WANNAN RAYUWAR CHAPTER 9

 WANNAN RAYUWAR CHAPTER 9

Shiru Hafsat tayi gaban ta na ta faman bugawa da sauri da sauri. Tunani take shin ta dauki shawarar Anty Fauziyya ta fadawa Ahmad gaskiya. Wata zuciyar tace

“ki fada masa gaskiya ki huta in yana son ki a haka shikenan in ma baya son ki Allah ya kawo me son ki a haka.”+

Wata zuciyar kuma da ta riga ta kamu da son sa. Dan Ahmad ya burge ta tace mata

“A’ah Hafsat kada ki fara. Ahmad ba kamar Muhammad mijin Fauziyya bane shi daman yasan ta a kuma ta fada masa amman ke fa kin tabbatar da irin son da yake miki ne da zaki fada masa salon ya zo ya gudu bayan kuma kina bakatar auren.”

Dayar zuciyar yace

“Ki fadi dai gaskiya ki huta Hafsat!”

Kai ta girgiza.

Jin tayi shiru yasa Ahmad fad’in,

“lafiya kuwa? “

‘Kago murmushi tayi tare da fad’in

“Sunana…”

Dakatar da ita yayi yana fadin

“Ko dan ban fara miki bayanin ko ni wanene ba ko?”

Kan tai magana yace

“Sunana Ahmad Aminu kamar yadda na fada miki mahaifina Alhaji Aminu babban likita ne sai mahaifiyya ta Hajiya Amina. Mu shida ne a gidan mu. Yayye na mata hudu sai ni sai kanwata Basma. Nayi karatu A bangaren economic wanda yanzu nake aiki a bank a Abuja…..”

Shiru yayi sai kuma yace

“Ranar da na fara tsayar dake a ranar akai dinner partyn biki na…”

Dam taji gabanta ya fad’i Wanda bata san dalili batare da kallon shi da sauri ganin Sun had’a ido domin shima ita yake kallo yasa tayi kasa dakai.

Murmushi ya dan saki yace

“Hafsat iyaye na sun sha bani mata amma naki yarda. A duniya ban da buri da ya wuce na samu mace mai hankali da nutsuwa da tarbiyya wanda sai da lokaci ya kure na sameki. Momy na ita tai min zabin Hannah yar kanwar ta ce cousin muke.”

Yai shiru yana kallon ta sannan yace

“Hannah kanwa ce a guna dan haka ba zan taba cewa bana son ta ba dan ko ba aure tsakanin mu ni me rike tane bama da a gidan mu ta taso. na fad’a miki wannan maganan ne saboda ina sonki ban son boye miki komai dake tare dani,  Hafsat son ki ya gama zama jinin jiki na rabani da shi tamkar rabani da farin ciki nane. Ina son ki har ban san adadin son da nake miki ba. Bana karya gaskiya na fada miki abinda ke cikin zuciya ta kenan. ina son Kema ki fad’amin abunda ya kamata in sani.”

Dagowa tayi tana kallon sa ta gefen ido. Idanun ta sunyi ja alamar tana cikin wani hali. Zuciyar ta in banda bugawa ba abinda take yi. A hankali cikin sanyin murya tace

“Sunana Hafsat Kasim muna da yawa a gidan mu amman nice ta hudu kanne na sunfi goma sha bakwai. Ni haifaffiyar garin nan ce, mahaifina dan kasuwa ne. Sai mahaifiya ta. Matan babban mu hudu daya ta rasu yanzu sauran uku. Alhamdulillah yan gidan mu munyi makaranta boko da isilamyya dan munyi graduation a isilamiyya kuma munyi sauka. Yaya ta daya Anty Fauziyya da ka ganmu ita akai wa aure dan yau kwanan ta uku da tarewa.”

STORY CONTINUES BELOW

Murmushi Ahmad yayi sannan yace

“Masha Allah. Allah sanya alheri ya bada zaman lafiya.”

“Amin!”

Ta fada murya a sanyaye. Yace

“Baki ban labarin samarin ki ba”

Kanta a kasa tace

“Ai bani dasu!”

“Kamar yaya kenan?”

“Anty Fauziyya ita ce babbar mu a mata duk ta daura mu akan tsarin da mahaifin mu keso. Kaima dalilin da yasa na tsaya da ai dan ita ta yarje min. Bama zance shiyasa.”

Murmushi Ahmad yayi tare da fad’in

“hakan na da kyau ai. naji dad’i Sosai da naji tarijin ki, babban abunda ya kara burgeni game dake suna da yawa. Hankalin ki nutsuwa,  tarbiyya,  uwa uba malama ce tina kin sauke kinga ‘kya na mana kari ko?”

“Kai da wa?”

“Ya’yan mu!”

Fuska ta rufe da hannayen ta tana murmushi yace

“Ai mana. Zanyi fatan Allah ya bani ya’ya masu kyan ki da irin tarbiyyar ki. Zanfi kowa farin ciki a rayuwa ta. Allah ya tabbatar mana da alheri!”

Kanta a kasa tace

“Allahumma Ameen Yaa Deedat…..”

Da sauri ya kalleta domin jin sunan yayi har tsakar kansa. Dan haka yace

“Me kika ce?”

Fuska ta rufe da hannu tana murmushi. Ya juyo yana kallon ta sosai yace

“Please say it again Sweetheart!”

Shiru tayi kanta a kasa tana wasa da yatsun ta. Hannu yasa ya kamo hannunta da take wasa dashi ya ri’ke hannun duka biyu tare da fadin

“Please mana. say it again pleaseee!”

Riike mata hannu da yayi yasa komai dake jikinta ya tsaya wannan ne karo na farko da namiji ya taba, taba mata jiki taji wani abu, danko mazan da take iskanci dasu bawai tana jin wani abu bane kawai tana dai yine, amma shi Ahmad hannunta ya ri’ke yasa tana jin wani abu tun daka tsakiyar kanta Kar kasan kafanta, kokarin Fara Jan hannunta tayi daka nashi, amma ta kasa.

Muryar ta na rawa tace

“Please ka sake min hannu ba kyau fa.”

“Time is going it’s almost time for prayer kan na tafi ina son naji ya matsayi na a gun ki yake.”

Shiru tayi ta kara yin kasa da kanta. Kallon ta yayi yace

“Talk to me mana!”

Kin cewa komai tayi. Yai murnushi yace

“Shikenan ni zan tafi sai munyi waya ko in na dawo. But ki sani ban da sukuni saboda ban san wane matsayi na samu agun ki ba. Nagode da kika fito sai anjima!”

Yana fadar haka ya fice a gidan. Da kallo ta bishi zuciyar ta na bugawa. Sai da taga tashin motar sa sannan tayi cikin gida. Daki ta shiga ta fada saman gado tana mai da numfashi kamar wacce tai gudu.

*

**

***

****

*****

******

Hajiyar na tsaye Khaleel ya shigo bai lura da ita ba ya shige ciki. Da sauri ta juyo tana kallon sa tace

“Khaleel!”

Juyowa yayi yana murmushi yace

“Na’am Mom ya gidan?”

“Ina kuka je kuka kai dare haka?”

Ido ya zaro yace

“Mom baki yadda dani bane? Kinsan hali na ni ko mata ban fiya kulawa ba kema kin sani.”

Ajiyar zuciya ta sauke ta karaso ta zauna shima zama yayi yace

“Mun kai sakon ne sai Marwa yai min waya akan yau ne birthday din sa. To wannan dalilin ne yasa mukai dare amman Mom ba wani abu fa.”

“Amman nace maka ka daina shishigewa Sakina ko?”

Kallon Hajiyar yayi yace

“To Mom why? Naga yarinyar nan bata da aibu Mom tana da nustuwa da hankali gata beauty!”

Baki ta saki tana kallon sa tace

“To bana so, na fada maka ko?”

“But Mom nifa na fara jin wani abu akan ta. Is like i love her. Kai i love her ma Mom wallahi tinda na daura ido na akan ta naji ina son ta.”

“What?”

Hajiyar ta fada  da karfi. Kai ya gyada yace

“Yes Mom i love her wallahi har na fara mafarkin ta xama uwar ya’ya na ta haifa min beautiful babies like her!”

STORY CONTINUES BELOW

“To Sakina dai ta kusa aure.”

“What aure kuma? Dawa? Tab wallahi sai dai in dani ba mai aurar ta sai ni. Ni kadai ne mijin ta dan ni aka hallice ta dan haka koma wanene zai aure ta to nafisa son ta.”

Sai kuma ya kama hannun Hajiyar yace

“Mom tinda ‘yar kawar kice ki shige min gaba akan abun nan. Wallahi Mom da gaske ina son ta ban taba son wani abu kamar yadda nake son ta ba dan Allah Mom ki tausaya min please 🙏 “

Hawaye ne ya shiga zubo masa. Hajiyar ba karamin tsorata tayi ba ta kwace hannun ta tace

“Khaleel ka bar maganar nan.”

“I can’t mom. I can…”

Mikewa tayi tace

“To ni ban yadda ba.”

“Why Mom menene aibun Sakina ne wai please naga yarinyar nan bata da aibu in da tana dashi ki fito ki fada min mana.”

“Babu but dan kawai an kusa auren tane.”

“But Mom ai ba a daura auren nata ba. Naga ko ran daurin aure ana iya canja miji bare yanzu da ba auren za ai ba.”

“Khaleel ka shiga hankalin ka fa.”

Kasa yayo da murya ya kara rike hannun ta yace

“Mom please wallahi am not joking i love sakina. I can’t do without her please Mom help me.”

Hannun ta ta kwace ta mike ta nufi stair. Khaleel ya mike a zafafe yace

“Wai what is going on Mom? I didn’t understand you. Meyasa kike haka sam na lura kece bakya son alakata da Sakina. At all bakya so kiga na mata magana just magana fa bare kuma ki same mu muna hira or something else, ki fada min menene illar yarinyar bayan tare nazo na tadda ku kuma kina son ta kina bata kulawa. In tana da aibu ai ba zaki sakar mata jiki haka ba. To ni naji ko tana da matsala ki fada min zan gyara ta tinda ina son ta. But please Mom kada kice ba zan aure ta ba please.”

Ya karasa maganar cikin muryar roko yana hade hannayen sa. Sama ta haye ta bar sa tsaye a gun kawai.

Kan kujera ya fada yana sakin ajiyar zuciya.

Sannan yace

“I can’t…. I can’t leave her. I love her.”

Da kyar ya mike ya haye sama shima ya shige dakin sa. Wanka yayi ya saka kayan bacci sannan ya nufi dakin Mom din sa.

Zaune ya same ta a saman gadon ta ta zuba tagumi. Karasowa yayi a hankali ya zauna a gefen ta hannun ta ya cire yana kallon ta yace

“Mom tell me the reason why u don’t want me marrying Sakina?”

Ajiyar zuciya ta sauke tace

“You will not understand Khalleel!”

Kallon ta yayi da mamaki yace

“Why will i not going to Understand Mom. Tell me i will understand everythig!”

Ido ta lumshe sai kuma tace

“Tashi kaje ka kwanta dare yayi.”

Ta koma ta kwanta tana jan bargon ta ta rufa. Mikewa yayi yana kallon ta yace

“Gud nyt Mom!”

“Aha Nyt have a nice dreams!”

Juyawa yayi ya nufi makunni ya kashe fitilar shima ya bar dakin.”

Dakin sa ya koma ya zauna ya fara tunanin dalilin da Mom bata son wannan abun bayan Mom tana masa duk abinda yake so. Wanda baya so kuma bata so sam.

Hajiyar kuwa bayan fitar Khaleel mikewa tayi zaune ta zuba tagumi tana tunanin makomar ta. Shin ta ina zata fara dan sam ta haramta aure tsakanin ta da Khaleel domin kuwa babu ta yadda za ai mu gama shai’danci da yarinya sannan dan ta ya aure ta. Zatafi yiwa dan ta sha’awar ya auri mace ta gari wacce zataga girman ta. Amman Sakina inaaa.

Ta ina zata fara me zata cewa Khaleel ya hakura da son yarinyar nan. Ya’yan ra biyu daga Khaleel sai Abbas wanda tafi son Khaleel nesa ba kusa ba bazata taba yadda ya auri Sakina ba. Ta ina haka zai faru ma.

Me zata fada masa da zai ce baya son yarinya lallai duk abinda zata fada ba yadda zai ba. Zama da yarinyar take a gidan ta kuma kamar yadda ya fada tana ji da son ta hakan ne.

Akwai matsala dan kuwa ba zata taba yadda tana ji tana gani Khaleel ya auri Sakina ba. Kai kome ya dawo dashi ma. Ga Khaleel da dan banzar zuciya kafiya taurin kai naci.

Ranar sam Hajiyar batai bacci ba kwana tayi sake sake ta kulla wannan tawarware. Can wajen ukun dare ta mike ta tafi dakin Sakina. Sakina na bacci cikin kwanciyyar hankali.

Hajiyar ce ta shigo ta zauna ta dan taba ta tace

“Baby!”

Juyi Sakina tayi tana mika tace

“Hajiyar gaskiya yau na gaji ba zan iyai miki komai ba.”

Ta juya ta koma ta kwanta.

“Ni ba wannan ya kawo ni ba magana zamuyi.”

“Da daren nan gaskiya ki bari sai da safe wallahi bacci nake ji sosai.”

Taja bargo ta rufe har kanta. Da ido Hajiyar ta bita da kallo tafi awa tana zaune sannan ta mike ta koma falo. Har asuba tana falo sannan ta koma sama dan tayi sallah.

A stair suka hadu da Khaleel da ya sauko sanye da jallabiyya zai tafi mosque. Kallon ta yayi yace

“Daga dakin ki nake naga bakya ciki.”

“Na sauko shan ruwa ne.”

“Alright bari naje massalaci sai na dawo.”

Ya sauka ta bishi da kallo can tace

“Why Khaleel and Sakina?. Why?”

Sai ta haye sama kawai ta shige daki ta.

*To fa qaqaqara qaaqa?*

Kwanan su uku amman sam Muhammad bai nuna yana son ya kusance ta ba. Itama kuma hakan da yayi sai ya kara bata damar sakewa dashi. Dan a kwana ukun nan sun kara shakuwa sosai. Tare suke yin komai na gidan shara wanke wanke sannan girki. Su zauna suci abincin su. Sannan suyi wanka kowa yai wa dan uwan sa kwalliya su zauna hira. A hirar yawanci akan gidan suke yi. Wanda Fauziyya ita ba abinda tafi ji kamar Hafsa da ta baro takira wayar ta a kashe kuma daman tasan ita waya bata dame ta ba ko dan  saboda abokan shashancin su su dame ta duk da ta canja sim amman Farisa sai take basu sabon sim din da ta canja.

Zaune suke a falo kan ta a kan cinyar sa tana kwance shi kuma yana zaune. Sanye take da wata atamfa kofi kala wacce take da zane circle an yiwa circle din colour da milk, orange,  and yellow. Dinkin riga da siket. Rigar three quarter ce kan ta a tsefe yake yana ta shafa shi dan baki ne sidik kuma mai yawo da laushi. Fuskar ta tashafa hoda da jan baki sai kwalli da tasa. Sai tashin kamshi mai dadi take.

Shi kuma yana sanye da milk kala shadda yai kyau in ka ganshi kaga sabo ango. Wayar sa ce tai kara wannan yasa ya dauka yana ganin Ummin sa ce ya saki murmushi sannan ya dauka ya kai kunnen sa yana fadin
“Gaskiya Ummi nayi fushi yau three days baki kira bi ba kuma na kira wayar ki a kashe.”

“Sorry mai babban su. Na barka ne ka dan huta da amarya. Kuma na bar Dubai ne ina China shiyasa. Ya kake ina ‘yar tawa.”
“Alhamdulillah! Ya kike to ya hanya?”

“Alhamdulillah. Bani ‘ya ta naji ya take.”
Mika mata wayar yayi ta kalle shi yace
“Ummi na ce.”

Da sauri ta amshi wayar ta mike zaune ta kara wayar a kunnen ta.
“Assalamu Alaikum!”
Ta fada cikin sanyin murya da nutswa.

Murmush Ummi ta saki sannan tace
“Wa’alaikum salam ‘ya ta ya kike?”
Alhamdulillah ina yini?”

“Lafiya lou. Ya sabon waje da bakunta ina fatan dai ba wata matsala ko? In da matsala ki fada min dan nasan Mai babban suna da damu kar ya na damun ki da yawa.”
Kai tayi kasa dashi dan kunya ma ta bata tace
“Ba komai.”

Hannun ta dayan ya kama yana wasa dashi. Ummi tace
“To madallah. Jibi zan dawo bansan yaushe zaku zo ba amman zan so da na dawo kuzo ayi komai da wuri.”

“Insha Allahu Ummi.”
“Yauwa. Allah miki albarka. Sai anjima”
Mika masa wayar tayi tai kasa da kanta. Ummi tace
“Mai babban suna a kula da ‘ya ta kada ka na takura mata.”

“Ummi wane takura mata zanyi?”
“Ni dai na fada maka.”

“To Ummi yaushe zaki dawo?”
“Jibi insha Allahu. Yaushe zaku taho?”

“In kin kwana biyu kin huta”
“Toh shikenan. Allah ya baku zaman lafiya”

“Amin Ummi nagode.”
Sukai sallama. Kallon Fauziyya yai da ta nutsu waje daya yace
“Ya dai Bae?”

Dagowa tayi yaga idon ta ya kawo ruwa matsowa yayi da sauri yana fadin
“Menene kuma.”

Jikin sa ta fada ta saki kuka.
“Ya salam! Whats wrong? 😤”
Kuka take sam ta kasa magana in banda shishshika ba abinda take yi.

STORY CONTINUES BELOW

Bayan ta yake bubbuga wa yana lallashin ta da kalamai masu yawa amman ji take kamar kara tunzura ta ake yi. Dago kanta yayi yaga yadda take zubar da hawaye. Harshen sa ya saka yana lashe hawayen nata. Yana gamawa ya hade bakin su yana bata wani hot kiss.

Shiru tayi tana amsar salon da yake aika mata. Jikin ta take yai sanyi tai lakwas a jikin sa kukan ya tafi. Sun jima a haka sannan a hankali yai pluging out. Jikin sa ta fada ya rumgume ta tsam kamar zai mai da ta cikin sa.

“Did u want me to say something?”
Ya tambaye ta. Kai ta gyada masa a hankali yace
“Tell me whats wrong?”

“Am scared! 😨”
“Scared of what?”

“Kada yan uwanka su gane wacece ni su ce ka sakeni.”
Tana fada ta fashe da kuka.

Murmushi yayi yana shafa kanta a hankali yace
“Su suke auren ki Baby. To ina ruwan yan uwa na dake? Ki kwantar da hankalin ki Ummi ce matsalar kuma Ummi knows something on you but not all dan haka kada ki damu since before u accept my love Ummi ta sanki kuma take son ki dan haka ki daina tsoron wannan ki fara tunanin a new life da muke gab da shigar ta. Kinji.”

Kai ta gyada. Rumgume ta yayi yace
“Yauwah. I love u Fauziyya i will always and forever love u till the entile of my life. Kinji. I promise u will now regard been with me. U will proud of been with me insha Allahu.”

“Allah ya yadda.”
Ta fada hawaye na zubo mata. Hannun sa ya saka yana goge mata yace
“Wai ni kukan nan na menene ne?”

Ya dago habar ta yana aika mata da wani irin kallo da yasa tajin kunya nan da nan ta saka hannun ta ta rufe fuskar ta. Yai murmushi ya dan ciji hannun. Da sauri fa dauke tana yarfe hannun hadi da turo baki ta fara magana cikin shagwaba da kuka tace
“Da zafi fa.”

Ido ya zaro yace
“Haba dai naga hannun!”
Mika masa tayi ya hau hurawa da bakin sa yace
“Sorry rama to.”

Kai ta make a kafada tana murmushi. Yace
“To ni bari na rama miki.”
Kan ta farga har ya kama hannun sa ya cije da sauri ya saka hannu ta janye hannun nasa. Tana kallon inda ya cixa ga shatin hakoran sa nan.
“Ni nace ka rama ne ba na hakura ba.”

Ta fada kamar zatai kuka.
“To am sorry don’t cry!”
Ya fada yana janyo ta jiki sa. Kan ta ta daura akan kafadar sa tayi lamo.

A hankali tace
“Ina son a gyara min kai na fa ka hanani zuwa kwata kwata a gida.”

“Sure?”
“Yes!”

“Ok don’t worry zan kaiki kinji?”
Kai ta gyada yace
“Amman ni banga abinda kan yayi ba ma.”
Yana fada ya daura hancin sa a kanta yana shakar kamshin man da take amfani dashi mai dadi.

“Kai ai daman haka zaka ce.”
Ta fada tana lumshe ido. Dan bacci ta fara. Bata baccin rana amman daga auren su ya koya mata kullum sai sunyi wanda tare suke kwanciyya makale da junan su.

*
**
***
****
*****
******
Kabir ne zaune yana operating system dinsa. Sallama yaji anyi
“Assalamu alaikum!”

Wannan yasa ya dago yana amsa sallamar tasa. Yace
“Wa’alaikim sallam!”
Bayan ya amsa ya dauke kansa. Yana cigaba da danna system din sa.
Zama Isma’il yayi ya mika masa hannu ba tare da ya kalle shi ba ya mika masa sukai musabaha. zaman shiru sukai. Can Isma’il yace
“Wai me ke faruwa ne Kabir?”

“Me ka gani?”
“Gani nai sai wani share ni kake yi ne,”

“Da ina share ka haka kawai ne,?”
“Wannan yasa nake son sanin me nayi maka?”

“Me ka dauki Halima ne tukkuna. Jiya naga yarinya a supermarket ka rikice mata ita kuma Halima ka kai ta ina? Isma’il kar kace min ita ma yadda kake da sauran yan matan kayi da ita bayan u promise ba zaka kara kusantar ta ba kuma kace min zaka aure ta ko ba haka mukai ba.”
Murmushi Isma’il yayi yacr
“To shine me? Kana zaton dan zan auri Halima shine ba zan kula ko wacce mace ba ko na fada maka ita ka dai zan aura kada ka manta fa ni mijin mace hudu ne. Kai kasan Halima is too young a cikin kalar matan da nake mu’amala dasu kasan me she is special dan duk da wadan can sun girme ta kuma suna da wasu abu da yafi nata amman fa itama tana da zafi. Ko da yake ba wannan xancen muke ba.
Gaskiya ko na auri Halima sai na kara da wata.”

STORY CONTINUES BELOW

Jingina Kabir yai yana kallon sa. Can ya dauke kai ya cigaba da abinda yake dan he is just out of word bai san mema zai ce ba. Ya na tausayin Halima da ta kamu da son wannan abokin nasa kuma yana tausayin Isma’il dan yasan abinda yai dai an masa………..

“Gaskiya yarinyar nan ta tafi dani sai yanzu na samu matar aure.”
Isma’il ya fada wanda hakan ya katsewa Kabir tunanin da yake ya dago yana kallon sa.

“Yes wallahi ban taba jin son mace kamar ita ba. Da aure nake son ta seriouslly. Please friend help me,!”
Wani kallo Kabir ya watsa masa yace
“Haliman fa?”

“Itama ina son ta amman tinda Mahaifin ta yaki yadda dole na fara da wannan.”
“No!”
Kabir ya fada a tsawace. Yace
“Baka isa ba baza ka fara auren wannan ba in ma dole sai ka aure ta sai munje mun samu mahaifin Halima tukkuna”

Wani kallo Isma’il yai masa yace
“Kai uba nane wai!”
Ido Kabir ya zare yana kallon sa. Mikewa Isma’il yayi yace
“Ko dan kaga ina son ka ina bin abinda kake so ne. To wallahi ka sani ba zan abun da kake so ba zabin raina zan bi.”

Yana gama fadar haka ya fice a office don. Da ido kawai Kabir ya bishi yana girgiza kai.
“Duk yadda akai Isma’il ya gama da Halima ba sau daya kadai sukai having sex da ita ba”

Ya fada yana tusa yatsun sa a cikin sumar kan sa.
“Innalillahi wa’inna illahir rajiun! Halima me yasa kika sake da Isma’il duk yadda naso tsairatar dake. He just want to broke ur heart not only ur herat he takes what is more important in your life. Ya Allah!”

Ya sauke hannun sa bisa fuskar sa. Ya jima hannun sa na rufe da idon sa sai kuma.ya janye su. Hawaye ne kwance a idon sa.
“Tayaya zan taimake ta. Dan nasan Isma’il will never marry you.”

Baki ya cije ya saki tsaki
“To ina ruwa na ni nace ta bashi kan ta.”
Sai kuma yai shiru yace
“But i love her why Halima Yaa Allah! Meyasa nake son ta. Meyasa Allah ya jarabcen da son ta. After all ni ba mazinaci bane.”

“Dan ka ceto ta daga halin da Isma’il zai jefa ta.”
Zuciyar sa ta fada da sauri ya furta
“Tayaya?”

Zuciyar sa tace
“Yanzu in Isma’il ya rabu da ita bayan ya lalata mata rayuwa wani hali kake tunani zata shiga.”

“Wane hali zata shiga?”
Ya kara questioning kansa. Zuciyar sa tace
“Kila ta wannan sanadin ta rasa ranta farin cikin ta iyayen ta karshe ma ta zama karuwa.”

“Ya salam!”
Ya fada yana girgiza kan da.
“No… No Halima. Ba zata zama ba. Tayaya xan taimaka mata Ya Allah ka bani mafita.”
Haka ya dinga surutai kamar wani zararre. Can yace
“Ita waccan da yake so fa zata amshe shi.”

Yai shiru can yace
“Nasan waye Isma’il zai iya yin komai dan ta amshe shi.”
Baki ya cije yace
“In har ina rayuwa ba zata amshe ka ba kuma ba zaka same ta ba dai dai ka samu dai dai da kai.”

Ido ya runtse yana jin wani zafi a can kasan zuciyar sa. Aikin da bai karasa ba kenan rayuwar sa duk ta dagule a lokacin.

*
Halima ce zaune rike da wayar ta. Ta kira layin Isma’il yafi sau bakwai bai dauka ba.
“Na shiga uku Allah dai yasa lafiya!”

Ta fada tana kara trying dailing number tasa amman dai bai picking ba tagumi ta saki tana fadin
“Kwana biyu fa kenan ina ka shiga ka barni da damuwa da tunanin ka My Love. Anya kuwa lafiya two days.”

Tagumi ta saki tana jin zuciyar ta na mata zafi. Hajara ce ta shigo ta tsaya kallon ta can tace
“Sis lafiya kuwa?”

Tagumi Halima ta sauke tana ajiye wayar ta tace
“Kwana biyu sam Isma’il bai kira ba kuma in na kira baya dauka.”

“Me ya faru to? Ko kunyi fada ne?”
“Ina fa ba abinda ya hada mu wallahi.”

“To Allah yasa lafiya.”
“Gaskiya da kyar in lafiya saboda wallahi sam Isma’il baya iya kwana bai kira ni ba amman yau kwana biyu fa. Ni dai ina tsoro!”

“Kada ki damu insha Allahu lafiya kalou. Ki daina saka damuwa kijin.”
Hawaye ne ya zubo maya tace
“Dole fa na damu Hajara. Dan Isma’il ya riga ya koyan son sa da rayuwa dashi in na rasa sa ban san ya zanyi ba gaskiya.”

“Kina tunanin abu me kyau sister nothing bad will happened insha Allahu kinji.”
“Uhmm thanks!”

“Daman wata magana nazo muyi.”
“Ina jin ki.”

“Gani nayi tinda Baba ya sauko mai zai hana ki tare shi da kanki da zancen Isma’il ki nuna kina son sa kiji mai zaice.”
“Hajara ina tsoron Baba fa kinsan halin sa zai iya zaneni.”

“Amman ni a ganina zai fuskance ki tinda fa kanki kika kai masa maganar ko?”
“Uhmm da dai ba Baba bane da Isma’il yaje ba cewa yai wai nawa nake. bayan ni din menene ba zan iya ba.”

“Ki daure ki sameshi kiyi addu’a Allah daura ki akan sa ya yadda.”
“Ina tsoro fa”

“Ki ajiye tsoro ki saka kwarin gwiwa kinji?”
“To shikenan zan gwada ko ni da Isma’il ma huta da *Wannan rayuwar* da muke gudanar wa.”

“Wacce rayuwa fa!”
Ido ta zaro dan bata san maganar ma.ta fito fili ba tace
“Kina gani irin tafa yanzu ban san a halin da yake ba. Kan yazo gdn nan yakan dade in muyi aure fa kullum muna tare.”

“Haka ne. Allah ya bada sa’a!”
“Amin nagode.”

Sai bayan isha’i ya koma gidan sa. Bata falo dan haka ya nufi dining tin kayan da tayi amfani dasu na break har lokacin bata dauke ba. Kai ya girgixa sai ya juya ya nufi dakin ta.

Tana kwance akan gado hannun ta rike da wayar ta tana chat sai ganin sa tayi a kanta kawai dan ita ta zata ta rufe kofa. Da sauri ta mike tana zazzare ido.

Kallon ta yayi ya ga daga ita sai wani dan gajeren wando da half vest a jikin ta. Kai ya dan dauke yai gefe dashi yace
“Me kika dafa ne?”

“Banyi girki ba.”
“Saboda me?”

“Saboda naga akwai ragowar kwan da na soya da safe sai kawai na kara shan tea.”
“Ni kuma fa?”

Shiru tayi sai kuma tace
“Bari na samar maka wani abun!”

Kan yai magana ta fice da sauri. Dakin sa ya koma ya kakkabe gadon sa sannan ya shiga ya watsa ruwa ya fito. Gajeren wando kawai ya saka ya zauna a gefen gadon sa yana dailing number Hafsat amman a kashe.

Tsaki ya saki ya ajiye wayar dan kuwa ya manta sam number ta bata shiga. Yana zaune wayar ta hau kara ya dauka. Abokin aikin sa  ne lawan dan haka ya dauka yana fadin
“Assalamu Alaikum!”

Daga dayan bangaren aka amsa da
“Wa’alaikum salam ango kasha kamshi.”
Yai murmsuhi yace
“Ya aiki?”

“Alhamdulillah ya hutu?”
“Hutu ya kare jibi zamu taho ai.”

“Ok Allah kaimu agaida amarya sai da safe.”
Ya fada yana kashe wayar. Hannah ce ta shigo hannun ta dauke da tray. Ajiyewa tayi plate ne sai juice da cup. Sauka yayi ya zauna ta mike zata fita yace
“Zauna in gama.”

Kamar tayi kuka haka ta zauna ya bude plate din yaga indome ta dafa sai kwai da ta dafa. Ci yayi dan yai bai ci komai ba. Ya gama yasha lemo sannan ya ce
“Kwashe kayan ki dawo.”

Debewa tayi ta kai ta dawo kallon ta yayi yace cire hijab din. Kallon sa ta tsaya ya mike ya shiga bathroom bai jima ba ya fito yace
“Me nace miki?”

Yadda ya hade fuska yasa ta zare hijab din. Zama yayi yana sakin murmushi yace
“Ko kefa.”

Sai kuma yace
“Yanzu Hannah wane aiki ne a gidan nan da ba zaki iya ba. Just shara da wanke wanke ne fa kawai.”

“Haba Yaa Ahmad amman ai yanzu da nai aure na huta ko? Nima a ajiye min masu min aiki na samu na huta.”
“Au dan hutu kawai kike son masu aiki?”

Kai ta gyada yace
“Zan na taya ki sai muna yi tare kinga ai ba zaki wahala ba ko?”
“A’ah ni dai dan Allah ka bari kaga Momy ma ta kirani tace guda nawa nake so?”

Kallon ta yayi yace
“Nawa kike so to?”
” nace ko.uku ma sun yi.”

“Uku kiyi me da guda uku?”
“Shara,  wanke wanke da girki.”

“Ke kuma kiiyi me?”
“Nothing “

“To ban yadda ba.”
“Kamar ya?”

“Ni ba zanci abincin masu aiki ba kuma daki na ma ba za a gyara min ba in ba ke ba dan haka ko an kawo yan aiki ke zasu nayiwa aiki bani ba kin gane?”
Shiru tayi. Ya kama hannun ta yace
“Ba zan hana ki yan aiki ba amman ki gane ni bana son su. Amman tinda kina so na barki a kawo amman ni koma nawa ke zaki na min kinji ko?”

STORY CONTINUES BELOW

Bari ta turo. bakin ya cafke ya fara kising nata. Daga haka dai labarin ya canja. Sai da ya gurje ta san ransa sannan ya kyale ta. Kuka ta fara ya matsa kusa da ita yace
“To menene kuma?”

Juyawa tayi tana kuka. Dagota yayi yace
“Tell me da zafi ne? Ko bakya jin dadi ko bakya gamsuwa ne?”

Baki ta turo. Yai murmsuhi yace
“Fada min menene matsalar?”
Kai ta girgiza yace
“Oh nagane nine bakya son na kusance ki ko? Da farko ke kikai min tayin kanki gashi yanzu kuma naji abinda ba zan iya rayuwa ba shi ba. Amman ki ban lokaci nan kusa zan kara aure na samu wacce zata na rage min damuwa da deben kewa in mun gama mu’amala ta rumgume ni tana min godiya ba ke ba in mun gama ki sa min kuka. In na farko na ji miki ciwo to na biyu da yau fa.”

Yana fadar haka ya mike ya shige bandaki. Mikewa tayi ta nufi dakin ta. Wanka tayi ta fito sannan ta saka kayan bacci. Itama tana son mijin ta amman kawar ta tace kar ta sakar masa ya gama rainata wai da baya son ta amman ganin tana da mamora shine zai takura mata to taja ajin ta. Wannan yasa take kin sakewa dashi tana shashare shi amman itama fa ba ta son hakan tana son mijin ta to ya zatai.

Tuno abinda ya fada wai zai aure ya kara bata mata rai. Har yaushe sukai auren da zai ce zaiyi aure yana fada ne dan kawai  ta sakar masa jiki ya durje ta haka kawai taje ta tsufa to ba zata yadda ba kuma tasan ko zai auren ma Momy ba zata bar shi ba da haka ta samu relief ta koma ta kwanta.

Yana fitowa yaga bata dakin ya gyara gadon sa sannan ya koma ya kwanta yana jan pillow. Zai so ace matar sa ya rumgume amman ina ta tafi ta barshi. Ido ya lumshe yana tunanin Hafsa. Da tunanin ta bacci ya dauke sa.

Washe gari da safe sai karfe goma ya tashi. Bai fito ba sai da yai wanka ya shirya tsaf sannan ya fito lokacin karfe sha biyu saura. Kallon ta yayi tana zaune a falo ta ci kwalliya cikin wata doguwar riga ta atamfa tayi kyau har ta gaji da yin kyau. Kai ya dauke ya nufi kitchen kawai.
Ruwa ya dauka yasha sannan ya fice a compound ya zauna har akai kiran sallah karfe daya yaje yayi sallah. gidan da ya dawo ya same ta tana  kallo  ya kalle ta uace
“Kinyi sallah ne?”

“Sai biyiu!”
“Ok ki tashi muje ki gaida Momy dan gobe zamu ….”
Bai karasa maganar da zai ba ta mike da sauri tana fadin
“Da gaske?”

Sai kuma tayi dakin ta tana murna. Mayafi ta dauke ta kara feshe jikin ta da turaruka masu dadin kamshi. A falo ta same shi a tsaye ta kalle shi tace
“Na shirya.”

Kallon ta yayi ya dauke kai ya fice ta bishi da sauri. Gidan su ya nufa suna zuwa yai parking kan ya fito har tayi cikin gida da gudu. Yana shiga ya tadda ta jikin Momy. Kallon su yayi kawai ya dauke kai ya wuce dining dan yunwa yake ji sosai.

Yana zuwa ya zuba abinci ya fara ci. Yana cikin ci Basma ta fito daga kitchen kallon sa tayi yace
“Ina yini Yaya?”

Hannu kawai ya daga mata. Tana gano Hannah ta karasa wajen da sauri tana fadin
“Sis!”

Sai kuma suka rumgume juna suna ihu. Tsaki ya saki kawai ya mike ya fice a gidan.

*
Wani shagon siyar da waya ya nufa. Ya fada musu wayar da yake su so bashi ya biya sannan ya fito. Ya shiga motar sa.

Hudu da hamsin dai dai yana kofar gidan su Hafsa yaro ya aika a kira ta bata jima ba ta fito. A soro ta tsaya kamar jiya ya karasa ciki. Kallon ta ya tsaya yi kan ta a kasa tace
“Ina yini?”

“Lafiya lou na same ki lafiya?”
“Alhamdulillah!”

“Tin da na tafi kike raina da tunani na dake na kwana Hafsa. Na kira wayar ki ban san meyasa ba a kashe, ina sonki da gaske bada wasa ba, tunda na ganki nake sonki, bana tunanin akwai abunda zai saka in daina sonki, Hafsat daga lokacin da na hadu dake na fuskanci abubuwa da dama, kina da addini kin fito gidan mutunci iya wannan ya isheni, Hafsa duk irin yanda nake son matar da zan aura ta kasance kina dashi, ina da kishin abunda nake so, ina son mace Mai suturta jikinta Wanda ke gashi kullum kina suturce da hijab,  wannan abubuwan ya isa duk wani namiji yayi burin samunki a matsayin matar auransa kuma Uwar y’ay’ansa, I don’t care ko daka ina kika fito ke nake so bawai wani abuba, inda kin San yanda nake jinki a raina da kin tausaya min. Kina da kyau wanda yake da sanyi da kara min son ki Hafsa. Nasan nayi dace kuma mun dace a haka ma. Love u Hafsa dan Allah kice kina so na ko nai miki kuka.”

Yadda yai maganar ne ya bata dariya. Dan Bata san lokacin da  ta saki dariya. Domin yadda yai maganan shi ya bata dariya.
Ganin tayi dariya shima yayi murmushi tare da fadin
“Yauwa na saki dariya am happy now to please accept my love!”

Murmushi tayi. Sai kuma tace
“Har yaushe kayi aure kake kara neman wani aure!”

“Haramun ne?”
Ya tambaya yana kallon cikin ido ta. Kai tayi kasa dashi yace
“Naga ina da damar auren mata hudu a lokaci guda ko? To bare ni yau kwana mu sha shida da aure kinga ai zan iya ko?”

“Amman yai kusa!”
“Ke kike ganin haka ni buri na kawai na sameki Hafsa. Dan Allah ki ban dama Hafsat.”

Shiru tayi yace
“Ko ban miki bane?”
Satar kallon sa tayi a ranta tace
“Ai kafi karfi na ma.”

“Banfi karfin ki ba Hafsa.”
Da sauri ta dago yai murmushi yace
“Eh banfi karfin ki ba wallahi kada ki kara fadar haka. Ki yadda dani dan ban jima da aure ba bashi yake nuna cewa gun ki nazo na yaudare ki ba. Na yiwa Dady na maganar ki tin kan nai aure nace ina da wacce nake so kuma yace min ya yadda ki fada min indai kina son auren mu ko a yau ne sai an daura shi dan ni a shirye nake Dad dina bai da matsala shi yai min alkawari nasan zai shigen gaba Hafsa.”

“Zanyi tunani toh!”
“Wane tunani? Ko da yake shikenan Allah yasa tunanin ya baki damar yadda dani.”

Tai murmushi yace
“Gobe zan koma gun aiki na zan yi sati biyu sannan in zo in ganki ina fatan kan lokacin an gama tunani da ya dace.”

Kai ta gyada yace
“Wayar ki fa meyasa bana samun ki?”
“Ba komai!”

“Au dan kar na kira ne kike kashe ta?”
Kai ta girgiza yace
“To shikenan. Ya su amarya suke?”

“Suna lafiya!”
“Masha Allah. Ni zan tafi Hafsa sai nan da sati biyu amman ki sani i love u!”
Murmushi kawainm tayi sai kuma tace
“Nagode!”

Ya ce
“Nike da godiya.,”
Ya juya ya fita. Cikin gida ta shiga.
Mota ya koma ya dauko ledar da yazo da ita. Yaro ya sama ya ce
“Ungo kaiwa Hafsa!”
Ya bashi dari biyar ya shiga mota ya tafi.

Shigar ta daki kenan yaron ya shigo ya mika mata yace
“Inji wani a waje wai in kawo miki!”
Amsa tayi ta shiga daki. kwanciya tayi tare da lumshe ido duk abunda ya faru ita da Ahmad yake dawo mata, da sauri ta bud’e ido tare da tashi ta dauko ledar da ya aiko mata. Ta bud’e takarda ta gani ta dauka ta bude ta
“I love u Hafsa. In nace miki ban taba son wata ba a duniya kada ki karya tani ko ki zata da wasa nake wallahi da gaske nake zan iya komai dan samun ki zan kuma iya baki komai dan ki soni lokaci na kulawa ta da rayuwa ta. Hafsa da gaske nake son ki ki tausayawa bawan nan ki amshi soyayya ta.
Ni dai na gaji da rashin kunna wayar ki ga wannan nan kiyi manage da ita kuma ga sim nan ki kular min da kanki har naje na dawo gare ki i love u!”

Ido ta lumshe Bayan ta gama karantawa a hankali ta furta
“I love u Ahmad tin da na ganka na kamu da son ka amman ina tsoro ne. But i really love u with all my heart!”

Ledan daya ta bude sai taga kwalin waya ta iPhone 11+ sai su turare masu tsadan gaske guda biyar sai bandir din 1k guda biyu dubu dari biyu.

Daukan kwalin wayan tayi ta bud’e tare da sawa a caji, ba karamin jin dad’in kyautar tayi ba, Sallah ta ta shi yi.
Karfe tara wayar tayi full dan haka ta cire ta saka sim sannan ta fara operating nata. Number sa da ya rubuta mata a jikin takarda ta dauka ta saving da My Deedat sannan ta fara tura masa sako kamar haka.
“Naga sakko nagode Sosai ban San wani irin godiya zanyi ba, Allah ya biyaka da gidan Aljanna, amma wannan kayan kaman sun min yawa kuma ni bana son kana wahala dan Allah. Da fatan kaje gida lafiya. Nagode!”
Tunani tayi ta tura mai ko Karta tura, tayi wajan minti biyar tana tunani sannan ta tura mai.Yana wasa da gashin kanta ma bai san har tayi bacci ba sai da yace

“Bae! Bae!!”

Yaji shiru sannan ya leka fuskar ta. Baccin ta take sosai hankali kwance. Murmushi ya saki ya gyara zaman sa yadda zata ji dadin baccin nata.

Sosai tayi baccin dan tun wajen karfe biyu sai hudu saura ta farka. A jikin sa taji ta. Dagowa tayi tagan ta kwance akan sa shi kuma yana kan kujera. Mikewa tayi wanda hakan ya farkar da shi.

“Har kin tashi?”

Ido ta zaro ta kalli agogo tace

“Har kuma? It’s almost time for asar fa.”

Agogo ya kalla ya mike da sauri yace

“Tab ai kam gashi kuma sai nayi wanka ba.”

“Wanka kuma?”

Ta tambaya.

Murmushi yayi yace

“Ai indai zan jini jiki a jikina sai kin haifar min da wani abun.”

Ido ta zaro sai kuma ta mike tayi daki da sauri tana fadin

“Kaii dan Allah!”

Mikewa yayi yana murmushi ya bi bayan ta. Zaune ya same ta a gefen gado. Zama yayi yace

“Ko zaki taimaka min?”

“Dame fa?”

“Wankan mana.”

Ido ta zaro tace

“Wayoo ni dai dan Allah kayi hakuri wallahi kunya nake ji.”

“Naga alama but wannan kunyar zan cire ta in ajiye ta gefe saboda naga alama in na bar ta zatana cutar dani.”

Ya fada yana zare rigar sa. Da sauri ta mike ta fice falo. Tana zaune ya fito daure da towel kan ta tai sauri tayi kasa dashi tana wasa da yatsun hannun ta.

Fita yai bai jima ba ya dawo kallon sa tayi ta gefen ido taga yana goge kansa da karamin towel Daki ta mike ta shiga ta fito daure da xani da hijab a jikin.

Wankan ita ma tayo ta dawo taga har ya canja kaya zai fita dan ana kiran sallah.

“Wankan me kikai?”

Ya fada yana kallon idon ta. Kanta tai saurin daukewa tana fadin

“Daman wankan kala kala ne?”

“Baki sani ba?”

Ya tambaya. Kai ta dauke zata shige yace

“Kema kin sani ai!”

“A’ah!”

“Au haka kika ce ko? Shikenan zan saka ki yin wani daban ba wanda kike son kice min kin sanin.

Yai murmushi ya fice.

Shiryawa tayi tai sallah sannan ta zauna tana tasbihi tare da godiya ga Allah sannan ya kara neman yafiyar Allah akan abubuwa da ta aikata a baya.

Tana zaune har biyar da rabi tai mamakin to ina Muhammad ya tafi har yanxu bai dawo ba. Tagumi ta zuba tana Addu’a Allah yasa lafiya domin kuwa da an idar da sallah yake dawowa. Sai karfe shida ya dawo ya zauna yana maida numfashi daga gani ya sha yawo ne. Da sauri ta dauko masa ruwa a kula mai sanyi ta bashi. Amsa yayi ya sha ya sauke ajiyar zuciya sannan ya kalle ta yace

“Allah miki albarka.”

“Amin. Amman ina kaje?”

Ta fada cike da damuwa. Kallom ta yai ya dan saki murmushi yace

“Kudin hannu na ya kare naje na samo bashi ne kinga ba komai a gidan ko?”

“Amman meyasa baka fada min ba akwai kudi a guna in baka kana juya su muna rufawa kan mu asiri.”

“A’ah ba zan amshi kudin ki ba.”

“Haba Mijina abu na ai naka ne. Dan Allah ka amsa dubu dari shida ne akwai wani store da na bude me zai hana ka amsa kana kular mana dashi kudin kuma in akwai wani abu da ya dace sai ayi me kace?”

Kallo ta ya tsaya yi sai kuma can yace

“Ni bana son in amshi kudin ki kuma su zo su dulmiye ne….”

“To menene ai shikenan haka Allah ya tsara.”

“Baby ni dai bana so na amshi kudin ki.”

“Saboda baka yadda dani ba. Ko saboda kana ganin zan maka gori ko ince ka ban abu na wata rana?”

“Ba ko daya Baby amma…..”

“Amman me? Ni dai in har ba dan abinda na fada bane ka amsa.”

“To shikenan!”

“Yauwah yau me xamu yi to? Me kake so kaci?”

“Komai my queen ta bani ina so.”

“Sure?”

“Yes!”

“Ok yau babu girki anjima muje resturant kawai muci abinci hakan yayi maka?”

“Indai yayi miki nima ya min.”

Fuska ta bata tace

“A’ah ban yadda ba gaskiya. Ka daina yadda da komai xan fada ka sani ko ban yi dai dai ba.”

“No Zabin Fauziyya shine nawa?”

“To ni kuma naka shine nawa!”

Yai murmushi ya dan ja hancin ta yace

“Kin ganki nan ko akwai wayo.”

Murmushi kawai tayi.

Bayan sunyi sallah isha’i suka shirya tsaf. Fauziyya sanye da riga da siket na material cotton ne sun mata kyau sai Muhammad dake sanye da bakin wando da blue black t-shirt.  hijab ya dauko ya mika mata. amsa tayi ta saka ya saukar mata har kasa. Murmushi yayi yace

“Yauwah.”

Ta kalli kan ta tace

“Me?”

“Kinyi kyau mana.”

“A hakan?”

Ta fada tana fita falo. Yace

“Ai ni a ko yaya ma kyau kike min. Wannan shigar kuma kinga tana miki kyau bame kallon min mata sai ni kadai.”

Murmushi tayi ta mika masa ATM din ta ya amsa suka fita. A kasa suka karasa titi suka hau napep suka karasa wani wajen cin abinci mai kyau. Suna sauka suka biya mai napep din ciki suka shiga suka samu waje suka zauna.

Waitress tazo ta basu menu amsa yayi ya mikawa Fauziyya ta kalle shi tace

“Ka zabar mana man.”

“No abinda kike so shi zanci.”

Amsa tayi tai selecting ta mika. Nan da nan akai serving nasu.

Shi ya dinga bata tana bashi a haka suka dinga cin abincin kamar ba za a gama ba dan suna yi suna soyayyar su. A haka suka gama suka mike suka je ta fada masa pin din ta aka tura kudin suka fito. Zasu tsallaka titi kenan taji ance

“Fauziyya!”

Da sauri ta juyo. Shema ce daya daga cikin kawayen ta na bariki kallon ta ta tsaya tace

“A sannu ya gida?”

“Baki ganeni bane Fauziyya?”

“Na gane ki mana.”

Kallon Muhammad tayi dake nesa dasu kadan tace

“Wannan handsome din fa amman gaskiya yayi gashi yaro dashi.”

*

**

***

****

*****

******

*******

*Am sorry it’s too short but akace da babu gwara ba dadi ko. Please manage in na samu chance gobe zan kara muku typing*

*Sai kuma ban hakuri da zan yi duk da baku san meya rike ni haka ba kusan kwana goma sha no update but wadan da suka kira ni duk na fada musu ban da lafiya da masu bibiyar WA NAKE SO? ayi hakuri nima ban so hakan ba amman haka Allah ya tsara bani da lafiya ne amman Alhamdulillah am ok now. Sai kuma biki da muke na daya daga cikin assocition din mu wato FATIMA MUHAMMAD SANI ZARAHARKEL (HABIBTY NAH) ina me rokar ku sa mata albarka ku mata addu’a Allah ya basu zaman lafiya da zuri’a mai albarka Allah kore duk wata fitina da abun ki. Amin.*

*Bayan shi kuma ku saka kanwa ta Nusaiba S Indabawa a addu’a akan Allah ya bata lafiya yasa kaffara Allah tashi kafadun ta. Amin*

.*Nagode da kaunar da kuke min. Wanda suka kira ban dauka ba kuyi hakuri wanda suka kira kuma mukai magana da masu text duk nagode Allah saka da alheri.*

Yana karasa gida gab da magrib, dan haka yana parking yai alwala sannan ya wuce masallaci yana zuwa ana kiran sallah sai da yayi ya shiga gaba d’aya, har sai da akayi sallah isha’i sannan ya  fito ya shiga gida.
Yana shiga ya tadda su dukkan su a falo. Momy ya gaisar ya nufi dining sai da yaci abinci sannan ya taso yace
“Tashi mu tafi.”
“Momy kice ya barni na kwana.”
Hannah ta fada.
“Gaskiya ba zaki kwana ba kuma ko kin kwana gaskiya gobe ba zan biyo tanan ba gwara ma kije ki shirya abinda zaki dauka.”
Yana fadar haka ya fice. Kallon sa sukai. Momy tace
“Kinga rabu dashi tashi kuje kiyi hakuri kinji. Yan aikin suna nan tafe.”
“To Momy nagdoe!”
Suka fita ita da Basma. A cikin mota suka same sa yana shirin tada mota. Tazo ta shiga. Basma tace
“Yaya Aah kyaye to.”
“Amim!”
Ya fada ya tada motar ya bar gidan. Suna zuwa gida kan ta fito ya fice ya na shiga direct gefen shi ya shiga ya fad’a toilet, shower ya saki ya dad’e ruwa yana dukanshi ba komai yake tunani ba saina gimbiyarsa ya dad’e a haka Kafin ya fito, kayan bacci ya saka, dan shirin kwanciya, kan gado ya hau ya dauki wayar sa da ya jona a charge.
Sakon ta ya gani yai murmushi sannan ya tura mata da reply kamar haka
“My Love I really miss you, komai na baki u deserve it, so ban son daka yau ki karamin godiya, love you so much!”
Tana kwamce sakon ya shigo bayan ta karanta ta saki murmushi. Ido ta lumshe lokaci d’aya kuma ta bud’e idon tare da kashe wayar dan tasan tsaf zai ce za kira.
Tagumi ta zuba tana me fadin
“Ina son ka Ahmad amman bazan cuceka ba, nasan da kyakyawan zuciya kazo min, rayuwa ta ni abun kyamace ga duk wani namiji mai kishin kanshi, na tabbata rabuwa dakai shine Alheri a tare dani, domin bazan iya fad’a maka wacece ni ba, “
Lokaci d’aya tasa hannu ta goge hawayen da ya zubo mata.
Yana tura text da ya tabbatar ta karanta ya fara  kira, amma sai me? Yaji ance number din a kashe, abun mamaki ya bashi dan yaga deliived report din da yaje. dan haka ya kara kira amma switch off, d’an shiru yayi alaman damuwa, tare da fadin
“Lafiya?”
“Nasan yanzu zai kira kuma in ya kira zai ji ba dadi shin na kyauta masa kenan in sa yaji ba dadi?”
Ta fada a zuciyar ta. Zuciyar tace
“Sam baki kyauta ba ki kunna ko da ya kira ai yaji a kunne yaji dadi ya zata bacci kike baki dauka ba.”
Da sauri ta dauki wayar. Kunnawa tayi ai kuwa taba gama oprrating ta hau kara tana dubawa taga shine. To daman wa zai kira in ba shi ba. Ta fada a ranta.
“Assalamu alaikun!”
Ta fada murya a sanyaye.
Ajiyar zuciya ya sauke yace
“Wa’aialkum salam Baby na bacci kika fara ne na tashe ki?”
“Wallahi har na kashe wayar zan kwanta nace kada ka kira kaji kuma a kashe.”
Murmushi yayi yace
“Amma naji dadi dan kuwa yanzu na gama kira naji a kashe amman na kasa hakura.”
STORY CONTINUES BELOW
“To ya kaje gida?”
“Lafiya  Alhmdulillah sai dai gaskiya I really miss you, Anya zan iya tafiya naje nayi har sati biyun nan kuwa Baby.”
Murmushi tayi tace
“Haba dai ai kaman yau ne kayi hakuri ka kuma daure.”
Yace
“Allah yasa dai na iya. Wallahi i miss u sam ban son na daina ganin ki.”
D’an shuru yayi Kafin yace
“Gaskiya Hafsat nan kusa za ai bikin mu!”
Dariya tayi tace
“Kai ba mun gama magana ba ne. Ka bari na gama tunani tukkuna mana.”
“Hmmm wallahi baki san halin da nake ciki bane. Ina son kasancewa dake. Ina kaunar ki. Ni har na gano kin yadda dani an mana aure nan ba da jimawa ba. Da na dawo ina son ki bari inga iyayenki nayi miki alkawarin Indai na gansu suka bani izini Indai bamu dai daita ba zan hakura, bazan bari ayi miki dole ba. Amman nasan shikenan tawa ta kare.”
Kasa magana tayi, domin bata san mai zata cemai ba.
Yace
“Hafsa nasan yanzu ba Abu bane mai sauki ki yarda dani lokaci d’aya ba, but Ina son kiyi trusting dina bazan taba cutanki ba, so plz ki yadda dani ki amshi soyayya ta da na dawo inga iyayenki”
Tace
“To ka bari zuwa sati biyun mana. Kaga in kazo na baka amsa in na yadda bayan wata biyar sai kazo ai maganar auren mu.”
Murmushi yayi tare da fad’in
“Duk yanda kika ce haka za’ayi,  amman wata biyar yai yawa ko wata daya bana ji xa a yi gaskiya. Bari in barki ki huta sai munyi magana gobe.”
Tace
“To sai da safe.”
Yace
” Allah ya kaimu. “
” Ameen!”
“I love you!”
Ya fada
Murmushi tayi tare da fad’in
“Nagode.”
Yace
“Ni kam ba haka zan so kice ba. ai ba wannan ake amasawa ba in ance i love u.”
“Ni ban san me ake cewa ba.”
Murmushi yayi tare da fad’in
“I love u more zaki ce. Ko i love u ko wani sweet abu dai.”
Shiru tayi tace
“Shikenan Allah kai mu lokacin da zaki ce min i love u ba ma sai na roka ba.”
Tai murmushi yace
“Swt dreams!”
Ta kashe wayar.
Daga ita har shi wani irin nishad’i suke ji, tare da mamakin kansu. Ita tana mamakin yadda ta samu nutsuwa da Ahmad. Shi kuma wai shi ke magana haka. Ikon Allah.
*
**
***
****
*****
******
*******
Halima duk ta rame dan bata cikin nutsuwar ta gaba daya ta fita a haiyacin ta. In ta kira number Isma’il sam bai dauka in tai masa text no reply haka nan taje gidan sa amman baya nan taje kasuwa duk bata samun sa.
Tafe take bayan ta sauka akan napep zata je wajen Isma’il. Tana shan kwanar shagon nasu ya hango ta dan haka da sauri ya mike yace
“In tazo kuce bana nan.”
Yai sauri ya shige cikin shagon. A hankali ta karaso tana haki dan kwana biyu abunda take fama dashi kenan daga tayi tafiya sai haki. Karasawa tayi ta tsaya tana haki. Sai da ta samu nutsuwa sannan ta kalli mai jiran shagon tace
“Sannu!”
Ya ce
“Yauwah!”
Ya mika mata ruwa. Amsa tayi ta sha sannan ta sauke wata ajiyar zuciya. Sai da taji ta nutsu sannan tace
“Isma’il yana nan kuwa?”
Shagon ya kalla yace
“Bai shigo ba.”
Kallon sa tayi da damuwa tace
“Lafiya kuwa yake kwana biyu bai zuwa kuma ko na kira bai dauka?”
“Nima Hajiya in na kira bai dauka kuma ya daina zuwa kasuwa.”
Hawaye ne ya cika idon ta ta juya.
Kabir da ke tsaye tin karasowar ta a nesa ya juya da sauri tazl ta wuce ya bita da kallo har ta fita daga layin ta nufi titi. Kai ya girgiza sannan ya nufi shagon Isma’il. Yana shiga ya zarce office din shi dake cikin shagon zaune ya same shi da waya a kunnen sa. Sai wani lumshe ido yake yana magana kasa kasa.
Kallon sa Isma’il yayi ya mike yace
“I will call u later.”
Sannan ya kashe wayar.
“Zauna mana!”
Ya fada yana nuna masa kujera.
“Ba zama ya kawo ni ba!”
“Haba friend kasan dai ba me raba mu ko? Please ka zauna muyi maganar fahimta.”
Kallon sa Kabir yayi. Isma’il yace
“Please!”
Zama yayi ya ce
“Kafin nan me ya hada ku da Halima me yasa kake gudar mata?”
“Wa? Haliman? Ita ta fada maka?”
Wani kallo Isma’il ya jefa masa yace
“Ban sani ba.”
Murmushi Isma’il yayi yace
“Fada mukai but yanzu ma da ita na gama waya komai ya wuce na dauke mata kafa ne saboda naga zata raina ni. Amman yanzu ya wuce anjima ma zanje. Please friend wannan bae din ka tayani shawo kanta ni nai maka alkawarin zan hada in aure su su biyu da Halima.”
Kallon sa Kabir yayi yace
“Ce maka tayi zata yadda!”
“Wa?”
Ya tambaya
“Halima!”
Ya bashi amsa. Shiru yayi sai kuma can yace
“To menene a ciki dole sai abinda take so zanyi naga ni mijin mace hudu ne.”
Wani murmushi Kabir yayi yace
“Haka ne fa. Yanzu ka samon addreas din yarinya ko  inda take zanyi taking over everything.”
“Da gaske?”
Isma’il ya tambaya. Kai Kabir ya gyada yace
“Really!”
Mikewa yayi ya taho gun sa ya rumgume shi yana fadin
“Amman naji dadi sosai nagode Allah saka da alheri Allah bar min kai. Ban da aboki kamar ka nagode.”
Wani murmushi Kabir yayi yace
“Kar ka damu amman ka kula da Halima shine kawai abinda nake so.”
“Hmm kar ka damu.”
Mikewa Kabir yayi yace
“Zan tafi sai anjima!”
“Tin yanzu?”
Kainya gyada yace
“Zanje wani waje ne.”
“Nazo na rakaka?”
“No nagode!”
Ya fice a office din. Komawa yayi ya zauna yana fadin
“KB kenan har yanzu baka gama sanin waye Isma’il ba Allah sauwake na aure wacce na gama lalata da ita. a ni sabuwa zan dauka fil a leda.”
Yai wani murmushi yace
“Ka dai gama shawo min kan ta komai zai zo daga baya.”
Ya cije baki sai kuma ya saki tsaki yace
“Dole na yiwa yarinyar nan warning kar ta kara nema na haba sai kace wanda naci mata bashi ta ishen da waya nema na gida da kasuwa.”
Ya kuma tsaki ya lumshe ido sai kuma ya saki murmushi yana fadin
“Fine Baby zan more yadda kike yar duma dumar nan. I love u baby with all my heart ban taba xatan zan so mace haka ba sai ke.”
Baki ya lashe sai kuma ya dauki waya ya dailing number ya kai kunnen sa. Bai jima ba aka dauka yace
“Kina ina?”
Shiru yayi aka bashi amsa sai yace
“Room nawa?”
Nan ma ya kara shiru sai yace
“Ok gani nan zuwa ki tanadar min kayan dadi please.”
Mikewa yayi ya dau key din sa ya fice a office din sa. Yana fita ya nufi parking lot din kasuwar ya dau motar sa ya nufi hotel din Shema’u take.
Yana zuwa ya nufi dakin da take bayan ya cike form da tambayoyi. Dakin ya nufa ya fara knocking. Ba a jima ba aka bude masa. Sanye take da bra da pant kadai a jikin ta. Tana ganin shine ta rumgumo sa tana fadin
“Isma’il mayan kasa daman ana ganin ku. But i miss u badly!”
Kwatawa yayi a kafadar ta yana fadin
“Same daer kinsan duk inda xanje na dawo sai na neme ki domin u re special.”
“Na sani inda ban da mamora ai nasan da tini ka yada ni. Kai ma ina kula ka ne kawai dan….”
Ta fada taba shafo kasan wandon sa. Hannun sa ya saka ya danna hannun nata yana lumshe ido hadi da sakin wani irin numfashi.
Maballin rigar sa ta fara cirewa ta gamanta zare masa sannan ta saka hannu ta ta cire masa belt din jikin sa. Yadda take masa abu cikin salon ta na yan bariki yasa har jikin sa daukar rawa yake yana sakin wani irin nishi hadi da kara mannewa a jikin ta.

Kabir na fita a office din Isma’il ya nufi patking lot. Motar sa ya dauka ya nufi gidan su Halima. Yana isa yai parking ya jima zaune a mota yana tunanin ta ina zai fara. Cam dai ya bude motar ya fito. Kalle kalle ya fara ta ina zai samu yaro ya aika sa. Ana haka sai ga Hajara zata shiga gidan. Da sauri ya karasa yace
“Sister Halima!”

Da sauri ta juyo. Tsayawa tayo har ya karaso tana kallon sa da tina a ina ta sanshi amman ta kasa har ya karaso ta dan durkusa tace
“Ina yini?”

“Lafiya lou. Baki sanni ba ni abokin Isma’il ne!”
Murmushi ta saki tace
“Allah sarki. Ya Yake kuwa dan Anty Halima duk ta rasa nutsuwar ta kwana biyu bai zo ba kuma bai kira ba.”

Ajiyar zuciya ya sauke yace
“Abinda ya kawo ni kenan. Nima na rasa gane kan sa. amman ina son ki tayani tambayar ta me yake faruwa a tsakanin su ki tambaye ta ko fada sukai duk yadda kukai ki fada min. Ki bani nunber ki sai na kira naji.”

“Bani da waya sai dai na baka number ta.”
“No!
Ya fada ya zura hannu a aljihu ya zaro wata karamar waya ya mika mata yace
“Ki rike wannan zamuyi magana please k tabbata kin gano mana menene kinji kanwata.”
Amsa tayi yace
“Insha Allahu nagode.”

Ya juya ya koma motar sa ya bar wajen gida ta shiga. A daki ta samu Halima kwance na rawar sanyi da sauri ta karasa wajen ta tana fadin
“Lafiya me yake damun ki.”

“Sanyi nake ji Hajara samon abun rufa please.”
Mikewa tayi ta mika mata abun rufa sannan ta dauko mata paracetamol da ruwa. amsa tayi ta sha sannan ta koma ta kwanta. Bata jiima ba bacci ya dauke ta.

Zama Hajara tayi ta zubawa Yayar tata ido. Ta rame duk bata da nutsuwa. Lallai akwai wani babba tsakanin ta da Isma’il. Yadda Isma’il yake son ta da damuwa da ita amman yanzi ba kira bare yasan a halin da take. Lallai zata taimakawa yar uwar ta ganin komai ya tafi dai dai. Zata bawa Kabir gudunmawa lallai kuma Kabir me son Anty Halima ne tinda har yake son mahance matsalar yayar ta yake son ya cire ta daga damuwa.
“Allah na roke ka ma magance wa Anty Halima abinda ke damun ta.”
Ta fada tana gyara mata rufa.

“Hajara! Hajara!!”
Umma ta kwada mata kira tana daga tsakar gida.
“Na’am!”
Ta fada a hankali dan kada ta tashi Haliman.

A tsakar gida ta tadda ta tana ruden tuwo tace
“Me yake damun Halima ne Hajara?”

“Yanzu dai na shiga tace min sanyi take ji na bata magani tasha ta fara bacci”
“Allah bata lafiya.”

“Amin!”
“Amman fa na lura tana cikin damuwa!”

Shiru Hajara tayi. Umma tace
“Me kike tunanin yake damun ta kwana biyu sam bata da kuzari ga damuwa kwance a fuskar ta.”

Shiru Hajara ta karayi. Ummah tacr
“Na gane rayuwa Hajara a da na biyewa kawa ta kaini ta baro ni a yawon bara na rasa ya’ya na guda biyu daya an kade shi da mota daya kuma an sace shi dana tashi ganin sa ba wasu sassan jikin sa. Hakika nayi wasa da rayuwar ya’ya na ban zauna ba bare na gane damuwar ku. A da komai kuka kwaso ni kuke fadawa amman a yanzu na gane baku sanar dani komai kuma ba komai ya jawo hakan ba sai rashin zama na. In na fita tin safe sai dare.”

STORY CONTINUES BELOW

Ta goge hawaye idon ta. Hajara tace
“Umma kiyi hakuri wannan jarabawa ce daga Allah ki daure ki cinye ta ki tuba abisa abinda kike Allah gafuru rahim ne. Insha Allahu komai zai yi dai dai.”

“Allah yasa. Hakika mahaifin ku duk shi ya jefa mu a halin da muke ciki. Muna ji muna gani Haule ta rasu ga Maman ku sam wata nawa bata gida Antyn ku kuwa in ta fita tin safe sai dare wata rana ma.bata kwana a gida shin wannan wacce irin rayuwa ce. Yaki ya tsaya ya kula da hakkin mu bare na ya’yan sa ba zai ajiye manA abinci yaya yake so muyi eyye?”
“Umma Addu’a zamuyi tayi masa Allah ya ganar dashi.”

Kai Umma ta gyada tace
“Nasan Halima ta fada miki me.yake damun ta ki sanar dani.”

Nan Hajara ta kwashe komai tin haduwar su da Isma’il har zuwa wajen Baba da yayi. Kuka Umma ta fashe dashi tana fadin
“Kiji dan Allah yanxu Haliman ce bata kai shekara goma ba. Wai me mahaifin ku ya mai daku ne ko so yake ya jika ku ya sha ne. Baki ga auren da yai wa yar uwar ku ba ba sanin mu bare mu sanya alheri haka aka tafi da ita bamu san inda take ba. Yanzu inda ya yadda tin farko da ba itama Halima tana dakin ta ba. Kina gani yayar ku Hafsat ita ma tin ana zuwa neman auren nata har maxan sun daina. Sakina ma.har ta hakura bare Farisa. Ita dai fauziyyar ce Allah ya daura ta akan sa shima kuma kiiga ta yadda auren ya yiyu dai.”

Ta zuba tagumi. Tace
“A gaskiya hakuri ba ya kai karshe a yanzu xab iya yin komai duk me manemi a cikin ku wallahi ya fito kawai ni zan nemo masu muki aure.”

“Umma bakya ganin hakan zai zama.gori a gare mu.”
Shiru Umma tayi can kuma tace
“To haka xakuyi ta zama Hajara kun girma kun isa aure amman yaki ko ke shekarar kibfa ashirin ina ga yayen ki kina kanwar Sakkina ta wajen hudu fa ita kuma.kice yanzu shekarar ta nawa. Allah na roke ka ka kawo mana mafita cikin wannan al amarin.”

“Amin!”
Hajara ta fada. Daddawa ta dauko zata daka Hajara ta amsa ta daka daddawa da wake sai dan barkono dan ko attaruhun da za a saka ma babu.  Tare suka gama gurkin suna gamawa suka fito.

Hafsa suka gani tana sharar tsakar gida. Hajara ta karasa tace
“Kawo na karasa.”

“A’ah barshi ina Halima ne?”
“Tana daki bata da lafiya.”
Da sauri ta dago tace
“Me yake damun ta?”

“Zazzabi take.”
“Tasha magani?”

“Eh bacci ma take.”
“Allah bata lafiya. Anjima na shigo na dubata.”

“Anty Hafsa ba zaki dawo daki ba kin zauna anan ke kadai.”
“A’ah kar kuma a bar dakin ba kowa ai. Tinda muna gida daya ai duk muna tare ko?”

“Haka ne. Ya labarin Anty Fauziyya kuwa?”
Murmushi Hafsa tayi tace
“Tana lafiya na sani amman bamuyi waya ba anjima dai na.kira ta ai nasan by now an gama cin amarcin!”

Hajara tayi murmushi tace
“Lallai kam.”
Ta juya tai daki. Da kallo Hafsa ta bita. Hannu ta saka ta goge idon da ya kawo ruwa. Sharar ta kwashe ta nufi daki.

*
**
***
****
*****
******
Da sauri ta juyo. Shema ce daya daga cikin kawayen ta na bariki kallon ta ta tsaya tace
“A sannu ya gida?”

“Baki ganeni bane Fauziyya?”
“Na gane ki mana.”

Kallon Muhammad tayi dake nesa dasu kadan tace
“Wannan handsome din fa amman gaskiya yayi gashi yaro dashi.”

Ran Fauziyya ne ya baci tace
“Ke tinkiya. Miji nane kike kalla kina fadi wannan handsome din wallahi kika kara kallonsa sai na tsokane miki ido nonsense!”

Tana fadar haka ta bar wajen ta tafi gun Muhammad hannun sa kawai ta kama suka tsallaka titi Napep ta tsaya ta fada masa inda zasu suna shiga ta zauna shima ya shiga ya zauna.

“Ya dai?”
Muhammad ya tambaya. Dan murmushi ta saki tace
“Uhmm kawai.”

“Shikenan!”
Ganin su zo wajen masu saida fruit tace
“Please mai napep zan siya fruits.”

Tsayawa yayi ta kalli Muhammad tace
“Ka siya mana.”
Fita yayi ya siyo sannan ya dawo suka dauki hanya suna zuwa gida suka biya suka shiga ciki.

Hijab din ta ta cire ta shige daki ta zauna a gefen gado. Ta zuba tagumi ba abinda ke damun ta kamar yadda ta zubar da ajin ta tai ‘kawance da irin wadan nan karuwan wanda suke kamar mayu akan namiji da sun ga namiji zasu karance shi da komai akan sa.

Tsaki tayi tana cije lebe. Muhammad dake tsaya a kan ta ya zauna ya kama hannun ta wanda sai a lokacin ta lura dashi ta dago da sauri yace
“Lafiya dazu na tambaye ki kince ba komai to menene ki fada min kada ki manta fa ni mijin ki ne.”

Idon ta ne ya kawo hawaye yace
“In har sai kinyi kuka zaki fada min bana so. Na fada miki bana son kukan ki amman ke ban san meyasa ba kike son kina min kuka.”

Hannu tasa ta goge tace
“I love u Muhammad wallahi ina son ka ina kishin ka.”
“Nima ina son ki wanda bansan adadin sa. But me ya kawo wannan.”

“Bana son na rasa ka. Bana taba so na rasa ka dan Allah kada ka barni. Ina son ka.”
“Ba zan barki ba baby ki daina kuka kinji.”
Kai ta gyada tace
“Nagode!”

Hannu ya saka ya goge mata idon ta yace
“Nike da godiya. Menene fadan?”
“Wata ce dazu tace tana son ka.”

Dan murmushi yayi yace
“Shine kike kuka?”
“Au kada nayi?”

“Ai ni bana son kukan naki ne. Amman ki sani ni Muhammad na Fauziyyya ne ita kadai. Mutu ka raba mu. Dan haka ki kwantar da hankalin ki. A duniyar nan ke kadai nakewa kallon mace duk sauran maza nake ganin su. Kece makullin zuciya dan haka ba mai shiga zuciya ta sai da izinin ki. Ki kwantar da hankalim ki kjii.”
Rumguneshi kawai tayi tana sheshekar kukq. Nan ya hau lallashin ta amman sam ta kasa daina kukan wannan yasa ya hade bakin su kadai. Ai kuwa take ta hadiye kukan nata.

Kissing nata yake kamar wanda ya samu alawa hannun sa ya daura akan kirjin tana yana latsawa wanda Fauziyya taji kamar numfashin ta zai fice. Tayi bariki amman abinda take ji daga Muhammad da ban ne.
Kiss kadai yai mata tana rasa nutsuwar ta bare taji hanmun sa a jikin ta. Sauran da tayi tana yi ne kawai ba dan dadi ba ko wani abu. Amman abinda Muhammad yake mata jin sa take har tsakiyar kwakwalwar ta.

Sam batai aune ba sai ji tayi ya zare mata rigar ta. Hannun sa ya daura akan soft jikin ta wannan yasa ta sauke wata nannauyar ajiyar zuciya wacce ta sauke ta a kunnen Muhammad ta kara birkita shi. Wasanni ya dinga aika mata wanda sam ta kasa tabuka komai komai nata ya tsaya saboda yadda abun ke shigar ta.

Jin yana neman zare mata siket yasa ta rike hannun sa. Dauke hannun yayi ya cigaba da abinda yake yi. Ya jima a haka sannan ya kamkame ta yayi minti biyu a haka sannan kuma jikin sa ya saki. A hankali yake sauke numfashin sa.
Dakin shiru yayi sun jima a haka sannan ya mike kiss ya sakar mata a goshin ta da lips din ta da kan kirjin ta. Take tsigar jikin ta ta mike. Ido ta kara runtsewa murmushi ya saki sannan ya fita. Ruwa ya daura ya dawo ya tadda ta ta rufa da hijab din ta idon ta a lunshe. Kayan sa ya fara cirewa yana gamawa yaje ya hada ruwan wanka sannan ya dawo dakin.

A inda ya ganta a haka ya dawo ya same ta. Dan haka dagata yai cak ai kam da sauri ya bude idon ta. Murmushi ya saki yai kissing idon ta yace
“Na tsorata kine?”

Kan ta ta daura a kirjin ta tana kara rike hijab din dake jikin ta.

Hafsa na shiga daki ta dauki wayar da Ahmad ya bata wanda yanzu ita kadai take kunnawa dayar tana nan a kashe. Missed call ta gani ko ba a fada ba tasan ba me kira sai shi.

Murmushi tayi tana girgirza kai sai kuma ta fara neman layin Anty Fauziyya. Ringin daya, biyu aka dauka.
“Assalamu alaikum!”

Fauziyya tayi sallama.
“Wa’alaikun salam. Anty Fauziyya ina yini?”

“Hafsa lafiya kou ya kuke ya gida dasu Umma da Baba da kannena? Na ta kiran wayar ki a kashe dan Allah ki kunna ina neman ki muna gaisawa ina jin yaya kuke kinji?’
“Kai Anty Fauziyya duk missing din mu kike ni gani nake duk wanda ya bar gidan mu ba zai kewar sa ba saboda *wannan rayuwar* da muke ciki a cikin sa.”

“Haba Hafsa duk lalacewa gidan mu gidan mune kuma dole nayi tin kaho da alfahari dashi. Da ace ban da iyaye fa. amman kowa yanzu yasan gidan mu da iyaye na da kanne na. Kuma alhamdulillah ba wanda zai ce ga wani abu da muka aikata ba mai kyau ba ko?”
“Haka ne. To ya kike ya gida da amarci?”

“Alhamduliah. Ina Umma,  Halima,  Hajara da kowa dai?”
“Duk suna lafiya. Halima ce ma bata dan jin dadi.”

“Subhanallah me ya same ta?”
“Zazzabi ne.”

“Ya salam. Dan Allah a kai ta asibiti. Ina fatan dai ba wata matsala a gidan ko?”
“Gida na nan yadda kika san shi.”

“Allah taimaka to.”
“Amim! Ina Yaa Muhammad!”

“Ya fita yanzu amman zai dawo.”
“Agaishe shi to…”

Sallamar sa ta jiyo daga waje ta amsa tana fadin
“kinji dan halak ko?”
Kan ta rufe baki ya shigo yana fadin
“Baby ba oyoyo ko? In koma kenan!”

“No am answering call ne.”
Ta fada tana mikewa. Ta rumgume shi tace
“Sannu da zuwa.”

Yai kissing dinta yace
“Yauwah ya gidan!”

Waya ta kara masa a kunne Hafsa tace
“A gabana kuke soyayya ko?”

Kallon Fauziyya yayi yai mata alamar tambayatace
“Hafsat ce.”

Yai murmushi yace
“Au kada muyi?”

“A’ah Yaya kuyi abarku. Ina yini?”
“Lafiya lou ‘kanwata ya kike ya gida? Kullum sai an kira  ki wayar ki a kashe yau dai kin ga dama.kin kunna ta kira ki ko?”

“Ni na kira ta ai!”
“Ba wani nan ita ce ta damu dake amman ke baki damu da ita ba.”

“Kai Yaya wallahi nima ina ta missing nata ka dauke min Anty na.”
Dariya yayi yace
“Soon kema wani zai daike ki but kan nan sai mun fara daike ki.”

Tai murmusbi yace
“Ya mutanen gidan ina fatan komai dai lafiya.”
“Alhamdulillah.”

“Masha Aah agaida kowa.”
“Zasuji nagode.”
Ya mikawa Fauziyya waya. Amsa tayi tace
“Sister ya xancen guy din nan kuwa.”

“Anty Yaya na ya dawo a kula dashi anjima zan baki labarinsa.”
“To amman ki kunna wayar ki.”

“Ai na canja sim shine ya kawon waya.”
“Da gaske?”
Ta tambaya cike da farin ciki. Sannan tace
“Abu dai na ta tafiya ko? Ina fatan kin fada masa?”

STORY CONTINUES BELOW

“Anty kije gun Yayan na zamuyi magana later kinji.”
“Shijenan zan kira ki.”
Ta kashe wayar.
Tayi wajen Ahmad ta kawo masa ruwa amsa yayi yacr mm e
“Dan kin samu Hafsa shine kika manta dani ko?”

“Am sorry daer tayaya zan manta da kai.”
“Gashi nan kuwa.”

“Kai Habibi ni ban manta da kai ba tayaya zan manta da kaina.”
Gira ya daga mata yace
“Sure?”

Ta gyada masa kai. Ya rungume ta yana fadin
“I love u Baby i really do so.”

“Love u More Habibi.”

*
Tana kashe wayar ta,  ta duba taga missed din Ahmad ido ta zaro dan ya kira wajen sau biyar amman kuma duk bata ji lokacin da kiran ya shigo ba. Zatai dailing kenan sai ga kiran sa nan. Receive ta dannan ta kara a kunnen ta. Sannan tai sallama cikin sanyin murya.

Ido ya lunshe tare da sauke ajiyar zuciya ya amsa sallamar yace
“Ina kika shiga my love! Da wa kuma kike ta waya?”

“Shara nake dazu yanzu kuma da Anty Fauziyya na gama waya sam banji shigowa kiran ka ba kayi hakuri.”
“Ai bakya laifi My princess ya kika ya gidan?”

“Alhamdulillah ya aiki da Madam?”
“Alhamdulillah but bana jin dadi  fa.”

“What’s wrong with you?.”
“Missing nake My love. Wallahi i missed you just two days but i feel like two years. Na fada miki ba zan iya zama har na sati biyu ban ganki ba. Dis weekend ki shirya zaki ganni insha Allahu!”

“Kai Deedat amman yaushe ka tafi gaskiya ni bana son kana bin titi a kai kayi hakuri da yau da sati biyun ai duk daya ne.”
“No dear yau fa two days ne kawai rabo na dake amman ni kadai nasan what am going on,  sannan ace har na da kwana goma sha biyu by then kuma kilan na mutu gaskiya ba zan iya ba. Kiyi hakuri kawai zan zo gaskiya.”

Murmushi tayi tace
“Sai ka bar matar ka ita kadai kuma gaskiya bai dai dai ba.”

“Ita da na zauna da ita har sati fa.”
“Ai she is ur wife.”

“Ke kuma my wife to be ko?”
Murmushi tayi yace
“In kuma da na aure ki nefa shima ba zan bar ta ita kadai ba.”

“No amman ai bata saba ba sabon waje!”
“Menene rashin sabon? Gidan da security ba nai taba ta kuma ita ba matsoraciyya bace. Ga dukkan alamu ke matsoracuyha ce.”

Murmushi kawai tayi yace
“Any way dai ni dai zan zo. Yanzu na tashi aiki zani gida zaki rakani?”

“No!”
“Why?”

“Just!”
“Ni kuma sai kin rakani zan saka waya ta da speaker muna hira har na karasa kinji please!”

“Alright!”
Ya mije ya dau bag din sa ya nufi kofa. Tana jin sa suna sallama da ma’aikatan wajen har ya shiga mota sannan yace
“Are there?”

Tace
“Yes!”

Yai connecting sannan ya tada motar yace
“Ina son ki Hafsa da fatan dai kin gama tunanin ko?”

“No ni ko farawa ma ban ba.”
“Kice dai ba tunanin da zakiyi u just accept my love.”

“Ni bance ba.”
“Xama ki fada ne.”
Ya fada yana murmushi.

Shiru tayi yace
“Ya kikai shiru?”
“To me zance?”

“Na kure ki dai kenan na fadi gaskiya ko?”
Murmushi kawai tayi yace
“Shikenan na baki labarin abubuwan da nake gani a hanya?”

“Yes!”
Nan yace gani a junction kaza da kaza. Haka ya dinga fada mata har ya kusan xuwa ya gida yace
“Na kusa shiga gida!”

“Me zaka kai wa Madam to?”
“Me kuwa zan kai mata zanje ta ganni kawai.”

STORY CONTINUES BELOW

“Haba dai!”
“To me zan siya mata?”

“Duk abinda idon ka ya sauka akai!”
Murmushi yayi ya kalli taga yaga mai dafa masara da gasawa yace
“Ok!”

Karasawa yayi yai parking ya sauke glass yace
“saka min guda bibbiyu nawa nawa?”
Tace
“Four hundred!”

Mika mata five hundred yayi ya yaja motar tace
“Ur change!”
Ya daga mata hannu kawai.

Tace
“Thanks you!”
Yaja motar yace
“Kinsan me na gani?”

Tace
“A’ah!”
Yace
“Maize!”
Bakin ta ta danne tana murmushi tace
“Where is mine?”

“Au zaki ci?”
“Yes!”

“Ok let me go back and get it for u!”
Ya fara saka signal tace
“Tayaya zaka bani to?”

Tsayawa yayi yace
“Oh ashe bama gari daya fa. But ranar da zan zo zan taho miki da ita.”

“Kai Deedat am just joking fa ni dan nasan ba ta yadda zaka ban ne nace where is mine but da wasa nake.”
“Ko? Ni dai sai kinci to.”
Dai dai lokacin da ya iso gidan sa tana ji mai gadi na masa sannu da zuwa. Yai parking ya kashe motar ya dauki waya da jakar sa da leda
Wayar yasa a kunne ya fita a motar yace
“Am back dear!”

“Sannu yanzu kaje Madam ta gasa maka jiki kai sallah sai kaci abinci. Allah ya huce gajiya!”
“No kizo ki min mana.”

Ido ta zaro tace
“Ka rufan asiri man. Bye my regard to Madam!”
Tana fadin haka ta kashe wayar. Dakin ya shiga da sallama yana kallon screen din wayar yana murmushi.
Tana zaune a falon sanye da dogon bakin siket sai vest fara. Kan ta ba dan kwalli. Sallamar ta amsa ta dauke kai tana kallon TV  ledar da ya shigo da ita ya ajiye yace
“Ya gidan?”

“Alhamdulillah!”
Ta fada tana kallon TV. Kai ya girgiza kawai ya nufi lart din sa yana shiga ya ajiye jakar hannun sa sannan ya kwanta yana fadin
“Yaa Allah.”

Sai kuma yai sauri ya mike dan har 6:30 tayi. Bandaki ya shiga ya sakar wa kan sa ruwa bai jima ba ya fito ya shirya ya fita dan zuwa masallaci.

*
Bayan ya shiga ta janyo ledar da ya shigo dashi ta bude. Ganin masara ta saki tsaki sannan ta maida ledar ta ajiye tana bata fuska.

Bai dawo gidan ba sai bayan isha’i. Ya shigo ya tadda ta a yadda ya fita ya barta ya xauna yana kallon ya kalli ledar da ya shigo dashi yace
“Ga masara na gani a hanya nace bari na kawo.miki.”

“Bqna ci.”
Ta fada tana kallo.
“Kinyi sallah ne?”
“Haba Yaa Ahmad ina kallo kana dauken hankali. Banyi ba sai an gama series din nan zanyi.”

“What sallah ce sai an gama series din zakiyi kinyi magarib ma kuwa bare isha’i. Haba Hanna!”
“Ni dai ka kyale ne remain just ten minute ma fa a gama.”

Mikewa yayi ya isa gun swith din ya kashe dagowa tayi tace
“Menene haka?”

Fuska ya hade yace
“Tashi kije kiyi sallah.”

Yadda ya hade rai yasa ta shiga hankalin ta ta mike da sauri tayi daki. Tana shiga ta xauna akan gadon ta tace
“Ana dole ne?”

Sai kuna ta saki tsaki ta mike ta shiga bayi ta dauro alwala ta fito ta tada sallah. Tana idar wa ta mike dan akwai film din da za a fara 8pm bata son ta rasa kallon sa. Dan haka ta fito tana tura baki. Zaune ta same shi yana danna wayar sa. Swith ta kunna ta koma ta zauna.

Yace
“Where is my food?”
“Nima fa shayi na sha!”

“Me kike nufi kenan?”
“Kai ma kasha shi.”

“Haba dai in sha tea da safe in sha da dare bayan kinsan ba wani abinci nake ci a office ba.”
“Ni wallahi gajiya nayi shiyasa. Dakin ka fa da kyar na gyara shi.”

Kallon ta ya tsaya yi yace
“Hanna wai menene haka kike? a gida ma abinda kike yi kenan wai?”

Baki ta turo ta maida kai TV saboda taga an sako film din da zata kalla.
“Magana nake miki!”

“ease Yaya leave alone. Kallo fa nake!”
Kwafa yayi yace
“Zanyi maganin ki”

Ya mike ya fita da sauri. Ta bishi da kallo tana murmushi tace
“Yaya kenan sai na kwatar wa kai na yanci ba zan zauna dan ina kanwar ka ka raina ni ba. Inaaa!”

Yana fita ya nufi wani resturant. Ya jima zaune a mota ya rasa me zai ce a basa in ta shiga can ya mike ya shiga ya isa yace
“Chicken nake so! Takeaway!”

“How many?”
“Biyu but daban daban!”

“Ok Sir!”
Yana tsaye aka kawo masa ta fada masa kudin ya bata sannan ya fita da sauri.  Gida ya koma.
Yana shiga gidan ya ajiye mata leda daya ya shiga dakin sa. Zama yayi ya dauko lemo da ruwa ya fara ci kadan yaci yaji duk ta fita a ransa dan abinci kadai yake son ci. A firij ya saka ya dawo ya hau kan gado ya kwanta.

Wayar sa ya dauka ya fara dailing number Hafsa.
Hafsa na kwance tana tunanin sa taji karar wayar sa. Dauka tayi tana kallom screem din sai ta saki murmushi tana fadin
“Dan halak!”

Wayar ta dauka ta kai kunne sallama yai mata ta amsa tare da fadin
“Ya gajiyar aiki?”

Ido ya lumshe yace
“Alhamdulilla!”

Tace
“Ai ya kamata ka kwanta ka huta kuma kaga da wuri kake fita.”

“Haka ne but i miss ur voice shiyasa na kira naji.”
“Deedat kenan ai gwara kaje kaji ta madam.tin da ka jima kana jin tawa ko?”

“I have heared it ai yanzu taki nake so. Ina son ki bani labari ko kissa ko wani abu har nai bacci.”
“But Deedat ur wife fa? Ai bai kamata ba kaga dare ne yanzu time din tane.”

“I know Hafsat but kallo take. Anjima zata shigo ki ban labarin please har nai bacci.”
“Labarin ko kiissa ko karatun?”

“Karatun!”
“Ok!”
Nan tayi basmallah ta fara karatun cikin muryar ta mai dadi da zaki. Ido ya lumshe tin yana bin ta a cikin zuciya har baccin ya dauke shi da gaske. Sai wajen 11pm ta kai aya sannan tace
“Are there?”

Jin shiru yasa tasan yai bacci dan haka tai murmushi kawai ta kashe wayar ta mike ta dauro alwala tazo ta kwanta.

*(Jan hankali ku daina barin mazajen ku su kadai zaune a daki ke kina can kina wani banzan klo ga inda zaki samu lada amman kin tafi ina kallo daga haka yke neman me.debe masa kewa. Wani in hira zaiyi da ita wani shashanci zaiyi dan haka ki xama abokiyar zaman sa wanda ba zai iya barin ki ba sai ala dole.  Wanda ko kallo zaki zai iya zama yana jiran ki dan haka mu kula mu kula da mazajen mu ba wai dan kada suyi mana kishi ba a’ah dan ko sunyi ya zama muna da wani matsayi ko yana gun ta zai na missing naki dasu abubuwan please ku gyara kuma.mu farka mata)*

9:00am+
“Son kaci abincin in aike ka mana!”
Hajiyar ya kalla yace
“Mom where is Sakina ne? I can’t eat untill i see her!”
Ido ta zaro tace
“Ibrahim!”
Da sauri ya dago dan bata taba kiran sunan sa haka ba.
“Ka fita a ido na in rufe wallahi!”
Kallon ta kawai yake ya kasa magana. Mikewa tayi ta haye sama da sauri idon ta na kawo ruwa.
Tana hawa sama ya mike ya nufi dakin da Sakina ke. A gaban mirrow ya same ta tana gyara fuskar ta. Sanye take da riga da siket na atamfa sun amshe ta batai make up ba amman tayi kyau tayi daurin ta mai kyau. Ta mirrow ta hango shi yana kallon ta. Itama kallon nasa take ta kasa ko da dauke kai ne.
Sun jima a haka sannan ya tako a hankali ya shigo cikin dakin. A jikin kofa  ya tsaya ya rumgume hannun sa a kurji yana kallon ta. Kai tayi kasa dashi ta juyo a hankali tace
“Ina kwana?”
“Lafiya lou Baby mie kin tashi lafiya?”
“Alhamdulillah.”
“Na kasa cin komai saboda ban ganki ba.”
Dagowa tayi da sauri. Yace
“Sure. Muje mu karya ko?”
Ya bude kofar yana nuna mata waje. A hankali ta taka ta fita ya bi bayan ta. Shi ya ja mata kujera ta zauna ya hada mata tea ya zuba mata cheeps sannan ya tura mata gaban ta. Nasa ya hada amman ya kasa taba komai in banda kallon ta da yake. Kasa ci itama tayi da ta dago sai su hada ido yana sakar mata murmushi. Ganin sun kasa cin abincin gaba dayan su yace
“Bismillah mana!”
Kai ta make a kafada tace
“Ka daina kallo na to!”
Murmushi yayi ya dauki mug din tea din ya kurba sannan yace
“Na daina.”
Nata ta dauka ta fara sha tana ci a hankali bata yadda ta dago ba dan tin bata dago ba tana jin idon sa a kan ta. Bayan ta gama ta dago taga ya kure ta da ido. Kai ta gyada masa alamar
“Ya dai?”
Kan sa ya shafa yana murmushi yace
“I love u Sakina.”
Shiru tayi tai kasa da kanta. Yace
“Baki ce komai ba.”
“Khaleel kayi hakuri!”
“Inyi hakuri dame Sakina. Kada kice nayi hakuri da sonki dan sonki ya riga ya gama shiga jiki na ta yadda ba zan iya rayuwa babu shi ba.”
Kwarewa tayi ta fara tari dan yadda ta tsorata. Da sauri ya mike ya dauko mata ruwa ya kawo mata ta. amsa ta sha sannan ta lumshe idon ta sai sannu yake mata ta jima a haka sannan taji ya fada mata dan haka ta mike tayi dakin da take. Da kallo ya bi ta. Mikewa yayi ta tafi sama dan amsar sako wajen Mom din sa.
*
Hajiyar ce zaune a gefen Sakina,  tace
“Yaushe zaki tafi ne?”
Kallon ta Sakina tayi ta dauke kai dan wani tsanar Hajiyar take ji. Tace
“Ni ko yau ma ina son tafiya Hajiyar!”
“Da gaske?”
Kai ta gyada. Hajiyar tace
“Shikenan ki hada kayan ki in kin tafi zan neme ki amman yanzu nayi missing din ki ba zaki dan ragen zafi ba.”
STORY CONTINUES BELOW
Wani kallo Sakina ta sakarwa Hajiyar tace
“Ina bukatar kudi kan na tafi.”
Wayar ta ta dannan ta mika mata tace
“Saka amount din da kike so?”
Amsa Sakina tayi ta saka ta mika mata wayar.
Amsa tayi ta saka pin sannan ta turo mata. Mikewa Sakina tayi ta dauki akwatinta ta bude wardrobe ta fara zuba abubuwan da take bukata. Mikewa Hajiyar tayi ta fitq tana sakin murmushi dan gani take kamar ta gama da wannan matsalar tata.
*
*
*
Zaune suke a falo Hajiyar da Khaleel bayan ya dawo mata da sakon aiken da tai masa. Sakina ce ta fito tana jan akwatinta.
Hajiyar ta mike tace
“Ah ah Sakina tafiyar ce?”
Kai ta gyada tace
“Eh Hajiya. Zan tafi.
Khaleel ne ya mike yace
“Muje na kaiki airport!”
“A mota zan tafi.”
“No jirgi zaki hau muje mu samu jirgi kinji.”
Hajiyar yace
“A’ah ka bari driver ya kaita mana,”
“No Mom bari na sauke ta kawai.”
Babu yanda Hajiyar tayi dan dole ta bar Khaleel suka tafi da Sakina.
Sakina tayi gaba Khaleel na binta a baya. Gidan gaba ya bude mata ta shiga sannan ya zaga ya shiga  mazaunin driver.
Airport suka shiga suna zuwa yaje ya samar mata jirgin da zai tashi a lokacin. Nan akai komai inda aka ce nan da thirty minute jirgin zai tashi.
Tayi zaton tafiya zai yi amman sai ta ga ya samu waje ya zauna yace
“Come over!”
Karasawa tayi ta zauna ya kura mata ido yace
“Saboda ni zaki tafi ko Baby!”
Kai ta girgixa. Yace
“Da gaske wai aure za kiyi?”
Dagowa tayi tace
“Aure kuma?”
Ta girgiza kai tace
“A’ah”
Shiru yayi yana murmushi can a ransa yace
“Wai saboda me Mom bata sona da Sakina menene aibun ta. Tace aure zatai ita kuma ta nunan bata san da wani aure ba.”
“Why silent?”
Kallon ta yayi yace
“Baki da wanda yake neman ki.”
Idon ta ne ya kawo ruwa tace
“Ada naso aure dan na kasance mai tsananin sha’awa. Amman kasan me Baba na sam bai son aurar damu ban san meyasa ba. Tin masu neman auren mu na zuwa yana kora har wanda ba auren mu ba suka fara zuwa. Wannan shi ya jawon lallacewar komai nawa. Har yanzu ina son nayi aure amman ban san tayaya ba sai dai ina addu’ar Allah ya kawo mai sona na gaskiya da zai auren ba tare daya duba tarin laifi na da kura kurai na ba. Amman a yanzu ban da wanda yake so na ko zan aura.”
*
**
***
****
*****
******
*******
Rayuwar da Farisa take abar tausayi ce amman fa game hankali da tsoron Allah. Wanda ita take ganin waye wa ce da jin dadi. Dan ba abinda take nema take rasawa. Duk abinda take so zata samu haka nan duk kasar da take son zuwa zata je ta taka wanda take so ba dan an tsaya mata.
Sam gida ta fitar dashi a tsarin ta ta manta da iyaye ta. Ta tara abin duniya kawai take yi. Wanda ita a tunanin ta in ta tara daga baya zata tuba ta koma ga Allah tayi aure ne.
Kwance take a wani makeken gado a gidan daya daga cikin sanata da take tare dasu. Idon ta a lumshe. Kofa aka bude wani matashin ya daure da towel a kugun sa. Kan gadon ya zauna ya yarfa mata ruwan hannun sa. A hankali ta bude idanun ta masu kashe jikin maza tana kada kwayar idon ta dan turo baki tana turo kirji.
“Baby in na biye miki ba zaki barni naje meeting din nan ba bayan na fada miki akwai alheran da za a samu a shi sosai. Ki kwantar da hankalin ki in abinda ake nema ya samu nayi alkawarin baki 50% amman dan Allah ki xauna kar ki tafi.”
Hannu tasa ta shafi fuska sa tace
“Naki ka futa ka barni a gida nima sai na fita gaskiya na bawa idanu na abincin su.”
“Please Bae!”
“Kasan me? In kaga ban fita ba to tabbas kai ma ba inda xakaje ne.”
“Ni ba fitar ne bana so kiyi ba kar ki fita wani ya kwashen ragowar gara tane!”
Wani kallo ta watsa masa tace
“Yaushe ta zama taka. Kamar yadda kake lasa haka kowa zai iya ya tafi ya bar ta Mai dauwama da ita sai miji na.”
“Baby baki da dama!”
“Naji gaskiya na fada ai.”
Murmushi yayi yace
“In fita dake in na dawo in dauko ki.”
“Yau fa ina son naje club gaskiya.”
“Wai me kike ji a zuwa club!”
“Entertainment!”
“Naji kamar yaushe zan zo na dauke ki.”
“2:00am!”
“Amman gida zan zo ko?”
“No kabiyo ta can kawai.”
“Haba dai kar fa wani ya ganni da girma na zan dai zo gida na dauke ki.”
“Baka da matsala.”
“To taso nai miki wankan.”
Kan tai magana ya dauke ta cak sukai bandaki.
*
*
*
2:00am
Shema ce zaune tana zukar sigari hadi da kwankwadar giwa. Farisa da Momyn sune suka shigo dakin suka tsaya a bakin kofa suna kallon ta.
Farisa sanye da wasu kananun kaya wanda dasu da babu duk daya dan tarnsparent ne.
Farisa ce ta fara shigowa ta zauna tana fadin
“Shema lafiya dai?”
Dagowa tayi idon ta jajir tace
“Dan yar uwar ki ta raina ni ni zata zaga akan ‘da namiji. Namijin da ba dan goyo ba kuma sai dai in ban je gun sa ba nasan dole ya biye min.”
“Wacce yar uwar tawa?”
“Fauziyya mana.”
Momy ce ta shigo dakin da sauri tace
“What Fauziyya kuma ta dawo harka ne!”
Kai Farisa ta girgiza tace
“Ina nasan Yaya Fauziyya bazata taba dawowa ba dan tana da kafiyya bama da tasan akan gaskiya take a baya ma dan ba yadda zatayi ne.”
DafataMomy tayi  wannan yasa Farisa tayi shiru zama Momyn tasu tayi a kusa da Shema sannan ta kalli Shema tace
“Me ya hada ku?”
“Wai dan na ganta nace wannan handsome guy din fa shine wai na kara kallon sa sai ta tsokanan ido. Wai mijin ta ne!”
A zabure Momy ta mike daga zaunen da take tana kallon Farisa da itama ta zaro ido tana kallon Shema a tsorace.
“Tayi aure kenan?”
Momy ta fada. Shiru dakin yayi. Wajen Farisa tayi tace
“Yaushe Fauziyya tayi aure?”
Kai ta hau girgizawa dan ta kasa magana. Bango Momy ta kaiwa duka tace
“Akan me zatai aure bayan ban biya bukatata da ita ba. Sam Fauziyya bata ida tai aure ba in har ban biya bukatata da ita ba dole ta fito ta biyan bukatata. duk cikin yan matan nan ba wacce nake so da sha’awa kamar ita dan haka dole ta biyan bukata ta ko na kwana daya ne.”
Farisa ta kalla tace
“Gobe kije gida ki samar mana information akan ta. Wallahi ba zan taba barin ta ba har sai buri na ya cika.”
Kai Farisa ta gyada ta shige daki tana tunanin yaushe to Fauziyya tayi aure bata samu labari ba. Anya kuwa da gaske ne. Tayaya Baba ya yadda ya aurar da ita. Anya kuwa ba buguwa Shema tayi ba. Dakin ta ta nufa tana shiga ta tadda Antyn ta kwance ita da wani namiji. Juyowa tayi ta buga tsaki tana fadin
“Dan rashin mutunci a dakina kuma to wallahi ku fito min dan bacci zanyi.”
A falo ta zauna ta zuba tagumi can ta saki tsaki tace
“Can ta matse miku.”
Tana zaune Antyn ta Samira ta fito da daurin kirji. Hararar Farisa tayi. Farisa ta saki tsaki tace
“Ina ruwa na to. Dan rashin kunyar ki a daki na.”Kabir ne zaune a dakin sa yayi nisa wajen tunanin Halima. Wayar sa ce ta hau kara wannan yasa ya dago ta da sauri yana dubawa. Isma’il ne tsaki ya saki dan yanzu ba wanda yake jin haushi kamar Isma’il na ganin halin da ya jefa Halima. Duk da bai gama bincikawa ba amman yasan tabbas da wani abu a kasa. Har ta katse bai dauka ba,  wani kiran ne ya kara shigowa da bazai daika ba amman yana tuna wani abu sai yai saurin dannan receive  kan yayi magana Isma’il ya riga shi yin magana
“Hae guy where are you ne?”+
Dakin sa ya kalla sannan yace
“Menene?”
“Yarinyar mana na samo mana inda take yanzu dan Allah kazo ka taimaka min.”
Wani murmushi Kabir yayi yace
“Ok send me the address!”
“Kazo mu tafi dai.”
“No in kana son in taimaka maka ai ba sai ka sani a gaba ba ko?”
Kai ya gyada yace
“Shikenan dan Allah ka tsara min ita sosai.”
“Kar ka damu send me the address!”
“Ok thanks you!”
“Never mind!”
Ya kashe wayar ya mike ya  fara cire kayan jikin sa. Yana gamawa ya shiga bandaki wanka yayi ya fito ya tsane jikin sa sannan ya shafa mai bayan ya gama ya saka wata dakakiyar shadda mai kyau ruwan kwai wacce ta amshi jikin sa. Wanka yayi da ruwan turare sannan ya saka agogo ya dauki sandal ya saka kalar shaddar sa. Bai saka hula ba gashin kan sa dake a kanannede saboda yadda yake da tsantsi yana samun gyara ya kwanta yai luf luf.
Fita yayi ya nufi cikin gidan nasu. Main parlon ya nufa a cikin gidan su.  Da sallama ya shiga katon falon da aka kawata shi da kayan more rayuwa kamar ba mutu ba. Hajiyar sa na zaune a hakince akan kujera taci kwalliya tana kallon sunnaTV. tana ganin sa ta saki murmushi tana fadin
“Wannan wankan fa ina fatan dai gun suruka ta zaka je.”
Kai ya dan shafa yana murmushi yace
“Ina neman addu’ar ki Ummi. Allah ya ban sa’a;”
“Kabir kenan kullum cikin maka adsu’a nake Allah ya baka sa’a ya shige gaba ya baka mace ta gari ya saka gama da duniya lafiya. Dan haka duk inda kake sa’a na biye dakai da izinin Allah. Allah dai ya kiyaye min kai.”
“Amin Ummi nagode!”
“Zan tafi Ummi sai na dawo.”
“Allah ya tsare ya kiyaye hanya ya dawo dakai lafoya.”
Kai yayi kasa dashi sannan ya amsa da
“Amin Ummi nagode!”
Ya mike cikin nutsuwa ya fita. Yana fita ya nufi gun motoci ya zabi wacce zai shiga ya shiga sannan ya zaro wayar sa a aljihu yana duba text din Isma’il yai masa. Karantawa yayi ya ajiye wayar sannan yayi bismillah ya tafa motar ya nufi katon gate din gidan nasu.
Mai gadi na ganin sa ya bude masa gate yana zuwa ya daga masa hannu kawai ya fice a guje. Park din da aka turo masa ya nufi. Parking yayi ya fito ya nufi entrance din. Yana shiga ya nufi inda aka fada masa.
Tin daga nesa ya hange ta sanye da golding yellow doguwar riga wacce aka bi gaban ta da tsakiyar ta da silver stone. Tayi rolling kanta da mayafin rigar sai ta fito tamkar yar saudiyya wato balarabiyya.
Kirjin sa ne ya buga da sauri ya runtsa id kan yayi ta maza ya fara tafiya toward her. Yana karasawa yai sallama cikin muryar sa mai dadi. Dannana waya take ta dago a hankali tana amsa masa sallamar sa.
STORY CONTINUES BELOW
“Zan iya zama?”
Ya fada yana kallon gefe dan ya kasa kallon ta sosai. Dagowa tayi tana kallon sa, ganin abinda yayi sai ya bata dariya ta dan murmusa tace
“In ba zaka damen ba.”
Zama yayi a kujerar dake facing na ya fara danna wayar sa. waitress ne ya zo ya kawo masa lemo ya juya. Dagowa yayi a karo na farko zai kalle ta cikin rashin sa’a itama ta dago dan ta kalle sa. Da sauri ya dauke kai ya mai da kan wayar sa.
Sai da sukai haka sau uku sannan tace
“Hae!”
Dagowa yayi da dara daran idanun sa ya zuba mata ido wanda idanun nasa suka firgita ta tai saurin dauke kan ta.
Kallon ta ya cigaba dayi yana murmushi yana kare mata kallo. Lallai dole abokin sa ya susuce akan ta dan ta hadu iya hadu. Kyakyawa ce mai madaidaiciyar fuska doguwa ga idanu hancin ta a tsaye yake tana da karamin baki kuma pink tana da diri mai kyau.
Cikin minti daya ya gama kallon ta ya dauke kan sa yace
“Kin min magana kuma kin yi shiru!”
Baki ta dan turo na shagawa ta da kalli gefen su inda samari da yan matan su ne zaune suna hira cikin nishadi da walwala. Sai kuma ta kalle shi kamar zatai kuka tace
“Kalli kowa fa sai hira suke da farin ciki van damu kai waya a hannu nima haka!”
Ido ya bude yana kallon ta sai ya saki murmushi yace
“Au kina son muyi hira kamar su ne?”
Kai ta gyada yace
“Amman kika ce bakya son damu!”
“Ai naga kai baka da hayani!”
“How did you know?”
Daga kallon ka da yanayin ka.”
“Sure?”
“Yes!”
Lemo ya bude ya tsiyaya a cup yace
“Ok then ina jin ki!”
Murmushi tayi tace
“What?”
“I want to know somethibg about you!”
Dagowa tayi ta kalle shi sai kuma tace
“Uhmm My Name is Sadiya Muhammad,  i was born and bred up here in Kano, last daugther of the family, my primary and secondary education all in Kano, before I proceed to Sudan where I had my degree and msc i am a medical doctor now. I have seven sibling my Mom has dead since i am 6 month!”
Idon ta ya kawo ruwa ta saka hannu ta dan share tace
“Thur my step mum ta rike ni tamkar uwata a idon duniya da Dad dina but in ni da ita ne ba wanda ta tsana kamar ni duk da ba fada min tayi ba amman yadda take min abubuwa da ban gurguwar shawara ina nuna mata na dauka amman fa bana dauka. Allah ya ban basira da hazaka wanda nake saurin gane abu. Duk da haka ina son kishiyar mama na dan ta rike ni in kaga yadda take min zaka zata bata da kamar ni. Ya’yan ta biyar duk mata ne. Mama na kuma mu biyu ta haifa daga Yaa Abba sai ni. I miss my mom and i really love her duk da ban san ta ba kullum ina mata addu’a.
Kasan me Dad na yana so na sosai ba dan duk ya’yan sa yafi so na, kasan dalili saboda na tashi ba uwa Mama na ta rasu wannan yasa yake tausayi na. Ya gatata ni amman hakan bai sa ya sangartani ba. Ya ban komai a rayuwa ilimi addini da boko dan nayi graduation in my islamiyya with many books. Yanzu me kake zaton ya ragen a rayuwa? “
Kan ya bata amsa ta katse masa tunani tace
“Aure!”
Sai kuma ta bata fuska kamar zatai kuka tace
“Amman kasan me na tsani maza apart from my Dad and Bro!”
Dagowa tayi ta kalle shi fuska da damuwa sai kuma tace
“Kasan dalili na samu many cases akan mazan dake cutar matan su. Asibiti an kawo more than twenty pateint having HIV/AIDs and did you know what basu san suna dashi ba mazajen kuma are under medication.
Abu na daya da ya fara ban haushi kenan tayaya za ai ace kana da mata kasan kana da wannan ciwon ka boye mata dan Allah tayaya uwar ya’yan ka wanda wannan matsalar zai iya sawa ta shafawa ya’yan ka. Kamar ace tana yanke farce garin wannan ta yanke in tazo yankewa ya’yan bata lura ba suma tsautsaye yasa ta yanke su kaga me kenan ta nan kila ta  shafa musu ciwon kenan. At large taje gidan su tai using knife ta yanke ko wani abu wani dan gidan ga dauka yayi using ya yanke daga fa nan tayin spreading ciwon kenan ba tare da ta sani ba. Not that ma ace tana shayar wa haka zatana shayar da Babyn bata san tana da ciwon ba bare a basu kariya ita da babyn ko ta dauki ciki in ba a kula ba har Babyn cikin ta ya shafa saboda not proper Care wanda hakan ya janyo wata matsala haka zaka ga kananun yara da ita wanda suke ban tausayi ya rayuwar su ta gaba zata kaya? Amman ace kai kana nan kana amsar medicatoin suka barsu.”
STORY CONTINUES BELOW
Handkerchief ya mika mata ta amsa ta goge idon ta sannan tace
“Maza na cutar mata a wannan zamanin sosai. Na tashi a cikin jin dadi kuma a harkar zaman takewa ta gidan mu nasan mahaifina is perfect but ba zance bai batawa Mama nah ba but kasan me ina shiga cikin mata da yawa pateint in sun zo muyi hira wasu ma basu san am a doctor ba sai sun zo zan gansu. A gaskiya now a day maza na cutar mata ba kadan ba su suka jawowa da yawan mata kan fada halaka.
Ace mutum yana da hali ba zai dau responsibility gidan sa ba. Yanzu wai eun koma 50-50 da matan nasu kuma in ka lura wasu matan ba abnda suke na neman kudi tayaya hakan ba zai sa su fada a halaka ba ko ta halin yaya ne su samo dan su bawa ya’yan su.”
Handkerchief din hannun ta ta saka ta dan goge idon ta tace
“Ranan haka aka kawon wata mata tana labour abin tausayi baka ganta ba. Da muja duba bata da energy da zata iya haihu saboda tana lacking balance diet shi kan sa Babyn bai da cikakkiyar lafiya. Ga ba jini  a jikin ta abin dai is too much daga karshe aiki mukai mata amman kasan me at long last daga ita har babyn mutuwa sukai dan ba karamin jigata sukai ba. Lokacin da muka ce sai  mijin yazo zamu badasu zakai mamakin irin shigar mutumin kana gani zaka san mai kudi ne amman ita matar ko abinci da kyar in tana samu kai bama abinci ba ko awo bata zuwa in tace ya bata kudi tazo awo ko ba lafiya sai ya ta dirka mata magani yana sata tana abusibg drugs wanda yake da illa ga normal person bare kuma ga pregnant woman.”
“Kana dashi baka bawa iyalan ka ba to w zaka bawa matan banza?”
Tayi tsaki tace
“Allah ya kyauta! Haka nan Wasu mazan ba abinda suka saka a gaba in ba su lalata rayuwar Yan Mata ba. Sunawa Yan Mata wayo da nuna musu abin duniya, su rinjaye su lalata musu rayuwar.”
Ta dago ta kalli Kabir da jikin sa yai sanyi ya zuba Mata Ido tace
“Kaji abinda yasa na tsani maza duk da ba dukka ne suka hadu suka zama daya ba. Amman yawanci haka suke. Mata da yawa suna mamakin ta yadda nake sanin wasu matsalar tasu da yadda nake shiga cikin su dan kwato musu yancin su. To ni ba mutum bace Dan me Ina da halin taimaka musun zanyi shiru in zauna ana zalintar su.”
Ta kalle shi tai murmushi tace
“Ni likita ce Dole nasan wasu daga halaiyar Dan Adam Wanda Allah ya ban wannan ilimin da Naga mutum na kan karantar me ke cikin zuciya Sa.”
Ta dago a hankali ta kalle shi Ido cikin Ido tace
“Kai ma ko na fada maka me ya kawo ka?”
Kai ta girgiza tace
“Kana daya daga cikin maza masu hankali da nutsuwa da kame kai.”
Sai tayi murmushi tayi Kasa da Kai tace
“Kaji abinda yasa na kasa tsaida miji Ina da manema Amman wasun su duk Yan banza ne ba aure suka zo ba in Kuma aure suka zo in na bincika sai na gane suna boye wani Abu a rayuwar su saboda haka auren irin su bai da amfani dan hada zuri’a dasu Kai ma Bata taka ce Dan abinda sukai kila ayiwa Dan ka ni Kuma ba Zan iya jura ba Dan kasan yadda nake ji kuwa a duk lokacin da na samu wani case Akan abubuwan da na fada maka wallahi Ina rasa nustuwa ta in shiga tashin hankali in ya zo kaina ban San ya Zan ji ba. Ban taba cutar da wani ba Dan haka fata a cutar dani ban zuluntar mutum Nima bana so a zulunce ni. Kullum addu’ar iyaye na da tawa ya ban mijin aure nayi aure Amman tsoro nake ji. Ina mamakin matan da iyayen da basa bincika ainahin wanda ya’yan suke mu’amala dasu kamar kawaye da manema abinda yafi ban haushi kuma ace a bawa mutum auren ‘ya ba a gama sanin waye ahi ba ba ayi bincike wannan yaba daga cikin abinda na saka a kunciya ta ta wayar da kan yan mata akan ko da iyaye zasuyi bincike ya kasance suma kan alakar su tayi zurfi suyi bincike cikin dabara tin kan abu yayi gaba.”
Ruwan kan table din ta dauka ta kurba sannan ta kalle shi tace
“Na cika ka da surutu ko? Ana cewa likitoci basu da surutu amman ni kam in na zauna kamar aku haka nake in kana son nai ta magana to ka kawon maganar da zanyi dan taimako ko cigaban wani. Anan zaka san na fiya surutu.”
Sai ta shagwabe fuska tace
“Kai ya sunan ka?”
Kai ya dauke daga kallon ta. Yana murmushi
“Kabir Abubakar!”
Ya dago ya kalleta yaga ta gyada kai tana kallon sa.
“Inayi karatu na a UK inda nayi degree har master but am helping my father’s in his business. Kamar yadda kika fada i hate irin mazan da kike magana akan su,  wanda nake jin tsanar su kuma zan iya komai dan ganin na kwatar musu yancin su. In kinga ina kula mutum sosai tausayin sa nake ji. I like helping people.”
STORY CONTINUES BELOW
Murmushi ta saka tace
“Mun hadu a waje daya kenan taimakon mutane. Yadda na lura kai baka da magana da son hayaniya gashi ka hadu dani talkative ko?”
Dagowa yayi ya kalle ta ya saki murmushi kawai. Tayi kasa da kai tace
“Ka burgeni!”
“Haba?”
Ya fada yana kallon ta. Kai ta gyada tace
“Sosai! I have meet so many gentle men but u re among the special one a meet. I like to meet nice people and have a relationship can i be your friend?”
Ta fada tana kallon sa. Murmushi ya saki yace
“Why not?”
“Thanks You!”
“U re welcome!”
“Baka fada unguwar da kake ba!”
“Ina shagari quaters!”
“Ni kuma can CBN quaters near Ahmad Musa.”
Yai murmushi tace
“Me za a kawo maka?”
Kai ya girgiza yace
“Bana jin yunwa!”
“Allah sai kaci wani abu.”
Waya ta buga nan da nan aka kawo musu snacks da lemo.
Wayar sa ce tayi kara yana dubawa yaga Isma’il ne wani murmushi ya saki sannan ya danna receive ya kai kunnen sa sannan ya ce
“Assalamu alaikum!”
Isma’il bai amsa ba yace
“Ya kaganta ka gane ta ko?”
“Yes menene?”
“Ya ka fara abinda ya kamata?”
“Kar ka damu in na dawo ai zamu hadu!”
“Shikenan dan Allah ka tsara ta sosai aboki.”
“Kar ka damu ka kira Halima kuwa?”
“Nop amman zan kira ta!”
“Alright!”
Ya kashe wayar. Cake ta dauka ta gutsura ta kora da lemo ta kalle shi tace
“Bismillah!”
Zai magana ta bata fuska tace
“Ba kyau mai da hannun kyauta baya dan Allah!”
Cake daya ya dauka ya dan gutsura sannan ya ajiye. Daga haka hira ta barke sosai tsakanin Sadiya da Kabir har wajen karfe shida. Ganin magariba ta gabato ta mike tana kallon sa tace
“A gaskiya naji dadin haduwa da kai Kabir nagode sosai da ban lokacin ka da kayi da tsayawa kayi ka saurare ni duk da baka sanni ba.”
“Kada ki damu!”
Ya fada yana mikewa shima yace
“Magariba ta gabato ko ya jamata ki tfi gida!”
“Haka ne. Nagode sai anjima!”
Ta fada tana daga masa hannu har tayi gaba sai ta juyo. Tsaye ta ganshi ya zuba mata ido. Ta karaso wajen sa tace
“Na manta ban amshi number ka ba.”
Ta fada tana mika masa wayar ta. Amsa yayi ya saka mata sannan ta amsa taui saving ta fara dailing number kara ta dauka ya zaro a aljihu tace
“Save it is my number!”
“Ok thanks you bye!”
Ya fada. Hannu ta daga masa ta juya ta tafi. Ya jima a gun sannan ya kalli wayar sa dake vibrating ya saki tsaki ya kashe wayar gaba daya sannan ya nufi wajen motarsa.
Yasan halin Isma’il ba zai bar shi ba dan haka gari ya kara shiga kawai.
*
**
***
****
*****
******
*******
6:00pm
Halima ta farka sakamakon aman da taji yana damun ta. Da sauri ta mike amman kan ta fita a dakin ta fara kelaya aman anan. A wajen ta durkusa tana aman. Hajara dake tsakar gida tajiyo kakarin ta ta mike da sauri tayo dakin. Dafata tayi ta gama aman sannan ta mike ta dauko bucket ta kawo ta dauraye bakin ta,  ta gyara wajen sannan ta fesa fresher a dakin.
Kayan ta fitar ta dawo ta zauna a gefen Halima dake kwance ta dafata taji jikin ta zafi zau. Kallon ta tayi tace
“Sannu Yaya!”
“Yauwah!”
Halima ta fada tana gyara kwanciyya. Hajara tace
“Yaya kunyi waya da Isma’il din kuwa?”
Idon Halima ne ya kawo ruwa tace
“Yaki yai picking Hajara. Yau na kara zuwa kasuwa amman bai nan. Na rasa yaya zanyi Hajara bansan me nayiwa Isma’il ba ya daina picking call dina ba. Rasa Isma’il wallahi tamkar rasa rayuwa tane. Ina son Isma’il dan Allah Hajara ki taimaka ki nemon Isma’il in wani laifin nai masa yayi hakuri ba zan sake ba amman kada ya kara hukuntani ta yin nesa dani ba zan jure ba kwata kwata.”
Ta karasa maganar tana fashewa da kuka. Tana fadin
“Yaya zan yi yau in Isma’il ya juyan baya? Yaya zanyi Hajara mutuwa kawai zanyi Hajara domin Isma’il shine farin ciki na.”
Dafata Hajara tayi tana fadin
“Haba Yaya ki daina kuka Isma’il ba zai barki ba kada ki manta yadda yake son ki dan haka ba zai barki ba ki daina kuka. Ni na miki alkawarin nemo sa na tambaye sa laifin da kikai masa dan haka ki daina kuka Yaya ba abinda kikai masa kinji?”
“Nagode Hajara!”
Ta fada tana kama hannun ta. Shiru dakin yayi kan ta dago har Halima ta koma bacci. Hannun ta ta zame a hankali tana kallon Haliman yadda ta kara kyau da cika da ita sai kace ba mai ciwo ba sai dai kana kallon ta zaka san tana cikin damuwa.
Hawayen da ya kawo idon ta tasa hannu ta goge tana fadin
“Duk Baba ya janyo koma menene ai da yanzu kunyi auren ku. In kuma wata ya samu zai aura fa. Yaa Allah ka yayewa Yaya damuwar ta ka dawo mata da Isma’il din ta.

Zaune take bayan ta idar da sallah magariba ta jinginar da kan ta da gado idon ta a lumshe. In banda ciwo ba abinda kan ta yake yi.

Hajara ce ta shigo dakin rike da kwano ta ajiye a gaban Halima. Halima na shakar kamshin miyar ta mike da sauri tayi waje. A bakin rariya ta dinga kwalaya amai kamar zata amayar da ya’yan cikin ta. Sai da ta gama Hajara dake bayan ta ta taimaka mata ta dauraye bakin ta ta gyara wajen.
Tsayawa tayi rike da kai tana fadin
” Kije ki fitar da tuwon can bana son warin sa.”

Daki Hajara ta shiga ta fitar da tuwon sannan ta fesa freshner ta dawo tace
“Na fitar.”

Hijab ta saka ta toshe hancin ta ta wuce ta falo inda kannen ta ke cin tuwon ta nufi dakin su. Tana shiga ta fada saman gadon tana fadin
“Wash!”

Ta dafe kanta.
“Sannu Yaya!”
Hajara ta fada. Kai ta gyada mata. Hajara tace
“Me zakici to?”

“Hajara gurasar mai balango nake so ki siyon.”
“Toh!”

“Duba jaka ta da ragowar dubu daya ki siyo min da lemon fata.”
Mikewa Hajara tayi ta dauki kudin sannan ta dawo tace
“Yaya ko zamu asibiti dai?”

Kai ta girgiza tace
“Anjima nasha paracetamol sai daina ciwo.”
“Sannu Allah sauwake!”

Ta fada ta mike ta fita. Tana fita soro wayar da Kabir ya bata ta dau kara zaro ta tayi ta daha ta kai kunnen ta.
“Assalamu Alaikum!”
“Wa’alaikum salam ina yini?”

“Lafiya lou! Ya Haliman?”
“Wallahi bata da lafiya!”

“Me yake damun ta?”
Ya fada da sauri.
“Nima dai ban sani ba amman tana yawan cewa ciwon kai yanzu kuma tayi amai dazu ma haka.”

“Ya salam kunje asibiti!”
“A’ah tace in tasha paracetamol ma zai sauka!”

“Alright gani nan ina gefen unguwar ku zan karaso me zata ci?”
Shiru Hajara tayi. Yace
“Kar ki damu ki fadan me zataci!”

“Gurasa tace na siyo mata!”
“Wacce irin gurasa?”

“Ta masu nama.”
“Alright gani nan ki tsaya a waje.”

“Toh!”
Batai minti ashirin ba sai gashi nan. Parking motar yayi ya fito da manyan ledoji guda uku sai karama guda daya. Yana karaso ya mika mata. Amsa tayi tace
“Angode!”

Yai murmushi yace
“Ba komai! Kunyi magana kuwa?”

“Eh to dazu dai na mata magana take fadin taje kasuwa bata same sa ba in ta kira bata samun sa. Ita bata san me tai masa ba in wani laifi tai masa ya fada mata ta bashi hakuri. Gaskiya Yaya na son Isma’il dan Allah ka taimaka ka tambayrme shi mai tayi masa dan ta bashi hakurivdan tana ikirarin in ta rasa sa zata iya rasa ranta ni kuma ba zan juri rasa yar uwa ta ba dan Allah ka taimaka mana.”

Ta fada idon ta na kawo kwalla. Ajiyar zuciya ya sauke yace
“Kada kiyi kuka insha Allahu zanyi iya yina kinji.”

“Kai ta gyada. Yace
“Ki mata sannu zamuyi waya gobe Allah sauwake!”

STORY CONTINUES BELOW

“Amin mun gode!”
Ya juya ya shiga mota. Sai ya fito ya kalle ta yace
“Inda da matsala ko tana bukatar wani abu ki kirani ki sanar min. Allah sauwake.”

“To angode!”
Ta fada ya koma cikin mota ya tayar ya tafi. Rabon sa da gida tin yamma kuma a time din ma ba gida yayi ba dan yasan kila Isma’il na can yana ta jiran sa shi kuma bai shurya ganin sa ayanzu ba
Hajara Gida ta shiga a daki ta tada Halima dake bacci tace
“Tashi kici.”

Mikewa tayi ta sauko. Hajara ta bude ledar da taji dumi ta bude nadu biyu ne daya kazace gasashiya dayar kuma gurasa ce da nama. Dayar ledar kuma kayan tea ne a ciki dayar kuma karama paracetamol ne a ciki. Kallon ta Halima tayi tace
“A ina kika samo wannan kayan?”

“Kabir ne abokin Isma’il ya siyo miki.”
Da saurita dago tace
“Shi da Isma’il ne suka zo?”
“A’ah shi kadai ne yazo.”
Gurasar da nama Halima taci ta sha lemon fata sannan ta koma ta kwanta bayan tacewa Hajara ta diba ta ragemata gurasar ragiwar ta kawai Umma. Yadda tace haka tayi.

*
Karfe sha biyu ya nufi gidan su a gajiye dan bai taba yin dare irin haka ba yana nufar parking space yaga motar Isma’il tsaki ya saki yace
“Maye kawai!”

Sannan ya fito a hankali ya nufi bangaren Hajiyar sa duk da yasan tayi bacci. Ai kam bangaren duk an kashe kayan wuta dan haka ya juya ya nufi part din sa.

Kwance ya same shi akan kujera yana gyangyadi. Kai ya dauke ya nufi bedroom dinsa. Yana shiga ya soma cire kaya ya shige  bandaki. Wanka yayi ya fito ya saka kayan bacci ya nufi parlour’n sa. A yadda ya barshi a haka same shi. Robar ruwan dake kan center table ya bude ya dan diba a hannu ya yayyafa masa. Da sauri ya bude ido yana ganin Kabir ya sauke ajiyar zuciya yana fadin
“Yaushe ka dawo?”

“Na jima  ya akayi ne?”
Fuska Isma’il ya bata yace
“Kai nake jira ina ta kiran wayar ka a akashe ina ka shiga ne?”

“Bashin ka naci ne?”
“A’ah! Amman ai kasan batun dai ko?”

“Batun me?”
“Yarinyar nan mana!”
Tsaki yayi yace
“Tab akan wannan ka zauna jira na ai kwara ma ka tashi kaje ka kwanta dan gaskiya na gaji bacci kuma.nake ji kaima kasan by now na jima da bacci ko?”

“Nayi mamakin da ka kai 11 awaje!”
“Kamawa tayi ai!”

“To please ya kukai!”
“Kasan Allah sai gobe kawai ka barni inje in kwanta kai ma ka kwanta ka huta!”

“Wai me kake nufi?”
“Abinda kaji.”
Ya fada ya juya yace
“Ka taso ka watsa ruwa kazo mu kwanta.”

Yana fadar haka ya shige daki. Ran Isma’il in yai dubu ya baci dan haka ya mike ya fice a dakin kawai. Kabir na addu’ar bacci yaji tashin motar sa kan ya leka ma har ya fice. wayar sa ya kunna ya fara kiran sa amman yaki ya dauka dan haka shima ya ajiye ya koma ya kwanta kawai.
*
2:00am
Zazzabi mai zafi ya tada Halima dake bacci har shaking jikin ta yake yi. Ga kan ta dake ciwo cikin ta na hautsinawa. Hajara ce ta farka jin tana kakarin amai nan ta mike taga a halin da take. Nan ta dinga kwara amai dan ta kasa tashi gaba daya.

Daga ta Hajara tayi taji jikin taya dau zafi daga ta tayi ta gyara mata jiki sannan ta gyara wajen. Waje tayi tana kwadawa Umma kira.

Hafsa dake zaune akan sallaya ta fito da sauri tana fadin
“Lafiya Hajara?”

“Anty Hafsat Yaya Halima ce ba lafiya.”
Da gudu Hafsat tayi dakin nasu. Hajara tayi dakin baban su tana knocking Umma ce ta fito tana fadin
“Waye?”

Ganin Hajara ce yasa Umma ta tsorata tace
“Lafiya?”

“Ummah Yaya Halima ce ba Lafiya!”
Da gudu itama tayi dakin. Nan suka hadu da Hafsat suna mata sannu. Umma ta koma dakin mai gidan da yake ta baccin sa tace
“Alhaji! Alhaji!!”

STORY CONTINUES BELOW

Da kyar ya bude ido yana fadin
“Menene haka?”

“Alhaji Halima ce ba lafiya bakaji jikin ta fa har suma takeyi wallahi.”
Tsaki ya saki yace
“To shine zaki tashen ba sai ki daukar mata magani ba a kwandon magunguna.”

“Aibansa wanda zan bata ba.”
“Jeki daukon kwandon!”

Ta mike da sauri ta kawo masa. Nan ya ba ballar mata wajen kala biyar wanda wasu sunyi expire ma ya bata ta amsa ta fita a guje. Tana zuwa ta dauki ruwa ta bata tasha sannan tana sha ta rike ciki tana juyi. Kan kace me jini ya ballewa Halima nan hankalin kowa ya tashi.

Umma ta koma gun Mai gidan amman ta tadda ya rufe kofar sa da ta buga ma yace
“Kada ta sake buga masa kofa.”

Haka ta juyo ta dawo jini ya zuba a jikin Halima sai kuma ta sume. Rasa yadda zasu yi sukai fita sukai. Hajara da Hafsa ko zasu samo mai adaidaita amman ba kowa a titin dan dare yayi sosai. Rasa yadda zasu sukai.
Dan haka Hajara ta dauki waya ta fara kiran layin Kabir. Yana dauka tace
“Dan Allah ka taimaka mana kada mu rasa ta zata mutu.”

“Wace zata mutu?”
Ya tambaya a firgice.
“Yaya Halima!”

“Innalillahi wainna illahir rajiun.”
Ya fada yana mikewa akan sallayar da yake. Mota ya dauka ya fito a gidan su gidan su Halima ya isa yana zuwa ya kira Hajara ta fito yace
“Ku dauko ta mu tafi asibiti!”

Nan Hajara da Hafsa suka fito da ita suka ce Umma ta zauna bari suje. Haka suka tafi suka bar Umma tsaya ta kasa komawa da kyar ta koma ta daura alwala ta koma kan sallaya tana sallah da addu’a Allah bawa Halima lafiya……….

*
**
***
****
*****
******
*******
Dagowa Sakina tayi tace
“Aure kuma?”
Ta girgiza kai tace
“A’ah”

Shiru yayi yana murmushi can a ransa yace
“Wai saboda me Mom bata sona da Sakina menene aibun ta. Tace aure zatai ita kuma ta nunan bata san da da wani aure ba.”

“Why silent?”
Kallon ta yayi yace
“Baki da wanda yake neman ki.”

Idon ta ne ya kawo ruwa tace
“Ada naso aure dan na kasance mai tsananin sha’awa. Amman kasan me Baba na sam bai son aurar damu ban san meyasa ba. Tin masu neman auren mu na zuwa yana kora har wanda ba auren mu ba suka fara zuwa. Wannan shi ya jawon lallacewar komai nawa. Har yanzu ina son nayi aure amman ban san tayaya ba sai dai ina addu’ar Allah ya kawo mai sona na gaskiya da zai auren ba tare daya duba tarin laifi na da kura kurai na ba. Amman a yanzu ban da wanda yake so na ko zan aura.”

Wani irin ajiyan zuciya Khaleel ya sauke, tare da kallonta cikin ido  yace
“Alhamdulillah!”

Sai kuma ya kama hannun ta yace
“zaki aureni?”
Da sauri ta dago suka hada ido kurawa juna ido sukai kowa ya kasa dauke idon sa daga kallon dan uwan sa. Shi yana jin son ta da kaunar ta na kara shigar sa. Ita kuma in banda bugawa ba abinda zuciyar ta take.
Ina ita ina Khaleel. Khaleel yafi karfin ta dan masu kudi ne gashi mai ilimi dan gaye ya hada komai da komai. Hakika in har da zata iya itama tasan tana son sa dan Khaleel daban yake ya iya kula daga jiya zuwa yau yadda yake mata kadai ya tsaya mata a rai.

Khaleel ne ya Katse ma sakina tunani da fad’in
“Baby why silent and stare at me like this? Ko ban miki bane?”

Kai ta girgiza tace
“Ina mamakin ne Khaleel tayaya kamar ka zaka ce kana so na. Kasan ni wacece kuwa? Bama wannan ba,  kafi karfi na.”

“Karkice haka Sakina. Banfi karfin ki ba kefa macece sai dai in kawai bakya so nane kike son ki fake ta haka.”
Yace
“Tun ranan dana ganki Allah yasa min sonki, Wlh Sakina so nake na aureki in har kin amince Kece mace ta farko dana Fara ji ina burin in aura.”

Shiru tayi ya daga hannun ta yace
“Kinyi shiru!”

“Zanyi tunani Khaleel!”
“Shikenan”

Jin an fara kiran masu tashi yasa ya mike yace
“When zaki dawo?”

Ido ta dan zaro tace
“Gaskiya da kyar!”
Yace
“Kenan dai ni ne zan zo ko?”

Murmushi tayi. Ya amshi wayar ta ya dau number ya saka mata tasa sannan ya mika mata waya yace
“Put me ur address!”

Amsa tayi tai typing sannan ta mika masa. Karba yayi ya karanta yace
“Thanks you!”

Mota ya koma ya dauko wata karamar leda ya mika mata sannan yace
“Ba yawa!”

Kai ta make tace
“A’ah nagode!”

Fuska ya bata yace
“Please dear!”
Amsa tayi tana fadin
“Nagode!”

Sannan ta fara tafiya. Har ta shiga jirgi yana tsaye yana kallon ta sannan ya juya.

Koda Sakina ta shiga jirgi tunanin Khaleel tai tayi wanda ta rasa dalili. Can kuma sai tunanin abinda suke aikatawa Hajiyar Mahaifiyar Khaleel. Yau kuma aka wayi gari dan ta yana son ta. Hakika itama tana son Khaleel amman kuma tana tsoro kuma tayaya zata ce bata son sa dole sai ya so jin dalili. Ido ta lumshe tare da fadin
“Anya wannan abun zaiyi kuwa? Maganan Khaleel bai kamata in daukeshi da muhimmanci ba, domin ba Abu bane mai yiyuwa naga tsiraicin Mom dinshi na… Yanzu kuma sai kawai inzo in auri d’anta Kai no way. “

Ta fada tana Bude ido can kuma tace
“But nima ina son sa ya zanyi da soyayyar sa da ban san lokacin da ta shigen ba.”

“Dole kiyi hakuri Sakina!”
Zuciyar ta ta fada mata. Kai ta gyada tace
“Tabbas dole na hakura da kai Khaleel ba dan bana son ka ba.”

Ledan daya bata ta bude tana kallon abin ciki. Wani card ne mai kyau sai bandir din kudi yan 1k guda biyu da turaruka. Bata san lokacin da ta saki mumushi ba ta sumbaci ledar ta rumgume a jikin ta.

Tana sauka ta samu taxi ta dauke ta da kayan ta ta nufi gida. Tin da ta nufi gida taji kirjin ta na bugawa. Addu’a ta fara har suka isa kofar gida.

Ta biya mai mota ta kwashe kayan ta ta fito ta tsaya tana kallon gidan nasu idon ta na kawo ruwa. A hankali ta shiga cikin soron tana sallama. Kannen ta da suka fito zasu fita suka ganta nan suka hau ihu suna fadin
“Oyoyo Anty Sakina Oyoyo Anty Sakina.”

Nan suka kwashe kayan ta sukai ciki dasu. A hankali ta karasa cikin gidan har ta shiga dakin su.

Akan sallaya ta samu Umma zaune ya zuba tagumi ta zauna tace
“Umma ina yini?”

Dagowa tayo ta kalle ta da idon ta da sukai jajir tac
“Lafiya lou .”

“Lafiya Umma?”
Hawaye ne ya zubo a fuskar Umma nan hankalin Sakina ya tashi ta matso tana fadin
“Umma kiyi hakuri ki daina kuka ki fada min me yake damun ki?”

“Halima ce ba lafiya tin jiya da dare suka tafi asibiti basan a halin da take ciki ba.”
“Ita da wa suka tafi?”

“Ita da Hafsa da Hajara!”
“Ba number wayar su?”

“Duk sun bar wayar a gida.”
Tagumi Sakina ta saki tace
“To Allah yasa lafiya.”

“Amin dai. Daga ina kike?”
Gaban Sakina ne ya fadi dan tinda take yawace yawance ta Umma bata taba tambayar ta daga ina take ba.

*Wai me yake damun Halima ne?*
*Ya kuke ganin alakar Sakina da Khaleel?*

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *