WANNAN RAYUWAR CHAPTER 8

 WANNAN RAYUWAR CHAPTER 8

Tana shiga dakin ta samu Mama zaune a falon ta. Zama tayi a kasa tana fadin
“Mama ina yini?”

“Lafiya lou. Me zan samu ne?”
“Mama ni ban da komai dan yaushe rabon da na fita ma.”

“To meyasa baza kije ki samo ba. Itama Fauziyyan naga yanzu ta daina fita. Daga Farisa sai Sakina da Halima da Hajara ke nemo mana kudi amman ku biyun nan kun daina fita to saboda me?”
“Mama mu makaranta ma zamu koma.”

“Waye zai dauki nauyin karatun naku?”
“Mu mana.”

Tsaki Mama tayi tace
“Allah bada sa’a.”

“Ina Halima?”
Hafsat ta tambayi Mama.

“Tana daki!”
Mikewa tayi tai cikin dakin. Mama ta bita da kallo.

A kwance ta samu Halima. Halima na ganin Hafsa ta mike zaune. Hafsa ta zauna a gefen ta tana kare mata kallo. Gani tayi tayi kiba da ita har sheki take yi ga yadda ta cika kamar me. Wannan yasa Gaban Hafsa ya fadi domin suma fara bin mazan su duk sunyi irin wannan kyan.

“Zauna mana Anty Hafsa.”
Halima ta fada. Zama Hafsa tayi tace
“Ya jikin?”

“Da sauki.”
“Allah kara sauki.”

“Amin amman ya naga…”
Sai kuma tayi shiru tace
“Ina kike zuwa yawon barar ne?”

“Kasuwa da wajaje.”
Kallon ta Hafsa ta tsaya yi tace
“Daga yau kada ki kara zuwa barar nan ki san yadda zaki ki daina dan ba girma da mutuncin ki bane ki zauna bakin da Allah ya tsaga ba zai rasa abinda zai ci ba kinji ko?”

Kai ta gyada tace
“Amman kinsan Halin Mama ko?”

“Ba tana riga ku fita ba da ta fita kar kuje in ta dawo kuce baku samo komai ba.”
“Shikenan!”

Dakin Hafsa ta  fara bi da kallo idon ta ya fada akan ledar da aka kawo mata fruit yanzu. Ledar ta janyo taga abubuwa a ciki tace
“Wannan fa?”

“Abokin saurayi na ne ya kawon kayan dubiya.”
“Saurayi kuma a ina kuka hadu?”

“Kasuwa!”
“Da gaske yake?”
Hafsa ta tambaya.

Kai ta gyada tace
“Yazo gun Baba ma amman bai bashi dama ba wai nayi yarinya.”

Kai Hafsa ta girgiza tace
“Allah ya kawo mana karshen *wannan rayuwar* ta cikin gidan nan. Daman Baba ba yadda zai ba tinda ko babbar mu Anty Fauziyya bai yadda ba bare kuma Yaya Saki da Yaya Farisa.”

“Nima na fada masa haka amman yace zai jira har lokacin da Baba ya yadda.”
“Ya dabiun sa suke?”

Gaban Halima ne ya yanke ya fadi ciki inda inda tace
“Yana da hankali da nutsuwa Hajara ma ta san shi”

Kallon ta Hafsa take tace
“Shikenan ki rike mutuncin ki dai kada ki soma nuna son abun duniya.”

“Insha Allahu!”
“Yanzu ya jikin kinje asibiti?”

“Jiya yazo munje har da Hajara.”
“To Allah kara sauki kina shan maganin.”

“Insha Allah.”
Ta mike tana fadin
“Bari naje ana  kiran sallah magariba kema ki tashi kiyo alwala kizo kiyi sallah.”

STORY CONTINUES BELOW

Mikewa tayi suka fita tare sukai alwala kowa yayi daki. Mama kuwa tana ganin fitar su ta dinga harara Hafsa tana fadin
“Kin kwaso halin Jummai dai kin koma dakin ta sai kace ita ta haife ki.”

Halima da ta shigo taji Mama na maganar bata tanka mata ba ta shige daki tana fadin
“Mama ke da ba halin ki ba bayan duk girman kine yaran gidan.”

Hafsa na shiga daki ta fara tunani rayuwa wai yau Mama ke nuna baa son su karo karatu gwara su na yawo su samo kudi bayan sam tasan Mama bata da son kudi kamar kishiyoyin ta. Ko da yake *Wannan rayuwar* ta cikin gidan su ta isa ta sa Mama son kudi ko ta halin yaya ne.

A gasiya mahaifin su bai musu adalci ba ace duk matan ka babu tsayayya. Daga auri saki sai Anty Haule da ta rasu Anty su ma yanzu bin maza. Umma mahaifiyar su Fauziyya ta tafi wata uwa duniya neman kudi Mama ta jefa kan ta a bara. Banda ya’ya da kowa yayi ta kansa wanda a dalilin haka suka fada halaka a rayuwar su.
Fauziyya ce ta fito zatai alwala tace
“Tsaiwar me kike?”

“Tunanin *wannan rayuwar* Anty. Ina tsoro kar kannen mu suma su lalace kamar yadda muka lalace.”
Dafa ta Fauziyya tayi tace
“Insha Allah ba zasu lalace ba akan kanne na sai inda karfi na ya kare da izinin Allah.”

“Allah ya kiyaye. Nagode Anty na ina son ki.”
Murmushi Fauziyya tayi tace
“Nima haka. Allah dai ya kawo miji kiyi aure.”

“Anty sai kin fara.”
Dariya Fauziyya tayi tace
“Na kusa na tafi na barku ai ko da yake kafa ta kafar ki.”

“Da kuwa naji dadi.”
“Ina wanda yazo rannan kuwa.”

Yanayin Hafaa ne ya canja tace
“Kila yaji koni wacece ya bar ni.”
“A’ah ana yin kyakyawan zato.”
“To Anty.”

“Bari nayo alwala na dawo.”
Ta fice. Hafsa kuma ta dauki Hijab ta saka.

***
Yana asibitin Momy ta kira shi kan ta aika masa da abinci gida wannan yasa cikin sauri ya tafi gida yana zuwa yai wanka ya canja kaya. Kan ya fito har driver ya kawo break din dan haka ya amsa ya fita a gidan ya koma asibitin.

Ko da ya kai abincin Dr Hauwa ce ta kai mata taci ta saka tai wanka ta gasa jikin ta sannan tayi sallah. Allura ta karai mata.

Sai wajen karfe sha biyu Dr Hauwa ta sallami su Ahmad bayan ta kara basu shawara da dokoki sannan ta basu wasu magunguna.
Lokacin da ya shiga dakin da take Hannah na ganin sa ta sunkuyar da kanta. Murmushi yayi ya karasa wajen ta yana fdin
“Sannu amarya ta.”

Baki ta turo masa. Hannun ta ya kama tai saurin janyewa. Dariya yayi yace
“Sorry ya jikin?”

Kamar zatai kuka tace
“Da sauki.”

“To sannu kinji.”
Kai ta gyada yace
“Bari na kai wannan kayan mota ki shirya sai mu tafi.”

Ya debi kayan da ya kawo ya fita da ido ta bishi dan har ga Allah yanzu tsoron Ahmad take ji.

Yana dawowa ya zo ya kamata amman ta kwace tace zata iya tafiya. Haka ta mike tana tafiya a hankali hadi da dafa bango a haka ta fita a dakin. Har suka iso reception din asibitin tana wannan tafiyar dai dai kamar me koyan tafiya.
Ahmad ganin yadda ake kallon su bai san lokacin da ya dauke ta suka fice a wajen ba.
“Ni ka ajiye ni kada ka fama ni.”

Abinda take fadi kenan tana kuka. Sai da ya saka ta a mota sannan ya ajiye ta. Ya zaga suka dauki hanya. Ba nisa dan haka nan da nan suka koma gida.

Wanka ta kara ta saka kaya sannan ta zauna a bakin gadon dakin. Ahmad ne ya shigo da sauri ta mike har tana kusan faduwa yai sauri ya taro ta. Jikinta ta janye da sauri cikin tsoro.

Murmushi yayi yace
“Haba Hannah ashe ke ba jaruma bace. To ki kwantar da hankalin ki ba abinda zan miki su Basma ne suka zo”

“Da gaske?”
Ta fada tana yin hanyar falo. Kallon ta yake yadda take tafiyar kamar zata fadi dan tana son tai sauri amman dinkin jikin ra yasa ta rasa yadda zatai dan sai da ta durkushe. Yai sauri ya karasa wajen ta yana fadin
“Ko na dauke ki ne?”

Kai ta gurgiza ta mike da sauri duk yadda take jin zafi ta daga kafa amman sai me sai taji kafar ta rike mata wannan yasa ta kara durkushewa. Murmushi yayi ya karaso ya sa hannu ya dauke ta. Suka fice.

Basma da wasu cousin nata na zaune suka ga Yaa Ahmad dauke da Hannah kamar Baby wannan ya mugun burge su. Basma mamaki take yaushe yayan ta ya fara son Hanna har haka ta faru.

Mikewa tayi ta tana musu pics tace
“Kai amarya da ango perfect match.”
Ajiye ta yayi akan kujera. Yana ajiye ta ta matsa daga kusa dashi. Murmushi yayi ya kalle ta yace
“Bari zanje na dawo bye.”

Ya fice a gidan. Da kallo kawai ta bishi yana fita Basma ta matso kusa da Hannah tace
“Sister ya naga har Yaya ya sauko ne? Kace kin sauke masa wannan girman kan. Ai nasan ke kam daman ba daga nan ba. Allah ya kara soyayya.”

Hararar Basma Hannah tayi tace
“Wallahi Yaa Ahmad mugu ne.”

Dariya suka sheke da ita suna fadin
“Haba Hannah kefa jaruma ce kar ki manta abinda kika fada a daren ana gobe kawo ki gidan nan. Haba kuma kya ce Yaya Mugu ne bayan abinda kk so yai miki.”

“Ba zaku gane bane.”
Ta fada tana goge hawayen idonta sai kuma duk jikin su yai sanyi suka tsora ta dan haka suka hau lallashin ta da bata baki.

Su suka gyara mata gidan suka daura abinci sannan suka zauna hira abin su.

Ahmad na fita ya nufi gidan su. Lokacin da yaje har lokacin da wasu daga cikin mutane dan gaka bangaren Dady ya nufa kawai. Yana shiga ya fada kan kujera ya lumshe ido take bacci ya dauke sa.

Bashi ya tashi ba sai da aka fara kiran sallah la’asar na da nan ya daura alwala.ya fita.

***
Mama dai har kwana na biyu ba Halifa ba alamun sa dan da taje gidan mai unguwa ce har lokacin shiru zubewa tayi agun tana kuka matan mai unguwa na bata hakuri. Ana cikin wannan halin suka jiyo hayaniya a waje.

Mai Unguwa ne ya fita amman jin yadda hayaniyar tai yawa yasa su Mama da matan mai unguwa tafiya soro dan suga me ke faduwa.

Suna zuwa suka ji wani yana fadin
“Wallahi a can muga sa kwance an cire masa ido da wasu sassa na jikin sa.”

Mai unguwa yace
“Ikon Allah. Yanzu aje a kai report gun yan sanda a tafi da yaron.”

Mama na jin haka ta firo da sauri. Tana fitowa taga Halifa kwancce ba idanu. Wani ihu ta saki ta fadi
“Inna lilahi wainna illahir rajiyn. Halifa. Halifa.”

Ta fada tana girgiza kai sai kuma ta zube a wajen sumammiya. Matan mai unguwa ne suka yayyafa mata ruwa ta tashi. Nan ta daura a inda ta tsaya da kuka dan haka aka dauke ta da yaron suka tafi police station. Information aka dauka agun ta ta fada tana kuka daga nan akai hotuna aka kira likitoci suka gwaje gwajen su. Sai dare suka bada gawar Halifa aka tafi da ita.
Kowa na gdan ya shiga tashin hankali haka akai masa sutura a daren aka kai shi dan lokacin Baba baya gari ma ya tafi sarin kaya.

Mutuwar Halifa ba karamin dukan Mama da mutane gidan tayi ba.

Samira wato matar Baban su Fauziyya wacce take ta uku. Itace wacce ta shiga kungiyar su Farisa in ba zaku manta ba tin a lokacin baya.

Zaune take ita da irin ta wadan da suka saba bin maza da auren su. Kamar yadda na fada muku tin baya wasu a ciki mazajen nasu basa zama ne suna can wata uwa duniya basa kula da lallurar iyalan su. Wasu kuma kwadayi yasa suka fada hanyar wasu kuma kuncin rayuwa a ciki har da Samira da kuncin gidan mijin ta ne ya jefata a cikin *wannan rayuwar.*

Zaune suke da Samira da Rabi’at wacce rashin zaman mijin ta shi ya jefa ta a wannan halin domin ita mace ce mai yawan bukata. Sai kuma Farida da kwadayi shi ya sa take bin maza dan mijin ta bashi da hali (Ku biyo Chapter 2/3) na labarin nan zakuji labarin sauran yan uwan nasu.

Rabi’at a cikin tafisu wayewa nesa ba kusa ba tana da ilimin boko da na addnin sai dai bata amfani dashi. Fara ce ga shi ta dada da mai sai ta kara haske. Tana da tsayi kuma kirar jikin ta na da kyau abinda yasa maza ke kara rubibi akan ta ne. Ga ta tana kula da kan ta da gyara jikin ta.

Ta yi kissa kallo tarairaya wanda duk su muke rasawa mazajen mu mafi a kasati ke neman matan waje. Matan banza na waje basu da kunya basu ki su side na miji ba indai zai ji dadi ya biya su. Amman mu sai mu zauna muce muna jin kunya. A ina kunyar take. Ai ba a wajen kula da miji kunya take ba. Kuma ma ku da akwai ta anan ai akwai lokacin da zaki nuna kina jin kunyar wani lokacin kuma ki nuna masa kema fa yar….. Dan Allah mata mu gyara mu kula da gyaran jikin mu tsabta da kula da abinda zai na kara mana ni’ima.

Kamar yadda nayi magana a some oage back akan magungunan mata. Waninillar tashi shine kin sa kudi mai yawa kin siya sai ya kare kuma baki da kudin siyar sa anan miji zai ji test din ki ya sauya bayan kin sabar masa da previous test kinga dole kullum yana neman na bayan. Amman in ke kika zauna kika hada abin ki da yar gyadar ki alkama aya ridi da sauran su kike yin kunun su kina saka madara a cikinina laifi. Ko kuma ki kasance kullum cikin tsarki da ruwan dumi bayan kinyi tsarki ki shafe gaban ki da al muski ko man zaibun. Haka nan kirjin ki kin yi yaye kinaso kar ya zube ki samu shinkafar ki ki dake ta da kanki kiyi gunbar ta kina sha da madara kina shafe shi da man hulba. Ko kuma ki samu kankana ki markada ki zuba mata madara a ciki. Haka nan yar ayar ki wanke ki markada ki tace ki zuba madara ko babu ki yini kina sha. Dan kifin ki in kin samu kiyi masa romo ki cinye ki shanye. Wallai kika riki yin abubuwan kula da kan ki zaki more rayuwar ki da kudin ki kadan kin biya bukata miji yasa miki albarka (Insha Allahu zan dubo muku wasu sinadaren na karin ni’ima wanda zaki hada  kanki ba sai kin fitae da makudan kudi ba.) Domin duk aikin daya ne dai.

Rabi’at ce rike da waya tana dubawa. Samira tace

“Wai ke me kike yawan yi a wayar nan ne?”

“Uhmm group ne dani kala kala na novels wallahi.”

“Novels kuma?”

“Eh wallahi!”

“Menene a ciki da kike karantawa to?”

Dariya Rabi’at tayi tace

“Hmmm ke a novels din yanzu bama na online baki ga yadda nake kara samon salon kula da namiji ba shiyasa nake hargitsa tunanin duk wanda muke mu’amala.”

STORY CONTINUES BELOW

Tabbas Rabi’a na daya daga cikin wadan da ake nema duk da matar aure ce. Dan haka Rabi’at tace

“Groups ne kala kala. Akwai na novels din wallahi kan ki gama karantawa kin gama jikewa akwai kuma na salihan bayi kamar wani da nake ciki *Indabawa hausa novels* kinga wannan group din da yan kungiyar wallahi su basa batsa a cikin littafin su amman kuma akwai dan karen dadi shiyasa sam bana barin littafi mai group din wato *Maryam S Indabawa* ya wuce ni ke bama ita kadai ba har na association din su *Hakuri da Juriyya Online writers* wato *HAJOW* Ya wuce ni. Hmmm wallahi in kina karanta buks din su ko dadin sa kamar me sam bana son littafin ta ya kare in ina karantawa. yana deben kewa sannan ina karuwa a wasu fannin rayuwar ga shi group din nasu da nata kullum sai an turo *azkhar* safe da  yamma, bama haka ba ga *HAJOW kitchen* da ake koya girke girke  wanda ko bakiniya ba zaki koyi kalolin girke girke da snacks. ga kuma *Ina Mafita* shirin dake kawo mana matsala da mafita da ta dace cikin hikima da dabara. Ga *Asan mutum asan sa’anar sa* shiri dake zaburar da al umma akan su nemi na kansu,  ba su tsaya sai abinda miji ya basu ba.  Ga *Hasken Musulunci* shima shiri ne dake wayar da al umma akan addinin musulunci bayan shi akwai *Musan Juna* inda ake tattaunawa da writers din association din har da member. Dadi da gari ga saukin kai ga dukkan marubutan kungiyar. Kinga ita *Indabawar* na sani ko? Amman wallahi baki ga yadda muke mutunci ba tana burge ni yarinya ce amman ba ruwan ta kowa nata ne ba girman kai.”

Tsaki Samira da sauran suka saki dayar tace

“Ke yanzu menene amfanin wadan nan program din ni na zata zaki ce ga shi ana koya yadda ake kunciyya da mu’amalar auratayya.”

Dariya Samira tayi tace

“Ai kun san ni bana tabarbarewa dukka. Wadan nan group din novels din ma duk ina ciki Na fada miki akwai novel din da na siya dari biyar amman fa ba karya akwai show. Amman kunsan me wallahi ko nawa *Indabawa* zata siyar da littafi sai na siya saboda akwai abun da ba zaka gane ba cikin hikima take yin sa.”

“Yauwah ni dan Allah ki taimakan da wanda kan na gama na gama jikewa na karanta.”

Bilkisu ta fada.

Samira tace

“Nima dai.”

Dariya tayi tace

“Bakwa son na Allah sai irin wadan nan ko. Wallahi a duk lokacin da nake karatun littafi *Indabawa* in har naji ance wane ta tashi yai sallah to bana bari a barni a baya ko banyi tawa ba zan mike na yi. Bama haka ba in naji wani abu anyi na karuwar addini nima rike shi nake yi. Uhmm ni ba abinda yafi burge ni sai Azhkar wanda yanzu daga na safiyya har na yamma baya wuce ni tin asuba wani lokacin take turo shi wanda ina hawa dashi nake cin karo na karanta. Haka na yamma da anyi la’asar wanda nima dana ganshi ko banyi sallah ba zan mike nayi nazo nayi azhkar dina. Kunsan duk iskancin da zakai kar kayi wasa da ibada.”

Tsaki Samira ta saki tace

“To malama!”

Rabi’at tace

“Naji malamar ke Allah ko….”

Sai tayi shiru dai. Bilkisu tace

“Ni dai ki an tayo ni a cikin group din sex books.”

“Kar ki damu xan sa a saka ki a ciki akwai wani da ake kan yi a yanzu ma.”

Binta dake zaune tace

“Please ni dai a saka ni a *Indabawa* ko dan na ga me kike son sanar manan nan.”

“Kar ki damu ina da number ta zan bata taki a saka ki.”

“Nagode.”

Suna zaune aka kira Rabi’a nan ta dinga waya a fili har da batsa tsakanin ta da samarin nata ko kunya a cikin mutane can tace

“Ok yau tare zamu kwana kenan?”

Shiru tayi tana sauraran abinda suke fadi can tace

“Ai shikenan zan kwantar da ita tinda na mikar da ita. Gani nan.”

Ta mike tana daukar jakar ta tace

“To ni sai gobe kuma”

Ta fice. Tsaki Samira tayi tace

“Sai iyayin banza ji a haka take son ta nuna mana ita ta Allah ce duk dan kar muna karanta wadan da take karantawa tana samun sabon salon rike maza.”

STORY CONTINUES BELOW

“Rabu da ita dai”

Bilkisu ta fada.

Binta tace

“Ku daina haka dai.”

Bilkisu tace

“Bariki ai ba amana.”

Samira tace

“Wallahi.”

*

**

***

*****

*******

**********

*************

Ummu ce ta dawo daga makaranta cikin shigar ta ta kullum wato doguwar riga ce da hijab har da nikaf kafar ta cikin half cover takalmi yai mata kyau. Anan falo ta dire jakar hannun ta tana fadin

“Washh Allah!”

Anty Zainab da ta fito daga kitchen tace

“A’ah kin dawo?”

Kai ta gyada mata tana jingina kan ta a saman kujera. Anty Zainab tace

“Ya exam din?”

“Wallahi ta dau zafi Anty Allah bada sa’a daba dan Doctor Hisham jiya ya taimaka yai koyan wannan abun ba da yau na kade kinsan mutumin min taba shi yayi da mukai masa magana yace ai ba komai zai bamu ba kuma wai ba lallai ya fito ba. Kinsan Anty wallahi sai da aka tsara two good question with it. Ina jin mutane na ta complain nima ya batan rai wallahi.”

“Haka lecturers din nan suke ai. Sai dai kuyi ta addu’a Allah bada sa’a bama sunga zaku kamo su sai mugun ta.”

“Haka ne.”

Ta zame hijab din ta mike Anty tayi Kitchen. Tana shiga daki ta hau cire kayan ta ta daura towel. Anty ce ta shigo ta mika mata wata leda tace

“Ga shi nan turaren wanka ne kina zubawa a cikin ruwan wankan ki zakiga na wuta kina turarawa akwai wani kadan a roba shi kuma tsugunno zakina yi.”

“Amsa Ummu tayi tana fadin

“Nagode.”

Sannan ta nufi bandaki da ledar ta ajiye na wanka ta fito ta ajiye sauran. Ta shige ban daki. Bude turaren tayi ta zuba a ruwan wankan ta. Wani kamshi ya dumame bandakin mai dadi. Ido ta lumshe sannan ta fara wanka kamshin na tashi. Tana gamawa ta dauro alwala sannan ta fito.

Tana fitowa dakin ta dumame da kamshin turare kamar a dakin akai wankan. Burner ta jona ta saka turare nan kamshin mai dadi ya cika dakin tana gamawa tayo na tsugunnen sannan ta mike ta shafa mai.

Kamshin jikin ta ya cika dakin ita kanta duk yadda ta juya kamshi take ji mai dadi. Doguwar riga ta saka da dauki mayafin ta ta yafa sannan ta wuce dining dan yunwa take ji.

Tana zama ta fara zuba dambun shinkafar da akayi wanda yaji gyada har da hadin cabbage da carrot da kulun wake da kifi. (My Indo an tuno…. Ko zaki ci ne? A bawa My Baby hakuri zan kawo masa nasa har gida. Hhhhh 😉) Zubawa tayi ta tsiyayi lemon kwakwan da akayi ta kurba dadin sa yasa ta lumshe ido sannan ta bude ta fara cin abincin. Ta gama ta mike ta koma falo tana kallo Wayar tace tayi kara. Tana dubawa taga Yaa Muhammad ne dan haka ta dauka cikin zumudi.

Sallama tayi masa cikin zakin muryar ta. Ya amsa yana lumshe ido yace

“Ashe kin koma gida!”

“Har nayi wanka na ci abinci.”

“Shine baki nemi taimako na nai miki wankan ba ko?”

Murmushi tayi tace

“Sorry to.”

“Me kike ci?”

“Dambu ne!”

“Uhmm har kinsa na fara kwadayi sa. Kinsan yadda nake son sakuwa gashi nayi missing nasa.”

Murmushi tayi tace

“Ko na zubo maka ne?”

“Hmmm zan kama kine!”

“Sorry!”

“Sai aukin bada hakuri. Ya exam din?”

“Alhamdulilah!”

“Allah bada sa’a daga yau sai jibi kun gama fa!”

“Eh!”

“Sai jiran ango ko?”

Murmushi Ummu tayi tace

“Yaa Muhammad kenan!”

Dariya yahi yace

“Ummu kenan. Kullum na tashi sai na kirga kwana kin dasuka rage min.”

Tai murnushi tace

“Sauran kwana nawa?”

“Dari!”

Ya fada yana dariya. Itama dariyar tayi tace

“Kai din ko?”

Yai murmushi yace

“Ai da sai dai ki ganni kawai.”

“Ko?”

“Kina kokonto ne?”

Kai ta girgiiza tace

“Yaa Muhhammad kenan.”

“Ummu na ina son ki. Son ki ya mamayen zuciya ban da tunani da bege sai naki dan Allah in mun gama waya ki turon picture naki.”

“Nagode Yaa Muhammad da soyayyar ka. Picture kuma yanzu zan turo maka.”

“Nagode Ummu nah. Allah miki albarka ya sa kece matata anan duniya da kiyama. Sam ban san lokacin da son ki ya sacen zuciya ta ba. Ban ganin kowa sai ke. Ina son ki Ummu.”

“Nima haka Yaa Muhammad.”

“Kema haka me?”

“Uhmm….”

Tayi shiru. Dariya yayi yace

“Ummu kunyar nan taki ko?… Kada ki manta nifa mijin kine.”

Shiru tayi yace

“In nazo zan ga idon mai kunya.”

Murmushi tayi shi kuma yace

“Nifa na kashe bakin ki kuma. Nasan ba kara magana zaki ba. Sai anjima zan kira ki ki debe min kewar ki da tsayin dare. Ki gaida Anty Zainab da yaran. Kada ki manta da pictire din.”

“Insha Allahu.”

Ya kashe wayar ta daura wayar a kirjin ta tana sakin murmushi. Anty Zainab ce ta fito ganin ta a haka ta zauna tana fadin

“Lafiya?”

“Waya muka gama da Yaa Muhammad.”

“Uhmm an sha soyayya kenan.”

“Kai Anty.”

“Allah kuwan. Kinga shawara daya da zan baki kada ki soma bari kunya ta sa ki kasa farantawa mijin ki. Ko kice dan mijin yayar kine ki rike abin ki. Arziki na Allah ne. Da ni ba raina mijina su Mamah sukai ba amman yanzu fa. Allah ya rufa mana asiri kuma bayan haka ma abinda Honey yake musu su nasu sunawa Abbah ne. Ai kam kinga ina arzikin yake kenan. Mu da aka raina ai alhamdulilah kuma insha Allah shima da suka raina Allah zai buda masa.”

“Allah yasa.”

“Amin. Kar ki damu ai ansha wuyar a da yanzu dadin za a ji tinda an gama karatun nasan zai samu aiki kema kuma in zai barki kiyi aikin ki sai ku taru ku rufawa kan ku asiri.”

“Haka ne!”

“Yauwah! Ya kika ji turarrn duk kin cuka falon da kamshin sa. Haka nake son kan Muhammad ya dawo ya rsuma jiikin ki shiyasa na baki dan naga daga jibi ba xaki kara fita ba aikin ma ki ajiye shi kawai. So nake kamshi ya rike jikin ki ki rikita min kanin nawa.”

Fuska Ummu ta rike. Anty Zainab tayi dariya tace

“In ban fada miki ba waye zai fada miki wallahi Umma ba abibda zata ce miki dan Ummu tayo gadon fulanin ta sam bata sakea damu bama ni.”

Murmushi Ummu tayi. Antu Zainab tace

“Ke dai wajen tsabta bani da matsaladake haka nan girki da gyara. Abu kadan ya rage min in fada miki yadda zaki mallake zuciyar sa da kua sauran.”

Dariya sukai Anty Zainab cikin dabara take fada mata yadda zatayi abubuwa da gyaran kanta da sauran su. Ummu dai naji tana sunkuyar da kanta wai kunya.

Suna zaune Yaran suka dawo nan suka rumgune uwar sannan suka rumgume Antyn su. Suka mike suka tafi daki dan ana kiran sallah. Wanka Ummu tai musu sukai alwala sukai sallah gaba dayan su.

Bayan kwana biyar Fauziyya da Hafsat na zaune Arfat ya shigo da gudu ya kalli Fauziyya yace
“Anty Wai kizo a waje?”+

Kallon sa take da alamar mamaki dan ita har ta fitar da rai da zuwan Muhammad dan haka bata kawo shi bane shiyasa tace
“Je kace wanene?”

Ya fita ai jima ba ya dawo yace
“Wai Muhammad ne.”

Ai bata san lokacin da ta mike ba. Kallon ta Hafsat tayi sai ga hawaye a idon Fauziyya mikewa Hafsat tayi ta dafa tace
“To menene na kukan Anty?”

“Hafsat yau fa kwana bakwai ba shi ba alamun sa. Hafsat tsoro nake kar yace ya….”
Sai kuma tayi shiru.

Hafsat tace
“Anty ke fa kike bani kwarin gwiwa akan irin wadan nan abubuwan dan Allah Anty ki daina kuka ba abinda zai faru sai alheri.”

Hawayen ta fuskar ta Hafsat ta hau goge mata nan ta dauki Hijab din ta ta saka ta fita.

Tsaye ta same shi cikin wata maroon yadi dinkin riga da wando ne yai masa kyau sosai kyan sa da hasken jikin sa sun kara fitowa. Yai wani fresh dashi alamar bai da damuwa yana cikin jin dadi. Fuskar sa dauke da murmushi. Hannun sa sakale da golding kalar agogo kan sa ba hula gashin kansa ya kwanta luf luf dashi.

Kallon sa ta tsaya yi Muhammad kyakyawa ne dan yana da manyan idanu sanan yana da dogon hanci siriri kuma bakin sa madai daici ne. Yana da saje da ya zagaye fuskar ya dada mata kyau da kwarjini sai sheki yake yi. Dogone bashi da kiba. Ganin shima cikin kwayar idon ta yake kalla yana murmushi yasa ta dauke idon ta daga kallom sa.
Matsowa yayi kusa da ita yadda har suna jin fitar mumfashin junan su. Kan ta a kasa ta kasa dago shi. Hannunsa dake harde a kirji ya zare ya dago fuskar ta. Hawaye ya gani yana gangarowa daga cikin idon ta nan da nan cikin tashin hankali ya fara magana.
“Ya salam Fauziyya me ya faru ni na bata miki rai?”

Cikin kuka ta daga masa kai. Shiru yayi yana kallon ta yace
“Naji amman dan Allah daina kukan nan ki fada min me nayi? Amman ki daina kukan wallahi baki ji yadda nake ji ba a cikin zuciya ta.”

“Ba kai bane ka tafi ka barni ba ko waya bare kazo?”
Ta fada tana turo baki. Murmushi Muhammad yayi yana shafa sumar kansa yace
“Ba zan baki amsa ba sai anjima da dare in kina jiki na.”

Ido ta rufe da hannayen ta dan ya bata kunya. Hannun sa ya saka ya zare hannayen ta yace
“Menene na kunyar yanzu fa ni mijin ki ne. Ina fatan kin shirya tahowa waje na da soyayyar ki kala kala.”

Shiru tayi ya kalle ta yace
“Nayi kewar ki Fauziyya yadda baki ba zai iya furtawa ba sai zuciya ce tasan halin da na shiga kawai! Ina fatan kina lafiya?”

Baki ta turo taki magana yace
“Naji anjima zanzo na amshe ki dai daga wannan gidan!”

Dagowa tayi tana kallon sa. Yai murmushi yace
“Eh mana ai na dada miki kwanaki ma inajin ko?”

STORY CONTINUES BELOW

“Wai yau zan tare!”
Kai ya gyada tace
“Amman ai ban sani ba.”

“In kin sani me zakiyi.”
Juya masa baya tayi tace
“In maka ado mana!”

Murmushi yayi dan yana son Fauziyya da kunyar ta. Yace
“Wane irin ado kuma? Fauziyya ni a haka ma kin ishe ni fadan wane irin ado?”

“Lalle da gyaran kai fa.”
“Kizo min a haka ma ni na fiso da kai na zan kai ki inda za a gayara min ke kinji ko?”

Kai ta gyada yace
“To juyon na ganki wallahi ban gaji da kallon ki ba.”

Kin jiyowa tayi wannan yasa ya saka hannu ya juyo da ita. Sai kuma ya jata gaban sa yana leken fuskar ta da tayi kasa da ita.

Murmushi take ya kurawa lips dinta ido sannan ya lunshe idon sa ya dago kansa.
“I love u Fauziyya i really love u!”

Shiru tayi yace
“Ni ba zaki ce kina so na ba?”

Kafada ta make tana murmushi yace
“Ko duk dan nayi laifin ne?”

Kai ta gyada yace
“Naji anjima in na fada miki uzuri na in bai miki ba ki hukunta ni in kuma ya miki sai kin biya ni rowar muryar ki da fada min I Love u din da kika ki.”

“Wai da gaske yau din?”
Ta tambaya tana wasa da yatsun hannayen ta.
Kai ya gyada yace
“Gaskiya yau ba zan iya bacci ba matatah ta ba.”

Tsigar jikin ta ce ta tashi jin yadda yai maganar.shiru tayi yace
“Kiyi hakuri ki amince kibi mijin ki na miki alkawarin zaki same ni fiye da tunanin ki kuma zan so ki da zuciya daya zan kula dake ba zaki taba kuka ba sai na farin ciki shima bana son zubar hawayen ki I love u Baby na i really do so.”

Kasa magana tayi. A kwanakin baya tayi zaton Muhammad baya son ra amman a yanzu yadda yake zumudin kasancewa da ita yasa komai ya kore a zuciyar ta. Hakika ta yadda da Muhammad tana fatan kuma Allah basu zaman lafiya.
“Bari na tafi na barki kiyi sallama da yan gida anjima zan zo after isha’i.”
“Nagode!’

Ta fada. Kallon ta ya tsaya can yace
” To tafi mana.”

Juyawa tayi ta shige sai da yaga ta shige sannan ya juya ya bar soron.”
Tana shiga daki ta kira Hafsa. Zuwa Hafsa tayi. Kallon ta Fauziyya take ciki da tausayi tace
“Hafsa tafi xan yi na barki fa.”

“Ina zaki tafi ki barni Anty?”
“Hafsat yau sati daya da daura min aure da Muhammad naki na fadawa kowa ne dan kar abun yazo bai yiyu ba. Kuma bayan daurin auren sai hakan taso ta faru domim kina gani dai ya dauken kafa. Amman daman kwana uku ya bani yace nayi komai to kinga kwana uku ya wuce. Amman yau ya zo min yace anjima zai zo zamu tafi. Daman Baba ya fada min ya dauran aure kuma ya fada min cewa nan da kwana uku mijin zai zo to yau yace zai zo sam ban son na tafi na barki kimin alkawarin ba zaki koma gidan jiya ba.”

Hawaye ya zubo a idon Hafsa ta rumgume Fauziyya tace
“Ina taya ki murna Anty zanyi kewar ki amman me yasa ko ni ce baki fada min ba?”

“Kiyi hakuri ai yanzu na fada miki!”
“Shikenan.”

“Hafsar ki sani ke tawa ce in naga yanayin inda nake zan zo na dauke ki.”
“Da kuwa naji dadi Anty. Domin ina tsoron *Wannan rayuwar* ta gidan nan.”

“Ba abinda zai faru insha Allahu. Kuma zan zo na dauke kin kinji.”
“Nagode Anty!”

“Yauwah!”
“Bari na hada miki kayan ki ko?”

“Nagode.”
Nan Hafsat ta fara hada mata a akwatu nan ta. Masu kyan ta diba wasu ta bawa Hafsa sauran ta rabawa Halima da Hajara. Duk sukai mata godiya.

Ana magariba ta shiga tai wanka ta fito tai alwala ita da kanta ta turare kan ta sannan ta shafa turare masu dadin kamshi ta saka daya daga cikin sabon dinkin da tayi. Ai kam tayi kyau da ita kamar ka sace ta gudu.
Sallah tayi tana kan sallayar har akai isha’i.

STORY CONTINUES BELOW

Idon ta na kan agogo har karfe takwas da rabi tayi gaban ta taji ya fadi ta dafe da hannu tana addu’a a cikin ranta.

*
**
***
****
*****
******
*******
********

Su Basma basu tafi ba sai magariba. Hannah taji dadin zuwan su domin kuwa sun debe mata kewa dan da zasu tafi har da hawayen ta haka suka tafi bayan sun lalashe ta.
Suna tafiya ta shiga tai wanka ta dauro alwala. Fitowa tayi ta shirya cikin wata atamfa baka mai adon pink and yellow. Dinkin riga da siket ne yai mata kyau sosai batai kwalliya ba turare kawai ta shafa taji ana kiran sallah isha’i mikewa tayi tai sallah ta idar ta zauna akan sallaya taba addu’a.

Bayan yayi sallah magariba ne ya koma cikin gida dakin Momy ya shiga ya same ta zaune a falo masu aikin ta na ta aikin kukkula dubulan da alkaki da nakiya da cincin a cikin leda.

Tana ganin sa ta saki fara’a tana fadin
“Daman baka tafi ba?”

Kai ya shafa yana fadin
“Eh yanzu zan tafi.”

“Ok yanzu mukai waya da su Basma ma suna hanya dawowa. Dan haka ka tashi ka tafi kar a barta ita kadai.”
“Toh Momy sai da safe.”

“Allah tashe mu lafiya. Allah yayi albarka.”
Kansa a kasa ya amsa da amin ya mike ya fita.
A compound ya hadu da su Basma sun dawo. Basma tace
“Yaya shine har muka taho baka koma ba ko?”

“To me zan muku?”
“Hira mana.”

Murmushi yayi yace
“Ai kunyi da Antyn ku.”

Sukai dariya. Yace
“Zakuga sako kowa zan turo masa.”

Rumgume shi sukai suna masa godiya suna a haka motar Dady ta shigo gidan. Yana parking gaba dayan su suka nufi motar. Ahmad shi ya bude masa kofar yana yin kasa da kai yace
“Sannu da zuwa.”

Dafa kafadar sa Dady yayi yana fadin
“Yauwah ango ya iyalan?”

Kai yai kasa dashi yana murmushi. Basma tace
“Ai yanzu muka dawo daga can ma.”

“To Allah yayi albarka ina fatan dai tana lafiya ko?”
“Eh Dady tace ma agaishe ka.”

“Ina amsawa. Allah yayi albarka.”
Ahmad ne ya dauki jakar sa suka jera suna tafe suna hira gaba dayan su. A bakin kofa su Basma suka bar Dady da Yaa Ahmad suka wuce.
Ajiye jakar yayi sannan ya durkusa suka gaisa. Dady yace
“Ina fatan komai lafiya dai ko?”

“Eh Dady.”
“To Allah yayi albarka.”

“Amin Dady.”
Daga haka yace
“Dady ni zan wuce.”

“Toh Allah yayi albarka ka gaishe min da Hannah.”
“Zata ji.”

Ya mike ya fita. Gun motar sa yayi ya shiga ya bar gidan. A hanya ya tsaya ya siyo musu gashin kaza sannan ya dauke hanyar gida. Yana shiga unguwar yaji ana kiran sallah yasan in har ya karasa gida ba samun jam’i zai ba dan haka ya paka motar anan bakin masallacin ya fita yai alwala sannan ya shige ya hau sahu.

Ana idar wa yai shafa’i da wuturi sannan yai addu’a ya mike ya fito. Motar sa ya shiga ya nufi gidan. Mai gadi ne ya bude masa gate sannan ya shige bayan sun gaisa.
Ya fito ya dauki ledar ya shiga bata falo dan haka ya shiga bedroom din ta tana zauna akan sallaya yana sallama ta mike a zabure zata bar wajen da sauri ya kamonta yana fadin
“Menene haka?”

“Ni dai ka sake ni.”
Ta fada hakawaye na zubowa a idon ta. Daga kallon ta zaka san cikin tsoro take wannan yasa ya sake ta ya ajiye mata ledar hannun sa yace
“Gashi nan kici kinji?”

Kai ta gyada masa kan ta a kasa bata yadda sun hada ido ba. Fita yayi ya koma dakin sa. Yana shiga ya fada kan gado yana lumshe idon sa.
A yanzu ba abinda yake bukata sai matar sa tin jiya da ya dandani zumar ta yake cikin kishirwar ta. Amman kuma Dr tace ya barta ta huta. Ko ba haka bama yaga Hannah yanzu tana jin tsoron sa ba kamar da da take masa rawar kai ba. Murmushi ya saki yana mikewa. Bandaki ya shiga ya sakar wa kansa ruwa yana fitowa ya fito. Kayan bacci ya saka sannan ya dauki wayar sa yaiwa kannen sa transfer din dubu biyar biyar. Sai da ya gama yai wa abokan sa text din ban gajiya.
Bayan ya gama sannan ya mike ya fita. Kitchen ya shiga ya dauki lemo.ya koma falo yana sha yana kallo. Karfe goma yaga bata fito ba mikewa yayi ya shiga dakin ra kwance ya ganta akan gado cikin kayan bacci cotton doguwar riga ta wuce gwiwar ta.

Ido ya lumshe ya bude a hankali sannan ya hau kan gadon. Janyo ta jikin sa yayi a firgice ta bude idon ta tana ganin shine ta zaro ido cike da tsoro tayi baya.

“Wai menene haka Hannah?”
“Dr fa tace ka barni na huta.”
Ta fada kamar zatai kuka.

“To ni me kika ji nace zan miki bacci kawai zamuyi.”
“Ni dai dan Allah kayi hakuri ka tafi dakin ka.”

Murmushi yayi yace
“Kada ki manta abinda kika fada min jiya fa cewa ba haka akewa amare ba. Nima yau wane angon ne kika taba ganin ya kwana ba mace a jikin sa.”

Hawaye ne ya zubo idon ta dan yadda take cike da tsoron Yaa Ahmad dan haka tace
“Ni dai dan Yaa Ahmad kayi hakuri yau ka kwana a dakin ka dan Allah.”

“Amman kinsan hukuncin wanda ya nemi matar sa taki amince masa kuwa?”
Hawaye ne ya zubo a kumatun ta ta gyada kai tace
“Amman ai ni ance ka barni na huta.”

“Nima kinji nace miki wani abu zanyi ne. Kawai dai dumin jikin nake so!”
Fuska ta shagwabe tayi kalar tausayi dan haka ya mike ya yace
“Shikenan ni gaskiya zan kara aure na samo jaruma.”

“Kayi hakuri.”
Mikewa yayi yace
“Koma ki kwanta sai da safe.”

Kai ta gyada ta koma ta kwanta tana ganin sa har ya fice a dakin. Ido ta lumshe hawayr na zubo mata. Hannu tasa ta goge sannan taja bargo ta rufa bacci ya dauke ta.

Farisa ce kwance jikin Alhaji Labaran sabon Alhajin da tayi kamu wanda ba abinda baya mata sai dai bata ce ba. Domin ita ma ba karamin wahalta masa take ba. Ko ina zata bishi domin bai taba samun mace mai kyau da kuruciya kamar Farisa ba. Ga ni’ima wanda daga halittar yan gidan su ne. Allah ya basu kyau,  kyan diri ga ni’ima wannan yasa maza ke haukace musu dan in sukai mu’amala da mutum ba zai kara jin dadin wata kamar su ba.+
Gashin kan ta yake shafawa yana wasa dashi. Idon ta a lumshe a hankali yace
“Baby!”

Ido ta bude wanda suke son su rufe kamar me jin bacci ko dan menene oho? Kissing bakin ta yayi yace
“Na fada miki ki yadda na aure ki dan Allah wallahi da gaske nake son ki.”

Ido ta bude tana kallon sa sai ta sheke da dariya sannan ta gyara kwamciyya tace
“Abinda kusan duk wanda nai taraiyya yake fada min kenan. Ban taba tambayar su dalili ba amman kai zan tambaye ka saboda me?”

“Saboda ina son ki!”
Wani kallo take masa tace
“A’ah fadi gaskiya dai cene min kada gaba na guje maka ko? To Alhaji a gaskiya zan fada maka ko na aure ka ko is fot just 2/3 month dan haka tsarin kungiyar mu yake kaga kenan gwara mu karasa a hakan ko?”

“Baby ba zaki gane bane? Ni babban mutum ne a yanzu bana son ina yawan neman mata saboda kar asiri na ya tonu. Kuma ni tinda nake neman mata ban taba samun wacce tai min kamar ki ba. Gashi young ga kyau ga sweet in dai zaki ban dama zan zama abokin rayuwar ki na har abada.”
Ya fada in a serious tongue.

Kallon sa tayi ta girgiza kai tace
“A gaskiya Alhaji kayi hakuri a yanzu ba zancen aure a gaba na. Sai na gama abinda na shigo bariki dan shi.”

“Me ya kawo ki bariki me kike bukata?”
“Kudi!”

Ta bashi amsa tana tsare shi da ido. Murmushi yayi yace
“In dai sune zan baki iya yadda kike so?”

Murmushi tayi tace
“Nawa kake dasu kai kam bayan ban taba jin sunan ka a jerin masu kudin nigeria ko masu kudin yan siyasa ba. Bayan ni kuma so nake kudin da xan mallaka ya zama za a na kira na a cikin jerin masu kudi. Domin ina son na inganta rayuwar yan uwa na da ya’yan da zan haifa bana son ko kadan su tashi a cikin irin *wannan rayuwar* Alhaji ka bar zancen kawai ka sha abinda zaka sha ka ban rabo na a wajen ka in kara gaba.”

Ta fada tana shafo fuskar sa. Ido ta kanne masa tace
“Kada ka damu nima kana daya daga cikin wadan da nafi so a barik domin kana daya daga cikin masu min abinda nake so da kulawa dani sosai.”

“Baby manya kenan. Ina son ki.”
Ya hade bakin su. Nan suka cigaba da yin masha’ar su.
Sai da suka gama sukai wanka sannan ya dauke ta suka nufi supermarket dinsa ta dinga jidar abinda take so har da sabuwar waya ta dauka sannan ya bata kudi masu yawa ta koma gidan ta.
Tana shiga ta tadda su Anty Samira da Rabi’a da Bilkisu. Tana zama aka shigo mata da manyan ledojin hannun ta aka ajiye mata anan tsakar dakin.

Anty Samira uwar son abin duniya ta mike tana leka cikin ledoji ido ta zaro tace
“Me nake gani haka Farisa. Gaskiya ke me sa’a ce.”

STORY CONTINUES BELOW

Bilkisu tace
“Duk sa’ar ta takai yayar ta ne wacce ake dambe da fada tsakanin manyan alhazawa wannan yace ya riga booking nata wani ma haka. Ke in kinga yadda Momy ta samu kudi da Fauziyya sai kin rike baki ga ta bata da son abin hannun ta ko mu nan mun dandani arziki.”

Rabi’ah dake karatun novel ma bata san me suke yi ba dai da Farisa ta tabo ta sannan ta dago. Kallon ta tayo tace
“Yaushe kika dawo ince ya jika ki da naira.”

Ido Farisa ta juya tace
“Da dolar ya jika ni ba da naira ba.”

Dariya Rabi’a tayi tace
“Ai na fada miki kika ki amsar tayin sa ba karamin mutum bane.”

“Haka ne. Ai naga hakan domin one week din da nayi na ga abinda ban taba gani ba kinsan me?”
Duk ido suka zubawa Farisa suka ce
“Sai kin fada”

“Hmmm wallahi wai aure na yake son yayi.”
Murmushi Rabi’a tayi tace
“To menene sai ayi na wata biyu zuwa ukun ko?”

Kai Farisa ta girgiza kan tai magana Anty Samira tace
“Tab kada ki soma yadda wallahi me zakiyi da wannan tsohon?”

Kallon ta Rabi’a tayi ta saki murmushi domin ta gane mai Samira ke nufi kishi kawai take da Farisa.

Dan haka Rabi’ah ta mike ta kalli Farisa tace
“Ki sameni a daki.”

Tayi ciki. Da kallo dukka suka bita. Mikewa Farisa tayi tace
“Ku zabi abinda kuke so. Ina zuwa!”

Ta mike tabi bayan Rabi’ah. Da kallo suka bita Samira da Bilkisu.
Tana shiga Samira ta juyo ta kalli Bilkisu tace
“Allah ya sani na tsani Rabi’a. A duniya kuma ba wacce nafi tsana kamar Farisa domin kuwa yadda maza ke rububin ta shin dame ta fimu.”

Dariya Bilkisu tayi tace
“Samira kenan kada ki manta Farisa yarinya ce shakaf yanzu take tashen komai sannan tayaya zaki hada kan ki da ita da farko ita budurwa ce i means bata da aure a yau da za a bi hadin shari’a mu jefe mu za ai ita kuwa bulala ce shikenan watakila daga nan ta shiryu tai aure ta haihu ta bautawa Allah karshe kiga ta shiga gidan Aljanna. Mu kuwa fa an jefe mu sai in Allah ya amshi shahadar mu ne sannan zamu samu tsira dan haka ko tana da bambamci ta fiki. Sai na biyu kinsan Farisa dai tafi mata dubu ko? Kyakyawa ce sannan ga diri menene bata dashi. Dace ne kawai batai da iyayen kwarai ba dan tayi dace da yanzu tana gidan mijin ta tana bautar aure. Na uku Farisa na da zuciya mai kyau. Tinda muke bata taba kawon zancen wani ko wata bayan nan abun hannun ra bai rufe mata ido ba ki kalla fa a gidan ta muke zaune bayan nan yanzu ta dawo an mata siyayya bata dau komai ba tace mu zabi abinda muke so. Farisa bata  aibu gaskiya ina fatan ta shiryu tai auren ta da tani ne da ta yadda ta auri Alhaji Labaran menene a ciki dan tsoho ne.”

Baki Samira ta tabe dan duk a banza ita kam bata son su kuma ba zata taba ba. Dan kishi sosai take dasu.

Rabi’a na shiga daki ta zauna a bakin gado sannan ta bude wayar ta. Cikin *Indabawa Hausa Novel* ta shiga. Tana shiga taga anyi sending video bude sa tayi a hankali ya gama budewa. Play ta dannan.
Wata mata ta gani ta taho sanye da hijan ash kala yar uwar ta a gefen ta ta karaso ta tsaya ita kuma dayar ta shiga cikin rami. Bayan ta shiga aka fara zuba mata kasa a ciki.
Abin da ta gane shine jefe matar za ai tin daga nan jikin ta yai bala’in sanyi.
Tana gani aka zo aka kulle mata idanun ta da bakin kyale wanda har aka rufe hancin ta amman ta saka hannu ta gyara. Haka aka dinga zuba mata kasar nan har aka rufe ta a cikin ramin iyakar kan ta ne kadai a waje amman tin daga wuyan ta kasa ta rufe shi ko motsi bata iyawa. 😢😭😭😭😭

Mutane ta gani sun fara jefa mata dutse suna fadin  “Allahu Akbar” ita kuma matar ba abinda take sai fadin “Lailaha illah Muhammad Rasulillah Sallahu Alaiyu wasalam.”
STORY CONTINUES BELOW

Abinda take ta fada kenan nan suka fara jefa mata duwatsun. Ido ta runtse hawaye na zuba a idon ta. Tafi second biyar a haka sannan ta hude idon nata. Gani tayi kan matar yana yawo sakamakon duwasun da ake jefa mata yasa har kan ya fara fita daga jikin wuyan ta. (Ya Salam 😭😭😭😭 Allah Allah kasa mufi karfin zuciyarmu. Allah Allah ka shirya mu ka kare mu ka shirya zuri’ar mu da alummat musulmai. Amin)

Ido ta kara rufewa hawaye na zuba a idon ta zuciyar ta na bugawa da karfi da karfi dan har rigar ta dagawa take. Tana bude ido taga Kan kwance a kasa. Ido ta runtse tana rufe bakin ta da hannu daya. A ranta take fadin
“Inna lillahi wainna ilaihir rajiun. Ya Allahu. Astagafurullah. Astagafurullah.”

Abinda take ta nana tawa a cikin zuciyar ta kenan. Hawaye na ta zuba a idon ta. Ta kurawa allon wayar ido bata ko kiftawa saboda yadda ta shiga tashin hankali,  fargaba,  tsoro dukka ita kadai.

Farisa na shiga dakin da Rabi’a ta shiga ta zauna gefen gado tana kallon Rabi’a da ke kallon allon wayar ta hawaye na zubo mata a idanun ta.
“Lafiya Rabi’ah!”

Farisa ta fada. Wayar hannun ta ta mika mata zata amsa kenan wayar ta ta hau kara Kawar ta Munasha ce ke kira ta wannan yasa ta amshi wayar hannun Rabi’a. Sannan ta dannan receive a tata ta kara a kunnen ta.
“Hello dear yane?”

Shiru tayi tana zaro ido tace
“Dan Allah fa gani nan gani nan.”

Ta mike da sauri tana ajiye wayar Rabi’a da ta bata duba abinda take nuna mata ba. Tace
“Bari naje na dawo.”

Tana fadar haka ta fita ba tare da ta kuma kallon ta ba. Rabi’a da hankalin ta yai mugun tashi. Tsigar jikin ta duk ta mike zuciyar ta ta girgiza duniyar ta tsaya mata. Sam bata gane a wane hali take ciki. Hawaye take na nadama da dana sani da tsoron Allah shin me ya kai ta shiga *Wannan Rayuwa* bata san lokacin da ta tashi daga inda take ba. Mayafi ta ta yafa ta dauki jaka ta fita a dakin idon ta na zubar da hawaye.
Da kallo Samira da Bilki suka bita. Bilki ganin zata fita tace
“Rabi’a lafiya?”

Kai ta hau girgizawa kawai ta fice a dakin. Tana fita Samira ta tabe baki tace
“Ita ta sani.”

Bilki yace
“Amman ya kamata muje muji komenene ko?”

“Ba inda zani. In wani abu ne ma Allah ya kara.”
Ta fada tana daukar wayar ta.
Mikewa Bilki tayi ta fita hango Rabi’a tayi tana tafiya kamar ba zata iya ba da gudu ta karasa ta sha gaban ta. Kaucewa Rabi’a tayi xata wuce da sauri Bilki ta kamo hannun ta. Bata juyo ba tace
“Wai Lafiya?”

Kasa magana tayi in banda hawaye ba abinda yake zubowa a idon ta. Mai Napep Bilki ta tsayar ta fada masa unguwar da Rabi’a take nan da nan suka shiga suka tafi.

Suna zuwa Rabi’a ta kifa kanta a bangon gidan. Bilki da jikin ta yai mugun sanyi ta amshi jakar ta ta dauko mukulli ta bude gidan sannan ta kamo hannun Rabi’a suka shiga.  Suna shiga Falo Rabi’a ta zube a kasan falon ta hade kan ta da gwiwa.

Zama Bilki tayi ta zuba tagumi ta zubawa Rabi’a idanu. Bata taba ganin Rabi’a na kuka ba to mutuwa akai mata kome? Rabi’a mutum ce mai hakuri da mutunci da saukin kai. Shin me yake faruwa?

“Dan Allah Rabi’a ki fada min mutuwa akai miki ne?”
Bata dago ba kuma batai magana ba. Haka Bilki ta gama tambayar ta amman taki tai magana daga baya Bilki ta mike dan ana ta neman ta tace
“To ni dai zan wuce Allah ya kiyaye.”
Bata jima da Fita ba aka kira sallah magariba. Rabi’a na a inda take ta mike tayo alwala sai a sannan ta tina batai sallah la’asar ba. Sallah la’asar tayi sannan ta tada sallah magariba bayan ta idar ta jawo wayar ta ta duba azkhar din da aka turo a group din *Indabawa Hausa Novels* tana gamawa ta kifa kan ta akan kujera ta kuma fashewa da wani kukan.
STORY CONTINUES BELOW

A zuciyar ta ba abinda take fadi ko yi sai istigifari na Allah ya yafe mata. Tsoro duniyar duk ya kamata shin in da a kasar da ake yanke hukunci ne itama haka za ai mata. Tana tina haka taji zuciyar ta ta kuma karyewa.
Lallai Zina Babbar masifa ce bama ace da auren ka kake yi. Me ya hau kanta har take irin *Wannan Rayuwar* bayan tasan illar abun. Shin da ta mutu tana aikata wanna abun taje ta cewa Allah me? Da wane ido zata amshi rayuwar ta a gobe kiyama? Me rayuwar bariki ta kara mata? Wane dadi taji a ciki? Bayan da ta gama take shiga kunxi da nadama amman me ya hau kanta?
Wadan nan sune abubuwa da take ta juyawa a ranta. Take ta fara tunanin rayuwar ta.

*
Sunyi auren soyayya ita da Mustapha wanda lokacin da sukai aure Mustapha ba wani kudi gare shi ba sai rufin asiri. Domin dinki yake yi dashi suke rufawa kan su asiri suna zaune lafiya cikin kwanciyyar hankali.

Da yake Mustapha yayi karatu har degree yayi wani abokin sa soja shi ya zo yace mai zai hana ya nemi aikin yaje ya kara shekara daya a bashi training tunda ana neman masu aiki.

Da yazo ya fada mata tayi murna sosai kyma ta bashi goyan baya wanda wannan shi yasa yaje yayi kuma cikin hukuncin Allah. Allah ya bashi sa’a suka dauke shi bayan an hora su.

Wannan shine mafarin komai domin a lokacin da aka dauke su can wata kasar iyamure aka tura shi wannan yasa yabtafi ya bar Rabi’a.

Tin da Mustapha ya tafi bai kara dawowa ba har sai da yai wata biyar kullum sai waya da turo mata kudi. Bata rasa komai ba na jin dadin ba sai dai rashin mijin ta a tare da ita.

Bayan ya dawo ya sameta nan suka shiga farin ciki ganin juna. Satin sa biyu ya fara shirin komawa abinda yasa Rabi’a a cikin tashin hankali kenan. Domin har ga Allah tana matukar bukatar mijin ta. Ita mace ce mai yawan bukata.

Haka ya lallashe ya tafi ya barta wannan tafiyar da yayi ba karamin wahala ta shiga ba domin har hakurin ta ya fara karewa. Dan watan sa bakwai bai dawo ba.

A haka ta hadu da Momy wata rana taje shopping. ATM din  Momy ne ya fadi a cikin jakar ta Rabi’a ta gani ta dauka ta kai ma. Nan Momy taji dadi har ta saka mata albarka anan ta biya mata kudin siyayyar da tayi duk yawan su. Tare suka fito Momy ta nufi Motar ta ita kuma ta nufi gate din fita daga Mall din. Momy ce tace
“Baiwar Allah!”

Rabi’a ta juya ta koma Momy tace
“Shigo na rage miki hanya mana.”

Ba musu ta shiga nan suka fita Momy ta tambaye ta unguwar ta fada mata har suka karaso kofar gidan Anan Momy ta amshi number itama haka sannan tai godiya ta tafi.

Tin daga lokacin suke mutunci da Rabi’a duk da Rabi’a a uwa ta dauke ta. Har chat suke yi.
Wata rana Rabi’a ta tashi da dare wajen sha biyun dare ta hau whatsapp dun ta. Tana gawa taga Momy Online nan tace
“Momy baki bacci ba?”

“Eh wallahi. Ke fa ina mai gidan?”
Rabi’a tace
“Uhmm ai baya nan.”

“Au kace gauruwa ce ke yau.”
Rabia’a tace
“Na jima a gauruwar ai Momy yau kusan wata bakwai fa”

Emoji Momy ta nuno na zaro ido wato tayi mamaki tace
“A haka kike zaune?”

“Eh Momy to ya zanyi?”
“Bakya dan samun me debe miki kewa?”

“Sai whatsapp Momy!”
“Wane irin whatsapp me zai debe miki. Ba zaki nemi wata tana rage miki zafi ba.”

Ido Rabi’a ta zaro tace
“Wata kamar ya?”

“Eh ki gane man.”
“Wai kina nufin lesbian?”

“Yauwah yar gari.”
“Allah ya tsare ni. Momy bakyau fa akan shi aka dilmiyar da alumma guda fa.”

“Ai baki sani ba kan mu mutu ba sai mu koma.ga Allah ba.”
Ido Rabi’a ta zaro tace
“Momy kinsan lokacin da zaki mutun ne?”

“To ya isa. Kije ki kwanta sai da safe.”
Momyn ta fada. Sauka Rabi’a tayi zuciya ta a tsorace da abinda Momy ta fada.

Tin daga lokacin bata kara kula Momy ba kuma Momyn ma haka sai da sukai sati sannan tayiwa Momy sallama. Momy ta amsa tace
“Ince Mijin ya dawo najiki shiru.”

“A’ah wallahi ya gida?”
“Alhamdulillah. Ya kike ya kadaici?”

“Lafiya.”
“Ba dai zaki samu me rage miki zafi ba ko?”

“Kai Momy nifa ba zan taba iya aikata Lesbian ba.”
“Naji in na samar miki namiji fa?”

“Kai Momy duk va kyau ai. Kuna cin amana ne.”
“To xauna ki mutu. Shi yana can yana sheke ayar sa. Kina zaton zai iya zama har na wannan tsawon lokacin ba tare da ya ji dadi ya biya bukatar sa ba.”

Shiru Rabi’a tayi tana tunani can tace
“Uhmm ni dai tsoro nake.”

“Ai shikenan ki tajin tsoro. Ni dai in iina neman taimako kya min magana.”
“Nagode.”

Sai da Mustapha yai wata tara sannan ya dawo. Wannan ma sunyi dadi kuma sun sha soyayya dan yayi wata daya da sati daya ya fara shirin tafiya amman Rabi’a ta saka masa kuka wannan ya tada hankali sa.
“Yanzu me kike so in bar aikin Baby?”

Kai ta girgiza tace
“Ni dai ka tafi dani.”

Zama yayi yace
“Baby ina wannan kokarin amman ki sani a halin yanzu mu kan mu ba a guda muke zaune ba. Yau muna can jejin gobe muna wani saboda yanayin rashin tsoron. Amman ki sani duk lokacin da mukai koma mazaunin mu nima dauke ki zanyi Baby nah. Baki san yadda nake kewar ki ba kullum cikin azumi nake ba dan bana son na kaucewa Allah kuma naci amanar ki.”

Hawaye ne ya hau zubowa a idon ta. Durkusawa yayi yana goge mata yace
“Baby indai aiki na na cutar dake wallahi na hakura dashi zan ajiye shi sai a nemi wani.”

Jikin sa ta fada tana kuka tasan Mustapha na son ta kuma tasan aikin na matukar rufa musu asiri ba abinda ta nema ta rasa sai kawai rashin mijin ta amman taci mai kyau tasha mai kyau ta kwanta a gu mai kyau ta sa sutura mai tsada sai yadda tayi da kudi.
Haka ya tafi a lokacin kuma Momy ta kara shige mata sosai dan bata da aminiyya sa ita. Haka ta dinga zugata.

Haka ya tafi a lokacin kuma Momy ta kara shige mata sosai dan bata da aminiyya sa ita. Haka ta dinga zugata har ita da kanta ta hada ta da wani babban Alhaji.

Rabi’a yadda taje jin ta a matse yasa ta bada kai bori ya hau. Ranar da ta fara bata iya runtsawa ba dan tsoro da fargaba ta dinga neman yafiyar Allah kuma tayi nada cewar ba zata kara ba.
Kwana tayi sallah da rokar Allah ya yafe mata. Washe gari haka ta yin wani iri. Amman Momy ta dinga zuga ta da mata hudubar tsiya a haka har Rabi’a ta yadda ta cigaba da hakar tayi tsamo tsamo a ciki.
Wanda sosai takejin dadi da samun kudi duk da ba dan kudi take ba kuma wani abun a duk lokacin da ta je ga wani ranar bata bacci sai rokar Allah ya yafe mata ya shiryata take.
In mijin ta ya dawo kuwa ko waje bata fita in ba tare zasu fita ba. Kuma sosai yake samun kulawa. Haka rayuwa ta dinga tafiya sai dai sam bata yadda ta dauki ciki ba dan tace in ta dauka bata san na waye ba dan haka ba zata shigar da dan shege cikin zuri’ar ta ba bare abin ya kara zama mata tashin hankali.

*
Juyi tayi akan gado tana me fashewa da kuka. Tabbas a yanzu ba zata kara biyewa rudin zuciya da shawarar Momy ba. Ta bar harkar nan ta har abada.

A haka ta mika komai ga Allah bata da abin yi sai rokar Allah ya yafe mata yini take zaune akan sallaya daga tayi sallah sai karatun alkur’ani.
Cikin kwana biyu ta rame tayi baki. Wayar ta gaba daya ta kashe ta ta daina kunnawa bare a dame ta.

Satin ta daya da ganin wannan abun tana zaune ta kunna wayar ta. Irin sakonnin da taga an turo mata ya bala’in kona mata rai. sai na mijin ta da yake ta tambaya lafiya wayar a  kashe.

Mikewa tayi ta cirw Sim din bayan ta dauki wasu numbers din. Wani sim da bata amfani dashi ta saka ta karya wamcan.

Sabon Whatsapo ta adaura da sabuwar number. Mijin ta tai wa text sannan ta dauki number Maryam S Indabawa tai mata magana cikin ikon Allah kuwa tana online wannan yasa tace
“Sister Rabi’ah ce please ina son ki sakani a Indabawa group na canja number ne.

“Ok ba damuwa.”
Nan da nan tai adding nata. Sauka tayi tana mai dage kanta dan duk lokacin da ta tuna dan irin abinda ta aikata ita kanta kunyar kanta take.

Tana zaune Mustapha mijin ya kira ta. Dauka tayi tai sallama cikin sanyin murya.
“Assalamu Alaikum!”

“Wa’alaikum salam Baby ina kika shiga kwana biyu duk hankali na ya tashi.”
Hawayen idon ne ya hau saukowa ta goge tace
“Wayar ce ta fadi na canja wata.”

“Amman Baby har sati kika dauka baki canja ba ko ba kudi a gun ki?”
“A’ah!”

“Why to? Kinsan halin da na shiga kuwa.”
“Am sorry.”
Ta fada a sanyaye.

STORY CONTINUES BELOW

“Anjima zan karaso dan na riga na dau hutu hankali na ya tashi ban taba kwana daya ban ji muryar ki ba amman yau kar sati dole yasa na taho ina hanya.”
“To sai ka karaso”

Nan ta mike ya  hau gyaran gidan nan da nan ta gama dan gidan daman a gyaran sa yake kitchen ta hada masa abincin da yafi so sannan ta shiga ta caba wanka tai ado cikin wata shaddar ta da akai wa dinkin three quarter da pencil siket. Tai kyau ta saka gold a kunne da wuyanta da hannun ta tai daura dauri tai kyau da ita kamar ka sace ka gudu.

Sai daga kallo daya zaka gane tana cikin damuwa sosai. Tana zaune ta kasa cin abinci ta zauna. Kayan kallo t kunna amman tunanin ta gaba daya baya wajen
Tana zaune kawai taji an rufe mata ido ta baya da sauri ta mike tana juyowa tana ganin sa ta daka wani uban tsalle ta dane sa tana fasshewa da kuka.
Sosai jikin sa yai sanyi yasan in ya dawo tana danne sa wani lokacin har da kuka amman na yau ya bambanta da na kullum dan na tanayi tana murmushi hadi da kissing nasa amman na yau kukan take bil hakki da gaskiya. Gashi tai lamo a jikin sa ko dan kiss din nan babu
Wannan yasa ya zagayo suka zauna akan kujera ya dago kanta yana fadin
“Ya dai Baby na me yake faruwa ne?”

Kan ta ta kara kwantar wa a jikin sa tana kamkamshi. Fadi take
“Dan Allah Honey kada ka kara tafiya ka barni dan Allah.”

Bayan ta yake shafawa a hankali yace
“Insha Allah ba zan kara ba. Menene?”

Kai ta girgiza yace
“Amman kin min kwalliya kuma kika bata min ita”

Kai tayi kasa dashi. Yace
“No special kiss kuma.”

Dagowa tayi tana kallon sa. Ya sakar mata murmushi itma murmushin tayi a hankali ta hade bakin su tana bashi sumba ta musamman.

Daga nan suka shige daki. Bayan komai ya kamalla tare sukai wanka suka fito ta dinga basa abinci a baki yana ci yana santi. A haka suka gama suka koma falo.

Kwance take a jikin sa yana shafa gashin kanta tace
“Honey dan Allah ka yafe min!”

“Me kikai min Baby?”
“Ni dai ka yafe min.”

“Baki da damuwa na yafe miki kome kikai min da wanda na sani da wanda ban sani Allah ubangijinya yafe mana gaba daya. Nima ki yafen.”
“Ba kai min komai ba.”

“Nagode.”
Nan ya sumbace ta. Yana matse ta a jikin sa. Hannun sa ya saka a kan cikin ta yana fadin
“Gaskiya ina son naga Ya’yan Baby nah.”

“Allah kawo masu albarka.”
“Amin. A yau nake son nayi ajiya ta wannan cikin naki ina fatan kina maraba dani.”

“A ko da yaushe u re welcome Honey.”
“Thnaks u Baby na i love u so much.”

“I love u more.”
Kallon ta yake ta dago suna hada ido ya kanne mata ido daya da sauri tai kasa da kanta tana murmushi.

*
*
*
*
Sakina kuwa ta gama zama yar kanta in kaga yadda tai kyau ta kara zama fara gashi ta ciki saboda cima da mayukan da take shafawa ba zaka ce Sakinan da ka sani bace.

Ta amshi Lesbian sosai dan har waje take fita Hajiyar ta dai har yanzu suna tare dan duk inda take indai ta kira ta zata amsa gayyatar.

Sun shaku. Soyayya suke sosai kamar ba gobe wanda har mijin ta yasan Sakina sai dai tace masa yar kawar ta ce dan haka bai damu ba. Kasancewa ba mazauni bane. Ya’yan ta biyu maza duk suna kasar waje suna karatu wannan yasa in miji baya nan daga ita sai sakina sai abinda suka ga dama suke aikatawa a cikin gidan.

Sakina bata da damuwa tayi bubul da ita ko gida bata zuwa sai dai ta bada sako a kaiwa Umman ta. Wani lokacin suna dan gaba wata da Fauziyya da Farisa.

STORY CONTINUES BELOW

Zaune suke a falon Hajiyar ta sam basu san da zuwan wani ba sai sallamar sa suka ji. Da sauki Sakina ta mike zaune tana gyara rigar ta. sai da suka amsa sannan ya shigo.

Saurayi ne kyakyawa dashu dogo da ka gansa zaka zata black american nan ne. Yana sanye cikin black colour suit yai kyau dashi kafar sa sanye cikin sau ciki shima baki. Hannun sa daya rike da trolly din sa dayan kuma wayar sa ce rike a hannun. Yana shigowa dakin kamshin turaren sa ya ciki dakin.

Hajiyar na ganin sa ta mike tana fadin
“Son daman kana hanya baka fada min ba bare na sa a zo a dauke ka.”

Tin da ya shigo idon sa ke kan Sakina. (Na fada muku ya’yan gidan su Sakina Fulani ne dan haka kyawawa ne dan sai dai baka gansu ba ga shiga rai.

Maganar Hajiyar sa da yaji yasa ya juya yana kallon yana shafa gashin kan sa  sannan yace
“Wallahi Mom i just want to give u a surprise ne.”

“Amman bana ce maka bana so. Meyasa bakaji. Yanzu in ka taho something wrong happen fa? In na sani ai za muna communication ko?”
“Yes am sorry Mom.”

Sakina ta kalla dake tsaye a wajen tace
“Shiga ciki Sakina.”

Da sauri Sakina tayi ciki gaban ta na faduwa dan tinda taga Khaleel ta tsinci kanta da faduwar gaba dan gaka tana shiga ta fada saman gado.

Da kallo Khaleel ya bita har ya shige Hajiyar dake kallon sa gaban ta ya fadi tace
“Lafiya?”

“Mom who is she?”
Ya tambaya. Ido ta zaro tana fadin
“Allah yasa dai bai taba ganin ta a yawace yawacen ta ba.”

“Yar kawata ce tazo tana deben kewar zama ni kadai.”
Hajiyar ta bashi amsa tana mikewa tace
“Muje ka watsa ruwa nazo na samar maka abinda zaka ci. Ai ga irin ta nan da ka fadan zuwan ka ai da tini yanzu na samar maka abunda kake so amman dole yanzu kayi manage da wanda zaka samu.”

Murmushi yayi yace
“Hakan ma nagode Mom.”

“Ina dan uwan naka?”
“Yana nan yana gaishe ki. Nima na dauki hutu ne na gaji da can nace bari nazo gida wannan karan a gunki zanyi hutu.”

Duk da taji dadi amman kuma tasan dole zata rage hulewar da take yi dan haka suna shiga part din sa ta juyo tayi dakun da Sakina take

Kwance ta samu Sakina. Tana shiga ta bude ido tace
“Hajiyar waye wannan?”

“Shine babban ‘dana.”
“Oh!”

“Dan Allah Sakina ki kula bana son kiyi abunda zai gane wacece ke. Na fada masa ke yar kawata ce kinji.”
Kai kawai Sakina ta gyada.
Hajuyar tace
“Taso muje mu samar masa something light kinsan Jamila bata nan.”

“Ok!”
Ta mike sukai kitchen. Fried supergette suka dafa masa da lemon kwakwa sai pepper chicken da hadin salad.

Sakina na ajiyewa akan Dining ya shigo falon. Tana ganin sa tayi kasa da kai ta ajiye ta juya ta zata tafi taji yace
“Hae Sis!”

Juyowa tayi kan ta a kasa gaban ta na faduwa ta dan durkusa tace
“Ina yini?”

“Lafiya lou. Am Khaleel Muhammad and u?”
“Sakina Khamis!”

“Nice to meet u Sakina ya gida ya karatu da Maman ki?”
“Alhamdulilah.”

“Gud zo kiyi serving nawa mana.”
Ya fada yana zama akan kujera nan ta fara zuba masa abincin da kamshin sa ya cika dakin ido ya lumshe ya bude ya sauke akan Sakina dake zuba masa abincu. Kallon ta yake ba ko kiftawa har ta gama ta miko masa dagowar da zatayi suka hada ido da sauri ta saukar da kanta ta juya zata tafi.

“Hae come let eat!”
Kai ta girgiza tace
“Am ok!”

“But ai da kin zauna munyi hira ina cin abincin ki deben kewa ko?”
“Aiki zanje nayi ne.”

“Ok tnc!”
Ya fada yana yin bismillah ya fara cin abincin yana ci yana lumshe idon sa.

Daki ta shige da sauri tana sakin ajiyar zuciya. Zuciyar ta ta dafe da har lokacin ke bugawa. Hajiyar ce ta shigo tana kallon ta tace
“Lafiya?”

Kai ta girgiza ta koma ta zauna tace
“Ba komai.”

“Kin tabbata?”
Ta tambaye ta.

Kai ta gyada kawai ta zauna a bakin gado tana daukar wayar ta.

Fita Hajiyar tayi ta koma falo tana girgiza kai.

*
*
*
*
Mama ce zaune rabon ta da bara tin da ta ga gawar Halifa wanda a yanzu kwana goma kenan. Shin ita me Bara ta kara mata ta rasa ya’ya biyu ta dalilin bara.
Na farko yai hatsarin mota ya mutu dayan kuma gashi an dauke shi an cire masa wasu sassan jikin sa. shin ya me bara ta kara mata. Nawa ta sama a barar da ba zata siya mata yaran ta ba.

Hawaye ne ya zubo mata domin *Wannan Rayuwar* da suke ciki duk Mijin su shi ya jefa su a ciki. Na farko Ita bara take fita Samira wa yasan inda take zuwa amman tayi kudi. Ga Jummai mahaifiyar su Fauziyya da yaushe rabon da ta ganta. Haule Allah yai mata rasuwa banda wasu matan da suka bar gidan.

Lallai rayuwar gidan nan nasu rayuwa ce mai ban tsoro. Duk Alhaji yaki ya dauki nauyin su gaba daya kowa ya kama hanyar gaban sa.
Ga Fauziyya da tana samun yanzu ta dawo ko fita batayi haka Hafsa. Sai Farisa da Sakina ne yanzu ke nema. Auwal babban dan gidan sai walagigi. Ishaq kuma.ya fara shaye shaye. Duk yaran gudan ba wanda zaka daga ka nuna kace yau yayi karatu ko wani abu.

Hakika a yanzu tana ganin aibun barar da suke kuma har tana kyamatar ta shin me ya hana ta zauna ta nemi kudi a gida ta biyewa kawar ta gashi nan ta kai ta ta baro ta tayi asarar yara biyu a *Sanadin Bara*
Tagumin ta dauke tana kallon dakin da take cikin ko leda babu bare labule. Duk dakin yai wani iri dashi. Tsakar gidan duk sumuntin ya fashe sai kasa.

Shin yanzu ina mafita wane sana’a zata nayi? Shine abinda take ta juyawa a zuciyar ta.

Karfe tara ya iso soron gidan. Wani yaro ya gani zai fito yace
“Abokin na dan Allah kaje kacewa Baba ana sallama dashi a waje.”

Bai jima ba yaron yazo yace
“Wai yace inji wa?”

“Kace masa Muhammad ne.”
Nan yaron ya koma. Tare da Baba suka fito Baba yana ganin sa ya washe baki yace
“Ashe kai ne bismillah.”

Suka shiga ciki. A falon Baba ya zauna a kasa. Kan sa a kasa yace
“Ina yini?”

“Lafiya Alhamdulilah ya Manyan?”
“Suna Lafiya.”

“To Madallah.”
Kan Muhammad a kasa yace
“Baba daman nazo tafiya da Fauziyyar ne.”

Baba yace
“Ai ba matsala bari na saka a kira ta sai ku wuce.”

Nan Baba ya mike ya fita yana kwalawa Yaya Babba kira
“Sa’adatu! Sa’adatu!! Sa’adatu!!!”

Yaya Babba dake daku ta fito da sauri tana amsawa da
“Na’am Alhaji Lafiya?”

Ganin har ya koma daki yasa ta shiga. Ganin bako a zaune ta samu waje ta zauna. Muhammad kan sa a kasa yace
“Ina yini Baba?”

“Lafiya lou!”
Ta amsa tana kallon mai gidan nata.
“Wannan mijin Fauziyya ne. an daura dauren goma da suka wuce daman munyi dashi zai zo ya dauke ta to Allah ya kawo shi. Ki shiga ki kira ta sai tazo su tafi.”
Kallon Alhaji ta tsaya yi baki bude yace
“Baki ji bane?”

“Naji Alhaji Amman ai da ka fada tin wuri an kintsa ta ko? Kuma ai ya kamata muma mu rakata muga gidan nata ko?”
“Ke zaki fadan abinda zanyi. In ba zakije ki kirata ba sai ni naje da kai na.”

“Allah baka hakuri.”
Ta mike ta fita tana jimamin abun. Dakin ta ta shiga ta tadda Halima da Hajara na zaune tace
“Ku taso kuje kuyiwa Yayar ku sallama zata tafi.”

“Ina?”
Suka hada baki suka tambaya a tare. Mama tace
“Gidan mijinta.”

Da mamaki Halima tace
“Gidan mijin ta kuma yaushe aka daura auren.”

“Hmm yanzu Alhaji ke fadain. Anyi sati ba da daura auren amman ya kamata dai ya fada mana a dan mata wani abun ko?”
“Gaskiya dai!”
Hajara ta fada.

Mikewa sukai suka karasa dakin Umma. Fauziyya da Hafsa zaune a daki duk sunyi jugum jugum bama Fauziyya da zuviyar ta ke ta bugawa. Hafsat kuma jimamin kewar yayar ta take.
Mama ta shiga dakin da sallama tana fadin
“Fauziyya! Alhaji ne yace nazo na fto dake za a tafi dake gidan mijin ki.”

Hafsat ce ta rumgume Fauziyya sai suja fashe da kuka haka Hajara da Halima suka taho suma suka rumgume su suna kuka rabuwa. dan duk gidan Fauziyya ba ruwan ta kowa nata ne tana son yan uwan ta.

Sun jima suna kukan Mama na tsaye tana kallon su itama sai taji duk babu dadi dan haka tace
“Ku taso an bar yaron acan fa.”

Kasa mikewa Fauziyya tayi. Tana kuka ta tunanin rayuwa. Wai daman haka ake aure ba yan war uwar ta bare na uban ta. Bama wannan ba uwar ta na da rai amman ji bata san a halin da suke ba. Tana can yawon duniya. Oh ita kam taga rayuwa. *wannan rayuwar* sam batai mata ba.
STORY CONTINUES BELOW

A haka Mama ta dago ta. Hafsat ta dauko manyan akwatin ta biyu Halima ta amshi daya Ita kuma tana jan daya. A tsakar gida suka tsaya Mama da hannun ta ke rikw da na Fauziyya tana kuka suka shiga dakin.

A kasa ta zaunar da ita gefen Muhammad sannan tace
“Gata nan Alhaji.”

“To Fauziyya kamar yadda na fada miki yau ga mijin naki nan yazo zai tafi dake dan haka Allah ya kiyaye hanya”
Ya kalli Muhammad yace
“Ga matar taka nan. Shikenan ko?”

Kai Muhammad ya gyada yace
“Angode Baba Allah ya saka da alheri.”

Ya zura hannu a aljihu ya zaro bandir din 1k guda uku ya ajiye yace
“Nagode Allah ya saka.”

Baki Baba ya washe yana fadin
“To madallah. Ai sai ku tafi ko?”

Muhammad ya mike Fauziyya kan na zaune kan ta a kasa ta kasa mikewa. Ji wai a haka za a tafo da ita ba ko fada bare saka albarka. Wannan ya karasawa ta saki kuka tana inda take tace
“Baba ka yafe min.”

“Ba komai Fauziyya baki min komai ba. Allah ya yafe mana baki daya.”
Kuka ta kuma fashewa dashi wato dai Baba ko sau daya ba zai saka mata albarka ba.
Mama ce ta daga ta tana fadin
“Haba kukan ya isa haka mana.”

Suka fita Muhammad yabi bayan su. Suna fita sakar gida yan uwan suka yo gunta suma suna hawaye. Mama na lallashi su. A haka suka fita.

A bakin wata mota suka samu Muhammad. Suna fitowa ya bude mata gidan gaba aka saka ta sannan ya bud boot aka saka akwati nan ta. Mama yai wa godiya ita ma ya mika mata bandir din 1k guda daya ta amsa tana juya kudin gami da godiya.

Hafsat kuwa na jikin Fauziyya tana kuka itama an rasa mai lallashin wani. A haka Mama tazo ta janye ta sukai ciki shi kuma ya rufe motar ya zaga ya shiga bangaren driver.

Motar ya tayar ya dau hanyar titi duk da gidan a cikin unguwar yake. Fauziyya kuwa ta kufa kanta akan cinyar ta tana kuka mara sauti. Mamaki take wai yau ita ce tai aure ikon Allah.

A haka taji yayi parking ya fita. Bata dago ba. Har ya dawo hannun sa dauke da manyan ledoji sannan ya saka a bayan mota ya tada motar suka bar wajen.

Gidan sa ya nufa da ita. Gida ne karami mai daki biyu da bandaki da kitchen sai dan tsakar gida.
Yana parking ya fito ya bude mata kofa sannan ya bude kofar gidan ya shiga da ita. Afalon sa madaidaici mai dauke da center karfet da kujeru na karfe sai kayan kallo da labulaye dakin sai kamshi yake kamar na amaren dai.

Akan kujera ya ajiye ta sannan ya juya  da sauri ya koma mota ya dauko akwatunan ta ya shigo dasu ya kai su bedroom din su. Sannan ya koma ya dauko wasu ledojin da ya shiga dakin dasu.

Sai da ya gama shigo da komai sannan ya koma ya rufe kofar ya shigo gidan shima ya rufe shi.

A inda ya xaunar da ita ya same ta ta hade kai da gwiwa tana ta kuka. Zama yayi a gefen ta ya janyo ta ya rumgume ta tsam a jikin sa yana fadin
“Haba Baby nah menene na kukan kuma ehee? Kada ki manta gun masoyin ki fa kika zo ba kuma hakan na nuna cewa kin bar gidan ku bane har abada. Ko gobe kika so kije zakije dan haka to menene na kuma ehumm? Please ki daina kukan ki tsaya ki fuskanci sabuwar rayuwa wacce zaki samu farin ciki a cikin ta na har abada insha Allahu. Dan Allah ki daina kukan nan wallahi in kina kukan nan har cikin zuciya ta nake jin sa. Am sorry nasan ba dadi amman please ki daina kinji.”

Kukan tane ya tsaya cak jin dadan kamalan sa da yake mata da kwantar mata da hankalin ta. Ga ta taji ta a jikin sa kamar zai mai da ta cikin jikin sa. Wannan ya haifar mata da sanyin jiki ya karasawa tai shiru.

Sun jima a haka yana shafa bayan ta a hankali. Sannan ya dago ta yace
“Taso muje muyi alwala muyi sallah ko?”

Ya kamata hannun ta suka fita. Alwala sukai suka dawo daki sannan ya shimfidda musu sallaya ya jata sallah. Raka’a biyu suka yi sannan yai musu addu’a bayan sun idar ya juyo ya kalle ta ya dafa kanta yana mata addu’a sai da ya jima sannan ya dago yana kallon ta. Tambayoyi yai mata akan addini wanda duk ta bashi amsar su.

Mikewa yayi ya dauko kayan da shigo dasu sannan ya shiga kitchen ya dauko plate da cup. Zama yayi ya bude hadin kazar da aka hada da dankali da kayan hadi. Sannan ya siyayya masu fresh milk a cup. Nama ya tura mata gaban ta yace
“Bismillah!”

Kai ta girgiza. Murmushi yayi ya dauka yayi wajen bakin ta yana fadin
“Please Honey!”

Ya fada yaba langwabar da kansa hadi da lumshe idon sa. Wannan yasa ta lumshe idon ta sannan ta bude bakin a hankali saka mata yayi ta yagi kadan. Dadin ta yasa ta lumshe ido sannan ta tauna a hankali. Idon sa a kanta yana kallon yadda take taunar sai ta burge shi. A haka ya dinga bata kanta a kasa. Har ta koshi ya bata madarar ta sha sannan shima.ya danci ya kwashe ya kai kitchen.

Mikewa yayi ya fita ya hada mata ruwan wanka ya dawo ya zauna a gefen ta yace
“Ki tashi kiyi wanka ko?”

Mikewa tayi a hankali. Ya shiga daki da sauri sabon towel ya dauko mata da toothbrush ya mika mata. Ban dakin ta nufa ta sama ya hada mata ruwan wankan.

Wanka tayi ta fara ta gama ta wanke bakin ta. Sannan ta fito daure da towel a jikin ta ta rufe jikin ta da babban mayafin da ta rufe jikin ta.

Tana shigowa dakin ya fita shima dan yayi wankan. Bata shafa wani mai ba kayan baccin ta kawai ta saka riga da wando wanda suke sabbabi a tafiyar da tayi ta siyo su masu kyau dasu sun mata kyau a jikin ta.

Turaren ta ta shafa ta dauki Hijab ta saka sannan ta zauna a gefen gadon tana bin dakin da kallo. Gado be madaidaici da wardrobe da dressing mirror sai labulaye kasan dakin an shimfida masa leda.
Tana zaune ya shigo daure da towel a kugun sa. Kanta tayi saurin daukewa. Mai ya shafa ya saka kayan baccin sa sannan ya feshe jikin sa da turaren sa mai dadin kamshi.

Kan gadon yayo ya zauna a kusa da ita ya fara kokarin cire mata hijab yana fadin
“Bakya jin zafi ne.”

Kafada ta make. Yai murmushi bayan ya cire hijab din da ido ya bita da kallo yadda tayi kyau da ita cikin kayan baccin. Cream kala ne sun mata kyau kuma a kirjin rigar duk net ne ana ganin kirjin ta duk da da bra a jikin ta.

Kanta a kasa ta ja baya ta kwanta. Ido ya lumshe yana mai sakin murmushi yace
“Ai ba kwanciyya zaki ba kin manta me na fada miki dazu zan fada miki dalilina na  dauke kafata a gidan ku ke kuma sai ki fada min i love u cikin daren nan.”

“Ni dai na yafe ba sai ka fada ba.”
“Sure!”

Ya fada yana dago ta yana fadin
“Ni ban hakuri da fadar min I love u din da zaki ba. Am all ears…”

Ya fada yana kama kunnen sa. Ta dan marairaice masa fuska tace
“Ni to bacci nake ji.”

“Haba amarya tah since now. Ai na zata yau kwana zamuyi muna shan soyayya.”
Ido ta rufe da hannun ta tana murmushi. Matsawa yayi ya rumgumota jikin sa yana sakin ajiyar zuciya. Sannan yace
“I really love u Baby. I love u so much.”

Ido ta lumshe ya hau gadon ya kwanta sannan ya janyo ta jikin ta ya rumgume ta kamar zai mai da ta a cikin jikin sa. Ido ta lunshe a hankali ya dinga shafa mata bayan ta yana fada mata kalamai masu dadi da narka zuciyar. Wanda take jin ta kamar bata da wata damuwa. Wani sanyi take ji yana shiga cikin zuciyar ta tare da jin son Muhammad na kara shiga zuciyar sa.
A haka bata san lokacin da bacci ya dauke ta ba. Muhammad ma idon sa a lumshe wani dadi da farin ciki ya cika zuciyar sa yau dai gashi ga Fauziyya ta zama matar sa.
Da kyar bacci ya dauke shi yana rumgume da Fauziyya kamar wanda za a kwace masa ita. Ranar wani bacci mai dadi ne ya dauke sa. Itama baccin take cikin kwanciyyar hankali ta wanda rabon ta dashi ta jima.Ummu ce zaune gaban ta peppersoup ne da Anty Zainab tai mata sai wani cup da aka markada kankana aka zuba mata madara da zuma.

In kaga Ummu yadda tayi haske ta kara cika fatar ta kamar ka taba jini ya fito tayi kyau sosai dan tin da ta gama exam ba inda take zuwa ta dauki hutu a gun aikin ta. Kamshi na daban jikin ta ke fitar wa saboda tsumin turaren da ake mata da gyaran amare

Bowl 🍜 din da pepper soup din ke ciki ta ja ta fara ci kamar bata son taci. Anty Zainab ce ta shigo hannun ta rike da cup 🍵 wanda ta tsumi ne a ciki sai tashin kayan kamshi yake. Tana ganin Anty Zaunab ta bata fuska tace

“Amman Anty ni ina zan kai dukka wadan nan?

“Cikin ki kuma na fada miki har romon ki shanye shi tas kinji ko?”

Fuska Ummu ta bata tace

“So kike na zama narkekiya ko?”

“A’ah so nake kawai ki rikita Muhammad!”

Kai Ummu tayi kasa dashi. Anty tai murmushi ta ajiye tace

“Ki maza ki cinye mai gyara na nan zuwa.”

Fuska Ummu ta kara batawa bata ce komai ba. Kadan taci pepper soup din sannan ta dauki hadin kankanar ta sha ta ajiye. Ji tayi cikin ta yayi masifar cika har kirji dan haka sai ta dauke tsumin ta ajiye a karkashin gado sannan ta rufe sauran papper soup din ta fita da cup din da ta gama dashi. Dauraye shi tayi sannan ta ajiye a mazaunin sa.

Daki ta koma ta fara cire riga dan wanka zatayi sai jin wayar ta tayi tana kara dauka tayi taga mai kira sai ta saki mumushi ta kai wayar kunnen ta.

“Assalamu alaikum!”

Ta fada cikin muryar ta mai dadi da kwantar masa da hankali.

“Wa’alaikum salam My wife ya kike ya gida?”

“Alhamdulillah ya kake?”

“Lafiya. Ya shirye shiryen tarbar mijin ki?”

Murmushi tayi tace

“Ni ba wani shirye shirye da nake?”

“Really?’

Ya tambaya shiru tayi yace

” kenan ni ba aji dani da ba za ai min shirye shiryen tarba ta na ko? Ni kam nan ina nan ina ta dauki da Allah Allah jibi tayi na taso. Ni kam wane irin bakin jini gareni yayar taki kanwar ma ga alama nan.”

“Kai Yaa Muhammad ni na fada maka bana son ka.”

“Ga alama nan!”

“Wannan ba alama bace ka dawo mana mu xauna a gida daya anan zaka shaida da abinda ni bazan iya fada maka ba!”

“Saboda me?”

“Kunyar ka nake ji.”

Murmushi yayi yace

“Ummu kenan. Acan din ma kunyar ce zata hana ki ki min abinda zai sa na tabbatar. Ki saka a ranki da zuciyar ki ni mijin ki ne kuma sirrin ki wanda baki da kamar sa to daga nan zaki samu ki saki jikin ki dani. Dan Allah a dan rage kunyar nan kada ta cutar da mijin nan naki. Ni ban da buri da ya wuce nazo naga Ummu na kwana nake mafarkin ki na yini tunanin ki ina son ki Ummu ban san lokacin da son ki ya gama cafke min zuciya ta. Nai miki alkawarin faran ta miki a ko wanne hali Ummu. Abba uba ne a guna wanda lokacin da ya banke ban yi zaton zan so ki ko zaki kula ni ki amshi auren mu. Sai abun ya ban mamaki duk da nasan wacece ke sam halaiyar ki ba irin ta Rukayya bace. Ke yarinya ce mai hakuri da nutsuwa da amfani da ilimin ki. Tin ina auren Rukayya nasan da wannan lokacin da xaki kira kina ban hakuri akan abinda tai min banda zuwa gaishe da Hajiya ta da kai mata alherai ni kai na baki kyale ni ba haka nan yar mu yadda kike sonta da yiwa mahaifiyar ta nasiha. Ummu tin a lokacin na fara jin wani abu a tare dake da na rasa ko na menene. Daga baya da na zauna na fara wadan nan tunanin naji na kara aminta dake da nustuwa da auren da Abba yai  min dake. Ta bangare na baki da matsala dan sai abinda kike so zan miki dan haka ki kwantar da hankalin ki Ummu. Ina sonki a cikin zuciya ta. A kwanakin nan na fara wani tunani wallahi Ummu tin kan na ce ina son Rukayya a rayuwar mu kike burge ni da ban sha’awa saboda yadda kike daban a cikin yan gidan ku. Sai da na auri Rukayya take kara bani labarin kyawawan dabi’un ki. Hakika ke macen da za ai alfahari da ita ce. Kuma Allah miki albarka ya bani ya’ya masu irin dabi’un ki Amin. Ina son ki ummu har ban son iya adadin sa ba. Wallahi ban tabai wa wata ko wani irin son da nake miki ba a yanzu. Ina son ki Ummu kece hasken idaniyya ta.”

STORY CONTINUES BELOW

Wani sanyi da nutsuwa taji suna shigar ta dan haka a hankali tace

“Nima haka Yaa Muhammad!”

“Kema me?”

Ya tambaya duk da yasan me take nufi. Kan ta bashi amsa Anty Zainab ta shirgo kallon Ummu ta tsaya tace

“Wai baki wankan ba gashi har mai gyaran tazo.”

Idon ta da ta lumshe tai saurin budewa tana fadin

“Yanzu zanyi.”

Juyawa Anty Zainab tayi Yaa Muhammad yace

“Kije kiyi wankan Ummu amman kan ki tafi ki ce min kina sona dan Allah.”

Ido ta runtse yace

“Please!”

“Ina son ka Yaa Muhammad!”

Tana fada ta katse wayar tana sauke ajiyar zuciya. Wayar ta ajiye ta shiga tai wanka ta fito ta saka wata yar doguwar riga dannan ta fita.  Daki guda Anty Zainab ta ware na gyara Ummu wanda yau kusan sati uku kenan ana mata dan nan da kwana biyu zasu wuce kano dan Muhammad ma yana hanya a gata zai sauka.

Sai da matar ta bata madara ta sa kan a tara sannan aka fara ta murje ta ta turare ta wanda kamshin har ya kama jikin ta. Sannan aka gama madara shima ta kara bata ta sha sannan ta hau wani bangaren na gyaran ta kwaba mata madara da wani magani ta bata. Ummu na bata fuska ta sha.

*

**

***

****

*****

******

Asubar fari Fauziyya ta farka sai dai jikin ta kane kane a jikin Muhammad yasa ta kwantar da kan ta kawai. Kallon sa take cikin so da kauna tana karewa fuskar sa mai kyau kallo. Gaskiya Muhammad kyakyawa ne na karshe.

Abinda bata sani ba tin motsin ta na farko shima ya farka dan haka yana kallonnta ta kasan ido yadda take kallon sa ba ko kiftawa. Batai aune ba sai kawai gani tayi ya bude idon sa gaba daya. Saurin runtse idon ta tayi.

Murmushi ya saki sai kuma ya kai wa lips din ta kiss nan da nan ta bude ido. Kallon juna suka tsaya yi. Idon ta ya sumbata yana fadin

“Kin tashi lafiya?”

Wani yarr taji saboda yadda ya zura hannun ta ta kasan rigar ta kokarin mikewa ta fara ya kara makale ta dole ta lafe a jikin sa ta na mai lumshe idanun ta.

Habar ta ya dago yana kallon kyakyawar fuskar ta. Idon ta sai motsi yake. Batai aune ba sai kawai jin bakin sa tayi a cikin nata. Abinda ya matar mata da jiki kenan ta kasa ko da kwakwaran motsi ne.

Yadda yake kissing nata yasa duk wata gaba dake jikin ta saki ya jima yana tsotsar bakin ta sai kace wanda ya samu sweet. Jin ana kiran sallah yasa ya zame bakin sa ya daura kan sa a kirjin ta yana maida ajiyar zuciya.

A hankalin ya zame jikin sa daga nata sai tai saurin juya masa baya tana boye fuskar ta. Fita yayi ya daura ruwa sannan shi ya shigan yai wanka da ruwan sanyi. Yana fitowa ya juye mata ya hada mata sannan ya kai bandaki.

Dakin ya dawo ya same ta a yadda take. Dago ta yayi yana fadin

“Muje nai miki wanka kada mu rasa sallah ko?”

Ya fita da ita suna zuwa bakin ban dakin ta tsaya kallon ta yayi yace

“Ya dai?”

Kan ta a kasa tace

“Kaje kada ka rasa jam’i.”

“Ki bari nai miki wankan ko na rasa ai mayi tare.”

Kafada ta make tana fadin

“Uhmm uhmm ni dai!”

Murmushi yayi yace

“To naji shiga kiyi.”

Da sauri ta shige ya bita da kallo sannan ya koma daki. Jallabiya kadai ya saka sannan ya fita da sauri bayan ya rufe gidan.

Tana fitowa ta yi alwala sannan ta shiga daki. Doguwar riga ta saka ta zura hijab ta tada sallah. Ta jima akan sallaya tana addu’a akan Allah ya daurar da zaman lafiya a tsakanin ta da mijin ta. Sai da ta gama addu’a ta mike ta hau kan gadon kan kace me har bacci ya dauke ta.

Sai shida da rabi ya dawo gidan kamar yadda ya zata bacci take dan haka ya hau share falon ya fito ya share tsakar gidan ya wanke ban daki. Dankali ya fere ya soya sannan ya soya kwai. Ya daura ruwan tea. Yana gamawa ya kai komai daki sannan ya koma ya kara wanka ya shiga dakin.

Gun kayan da ya nufa ya dauki wata shadda milk kala ya saka ya feshe turare a kam dakin ya dumame da kamshin turaren sa. Zama yayi a gefen ta yana kallon agogon hannun sa. Karfe takwas da minti biyar.

Yatsun kafar ta ya fara ja a hankali motsa kafar tayi sai ya kara ja ido ta bude tana mikewa zaune. Ido suka hada tai saurin dauke kanta.

“Ina kwana?”

Ta fada a hankali.

“No Baby na. Wannan ai ba ita ce irin gaisuwar ma’aurata ba.”

Dagowa tayi tana kallon sa sai kuma ta dauke kai ta tace

“Au su ma’auratan har wani gaisuwa ce dasu ta musamman?”

“Eh mana! Ke baki sani ba.”

Kai ta gyada yace

“Ni kuma kinga nasani. Dan haka ban son wannan waccen nake so?”

Murmushi tayi ganin yadda ya maganar a shagwabe

“Hmm to ya aike yin ta?”

Murmushi yayi sai dai na gwada miki. Kan tai magana ya janyo ta ya daura a cinyar sa. Kiss yayi wa lips dinta sai kuma yace

“Morning Bae!”

Murmushi tayi tai kasa da kai dan ita kunya yake bata. Dago kanta yayi yace

“Before ki gaishe ni ina son na fara jin dumin jikin ki with a kiss and something sweet then u great me are u clear?”

Ya tambaya kai tayi kasa dashi  daga ta yayi ya mike sannan ya kama hannun ta ya kai ta falo. Zaunar da ita yayi sannan ya dauko kayan da ya hada. Tea mai kauri ya hada mata sannan ya fara ba ta a kunyace take amsa yana bata hade da dankalin da ya soya. Kadan taci ta janye kan ta tace

“Na koshi!”

“Haba dai jifa dan abunda kika ci.”

Kai ta make a kafada ta dauki cup ta fara hada masa tea sannan ta mika masa tace

“Uhmm bismillah!”

Kafada ya make yace

“Ni a’ah ke zaki ban kamar yadda na baki.”

Ido ta zaro yace

“Baby please ki ajiye kunua a gefe ni mijin ki ne ki min abunda zan ji dadi na sa miki albarka kinji.”

Sai kuma ya shagwabe yace

“In ba haka ba ni kam am ok ban cin komai yau in ba da hannun ki zaki bani ba.”

Dauka tayi ta fara bashi yana ci yana murmushi wani abun ma sai ya dan hada da hannun ta a haka suka gama zata kwashe kayan yace

“No! Barshi ni zanyi.”

Ba yadda ta iya ta barshi ya kwashe kayan. Mikewa tayi ta koma dakin ta fara gyara katifar da suka kwana ta dauki tsintsiya kenan ya shigo dakin amsa yayi yace

“Kije kiyi wanka!”

“Shara zan yi sai nayi!”

Hannun ta ya kama ya kai ta bakin ban dakin yace

“Kiyi wanka kawai.”

Sannan ya juya. Bandakin ta shiga tai wanka ta fito tana shiga ta tadda har ya share dakin ya saka turaren wuta. Zama tayi zata bude jakar ta dan daukar kayan shafawar ta. Sai gashi ya shigo da karamin kit ya ajiye shi sannan ya bude.

Mai ne a ciki da turare da kayan kwalliya. Man ya bude ya lakata ya murxa a hannun sa. Kallon sa ta tsaya batai aune ba sai ji tayi ya janyo kafar ta ya fara murza mata a jikin ta. Ido ta zaro tana kokarin janye kafar ya dago yace

“Bakya so ne?”

Kasa tayi da kanta kawai dan bata jin zata iya cewa bata son. Dan haka ya cigaba da shafa mata kan ya gama kuwa ya saukar mata da wata irin kasala. Har powder shi ya saka mata da man lebe kwalli ne ya bata ta saka da kanta kawai.

Acikin sababin kayan ta dauki wata atampa baka mai ado red a ciki ta saka dinkin riga da siket ne sun mata kyau sun zauna a jikinta sosai.

Fashion ta saka jajjaye ta feshe jikin ta da turare. Muhammad dake zaune a gefe ya kura mata ido yana kallon ta yadda tai masa kyau kamar a sace ta a gudu.

A hankali ya mike ya karaso inda take ya rungume ta yana sauke ajiyar zuciya. A hankali yace

“Kinyi kyau my beauty!”

Murmush tayi tace

“Nagode!”

Hannah kuwa sosai take tsoron Ahmad dan sai baya gidan take sakewa daga ance ya dawo take shigewa daki ko wani abu zata dauko da kyar take fitowa shima sai ya zame mata dole. Kuma hijab take sakawa har kasa. Da ta shiga daki kuma take saka key ta kulle kan ta.
A haka sukai sati biyu shi dai abin ma mamaki da dariya yake bashi.
+
Tana xaune a daki taji tana jin kishirwa kuma a iya sanin ta tasan Yaa Ahmad bai dawo ba dan haka ta mike ta fito falon ta. Fitilar dakin a kunne take sau television dake aiki dan haka ba haske sosaj. Kitchen ta shige.
Yaa Ahmad dake kwance akan three sitter ya buta da kallo dan daga ita sai wani wando iya kar sa cinya sai yar vest da ta kamta ta kan ta ba dankwali dan haka gashin ta ya zubo gadon baya. Ido ya lunshe take kuma yaji marar sa ta kulle. Dan har ga Allah bai taba neman matan banza ba. Fara yin mu’amala da mace sai da aka kawo Hannah dan haka tin daga lokacin da ya yi abun yaji yana matukar bukatar ta.
Ba abinda yake so sau ya kara kusantar ta dan yadda yake jin feeling ma yasa yake fama da ciwon mara. Hannun sa ya daura akan marar sa yana shafawaba hankalu.
Tana shiga kitchen ta dauki ruwa ta zauna ta sha sannan ta fito dan komawa dakun ta. Har ta kusa kofa taji an finciko ta da sauri ta juyo a tsorace.
Ganin shine yasa ta dan saki ajiyar zucuya amman jikin ta na ta rawa. Kwace kan ta take son yi yai sauri ya rumgume ta tsam a jikin sa yana sauke ajiyar zuciya.
“Yaya dan Allah ka sake n…”
Bata rufe baki ba ya cafki bakin nata duj yadda ta dinga mutsu mutsu Kin sakin ta yayi sai hannun sa da ya zura a cikin rigar ta. Hawaye ne ya fara zubowa a idon ta.
Daukar ta yayi ak ya nufi dakin sa da ita. Yana shiga ya ajiye ta akan gado kan tai wani motsin ya haye kan ta. Romancing nata ya dinga yi dan baya so yaje mata ta karfi.
Sai da ya tabbata ya gama kashe mata jikin ta sosai dan itama tai shiru tana amsar sakon da yake aika mata sai kawai ji tayi yana kokarin shigar ta. Kuka ta fara tana fadin
“Yaya har yanzu da zafi fa dan Allah kada ka kara ji min ciwo.”
Ina bai ma san tana yi ba dan kukan nata kamar kara ingiza shi yake yi dan haka ya fara kokarin shiga a hankali. Sam hata da karfin da zata iya kwace kan ta dan haka in ba kuka ba,  ba abinda take yi.
Lokacin da ya shiga ta dan saki kara sau kuma tayi shiru hawaye na zuba a idon ta. Ya jima yana abu daya sannan ya sauka yai ruf da ciki yana sauke ajiyar zuciya. Ita ma ido kawai ta lumshe tana sakin ajiyar zuciya.
Ya jima sannan ya mike ya shiga bayi. Wanka yayi ya hada mata ruwan sannan fito. Agefen gado ya zauna sannan ya daga ta dukkan ta ya nufi bandakin da ita. Bata ji komai ba sai jin ta tayi a ruwan zafi.
Ido ta bude a tsorace tana ganin sa sai kuma ta rufe idon. Sai da ya gasa ta sosai sannan ya hada mata ruwa ya fita ya barta tai wankan tsarki.
Wankan tayi ta fito daure da towel din sa. Kwamce ta same shi a saman gado. Yana jin fitowar ta ya mike yana kallon ta. Hanyar kofa tayi sai kuma yace
“Zo!”
STORY CONTINUES BELOW
Kallon sa ta tsaya yi. Hannu ya mika mata ya gyada mata kai. a hankali ta karaso tana dingishi kadan kadan. Tana zuwa ya janyo ta ya daura a saman cinyar sa yace
“Da zafi ne yau ma?”
Kai ta gyada yace
“But ba kamar the first time ba ko?”
Kai nan ma ta gyada yace
“Yauwah a haka zaki daina ji ma gaba daya kinji?”
Kai ta gyada yace
“To taho muyi bacci kinga har daya tayi.”
“Kaya zan je na daka!”
“No nafi son naji naked body dinki manne da nawa!”
Ya janyo ta ya zare towel din ya rumgumeta suka shige bargo. Tana jin sa yana mata wasu abubuwan tai masa shiru sai da taji yana neman kara son yin abun sannan ta saka masa kuka ba dan yaso ba haka ya barta tai bacci shi kuwa da kyar yai bacci dan sam ji yayi yana kara bukatar ta. Tin da yai aure ya gane cewa yana da matsananciyar bukata.
Da asuba ma shi ya hada mata ruwan wanka tai wanka sannan ta wuce dakin ta shi kuma ya tafi masallaci. Tana sallah ta koma ta kwanta ba ita ta tashi ba sai karfe goma.
Dakin ta ta gyara ta fito ta fara gyaran falo tana tsaki ita gaskiya a dauko mata yar aiki aikin yai mata yawa bata gama ba ta shiga kitchen ta daura ruwan zafi.
Tana tafasawa ta soya kwai sannan ta wuce ta ajiye a dining ta zauna ta fara hada tea din. Tea ta hada sannan ta dauki bread zata fara ci kenan ya fito cikin wata army green din shadda wacce tai masa kyau. Fuskar sa ta kara kyau sai tashin kamshi yake ya nufo dining din ya zauna.
Kasa tayi da kanta tace
“Ina kwana?”
“Lafiya lou! Kin tashi lafoya?”
“Lafiya!”
Ta fada. Cup ya dauka ya fara hada tea sannan ya bude plate din gaban ta yaga kwai ne kadai a ciki. kallon ta yayi yace
“Meyasa baki dan soya kwai ko doya ba.”
Fuska ta bata tace
“Dan Allah Yaa Ahmad ka samar min me aiki, aikin ne yai min yawa.”
“Yanzu menene aiki a gidan nan Hanna? Ke bakya son lada in ki kai aiki a gidan nan lada fa zaki samu. Just two bedroom and two falo sune ba zaki iya ba sai dan abincin cikin ki da nawa. To ki sani gaskiya ni bana son masu aiki. Ko da yake in an kawo masu aiki me zasu nayi miki?”
Ya tambaya yana kallon ta.
Bata dago ba tace
“Gyaran dakuna da girki mana.”
“Oh ke kuma menene aikin ki a gidan?”
Shiru tayi. Yace
“To ki sani ni ba zan ci abincin mai aiki ba kuma ba zan yadda mai aiki ta gyaran daki ba dan haka ni ban da tsarin masu aiki kinji ko?”
Ya fada yana mikewa karyawar da bai yi ba kenan sai maltina da yasha a mota. Ya nufi gudan su can.
Baki ta tabe ta mike tana hamma ta nufi falo ta kwanta tana fadin
“Ai dakin bai ma datti ba,  ba sai na share ba.”
Tana kwanciyya bacci ya dauke ta. Ba ita ta farka ba sai uku yunwa taji tana ji dan haka ta karasa dining ta kara shan tea sannan ta shiga tai sallah. Falo ta dawo tana cigaba da kallo har akai la’asar bata tashi ba.
Sai biyar ta mike tayo sallah sannan ta kara dawowa kallo tana yi tana chatting.
Yana zuwa ya tadda Momy a kitchen ita da Basma suna girkin rana. Shiga yayi bayan sun gaisa yace
“Momy ai da barin ta kikai ita daya tai girkin!”
“A’ah bari dai muyi tare kada aikin yai mata yawa.”
“Daman ke kike sangarta su ga waccan can wai masu aiki take so!”
“Ai fa ya kamata a samar mata masu aiki gaskiya dan aikin gidan yai mata yawa.”
Ido ya zaro yace
“Haba Momy ai bai dace ba. Ina aikin yake kawai daga dakin ta sai nawa sai falo da sittingroom haba Momy. Ko ina Abuja fa da kaina nake gyara dakuna nan kuma kan na fita aiki ita menen ba zata iya ba.”
STORY CONTINUES BELOW
“Ai kai namiji ne.”
“Ai aikin gida na matane Momy ni dai bana son masu aiki gaskiya.”
“Ai fa sai kayi wallahi in zaku tafida masu aiki zan hada ku dan gidan ku na can nasan yafi na nan gurma dan haka ba za a je aiki yai mata yawa ba.”
Shiru kawai yayi ya kall Basma sai kuma ya fita kawai.
Motar sa ya shiga ya nufi unguwar su Hafsa ransa a bace dan daman yasan Momy bata da wanda take so kamat Hanna. In ba haka ba ai tasan gaskiya bama wannan ba ita kanta masu aikin ta me suke sai gyaran compound da in za ai biki ko wani abu sai ko aike amman ita take girkin ta to dan me ba zata hora su akan hakan ba.
*
**
***
****
*****
******
Isma’il da Halima kuwa a haka suka cigaba da rayuwa duk da a duk lokacin da Isma’il zai yi sex da ita ba a son ranta take ba. Sai ya nuna kamar zai kuka kuma ya hakura sai taji tausayin sa saboda yadda take son sa kamar me.
Kuma dadin bakin sa shi ke kara sa take kara macewa a kan sa. Domin kuwa ba abinda baya mata. Dan yanzu ta daina zuwa bara tana gida sai dai taje ko yazo ya dauke ta. Amman kudi daga naira daya zuwa dubu dari ko sama da haka zai kashe mata su.
Sam Kabir bai san da haka ba shi ya zata tin da akai na farko shikenan ba a kara ba. Dan kullum haka yake nunawa Kabir din.
*
Saukowa suke daga sama office din Kabir suka biyo ta cikin mall din. Suna saukowa Isma’il ya ga wata kyakyawar yarinya tsaye tana zabar wasu designers din perfum. Kallon ta ya tsaya ya kasa dauke idon sa yana hadiyar yawu. Duk da sideview din ta yake hanga amman ta gamai masa.
Sanye take da wata hadaddiyar doguwar riga wacce take irin yan dubai din nan. Baka ce sai daga saman da akai mata babban hannu da wani material mai santsi golding kala. Riga tayi kyau dan bata kamata ba. Sai mayafi golding kala da tayi rolling sannan ta saka cover shoe shima golding colour. Kallon ta ya tsaya yi har Kabir ya kusan fita a mall din. Magana yake son yai masa yasa ya juyo. Tsayawa yayi yana dubawa acan nesa wajeb stairs ya hango shi ya harde hannu a kirji. Tsayawa yayi a gefen kofa yana kallon sa.
A hankali ya taka yayi kusa da ita lokacin ta gama dauka ta juya baya dan tafiya gun countet.
“Assalamu Alaikum Beauty!”
Juyowa tayi a hankali ta daga idanun ta ta zube akan fuskar sa. sai kuma ta tabe baki tace
“Wa’alaikum salam! Lafiya?”
“Am daman naga kaya a hannun ki ne nace bai dace mai kyau kamar ki da daukar kaya haka ba.”
Basket din ta ta kalla wanda perfums ne a ciki kala biyar kawai kuma ba wani nauyi.
A hankali ta dago ta kalle shi tace
“And then?…”
Kai ya dan shafa yace
“Wai da kin kawo an taumaka muki ko?”
“Bana so!”
Ta fada kawai tana nufar wajen counter din. Tana zuwa ta mika musu suka hau lissafawa. Suna fadar kudin ta dauko ATM card zata mika kenan taga an mika wani.
“Dauki a ciki!”
Ya fada. Juyowa tayi taga Isma’il ne wannan yasa ta saki wani tsaki sannan ta juya ta nufi kofar fita. Ana parkaging turarukan ya amsa yabi bayan ta.
Tafiya take a nutse kamar bazata taka kasa ba. A haka tazo dai dai Kabir dake tsaye dagowa tayi a hankali suka hada ido. Daga ita har shi sukaji gaban su ya fadi. Kai ya dauke da sauri dan haka har ta fita tana waiwayen sa.
“Waye wannan da har zai ganta ya dauke kai?”
Ta fada tana tafiya. Gun motar ta ta karasa tana zuwa driver dake tsaye ya bude mata zata shige kenan Isma’il da ya taho da turaruka ta ya karaso yana fadin
“Hajiya ai baki amshi kayan ba.”
Juyowa tayi ta tsaya ta harde hannun ta a kirji tana kallon sa a yatsine kamar taga kashi. Sannan ta bude baki a hankali tace
“Malam ban nemi taimakon ka ba haka nan ni ba matsiyaciya bace dan haka find ur way out am not your mate!”
Tana fadar haka ta shige cikin mota da sauri driver ya zaga ledar hannun sa Isma’il ya zura mata kan ya bar wajen ta bude murfin motar a fadace ta fito. Turarukan ta jefar wasu suka fashe tace
“Ana dole ne?”
Ta fada a tsawace
“In ina son duka mall din nan zan iya mallakar sa. Ni bana son kaji ko? Am not a begging you, ni ba irin yan matan da ake siya da kudi bace. I have them alot. Dan haka kada in kara ganin ka a gabana kana ji ko? Mtszzz!”
Ta saki tsaki sannan ta juya ta shiga mota. Kabir da akan idon sa akai murmushi kawai yake yi dan yau yaji dadi da mace bata biyewa Isma’il ba duk dadin bakin sa.
Motar aka tayar suka bar wajen aka bar Isma’il tsaye a wajen baki bude. Kabir ne ya karaso ya dauki ledar ya mika masa. Amsa yayi tai jifa da ita. Ya wuce ya shiga motar sa ya bar wajen.
Ledar Kabir ya dauka yana murmushi ya nufi motar sa ya saka sannan shima ya bar wajen.Rabi’a ce zaune a falon ta sanye da wata atamfa ja da fara wacce akai mata dinkin riga da siket sun mata kyau sosai. Ta yi kwaliyya sosai tana rije da waya da ta hau whatsapp. Ba group din da ta shiga sai na Indabawa Hausa Novel. Sako ta gani wanda akai highligting akan Novel din daya daga cikin marubutan online writers. Ba kowa bane yayi sai group admin din kamar haka

_Complete on wattpad. Labari mai taba zuciya da saka mutum ya kara jin tsoron Allah da kiyaye iyakokin Allah. Labarin ya saka ni kuka sosai 😭😭 Please mu daure munemi buk din nan ko dan mu samu darasin da ke ciki domin abinda ke faruwa a wannan zamanin da rayuwar kenan amman bama halkanta. Na tabbata duk mai irin halin yaji zai shiga hankalin sa ya koma ga Allah tin kan wankin hula ya kai shi bango. Hakika marubuciyar tayi amfani da baisrar ta wajen fadakarwa. Allah ya baki ladan fadarkawa ya kara basira da daukaka. Allah ya kiyaye mana ke. Amin._

Duba cikin highlighting din tayi sai taga an rubuta
*KWA’DAYI…! (Mabudin wahala) by Firdausi Musa. FEEDOHM*

Kan abun taje tai mata magana tace
“Anty Maryam dan Allah taimaka min da decoment dinsa. “

Ai kuwa take ta turo decoment din nasa. Zama tayi ta fara karantawa. Labarin ya dauko dadi kenan sai ga sallamar Mijin ta Mustapha nan dan haka da sauri ta mike ta masa sannu da zuwa. Zama yayi yace
“My dear ya gidan?”

“Alhamdulillah ya hanya?”
“Lafiya lou gobe zamu tafi sokkoton fa.”

Fuska ta bata tace
“Yaushe ne daurin auren ne?”

“Jibi ne kinga in muka tafi gobe da rana jibi ana daura auren zamu juyo ko?”
“Uhmm ni gaskiya zanyi missing naka.”

“Kada ki damu Baby na. In na dawo kada ki manta tare zamu tafi fa.”
Tunawa da hakan yasa ta ce
“Shikenan Allah ya tsare.”

Ta mike da sauri ya kamo hannun ta yaba fadin
“Ina kuma zaki!”
“Lemo zan kawo maka!”

“No barshi zauna naji dumin jikin ki kawai!”
Komawa tayi ta lafe a jikin sa.

Washe gari bayan sallah friday suka daga sokkoto bayan ta gamai masa addu’a da fatan alheri. Tana komawa ta dauki wayar ta a inda ta tsaya da karatun ta daura sam ranar ba abinda ke tayar da ita tin bayan sallah friday sai sallah ko abinci batai ba drinks kawai take sha dan ba abinda take so ya tashe ta daga karatun da take.

A haka take jinjina irin soyayyar da saddiku yakewa Zainaba wanda yake fifita farin cikin ta akan nashi. Ita kuma Zainaba sam bata lura da haka. Kwadayi ya rufe mata ido sam abinda yake mata bata godiya.

SS ne duk ya fara bata ta wanda kwadayin ta ne ya jawo mata. Akan yan kayan kwalliya da waya ta fara bada kanta duk da a time din ba wani abu ya shiga tsakanin su ba kawai dai romancing suke yi.
Daga haka kuma ta hafu da Dr MK. Wanda Dr MK shi ya kara tsarwa mata rayuwa. Dan shi ya fara disvigin nata. Kuma bai var ta anan ba sai da yanjarai nata huduba kan cewa ko da auren ta zasu cigaba a inda suka tsaya. Wanda hakan yasa da auren nata take bin maza bayan tai aure. Ita kuma duk ilimin ta ta biye masa sam bata tuna ranar gobe kiyama ko ta mutu akan alfasha. *Ya salam wai ina zaki damu ne duniya*

STORY CONTINUES BELOW

Wanda tin ba aje ko ina ba kuma ya guje ta dan ta samu wani ciwo amman wannan duk bai zamar mata izina ba a haka take waya da chat da karfin banza, wanda anan ta kara haduwa da silar jefa ta a kunci da kuma silar barin ta duniya.

Bayan mijin ta bai rage ta da komai ba. dan abinda taje ci ko gidan wani attajirin ma sai haka duk abinda yake mata wanda ko wata matar da mijin ta ke da kudi ba zata samu abunda yake mata ba. Amman sam taki ta godewa Allah. Bama taga yana mata ba ita tafi son ta mallaki kudi ko ta halin yaya ne
A garin chatting nata anan ta hadu da sanata Muntari wanda shine silar lalacewar koma. *Wa’iyazubillah.* wanda tai wa mijin ta karyar mutuwa tatafi can wata uwa duniya dan tai lalata da auren ta.

*Ya salam* ai kuwa wannan zuwa ya zamar mata nadama da danasani da ake kira da kyeya. Domin kuwa a zuwan ne suna kwance da Senator Muntari gobara ta kama wanda sai farkawa tayi ta ganta a gadon asibiti ko ina ya kone a jikin banda fuska. Anan taji labarin Senator Muntari ya rasu kuma suma iyakan sa sun zo sunce sai sun kashe ta
Tayi nadama tayi danasani. Bayan ta baro mijin ta acan hankali a tashe da yaya aka gano ta akazo akai jinya. Sai dai fa bayan nan kuma mahaifin yace dole taje a jefe ta wanda ita kuma taki yadda wannan yasa ya sallame ta a ya’yan sa duk son da yake mata kuma ya umarci mijin ta da kada ya kuskura ya jikan ta shima ya sake ta.

Duniya ta juyawa Zainaba baya ta mata atishawar da ba zata taba gyarawa. Duk ilimin ta sai gashi tayi watsi dashi wanda yau ga a yadda ta koma bata da kowa haka ta dibga rayuwa a kofar gidan su amman kallo mahaifin bai mata bare ta sa ran samun rahamar sa.
Tana cikin haka ta gane tana da cikin senator Muntari domin kuwa in ba zata manta ba kan taje gun sa tafi sati nawa rabon ta da mijin ta duk da yana bukatar ta……………………………………………….. Labari ne mai taba zuciya kunemi *Kwa’dayi na Feedohm* dan kuji komai filla filla daki daki.

But at the end dai Zainaba ta yadda aje a jefe ta domin tayi na dama a gani duniyar nawa take gwara a wanke ta tin a duniya kan ta koma ga Allah.

Haka ta tafi ta bar yar ta da mijin ta da mahaifin ta suna kuka. *Allahu Akbar* 😢 😢 abun ban ya taban zuciya sosai.

Jikin Rabi’a ne yai matukar sanyi ta fashe da kuka domin kuwa itama ta aikata same abinda Zainaba ta aikata.

Take tsoron Allah da nadama da danasani suka durar mata. Ranar kwana tayi kuka da neman yafiyar ubangiji.

Tayi kuka har ba gobe ta shiga damuwa tashin hankali rokar Allah take tare da nadama da jin kunyar kanta. Ta cuci mijin ta ta ina zata fara neman gafarar sa.

Washe gari da safe bayab ta gwara gidan tai wanka ta saka wata bakar doguwar riga sannan tai alwala ta hau kan sallaya. Ranar ba abunda ta yini tana yi in banda sallah da istigifari. Akan Allah ya yafe mata. A cikin kwana daya kawai tai sanyi ta rame sosai.
Dan daga jiya zuwa yau ba abinda ta iya kara sakawa a cikin ta ko ruwa ta kasa sha. Tana godiya ga Allah da yasa bata mutu tana aikata alfasha ba.
Karfe hudu Mustapha ya dawo sosai yaga canji a gun Rabi’a. Dan ko oyoyo batai nasa ba. Sannu da zuwa kawai tai masa dan haka ya dinga binta da kallo. Dagowa tayi suna gada udo ta dauke kai.
“Me yake damun ki ne?”

“Ba komai!”
“Muje na hada maka ruwan wanka.”
Kan ya bata amsa ta shige daki. Yana shiga dakin ta fita ta fara hada masa wajen cin abinci.

Yana fitowa ta fara serving nasa ta koma ta zauna tana jan carbi. Kallon ta yayi yace
“Zo muci mana!”

Kai ta girgiza tace
“Ba koshi!”

Ture abincun yayu yace
“Nima haka.”
Da sauri ta mike tazo taja plate din tana bashi. Sai da ya gama ta gyara wajen.

STORY CONTINUES BELOW

Falo ta zauna yazo shima ya zauna yace
“Baby akwai wata matsala ne?”

Kai ta girgiza. Yace
“To me yake damun ki?”

“Ba komai fa.”
Kallon ta kawai yake yace
“Tayaya zaki ce min ba komai bayan ga koman nan ina gani.”

Ido ta lunshe tana jin wani iri Mustapha na son ta ya kuma damu da ita. Hannun ta ya kama.yana wasa dashi yace
“Sannu toh!”

Ido ta bude sai kuma ta dan sakar masa murmushi. Duk tambayar da yayi tace masa ba komai. Da ya matsa sai tace
“Bana jin dadi ne.”

“Amman kuma kika ce ba komai!”
“Bana son hankalin ka ya tashi ne.”

“Baki san rashin fada min yafi komai daga min hankali ba.”
“Am sorry toh!”

Janyo ta yayi jikin sa yace
“Bakya laifi Baby na. Ki daina boyen damuwar ki. Ki sani banda buri sai na inga na faranta miki please Baby ki daina damuwa yanzu fa zamu dauwama tare kinji.”

Kai ta gyada kawai. Nan yai a bata kulawa yana nan nan da ita har ya fara bata tausayi. Dan ko matsi tayi yace
“Menene?”

Da daddare ne ya fita ya siyo mata gasasshen nama da madara. Tana kwance akan kujera hannun ta rike da carbi ya shigo. Daga ta yayi yana kallon ta yace
“Nace muje asibiti kinki ko saboda me?”

“Ciwo na bana asibiti bane.”
“Tayaya kika san ciwon ki bana asibiti bane?”

“Nidai kawai!”
Ido ya zuba mata sai kuma ta fshe da kuka da sauri ya mike a dawo kusa da ita ya rumgume ta yana lallashin ta
“Haba Baby na menene na kuka bayan gani a tare dake dan Allah ki daina kukan nan.”

“Uhmm Honey dan Allah ka yafe min.”
“Me kikai min da zan yafe miki Baby!”

“Ni dai dan Allah na kasance me maka laifi ka yafe min dan All…”
Kuka ne yaci karfin ta. Rumgume ta yayi yace
“Kada ki damu na yafe miki duniya da lahira. daman ni baki tabai min komai ba. In ma kinyi ban sani ba na yafe miki. Allah ya yafe mana gaba daya dan Allah ki bar kukan nan da saka damuwa a ranki kinji?”

Kai ta gyada yace
“To taso muci abinci kinji.”

Haka ya dnga bata ba dan tana iin dadin sa ba ta dinga ci bayan sun gama da kan sa yai mata wanka ya saka mata kayan bacci sannan suka kwanta rumgume da juna kamar za a kwace masa ita.

Ita dai in banda ajiyar zuciya ba abinda take saukewa. shi kuma sai bayan ta yake shafawa a hankali a hankali. Har bacci ya dauke ya. Kwanciyya ya gyara mata yai mata addu’a sannan shima ya fara bacci.

*
**
***
****
*****
******
Sakina ce zaune a garden din gidan Hajiyar wacce bata nan wannan yasa ta tafi can tana shan iska. Sanye take da doguwar riga ta material peach kala tai mata kyau ta yafa bakin mayafi kanta ba dan kwalli. Wayar ta take dannawa tana dab shan juice din dake ajiye akan table din gaban ta.

Khaleel da shima a lokacin ya fto daga cikin gida kawai ya nufo gardeb din. Yana shigowa ya hangi Sakina. Wani murmushi ya saki ya karaso wajen da take.

Zama yayi a kujerar dake kusa da ita yanayin sallama cikin cool voice dinshi. Da sauri ta dago kirjin ta na bugawa kasa amsawa tayi. Murmushi yayi yace
“Please ki amsa min sallamar ta mana wannan zai nuna kina murna da zuwa na fa.”

“Wa’alikum salam! Ina yini?”
Ta fada kan ta a kasa. Tana cigaba da danna waya duk da ba gane mai take yi take ba.

“Lafiya lou!”
Ya fada yana kura mata ido. Shiru taji dan haka ta dago suka hada ido da sauri ta dauke kan ta. Murmushi yayi yace
“Me kike yi da wayar ne?”

“Chat!”
Ta bashi amsa tana kallon gefe. Kainya gyada yace
“Naga kina bawa waya mahimanci dan naga kamar kin fi jin dadin maganata nan ko?”

Kai kawai ta gyada. Wayar sa ya mika ata yace
“Samin number dinki.”

Dagowa tayi tana kallon sa. wani mrmushi ya sakar mata mau tsada sannan ta amsa da sauri ta saka masa. Amsa yayi yaga batai saving ba dan haka ya mika mata yace
“Kiyi saving dinta.”

*Sakina* ta saka ta miko masa amsa yayi ya kalla yace
“Jusy *Sakina*”

Kallon sa tayi da alamar tambaya tace
“Kamar ya??”
Murmushi yayi yace
“Sai kisa *Swt Sakee*”

Ido ta dan zaro tana yin kasa da kan ta yai murmushi yace
“Ko bakya son sa ne? A canja wani.”

Kai ta girgiza kawai. Yace
“Ko in saka my love?”

Da sauri ta dago tace
“Your love kuma?”
Murmushi yayi yace
“Banda masoyiya me zai hana ki mayen gurbi.”

Murmushi kawai tayi.
Hajiyar da dawowar ta kenan daga unguwa ta shiga ta duba taga ba Sakina. Wayar ta ta dauka ya fara kiranta.
Dai dai lokacin da Khaleel zai magana kenan wayar ta ta dau kara dauka tayi da sauri takai kunne.
“Kina ina ne?”

“Ina garden!”
“Ok!”

Kawai ta fada tayo garden din dan daman tana compound. Kallon ta Khaleel yayi yace
“Waye?”

“Hajiyar ce!”
“Ok ta dawo kenan…”

Hango ta yayi ta shigo wajen tana ganin su tare ta hade fuska. Khaleel ta kalla tace
“Tashi na aika ka.”

Mikewa yayi yana kallon ta .tace
“Kaje ka amson sako gun Hajiya Ni’ima.”

“Ok Mom!”
Sakina ya kalla yace
“Swt Sakee au my love zo ki rakani man.”

Hajiyar ta kalla sannan ta mike tabi bayan sa. Zama Hajiyar tayi tana zuba tagumi. duk yadda taiwa Khaleel kashedi akan ya daina shiga harjar Sakina amman kamar tunzura shi tayi kenan ko?

Sunan da ya kirabta dashi shi yafi daga mata hankali ma. Kwafa tayi tace
“Nasan me zanyi ta tashi ta koma ciki.”

A cikin ma ba abinda take sai safa da marwa. Ta kasa samun nutsuwa bini bini ta daga kai ta kalli agogon dakin. Tin bayan la’asar suka fita amman gashi har magariba basu dawo ba. Ta kira Hajiya Ni’ima tace mata ai ko zama basu yi ba suka bar gidan.
Take taji ta rasa nutsuwar ta nan ta hau neman layin su amman sam bata shiga gaba daya layin nasu.
Sakina da Khaleel kuwa suna fitowa daga gidan Hajiya Ni’ima abokin Khaleel Marwan ya kira sa. Yana dagawa yace
“Yanaga baka zo ba?”
“Ina?”
“My birthday mana kada kace baka ga text.”
“Wallahi ban gani ba bro ya za ayi kenan?”
“Malam ka taho kawai.”
“Ok ba damuwa.”
Ya juyo ya kalli Sakina da tin da suka fito batai magana ba.
“My love kin ji fa,  friend dina ke birthday please zaki rakani?”
Dagowa tayi ta kalle shi. Ya marairaice mata yace
“Please!”
“Ok but ai ban shirya ba.”
Kallon ta yayi yace
“Menene da ke a hakan u re beauty ba abinda kik bukata more. But in kina son canja shiga muje a siyi wasu yanzu.”
“No ka barshi kawai.”
Kai ya girgiza yace
“Ina ai kuma sai an je fa.”
A wani hadadden wajen sai da kaya yai parking sannan ya kalle ta ya fita. Xagayawa yayi ya bude mata kofa ta fito a hankali.
Kai daga ganin wajen kasan wajen masu kudi ne dan tin daga enterance din abin kallo ne har ciki. Shi da kansa ya zabar mata wani blue black gown mai sky blue stone. Sanna ya daukar mata cover shoe da vail.
Wani daki aka kai ta ta shirya ita kanta sai a ta tsaya kallon kan ra a mirrow dan tadda tai kyau kamar aljanna.a hankali ta fito daga dakin.  Tin da ya daura idon sa akan ta ya nemi komai nasa ya rasa. Har ta karaso bai sani ba. Dan sai da ta masa tafi sannan ya dawo cikin hayacin sa.
Murmushi ya saki yace
“Kinyi kyau Baby sosai.”
“Thanks you!”
Fita sukai suka koma mota. Wajen party suka zarce waje ne da ya hada ya’yan manya masu ji da kansu. Sai rawa ake wasu na zaune suna hira da yan mata wasu na pictures haka dai.
Tana shiga wajen wani tsoro ya kamata dan bata taba zuwa waje irin haka ba duk abun ta. Dan haka a bayan Khaleel ta dinga buya.
Suna shiga wata kawar Khaleel Ase ta taho ta mika masa hannu. Hannu ya mika mata suka gaisa tana cewa
“Yaushe ka shigo kasar?”
“Sati na daya.”
“Amman naji dadin ganin ka wajen two years rabona da kai fa.”
Yai murmushi kawai. Sakina ta gani a bayan sa ta janyo hannun ta tana fadin
“Wow budurwar ka ce?”
Kai ya gyada yace
“Ita zan aura insha Allah.”
“Wow amman tayi kyau kuma kun dace sa juna.”
“Thanks!”
Marwan ne ya karaso sjna haduwa sukai side hug da juna yace
“Happy birthday Guy!”
“Thanks you!  Mu karasa.”
Ya kamo hannun sa ya kai shi gu ya zauna dagowar da zai suka hada ido da Sakina.
STORY CONTINUES BELOW
“Wow tare kuke?”
Kallon sa Khaleel yayi ya kalli Sakina sai yaji kishi dan haka ya dan gintae fuska yace
“Yes!”
Ya kalli Sakina yace
“Have a sit!”
Zama tayi tana yin kasa da kanta dan ji tayi bata sake da gun ba
Yayan manya ne sosai yan gayu masu ji da gayu da kudi kuma. Tin da ta shigo wajen wasu ke binta da kallo daga maza har matan. Ita bata san yan matan kishi suke ba wasu kuma kyau tai nusu ba.
Serving din su akai da lemo da kalolin abinci. Bata taba komai ba ya kalle ta yace
“Bismillah man!”
Kai ta girgiza tace
“Na koshi.”
Kai shima girgiza yace
“No ba za ai haka ba.”
Ya mika mata cup da ya zuba mata lemo a ciki. Hannu ta saka zata amsa sai yayi wajen bakin ta. Kai ta dauke ya dan yi murmushi ya mika mata.
“Hae Khaleel!”
Suka jiyo wata murya mai zaki tana kira sunan sa. Juyawa yayi sai kuma ya mike yana fadin
“Amal!”
Jikin sa ta fada ya dan rumgume ta yace
“Ya kwana da yawa?”
“Alhamdulillah!”
“Miss u khaleel ka yada ni ban san me nai maka ba. In na kira baka picking daga baya number ya daina shiga gaba daya.”
Kai ya shafa ya ce
“Just forget ya kike?”
“Tayaya xan manta Khaleel bayan kasan i love u!”
Wani murmushi yayi yace
“Da kenan Amal but now..”
Ya girgiza kai. Ya juya ya xauna yana nuna mata kujerar kusa dashi yace
“Sit!”
Zata zauna kenan taga Sakina dan haka sai tayi still taki zama gaba daya.
“Wacce wannan?”
Ta fada tana nuna Sakina. Kallon Sakina yayi yace
“Oh She is my Love my wife to be insha Allah!”
Ido daga Sakina har Amal suka zaro. Amman Sakina dai kallon sa ta tsaya yi sannan tace
“What?”
Yana murmushi yace
“Abinda kika ji na fada.”
Da sauri ta juya ta bar wajen tana hawaye. Haka aka dinga gudanar da taron Sakina dai na zaune har karfe tara ta kalli Khaleel tace
“Dare fa yayi.”
Agogon hannun sa ya kalla yace
“Ok bari a yanka cake mu tafi ko?”
Zama tayi ya mike ya kalle ta yace
“Muje!”
Kamar kar ta mike dan idon dake kan ta amman ta mike tabi bayan ta kanta a kasa. Kusa da Marwan suka karasa inda zai yanka cake gefen sa budurwar sa. Yana tsaye suka yanka ya bata ta bashi sannan ya bawa Khaleel. Khaleel yaci ya amsa ya bawa  Sakina da tai kasa da kanta.
Tafi aka dauka a wajen. Marwan Khaleel ya kalla yace
“Friend we are going!”
“Ok thanks friend!”
Ya kalli Sakina yace
“Thanks you too Baby!”
Hannun Sakina Khaleel ya kama ya tafi suka fita. A mota ya saka ta ya zagaya ya shiga. Gida suka nufa. Karfe goma da rabi suka karasa gida.
Hajiyar dake ta taga tana kallon compound dan duk ta kasa nutsuwa tana jin shigowar mota ta bude ido tana kallon sa. Parking yayi ya fito da sauri ya budewa Sakina. Ta fito tana fadin
“Nagode!”
Murmushi yayi yace
“Nike da godiya!”
Tai gaba yabi bayan ta yana murmushi.
Tana shiga tayi hanyar dakin da take dan bata kula da Hajiyar dake tsaye a jikin taga ba.
Tana shigewa Khaleel da ya tsaya answering call sai da ya gama sannan ya shigo.
*
**
***
****
*****
******
Ahmad na baro gida ya zarto gidan su Hafsat.  A kofar gida yai parking sannan ya fito ya tsaya a jikin motar sa yana son wani yazo ya aika shi cikin gidan.
Yana tsaye daya daga cikin yaran gidan yazo zai wuce da sauri Ahmad yace
“Please kanina kaje kace ana sallama da Hafsat!”
Ciki yaron ya shiga.
Hafsa na zaune a falon Mama sanye da bakin siket da t-shirt orange kala. Kan ta sanye da bakar hula. Fuskar ta ba kwalliyya amman tai kyau tayi fresh da ita. Zaune take tayi tagumi a dakin ita kadai.  wanda a da suke zama ita da Fauziyya ta tafi ta shiga kadaici duk jin ta take wani iri.
Kanin ta ne shigo yace
“Anty Hafsat wai kizo a waje!”
Dagowa tayi tace
“Inji wa?”
“Nima ban sani ba.”
“Kaje ka tambayo sa.”
Da gudu ya fita ya koma gun Ahmad dake tsaye jikin mota yace
“Wai tace inji wa?”
“Kaje kace mata Ahmad ne.”
Ya juya a guje ya shiga gidan. A zaunenya same ta yace
“Wai Ahmad!”
Shiru tayi tana tunani can tace
“Jeka kace gani nan!”
Fita yayi ta mike ta saka hijab har kasa sannan ta fito sauro kofar gida ta leka sukai ido hudu dashi.
Da sauri ta koma tana dafe kirjin ta da ya buga. Murmushi ya saki a hankali ya tako ya taho soron. A tsaye ya tadda ta ya shiga ya tsaya daga can gefe.
Wani irin mugun kwarjin da kyau taga yayi mata, zuciyarta ta Fara buga mata da karfi, Ahmad dake kallon ta yace
“tsarki ya tabbata ga Allah da yayi wannan halittar. Alhamdulillah!”
Ya fada a zuciyar sa. Shi dai tin da ya daura ido akan  Hafsat Allah ya saka masa son ta. Hafsat da Kanta tayi kasa dashi tana wasa da y’an yatsun hannunta alaman kunya, tace
“Ina wuni?”
Ahmad idon shi na kanta yana kallon bakinta yanda take magana cikin nutsuwa yace
“lafiya kalao sweetheart,”
Dan shiru yayi yana kallon ta wani irin sonta yaji yana fusganshi… A hankali ya kira sunan ta da
“Hafsat!”
D’ago da kai tayi suka had’a ido da sauri tayi kasa da kanta. Murmushi yayi tare da fadin
“Hafsat da farko dai sunana Aliyu mu biyu iyayan mu suka haifa daga ni sai kanwata Basma.”
Shiru yayi yana kallon ta. Kanta a kasa. Yace
“Hafsat na dade Ina sonki tun lokacin da kina zuwa Tarauni.”
Da sauri ta d’ago ta kalleshi domin abunda yace ya bata mamaki Sosai, kenan tin tana zuwa gidan Alhaji Hamza kenan kome?
Katse mata tunani yayi da fadin
“tun lokacin nnake ganin ki kuma nak bibbiyar rayuwar ki. Ba komai ya kara daukar hankali na dake ba sai irin shigar da kike sanye da ita.”
Kallon ta yayi yace
“Kamar yadda dai kike a gabana yanzu kullum kina sanye da hijab har kasa…..”
Numfashi yaja yace
“Tin daga lokacin na kamu da son ki duk da ban san koke wacece ba ko matar aure ko akasin haka. Nayi imani haduwa na dake had’in Allah ne, tun sanda na ganki dan ni yan mata basa gaba na.”
Murmushi Hafsat tayi tace
“Ikon Allah Abun yaban mamaki
Kai ya gyada yace
“Ina son wani abu akan ki.”
Shiru Hafsat tayi gaban ta na ta faman bugawa da sauri da sauri.
*Toh Fa! Shin Hafsat zata fada masa ko ita wacece?*

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *