WATA BAKWAI CHAPTER 13

WATA BAKWAI CHAPTER 13

  Mintsininta yai a cinya bata zata ba. Tako saki wani qaramin ihu. Dan taji zafin mintsinin. Da sauri ya rufe mata baki yana zaro ido. “Shh hussy bamu kadai bane a motar fa akwai driver” Yake fadi cikin sanyin murya. Duk da akwai iyaka tsakaninsu. Ta rausayar dakai gefe tace “amman kasan da zafi aiko?” Kallonta yai ta qasan idanuwansa “umm qaramin wanda kikamin ne” ya fadi yana daga mata gira. Dariya tai sosai. Ta rasa yanda akai yake yawan sakata dariya. Tasan ammar kan sakata dariya amman ba kaman wannan ba. Yanayin yanda yake canza fuskarsa zuwa yanayin abinda yake so ne yake burgeta. Yana sa ta manta da damuwar da takanji a yanzun. Kewar ammar tana nan daram. Sai dai shi din ya cika wani gurbi da bata son da zamansa ba ma. Kallonta yake yanda tai zurfi cikin tunani. Zaiso sanin me yake yawo cikin kanta saidai shiba mutum bane mai yawan bincike. Muddin abinka bai shafe shiba yakan baka wajen da kake buqata kai taka rayuwar. Hannu yasa ya tallabo habarta ta sauke idanuwanta cikin nasa. Tsoro,shakku da fargaba da wani yanayi da baison meye ba cike da idanuwanta. Sauke su tai a hankali daga nasa idon zuwa fuskarsa. Gara ta kalli komai a yanzun da cikin qwayar idanuwansa da take fisgarta zuwa wata duniya mai zurfi. Hada goshinsa yai da nata. Tana jin hucin numfashinsa kan fuskarta. Ta rufe idanuwanta. Bata son yanayi ko daya da take ji a jikinta. In batai wasa ba prince ishaq zaisa ta manta kanta bama ammar kawai ba. Lokaci daya taji zuciyarta ta fisgeta zuwa wani lokaci. ‘ *** *** “tawan wlh kewarki ta dameni na ma kasa zama lectures” Na samu na gudo gida fa. Murmushi tai “haba nawan abinda zaka dawo ka sameni saika gudo. Bana son kana saka wasa kaga dai shekarar qarshe kake.” Dariyarsa yai mata cikin muryarsa mai sanyi yace “haba kin fiyemin lectures din yau. Inban ganki ba ba fahimtar komai zan ba” Hmm ammar…….! *** *** Bata son ta furta ammar’ a fili ba sai wani irin dilla taji mai zafi kan lebenta daya dawo da ita hayyacinta. STORY CONTINUES BELOW Owww ta fadi tana ture shi. Lebenta ta taba da dan yatsa ta dawo dashi zuwa dubanta dan zatonta yai jini. Tana shirin yin kuka ta kalli prince ishaq da saida ta tsorata da yanayin fuskarsa. * Wani abu yaji ya tokare masa wuya mai daci dashi bai fito ba shi bai koma inda yake ba. Qirjinsa yai wani zafi. Yana tare da hussy har tunaninta zai kaita kan ‘ammar. Hannuwan shi yasa ya janyo gab dashi sosai. Goshinsa ya hade da nata yana kallonta. Numfashi yake maidawa a hankali yana son controlling abinda yake ji. Da aurensa akanta takejin tana da iko ko damar da zatai tunanin wani. WATA BAKWAI 7!!! Kacal yake dasu ta so shi. “I am sorry” ta furta tun kamun abinda take gani a fuskarshi ya fito fili. Muryarta ta katse mashi tunanin da yake. Hannunta ya kamo ya dora saman qirjinsa.Ya hada da nasa ya danna. Tanajin yanda zuciyarsa ke dokawa. A dake yace “kinsa tana bugawa a bangaren da nai zaton ya jima da daina aiki. Zaki iya taimakawa yanayin raunin da ke jikinta. Ki danne son ‘ammar’……” Yanda ya fadi son ammar saida jikinta ya amsa. Yaci gaba “sorry na dillar maki lips ko? Ya qarasa yana yatsina fuska.Ta gyada kai alamar eh dan har lokacin wajen yana mata zafi kuma ta tabbata sai jini ya kwanta. Ta sake saka dan yatsa ta taba. Duk yana kallonta. “Good” ya furta ya dora da “inkinzo fadin sunanshi a gabana ki dinga tunawa dan zan maki wanda ya fishi a gaba” Goshinta ta cire daga nashi. Wato wanda yafi wannan ma. Naushin masa kafada tai da qarfi tako ji kaman ta naushi dutse saboda taurin muscles din dake tattare wajen. Ta lanqwashe yatsu. Wayyoo owwhh take fada tana yarfe hannu. Yai dariya dai dai lokacin da motar ta tsaya alamar sun qara so gida. Bude masu qofa akai suka fito. Husna riqe da hannunta tana murza yatsunta har suka qarasa can cikin gidan. Ya wani basar kamar bashi ya gama dariya cikin mota ba. * Cikin gida suka shiga. “Gentle” Ta fadi. Ya juyo yess! Saita rasa me ma zata ce masa saboda yanda ya kafa mata idanuwan shi din nan. Ta kasa sabawa da kalar kallon da yake mata. Kodan koyaushe daban take ganinsa. Intaso ta gane yanayin kallon anjima bada irinsa zai dubeta ba. “Ina jinki hussy” ya fadi a qagauce da son jin me zatace. A daburce tace masa “ina son inje saloon ne daman a wankemin kaina and…….” Daga mata gira yai data soma sabawa dan yana yawa yin hakan duk da ma.anarsa yawa gareta a wajensa. Duk ta daburce kaman mai koyon magana. Daqyar ta hadiye miyau ta ci gaba da fadin “Ina son inje wajen kausar in babu damuwa” Sauke ajiyar zuciya yai. “Ki kira kausar ta turo address dinta a kaiki.Masu tsaro zasu rakaki. Su jira ki gama ko yaushe ne su dawo dake gida” “Saloon dinfa?” Ta tambaya tana shagwabe mishi fuska.Ya girgiza kai “Ki haqura ba yauba. Saboda dalilai da yawa” “Amman…….” Ta soma yanda ya zuba mata idanuwa yasata yin shiru. Ta rasa me yasa yake bala.in mata kwarjini haka.. “Good Banson gardama…” Bata sake cewa komai ba harya wuce sashinsa. * Itama nata bangaren ta wuce. Kan gado ta kwanta. Yanayin komai da suke ita da prince ishaq na dawo mata. Wani abu na mata yawo cikin zuciya. Ga ammar ta kasa daina jin kome take ji a kansa. Abinda yake bata mamaki yanayi kala daban takeji akan su shida prince ishaq. Shin wanne ne so a ciki? Ko dai qauna, so da kuma shaquwa abubuwane daban bata sani ba wai. Tabbas basukai tsayin lokacin da a tunaninta zasu shaqu da prince ishaq ba. Qaunarsa fa? Tsana na juyewa zuwa qauna ne. Son shi fa? Um to zuciyarta na mata wasi wasi saboda indai yanda takejin ammar a zuciyarta shine so to wani abune daban kan prince ishaq. Abu can cikin zuciyarta manne da qamshin sa kawai intaji yakan tuna mata abu da yawa. Sai ta tuna wani lokaci can baya. Tana kwance kamar lokaci irin wannan a dakinta. Ammar ya kira wayarta suna hira yace “tawan kamar yan gidanku basa na.am da soyayyarmu. Ina tsoro har raina” Duk da itama ta soma tsoron hakan kuma tasan dalilinsu yafi nata qarfi bai hanata son ammar dinba. Cikin taushin murya tace “ba haka bane nawan kaima kasan dalilinsu kuma in shaa Allah zamu samo maganin matsalar kafin abin yai nisa ko?” “Hakane tawan ina tsoro ne kawai. Jiya nai mafarki ana daura aurenki amman da wani bani ba” Dariya tai mishi “nawan mafarkine fa Ba komai ba. Ka manta kawai. Me kake yanzun?” “Um waqa nake ji da wayana na kiraki kuma.” Ya amsata. “Wanne waqa?” “Cikin zuciya tana quna da so tai bankwana rabamu da juna soyayya a rai ya bugan naji zafi” ya soma raira mata waqar fitaccen mawaqin nan hussaini danko. Indai waqane kam muryar ammar daban take. Tason waqar jin yai shiru yasa tace “uhm nawan da dadi ka ci gaba” “Hmm” ya fadi ya dora da “waqar ta tunamin da yanayin da muke cikine shisa” Jin ya fadi hakan yasa ta dora dan shiya koya mata jin waqoqin danko “na yarda dakai kadai daya ke saka mini shauqi. Zancen da kake yasa na sarqe ka har a mafarki. Rabani dakai yakan sa na kashe kaina in rufe daki. Zamanmu dakai a zuci nakai ya yarda na mallaka mata kai” Sai lokacin yai dariya “tawan wlh ina shan dariya sosai in kikai waqa a tsayen nan kuma ko a jikinki” Itama dariyar take sam duk yanda ake fadin muryarta nada dadi bata lanqwasuwa indai wajen waqane. Haka ammar zaice tai mishi waqa kawai dan yaita dariya yakance tawan a haka nake sonki da kominki. Hawayen da suka bi mata fuska ta goge. Taya zata manta ammar ne a ranta. Sunyi wata irin shaquwa. A ko ina na rayuwarta yana ciki! Saidai yau take shirin yi masa sallama. Dan ta karbi aurenta da zuciya daya. Ta na fatan Allah ya yafe kata kuskuren data aikata. Bathtub ya shiga ya sakarwa kansa ruwa masu matsakaicin sanyi.+ Ko zai daina jin abinda yake ji. Zuciyarsa wata iri ce mai saurin shaquwa. Yana da kishi sosai. Har yanzun qirjinsa zafi yake. Rabon da ya ji haka an kai wata biyar. Tunda radadin rashin huddy ya soma sauqaqa zafin qirjin ya rage. Yakanji shi in yana tunaninta koda kuwa zaiyi murmushi ne. Amman ba irin nayau da yaji sunan ammar kan labban hussy ba. Ya dauki lokaci mai tsayi cikin kwamin wankan kamin ya fito. Towel ne kawai jikinsa ba tare da tunanin komai ba ya qarasa zuwa dakin baccin nasa yai tsaye jikin mudubi yana goge gashinsa da qaramin towel. * Wanka ta sake yi ta shirya cikin atamfa lemon mai dan duhu. Kwalliya tai sosai. Ta zo kiran kausar ta tuna babu lambar a ciki tana wayarta da prince ishaq ya fasa. Mantawa tai randa suka zo asibiti duba Nas ta karba. Amman tace mata zasu dawo ai ta karba tare da address din gaba daya. Ta yanke shawarar ta kira ta fada mishi abar zuwan sai wani lokaci bai dauka ba. Wajen kira shidda. Data share shi saita kasa haqura. Haka kawai taji ta damu tasan ko lafiya. Kamin kwakwalwarta ta gama natsuwa tabi shawarar zuciyarta ta fito daga dakinta ta nufi shashinsa. Duk da bata bata takawa wajenba. Wani dan karamin falo ne a ciki. Kawatacce. Tabi dan lungun da tasan zai kaita bedroom dinsa. Ta qwanqwasa taji shiru ta tura da sallama ba.a amsa ba. Dakin baccinsa gabaki daya kalar blue ne mai haske kaman na sararin samaniya. Da digon taurari yellow mai haske jikin komai. Harta da furnitures din. Kallon dakin kawai ya saukar mata wata natsuwa ta bangaren da bata fahimta ba. Kan gadon ta zauna daga gefe. Hatta zanin gadonsa irin kwalliyar gare shi. Tasa hannu ta shafi pillow din sa. Ko ina qamshinsa yake. Komai neat a tsare sai dakin ya wani burgeta. A nutse take qare ma dakin kallon. Idonta ya sauka kan bangon dake fuskantarta. Qaton hoton mahaifiyarsa ne da mahaifinsa. Dukansu sanye da shiga ta alfarma. Daga gefe ma wani hotonne na mahaifinsa da mumyn Nas shima yai kyau. Ta maida kallonta kan hoton Nas har guda biyu. Tai murmushi a ranta tana masa addu.ar samun sauqi. Dayan bangon ta juya cike yake da hoton wata kyakkyawar yarinya da duka shekarunta ba zasu qarasa goma sha shidda ba. Daya dayafi kowanne girma sanye take da riga da wando na pakistan ta yafa mayafin kan kafadarta. Gashin kanta ya sauka saman kafadarta. Idanuwanta ba kan mai hoton yake ba. Da alama wani take kallo can tasa hannu tana qoqarin rufe bakinta da dariyar da take. Sai husna ta samu kanta da yin dariya itama. Yarinyar a hotuna ne amman tana ji kaman tana qoqarin yi mata magana ne. Duka hotunan hankalinta yana wani waje ba kan hoton ba. Motsi taji dan haka ta juyo. Cik komai ya tsaya mata. Prince ishaq ne daga shi sai towel daure a qugunsa. Sai dan qarami da yake goge gashinsa. In tace jikinsa mai kyaune. To a nata ganin kaman ta rage masa daraja ne. Komai nasa. Tsayi da qirarsa yanda take misalta namijin da zatai rayuwa dashine a can duniyar tunaninta. Abin mamaki yau gashi a gabanta. Bugun zuciyarta taji ya tsaya. Har iskar wajen ma. Shi kawai ta zubawa idanuwa tana kallon yanda Allah yai namiji a wajen. * Jikinsa ya bashi ana kallonshi. Ya juya cike da mamaki ya fito da idanuwa. Lokaci daya mamakinsa ya juye zuwa nishadi ganin yanda husna ta zuba masa idanuwa. Har fitowa yaga idanunta sun qara irin yanda ka keyi inkaga wani bangare na abunka dayafi dayan barin kyau.Duk ihun da kwakwalwarta take mata a banza dan zuciyarta kan prince ishaq da kyawunsa take.+ Allah ya qera namiji a wajen. Bata taba zaton namijin da take mafarki a zuciyarta akwai shi bama. Da komai da yanayin jiki. Girma da tsayi haka take son taga namiji. “Hussy” ya kirata da wani yanayi a muryarsa. Hakan ya dawo da ita hayyacinta a kunyace ta sadda kanta qasa. “Lafiya dai ko?” Ya buqata. Duk da bata kalli fuskarsa ba taji murmushin dake cikin maganarsa. Cikin sanyin murya tace “na kiraka ne baka dauka ba shine nazo na duba ko lafiya” Takawa yai har zuwa inda take ya zauna gefen gadon. Kallonta yake sosai. “Ina wanka ne hussy shisa” Tana jin hucinsa a kusa da ita da qamshin da ba zata ce sabulai bane. Abin wanka ne ko na wanke kai. Wani fresh kamshi mai saukar da kasala. Duk ya hautsina mata lissafi so take kawai taji duminsa. Tana kuma so ta taba damtsensa da wata tsoka take dunqule. Cikin rawar murya tace masa “abar zuwa gidan kausar na duba banga number inta a wayana ba. Shine zan fada maka daman” Hannu yasa ya dago mata fuska taqi kallon shi. Miqewa tai da niyyar barin dakin ya riqo mata hannu. “Gentle inka gama shiryawa ina falo” ta furta tana qoqarin qwace hannunta. Muryansa a tabare yace “ke zaki tayani shiryawa tunda kinzo” Sai lokacin ta kalli fuskarshi sosak ta fito mishi da idanuwa tace “haba mana gentle kamin haquri ka shirya kam” Ita kadai tasan me take ji gashi yaqi ya sake mata hannu. Wayarshi tai qara,hamdala husna tai saboda sakar mata hannu yai ya dauko wayarshi. Hankalinsa gabaki daya kan wayar dayake yi ya koma. Hakan yaba husna damar lallabawa ta fice daga dakin. * Falonshi ta zauna harya fito. Suka hada ido tai mishi murmushi. Ya wani yatsina fuska hadi da fadin “shine kika gudu ko?” Dariya ya bata. Ya zagayo ya dauki pillow din kujera ya jefa mata tasa hannaye ta kare tana dariya. “Ka kyaleni ka cika rigima” ta fadi muryarta da alamun dariya. Wani dogon numfashi ya fitar dayasa husna tambayarshi “yadai?” Saida ya fuskanceta sannan yace “nagajine kawai, nagaji da komai ina son zama normal kaman kowa.” Tai shiru saboda batasan meya kamata tace mishi ba. Shima shirun yai dan bai tsammaci amsa daga wajenta ba. Yai maganar ne kawai danta tsaya mishi a wuya. “Hotunan huddy ne a dakinka?” Ta tambaye shi cikin sanyin murya. Idanuwanta kan fuskarsa. Tana kallon yanda tambayarta tasa ya rufe idanuwansa na yan daqiqae sanan ya bude su. Da dukkan alamu tambayar ta taba mishi zuciya. Hakan yasa husna fadin “kayi haquri ban……..” Katseta yai da fadin “karki damu,hotunantane” * Tare sukaci abinci. Shiru kowa da abinda yake tunani a zuciyarsa. Bayan sun gama ne suna zaune a falonsa take tambayarshi ko zasu koma wajen nas ne. Yace mata “sai gobe in Allah ya kaimu” “Allah ya kaimu” ta amsa mishi. Yatsine fuska tai yace “yadai?” “Gashi na ya isheni bana iya gyarawa da kaina ko a gida saloon nake zuwa ko mamana ta tayani mu gyara” Idanuwansa ya kafa mata yanayin yanda take maganarta yana burge shi. Murmushin sa yai. “Muje ki wanke in tayaki” Ta fito da idanuwa tana dariya “gentle ina ka iya? Ka taba yine” “Sai muyi downloading ingani” Ya fadi muryar sa babu alamar wasa. Hakan ya sake bata dariya. “Lallai barshi i will manage har lokacin da zanje saloon” Yasan zai iya sa a dauko hair stylist ta gyara mata har gida. Bazai yi bane sabo da yana son ta soshi kuma bashida wani wadataccen lokaci. So ba abu bane dake shiga lokaci daya. Musamman nashi a zuciyarta dake dauke dana wani. Hade fuska yai kaman maganarta ta taba mishi zuciya. “Ni ko?” Ya fadi yana tabare mata fuskarshi me kyau. Ta sake yin dariya. Tashi yai. “Ina zaka?” Ta buqata bai kulata ba ya kama hanya. Hannunshi ta riqo ta rasa me yasa jikinshi yake mata dumi haka. Sai kace yana zazzabi. Juyowa yai ya daga mata girarsa duk biyun. “Zo ai downloading din kagani sai mu gyara tare” ta fadi tana kallon idanuwanshi. Murmushin sa yai mata daya kai har cikin idanuwanshi ya samu waje ya zauna sukai downloading yanda ake wanke gashi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *