WANNAN RAYUWAR CHAPTER 14

 WANNAN RAYUWAR CHAPTER 14

Wani hadadden private hosipital suka je. Suna zuwa yai parking sannan ya fita ya zaga ya bude mata mota. Fitowa tayi ya kama hannun ta. Ta kalle shi tace

“Nifa Baby lafiya ta kalou.”+

“K shige muje ko na dauke ke.”

Gaba tayi ya mara mata baya. Cikin reception suka shiga suka nufi wajen yankar musu kati sannan aka kai su dakin da zasuga likita.

Zama sukai sannan Muhammad ya gaisa da Doctor. Sannan yace

“Waye ba lafiya?”

Da sauri Fauziyya ta nuna sa shima ya nunata. Dariya Doctor yayi yace

“Ikon Allah dukkan kune ba lafiya kenan.”

“A’ah ni lafiya ta kalou.”

Fauziyya ta fada. Muhammad yai murmushi yace

“Kagan ta nan kwana biyu bata jin dadi duk na rasa kan ta. Bata cin abinci amai ma ta gama yanzu da na matsa!”

Kallon ta Doctor yai yana murmushi yace

“To Madam ya kike ji?”

“Nifa ba abinda nake ji. Shine kawai dan ayi min allura.”

“Ba zan miki allura ba. Fada min kinji?”

“Nifa da safe ne nake zazzabi. Kuma sai naji zuciya ta tana yashi jikina ba kwari.”

Rubutu yayi a paper ya dauki waya ya fara neman layin nurse tana dauka yace tazo.

Ba ai minti daya ba ta shigo. Paper ya bata sannan yace

“Kuje ai mata test!”

Kallon Muhammad,  Fauziyya tayi yace

“Ni bana son allura Yaya!”

“Ba allura za ai miki ba. Fitsarin ki zaki bayar.”

Ta kalli Yaa Muhammad. Yace

“Muje!”

Suka fita. Suna zuwa aka amshi fitsarin sannan suka zauna minti goma Nurse din ta fito da papper tace

“Muje!”

Tare suka karasa office din doctor. Suka zauna ita kuma ta bashi result din ta juya ta fita. Budewa yayi yana kallon paper sai ya saki murmushu yana fadin

“Congratulation. Matar ka tana dauke da cikin wata daya.”

Ido Muhammad ya zaro yace

“Da gaske?”

Kai ya gyada masa. Kallon Fauziyya yayi ya kamo hannun ta yana fadin

“Baby kinji wai kina da ciki zaki haifa min ya’ya. Alhamdulillah! Allah nagode maka Allah ya rabaki da cikin nan lafiya.”

Hawaye ne ya fara zubowa daga idon ta ya tashi ya dawo gaban ta ya durkusa yasa hannu yana goge mata yana fadin

“Just say Alhamdulillah. Thanks Allah he will gove you more of what you didn’t expected.”

“Alhamdulillah! Alhamdulillah!! Alhamdulillah!!! Thank you Allah for blessing me.”

Ya sakar mata murmushi sannan ya mike ya kalli Doctor yace

“Thank you Dr mu zamu tafi.”

Doctor yai murmushi yace

“To Allah raba lafiya nan da sati hudu ko dawo in akwai wata matsala kuyi sauri ku fada mana Allah ya inganta.”

“Amin nagode.”

Ya kalli Fauziyya yace

“Madam kinga ko ba ai allura ba an samo abin farin ciki.”

Murmushi tayi tai kasa da kai ta mike,  Muhammad ya kama hannun ta suka fita.

Mota ya bude mata ta shiga sannan ya rufe. Ya xaga ya shiga. Motar ya tayar ya kamo hannun ta sannan ya fara neman layin Ummun sa. Tana dagawa yai connecting da wayar tace

“Mai babban suna ya akayi naga bamu jima da waya ba akwai wata matsala ne?”

STORY CONTINUES BELOW

“Ummu Albishirin ki?”

Ya fada yana kallon Fauziyya. Kai ta girgiza masa ya make kafada yace

“Ummu yanzu muka dawo daga asibiti Fauziyya bata jin dadi an duba ta an gano tana dauke da ciki.”

Ummu tace

“Kai Alhamdulillah Allah ya raya ya inganta ina Fauziyyan?”

“Gata nan.”

“Bata wayar.”

Fuska Fauziyya ta rufe da hannu yai dariya. Tace

“Ina yini Ummi?”

“Lafiya lou Fauziyya ashe mun samu karuwa?”

Shiru Fauziyya tayi tana yin kasa sa kanta kamar Ummin na gaban ta. Ummi da ta gane kunya take ji tace

“To sanni Fauziyya Allah raba lafiya. Ina nan nima zanzo na ganku tinda kunki ku dawo.”

“A’ah Ummi zamu dawo.”

Muhammad yace

“Ummi gaskiya ba yanzu ba sai nan da wajen wata uku lokacin anyi bikin kannen ta.”

“To Allah nuna mana ai kan lokacin ma mun zo kuna zamu bikin ma insha Allahu. Allah dai ya bamu aron ran ya nuna mana.”

“Amin Ummi mungode!”.

“To Fauziyya kina kula da kanki kinji?”

“Insha Allahu.”

Tace

“Kai kuma Muhammad kada kana takura mata kaga yanzu ba ita daya bace.”

“Kai Ummi na ni takura mata nake ki tambaye ta. Ai bana takura ki ko?”

Ya fada yana maida tambayar kan Fauziyya.

Hararar sa Fauziyya tayi ta girgiz kai. Ummi tace

“To dai a kiyaye. Allah ya inganta ya bata lafiya.”

“Amin mungode sai anjima.”

Ya kashe wayar. Kallon ta yayi yace

“Kika ki bata amsa ko?”

Kai ta dauke yai kwafa ya karasa bakin wani super market yai parking kallon sa tayi da alamar tambaya tace

“Me kuka zamuyi anan bayan jiya mukai shopping.”

“Ranan da muka zo shopping naga wasu kayan babies to su zan siya”

“Kayi me dasu?”

“Nayi me dasu kamar yaya Baby? Na tanadar wa our unborn Baby.”

“Haba dai tin yanzu honey!”

Mota ya bude ya futa tace

“Sai yaushe ai gwara mu fara tun yanzu.”

Ya zaga ya bude mata ta fito ya kama hannun ta suka shiga. Wajen kayan Babies din  suka shiga.

Fauziyya dai sai yar kallo ta tsaya tana kallo Dan yadda Muhammad yake jidar kaya baga mace ba baga namiji ba duk wanda yai masa dauka kawai yake. Ganin abun yai yawa yasa ta karasa wajen sa tana fadin

“Honey kayan sunyi yawa!”

Ya juyo yace

“Me na siya tukkuna dai Baby!”

“Nidai wallahi na gaji kuma yunwa nake ji.”

“Oh baki ci fa abinci ba ko? Me zan siyo miki kici?”

“Yaya shawarma nake so!”

Wajen accounter ya nufa akai total yai transfer sannan aka kai masa kayan su cikin mota. Ya kama hannun ta suka fita.

A hanya yaga ana sai da gasassun kaji ya tsaya ya siya sannan a gaba ya tsaya ya siya mata suka karasa gida.

*

**

***

****

*****

******

*******

********

*********

**********

***********

*************

Rukayya bayan ta bar gidan Ummu duk sai ta shiga cikin damuwa. Zaune take a falo ta zuba tagumi Yaya Sailuba ta shigo ta tsaya kallon ta.

Karasawa tayi ta zauna tana fadin

“Rukky lafiya?”

Dagowa tayi tace

“Yaya kinga gidan Ummu kinga rayuwar da su da ya’ya na. Wai ya’ya na basu sanni ba.”

“To shine me? Ke bagaki kina rayuwar ki ba da dasu fa da yanzu sun takura miki.”

“Amman Yaya Sailuba ai ya kamata su sanni ko?”

“Ke ni kyale ni da zancen wadan can ya’yan nak dasu Alhaji yake fada min Alhaji ya kawo karar ki,  kin ki kibashi dama ya turo.”

“Yaya ni…”

“Keme? Menene aibun sa bayan yana baki duk abinda kike so wallahi tin wuri ki shiga hankalin ki,  wa kike dashi a maneman naki sama da Alhaji Khamis din?”

“Yaya gani nayi ya min girma.”

“Kalle ki to saurayi kike tunanin samu kome? Ai ke kalar su Alhaji Khamis dince baki ganni bane. Kishiyoyi na uku kina gani amman duk suna can da yara sun tsufa ni kuwa gani anan ina shan shagali na sai abinda nake so Alhaji ke min su kuwan fana abinci ma wuya yake musu shiyasa gasu nan duk sun tsufa.”

Shiru tayi. Sailuba tace

“Yace zai gidanki da ban da sauran matan sa kuma yace sai abinda kike so to me kike nema.”

“Babu!”

“To anjima zai zo da yazo yai miki maganar ki bashi dama ya turo kinga shikenan ayi bikin ki kema ki huta ko ya kika ce?”

“Haka ne.”

“Yauwah.”

Ta mike tayi daki tana tunanin tayaya xata auri Alhaji Khamis.

Da yamma tana kwance Anty Sailuba ta shigo ta same ta tace

“Alhaji Khamis yazo naga nace miki zai zo naga baki ko shirya ba.”

“Me zanyi to Yaya a haka zani.”

“Ki rufa mana asiri haba dan Allah ki tashi dan gyara fuskarki yana sitting room.”

Tafita.  Mikewa tayi ta shafa hoda ta saka turare sannan ta fita. A falo ta samu Anty Sailuba tace

“Yaya na fito zan tafi.”

“Haba ko ke fa. Ki san yadda zaki ki tatso sa sannan a harkar biki a sha shagali muma mu nunawa su Ummu mun kere musu.”

Murnushi ta saki tace

“To yaya.”

Ta fita. Dakin da yake ta shiga da sallama. Alhaji Khamis dake zaune ya dago yana kallon ta tai murmushi ta samu waje ta zauna tana fadin

“Barka da yamma!”

“Baki ya washe yana fadin na samu gimbiyya ta lafiya?”

“Alhamdulillah!”

Ya zuba mata ido. Tace

“Kallon fa?”

“Kada na kalle ki ne?”

“A’ah!”

“To ni fa nace. Rukayya kin ki ki bani dama na turo ayi komai a gama”

“Ba haka bane”

“To Yaya ne?”

“Kawai dao saboda naga abu yaiwa Abbahn mu yawa ne shiyasa.”

“Me ya faru?”

“Bai jima da yiwa autar mu a mata aure ba.”

“Shine me?”

“Nima yanzu sai na dauko maganar aure bayan bai gama hutawa ba. Ga kashe kudi.”

“Haba Rukayya yanzu akan wannan ne daman kike wannan maganar to menene ni na dauki nauyin komai daga lefe har abinda kike so na daki kiyi lissafi da shagalin biki duk zan turo miki.”

“Nagode sosai Alhaji.”

“Ba komai yanzu ki fada masa za ayi bikin nan da wata daya lokacin nima zan aurar da yara har hudu kinga nima sai na angwace na more nayi kara’i na.”

“Wannan haka yake zan sanar masa insha Allah.”

“Nagode.”

Haka suka sha hira da zai tafi ya ajiye mata kudi masu yawan gaske ya tafi.

A guje ta shiga Falo Sailuba ta mike tana fadin

“Lafiya?”

“Yaya kinsan me kuwa?”

“Sai kin fada.”

“Yace zai yi komai na biki da kayan daki da laife ya ban dama duk nai lissafi zai bani kudi.”

“Kinji harkar girma ko ina kai ki kina zamewa.”

“Ai na gane Yaya zan kula”

“Ko ke fa! Nawa ya baki?”

“Gasu nan ko kirgawa banyiba.”

Ta zube su a wajen. Dauka tayi ta kirga ta dago tana fadin

“Kullum sai an dada dubu ashirin.”

Baki Rukky ta tabr tace

“Bari na shiga na kwanta zuwa anjima”

Tayi ciki ta ajiye kudin ta kwanta.

Da daddare sukai waya da Sakina ya fada mata sai da gaban ta ya fadi dan tsoro. Tace
“Khaleel Momy ta yadda ne?”
“Momy zaki aura ko ni?”
“Kai!”
“To shikenan ni na yadda na aminta.”
“To Allah kaimu.”
“Amin. Gobe zan kara ganin Baby na.”
“Uhmm!”
Haka yai ta janta da hira amman ina hankalin ta sam bai wajen yana ga tunanin irin zaman da zasuyi da sirikar ta. Duk sai taji ta damu da wanne ido zata kalle ta. Anya kuwa batai wauta ba na aminta da auren Khaleel.
Yaya Fauziyya ce ta shigo ta tsaya kallonta amman bata ma san ta shigo ba. Zama tayi a kusa da ita ta cire mata tagumin tace
“Tunanin me kike?”
Juyowa tayi fuskar ta cike da damuwa tace
“Tayaya zan kalli sirika ta da wanne ido.”
“Shine zaki damu. Shawara daya zan baki ki rike Allah irin matan nan ba haka suke zaune ba sannan ki kalle ta da daraja a matar mijin ki daga haka kada wata mu’amala ta hada ku ki girmamata tinda mijin ki na son ki ai shikenan.”
“Haka ne nagode Yaa Fauziyya.”
“Kada ki damu.”
Tai mata murmushi tace
“Mai gyara gobe zata zo zata ga me kuke bukata kan ta dawo ta fara gyara ku.”
“Allah kaimu amman kin fada mata…”
Sai tayi shiru fauziyya tai murmushi tace
“Na fada mata ku zawarawa ne zaku sake aure a gyaran ku sosai”
“Mungode Anty Fauziyya ba wannan a tsakanin mu.”
Ta mike tace
“Bari naje na kwanta kaina ke ciwo.”
“Ayyah sannu Anty ciwo ciwon nan ba zamu je asibiti ba kuwa?”
‘Me za ayi daga ciwon kai.”
“Ni gani nake ko dai an harbu!”
Dakuwa tai mata tace
“Gidan ku.”
“Tai dariya tace
“Allah inganta.”
Ta juya ta fita.
*
**
***
Soyayya suke sha Hafsat da Ahmad dan da ya tafi kamar kara shakuwa aka saka musu ko agun aiki tare suke yini makale da juna haka da dare dan sai ta taka masa birki sannan yake barin ta.
Haka ma Khaleel baya sati bai zo ba soyayya suke sha mai tsafta da fahintar juna abinsu.
Duk soyayyar Hajara da Sani tafi ta kowa burgewa domin Hajara yarinya ce karama mai kunya. Gashi Sani na masifar son ta da kaunar ta. Sai doki yake da son kasancewa da ita domin kuwa ba karamin son ta yake ba itama kuma tana son abun ta.
Halima da Kabir kuwa sun shaku sosai da junan su. Dan ko da yaushe zai kira ya take ya ka me take so ko ya aiko mata da abu in ya samu dama yazo su gaisa. wanna yasa ta kara sakewa dashi ta dauke shi a matsayin yayan ta. Sai take jin wani abu daban akan sa har take jin ina ma shi ne yaso ta a baya ba Isma’il ba.
Son da yakewa Halima bai sa ya kasa bawa Sadiya kulawa da nuna mata so badan bazaka taba cewa ita tace tana son sa ba. Dan yadda yake bata kulawa sun aminta da junan su sosai su kuma yadda da junan su.
STORY CONTINUES BELOW
*
Sun zo sun tambayi aure daga manema Sakina,  Hafsa,  Halima da Hajara kuma duk an tsayar nan da wata daya dan haka sai aka fara shirye shirye gaba dayan bangarorin dan cikin sati da farai musu gyara suka yi kyau suka fara canjawa gaba dayan su. Ita kuwa Halima mamaki take tayaya ake musu gyaran amare tare.
Muhammad shi ya bada order kayan dakin su komai da komai da wasu kayan kitchen din abunda ba za arasa ba kuma ya bawa Fauziyya kudi masu yawa suka shiga kasuwa suka siyo kayan.
Ana sati biyu biki aka kawo laifin Halima da Hafsa. kayan masu yawa da tsada Kabir yayi komai irin daya da Sadiya har da gold da mukullin mota iri daya sak.
A cikin satin aka kawo na Hajara da Sakina. Suma kaya masu uban daya da kada abin dai sai sam barka sai wanda ya gani. Kowa yazo yaga kaya sai ya saka albarka. Ba wanda ya kai Fauziyya murna da farin ciki.
Ba su shirya komai ba za adaura aure jumma ayi kamu da yini a ranar da dare a mika kowa gidan ta haka suka shirya. Halima tin da aka kawo lefe aka ce nata ta shiga tunani da zulumi ta rasa wa zata tambaya tace wa zata aura. dan ko da Yaya Fauziyya tazo bata wani jima ba dan tana shirin biki kayan fitar biki da order da za a bayar.
*
**
***
Muhammad ne yake driving ya kalli Fauzuyya da ta lafe a jikin kujera yace
“Gaskiya Baby kina wahala,  kalli yadda kika koma gaskiya ba zaki kara fita ba daga yau.”
“Na gama My love ai yanzu lokaci kawai zamu jira sai ana saura kwana biyu zamuje ai mana gyaran kai da lalle kan nan da kwana biyar zan huta.”
“See you ba inda zakije fa.”
“Haba Honey baka son na dawo nima amarya.”
“Ni a guna kullum amarya ce.”
“Duk da haka zan maka kwalliyya kada kace a’ah dan Allah.”
“Ba zance ba Allah ya kaimu.”
“Amin nagode.”
Yai horn mai gadi ya bude ya shiga yai parkinh ya fito ya bude mata mota ya kamo ta sukai cikin gida.
Akan kujera ta zauna ta mike kafar ta. Ya farai mata tausa yace
“Bari na kawo miki naman kici ko?”
“Baby ka farai min wanka ko?”
Ya durkusa ta haye bayan sa sukai sama. Shi yai mata wanka ya shirya suka dawo falo ya bata abinci taci ta koshi sannan ya hau mata tausa.
*
**
***
****
*****
******
*******
********
*********
**********
***********
Yau a gidan su ta yini dan jibi zasu daga su tafi a Abuja da su Jannah da Junaid zasu tafi inda in sunje zasu ajiye su,  su tafi yawon shakatawar su dan Muhammad yana hutu.
Tare sukaje da su Jannah duk suna dakin Umma suna zaune bayan sun gaisa tace
“Umma,  Abbah yana nan ne?”
“Yana nan.”
Ta mike tace
“Bari muje mu gaida Mama sai muje yaga matar sa da abokin sa.”
“To!”
Suka fita hannu ta daya rike da hannun Jannah dayan kuma rike da hannun Junaid. A haka suka karasa dakin Mama tana falo suka shiga ta bisu da kallo yadda duk sukai kyau sukai jajir ga shiga mai kyau kaya masu tsada a jikin su. Hatta turaren su mai tsada ne. Zama sukai suka gaishe ta sannan suka fita suka bar ta da kamshin su.
Dakin Abbah suka shiga yana ganin su yace
“Ah amarya tace yau a gidan?”
Jannah ta durkusa tace
“Ina yini Abbah.”
Ya kamo hannun ta yana fadin
“Lafiya lou Amarya ta ya Hajiyar taku?”
“Tana lafiya.”
Junaid ya dago ya kalla  yaga ya hade rai yace
“Haba angon Umma karaso mana dan Antyn da da Hajiya kai da ka kwashe su dukka.”
Ya karaso a guje ya haye cinyar sa yana dariya. Ummu tai murmushi. Abbah ya shafa kansa yace
“Ya kake?”
Sai yai sauri ya mike ya durkusa yace
“Ina yini Abbah?”
Abbah ya kamo shi yana fadin
“Lafiya ya makaranta?”
“Abbah munyi hutu shine zamu tafi unguwa da Mami da Abbi wai zamu wajen Auntue Zainab.”
Kai Abbah ya daga yana jin dadi. Domin tin yanzu ya fara ganin alfanun auren Muhammad da Ummu domin kuwa ko ba koma ya’yan yar uwar ta ba zasu shiga halin rashin uwa ba yasan ummu zata rike su tamkar ya’yan ta na cikin ta koma fiye da haka. Duk da suna wajen mahaifiyar sa amman itama zatana kulawa da basu shawara a matsayin uwa sanan zata na sa suna zuwa gida duk sanda zatazo ko in ana wani abu ba kamar in baita ke auren Muhammad ba sai abu na gaba zata sa yaran suna zumunci da ya’yan yan uwan ta ba kamar da ba da in bata tare ba sosai zasuna zuwa can ba.
STORY CONTINUES BELOW
Kai Alhamdulillah abinda yake ta fada a ransa kenan yana shafa kan Junaid dake cinyar sa yana masa surutu.
Ummu ta gyara zama tace
“Ina yinu Abbah?”
Ya kalle ta fuskar sa cike da fara’a da murmushi yace
“Lafiya lou Ummu ya kike ya gidan da mai gidan?”
“Alhamdulilah!”
“Ba dai wata matsala ko?”
“Babu Abbah!”
“Madallah haka ake so amman ki sani zaman aure dan hakuri ne dole ki ta hakuri kinji.”
Kai ta gyada yace
“Allah miki albarka! Allah yasa ki gana da duniya lafiya.”
“Amin”
“Hakika duk lokacin da na ganki ina jin dadi da alfahar dake kin sharen hawaye na kin zauna da mijin yayar ki lafiya Allah miki albarka. Nagode!”
“Amin Abbah. amman ba kai zakai min godiya ba ni zan maka godiya domin ka zama min miji na gari wanda ko wacce ‘ya xata fatan samu kuma tai alfaharu dashi. Hakika Abbah Yaa Muhammad ya wuce duk tunanin ka a halaiya mai kyau yana da tausayi da imani yana kula dani tamkar ina gida baya taba bari na da damuwa Abbah zan ce maka tinda nake dashi tsawon watannin nan bai taba batan rai ba. Kaga kuwa Abbah ni zan maka godiya Allah kara nisan kwana ya baka lafiya yasa ka gama dauniya lafiya. Allah jikan iyaye da kakanin yai maka tukuwici da gidan aljanna.”
Fara’ar kan fuskar sa ce ta dadu ya amsa da
“Amin yar aljanna. Ki cigaba da maza biyayya kema zaki tsinta zaki samu ya’ya masu biyayya insha Allahu.”
Tai kasa da kai yace
“Naji Junaid na fadin zaku hutu gidan Zainab ko?”
“Eh Abbah nazo nai muku sallama ne daman jibi zamu tashi gaba dayan mu.”
“Masha Allah. Allah kaimu Allah tsare ya baku ladan zumunci.”
“Amin!”
“Yaushe zaku tafi gida kenan?”
“Anjima zai zo ya dauke mu.”
“To in na fita zan taho da abunda za akai musu.”
“Toh Abbah!”
Ta bude jaka ya zaro kudi a ciki masu yaqa ta ajiye masa a gaba. Ya kalli kudib yace
“Kudin menene wannan Ummu?”
“Abbah tinda Yaa Muhammad ya fara aiki duk karshen wata sai ya bani kudi masu yawa nayi magana yace kada na kara magana shine na raba gida hudu na baka daya zan bawa Umma daya sai na ajiye daya zan masa hidima sai dayan na raba zan bawa Mama dayan uwana.”
Kai Abbah ya gyada yace
“Masha Allah. Allah miki albarka kinji. Yanzu ki dauki kudn nan ki ajiye kyayi amfani dasu wata rana.”
“Abbah ina da kudi dan Allah ka amshi wannan kasa albarka.”
Kai ya gyada yace
“Allah miki albarka.”
“Amin nagode.”
Nan sukai ta hira rabin hirar duk nasiha ce a ciki na tayi biyayya ga mijin ta sannan tayi hakuri a gare shi.
Sun jima tare har tace
“Abbah baka taba zuwa guda na ba.”
Yai murnushi yace
“Ummu ni gidan wa na taba zuaa a ya’ya na.”
“Abbah dan Allah kazo mun zan ji dadi sosai.”
Ya kalle ta yace
“To zan duba.”
“Dan Allah Abbah.”
“Zan zo Ummu insha Allahu.”
“Nagide Abbah.”
Kiran sallah la’asar yasa suka rabu ya tafi masallaci shi da Junaid ita da Jannah sukai dakin Umma. Sallah sukai sannan ta dauko kudin masu yawa ta dire ta cirewa Mama da Umma sannan sauran ta bawa Umma tace
“A rabawa Yaya Alkasim da Yaya Abdullahi da Khaleel.”
“Ummu kudin nan fa.”
“Umma kisa min albarka kar kice a’ah.”
“Ba zance a’ah ba amman sunyi yawa ribar taki kike son karar wa.”
“A’ah Umma…..”
Nan ta fada mata yadda abin yake. Ummata gyada kai tana fadin
“Allah yayi albarka.”
Nan ta bata na Mama tace ta kai mata da ta kai mata Mama ba kunya tasa hannu ta amshe abun ta.
Ana kiran isha’i Muhammad ya shigo unguwar a kofaf gidan su Ummuy yai alwala ya shiga masallacu. Abbah ya sama yana lazimi Junaid na gefen sa. Karasawa yayi ya hau jam’i aka tada sallah sai da aka gaba suka fito.
Abbah shi ya kamo Muhammad suka shiga har dakin sa. Abinci Umma ta kawo ta same shi a dakin. Tare suka ci abinci shi da Abbah da Junaid.
Sai da suka gama suka gaisa nan yai tai masa nasiha da bashi hakuri akan yana hakuru da Ummu ko da zata bata masa. Muhammad kan sa a kasa yace
“Abbah! Ummu bata taba batan rai ba. Ummu yar aljanna ce. Bata son bacin raina duk abinda nake so shi take min. Ina godiya da Allah dakai Abbah domin Allah ya min sauyi da sauyin alheri ba abinda zan ce sai dai godiya da addu’a Allah saka da alheri amman Abbah ka bani abinda ban taba zaton samu ba ka bani abunda zai kaini ga aljanna insha Allahu.”
“Masha Allah. Allah ya yadda.”
“Amin!”
Haka sukai ta hira. Da zai tafi ya zubewa Abbah kudi Abba zai magana Muhammad
“Abbah in dai ka dauken a ‘da kayi shiru kawai kai min addu’a!”
“Allah maka albarka ya jikan iyayen ka .”
“Amin!”
Ya mike ya fito. tare suka fito da Abbah. Abbah ya rakashi ya shiga dakin Mamah itama ya bata kudi dakin Umma suka shiga Jannah tayo gun su Nan suka zauna ya gauda Umma sannan ya dire kudi zatai magana itama ma ya rufe mata baki  haka ya dauki Ummu da yaran suka tafi.
Tana daki tana hada kayan ta ya shigo. Jikina yayi da kofa yana kallon ta. Ta dago tana fadin
“Yaya Muhammad ya dai?”+
Kura mata ido yayi yana murmushi. Ta ajiye kayan da ta dauko ta dago tana kallon sa. Karasowa yayi ciki yana fadin
“Me kike ganin za a kaiwa su Anty Zainab da Yara?”
“Haba dai ai ziyarar da zamu kai ma.ta isa ko?”
“Ki sauri ki shirya muje muyiwa Hajiya sallama sai mu biya mu sai musu abu. Tayaya zamuje musu hannu haka ba komai.”
Yana kaiwa nan ya fita. Tai murmushi ta karasa hada kayan sannan ta shiga ta shirya ta fito. Shi da yara ta same shi a falo duk suka dago suna kallon ta. Tace
“To muje kada yamma tayi.”
Ya mike yace
“Yarana ku kalli yadda Mamin ku tayi kyau.”
Junaid yace
“Sosai Abbi!”
Jannah tace
“Mami kinyi kyau!”
Rai murmushi tace
“Kuma haka muje kunji!”
Ta dago ta harare shi  yai mata gwalo yai gaba. Suka bi bayan sa mota ya bude mata ta shiga gaba yaran suka shiga baya. Gidan Hajiyar sa suka je suka gaisa sai da akai isha’i dan acan yaran duk suka ci abinci sannan sukai mata sallama suka taho.
A wani super market ya tsaya yai suka shiga. Yace
“Kowa ya dauki abinda yake so.”
Yaran suka shiga zagaye wajen duk abinda suka ga suna so suka dinga dauka.
Muhammad kuma yaiwa ya’yab Anty Zainab siyayya sosai. Ummu kuwa ba abinda ta dauka nata duk Muhammad taiwa siyayyar under wears da turaruka sai da suka je total ta daukar musu ice cream nan ya biya suka saka a mota suka tafi gida. Kan su karasa duk yaran sunyi bacci. Ya parking ta fito zata dauki Junaid yace
“No muje kawai zan dauko su “
Ya dauki Jannah ya kai dakin su tabi bayan sa ta canja mata kaya tai mata addu’a sannan ya kai Junaid dakin sa shima kaya ta canja tai masa addu’a sannan ta nufi dakin ta. Wanka ta shiga tayi ta fito daure da towel.
Akan karfet din dakin taga ya zube ledar kauan junaid ball ce da JC sai mota da biskit ya maida yana murnushi. Jannah kuma yar tsana ce da story book sai kayan kwalliya. Nan ma yai murmushi ya dauki ledar sa yace
“Ga kayan su Anty Zainab nan.”
Ta juyo tana fadin
“Allah ya saka ya kara budi.”
“Amin”
Ya januo ledar ta ya zazzage sai ya tsaya kallon kayan juyowa tayi tana ganin yana kallon kayan ta mike tayo gun sa tana fadin
“Wa yace ka buden kaya na?”
“Baby ke me kika siya?”
“Yaa Muhammad ba abinda nake bujata kai kawai nai wa siyayya.”
Ta fada tana mai da kayan cikin leda.
Janyo hannun ta yayi ta dago suna kallon juna nunfashin su na gauraya take ya fara sakin layi dan yadda yake jin shigar dumin jikin sa nata. Janta yayi jikin sa yace
“Allah miki albarka Baby nagode sosai “
“Kaji Yaya kudin ka ne fa.”
“Kudin mu dai!”
Ya fara kissing bakin ta daga nan kidan ya sauya.
Washe gari da safe suka daga karfe sha biyu suna garin Abuja sun karasa gidan Anty Zainab wacce tai musu tarba ta musamman ta rasa ina zata saka su komai suka samo su haka yaran sun hadu da yan uwan su duk sun kasa zama sai murna suke abinsu.
STORY CONTINUES BELOW
Da Yaa Suleiman ya dawo ma nan suka gaisa suka sha hirar su. Can gueat room aka kai Muhammad dan ya sake. Da dare Anty Zainab ta shigo dakin da Ummu take ta same ya tana shirin kwanciyya. Kayan bacci ta saka masu kyau sannan ta shafa turare amman sai me sai ta haye gado. Anty Zainab tace
“Me zakiyi ne?”
Hamma tayi tace
“Bacci!”
“A ina?”
Dakin ta kala tace
“Nan mana.”
“shi kuma Muhammad ki barshi shi kadai.”
Zama tayi a gefen gadob tace
“Nifa ba sirikar ku bace dan me zaki bar shi shi kadai kin sabar masa ko? Kina nuna halin ko in kula da mijin ki ko?”
Wayar Ummu ce tai kara ta dauko taga Muhammad ne. Kin dauka tayi Yaya Zainab tace
“Dauki mana!”
Ta dauka yace
“Baby kina ina?”
“Gani nan.”
“Ok i miss you!”
Ya kashe wayar. Tace
“Shine ko?”
Kai ta gyada. Tace
“Tashi kije kuma kayan ki ma can za a kawo miki haka ake.”
Ta mike ta fita. Tana falo Ummuta fito sanye da hijab har kasa. Anty Zaunab tace
“Zo nan!”
Ta mike tai kitchen Ummu ta bita. Nojo ta dauko ta zuba magani a ciki ta mika mata tace
“Shanye!”
Ta kurba sai taji ba suga ta sauke tace
“Ba suga fa.”
“Wa yace miki da suga ake sha. Ki Muhamad a haka zai ji ki da suga din ai.”
Da sauri Ummu ta juya mata baya ta dauki cup din ta kafa a bakin ta. Sai da ta shanye ta dire sannan ta bude lokar kitcen ta dauki alwala tace
“Sai da safe.”
“Ki dai kula da mijin ki. Allah tashe mu lafiya”
Ta fita tana shiga dakin ya mike yayo gun ta. Rumgume ta yayi yana fadun
“Yini daya da ban jiki a jikina ba duk na yi kewar ki.”
Tai murmushi tace
“Nima Yaya!”
“Me kike sha?”
Alawar ta dallaro da ita ta maida. Yace
“Zo musha tare!”
Ta matsa jikin ya rumgume ta ya hade bakin su. In ya tsotsa sau ya maida mata bakin ta ta tsotsa a haka suka dinga sha kan ta kare wasan ya sauya.
*
**
***
****
*****
******
*******
********
*********
**********
***********
Dady ne zaune a falo yana waya. Mami mahaifiyar Ahmad ta shiga. Zama tayi bayan ya gama waya ya kalle ta yace
“Au munje tambayar auren Ahmad fa. Nayi binkice na gane gidan mutunci ne. Dan haka an tsayar da biki nan da wata daya mai kanawa.”
“Wanne Ahmad din Alhaji?”
“Wanne Ahmad nake dashi?”
“Amman yaushe yayi aure Alhaji.”
“Shin haram ne dan bai jima da aure ba ya kuma aure. a yan uwan amaryar akwai waccesu biyu zai aura shine dan shi bai haka ba kike son ki nuna min haramcin abin!”
“Ba haka bane Alhaji amman kadaka manta Hannah ‘ya tace.”
“Masha Allah gwara da kika ce haka domin hakan shi zai sa na miki misali shikenan yanzu Basma in mai mata ya fito yana son ta ba zata aure shi ba ko kina so kice min dan bai jima da aure ba ba zai auri yar ki ba bayan suna son juna. In yar ki ce zaki haka. Wai ku mata meyasa kuke haka ne?”
“Alhaji kayi hakuri.”
“Yaron nan bari kiji tin kan ya auri Hannah ya samu yarinyar da yake so ni na dakatar dashi nace sai yayi aure tinda yai auren nan yake min magana ina ja masa lokaci ganin bai hakura ba na bashi dama iyayen yarinya suka ce na fito sai da nayi bincike na amince da auren to menene aibu yana son yarinyar itama tana son sa  bana son kananun maganganu ki sa masa albarka kawai.”
“Shikenan Alhaji Allah sanya alheri ya bada zaman lafiya.”
“Amin shikenan.”
“Ankai lefe domin maza suke son suyi komai ba mata ba.”
“Amman ai da an fada ko wani abu na bayar an saka ko?”
“Angode ki ajiye na gudunmawa ki sa musu albarka da addu’ar zaman lafiya.”
“Allah ya bada zaman lafiya ya sanya alheri.”
“Amin ko ke fa.”
Tai kasa da kai. Yace
“Sai ku fara shiri dan ba su gidan yarinyar ba sa son bidi’a dan haka cikin sanyi za ayi a gama.”
STORY CONTINUES BELOW
“Allah nuna mana lokacin!”
“Amin!”
Ta mike ta fita. Daki ta shiga ta samu Basma tace
“Ke kinji aure Ahmad zai yi?”
“Lah abin yazo ashe!”
Kallon ra Mamo ta tsaya yi sai tayi kasa da kai tace
“Dake ake cutar yar uwar ki kenan ko?”
“Ba haka bane Mami. Yaa Ahmad yana son Anty Hafsa nasan in ya same ta zai samu nutsuwa itama Anty Hanna ta huta kuma ni ba cuta bace ya jima da fada min dan tin kan bikin sa da Hanna ne dan da cewa yai ma ba zai auri Hanna ba kuma kinsan me yarinyar tana tarbiyya da ilimi addini abinda yaja hankalin Yaa Ahmad kenan kinsan yadda suka sha fama da Hanna ita tana son saka kananun kaya da mayafai to ita hijabai har kasa take sawa….”
“Ni rufe min baki kina son ki nuna kin fison ita wacce zai aura ne!”
“Ba haka bane. Amman Mami in ya aure ta ai ta zama mu domin kuwa zata haifa wa Yaya ya’ya to kinga ai dole mu so ta. Itama Anty hanna ta zauna lafiya da abokiyar zaman ta kinsan dai duk abinda Yaya yake so nima ina so ko?”
“Lallai ke kuwa mace ce. Ace bakya kishi akan yar uwar ki tashi ki ban waje.”
Mikewa tayi ta fita. Dakin Dady ta shiga ta same shi zaune ta zauna tana fadin
“Barka da hutawa Dady!”
“Yauwah Basma ya gidan?”
“Lafiya lou. Dady ashe bikin Yaya ya matso.”
“Eh ya matso kinsan da maganar ne ke?”
“Dady ya fada min tin kafin auren sa da Hanna. Kuma ina masa addu’a in alheri ce Alah tabbatar ya basu zaman lafiya.”
“Amin amin. Masha Allah haka ake so.”
“To Dady yanzu me da me za ayi?”
“Dagin amaryar basa son wani taro amman ki tambayi Yayan naki ko shi zai wani abun”
“Zan masa magana ai ko yar dinner ce ayi mana ko Dady?”
Dady yai murmushi. Ta mike tae
“Bari naje na kira Yayan nai masa Allah sanya alheri.”
Ta fice. Daki ta shiga ta dauki waya tana kira taji call waiting.
A lokacin waya yake da Hafsa yaji kiran Basma yace
“Kinga kanwar ki nakira”
“Basma?”
“Yes!”
“Ok ka dauka kaji bari na je nima nayi aiki”
“Ok sai anjima ko?”
“Yes!”
Sukai sallama. Layin Basma ya kira tana dauka tace
“Ango ango!”
“Na’am kanwar ango.”
Tayi dariya tace
“Allah sanya alheri.”
“Amin!”
“Yaya ai ni sai yanzu Mami tazo min da maganar!”
“Mami kuma waya fada mata?”
“Kila Dady ne!”
“Oh me tace?”
“Tana fada ne wai bana taya Anty Hannah kishi. Ni kuma na fada mata duk abinda kake so ina so.”
“Good girl. Yanzu ya ake ciki “
“Zan lallashi Mamin.”
“Alright!”
“Yanzu na baro Dady yake fada min konai Yaya mu me zamu shirya?”
“Hafsa bata son komai.”
“Kuma Yaya shine ba zamuyi ko dan event daya ba love of ur life ce fa.”
“Kai Basma!”
“Eh mana Yaya.”
“To yanzu ya za ayi?”
“Gaskiya muyi ko dinner ne!”
“To shikenan zamuyi ki shirya komai sai ki fadan.”
“Thats my Bro.”
Ya kashe yana dariya. Jingna yayi da kujera ya lumshe ido. Sai kuma ya dauki waya ya fara kira ana dauka yace
“Ku kai kayan gida na.”
“Alright!”
Ya kashe wayar ya mike ya dauki briefcase din sa ya fita. Mota ya shiga yai gida. Yana zuwa ana magarib a masallaci yai sallah sannan ya fito ya shiga.
A falo ya samu akwati nan a jibge. Ba kowa a falon daki ya shiga yai wanka sannan ya dauki wata leda da kudi ya fita falo. Hanna ya sama tana kallo. Ya fito ya zauna ta kalle shi tace
“Kayan menene wannan?”
“Kayan ki!”
“Kaya na?”
Kai ya gyada yace
“Eh ga kudi nan kiyi amfani dasu.”
Ya tura mata daukar ledar tayi ta bude taga bandir din 1k guda uku ajiyewa tayi a cinyar ta tace
“To duk na menene?”
Yai murmushi yace
“Zan kara aure naga haka ake aladar mu shine nima nai miki……”
Da sauri tamike ta cilla masa ledar kudin tace
“Aure zakai Yaya?”
Mikewa yayi ya kwada mata mari yace
“Ni sa’an kine da zaki jefe ni. Ko dan kinga ina bi dake yadda kike?”
“Yaya ni ka mara?”
“Na mare ki din kin ba zane ki ba. Daga yanzu na daina biye miki ina miki abinda kike so. Aure ne kuma ba fashi in kinga zaki zauna dani a haka fine and good.”
Ya fada yai dakin sa da kallo ta bisa sai kuma tayi dakin ta a guje ta fashe da kuka. Kuka take tana neman mafita. Waya ta dauka ta fara neman layin kawar ta tana dauka tace
“Billy na shiga uku Yaya aure zai kara!”
“What?”
“Wallahi aure zai!”
“Ki jira ni zuwa gobe.”
“Ok ina jiran ki fa.”
“Kada ki damu.”
Sai ta dan samu nutsuwa dan tasan zata samu wani rangwamin daga kawayen ta dan suna kawo mata mafita.
A bangaren Hajiyar ma dai lokacin da Alhaji ya dawo ta same shi a dakin sa. Zama tayi tace
“Wai Alhaji me yake faruwa ne?”
“Kamar yaya fa?”
“Naga baka zama kwana biyu!”
“Zan auren da ina naga ta zama.”
“Wanne d’an?”
“Wane ‘da nake dashu banda Khaleel”
“Au auren yana nan dai da wannan yarinyar?”
“Eh yana nan. Dan yau ma muka ki lefe biki sauran sati biyu.”
Ido tayi mitsin mitsin dashi tace
“Wai Alhaji da gaske?”
“Da gaske nake mana ko na tabai miki karya ne?”
“A’ah amman Alhaji nace muku bana son yarinyar nan ko?”
“Hajiya in har kina son auren nan ya fasu to ki fada min aibun yarinyar nan ni kuma in nai duba naga haka ne to ba zan aura masa ita ba.”
Yana kaiwa nan ya bar mata wajen.
Itama mikewa tayi ta shiga ta saka mayafi ta fice a gidan. Gidan kawar ta hajiya Balaraba taje tana zuwa ta samu abokan shashancin su nan ta zauna tayi jugun. Hajiya Balaraba tace
“Ya dai Hajiyar?”
“Ban ga amfanin wannan rayuwar da muke ba gashi nan ina ji ina gani ‘dana zai auri yarinyar da nake wannan harkar da ita.”
“Naga an baki shawara ko?”
“Wacce zan dauka a ciki?”
“Taya mana akawo miki ita kicigaba da mu’amala da ita ake gaba ta kai ki.”
“Allah ya kiyaye ba zan iya ba. Wallahi ba zan taba iya mu’amala da matar ‘dana ba sirika ta.”
“Sai ki bada kudi aje ai miki aiki tinda Alhaji yana nan ba zai bari kije ba.”
“Zan iya wannan ko nawa ne zan bayar ku fada min nawa zan bayar kuma wanene zashi.”
“Ai ko dan na cire ki daga wannan bala’in naje miki.”
“Da gaske?”
” gaske nake!”
“Nagode Balaraba Allah bar zumunci.”
“Amin amman fa Hajiyar ina bukatar ki kwana biyu kin daina biya mun bukata ko dan Alhaji yana nan ne.”
“Hmmm *wannan rayuwar* ta fita akai na. Tinda Khaleel ya kamani naji na tsani *wannan rayuwar* da muke yi dan haka ni na tuba.”
Tana fada ta dauki jakar ta tace
“Ki fadan ko nawa ne ta waya zan miki transfer.”
Ta juya ta fita. Wank tsaki Hajiya Balaraba ta saka tace
“Zaki dawo hannu ne dan in naje har ke sai an asirce minke. Ya za ai ki daina biya mun bukata.”
Tai wata dariya ta mike tana kallon yan matan dake dakin tace
“Uku suzo muje daki.”
A cikin yan mata bakwan dake dakin suka fara guje gujen mikewa su bita. Ta juyo tana kallon su tace
“Rabi,  Dije,  Jamsy ku zoku zo. Sauran ku bari da dare kunji?”
Gwalo sukai musu suka mike suka bi bayan su. Fatisha tace
‘Mu da zamu kwana tare kuma!”
Kaltum tace
“Bar banzaye dai.”
Asee tace
“Tinda mu hudu ne muma muje mu rage zafi bibbiyu ko?”
“Haba dai muje dukka kowa ya hau kan kowa kunsan tinda na saba da Hajiya Balaraba wallahi na ke jin in ban hada mata uku akai na ba bana samun gamsuwa.”
Suka dau shewa sai sukai ciki.
STORY CONTINUES BELOW
Kamar yadda sukai da Hajuya Balaraba haka tai mata total ta bata kudi masu waya ta tura mata nan ta ninka mata su ta tura mata. Hajiya Balaraba taji dadi dan a cikin yaranta sai da ta dauki biyu suka daga sai dai me kan su sauka jirgin su ya hatsari ya fado wanda daga Hajiya Balaraba har yaran ta ba wanda yayi rai a ciki su.
Hajiyar na zaune a falo tana kallon news taga an nuno jirgin da ya tashi da safe zai sauka a china anyi hatsari kuma da yawa daga cikin mutanen dake ciki sun mutu. Nan aka nuno fuskokin su. Hajiyar ba kaamin kidima tayi ba sai jikin ta yai sanyi ta rasa kuma.ya zatayi. Har da hawayen ta.
Washe gari ta shurya sai gidan wata kawar ta Hajiya Asabe. Bayan taje suka gaisa Hajiyar tace
“Hajiya wajen malami nake so ki kai ni!”
“Me ya faru?”
“Yaron waje nane zai aure!”
“Yaron wajen ki shine me to sai kace kishiya za ai miki .”
“Ba gwara kishiya ba Asabe!”
“To akan me kika ce haka?”
“Yarinyar da nake mu’amala ce fa yake nema.”
“Ikon Allah shiyasa nace mikk ki daina lazbian din nan amman kin ki.”
“Na daina amman yanzu ni auren ne bana so kwata kwata.”
“Akwai wani malami na zamu zai fada miki gaskiya akan komai.”
“Yauwah nagide muje.”
Suka mike suka fita. Suna sukai masa bayani yai dube duben sa ya buga kasa ya dago ya kalli Hajiyar yace
“Hakika in har kika matsa akan auren nan zaki iya rasa rayuwar ki. Auren nan ba abinda zai hana shi yiyuwa domin ga rabo nan da alherai masu yawa daga yarinyar shawarar da zan baki kawai ki amshi yarinyar nan.”
“Innalillahi wainna illahir rajiun!”
Hajiya Asabe tace
“Tinda ya fadi haka Hajiyar duk ina zaki sai dai suci kudin ki shiyasa nake zuwa wajen malamin nan domin yana fadan gaskiya akan komai da zai faru.”
Mikewa tayi ta fita tana hawaye. Tabi bayan ta tace
“yanzu hakuri zakiyi tinda kin tuba kiyi ta addu’a Allah ya kara shirya ki yarinyar ma ki mata addi’a Allah shirya ta ya basu zaman lafiya. Shawarat da zan baki kenan fa.”
Suka shiga mota ta mai da Hajuya Asabe ita kuma driver ya zarce dasu gida. Ti  daga lokacin ta mika komai ga Allah ta zubawa sarautar Allah ido.
*
**
***
****
*****
******
*******
********
*********
***********
Washe gari Hanna ta kura Mami tana kuka ta fada mata komai. Hankalin Mami ya tashi nan ta hau lallashin ta. Tace
“Nima jiya Alhaji yake fada min zan mgana ya hanani na rasa ta ina zan fara.”
“Mami ki hanasa auren nan dan Allah.”
“Hannah ban san tayaya zan hana ba domin kuwa har sadaki da lefe an kai kiyi hakuri kawai.”
“Innalillahi wainna illahir rajiun Mami ba zan iya zama da kiishiya ba.”
“Haba Hannah kada ki manta yayan kine fa.”
“Mami baki san yadda naku ji ba mami kice ya barni na taho gida ni ban san zaman nan yanzu kwata kwata.”
“Zan masa magana amman ki kwantar da hankalin ki kinji.”
“Toh!”
Nan ta kira Ahmad ya dauka yace
“Ina yini Mami?”
“Lafiya lou yanzu Ahmad abinda kayi ka kyauta kenan?”
“Mami kiyi hakuri ina son Hafsa ne dan Allah ki sa mana albarka ni nayi alkawarin yin adalci a tsakanin su.”
“Shikenan Allah sanya alheru ina son Hanna tazo gida gobe goben nan.”
“Mami amman saboda me?”
“Ni dai na fada maka.”
“To shikenan.”
Washe gari ya sa aka kai ta acan ma sai kuka takewa Mami. Mami sai lallashin ta take.
Haka nan kawayen ta sai zuba ta suke suna fadin kada ta soma yadda ai mata kishi ai wannan shine kaskanci mai muni ma ita kuma ta hau ta xauna.
STORY CONTINUES BELOW
*
**
***
****
*****
******
A bamgaren Sadiya ma kuwa sai shirye shirye take domin dagin mahaifiyar ta ne ma suka dauke ta suna mata gyaran amarci ta kara kyau tayi haske. Ba abinda take yi. Kuma suna shan siyayyar su da Kabir hankali kwance. Basu shirya komaj ba daga kamu sai yinu da walima dan Kabir baya son bidi’a
Lokacin da yaje kawai Isma’il kati daurin aure ya same shi da wata yarinya a gidan sa. ai kula ta ba ya ajiye masa katin ya juya. Dauka yayi ya duba a tsorace ya mike yana fadin
“What Halima da Sadiya?”
Kai ya gyada masa. Da sauri ya sha gabam sa yace
“Wallahi baka isa ka auri wacce nake so ba.”
“Ai sai ka hana.”
Ya juya ya fita. Katin Isma’il ya dinga kalla ya kasa gaskata abinda ya ke gani wai Kabir zai auri Halima da Sadiya ya akai haka?
Kabir na barin nan ya wuce gida. Hajiyar sa ya samu a falo ya shiga ya zauna tace
“Kabir ina abokin ka ne?”
“Wa fa?”
“Wanne abokin kake dashi sama da Isma’il!”
“Aiki ne yai masa yawa amman zaki ganshi.”
Bai rufe baki ba suka jiyo sallamar Isma’il. Kabir yace
“Hajiya kinga dan halak ko?”
“Lallai kam barka da zuwa Isma’il ina ka shiga ne haka?”
Kai yayi kasa dashi ya zauna yana gaishe da Hajiyar Kabir
Bayan sun gaisa tace
“Ai yanzu nake maganar ka nake cewa  me ya hada ku?  Ana ta shirye shirye biki babu kai.”
Kai ya shafa yace
“Wallahi fa Hajiya aiki ne yai yawa ban fiya zama ba.”
“To ai dai ka zauna a yi bikin da kai ko?”
“Insha Allahu. Amman Hajiya har mata biyu a lokaci daya!”
Mikewa Kabir yayi yace
“In ka gama gulmar ka taho.”
Ya fice. Hajiya tayi dariya tace
“Hmm to ya za ayi? Yace min  dayar sun dade dan ita kan na san da sun dade har dubata mun taba zuwa yi asibiti dayar yace min ko me? To ni me zance in ba addu’a ba.”
“To Allah sanya alheri bari naje me ake shirya mana.”
“To shikenan!”
“Sai anjima dan daga can zan wuce.”
“Allah kiyayr hanya to.”
Ya fita. Dakin Kabir ya shiga ya same shi zaune.
Dagowa yayi yace
“Ya dai?”
“Kabir kayi gangancin auren wacce nake so!”
“Hmmm wacce ka yaudara fa?”
“Wannan ina ruwa na na riga na same ta kafin ka na riga ka sanin wacece ita menene bansani ba ajikin ta, nasan komai nata in and out …..”
Baki Kabir ya cije dan takaicin abinda Isam’il ya fada. Sai kuma ya saki murmushi yana fadin
“Abinda baka sani ba san danakewa Halima ya wuce tunaninka, san Allah da Annabi nake mata ,I don’t care weather she’s a virgin or not, ko shekara dubu kayi kana sex da ita ko ajikina, domin badan jikinta nake santa, in baka sani ba gwara kasani, i love her for godsake and ba abinda zai taba sawa na ki ta.”
Isma’il sakin baki yayi yana kallon Kabir. Kabir yai murmushi yadafa kafadar Isma’il yace
“Kaga ni da ita mutu ka rana.”
“Kabir ka hakura da Halima kawai. Ba tsarar ka bace.”
“Kai tsarar ka ce ko?”
“No nima dan akwai abinda nake bujata a wajen ta ne.”
Murmushi Kabir yayi yace
“Halima ta kenan. Halima tafi mata duba kai kan ka kasan Halima ta gama haduwa matsara daya gidan da ta tashi shima tasu kalar kaddarar ne. Yarinya kyakyawa bafulatana ga diri gata mai hakuri ga ilimin addini. Kada ka manta kai ka cuce ta ka lalata mata rayuwa kuma ka guje ta shine nima kake so kace kar na aure ta. To xan fada maka wallahi ko bazan having sex with Halima ba zan zauna da ita har karshen rayuwa ta dan haka ka kula.”
Wata dariya Isma’il yayi yace
“Ai ita ba zata iya ba ta saba dani ta saba da salo na ta saba da yadda nake kiritata. Wallahi kk ka aure ta bazaka samu kwanciyyar hankali ba domin Halima ni kadai take so ba wanda zai shiha zuciyar ta.”
STORY CONTINUES BELOW
Wani murmushi Kabir yayi yace
“Ko to a dane wannan a yanzu itama tayi hankali. Kana ta mamagar nan ne dan na hakura da Halima ko? To ka sani kome zaka ce kace amman ,inkaga na hakura da Halima mutuwa nayi,  ko na.mutu amman ko ita dakanta ba zata sa na hakura da ita, domin nasan zan kula da ita ko da bata sona kuma a sannu zan koya mata so na.”
Murmushi Isma’il yayi, yace
“Toh shikenan abokina I wish you best of luck amma inaso kasani, Halima har ta mutu nasan bazata taba mantani ba, kuma nasan son da tayimin bazata ta taba maka rabinsa ba, gangar jikinta ka aura, kuma na mata training din da har abada koma waye zai kusanceta wlh sai ta tuna ni,”
“So what!”
“Hmmm ko? To Sadiya kuma ba zaka taba samuna kwanciyyar hankali da ita ba. Sai na zama barazana ga rayuwar ku.”
“Allah ya fiku!”
Yai murmushi yace
“Ko?”
Ya juya ya fice. Komawa Kabir yayi ya zauna zuciyar sa na masa zafi da kuna.
*
Cikin hukunci Allah lokacin biki yayi. Kan lokacin sai da Muhammad yasa aka yi kwaskwarimar gidan akai fenti komai na bikin nan ya tanade. Gidajen amare an tsara shi dan Yaa Muhammad yaiwa kowa two bedroom da two parlou sai kuma dining da restingroom. Hatta kayan kitchen shi yayi bai bar Fauziyya tayi komai ba haka Baba bai taba tambaya ya ake ciki ba. Duk sunyi kafi gidajen ango da amarya yayi kyau dashi. Dan har surukan Fauziyya sai da suka zo.
Kamu akayi da yini kawai. Wanda aka kama waje akayi shima ba maza mata ne kawai aka ci aka sha aka tashi daga taro lafiya.
Washe gari Juma’a aka daura auren su,  su hudu. Inda ya sami hallatar manyan mutane masu mulki dan har mahaifin Muhammad sai da yazo sai a ranar Baba yasan wa Fauziyya take aura yayi mamaki. Haka da yava surukansa ma ba karamin mamaki yai ma dukkan su babu talaka kowa yana da rufin asirin sa.
Daga nan kowa da abokan sa suka tafi akai reception bayan nan ne suka je gida aka sha hutuna. Da yamma akai walima wacce akai lacca mai tsuma zuciya.
Isma’il kuwa aranar daurin aure kulle kansa yayi yarasa mai ke mishi dadi, dan yaga wasa wasa Halima ta mishi nisa, mikewa yayi ya bude wardrobe ya dauki wasu kayan da ta taba mantawa data zo nan take ya tuna moment din da sukayi spending ranar ,bakaramin soyewa sukayi ba ranar ji yayi wani bakin ciki ya lullubeshi, sha,awar Halima ta kamashi ahaka ya kwantar yayi ta tunanin Halima dan yasan da kyar zai samu wata mace tamkar Halima. Halima tayi a rayuwa.
*
Halima kuwa duk ta shiga rudu bata san waye angon ta ba tsoro ta daya tayaya zata gamu da angon ta da wanne ido zata kalle shi. Da ka ganta zaka gane tana cike da damuwa sai da Hafsa har tafi ta rashin kwanciyyar hankali.
Yaya Fauziyya na lura dasu dan haka ana tashi daga walima sukai dakin Mama. Ba kowa aciki dan kulle shi sukai kayan amare  ne a ciki.
Zama tayi kannen nata suka zauna gaba dayan su Hajara,  Halima sai Hafsa da Sakina. Fauziyya ta kalle su tace
“Ina so ui bude kunnuwanki ku saurareni da kyau kuji abnda zan fada muku, yau nakeda lokacin dazan baku shawara dan ta iyayen mu ba zasu baku shawara ko wayar da kanku ba. A yau an daura auren ku buri na ya cika zan kai ku dakin ku. Kar kuji kunyata dan ni yayar kuce na san kuma  halin da kuke ciki ,bawanda yasani inaga da gamu sai mu. kaddara ta afka mana dukkan mu mun rasa  Abu mai mutukar girma da daraja, wato “budurci” nafiku jin ciwon abinda yafaru dan nasan mahimmacinsa agurin da namiji, amma amatsayina na yayar ku nayi Iya kokarina dan nadawo muku da martabarku. ta hanyar gyaraki ,amma inaso kuaan wani Abu,  gyaran damuka mukui bashi yake nufin mundawo muku da budurcinku ba, budurci daya ne inka rasa ka rasa shi kenan har abada, mundai Iya kokarinmu, kuma insha allahu bazaku fuskanci matsala agidan mijinku ba Indai kuka rike abubuwan dazan fada muku yanzu kuna jina?”
Kai suka gyada mata tace
“Shawarar dazan baku nafarko shine ku dogara ga Allah acikin al amuranku,  nasan halinku sosai ta bangaren addini bani da Matsala daku, amma ku kara dagewa, duk halin dazaku tsinci kanku, ku kai kukanku gurin mai kowa mai komai.
Na biyu ku riki hakuri da juriya, abinda yasa nace haka, shine, kowace mace da kika gani agidan miji hakuri takeyi, dan kowacce da irin abinda take fuskanta, kuma dole ma Allah ya jarrabcemu, dan abunda zakayi kasamu aljanarka, bada sauki ake samunsa ba sai ka dage, amma ku bayan wanan hakurin danake fada muku sai kun jure abubuwa da dama dalili kuww shine, kunga a cikin ku, ku kunada kishiya, kuma yara ne, kinga dole ita da budurcinta ta kai gidan mijinta matsayinku da nata ba daya bane, haka ma agurin mijinku, dole ma tafiki matsayi agurinsa, dan kyautar da zakayiwa mijinka arayuwa yaji duk duniya bazai Iya mantaki ba shine budurci, kunga kun rasa naku, saboda haka inaso kuyi hakuri ku kuma jure duk abinda zaki gani, amma insha Allahu na muku alkawarin da sannu zaku zama mowa  agidan mijinku dan ba asan raina zaku auru mai mata ba, dan naso yanda na auri miji saurayi kuma duk ku auri miji saurayi. Bama ke Halima da ayau za a kai masa mata har biyu dakin sa. Amma duk da haka ba matsala zan baku sirrinkan dazaku zama mowa awajen mijinku. Bangaren tsafta bani da matala daku. Domin a rayuwa indai mace mada tsafta duk muninta baza agani ba saboda kullum cikin ado take da kwalliya, kungane mai nake nufi abinda yayi daga  tsaftar jikinki na muhallinki ke da sauransu. “
Mikewa tayi ta dauko jakar ta ta zaro wata leda. Ta bude wasu kwalabe ne a ciki a kulle a leda kala kala kowacce leda guda hudu ne a ciki.  Mika musu tayi tace
“Kowa ya dauki daya. Mai ne da zaku ringa shafawa a kasan ku in kun gwada kwa ban labari. Ba abin wasa bane dan kuna ganun wannan yar kwalbar duk daya dubu goma ce.”
Ta mika musu dauan kullin tace
“Wannan wani hadin turare ne ko ya kika dangwala zai kama jikin ku yana tada sha’awa. Kusan ai kamshi wani sirri ne dan haka kada ku soma sake dashi ku kasance ko da yaushe cikin sa kala kala nai dadi da kwantar da hankali. akwai turaruka na musamman danasa aka kawo muku.”
Ta mika musu ta kalli Hafsa da Halina tace
“Kada ku sake ku yarda abokiyar zaman ku taji kanku da mijin ku. Haka tayi ta gaya musu  sirrika, nasu girman gaske.
Tana gamawa Halima ta fashe da kuka. Ta karasa wajen ta tana fadin
” menene na kukan Halima?”
“Dole nai kuka yaya ban san me zanje na tarar ba!”
“Insha Allahu Alheri zaki tarar “
“Yaya ban san fa mijin ba haka ake aure?”
“A da ai duk haka ake aure yanzu ne ya canja kuma ina mai fada miki in kika dauki shawara ta zaki farin ciki kuma zaki zauna lafiya ni na fada miki!”
“Yaya wa kuka tusawa ni?”
“Ba tusa ki mukai ba shi yace yana son ki!”
“Tayaya yake so na bayan mu biyu zai hada mu a rana daya.”
“Hmmm Halima ki yadda dani yana son ki kuma.yafi sonki waka a bakin me.ita tafi dadi zai rera miki ita kuma zaki fahimta yanzu ki tashi kije kiyi wanka kinji.”
Ta mike ta shiga tayo wanka. Hafsa ta zuba tagumi Fauziyya ta karasa tace
“Ke kuma  lafiya?”
“Tsoro nake ji!”
“Tsoron me?”
“Bansan yadda Ahmad zai amshe ni ba.”
“Kamar ya a yasan komai ba.”
Gaban ta ne ya fadi ta danne tace
“Eh amman….”
“Haba Hafsa kada ki damu nothing bad will happen kinji?”
Kai ta gyada tace
“Je kiyi wanka yanzu kuyi sallah kan azo tafiya daku.”
Ta mike itama ta bar wajen. Hajara ce ta rage a dakin kwance akan gado tai shiru. Yaya Fauziyya ta karasa tace
“Kanwata menene?”
“Yaya tsoro nakeji ance abin da zafi fa.”
“Haba dai ba wani zafi ba duk baki ga a haka muka saba ba bama ke da zaki kai budurcin ki zaki ji dadi wanjen Sani ki masa shagwaba kinji ba wani abun tsoro tubda duk kowa da haka ya saba ko kin taba jin wanda ya mutu akan abin?”
“A’ah!”
“Yauwah ki kwantar da hankalin ki kinji. Ba wani ciwo fa.”
Kai ta gyada tace
“Shiga kiyi wanka anan sai na fito miki da kayan.
Duk Yaya Fauziyya ce ta shirya su ta turare su sannan sukai sallah a daki  mota Muhammad ta sa aka kai mata kayan su dukka. Nan suka je sukai sallama da Umma ta saka musu albarka. Sannan ta kai su wajen Baba maimakon yai fada sai cewa yayi
” kun auri masu kudi dan haka ku zauna lafiya bana son yaji dan wallahi duk wacce auren ta ya mutu ba a gida na ba. Allah kiyaye.”
Wannan abun shi ya saka su kuka dukkan su. Halima ta fara kaiwa dakin ta dan daman tin yamma aka kai masu ganin gida. Dan haka ita ce kawai ta rakasu kuma ita ce uwar dan ita aka fara daurawa aure kuma ita aka fara kawo wa. Dan haka ita kadai ta baro a bangaren ta gidan shiru.
Daga ita suka kai Hajara wanda ita kan su taho abokan ango ma har sun kusa gidan dan haka suka tafi tana kara kwantar wa da Hajara hankali.
Daga ita sai Hafsa dan Sakina ita ta zama babbar ta raka kannen ta. Hafsa tibda ta shiga gaban ta yake faduwa addu’a kawai take yi. Daga nan gidan Sakina suka nufa dan basu bar gidan ba sai da Ango Khaleel yazo sai rawar kafa yake yi. Nan sukai mishi fatan alheri suka taho.Tana zaune taji sallamar angwaye gaban ta ne ya tsanan ta faduwa tana ji suka shigo suka zauna a falo. Sani ya taho dakin da take ciki ya bugo ji tayi kamar zuciyar ta zata fadi kasa dan tsoro. Yai sallama ta amsa murya na rawa tin daga nan ya gane a tsorace ta dan haka sai ya fara boye zalamar sa a fili ya mai da ta a boye. Ya karaso ya durkusa yana fadin
“Amarya ta kin iso lafiya?”
“Ina yini?”
“Lafiya lou kin iso lafiya?”
“Alhamdulillah!”
Ta bashi amsa. Hannu yasa ya dage abinda ta rufe fuska dashi ya sakar mata murmushi ya mike tare da kamo hannu ta ya mikar sai ya rumgume ta.
Mutsu mustu ta fara alamar bata saba ba zuciyar ta kuwa sai bugawa take shi kuwa har ya fada cikin wani yanayi da kyar ya zare ta a jikin sa yana fadin
“Finally dai you are now Mrs Sani and you are my halak my properties. Allah yadda muka tsare kan mu Allah ka bamu zaman lafiya da zuri’a mai albarka. Allah ka tsare mana zuriar mu. Allah ka bani ikon rike matata da amana Amin.”
Ya kamo hannun ta yace
“Muje mu sallami su Bashi ko?”
Suka fita ta zame hannun ta a kasa ta zauna ta gaisa da su suka amsa suna mata Allah sanya alheri anan sukai musu nasiha sannana akai addu’a suka ajiye musu kayan da suka kawo suka musu sallama. shine ya mike ya raka su ya rufe kofar ciki.
A inda take anan ya same ta ya karasa yace
“To ai sun tafi ko?”
Ya bude fuskar ta. Ledar da suka shigo da ita ya bude ya dauko naman da suka shiga dashi da lemo. Ya dauko cinyar kaza da kyar ta amsa tayi ci biyu tayi tace ta koshi. Dan haka yace
“Kije kiyi alwala bari nazo muyi sallah.”
Ya tattara kayan ya kai kichen yasa wasu a firij wasu kima ya ajiye. A bakin gado ya same ta tayi alwala. Ciki ya shiga yai alwala ya fito ya jasu sallah bayan sun idar ya mausu addu’a sannan yai mata tambayoyi akan addini duk ta amsa masa daga nan yace
“Tashi ki rage kayan ko?”
Kafada ta make yai murmushi ya fita ta mike ta haye gado ta kudindune da mayafin ta. Yana dawowa da shirib bacci ya kashe fitila ya hau gadon yana fadin
“Hira zamuyk fa ba bacci Honey!”
Ya mikar da ita nan ya fara bata labarai tin tana dar dar dashi har ga sake tana ta dariya wanda ya samu ta shige jikin sa hannun ta cikin nasa ta haka ya fara aika mata da sakon sa. Wanda kan kace me Hajara jiki yai sanyi domin kuwa bata saba jin irin wannan abubuwan ba.
Lokacin da ya fara kissing nata kuwa sai da nunfashin ta ya dauke na wicin gadi hankalin ta ya gushe dan ba tace ga abinda ke faruwa ba. Da haka yai mata wayo ya zuge zip din riga da siket din ta bata tashi aure ba sai ji tayi yana sucking boost din ta abinda ya sa taji wani iri nan ya cigaba da romancing nata a haka ya ya shige ta.
Ba karamar wahala ta sha a wajen sani ba domin sai da ya maida ta cikakkiyar mace sannan ya sarara mata. Yana sa mata albarka. A daren ya gyara ta ya canja zanin gado ya dawo ya kwantar da ita shima ya gyara jikin sa yazo ya rumgume ta a jikin ta yana jin wani son ta da kaunar ta na kara mamaye zuciyar sa.
STORY CONTINUES BELOW
Da asuba shi ya taimaka ta kara gasa jikin ta sannan tayi alwala tazo ya jasu sallah. Da safe kuwa shi yayi komai na gidan bayan ya gama.wajen tara yazo ya tashe ta ya kai ta bandaki da niyyar mata wanka amman tace ita kunya take ji ya barta. Haka ya fita tai wanka ta fito ta shirya tsaf da ita tai kwalliya. Kofar dakin taji an budo da sauri ta juya wa kofa baya. Ya tsaya kallon ta ta baya yadda tai kyau ya karaso a hankali ya tsaya ta bayan ta tare da daura hannun sa akan kugun ta.
Wani shock sukaji duk su biyun ta zame zatayi kasa ya riko ta yace
“Menene?”
“Uhmm ban gaisheka ba”
Juyo da ita yayi ya zauna akan stool ya daura ta akan cinyar ta yace
“Uhmm morning honey !”
“morning too ka tashi lafiya?”
“Alhamdulillah ban taba tashi da farin ciki da kuzari irin yau ba. Allah miki albarka Hajara.”
Kunya ya bata ta rufe fuskar ta da hannu tace
“Amin!”
Hannu ya zura a aljihu ya dauko wani dan box na sarkar gold ya kamo hannun ta ya daura a ciki yace
“Ga wannan ba yawa tukwici ne nagode da kyautar da akai min kuma na yaba.”
Ido ya bude ta kalli box din sai ta saka dayan hannun ta bude ido ta zaro ta dago ta kalli Sani tace
“Nagode sosai Mijina Allah kara budi ya tsare min kai.”
“Amin Honey!”
Ya dauki sakar ya cire maga wacce ta saka ya saka mata ita yace
“Kinga yadda tai kyau “
Ya kai ta gaban mirrow ya tsayar da ita. Kalla tayi ta shafa tace
“Thank you!”
“You are welcome!”
Ya saka aga dan kunnen da zoben sannan ya kamo hannun ta yace
“Muje kici abinci ko?”
Sukai falo shi ya dinga bata tana sunne kai kuma yaki ya kyale ta. Haka ya dinga dura mata abincin har tace zatai amai sannan ya kyale ta.
Nan suka koma falo suka zauna yana mata hirat soyayya wanda ya ke kashe mata zuciya da salon sa.
*Ni dai nace to Hajara Allah bada zaman lafiya*
*
**
***
****
*****
******
*******
********
*********
**********
************
Daga gidan su Sakina. Muhammad ya kalle ta yace
“Yau muma sabon amarci zamu karaci dan sun tunon da tawa ranar.”
“Kai dai baka gajiya da tsokana ni da na tsufa.”
“Wa ya fada miki tab ai wallahi bakya tsufa yadda kike haka kike sai ma wani dada dadi da kike.”
Tai murnushi yai bakin a bakin wani waje da ake sai da fruit da naman gashi kala kala. Yace
“Ina zuwa madam!”
Bai jima ba ya dawo mota yace
“Sannu!”
Ya kamo hannun ta. Tai masa murmushi. Ma’aikacin wajen ne ya karaso da leda ya bude masa baya ya zuba sannan yai masa isani suka tada motar sukai gida. Tin daga compound ya dauke ta sukai ciki sai akan gado ya dire ta yace
“Kin kara nauyi amman fa.”
“Babyn ka ne!”
“Ba ruwan Baby kawai dai.”
“Kai Baby wallahi ko zirga zirgar bikin nan ma sai ta saka na rame. Ni da ka barni na dada kwana biyu a gida na huta.”
“Ba inda zaki huta kamar nan Baby. Bazan iya barin ki kwana a can ba wallahi.”
Ya mike yace
“Ina zuwa.”
Ya koma mota ya dauko kayan da ya shigo dasu. Kwance ya same ta akan gado ta zame rigar ta daga ita sai red pant nd Bra. Ajiye kayan hannun sa yayi ya karasa kan gadon yana fadin
“Nai miki tausa ko?”
“Da kasamu lada kuwa!”
Nan ya farai mata tausa tana mimmike masa daga nan kuma suka hau farantawa juna su sai wajen dayan dare ya kyale ta suka shiga sukai wanka sannan tace
“Nifa yunwa nake ji.”
“Oh kinganki ko bamuyi yadda amare keyi na. Sai muka fara da babban karamin kuma a baya any way zo na baki kinji love!”
Ta zauna ya fara bata tavi ta koshi sannan ta wanke baki ta kwanta a jikin sa take bacci ya dauke shi.
STORY CONTINUES BELOW
Amman me kan safiyya jikin ta yai mugun tsami dan yadxa tasa wahala a bikin da kyar take tashi wanda Muhammad shi yai mata wabka da komai tana kwance sai tausa da yake mata ita kuma sai shagwaba take masa.
Kan rana kuma sai zazzabi wanda sai da ta kai su ga asibiti har da karin ruwa. Basu suka dawo gida ba sai yamma duk hankalin ta na ga kannen ta tana tunanin yaya suke ya komai ya wakana.
*
**
***
****
*****
******
*******
Khaleel na dawowa daga rakasun Yaya  Fauziyya ya koma daki. Rumgume yana saike ajiyar zuciya. Juyo da ita yayi yana fadin
“Finally dai kin zama tawa My love. Alhamdulillah Allah ka bamu zaman lafoya ya kade fitina Amin!”
Ta sakar masa murmushi yaja hancin ta yace
“Amarya ta!”
Kai tayi kasa dashi yace
“Me zamu fara? Muje muyi alwala muyi sallah farko ko?”
Kai ta gyada yace
“Mu godewa Allah da ya cika mana burinmu.”
Suka shiha sukai alwala suka fito sukayi sallah yai musu addu’a ya gabataf da komai na al’ada da sunna. Sanna ya dauko musu naman da suka shigo dashi ya ciyar da matar sa sannan suka gama ya kai ta suka wanke baki.
Da kan sa ya sauya mata kaya sannan suka haye gado bayan ya kashe musu fitila ya jata jiki yace
“Ko wanne ango ba abinda yake son ya kasance kamar irin wannan ranar. Ranar da zai mallaki matar sa ranar da matar sa zaya kasance ni’ima a garesa ta zama halak din sa yai komai da ita hakika nima ina murna domin na jima ina mafarkin ranar nan ashe tana kusa duk lokacin da yaja kamar ba zai zo ba dai gashi ya tabbata yau kin zama matata Mrs Khaleel!”
Hawaye ne ya zubo a fuskar ta  yace
“My first day with my wife will be unforgettable!”
Sheshekar kukan ta yaji yai saurin juyo da ita yana fadin
“Menene My love?”
“Gani nayi ka manta wacce ka aura ne? Ba wani abu da na kawo maka da zakai alfahari dashi a wannan daren ba sai sambatu kake yi akai dan Allah ka yafe min!”.
Ta fada tana hade hannayen ta. Saukar mata dasu yayi yace
“Dan ina murnar daren nan dole ne nace dan wani abu nake murna. Ina murna na  samu cikon buri na kuma ni ko a yaya kike a budurwa na dauke ki. Ki dauna kuka My Love ni na gani nace inaso to menene na tada hankali. Baki min komai ba ina son kiina kaunar ki zan zauna dake ko ayaya kike.”
Jikinsa ta fada ta fashe da kuka nan ya rumgume ta yana lallashin ta daga lallashi suka zarcr romancing juna. Wanda sun sauki tsawon lokaci a wanan halin kan Khaleel ya fara neman hanyar shigar ta. Lokacinda ya shiga da kyar ya samu ya tusa ya ratsa ta cikin jikin ta lokacin da ya saki wani ihun dadi dan ya ji abinda bai taba ji a rayuwar sa. Ya jima a kan ta kan ya matso dan abinda yaji yana taso masa tin daga tafin kafar sa har kansa.
Haka sukai spending wannan daren  da soyayya mai dadi. Da kyar Khaleel ya kyale ta suka suka shiga sukai wanka. Bayan sun fito ya zuba mata ido tana shiryawa juyoqa tayi taga yana kallon ta dan haka tace
“Ya dai?”
“Yar baiwa ta. Tunani nake shin me kika rasa na kasa ganewa anya kuwa My love ni dai zan iya fadawa kowa na same ki a budurwa. Ke to menene na fargaba kinsan me naji a tare dake kuma na kusa zaucewa My love in har haka zan na samu a gunki babu shakka wata rana zan zauce kuma babu shakka na zama rakumi da akalar ki.”
“Kai dai!”
“Ba karya nake ba. Abinda naji baki ba zai kwatanta ko misalta shi ba amman ki sani ke ta daban ce kuma kina da ni’ima wallahi ina tare na manta da komai da kowa.”
Ya rumgune ya yace
“Allah bar min ke.”
Hawaye ya zubo mata tasa hannu ta goge dan bata zata abin zai zo a haka ba. Hakika ta yadda Khalleel masoyun ta ne yana son ta dan Allah ba dan wani abu da take dashi ba. Alhamdulillah. Allah ka bani ikon kila da miji na ta fada ya dauke ta ya daura kan gado ya ja musu bargo suka hau baccin su mai dadi
Washe gari tare suka gyara gidan suka hada breakfast wanka ma tare suka yi suka fito suka shirya suka fita falo dan karya wa shi ya dinga bata a baki itama tana bashi. Haka ranar suka karar da ita da soyayya mai tsawa a rai.
*
**
***
****
*****
Da kyar ya fito a daki ransa a matukar bace yau Kabir ya aure wacce yake so ya aura sannan ya aure masa Babe din sa komai ya cskude masa zuciyar sa kamar ta fashe.
Mota ya shiga kawai yana zaga gari amman hankalin sa a matukar tashe saboda bakin ciki wai yau Kabir zai tara da Halima ko Sadiya. In Halima ce zai dan dani abibda zai kusan haukata in Sadiya ce zai samu abinda bai samu ba.
Yazo wani junction ya daga kai ya hange ta tsaye a bakin titi sanye da hijab har kasa. Murmushi yayi yace
“Nice wannan babyn tayi gwara nima nayi aure ko dan na kuntatawa Kabir.”
Karasawa yayi yai parking sannan ya fito yace
“Yan mata me kike da wannan daren!”
Matsawa tayi ya kara binta yace
“Dan Allah ki saurare ni.”
Dagowa tayi tace
“Au daman kai musulmi ne?”
“Kamar yaya fa?”
“Naga da kazo bakai min sallama ba.”
“Kiyi hakuri naga dare yayi bai kamata a ga yarinya kamar ki a waje bane.”
“Kada ka damu yanzu xan samu abin hawa.”
“Kinga bari nayi miki sallamar shikenan.”
Bata kula shi ba yace
“Assalamu alaikum!”
“Wa’alaikum salam!”
Ta amsa yace
“Yauwah ko xan rage miki hanya?”
“Kai a’ah nagode !”
“Saboda me?”
“A gida in aka ganni za a zane ni.”
“Sai na ajiyr ki daga bayan layin ku amman dare yayi bai kamata na barki anan ba.”
Haka yai ta lallabata har ta yadda ta shiga ta fada masa unguwar su. Tin daga titi ta sa ya sauke ta figa yabi bayan ta sai da suka kusa gida yace
“baki fadan sunan ki ba.”
“Humaira!”
“Ah Aishatul Humaira. Masha Allah to ki bani number wayar ki!”
“Waya? Ni bani da waya.”
“Haba dai kamar ki.”
“Wallahi bani da waya.”
Hannu ya zura a aljihu ya zaro waya ya mika mata yace
“Ki amsa mayi magana ta ciki.”
“Kayi hakuri a gida ba a yadda na rike waya ba.”
“Saboda me?”
“Haka tsarin gidan mu yake.”
“Shikenan.”
suka karaso bakin layin su tace
“To ka juya kada a ganmu tare ai min fada.”
“Dan an gamu tare?”
“Eh mana!”
“Amman saboda me?”
“Ba girma da darajar mace bane a ganta da namiji kayi hakuri dan Allah nagode.”
Tana fada tayi gaba ya tsaya yana kallon ta har ta shiga gidan su. Ya gyada kai yace
“Da rabon nima auri kamila kyakyawa gata yarinya.”
Ya koma wajen motar sa yana fadin
“Tana da tarbiyya daga gani bata san me duniya ke ciki ba ni zan aure ta na koya mata komai Allah kasa Humaira matata ce nima na nunawa Kabir zan auri mace mai tarbiyya ta ilimi yarinya karama ba kamar shi ba. Gata kyakyawa ga sturucture duk da sanye take da hijab amman kirjin ta ya daga kuma hips din ta a cike yake duk ya lura da wadan nan abubuwa.
Hannah kuwa sam taki ta kwantar da hankalin ta Mami sai biye mata take yi. Mahaifiyar Hannah ce taje ta fadawa babar su nan tasa Mami da Hannah suje. Bayan sunje tai musu fada sosai. Sannan ta kalli Hannah tace
“In auren ne bakya so ki dawo gida ai wannan rashi  hankali ne dake kadai zai zauna.ko zaki hana sa auren ne.”
Sai da tayi musu tatas sannan suka nustu amman Hanna sam bata saduda ba.
+
*
Ana kai Hafsa Basma tazo da me makeup nan da nan aka farai mata makeup kan kace me an gama amarya tayi kyau aka bata wasu kaya ta saka. Daga nan Basna ta dauki Hafsa suka tafi wajen Partyn. Tana mota Basma ta fita bata jima ba sai ga Ahmad nan cikin manyan kaya kalar kayan jikin Hafsa ya shiga motar ya dago fuskar ta.
Wani murmushi ya saki yana fadun
“Masha Allah kinyi kyau ma’ul ayn!”
Ta saki murmushi. Ya kamo hannun ta suka fito. Basma tai musu jagora zuwa cikin wajen taron. Manyan yan mata ne da samari haka suka karasa inda aka tanadar musu.
Aka fara gudanar da partyn cikin kwanciyyar hankali aka gudanar da komai har aka gama aka tashi suka fito aka maidasu gida.
Ahmad kuwa bakin sa ya ki rufuwa ya shigo dakin fuskar sa dauke da sallama ko yan rakiya bai nema ya shiga dakin. Hafsa na zaune a kan gado zuciyar ta sai bugawa takr ya shigo dakin.
Kallon ta ya tsaya yi tana rufe cikin mayafi ta. A hankali ya karasa ya durkusa a gaban ta yace
“Amincin Allah ya tabbata a gareki amarya ta.”
A hankali ta amsa ya saka hannu ya bude fuskar ta bai san lokacin da ya zame ya zauna ba. Ya kura mata ido ita kuma tayi kasa da kanta. Mikewa yayi ya dago kan ta sai yaga tana hawaye da sauri yace
“Me ya faru Ma’ul ayn?”
Kai ta hau girgizawa yace
“Fada min menene?”
Hannun sa ta kamo tace
“Ka yafe min Deedat!”
“Baki min komai ba Ma’ul ayn!”
Ya jata jikin sa ya rumgume yana fadin
“Menene?”
Kai ta hau girgizawa tace
“Zan fada maka wani abu amman ban san tayaya zaka amshe shi ba.”
“Baki da matsala komai daga gunki mai kyau ne kuma zan amsa hannu biyu,  amma kinsan me?”
Kai ta girgiza yace
“Ki daina kukan nan yana tadan hankali!”
Kai ta gyada.
Yace
“Kan komai ya kamata mu fara alwala muyi sallah ta godiya ga Allah sai mu zauna ki fadan ko menene ko?”
Kai ta gyada yace
“Muje muyi alwalar to!”
Ta mike ta shiga tayo shima ya shiga yayo alwalar. Yazo ya jasu sallah bayan sun idar yai mata addu’a sannan yai mata tambayoyi akan addini duk ta amsa masa. Murmushi yayi yace
“Alhamdulillah. Yanzu ina zuwa.”
Ya mike ya fita tabi bayan sa da kallo hawaye ne ya zubo mata. Yana fita ya dauko ledar hannun sa wayar sa yaji tana kara alamar shigowar sako. Zaro wayar yayi yana fadin
“Waye a wannan lokacin?”
Ya bude yaga sako ya bude yaga an rubuto
“Kasan wa ka aura kuwa? In kana son karin bayani ka hau whatsapp ka ga wani sako na turo maka.”
Data ya kunna ya bude app din yaga sako ya shigo yana budewa yaga Hafsa kwance a jikin wani namiji daga uta sai inners a jikin ta. Ledar hannun sa ce ta zame ta wadi ya wara ido. Layin ya fara nema ana dagawa aka sheke da dariya aka ce
“Hhhh kai kana ganin ka auri kamila ko? To saura nace. Ba wanda ya isa ya auri Hafsa sama dani. Hafsat tawa ce ni kadai kaji ko dan haka kasan inda dare yai maka.”
STORY CONTINUES BELOW
Ya kashe wayar. Ahmad bin wayar yayi da kallo kirjin sa na bugawa. Yafi minti goma tsaye ya rasa me yake faruwa. Idon sa ya ka yai jajir dan kishi. Saita kansa yayi ya shiga dakin.
A inda ya barta anan ya same ta a zaune ta hade kai da gwiwa. Tana jin ya zauna ta dago. sai da ta tsorata da ganin yanayin sa. Ta ja baya tana fadin
“Me ya faru?”
“Zan miki tambaya ki fada min gaskiya Hafsat!”
Gaban ta ne ya fadi dan ta manta yaushe rabon da Ahmad ya kira ta da sunan ta. Yace
“Wacece ke?”
Ido ta xaro sai kuma hawaye ya balle a idon ta yana zuba.
“Tambayar ki nake! Me ya faru dake a baya?”
“Deedat abinda nake so na fada maka kenan.”
“Kenan da gaske ke karuwa ce?”
Kai ta hau girgizawa hawaye na zuba a idon ta tace
“A’ah Deedat ba haka bane ka tsaya nai maka bayani.”
Wani kallo ya jefa mata wanda yasa tai saurin dafe bakin ta da hannun ta. Yace
“Da gaske nace miki? Kin taba bin maza?”
Kai tayi kasa dashi hawaye na zubo mata.
“Tambayar ki nake!”
Ya fada cikin tsawa wanda yasa ta dago a tsorace tana gyada masa kai.
Janyo ta yayi ya rike mata hannu yace
“Shine kika yaudaren ko kika ki,  fada min ko? Dan me kika yaudaren? Dan me kika auren to?”
“Please Deedat ka tsaya nai maka bayani!”
“Keep quite!”
Ya fada da karfi ya mike a fusace yana fadin
“Allah ya gani dan Allah nake son ki amman kin yaudaren…..”
Bai karasa magana ba ya juya ya fice. Falo ya koma ya dafe kai. Zuciya sa kamar zata fito. Wata zuciyar tace masa
“dan me kake son ta ne shin daman budurcin ta kake wa kome?”
Kai ya girgiza yace
“Ba haka bane bansa a wane mataki take ba shin ta tuba ne ko kuwa abinda ya batan rai kenan.”
Dayar zuciyar tace
“Kai dai ka tsaya ka saurare ta mana.”
Kai ya girgixa tana fadin
“Ba zan iya ba. Ace wacce nake so da kauna ta min karya ta boyen abu mai mahimmanci dan me bata fada min ba tana zaton zan ki amsar ta ne ni ita nake so amman dan me Hafsa ta bata rayuwar ta.”
Sai ga Ahmad yana kuka. Yana fadin
“Hafsa kin bata wayon ki gaki yarinya kyakyawa amman kin bata kyan ki. Har wani yana min tinkaho da yana son ki yafi son ki. Sai na sake ki. Akan me akan me kikai min haka Hafsat!”
Washe gari da asuba yai wanka ya fice ko da yai sallah bai koma gida ba sai da gari yai sha sannan ya tafi gidan su. dakin sa na da ya shiga ya kwanta yai baccin sa. Sai wajen goma ya tashi ya shiga cikin gida.
Da Basma ya fara karo tace
“Ango Ango ina Antyn tawa?”
“Tana gida me kika dafa ne?”
“Kana bukata ne?”
“Yes zan tafi dashi.”
Shiga tayi ta hafo masa ta bashi ya fita ya saka a mota ya tafa motar ya tafi gida.
Ko runtsawa bata samu tayi ba yadda taga rana haka ta ga dare ga kuka idon ta yai luhu luhu. Da tai sallah asuba ma akan sallaya ta zauna sai da taga gari yai haske sannan ta tashi ta gyara dakin ga. Falo ta fita amman taga ba kowa. Gyara dakin taui sannan ya koma tai wanka ta shirga batai wata kwalliya ba ta xauna a gefen gado.
Yana shigowa ya shiga kitchen ya dauki tea ya hada ya sha sannan ya dibi doya yaci sauran ya dauki basket ya kai mata daki yana shiga ta mike amman bai tsaya kallon ta ba ya wuce ya bar dakin. Ta koma ta zauna tana dafe kan ta
*
**
***
****
*****
******
Isma’il kuwa a washe gari ya koma gidan su Humaira yasa akai masa sallama da uta amman sai yayan ta ya fito. Nan suka gaisa yace
“Me ya kawo ka wajen ta?”
“Son ta nake kima da aure!”
“Madallah in har son ta kake ka aiko magabatan ka su fara magana dan sai anyi magana ma xan baku damar tsayawa da ita kuma lokaci kalilan xan baku in kun ji kuna son junan ku xaku iya rayuwa da juna a yi aure a gama bana son doguwar hirar nan.”
STORY CONTINUES BELOW
“Haka ne Yaya abin yai kyau kuma daman nima a shirye nake insha Allah za a turo din.
Ya tafi. Nan yaje ya samu uncles din sa yai musu bayani ba bata lokaci sukaje sannan yayan ta yace ya badu dama ya zo zance kuma ya basu iya sati biyu a yin zance. Dan Haka Isma’il yai ta murna ya samu yar gidan girma da mutunci shima zai alfahari da matar sa.
Ranar da zai fara zuwa zance zo kuga zumudi wajen Isma’il dan ji yake kamar ranar za a daura auren sa. Yai wanka yai kyau ya saka manyan kaya ya fito a mutumin kirki. Gidan su Humaira ya nufa. parking yayi ya fito ya tsaya kofar gidan su Humaira. Wani yaro yagani zai wuce ya kira sa yace
“Dan Allah shiga nan gidan kace a ana kiran Humaira inji Isnam’il.”
Yaron ya shiga bai jima ha ya dawo yace
“wai tace tana zuwa.”
Alkur’anin hannun ta ta ajiye ta bymike ta saka hijabnta har kasa taje ta fadawa Babar ta sannan ta fita, a bakin kofa ta tsaya tana kallon sa. Ganin ta fito ne yasa yakarasa inda take, sallama ya mata, ta amsa, yace
“Ranki ya Dade nasan Yaya yai miki bayani na ko?”
“Ya min amman yace na tsaya na duba ka sosai in ka min to ba wai yi na suffa ba na addini da zamantakewa kuma.”
Wani farinciki ne ya rufeshi dan irin matar dayake so ya samu kenan. Ya samu yarinya yar mutunci wacce daga babban gida.
“A gaskiya tinda na ganki naji kin kwantain kuma na samu irin matar dana dade ina nema, dan gaskia Humaira gaskia ba wasa ne yakawoni ba aurenki nakesan yi, dafatan zan samu karbuwa?”
Kai ta sun kuyar. Yace
“Baki ce komai ba?”
Fuska ta rufe yai murmushi yace
“Yayan ki yace minti talatin ya bani a kullum zuwa sati biyu. Zan tafi amman yau adaure a ban number waya.”
“Nace maka bani da waya!”
“Wai da gaske?”
“Eh a gida ba a bari mu rike waya.”
“Ai hakan yana da kyau. Domin tana lalata yan mata a *wannan rayuwar* ta yanzu.”
“Haka ne.”
Shi kuwa wani dadi ne ya kuma lullubeshi yana tunanin yasamu yarinya mai tarbiyan gaske,
“Toh yanxu ya za’ayi kenan?”
“Sai ka dawo kenan?”
“Eh nagode.”
Yasa hannu a aljihu ya zaro kudi masu waya ya mika mata. Kai ta girgiza tace
“Nagode amman ba zan amsa ba.”
“Saboda me?”
“Kawai.”
Yayi yayi ta amsa amman taki haka ya hakura sukal sallama ta koma cikin gida yabi bayan ta da kallo yana ayyana abubuwa aransa, yajuya yakoma gurin motarsa ya tafi.
*
**
***
****
*****
******
Ummu da Muhammad satin su daya a Abuja suka daga yawon amarcin su. Sosai suka sha soyayyar su ta samu kulawa a wajen Muhammad sosai dan sai abinda take so. Itama.ta zage tana kyautata masa da nuna masa soyayya take har mamakin Ummu yake dan tana da wayewar da Rukayya bata dashi tafi Rukayya abubuwa da yawa da yawa.
Sosai yake jin dadin xama da ita domin Ummu akwai hakuri da ladabi shiyasa kull cikin saka mata albarka yake da addu’ar gamawa da dubiya lafiya. A tafiyar ta su ya gano tana da ciki zo kuga murna sai kace bai taa haihuwa ba.
Sai da suka biya sukai umrah sannan suka koma Abuja lokacin har su Jannah sun koma dam hutunsu ya kare. Daga ita har Muhammad sun canja daga fatar sunyi kyau sun yi haske. Kwanan su biyu suka daga suka koma gida a haka sukacigaba da zaman su lpy.
*
**
***
****
A can gida kuwa Baba yana ganin ya kawar da su Hafsa ya fara matawa Rukaiyya akan tai magana a gida zai aiko. Haka taje ta samu Abba tace masa me son ta zai turo.
Abbah yace
“Allah ya kaimu yazo duk lokacin da ya shirya. Bayan kwana biyu Alhaji Kamis yaje wajen Abbah bayan gaisuwa suka nuna sun zo neman auren yar ba.
Abbah yace
” to xai basu yarinya amman sai anyi bincike.”
Haka suka tafi yace
“Duk abinda ake ciki zai aiko musu.”
Bayan kwana biyu ya gama bincike ya aika aka kira masa Rukayya. Bayan ta zo ta zauna yace
“Rukayya nayi bincike akan wanda kika kawon zaki aura sai dai an fada min bai rike gidan sa.”
“Abba anya kuwa shine!”
“Shine Rukayya domin na yi bincike sosai. Akwai shi da auri saki haka nan wasu matan nasa ma basa nan sun fita nema kuma bai wadata gidan sa daga haka ni ba xan iya bashi auren ki ba ki bashi hakuru.”
Shiru tayi yace
“Shikenan daman tashi kije.”
Ta mike tayi dakin babar ta. Mama na ganin ta tace
“Me ya faru?”
Nan ta fada mata komai. Mama tace
“Kaji Alhaji da ba dan shi ya haife ki ba da nace bakin ciki yakr miki. Yoo bakin ciki mana yaushe dan yaga mutum da rufin asiri yafi mazajen ya’yan sa zai kawoana wannan maganar ke kinason sa?”
“Eh Mama.”
“Tashie muje wajen sa.”
Nan suma mike suka shiga.
Bayan sun zauna ya dube su yace
“Lafiya?”
“Akan Rukayya ne tace ita tana son sa a haka.”
Rukayya ya kalla yace
“Ke wai haka?”
Kai ta gyada yace
“To ni a matsayi na  ba uba nayi bincike na kuma wanda kike so sam bai dace dake ba kuma ina ji ina gani ba xan ba dake gashi ba.”
“Baba sharri akai masa fa ba haka bane baka ga yadda yake kashen kudu ba.,”
“Nu da kai na nayi bincike dan haka ni ba zan aura miki shi ba amman in kinga kina so kije wani ya aura miki shu amman ni ba xan aura miki shi ba a xo ana kuka dani.”
“Baba ba zan kuka da kai ba.”
“A’ah Rukkayya kije ki aure shi ni nawa Allah bada zaman lafiya ne ku tashi kuje.
Suna fita Mama tace
” ki kwantar da hankalin ki ba ya bamu xabi ba xamu kai wani ya daura muku aure yanzu ki mada magana kawai azo a daka rana ayi a gama.”
“Toh Mama.”

A gida Kabir kuwa Sai da aka kai Halima sannan aka kai Sadiya wanda haka ya nuna Halima ce uwar gida. Sai wajen sha daya ya shigo gidan. Daki Sadiya ya fara shiga tana zaune a gefen gado. Ta yaye mayafin tana sakar masa murmushi tare da gaishe sa  ya amsa yana fadin
“Barka da zuwa gida.”+

“Nagode amma bani aka fara kawowa ba.”
Kai ya gyada yace
“Nazo naga lafiyar ki sannan na kawo mili kaza kici ko?”

“Nagode!”
“Kiyi hakuri Sadiya.”

“Haba miji na ba komai Allah bamu zaman lafiya.”
“Amin!”

“Amman kayi kyau angon mu nima ranar da zaka zo min irin wannan shigar nake so.”
“An gama amaryata amman ai kin fini yin kyau.”

“Anya kuwa kagan ka kuwa?”
Yai murmushi yace
“Kada dai ki fasan kai.”

“Ai gaskiya ce.”
“Hmm to nagode.”

Tai murnushi  yace
“Tin da rana daya aka kawo ku,  za a raba kwana zuwa kwana bibbiyu ba sai anyi sati sati ba yayi?”
“Ka je mata da maganar in ta yadda ba matsala.”

“Shikenan sai da safe ko?”
“Allah bamu alheri.”
Ya mike ta taso ta rakashi har ya fita ta maida kofa ta rufe daki ta koma sai taji shaidan na son mata huduba da sauri tayi addu’a ta zauna taci naman ta ta koshi sauran ta saka a firijn sannan ta shiga ta wanke bakin ta tai wanka ta fito ta saka kayan bacci ta kwanta taba addu’a.

Yana shiga bangaren Halima ya rufe kofar. Sannan ya nufi dakin da take. Nan yaga ba kowa. Ajiye ledar hannun sa yayi ya mike ya juya zai fita ta fifo daga bandaki dan ita ta gaji da jira ta zata ma ba zai shigo mata ba tinda ance su biyu ne kila yana wajen dayar. Dan haka sai ta tsaya cak ganin sa a dakin ya juya mata baya  gaban tane ya hau dukan tara tara.

Kallon sa ta tsaya yi. ta zubawa bayansa ido, tundaga kan kwantacen gashinsa har zuwa kafarsa. Bata san lokacin da ta furta
“Woaw ba. Taba fadin shin wannan shine miji na?”

Shima jin bude kofar shi ya tsayar dashi. Jin shiru kuma yasa ya juyo,  toxali yayi da iya tsaye a bakin bandakin tai masa kyau  wani irin murmushi ya sakar mata. Halima ta nuna sa da yatsa tace
“Kabir kaine? Kai ka rako angon nawa to yana ina?”
Bai ce mata komai ba in banda murmushi da yake yi, gaban Halima ne ya dinga bugawa da sauri da sauri sai ta fara leke ta ina zata gano angon nata bayan nan me yasa ya bar Kabir ya shigo har dakin auren su ko dan bata da daraja. Ganin baya gano kowa ba gashi ba mayafi a jikin ta yasa ta juya zata koma bandakin da sauri yace
“Halima.”

Ya kirata da voice dinsa mai dadin sauraro.  Cak ta tsaya tayi saurin juyowa tana kallon sa, yace
“Ba sai kinje ko ina ba. Nine dai mijin ki Kabir da kika sani ninr mijin ki?”

Kai ta hau girgizawa tana fadin
“Joke aside please waye miji na duk sunki su fada min kai nasan zaka fada nin.”
Murmushi yayi daya kara fido da zahirn kyaunsa, ya taka ya je gabanta, hannun ta ya kamo ya shigo da ita dakin ya zaunar akan gado.

“Ki yadda dani Halima kamar yadda kika yadda dani to nine mijin ki. Nine!”
Da sauri ta mike ta fara ja da baya,  hawaye na zubo mata tace
“No is not possible u cant be my husband!”

STORY CONTINUES BELOW

Ta fada da karfi. Kamo ta yayi yace
“Halima ki tsaya ki nutsu muyi magana ta fahimta.”
Kasa magana tayi ta kura masa ido hawaye na cigaba da zubo mata.

Zaunar da ita yayi ya zauna a kasan center carpet din dake gefen gadon. Yace
“Kada kiyiwa Allah butulci Halima. Ni din dai nine mijin ki ko bam miki bane?”
Shiru tayi ta zuba masa ido tana kallom sa. Kabir yace
“Halima say something kin zuba min ido kamar yau kika fara ganina,”

Kai ta girgiza tace
“Dole na zuba ma ido dan bangane komai ba ya akai haka ta faru?”
Yai murmushi nan ya fara  bata labarin tun lokacin da yake sonta, da yanda yaso ya kareta daga fadawa sharrin Isma’il ,da yanda ya boye number yake mata text, data rabu da Isma’il kar ta biye masa.

Tinda yafara bata labari take kuka, sai da ya gama tace
“yanzu dama Kai na aura mai yasa ka boyemin? Meyesa tun lokacin baka bayyana min irin San dakake min ba? Ka bari na biyewa Isma’il ya cuce ni?”

“Halima a lokacin ki ringa kinyi nisa asan Isma’il ko na fada miki ina sanki a lokacin bazaki saurareni ba, fada miki a lokacin bashida amfani, karkuma ki manta Isma’il abokina ne aminina, shiyasa kikaga bana son mu’amalar ku.”
“Innalillahi wa inna ilahi rajiun,”
Ta fada tana dafe kai, sai kuma ta fara magana
“Daka bayana min kanka lokacin ka gayamin halin Ismail zan yadda.”

Kai ya girgiza tace
“Bazaki yadda ba.”
“Why?”

“Saboda kinyi nisa zakiga kamar son kune banayi tare. Kin riga kin amshi soyayyar sa da gaske kuma bai nuna miki hali wanda inda zaki gane tin lokacin danake miki text zaki dau hanyar rabuwa da Isma’il amman ina kamar kara shakuwa kuke, shiyasa na hakura na cigaba da rainin soyayyarki araina, ina miki addu’a!”
Kallonsa ta dago tana yi tace
“kuma ahaka zaka aureni bayan kasan komai akaina, kasan abinda na aikata tunda kai ganau ne, ba jiyau ba “

Murmushi yayi, yace
“San da nake miki daga Allah ne badan wani Abu naki ba, wlh ko awane irin hali kike am sorry to say ko gurguncewa kikayi, kika makance, wlh ba abnda zai ragu asan danake miki, tinda Isma’il ya juya miki baya ma naji kamar karamin sanki ake azuciyata, karkiyi doubting din san da nake miki, a baya har addu’a nayi Allah ciren son ki saboda Isma’il yace min zai aure ki amman abun kamar da da min ake walahi ko da ace Isma’il ya aure ki bazan iya cireki ba a zuciya ta kila son ki ya zama ajali na.”

Tunda ya fara magana take kuka, can ta mike tace
“Am sorry Kabir ba zan iya zama da kai ba.”
Bai san lokacin da ya mike ba yace
“Whay?”

Kai ta girgiza tace
“Kayi hakuri amman ba zan iya ba.”
“Saboda me?”

*
**
***
****
*****
Rukayya taje taiwa Yaya Sailuba bayanin komai. Yaya Sailuba tace
“Shi Alhaji Khamis din aka cewa haka?”

“Haka Abbah yace.”
Nan ta dau waya ta kira mai gidan ta take ya dawo ta zayyane masa komai. Yai dariya yace
“Ikon Allah shi da Alhaji Kamis yana da maikiya bari na kira shi sai kuji waka a bakin mai ita amman gaskiya karya akai masa.”

“Ni ai na sani.”
Rukayya ta fada. Nan ya kira sa bai jima.ba yazo. Rukayya ta fadawa Alhaki Kamis duk abinda Abba ya fada. Alhaji Kamins yai murmushi yace
“Wai meyasa nake da abokan adawa ne?”

Mijin Yaya Sailuba yace
“Ahaf kinji ko?”
“Allah kuwa!”

Rukayya tace
“Ai ni na sani nayiwa Abba bayani amman yaki ya fahimta amman kasan me?”
“Sai kin fada.”

“Ya ban dama. naje wani ya dauran aure amman shi ba zai ba.”
“Kai madallah yanzu ya ake ciki kenan.”

“Zai daura mana aure.”
“Shikenan kin hado lefen?”

“Na hado amman ina bukatar kudi.”
“Baki da matsala.”
Nan ya dauki waya yai danne danne sannan ha mika mata wayar yace
“Saka amount.”

Ta amsa tasa ta mika masa. Ya saka pin a take alert ya shiga ba dubu dari biyar data saka. Basu tashi a wajen ba sai da aka saka ranar daurin aure.
*
**
***
****
*****
******
*******
********
Zancen sati biyun sukai Yayan Humaira Ansa yace ya turo. Nan kannen babban suka je akayi komai da komai cikin mutunci da mutuntawa ,suka sa wata daya.

Yayan Humaira hankalin sa ya tashi amman makwabcin su yace zau mata kkayan daki. Sati daya da gama magana aka kawo lefe, i akwatuna set biyu aka  hada aka kai.

Isma’il kuwa yana nan da so da sha,awar Halima dan har kasa bacci yake yi saboda da tunanin ta. Dadin ta ma auren da xai yi dan yana ganin da Zarar yayi aure zai cireta aransa.

Amarya Humaira kuwa sai gyara take sha  daga ta sha wanna sai ta sha wancan sai ta tusa wancan.

*Wacece Humaira?*
Humaira Ahmad suna ta. Itaxe ya ta uku a gun iyayen ta sai yayen ta maza biyu da Anas da Nazir. Sai kannen su biyar. Mahaifib ta ya jima da rasuwa. Daman kuma ba wani kudi ne dashi ba dan rufin asiri ne yake samu suke zaune lafiya da iyalan sa saingashi Allah yai masa rasuwa abinda ya hana ya’yan sa Ansa da Nazir karasa makaranta kenan suka ajiye ta. Haka yayyen ta suke fadi tashi dan ko government school basu saka ta ba dan ita kadai ce mace suna so su inganta rayuwar ta.

Wanda a makaranta sam bata abota da yayan talawa sai masu dashi fitinannu tun basa son mu’amala da ita har suka  fara so dan Humaira a waye take ga kokari da wayo.

Haduwa da kawaye ya’yan masu kudi yasa in ta gansu da abu itama sai ta sama daga haka ta fara kula samari a boye dab gidan su gidan mutunci ne da tarbiyya. Inda basu san halin da take ciki ba. A waje zaga bada jikin ta ayi tsotse tsose in ta siyo abu sai tace wata kawar ta da ita ta saka ta harkar ce ta bata wanda sai Baba ta kira ta tambaya ita kuma tace eh haka ne da haka ta ke shigo da abubuwa gida duk da a ko da yaushe zaka ganta da hijab har kasa amman da ta fita take cire shi wata shigar ba ko kyan gani.

A haka ta fara bin maza,  dan wannan kawar tata ita ta fara hada ta da maza, tun tana ‘dari da’ri har tazo tafara sakin jiki, ai kuwa nan da nan tafara samun kudi, kasancewar ta fara mai diri Alhazawa ne suke rububinta, suna kashe mata kudi aikuwa tasamu abinda takeso dan sutura masu tsada take sawa. Sai Hunaira tayi fice a cikin kawayen ta duk da ya’yan maya.

In kaga Humaira innocent face ce da ita dan bata magana gata a nutse kullum cikin hijab da karatun alkur’ani dan ta sauke abinda take kara siye iyayen ta kenan wani lokacin tace zasu musabakaa ko wani wajen dan makarantar da take zuwa ma ba a unguwar take ba,  ba wanda yasan ta shiyasa take abinda ta ga dama ba wanda ya sani. In ta samu kudi tace kyauta akai mata da yake ta samu wani malamin su shima dan hannu da yake kara saka ta a hanya in abu ya samu har gida yake zuwa yakewa su Baba bayani su kuma su zata da gaske ne dan har tafiya tana yi zuwa wani garin a zuwan daga makaranta nan kuwa yawon ta kawai take zuwa yi.

A yanzu ta gama secondary ibda yayen ta suka ce ta fito da mijin aure in tayi aure ta karasa karatun ta. Abinda ya tada mata da hankali dan ita bata kula masu son ta da aure duk korar su take. Na shashancin ma ba sa zuwa guda sai dai su hadu dan kk waya bata rikewa a cewar ta in kana rike waya kana lalacewa ita kuma bata son iyayen ta su zarge ta shiyasa sam.bata da waya in appointment ne xaku hada in ma kana neman ta zata baka number malamin su wanda shi kuma zai zo har guda da zumar koya mata karatu daga ban ya bata waya suyi da samarin ta.

Wannan yasa har ta bar Isma’il yazo gidan su kuma aka sa ya turo. Ganin da gaske auren zatai yasa ta hau gyaran kan ta a boye.
Wannan kenanTunda ya fara magana take kuka, can ta mike tace

“Am sorry Kabir ba zan iya zama da kai ba.”

Bai san lokacin da ya mike ba yace

“Whay?”

Kai ta girgiza tace

“Kayi hakuri amman ba zan iya ba.”

“Saboda me?”+

“karka manta ka san wacece ni kasan me na aikata. Nasan ba zaka taba manta wacece ni ba kuma a duk lokacin da kace zaka kusance ni zaka tuna wacece ni wannan zai sa ka tsane ni. Tayaya kake son zama dani bayan ban dace da kai ba. Daban kake ba zan lalata maka rayuwa da zuria ba.”

Tana fadar haka ta fashe da fashe wani irin kuka mai cin rai.

“Halima!”

Ya kira sunan ta amman bata amsa ba. Yace

“Halima abinda yafaru dake fa kaddara ne ,kina nufin ke kika tsarawa kanki rayuwa, ni nasan badan Isma’il shu’umi bane Yakuma yi amfani da San dakike masa ba, da ba yadda za ayi yaci galaba akanki, saboda haka karki damu, badan kin tuna min ba ma yanzu namanta da komai a tsakanin ki. Na dauke shi a budurwa ta ne,  burina arayuwa in ganki cikin farinciki da walwala, kuma duk ina wannan abun ne danke.”

“Tayaya tayaya? Ina tantamar wai kana so na. Gani nake kayi haka ne dan kana tausayi na.”

Durkusawa yayi yace

“Wallahi Halima a magana ta babu karya. Wallahi ina son ki “

“Ita kuma amaryar ka fa?”

“Itama ina son ta.”

“Wa ka fara so a cikin mu?”

“Ke!”

“Dan me ka so ta daga baya dan kaga na rasa mutunci na “

“Ki daina fadar haka na fada miki zan iya rayuwa dake a haka ba tare da munyi sex ba ni ba shine a gabana ba na kasance dake shi nafi kauna. Sadiya kuma ganin na rasa ki yasa na fara son tai tama kamar ki take tana da sanyin hali dan haka ki nutsu ina son ki manta da komai,  ki manta da kin taba haduwa da Isma’il, ki bani dama na shiga rayuwarki, kisoni ko yaya ne mu gina rayuwarmu cikin so da kauna please!”

Dagowa tayi tana kallonshi. Ya hade hannaye yace

“Please Baby! kin amince?”

Kai ta gyada masa. Baki ya washe, ya karaso ya rumgume ya a jikin sa wani bakon abu suka ji dashi har ita.

“I love you my love!”

Ya fada yana kissing wuyan ta. wata kunya ce ta kamata ta fara sunne kai. Sakin ta yayi tai saurin juyawa yai murmushi yace

“Oh yau ni ake jin kunya Baby!”

Ta make kafada yace

“Zama ki daina ne. Muje muyi alwala muyi sallah ta godiya ga Allah.”

Ya kamo hannun ta yana shafa cikin ta yace

“Wannan cikin ba abinda yaci.”

Ya kamata sukayo alwala. Wanda suna dawowan sukai sallah ya zauna ya ciyar da ita. Sannan suka haye gado. Ya rufe ta take bacci ya dauke ta. Shima yayi alwala bacci ya dauke sa. Cikin darr ta tashi da wani ciwon kai da zazzabi ga ciwon ciki saboda rashin abincin da bata ci ba na kwana biyu.

Haka tai tayi masa kuka wanda wajen asuba sai da suka je asibiti. Karin ruwa akai mata har asuba bai kare ba. Sai karfe shida ya kare aka kara saka mata wani wannan yasa Kabir ya kura Sadiya ya fada mata suna asibiti. Tace to gata nan.

Kan ta gama shirya musu abinxi ma an sallame su an bata magunguna. Sadiya na kitchen taji dawowar su  kan ta fito har sun shige dan haka ta koma ta karasa komai ta shirya musu tai wanka ta nufi sashen nata.

STORY CONTINUES BELOW

suna dawowa yai mata wanka ya shirya ta yaba shirin fita ya samo musu abin kari Sadiya ta shigo tana sallama ya fito ya amsa yace

“Amarya kin sha kamshi.”

“Kai da Sister ne kuka sha kamshi ya jikin nata?”

“Da sauki!”

Halima da ta jiyo shi yana magana ta mike ta fito tana dafa bango ya karasa ya kamo ta ya zaunar. Sadiya tace

“Sannu Allah kara sauki.”

“Amin kin tashi lafiya.”

“Alhamdulilah ya jiki?”

“Da sauki.”

“Allah kara sauki.”

“Amin….”

Sai ta dafe kai Kabir yace

“Menene sannu!”

Sadiya ta mike tace

“Ga break nan sai anjjma.”

Ta juya ta fita dan taga yadda Kabir yake kamar zai maida Halima cikin sa. Wannan ya nuna mata ya kwana da iya yaji abinda yaji shiyasa ita kuma labgwai kawai.”

Sadiya ta fada. Sai kuma tayi addu’a dan kada shaidan ya rinjaye ta.

Abinci ya bata taci sannan ya bata magani take bacci ya dauke ta ya kai ta daki shima ya kwanta dan jiya bai samu bacci ba sai azahar suka tashi ya tafi masallaci ita kuna tayi anan gida. Kabir na dawowa Sadiya ta kara kawo musu abincin rana duk da Halima tace ta koshi sau da ya bata. Kan dare sai gashi ta watsake dan cikin ya daina ciwo.

Da dare tana kwance ya shigo ya dawo daga yiwa Sadiya sallama  ya zauna yana fadin

“Ya cikin?”

“Naji sauki nagode!”

Gadon ya hau yace

“Menene abin godiya hakki nane.”

“Duk da haka nagode”

Yai murmushi ya janyo ta jikin sa yana fadin

“Ina son ki Halima.”

Ido ta lunshe. Na ya fara bata labarin asalin tin farkon ganun ta da ya kamu da son ta. Yace

“Ashe ke rabo na ce.”

Ya cigaba da fadin

“Duk lokacin da naga kinzo wajen Isma’il ji nake kamar na mutu. Ashe duk kishi ne.”

Haka yai ta bata labarin halin da ya dinga shi da rashin bacci da rashin lafiya duk da yayi akan ta. Ranar kwana hira, yana nuna mata irin  san dayake mata, azuciyarta kuma tana mamakin shi, dan bata taba tunanin yana da baki haka ba dan baya magana. Finally dai yau ta zama matar sa alhamdulillah daman akwai mai son ta haka.

Washe gari da safe ma.Sadiya ce ta hada musu abinci kari da na rana har dare. Sai da ya dawo da magariba ya samu Halima na daki akan sallaya. Shiga yayi ya zauna a gefen ta tace

“Sannu da zuwa!”

“Yauwah uwar gida!”

Tai murnushi yace

“Na manta ban miki wata magana ba “

“Wacce fa?”

“Shekaran jiya da aka kawo ku mun fara da Sadiya akan raba kwana. Ni nace tinda a lokaci daya aka kawo ku ba sai kowa an masa sati daya ba kowa zamu raba kwana bibiyu ita tace sai yadda kika ce.”

“Me yasa ka yanke haka to?”

Yai murmushi yace

“Saboda me kike son jin dalili?”

Baki ta turo tace

“Ni dak fada min.”

Yai murmushi yace

“To saboda in akacesati daya dayan yai yawa kuma zanyi missing Baby nah.”

Ya fada yaba shafa gefen fuskar ta. Ta dage gira tana fadin

“Nima duk yadda ka yanke.”

“Shikenan a barshi kwana biyun kinga yau zan tafi dakin ta kenan ko?”

“Yes Allah ya kiyaye to.”

Ta fada tana jin wani abu a ranta. Hannun ta ya kamo yace

“Baby ki sani ina sonki.”

Murmushi ta saki tai kasa da kanta. Yace

“Oh ni bakya so na ko?”

Kafada ta make yace

“Shikenan Allah nunan ranar da zakice kina so na.”

Tai murmushi tace

“Kaga tashi ka shirya ka tafi gun amaryar ka.”

“Me zan shirya haka ma yayi.”

“A’ah Mijina itama yau amarya take ka sani ko a samar mana Baby yau.”

“Ban sama a wajen ki ba sai ita “

STORY CONTINUES BELOW

“To kasani.”

Ta bude wardrobe ta dauko masa wata sabuwar shadda ta mkka masa ya amsa ya saka ta bade shi da turare. Ta kkma ta zauna tace

“Kayi kyau.”

“Ko?”

“Yes!”

“To kizo ki rakani.”

Shiru tayi sai kuma ta mike ta dauki mayafi ta yafa ta shafa turare ta kara gyara face din ta sai ta kara walwali. Ta fito suka fita

Tana falo suka shiga tana ganin su ta mike tsaye itama taci kwalliyar ta har ta gaji da kyau. Tana ganin Halina tace

“Bismillah!”

Ta shiga ta xauna shima ya zauna a kusa da Halima. Sadiya ta zauna a inda ta tashj.

Na ya musu nasiha sannan ya kara basu hakuri ya kara maganar raba kwana duk suka amsa da insha Allahu ba za ka same mu da karya dokar ka ko yin fada a tsakanin mu ba Allah ya bamu xaman lafiya da xuri’a mai albarka. Sosai yaji dadin kalaman nasu. Nan Halina ta mike tace

“To Amarya ga ango nan ni zan tafi sai da safe.”

Gaba daya suka mike,  suka rako ta bakin kofa Sadiya ta juya daga nan shi kuma ya rakata daki. Suna shiga yace

“To Baby zan tafi ki kular min da kan ki i miss you.”

Kai ta gyada masa ya janyo ta ya rumgume ta lafe a jikin sa ya dago ta ya hade bakin su yana aika mata dawani kiss wanda yasa daga ita har shi jikin su yai sanyi sai da yaji yana neman zubewa ya kamata ya kai ta kan gado ya rumgume ta yana dai dai ta kansa. Sai da ya nutsu ya mike yana kallon ta tayi saurin yin kasa da kai. Yace

“I will miss you take care.”

Ya juya ya fita ta dago ta mike ta rufe kofa. Yaba shiga daki Sadiya ta tare shi da lemo bayan ya sha sannan sukai alwala sukai sallah nan yai mata tanbayoyi sannan ya mike ya saka kayan bacci itama haka. Kan gado suka haye suka kwanta ya janyo ta jikin sa. Take yaji wank abu na yawo a jikin sa. Dan dama.kasancewar sa da Halima dauriyya kawai yayi gashi yanzu yai kissing nata ya kara janyo wa kan sa ruwa.

Duk yadda yake jin matsananciyar sha’awa haka ya daure da kyar bacci ya dauke su. Itama Sadiya tayi mamaki da bai neme ta ba ko da yake tayaya zai neme ta ya samu matar sa Halima. Take taji zuciyar ta ta karye amman sai tayi sauri ta ambato sunan Allah take taji nutsuwa ta nemi abinda taji ta rasa.

Washe gari da asuba ya tashe ta tayi alwala shima yayi ya fita. Bangaren Halima ya karasa ya buga yaji a rufe wannan yasa ya saka key ya bude ya shiga. Kwance ya same ta tana bacci dan bata samu tayi bacci ba a daren jiya tana kuka da kishin Kabir yana can da wata zai same ta a budurwa ita kuma ta rasa nata haka tai ta kuka sai goshin asuba bacci ya dauke ta.

“My love!”

Ya fada yana taba ta da sauri ta mike tana ganin sa ta fada jikin sa sai kuka. Hannu a daura a bayan ta yana fadin

“Menene My life?”

Kai ta hau girgizawa ya dago ta yace

“Fada min mana menene?”

“Kai ta kuma girgizawa ya dago ta yace

” to anyi kiran sallah kiyi alwala kinji bari naje masallaci.”

Sai da ya kai ta har bandakin sannan ya fita alwala ya karayi ya tafi masallaci. Yana dawowa ya wuce bangaren Sadiya. Ya same ta ta koma bacci shima kwanciha yayi ya koma bacci.

Halima kuwa ganin ba baccin zatai ba yasa ta shiga kitchen ta fara hada musu abin kari karfe takwas ta gama ta shiga tai wanka ta fito ta yi turaren jikin ta sannan ta saka wata doguwar riga ta atamfa milk mai adon peach tai mata kyau kirjin ta ya fito dan dinkin me haka ne. ta saka dan kunne da sarka suma peach ta Shafa turare.

Zama tayi a falo har tara sannan ta mike ta karasa bangaren Sadiya. Knocking tayi lokacin suka tashi daga bacci dan ba Kabir yai wanka yazo ya bude yana ganin ta yace

“Morning my Angel!”

“Morning too Ka tashi lafiya ya Sister,?”

“Tana lafiya.”

Basket ta mika masa tace

“Your breakfast!”

Thanks! “

STORY CONTINUES BELOW

Ya dago yana kallon ta,  yace

“Me ya samu idon ki.”

“Nothing bye!”

Ta juya ya bita da kallo yana murmushi. Ciki ya koma ya samu Sadiya ta fito daga wanka tana shiryawa. Bayan ta gama suka fito suka karya.

*

**

***

****

*****

******

*******

********

*********

**********

***********

Hafsat kuwa bata kara ganin Ahmad ba kullum dai sai ya tabbatar bata daki zai ajiye mata abinci ya bar wajen wanda ita kuma ko ta kan abincin bata bi. Ya daina zaman shashen ga gaba daya ya koma nasa ko ta fito bata ganin sa rayuwa tai mata kunci sunyi waya da Yaya Fauziyya tace mata ba matsala dan bata so ta daga mata hankali bama da taji itama bata da lafiya ga ciki.

A haka sukai kwana hudu a haka wanda zuwa Lokacin Hafsa damuwa tai mata yawa ga yunwa dan ko ta dauki abincin zata ci sai ta kasa.

Yau bayan ta shiga tai wanka ta fito ta saka kaya ta mike kenan zata saka turaren wuta wani jiri ya kwashe ta kan ta farka ta kife a wajen. Lokacin Ahmad ya shigo gidan da abincin ranar ta. Kofar bedroom din ta ya karasa ya kasa kunne jin ba motsi yasa ya tura amman abinda ya gani shi ya daga masa hankali da sauri ya saki ledar hannun sa ya karasa cikin dakin yana kwala mata kira.

“Ma’ul ayn! Ma’ul ayn!! Ma’ul Ayn!!! Hafsa Hafsa.”

Amman bata motsa ba mikewa yayi ya shiga toilet ya debo ruwa yazo ya shafa mata amman bata motsa ba. Daukar ta yayi ya fice ya sakata a mota sai asibiti yana zuwa aka amshe ta a emergency  aka shiva da ita.

Bayan awa daya aka fito da ita tana bacci aka kai ta dakin hutawa. Likita ne ya kira sa bayan yaje ya kalle shi yace

“Matar ka ce?”

Kai ya gyada yace

“Ya akai haka? Jinin ta yai mugun hawa wanda in yai sama sosai sai iya rufe kwakwalwar ta daga haka zata iya rasa rayuwar ta sai matsala ta biyu na gane bata cin cikakken abinci dan ba ruwa ma a jikin ta me ya faru haka?”

Kai ya hau shafawa yace

“Ranka ya dade bana garin ne shiyasa.”

“Dan baka garin shine ba zakana kula da ita ba?”

“Ba haka bane.”

“To yanzu dai mun cewa ta da kyar dole sauran kulawar ta zama taka da shan magani.”

“Insha Allahu.”

Ya mike ya koma dakin da take kwance. Bacci take ba ita ta farka ba sai kusan magariba tana mikewa ya karasa wajen ta yana fadin

“Sannu Ma’ul ayn!”

Kallon sa tayi sai ta fashe da kuka tana fadin

“Dan Allah Deedat ka tsaya ka saurare ni wallahi abunda ya faru dani kaddara ce kuma nayi nadama ka yafe min. Abinda nake son na fada maka kenan a lokacin kuma shine nake tsoron na fada maka a ko da yaushe amman dan Allah ka yafen kuma….”

Karasawa yayi wajen ta yana fadin

“Shitty ba komai My Baby kiyi shiru yanzu kina bukatar hutu kinji?”

Kai ta gyada masa ya mike ya fita bai jima ba ya dawo da likita nan ya duba ta sanan ya bada magani a bata acea bata abinci tukkuna. Da kansa ya bata abincin tana ci yana mata sannu taci da yawa bata sani ba dan sai kallon sa take yana bata yana mata murmushi ta gama ya bata magani sannan ya rumgume ta a jikin sa ta kwanta take bacci ya dauke ta.

Kwansu biyu a asibiti yana kulawa da ita sannan aka sallame su suka koma gida. Har daki ya kai ta ya shiga ya hada mata ruwa sannan ya fita. Shiga tayi tai wanka ta fito ta saka kaya ta dawo kan gado ta kwanta.

Kifar dakin ya bude ya shigo tai saurin mikewa ya ce

“Yi zaman ki.”

Ya karasa ya zauna yana fadin

“Ya jikin?”

Hawaye ne ya zubo mata yasa hannu ya goge mata yana fadin

“Haba My Baby nace ki dauna kukan nan ko?”

“Dole nayi kuka My Deedat na cuci kaina!”

“Ya riga ya wuce Baby! Nayi bincike dan har wajen Anty Fauziyya naje bata boyen komai ba kuma ban nuna mata kema kin boyen ba.”

Nan zato waya yace

“Abinda ya ban haushi saboda me baki fada min ba kuma sai wanda ya turon yace ba sona kike ba kin auren ne da wata manufa kuma ba ki barshi ba kamar yadda shima ba zai barki ba haka kuma kina son sa ki fada min tayaya ba zan ji haushi ba. Ba jikin ki nake so ba ke nake so amman ki sani dole nai kishin ki saboda me Baby meyasa meyasa kika biyewa shaidan?”

“Tawa kalar kaddarar kenan da rudin *wannan rayuwar* amman dan Allah Deedat ka yafe min.”

Rumgume ta yayi yace

“Na yafe miki Baby na yafe miki Allah ya yafe mana gaba daya ya shirya al umma musulmai da zuri’ar mu baki daya.”

Jikin sa ta fada ta fashe da kuka nan ya rumgume ta yana lallashin ta daga nan wasan ya sauya salo. Domin kuwa nan kusa hau farantawa juna su. Lokacin da Ahmad ya kusance ta ji yayi bai taba jin dadin da ya samu a jikin Hafsa ba. Ihu ya dinga yana sa mata albarka da kyar ya kyale Hafsa dan shima ya tina bata da lafiya ya jikin ta da ya dau zafi.

Rumgume ta yayi a jikin sa yana mai da nunfashi. sai da ya nutsu sannan ya dago yana fadin

“My life sannu.”

Fuska ta rufe dan ya bata kunya yace

“Allah miki albarka My life hakika da ba rasa ki da nayi babban rashi na aure ki nayi jihadi wanda ya zame min alheri domin abinda na samu ba kowa xai same shi ba sai dai bakin ciki na wasu sun sha min dadi amman ban.yafe musu ba. Allah ya barmin ke My life.”

“Amin my Hayyat!”

Ya dago ta ya kai bandaki ya tsarkake ta sannan suka dawo ya rumgume ta. Take bacci ya dauke su mai dadi. Sai asuba suka tashi sikai sallah.

Wanda yana dawowa daga masallaci ma suka koma gida. Washe gari da safe tare sukai hada abin karyawa sunayi suna soyayyar su. Sukai wanka suka karya abinsu. Da rana ma tare sukai girki suna kitchen Basma tazo ta shigo tana fadin

“Yaya kaine a kitchen.”

Hararar ta yayi yace

“Na bar my life tana girki ne?”

“A’ah kam!”

Hafsa tace

“Sannu da zuwa muje ki zauna ko?”

“A”ah muje na tayaku aikin dai.”

“Ah haba dai daga zuwa.”

“To Anty ai ba bakuwa bace.”

Tare suka gama abincin suka cigaba dayan su a plate daya. Suna gamawa suka zauna ana hira. Sai gab da magariba ta tafi bayan Hasa ta cika mata leda da kayan kwalliya da kudi.

Tana komawa gida ta samu Hannah dan tinda tazo tana gidan tana ganin ta tace

“Daga ina?”

“Gidan Yaya.”

“Gidan Yaya lallai bakya kishi na ko?”

“Kishib naki kenan abokiyar zaman ki bata da aibu gwara ki zauna ku rufawa kanki asiri.”

“Naki din kuma in har kina son ina kula ki bakye ba ita.”

“Wannan kuma baki isa ba kada ki manta Yaya wanane uwa daya uba daya dan haka ba abinda zai hana naso abinda yake so. Kila kwanan nan ma ta haihu kinga nayi da ko?”

“Ni kikewa gorin haihuwa ko?”

“Ni ba gori nai miki ba.”

Tayi ciki tana kwalawa Mami kira mami ta fito tace

“Menene?”

“Mami kinji Basma wai gorin haihuwa take min.”

“Ina Basman?”

“Tana daki.”

Suka futa ita da Mami. Mami tace

“Basma me kikewa Hannah?”

“Ni me nayi mata?”

“Tace kin mata gorin haihuwa shin ke kike bada haihuwar?”

“Mami bafa haka akai ba!”

“To ya akai?”

“Ni cewa nayi in amarayar Yaya ta haihu ai ya’ya nane!”

“Wallahi karya take.”

“Har da wallahi.”

“Eh!”

Basma ta kalli Mami tace

“To ni dai ban fada ba.”

Ta shige bandaki ta dauro alwala ta fito ta tada sallah tana jin Mami na lallashin Hannah.

*

**

***

****

*****

Alhaji Khamis bai tashi tunawa da matar sa ba dai da ya fara shiye shiryen aure sannan ya gane bata gidan. Kuma a kwalar sa dan Mama ma da ta tagi wajen shekara biyu bai damu ba barr ita.

Satin da ya aurar da ya’yan sa aka daura auren sa da Rukayya gida katoton gaske ya kama mata wanda ya cika mata shi da kayan daki.

Su Rukayya aka hau hura hanci aka shirya. party da dinner

Su Rukayya aka hau hura hanci aka shirya. party da dinner. Da ta ajiye kati na Umma da Ummu ma sai Anty Sailuba ta kwashe ta bayar. Da da tazo tana neman katin ta nema ta rasa shine ta tambayi Anty Sailuba tace

“Wa zaki bawa?”+

“Su Ummu!”

“Ba irin su muke nema ba mayan yara muke nema.”

Kallon ta Rukayya ta tsaya tace

“Amman Anty yan uwan mu ne fa.”

“Shine me ai da daurin gindin uwar ta hana Abba daura miki aure.”

“Kai Anty me zatayi ita dan Allah.”

“Rufen baki shashasha kawai kila kina zaune sa kashe miki aure.”

Bakin ta ta rufe amman ranta ya baci.

Ranar daurin auren mijin Anty Sailuba ya daura mata aure kamar yadda suka tsara akai party sannana akai dinner  an kaiwa Abba goro da alawa Abbah ya diba ya kaiwa Ummu sannan ya bawa Umma yace

“Allah sanya alheri.”

Ranar kai amarya da Rukayya tace a kai ta tayi sallama da Abba sai cewa sukai aah sai da Rukkay ta tubure sannan aka kai ta. Ana shiga da ita Abba yace

“A’ah Amarya ce?”

Durkusawa tayi tace

“Abba ka sa min albarka dan Allah.”

“Allah miki albarka Allah ya bada zaman lafiya”

“Amin!”

Yace

“Ku tafi”

Aka daga ta aka fita da ita. Ummu sai da aka kai mata alawa da goro sannan tasan da auren Rukayya. Daga nan aka dauki Rukayya aka kai katon gidan ta da Alhaji Khamis ya gyara mata ya zuba mata kaya a ciki.

Haka aka watse aka bar amarya. Alhaji Khamis ya shiga bayan kowa ya watse da kaji da lemuka. Haka suka ci suka sha sannan sukai sallah suka kwanta. Haka suka sha amarcin su cikin jin dadi da kwanviyyat hanlali. Rukayya komai a gidab ta kamar zai magana kaji da kayan dadi dan haka sai ta kara yadda da mijin ta tana ganin kamar daman can bakin ciki ake mata

*

**

***

****

*****

******

Kabir kuwa da lokacin komawar sa dakin Halima yayi har wani zumudi ua dinga yi dan maya boye saboda kada Sadiya tagane. Ana magariba ya shigo musu da kaji bangaren Halima ya nufa yana zuwa,  ya same su dukka su biyun zaune kowa yavi kwalliya kanar me masu zuwa biki wani dadi da farin ciki yaji ya ziyarce shi. Dan haka ya zauna yana fadin

“Halima da Sadiya matan Kabir!”

Sukai murmushi a tare Sannan suka ce

“Barka da zuwa!”

A tare kallon junan su sukai duk sai sukai murmushi shima yace

“Gaskiya ne suna iri daya magana ma a tare kun zama twins!”

“Haba dai ai ta girmenfa.”

Halima ta fada. Sadiya tace

“A aure kuma kece yaya ta ko?”

Sai tai murmushi kawai. Lesar hannun sa ya ajiye yace

“A kawo mana muci ko?”

Sadiya tace

“Anty a kawo mana.”

Halima ta baya fuska tace

“Ni dai bana son wata Anty ni bance miki ba sai ke.”

“To sorry sister! Tashi muje.”

Tayi murmushi ta mike sadiya ta dauki ledar sukai kitchen,  Kabir ya bisu da kallo yana jin dadi. Tare suka fito Halima rike da plate da yake cike da gashin kaji,  Sadiya kuma cups ne da lemo ta ajiye a kasa ya sauko ya zauna kowa ya zaua a gefen sa yace

“Bismillah!”

STORY CONTINUES BELOW

Sukai bismillah Halima ta dauka takai baki tana taunawa ahankali haka ma Sadiya. Ganin bawani ci suke ba shika dai ke ci yasa yace

“zan muku dure fa, tam bari ma in fara ta kanki ya fada yana kamo Sadiya, dasauri ta sa hannu ta dauko wani takai bakinta, hakane yasa ya cikata, yakoma kan Halima itama nan da nan ta dauka yace

“Allah ya taimake ku.”

A haka suka dan tsatsakura Halima tasha ruwa tace

“Alhamdulilah!”

Haka ma sadiya aka bar Kabir yana taci sai da ya koshi yasha lemo yai hamdala sannan ya ture plate din gefe, ya goge bakinsa da tissue.

Sadiya ceta kwashe kayan ta kai kitchen ta dawo suka zauna hira sai tara sannan ta mike tana hamma tace

“To ni zan tafi na kwanta sai da safe”

Ya mike ya kalli Halima yace

“Bari na raka ta ko?”

Ta gyada kai ya mike yabi bayan,  suna shiga yasa ta canja kaya sannan ya sa tayi alwala ta kwanta tayi addu’a ya mata sai da safe ta waje ya rufe yace

“zanyi missing dinki yau,”

“Nima haka ka kula da sister!”

Kai ya gyada sannan ya nufi ya gita.  dakin Halima ya koma bata falo ciki ya shiga.

A gefen gadon ta ya same ta har ta canja kaya zuwa na bacci sai kamshi take kusa da ita yaje ya zauna, yana kallonta kan ta a kasa yace

“Nayi kewar matata kwana, biyu kadai amman ni nasan yadda nake ji.”

Ya kama hannun ta ya daura kirjin sa yace

“Kinji yanda kirjina ke bugawa saboda san danake miki,”

Ita dai Halima tunda yafara magana ta sunkuyar dakai tana jin wani so da sha’awarsa na ratsa ta.

“Baby!”

Ya fada yana mikar da kallonta ta yayi dago kan ta suka kalli juna,  janyota yayi ya rungumeta yana sauke ajiyar zuciya, lumshe ido tayi tana jin wani irin dadi, saboda amatse take, dan tinda ya tafi ya barta na kwana biyun nan ga magungunan da ta sha yana aiki. Kabir ma wata irin sha’awa ne ya kuma taso masa dayaji tudun kirjin Halima dan ba laifi Halima nada dukiyar fulani, dan shima tin da tazo gidan yake a matse ya rasa ta ina zai fara ne

Kan gado ya jata, romancing dinta yafarayi jikinsa na rawa, kwantar da ita yayi  Yafara, kokarin cire mata ria, dan gaba daya ya fita hayyacinsa, Halima ma hankalinta ba, ajikinta yake ba, dan sai ta dauko hanyar mayar masa da martani sai tafasa, dan tana gudun Kabir yace dama tasaba, jin yana kokarin cire mata pant yasa ta rike hannuns, dagowa yayi dasauri, yafara magana da rawar murya

“Menene Baby ,dan Allah karkiyi min haka am badly in need please. nadade ina mafarkin wannan ranar pls don’t ruin my happiness”

Ganin ba zata sake shi ba yasa ya fusge hannunsa da ta rike rigat jikin ta ya zare ya yar nan yayi tozali da kirjinta, dake neman fitowa Daga rigar daya rage mata ajikinta, rikicewa Ya karayi yakai mata ya chafka, ya  fincike rigar ya yage gida biyu, ya cigaba da sarrafata, yana kokarin cire mata pant, ta kara rike hannun sa tare da zare jikin ta  karfi. Sai tayi bandaki a guje, binta yayi yana rokonta ta bude, taki, wani irin bacin rai ne ya rufeshi, nan take wata zuciyat yace

“Gaskiyar Isma’il ne da yace shi kadai take so,  shi zata iya bawa ragamar komai nata kuma ya amshi abinda shi bai san shi ba wanda shi saura zai tarar.”

Ya yadda da Isma’il tinda gashi shi dayake mijinta na sunna, taki yarda dashi, ji yayi zuciyarsa namasa zafi kansa yamasa nauyi, wani haushin Halima ya rufeshi, a fusace ya bybar dakin ya banko kofar da karfi Wanda karar banka kofar yasa Halima tsorata.

Durkushewa tayi ta fashe da kuka ba kukan komai bane sai na nadama marar iyaka. Yanzu da ba dan ta zubar da mutuncin ta ba me xata gudar wa. Tsoron ta daya daman kada yaje yaji ta a bude ya tsane ta.

Ta jima tana kuka sannan ta mike ta yi wanka ta fito  ta rufe kofa ta saka kaya ta hau kan gado tana kuka.

Kabir na barin dakin ya shiga dayan ya fada bandaki ya saki ruwa akan sa ransa ya masifar baci fadi yake

“Ni Halima zatayiwa haka, ni  zata guda amatsayina na mijin aurenta, ah lallai gaskiyar Isma’il ne dayace gangar jikinta zan Aura, gaskiyar Isma’il. Amman Halima meyesa zakimin haka, ina laifin san danake miki, da bakya sona, da kina sona bazaki gujeni ba yanda nadade ina jiran wanan ranar amma da abinda zaki sakamin kenan.”

STORY CONTINUES BELOW

Har ya kwanta ya mike ya fita a sashen nata gaba daya. Sittingroom ya tafi ya kwanta duk da ba bacci yayi ba sai tunani kala kala.

Halima ma tana kwance tana hawaye dan ita daman tana tsoron makomata, in Kabir ya kusance tane tasan sai ya tsaneni. Haka ta dinga saka da warwara tuna kalaman Yaa Fauziyya tayi da tace dole su zama.masu hakuri kuma kada suji kunyar bada hakuri dan haka ta mike da sauri dan ta bashi hakuri ta fita dayan dakin ta duba baya nan kofa ta duba ta ganta a bude take taji  hankalinta ya yatashi,  tayi tunanin ko wajen Sadiya ya tafi. Komawa tayi ta kwanta amman ta kasa nutsuwa mikewa tayi ta fita. Lokacin da Kabir yaji ba zai iya kwana a halin da yake ba in har ba a rage masa zafi ba.

Yana rufe kofar dakin Sadiya Halima na karasowa,  hawaye ne ya zubo mata ta koma daki ta hade kai da gwiwa tana kuka.

Kabir na shiga yayi dakin Sadiya yana kwance amman idon ta biyi ya shiga da sauri ta mike yace

“Baki bacci ba?”

“Na kasa!”

Ya karasa wajenta, ya zauna a gefen gadon ta karaso tana zuba masa ido sai taga duk ya sauya da sauri tace

“Lafiya kuwa? Ina Halima? Menya faru?”

Rungumeta yayi yfara mata kiss, mutsu mutsu tafarayi tana kokarin kwace kanta, matse ta yayi yacigaba da kissing dinta, kwace bakinta tayi da karfi tace

“Menene haka wai lafiya kuwa? Ina Halima din?”

Janyo ta ya kumayi ya cigaba da abinda yakeyi ,cire vest dinta yayi ya wurgar yafara kokarin cire mata karamin skirt din datasa fusge jikinta dakarfi ta hantsila Daga kan gadon, tadauko vest dinta takare kirjinta dashi tace

“Menene haka ne?”

Ido ya dago yana kallon ta wanda suke jajir ta kama hannun sa tace

“Ina ka baro sister?”

Hannun ta ya hau shafawa ta furge tana fadin

“Haba Kabir ina ganin ka kamar adali kada ka manta fa yau a wajen Halima kake me kake shirin yi.”

“Nasani amma kinsan ke matata ce kuma inada hakki akanki,”

“Na sani amman ai ba kwana na bane kuma ba kyau.”

“Na sani shiyasa nazo ai.”

“Ina Haliman to?”

“Baby ni fa ba wani abu zanyi ba kawai wasa zanyi dake.”

“Naji in tana da lalura amman meyasa ba zakai wasa da ita ba.”t

“Baby bana son tambayoyi in bazaki barmi ba shikenan. ai nasan da Halima din na taho gurinki.”

Shiru tayi yace

“Zo nan.”

A hankali ta karasa ya rungumota ya fara aika mata sakoni, sai daya samu minti talatin yana wasani da ita, sannan yasamu biyan bukatarsa, ya koma gefe, yana sauke numfashi dasauri dasauri.

Daga haka bacci ya dauke sa. Da asuba da ya mike ya tada ita wanka yayo yazo ya same ta rufe da bargo kallon ta yayi yace

“Menene haka yaran nan kuna garani ko? Na daga miki kafane jiya dan bake ce da girki ba amman ki sani duk ranar da zan dawo dakin ki shirya tarbata dan zan kasance dake a yadda nake so.”

Ya fada fuskar ta yace

“Kije kiyi wanka kada ki makara.”

Mikewa tayi da kyar ta shiga bandaki tana wanka tana tunani can zuciyar ta tace

“Kila tsoron azaba yasa Halima ta gudu shine yazo ya sauken gajiya har yake cewa zai nan next tab Allah ka kareni.”

Halima kuwa kuka take sosai tana danasanin abinda tayi dan tabbas laifinta, ne data bashi hadin kai da baije gurin Sadiya ba. ,haka tayi ta kuka sai da taji kanta na neman darewa gida biyu ta hakura,t a daina kukan,t ana Allah Allah take gari yawaye taje ta same ta bashi hakuri ahaka bacci barawo yayi awon gaba da ita  anan falon.

*

**

***

****

*****

******

*******

********

*********

**********

Sakina da Khaleel ma suna zaune lafiya satin su biyu da aure suka tafi Abuja. Sakina a tsorace take shin da wanne ido zata kalli Hajiyar. Suna zuwa ya bude mata kofa sai ta tsaya kallon gidan kallon ta yayo yace

“Menene dear?”

STORY CONTINUES BELOW

“Tsoro nake Khaleel!”

“Ba komai fito ai Dady yana nan.”

Ya kamo hannun ta,  ta fito yai gaba tana bin bayan sa,  da sallama suka shiga Dady dake falon ya dago yana amsawa. Hajiyar dake zuba masa lemo itama ta amsa ba tare da ta dago ba.  Dady ya saki murmushi yana fadin

“Ah Ango da Amarya ne?”

Sakina kunya taji tai kasa da kai Khaleel kuma ya murmushi ya karasa ya zauna a kan carpet yana gaishe sa Dady. Sakina ma gefe ta zauna tana gaishe shi ya amsa cikin sakin fuska yana fadin

“Ango kaga yadda kayi kyau kace amarya ta iya kula.”

Sakina dai kanta  na kasa. Khaleel ya kalli Hajiyar da ta zauna yace

“Ina yini Momy?”

“Lafiya kun sauka lafiya.”

“Alhamdulillah!”

Sakina kan taa kasa ta gaishe da ita ta amsa sannan tace

“Ya hanya?”

“Alhamdulilah!”

“Madallah!”

Sai kuma tace

“Ka kaita daki ko ta huta sai a kawo mata abinci.”

“Toh!”

Ya fada ya Mike ya kalli Sakina ta mike yai gaba tabi bayan sa.

Suna shiga dakin ya rumgume ta yaba fadin

“Please feel free my wife.”

Kai ta gyada. Yace

“Bari na dauko akwati ko,  ko zaki watsa ruwa.”

Kai ta gyada ya fita bai jima ba ya dawo da akwatin. Zaune ya same ta yace

“Muje muyi wanka sai muyo alwala ko?”

Kai ta gyada suka je suka yi wanka suka dauro alwala ta shirya suna cikin sallah Momy ta shigo da abincin su ajiyewa tayi ta juya. Bayan sun idar ya janyo sukaci. Suna gamawa ta kwanta bacci. Khaleel kuma ya sauka wajen Dady. Kiran Sallah Magariba yasa suka tafi masallaci bayan ya tashi Sakina.

Sai bayan isha’i suka dawo suka zauna a falo Momy ta fito tace

“Kun dawo ashe.”

“Eh!”

“To kuzo muci abinci “

Dady ya kalli Khaleel yace

“Je ka kira Sakina.”

Ya mike ya nufi dakin ta,  kwance ya same ta tana game ya zauna yana fadin

“My love!”

Mikewa zaune tayi tace

“Na’am.”

“Ki saukomuci abinci.”

“Toh!”

Ta ajiye waya ta mike ya fita tabi bayan sa su Momy suna dining suka karasa Khaleel ne ya zuba mata shima ya zuba ya zauna. Sai ta samu kanta da jin kunya ta kasa cin abincin sai juyawa take.

Dady da ya lura sai ya mike itama Mony haka suna tashi Khaleel yace

“Menene?”

Kai ta girgiza  yace

“Ko bakya son wannan?”

“A’ah!”

“To kici.”

Ta dan ci ta mike tayi sama ya bita da kallo yana gamawa shima yayi saman. Sqmun ta yayi tana sa kayan bacci ya zauna yana kallon ta.

Can yace

“Amman nace ki same kamar gidan ki ko?”

“Ai na sake My honey.”

Ta karaso ta zauna a gefen sa tana kama hannun sa ya sakar mata murmushi ta daura kan ta a kafadar sa,  ya janyo ya ya daura kanta a kan cinyar sa  yana shafa kan ta. Bacci ya dauke ta ya gyara mata kwanciyya sannan ya shiga yai wanka ya fito ya kwanta agefen ta.

Kwana su biyu ba wata matsala tsakanin ta da Momy konai zata ce a kai mata saboda ko sunce ta sauko a ci abinci bata iya ci. A kwana na uku suka daga inda Khaleel yake aiki dan yana gama karatu suka rike shi.

*

**

***

****

*****

******

*******

********

Rana bata karya akace dan yau ake daurin auren Humaira da Isma’il inda aka daura aure ya bada sadaki aure ya dauru a gidan su ba wata bidi’a da akayi anyi walima kawai sai yini wanda da dare aka kai amarya dakin ta.

Isma’il kuwa baki yaki rufuwa sai murna yake ya samu budurwa,  bayan an kai amarya yasa abokan sa suka sallami kawayen amarya dan baya so a bar masa kowa. Ana cewa ba kowa ya kamo hanya a hanya ya siya musu lemo da kaji sannan yaje chemist ya siyi maganin dada karfin sha’awa dan baya so Humaira ta guje masa har ya fito ya koma yace a bashi na karin karfi ya amsa ya shiga mota ya bude lemo ya saka kayar nasa kuma yasa a aljihu. Gida ya tafi jikin sa har rawa yake yana zuwa yai parking ya fito a dakin ta ya same ta ya zauna a kusa da ita tayi kasa da kai. Ya kamo hannun ya murza. Dago kanta yayi yaga idon ta yayi jajir yace

“Ba dai kuka kikai ba.”

Ai sai ta kara fashewa da kuka yace

“Oh My god dan Allah ki bar kukan nan please na roke ki.”

Kai ta gyada yasa hannu ya goge maya hawayen

Ledar da ya shigo da ita ya kalla ya mike ya dauko plate da cup ya ajiye yace

“Nasan baki wani ci abinci ba ko?”

Duk abinda yake tana gani sai taji tana tausayin kan ta da Isma’il yadda yake rawar kafar nan kar aje ya saketa. 

Taba ta yayi saboda yana ta magana bama ta san yana yi ba,  yace

“Dan Allah ki bar tunani da ni ba wani abu xan miki ba.”

Kai ta gyada yace

“To Bismillah,”

Ganin taki motsawa ne yasa ya dagota yadorata acinyarsa ya cire mata mayafin data rufe jikinta dashi,

“waw”

Ya furta da yayi tozali da na fulaninta, yakai musu kiss, taji wani yar ya dago yana kallonta har idansa yayi ja, yace

“Allah yamiki sura mai kyau Baby na. arayuwa inaso inga mace tanada dukiyar fulani,”

Kasa tayi da kai dan sai taji kunya duk da kunya bata tsarin ta. Ya dauki kaza ya kai bakin ta amman bama ta san ya dauko ba sai da ya taba ta yace

“bude bakinki”

Ta kalle shi. Ta bude ya saka mata yace

“Na rokeki dan Allah ki bar tunanin nan baki san tsoro ba dauke sha’awa ba?”

“Sha’awar me!”

Ido ya kamme mata tai kasa da kai. Ya cigaba yana bata yana mata kiss, har tace ta koshi sannan ya bata lemo ta sha da yawa. Yace

“Je kiyo alwala”

Ta shiga tayo alwala ta fito ta tsaya ya gama ya fitar da kayan sannan ya dawo ya shiga bandaki  wayar ta da ta boye ta dauko ta kunna data sako ne ya shigo mata tana budewa tava vedio ne ta bude me zata gani Isma’il ne kwance da wata yarinya wayar tabi da kallon mamaki kawar ta cr ta turo tana jin ya taba kofa ta sauri ta kashe gaba daya ta mayar taana mamaki kenan Isma’il shima dan hannu ne ko me inma hakane ya hadu da dai dai shi.”

Duk da haka tana tsoron sa saboda yadda taga hana zumudin na. Yana fitowa yayo wajen ta ya kamo ta ya dauketa cak yayi kan gado da ita, ya fara kokawar cire mata kaya, tace

“Alwala fa kayo.”

Ta fada tana fashewa da kukan munafirci,yace

“Na manta wallah kiyii hakuri babyna nasan tsoron mai kikeji, a hankali zan tafiyar dake bazan ji miki ciwo ba, fatana dai ki bani hadin kai.”

Ya mikar da ita ta saka hijab ya tada sallah suna idarwa ko adsu’a barr tambaya akan addini bai mata ba ya juyo ya hau cire mata riga. Yaba cire mata dukiyar fulanin ta suka bayyana,  nan da nan ya rikice jikin sa ya fara rawa, rungumota yayi yafara kissing dinta yana lashe ta kamar ya samu sweet, cikin minti biyu Humaira ta fita hayyacinta, dan Isma’il A ne ta bangaren nan,a a bata san lokacin data fara mayar masa da martani ba cikin kwarewa, tsayawa yayi cak da abunda yakeyi yadago da Jan idansa ya kalleta yaga idonta a rufe yake jikinsa ne yayi sanyi da yaga yadda ta ringa mayar mai da martani yana mamaki a zuciyarsa, amman sai ya tuna ya saka maga magani cigaba yayi da abinda yakeyi, har yasamu ya rabata da pant din jikinta ya rungumeta yamata rada a kunne

“Honey karki damu a hankali zan tafiyar dake,”

A hankali yafara kokarin shigarta ji yayi ya shige zuruf batare da ya wani sha wahala ba, a firgice ya dago tare da zare abar sa.

Humaira da tana jin shigar ta taji wani dadi taji ya zare, da sauri ta  bude idon ta daya kankance yayi ja dan jarrabawa tace

“Please kasaka.”

Wani wawan mari ya dauketa dashi yace

“U re not  virgin.”

Kunci ta dafe ta mike tace

“What?”

“Eh ke ba budurwa bace.”

“Tayaya ka gane hakan?”

“Kada ki rainawa hankali, inji ki abude, kamar kofar taxi kice min taya nasan hakan?”

“Kofar taxi kuma?”

Wani marin ya kuma dauke ta dashi yace

“Ina kika kai min budurcin ki?”

“Inda ka kai naka.”

“What?”

“Yes daya muke dakai,”

Isma’il  kuwa zuciyarsa bugawa take kamar zai fasa kirjinsa ya Faso jijjiyoyin kansa ya tashi saboda tsananin bacin rai, ya fusgota yayi da Iya karfin sa ya hadata da bango, yakama kirjinta yana murzawa

“Zaki gane baki da wayo. zaki gane inda na kai nawa kika kai naki. Yau zan nuna miki da bambanci tsakanin mu.”

Wata murza ya farai mata tin tana jin dadi taji azaba kokarin kwace kan ta take amman ta kasa wata dabara ce tazo mata ta bude abar sa da sauri ya sake ta ya dafe ta ta fita a guje zuwa dayan dakin.

sai da ya daina jin azaba sannan ya tashi ya bi bayan ta amman ta rufe koma falo ya koma yana jin kunci da kunar zuciya.  A ransa yana fadin

“Dama tantiriya na samo kai karuwa ma zance yo in ba karuwa ba wannan budewa har ina. Amman Humaira kin cuce ni. Ashe duk hijabi nan da kikesawa duk na munafirci ne gundumemiyar munafika ce ke, Allah ya isa ban yafe ba mikewa yayi ya fara safa da marwa adakin ransa a mutukar bace Humaira ta cuce shi. Ya riga ya gama timing shi zai bare abar sa a leda, ashe karuwa ce.Dakin Halima ya nufa dan ya tashe ta tayi sallah dan duk da abinda tayi mishi, hakkinsa ne ya tashe ta tayi sallah, kofar yayi knockind hade da sallama, tana kwance a kudundune, akasa tana bacci, kau da kansa yayi daga kallonta yace

“Halima! tashi kiyi sallah.”+

Yana fada ya juya ya bar dakin, kamar a mafarki taji sunan ta, mika tayi tai addu’ar tashi daga bacci sannan ta mike tayi alwala tazo ta tada sallah tana adduar Allah ya basu zaman lafiya mai dorewa tsakanin ita da Kabir.

 

Sadiya bayan tayi wanka tazo tai sallah tana zaune bayan tayi azkar ta tafi tunani shin me ya faru jiya. Duk yadda Kabir ke son Halima amman tayi wannan saken.

“Tab amman baki da wayyo Sis yadda Kabir ke son ki, ke a farkon ranar ki ya kusance ki, amman kika ki bashi hadin kai ai xafin da zakiji na baya ne sis.”

Tayi tagumi tace

“Zan bata shawara in ma baya sani bane a farko ne abun yake da zafi a sannu zaki sake kina jin dadin abun.”

Mikewa tayi ta shiga kitchen, ta fara kokarin hada musu breakfast, yana gab da gamawa, Kabir  yashigo, dan shigowar sa kenan har zai tafi bangaren Halima, ya jiyo buruntun ta a kitchen, ya nufa ji tayi ya rungume ta, ta baya, alokacin tana kwashe dankalin daya mata saura, lumshe ido tayi, yace

“Baby da asusuban nan bakya bari gari ya waye inzo in tayaki ba.”

“Yaya bakwai fa ta wuce gwara na gama da wuri na gyata bangaren. Sai na koma na kwanta kan safiyya ko?”

“Sannu to ni me zan taya ki?”

“Haba dai kaje ka taya Sister dai.”

Yai murmushi ya juyo da ita, ya mata kiss, ya cikata yayi waje, ido ta lumshe tabishi da kallo. A haka takarasa gama abunda takeyi tadauki kulolin takai dining, ta wuce bandaki dan tayi wanka.

Halima kuwa tana mikewa tayo alwala ta tada sallah bayan ta idar taji shiru shiru Kabir bai dawo ba. Mikewa tayi ta fara zagaye dakin ta daga baya ta fito falo ta zauna. Tana zaune taji an bude gate da sauri ta mike ta leka taga Kabir ne ya shigo har yayo bangaren ta ya juya ya tafi na Sadiya kan kujera ta koma ta kifa kai tana kuka.

Kabir bayan ya fito daga bangaren Sadiya yayo na Halima. Yana shiga ya tarar da Halima zaune ta kifa kan ta. Sallama kawai yayi ya shige dakin sa,  bai ko jira ta amsa ba ya shige dakin sa. Dagowa tayi yana goge hawayen idon ta.

Can ta mike tabi bayan sa dai dai lokacin da yake cire jallabiyar jikinsa, durkusawa  tayi ta sunkuyar dakai, a lokacin shivkuma ya zauna gefen gado yazuba mata ido, dagawo tayi da hawaye na bin fuskarta, tace

“Dan Allah dan Annabi Kabir kayi hakuri da abinda nayi maka nasan ban kyauta ba.”

Murmushi, yayi yace

“karki damu Halima daman nasan za’ayi haka dan saurayinki yaga min, yace gangar jiknki na aura bakya sona shi kikeso yace min ya miki training din da in zan kusanceki sai kin tuna shi kin gujeni, kuma na yarda da zancen sa Halima nasan bakya kaunata dan da kina kaunata bazaki min abinda kika min ba jiya.”

“Innalillahi wa inna ilahi rajiun, wlh ba haka  bane Kabir ina mutukar sanka, ina tsoron in ka kusanceni ka tsaneni shiyasa nayi haka jiya.”

“Bangane in tsaneki ba Halima!”

Ya fada a tsawace.

STORY CONTINUES BELOW

Ja da baya tayi ya kalle ta yace

“kinsan nasan komai akanki na yarda zan aureki, in zan tsaneki tun a lokacin dana ganki da Isma’il yakamata in tsaneki ban tsaneki ba sai yanzu, kinsan son da nake miki kuwa Halima? Kinga tashi kitafi dakinki, banasan raina ya baci magana.”

“Kabi…..”

“Nace ki tafi ko?”

Da gudu tabar dakin tana kuka, shikuma ya kwanta yarufe ido, soyayyar Halima,   tausayinta da sha’awarta na damunsa, ji yayi kamar yaje ya rarrasaheta, har ya mike, ya tina abinda tayi mishi komawa yayi ya kwanta tare da Jan tsaki.

Tana shiga daki ta fada saman gafkn ta tare da fashewa da kuka. tana fadin

“Innalillahi wa inna ilahi rajiun, Allahuma ajirni fi musibati wa aklifnin khairan minha, a yaushe zanji dadin rayuwa yaushe zan samu nutsuwa Isma’il ka cucen amman na bar ka da Allah Allah ya saka min,  nasan Allah dole ya jarabce ni ko dan abinda na aikata nayi zina. Yau ni na aikata zina Allah ka yafen ba dan ni ba dan darajat Annabi Muhammad (SAW) Allah ban zaman lafiya ka ban hakuri da juriya akan komai. Ya Allah ka dubeni da idan rahama ka ka jibanci al amurana, nasan nayi kuskure aruyuwata, nakuma yi nadamar abinda nayi, Allah ka yafemin, nasan abinda na aikata shi ke bibiyata yanzu wanda nake tunanin ya yarda dani yana kaunata yajuyamin baya, Allah kai ka jarrabceni dan nasan kowane bawa da irin jarrabtarsa Allah zuciyata tayi rauni ka taimaka min in cinye wanan jarrabawar ka bani ikon hakuri da juriya.”

Abinda ta dinga fadi kenan tana kuka mai tsuma zuciya.

Jin zazzabi na son rufe ta yasa ta mike  tashiga bandaki, tayi wanka, ta fito ta zura doguwar Riga, tadauko magani ta sha ta koma ta kwanta sai ciwon kai kan kace me jikin ta ya ruruce. Dan yadda take jin kanta kamar ya fado saboda ciwon dayake mata  zuciyar ta tayi kunci goma da ashirin sun hadar mata.

Karfe daya Kabir yai wanka yai alwala ya shirya ya tafi masallaci ana idar da sallah ya mike ya dawo bangaren Halima ba kowa a falon zama yayi yana tunanin me Halia taci. Sallamar Sadiya yaji ya amsa ta shigo ta zauna cikin shigar ta mai kyau. Ya kalle ya yace

“Kinyi kyau.”

“Nagode.”

Dakin ta kalla tace

“Ina Sis Halima?”

“Tana ciki.”

Mikewa tayi ta shiga dakin hade da sallama. Kwance ta hange ta akan gadon ta karasa tace

“Sister!”

Juyowa tayi idon ta jajir ta kalle ta da sauri ta karasa wajen ta tana fadin

“Me ya faru?”

Kanta ta nuna mata ta daura hannu akan ta taji ya dau zafi wuyan ta ta saka hannu nan ma taji zafi.

Da sauri ta shiga bandaki ta debo ruwa a bowl ta dauki karamin towel ta hau saka mata ruwan a jikin ta, ido Halima ta lumshe bayan ta gama ta gyara ta tace

“Kan ne ke miki ciwo kawai?”

Kai ta gyada. Ta mike tace

“Bari na fada masa gwara a yi miki test da Bp kan a baki magani sai muje asibiti.”

Kan Halima tai magana har ta fice. Ta girgiza kai duk da jiya yaje daki ta bata san me sukai ba amman Sadiya bata nuna mata ba da wata ce da yanzu ta farai mata fi’ili.

Yana zaune ta karasa tace

“Sister fa bata da lafiya.”

“Da sauri ya mike ya shiga dakin dago ta yayi yace

“Sannu Baby jikin ne?”

Ido ya bude ta kalle shi take ya kara rikicewa daukar ta yayi yai waje Sadiya tabi bayan sa a mota ya saka ta suka bar asibitin suna zuwa ya kai ta gun doctor nan ya hau bincike Sadiya da Kabir na tsaye. Bayan minti sama da talatin ta barta ya dawo ya zauna wajen Sadiya da Kabir.

Kallon su yayi yace

“Daman tana da hawan jini ne?”

Sadiya,  Kabir ta kalla! Kai ya gyadawa Doctor.

Yace

“Amman dan me ba zaku gujewa fadawar ta wani hali ba. Jinin ta ya hau sosai da sosai.”

“Innalillahi wainna illahir rajiun.”

Kabir ya fada.

Sadiya tace

“Yanzu ya zamuyi?”

“Magani zan bata amman ba wai tai ta sha ba na lokaci ne kadan dan tayi kan kanta ace za a daurata a kan maganin hawan jini tin yanzu.”

“Mungode Doctor amman ka duba bata da ciki ma.”

“Babu.”

“To mungode a bamu maganin.”

Nan ya rubuta ta amsa Kabir ya dauki Halima ya maida mota Sadiya ta je ta siyo maganin shi kuma sai sannu yakewa Halima da ke kwance idon ta a rufe.

Sadiya na dawowa suka wuce gida. Daki ya kai ta Sadiya ta kawo mata abinci taci ta bata magani kiran sallah la’asat akayi Kabir ya tafi masallaci su kuma sukai a daki. Bayan sun idar Sadiya ta kalli Halima tace

“Sannu!”

“Yauwah.”

“Amman me kika sa a ranki kike son halaka mana ke. Dan Allah ki cire damuwa. Kuma ma Sis abun fa na farko ne da zafi na biyu duk ba zafi.”

“Me fa?”

“Ki gane mana abinda Kabir ke nema a wajen ki wallahi da kin saba zaki gane ba wani zafi ne da abun ba duk da nima ina tsoron abun amman ke tinda kin amshe shi ai ya kamat tsoron ya ragu ki cigaba da bashi kulawa ko?”

Ganewa Halima tayi tai murmushi kawai ta kwanta tana fadin

“Kabir bai kusanci Sadiya ba kenan bayan nan tana ganin ko kin bashi hadin kai tayi saboda tsoro. Allah sarki Sadiya.”

Nan Sadiya tai ta bata baki daga baya ta tafi dan daura abincin dare. Tana kwance tana tunani duk matsalar ta Isma’il ne ya jefa rayuwar ta a hatsari da halaka ga hawan jini ta dalilin sa ga ya lalata mata rayuwa ta dalilin haka ta rasa farin ciki a gidan auren ta. Tana cikin tunani bacvi ya dauke ta saboda har da maganin bacci a cikin maganin ta.

Kabir ne ya shigo ya sameta tana bacci ya gyara mata kwanciyya sannan ya koma yana kallon ta cikin so da kauna da tausayin ta. Ido ya lumshe kawai yana tunani a ransa.

*

**

***

****

*****

******

*******

Washe gari da safe Isma’il ya bar gidan tana jin tashin motar sa ta fito ta dauki ragowar kaza da madarar jiya ta shige daki. Dauka tayi taci tana gamawa ta shiga tayi wanka ta fito ta shirya cikin kayan ta masu kyau kwanciyya tayi take bacci ya dauke ta.

Cikin bacci ta fara jin wata matsananciyar sha’awa tashi tayi tana mammatse kafafun ta idon ta yai jajir dan sha’awar da take ji. Kwanciya tayi kawai tana wannan hali aka budo kofa da sauri ta mike tsaye tana ganin Isma’il ta hau cire kaya. A guje ta fada jikin sa abinda ya haifar masa da wata matsanaciyar sha’awa kenan nan ymra hau cire mada kayan jikin sa ta daura hannun ta a kan abar sa. Daman abukace yake nan da nan ya biye mata sai dai yana kusantar ta yaji ya mata wata tsana saboda yadda yake shigewa ko karuwan da yake bi sunfi Humaira matsewa shin wanne irin maza tabi da suka buda ta haka.

Jikin sa ya zare yana tsaki ta tashi ta kamo shi tana fadin

“Wai menene haka?”

Duka ya kai mata ta kauce da sauri ya mike ya shige bandaki yana fito ya canja kaya yace

“Ki fito muje.”

Wanka tayi ta fito ta saka kaya ta dauki hijab har kasa ta saka tana fito ya bita da kallo a ransa yana fadin

“Ina ma yadda kike a rife a haka na same ki,  Allah ya kamani ya bani karuwa bayan yan matan da nake bi duk ba karuwai bane wasu ma ni nake bata su amman yau na dauki sauran wasu meyasa na bar Halima yarinya mai ni’ima Ita kadai xan iya aura saboda daban take ko da na bata ta bata kara bin wani ba nima da yayatake yadda dani sai nai mata kuja da dadin bakin zan aure ta yau na barta gashi na samu tantiriya ace kwana daya da aure haf mace ta san tanemi mijin ta ko da yake menene na mamaki tinda karuwa ce.”

“Wai ina xamu.”

Ta katse masa zancen zuci. Dagowa yayi ya aika mata da wani kallon tsana sannan ya gice ta bi bayan sa. Mota ya shiha itama ta shiga ta kalle shi tace

‘Ina zamu ne”

“Ban sani ba.”

Wani asibiti suka karasa yana zuwa ya shiga bai jima ba ya dawo yace

“muje.”

Lab sukaje aka debi jinin ta sannan suka koma suka zauna ba a jina ba aka kawo result ya amsa ya duba yaga negative wani kallo ya watsa mata ya mika mata sannan ya shiga ciki bai jima ba ya dawo yace

“Tashi mu tafi”

Mota suka shiga ta kalle shi tace

“Kana tsoro ne?”

Wani kallo ya aika mata. Tai murnushi tace

“Duk macen da zaka nema kana yin mata test ne kan ka neme ta kai wa ya sani ko kana da cuta.”

Bai kula ta ba har suka isa gida ya fice ya bar ta da kallo ta bishi tana jin son sa dan tana son Isma’il kuma tasan duk abinda yake mata laifin ta ne.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *