki.”
Gaban Halima ne ya fadi ta amsa da
“Toh!”
Ta mike ta fita. Ta kalli Ummah tace
“Ummah dan Allah kina sa ido akan yaran nan!”
“Me kika gani Fauziyya?”
“Ba komai Ummah amman kinsan hakkin tarbiyar mu na hannun ku a baya kunyi wasa da damar ku wadan ya jefa da yawa a cikin mu a halaka alhamdulillah Allah ya dubi zuciyoyin mu ya shirya mu ya kamata ace na kasa damu sun samu nutsuwa da tarbiya kar subi tafarkin da muka bi.”
“Haka ne Fauziyya insha Allah za a kiyaye Allah yayi albarka.”
“Amin!”
Ta mike tace
“Bari naje wajen Haliman!”
Ta fita.
Karfe bakwai ya tashi yai wanka ya shirya cikin milk wando da cofee kalar riga ya feshe jikin sa da turare cofe kalar takalmi ya saka ya futo ya kulle dakin sa.+
Resturant ya wuce kai tsaye abinci yasa akai masa order dankali ne da kwai sai juice. Kafin yaci ya tashi ya fita. Motar sa ya shiga ya tafi unguwar su Sakina. Layi layi ya dinga bi yana tambaya wanda ba karamim wahala yasha ba duk da a mota yake kan rana ya gaji a wani masallaci yai sallah azahar yai la’asar sannan ya daura daga inda yake. A unguwar yai magariba sai da yaga dare yayi ya hakura ya koma inda ya fitowa.
Washe gari ma tin safe yake bulayi a unguwar amma sam ya kasa samun gidan har yamma. Yunwa da yaji yana ji yasa ya nufi wani resturant acan akai masa order aka kawo masa amman sam ya kasa cin wani abun kirki. Tashi yayi ya shiga masallaci yai sallah ya zauna yana addu’a tare da fadin
“Ya Allah ina roka ka in Sakina alheri ce a rayuwa tavAllah ka bayyana min ita in kuma.l ba alheri bace Allah ka ciren ita azuciyata.”
Yana gama addu’ar ya rufe fuskar sa da hannu yana jin hawaye na zuba a idon sa. Hakika yau ya shiga tsaka mai wuya bai san damuwa ko rashi a rayuwar sa ba sai yau lallai yanzu ya gane rayuwa da abinda ke cikin ta.
In kaga Khaleel duk ya damu ga rashin lafiya da take damun sa na yadda ya saka damuwa a ransa. Wanda ya sa duk ya kara ramewa sam yaki fadawa Dad din sa komai.
Muhammad da ya idar da sallah ya mike zai fita ya hange shi yana kuka da sauri ya karasa yana fadin
“Bawan Allah lafiya?”
Kai ya hau girgizawa yana fadin
“Ka taimaka ka nemon ita wallahi ita ce rayuwa ta.”
“Ya isa daina kukan ka nutsu wa kake nema?”
Hawayen sa ya goge ya fara bashi labari briefly. Kai ya gyada yace
“Ya sunan ta Sakina!”
“Sakina wa?”
“Wallahi ban sani ba!”
“Baka da number ta.”
“Gata amman bata shiga.”
“Ikon Allah kuma number dai dai ce?”
Kai ya gyada amsa yayi yai trying amman a kashe. Yace
“Kuma nan unguwar tace maka?”
Kai ya gyada. Yace
“Yanzu ina da ina ka tambaya?”
“kasan unguwar babba ce na tambayi a layi yafi goma ba respond.”
“Ai gaskiya matsalar da kace sunan yarinyar kawai ka sani dama sunanvmahaifin tane da yafi sauki afi ganewa.”
“Haka ne.”
“Yanzu tashi na taya ka mu gani ko can kasan layi za a dace.”
Tare suka fita ya dinga rakashi suna zagawa.
*
Zaune ta same ta ita da Hafsa dake hada kayan ta, zama tayi a gefen gado ta kalli Halima tace
“Hafsa ta fada min duk abinda ya faru ba dan komai ba sai dan nice babbar ku kuma tasan ina kawo mata mafita a matsalar ta dan kinsan ko Ummah da Sakina bata fadawa ba Halima me ya ja hankalin ki. Nasan dai Hafsa ta miki fada amman kiji tsoron Allah in ada kinyi a rashin sani to yanzu kikai ke da Allah ki wallahi wuta xaki shiga dan zina babbar masifa ce kuma kika yi sai Allah ya kamaki kuma ki jawa jinin ki tabo. Allah ya yafe mana baki daya.”
STORY CONTINUES BELOW
“Amin!”
Duk suka amsa tace
“Yanzu ya kukai da shi yaron?”
Kuka ta saki tace
“Sam ya daina kira na in na kira baya picking yanzu ma yayi blocking dina Anty Yaya zanyi ina son Isma’il!”
Murmushi Fauziyya tayi tace
“Kina zaton akwai sauran sonki a ran yaron.”
Ta girgiza kai tace
“Ai tinda kika bashi abinda yake so ba kuma wani abu da zaki bashi da zai burge shi kawai sorryn ki, ai kinyi wasa da damar ki tin tini Halima Isama’il ba zai aure ki ba.”
“Wallahi yana so na Anty!”
“Ok shikenan yana sonki ya isa kice masa ya turo.”
“Zan fada masa insha Allahu!”
“To Allah tabbatar da alheri amman ki nutsu kada ki kara gigin aikata abinda kika aikata a baya na baki nan da sati biyu zuwa uku kan dai mu dawo ina son naji me aka tsaya ki fada masa ya turo in ya tashi turowa in Baba bai yadda ba wajen Mubammad zai zo Allah yasa mu dace.”
“Amin!”
“Ki fada min in kuna bukatar abu kada kuna tambayar maza daga abinda yake sawa suke fara lalata rayuwar yan mata kenan.”
“Hmmm Anty wallahi ban taba tambayar sa kwandala ba. Kisan duk rashin mubbamu da kwadayi.”
“Haka ne. Sai kiyi ta addu’a Allah ya yafe miki ya kuma shirya ki.”
“Insha Allahu.”
“Tashi kije!”
“Nagode Anty!”
Ta mike ta fita. Hafsat ta kalla tace
“Ke nifa abin nan ya ban mamaki ita ta kasa gane inda yaron ya dosa.”
“Anty kenan sai ma kin ga abokin sa da yake son ta yaro nutsatse mai hankali da haiba. Wallahi yafi saurayin nata.”
“To Allah zaba mafi alheri ammab ni nasan da wuya yaron na ya auri Halima.”
“Amin. Nima na jimabda gane hakan.”
Wayar Hafsa ce tayi kara ta kai hannu ta dauka tana ganin Ahmad ne ta ajiye. Fauziyya tace
“Ki daukavmana.’
“Anty kyale….”
“Ki dauka kar na bata miki rai.”
Dauka tayi tai sallam ya amsa yana fadin
“Amarya ta.”
“Na’am ina yini?”
“Lafiya lou alhamduliah ya gida?”
“Alhamdulillah!”
“Gani nan zan shigo anjima dan gobe da safe zan tafi.”
“Ayyah nima fita zanyi.”
Wani kallo Fauziyya ta aika mata tace
“Amman yaushe zaka shivo?”
“Nan zuwa magarib!”
Kai Anty Fauziyya ta daga mata tace
“To sai kazo nagode!”
“Aha i love you Baby!”
“Nima!”
“No no no say it out.”
Shiru tayi yace
“Ina jin ki”
“In kazo zan fada maka.”
“Shikenan me zan kawo miki?”
“Ba komai.”
“To sai nazo”
Ya kashe wayar. Fauziyya ta harare ta tace
“Ki zauna kiyi asara yaro yana son ki.”
“Uhmm Anty nifa tsoro nake ji.”
“Ki kwantar da hankalin ki.”
“Shikenan!”
Tace
“Kin gama hadawa.”
“Nagama.”
*
**
***
****
*****
******
*******
********
“Dan ina kallon ki shine zaki tufe jikin ki Ummu mijin kine fa ni.”
Kai tayi kasa dashi, ya matso yana rumgume ta ya saka kan sa a kaffadar ta yana shinshinar wuyan ta dake fitar da wani kamshi na daban dagowa yayi ya kissing firehead nata sannan yayi mata a kumatun ta, ido ta runtse yai wa idon ta sannan yai wa dogon hancin ta batai aune ba sai jin bakin sa tayi a cikin nata.
Komai tsaya mata yayi dan nunfashin tamavdaukewa yayi na wucin gadi shina Muhammad wani abu yaji yana yawo a jikin sa ga kamshin jikin Ummu dake hargitsa masa tunanin sa ba soft lips dinta ga numfashin ta dake fitar wani kamshin mai dadi wanda yawan shan kanumfari ya saka hakq bakin ta kuwa kamshin strawberry saboda tana amfani da sweet nd cingum na flavour strawberry.
STORY CONTINUES BELOW
Sai da yayi iya yin sa sannan ya sake ta da kyar ai kuwa jikin ta da ya gama yin sanyi tayi baya da sauri ya kamo ta ta fada jikin sa ya rumgume ta. Ido suka lunshe a tare. Sunfi minti biyu a haka sannan ya dago ta ya saka mata hijab yace
“Muje ko?”
Kan ta a kasa ta gyada masa kawai. Hannun ta ya kama ya dauki jakar ta da wayar ta suka fita. wajen manager suka koma yace a nemo wanda wanda sukaiwa Ummu aiki nan da nan aka kirawosu ya basu kyautar 15-15k sannan ya bawa Manager 20k suka tafi suna ta godiya.
Gidan gaba ya bude mata ta shiga ya rufe zannan ya bude baya ya ajiye handbag dinta mota ya shiga ya tayar ya kamo hannun ta yana fad8n
“Ya shirye shiryen Walima Ummu na?”
“Uhmm Alhamdulillah!”
Ta fada muryar ta na rawa. Ya kalle tabyace
“Are you ok?”
Kai ta gyada ya kai hannun ta dake rike a hannun sa dai dai bakin sa yai kissing ido ta runtse da sauri dan yadda taji ya shige ta har tafin kafar ta taji wani abu ya tsigar jikin ta ta tashi.
Tuki yake a haka har suka karasa gidan Anty Zainab ya parking ya fito kan ta fito ya bude mata ya bude baya ya dauki jakar ta sannan sukai cikin gidan tana gaba yana binta a baya.
A parlour suka samu da Anty Zainab, Muhammadbya zauna yana fadin
“Mun dawo Anty!”
“Sannunvku an gama kenan!”
“An gama!”
“To maza kizo kici abinci ki kawo wa Muhammad ma.”
“Anty ni na koshi wallahi.”
Yaa Muhammad ya fada. Ummu da kanta ke kasa tace
“Nimana koshi.”
“Me kika ci?”
“Nasha lemo da ake acan fa.”
“Shine abinci tin safe kina can yanzun an kusa magariba. Ke fa haka kike bakya son cin abinci ko?”
“A’ah Anty ai na koshin ne shiyasa.”
“Kanki ai!”
Ta mike ta bar wajen. Ya kalli Ummu yace
“Zo nan!”
Karasowa tayi ta zauna yace
“Meyasa bakya son cin abinci?”
“Ina ci fa na koshi ne yanzu. Ita Anty ta fiso tai ta durawa mutum abinci.”
“So take kiyi kiba.”
“Ni bana so!”
Hancin ta yaja yace
“Fada min me kike so kici.”
“Nifa na koshi!”
“Ok!”
Ya mike yace
“Ana kiran sallah bari naje nai sallah zan dawo.”
Kai ta gyada tace
“To a dawo lafiya.”
ya mike ya fita ta koma ta zauna sai kuma ta mioe ta shiga daki.
Tana shiga ta fada kan gado tana mai lumshe ido tuna abin dazu yasa tsigar jikin ta gaba daya tashi davsauri ta mike ta cire kaya ta daura towel sannan ta shiga tai wanka ta fito daure da alwala doguwar riga ta saka ta tada sallah. Tana idarwa ta shafa mai da hoda sai ta kara kyau. Zama tayi tana kallon zanen lallen hannun ta yadda yayi kyau ya zanu lallai ta yadda da abinda Muhammad ya fada lallen yai nata kyau kuma ya amshi jikin ta. Shafawa tayi ta lumshe ido sai ta tuna lokacin da yayi wa hannun ta kiss da sauri ta bude ido take ta tuno yadda yai kissing nata wanda a time din ji tayi komai ya tsaya mata. Ido ta bude tana mai sakin murmushi fuskar sa take hanga kawai yadda ya kara kyau da haske. Murmushi tayi ta mike tayi sallah isha’i da taji ana yi tana idawa ta mike ta fito falo ta zauna tare da yaran Anty Zainab.
8:00pm wayar ta ta hau kara dubawa tayi taga Muhammad ne, dauka tayi ta kai kunne ta tare da yin sallama. Amsawa yayi yace
“Sweetheart fito muyi sallama in tafi.”
“To!”
Ta mike ta shiga dakin Anty Zainab ganin ta tayi tana hada kaya ta tsaya dagowa tayi bayan ta amsa sallamar ta tace
“Menene?”
“Yana waje ne wai zai tafi.”
“Ya dawo ne?”
“A’ah yanzu ya kirani wai zai tafi.”
“To kije kice ya shigo yaci abinci.”
“Toh!”
Ta juya ta fita. Yana jikin motar sa a tsaye ta karasa ta tsaya tare da yin sallama. Amsawa yayi ta tsaya tana wasa da hannun ta, kallon ta yake yana jin don ta kamar zai fasa zuciyar sa ya fito. Ji yayi ina ma ba za ayi walima ba da yanzu yana tare da matar sa. amman ba komai gobe by now ma suna tare insha Allahu.
“Zan tafi Ummu amman ji nake kamar kar na tafi na barki.”
“Anty ma tace ka shigo kaci abinci.”
“Anya Ummu na koshi fa.”
“Haba dai Yaa Muhammad dan Allah ka shigo kaci ko na kai maka can sittingroom?”
Tai maganar kamar zatai kuka. Duk sai ya rkkice yace
“A’ah muje to.”
Tare suka shiga tana gaba yana binta a baya. Suna shiga tayi dining ya zauna ta hau zuba masa abincin sai da ta gama ya kalle ta kalle shi tace
“Bismillah!”
“Ai tare zamuci.”
“Nifa na koshi.”
“Nima haka!”
“Haba dai please!”
“Kinga na koshi kema kin koshi to abinda za ayi kawai kici nima sai naci kowa sai yaci ko?”
Shiru tayi yace
“Tinda ba zakici ba nima haka tashi ki rakani in tafi.”
“A’ah zanci.”
“To fara ci”
Spoon ta dauka zata zuba ya ce
“Me wannan zakici ai.”
Ido ta zaro ya gyada kai yana danne dariyar da dan ba karamin dariya ta bashi ba. Kai ta langwabe………..