WATA FUSKA CHAPTER 4

WATA FUSKA CHAPTER 4

Kujera ya samu ya zauna yace yana me mata nuni da hannu akan kujerar dake fuskantar tasa+ “Ki zauna anan” miqewa tayi ta zauna tana meci gaba da sharar qwallah….gyaran muryarshi yae sanan yace “Kinada kati a wayarki?” Kallonshi tae ta gyad’a masa kai alamar akwai yace “Yauwa saisaita nustuwarki kar kuma kiji tsoro!! Dukkanin wani tsohon saurayi da kike dashi ko kuma wani mutumin banza dakika san kun tab’a yin mu’a mala dashi ki kirasa a waya ki gaya masa kalmomin nan dazan fad’a miki…..a yanzu kuma” da sauri ta d’ago ta kallesa ya kawar dakanshi daga dubanta yace “Hand’s free zaki saka kice da duk wanda kika kira bayan kun gaisa ” Na gaji da wannan sab’awa Allah danakeyi yanzu mijin aure nake nema dan Allah ko zaka taimaka ka aureni?” Kallonshi ta qarayi a karo na barkatai kan tace “Bazan iyaba wlhy Maheer” “Idan bazaki iyaba ki tashi ki barmun gidana” Jikinta ne ya soma rawa, itada dai Nancy ta kasa gane inda ya dosa amma dai kanzil batace ba tun zuwansu “Kayi hakuri zan soma kiran” Wani Alhj Suraj ta kira wanda shine ya fara lalata mata duniyar ta kuma akan ze aureta yazo gidan su matashin me kudi daya gama da ita ya watsar,ya dauka suka gaisa a mutunce ta rattafomai yanda Maheer yace tae, dariya ya bushe da ita yace “Haba isy…tayaya zan aureki? Bayan na sanar dake tun farko bazan iyaba, islam dazan aureki aida na aureki tun farko tunda nasan nine silar b’ata rayuwarki, wlhy a gaskia bazan iya auren matar datake yawon tazubar ba, sabida haka kiyi hakuri kije ki nemi miji daidai dake” wani baqin cikine ya tinkarota tace cikin takaici “Amma suraj idan nime yawon tazubar ce ai kaine silar halakkkar da mutuncina ko, kakuma gujeni a lokacin dabanida wani gata se Allah yanzu yaya kakeso nayi da rayuwata?” Tsaki yaja “Kinga islam nifa wlhy sena wulaqantaki idan kikace zaki zomun da raini, haka kurun shekaru uku bama tare se yanzu dan cikar iskanci kice na aureki? Wama yasani ko kinada qanjamau” zafi zuciyarta keyi bazata iya saurara ba ta katse kiran da saurinta ta dafe qirjinta,tausayi ta bashi yace “Ki kira wani mana” Ba musu ta kira wank boy friend d’inta dake Arqillah Sameer yana d’aga kiran yace “Me bani kyauta!! Ta samu ne inzo muje mu hole?” Runtse idanta tae ta bud’e su kantace “Sameer Dan Allah zaka iya aurena?” Wata dariya ya bushe da ita cike da shaqiyanci kan yace ” ke kina tunanin aduniya akwai wanda ze aureki ne, ai daga zaran kikaji yarinya tafito yawon ta zubar tokuwa seta zubar d’in dan bame aurenta!! islam ko d’an iska baya son er iska se’a bariki” katse kiran tae ta kalli Maheer murya na rawa furta “Kayi hakuri Maheer bazan iyaba” shima kallonta yae “Sekin kirasu, su goma sha biyar tukunna zan barki, akwai abinda nakeso ki sani dan kiwa kanki hisabi da kanki islam” batare data qara cewa komai ba tai kiran wani!!!! Shima ya yab’a mata magana haka taita kiransu suna cin zarafinta har su goma sha biyar, zuwa wannan lokacin ta gama kaiwa qolin qoli wurin b’acin rai bata tab’a kasancewa cikin namada ba se’a wannan lokacin!! Ita dake taqama da kyau da isa acewarta seta gama cin duniyarta d tsinke sannan tae aure a lokacin da takeso sanda kuma tae ra’ayi!!! Yanzu tunkan aje ko ina taga ta kanta, kasa d’aga idanta tae ta kalli Maheer ita kuwa Nanuwabta qulu sosai da wannan tozarcin daya siyawa qawarta…..miqewa yae tsaye ya kalleta STORY CONTINUES BELOW “Islam dukda wannan abin daya faru acikin wa ennan susu goma shabiyar d’in bazamu karaya ba, zasu basu sati d’aya wataqil inshaa Allah wani ya sauya tunani yazo miki da zancen auren dan haka karki tashi hankalin ki kinji” Nanuwace ta miqe itama ta matso inda yake “Amma Maheer inaga idan ma bazaka hakura ba,be dace ka siya mata wannan tozarcin ba ko?” Ta qarashe maganar a hasale dason jin meze ce…. “Da bakyason a tozartar da ita aida kin koyar da ita saka niqafi yanda kikeyi, kinga ke sekinayin karuwan cinki asiri a rufe duk qwaqwar mutum be isa ya gane kiba” wani qululun baqin cikine ya tasowa Nanuwa ya tokare mata qahon zuci, wani qululun baqin ciki yaja zarya tsakanin harshenta zuwa maqogwaronta wani yawu me kauri da d’acin gaske yazo mata ta masa had’iyar bazata acikin bushashen maqoshinta….Da qyar ta tattaro kalaman ta “Niba karuwa bace balantana ka jefeni da mugwayen kalamai Maheer, bana daga cikin matan da duniyar su ke shawagi dasu acikin jirgin shed’an a wannan tafiyar, bana cikin matayen dasuke amfani da *WATA FUSKA* domin cinma wata muguwar manufa!! *WATA FUSKAR daka gani lullub’e a saman tawa bata Munafurtan mahalicci na bace!! Ban saka *WATA FUSKAR* ba seda na shirya kariyar mutuncin ta da nawa da kuma Fuskar dake a qarqashinta!! Ka sani wlhy *WATA FUSKAR* tafi gaban mari bare ka kalli tawa ka jefeta da muggayen kalamai irin wannan…. A taqamarka kaime hankaline baku ne kuke horewa matan kunne ba, kuke sabar musu da kud’i kuke rudar su da manyan motoci? Kuke miyar dasu qananun karuwai!! Yanzu banda kake d’aya daga cikin shaid’anun masu zuwar wa mata da *WATA FUSKA* menene ya sanya baka tsaya yin magana da ita a gidan ubanta ba ka kawo ta nan? Me qofar gidan ubanta yae maka?? Wlhy bazan gafarta maka ba idan har ka qara jifana da muggan kalamai irin wannan nasan darajar hijabina,nasan darajar mutuncina dana iyayena niba sakarai bace dazaka gasa mun magana nama shiru kuma zargin dakamun na zina Allah ya isa!! Lahira se an tsayar dani dakai kayi shedan hakan” dukkanin kalaman datake be kalle taba seda taja masa Allah ya isa! Da saurinsa ya d’ago ya kalleta yace “Bakida hankalina zaki jawa mutum Allah ya isa? Ni yaushe nace dake mazinaciya, ai bature yace show me ur friend and i will tell u who you are, so qawar ki danake ga bacci kad’ai ke rabaku ita nagani tana abinda na alaqantaki dani laifi ne wannan? Bance na tabbatar ba zargi nake” Wani takaicine ya qara lullub’eta tace “Agidan friend d’in naka daka ganota shiba friend d’inka bane? Idan haka ne dukkaninku mazinata ne kenan kaida abokin naka? Ya kamata ka sani cewar shiru shiru bawaifa tsoro bane gudun magana ne, idan kana takamar kai wanine nima haka nake taqamar ni watace! Idan kanajin cewa kaime arziqine nima haka nake taqamar cewar nidin nan me rufin asirin Allah ce, yanda baka neman komai a wurin kowa nima hakan take ina godiyawa Allah da ni’imonsa akaina” juyawa tae a fusace ga islam “Ke kuma mara zuciya ki tashi mu tafi idan bazaki jeba nai gaba abina,danni bazan zauna ana nunamun anfini sani ba” kallonta islam tae tana sharar qwallah “Kiyi hakuri muji tabakin sa mana Nancy” acikin niqafin ta hararota ta zare madubin idanta manyan idanuwata suka qara bayyana tace “Anan daikam banga wurin zamaba kinga tafiyana nikam” ta juya har tana had’a qafa shima ya bita da kallon mamaki lallai yarinyar nan ta wuce saninsa haka take da masifa tome yae zafi? ……. *************** Shirye shiryen auren Ameen akeyi da ummul babu qaqaquta se b’arin kud’i akeyi tamkar basusan zafin suba, Ameen ya zagewa Ummul bakin aljihunsa se wawura take tana murna batada labarin bashi takeci wanda zata fanshe shi…….Baba Azumi zaune ana lissafin kudaden da za’a kashe wurin yin datacciyar walima ta gani ta fad’a gefenta ummul ce da kuma Hafsat sedai sam hankalin hafsa baya jikinta yana cen wurin tunanin Maheer bata tab’a son wani namiji kamar yanda takeson Maheer ba kazalika bata tab’a jin tsanar mutum kwatankwacin yanda taji ta tsani maheer ba zargin dayike akanta ya mugun baqanta ranta sosai ba kad’an ba!! Mari taji an dire mata a kunce daya gigitar da ita sannan Baba Azumi tace “Er baqin ciki anata magana kinyi kamar bakijiba to wlhy ta Allah ba taki ba, kina duniyar nan Ummul zatai aure ta barki kegaki nan jiya iyau, kullum zaune a gida ko tsoho be tab’a cewa yana sanki ba bare kuma yaro” sadda kanta tae qasa batace komai ba “Akacewa kiwa ogarku waya inda kike zuwa koyon girki, abinci na mutum dari uku ranar walima da kaji asama da komai daya dace nawa zata mana?” Hakuri ta hau bayarwa ta kirata sukai magana sannan tae waje ganin wayarta na ringing kuma *Mahal* ne ya dameta akan yanasonta ita kuwa tasan na d’ibar takaicine yakeso yae da ita gashi bata shirya auren wanda bayya santa ba. *********** Maheer tunda yabar sokoto be qara neman Islam ba seda sati ya zago sannan tana kwance a d’akin innan ta, tayi wani rama tana tunanin duniya ba inda take zuwa tun faruwar abin, sega wayarsa yana kiranta a waya, jiki na bari ta daga yace da ita yana waje…….. “islam wadawa suka qara kiranki dasunan zasu aureki tun daga ranar?” Kallon shi tae bataso ko gaisawa basui ba ya bijiro mata da wannan maganar gashi bataza iya masa qaryaba tace a raunane “Babu ko d’aya daya qara kirana har abokinka ma Eashmal” gyaran zamansa yae “To Islam karki zata cewar cin zarafinki ne na saka akayi,wlhy bako d’aya so kawai nake kiwa kanki hisabi da kanki tun a duniya, kuma kimun adalci, yanda wa ennan suka gujeki suda ma suka saba dake shin ni zan iya kuwa? Kije kiyi tunani idan kinga ya dace ya cancanta ki zamto matana seki gayamun” shiru batace komai ba gyaran murya yae “Nizan tafi islam ina miki fatan alkhairi” murmushi ta sakar masa “Dan Allah ina roqon wata alfarma agareka ban saniba kozan samu” kallonta yae shima “Inehmm wace irin alfarma kenan?” “Sonakeyi ka saurari labarina, tarihin rayuwata da yanda na zinci kaina a yanayin daka ganni, bzan qara takuraka ba idan har kaji labarina, nima so nakeyi kawa kanka hisabi a kaina tun a duniya bayan jin labarina kaji” jinjina kansa yae yace “Ranar talata zan dawo zanzo muje gidana ki bani labarkn dakikace zaki bani” godiya tai masa ta juya zuwa cikin gidan…. Kallon Mahal take cikeda mamakin sauyawar halayensa, yanda yake roqarta akan ta daure ta auresa, cikin sanyin murya tace+ “Kayi hakuri Mahal wlhy bawai sanka ne bana yiba ko kuma na rainaka, ko d’aya wlhy ka sani bazan iyaba, na sani auren huce haushi kake shirin yi dani bawai soba, hakan kuma na sani cewar bakada labarin azabar da zansha a hannun su Ummul idan sukaji wannan maganar, ina roqon alfarma agareka daka janye wannan qudurin naka” nisawa yae yace “Amma menene zesa ki damu da abinda zasu mikin keda bawai dad’ewa zakiyi a gidan ba, auren danakeso nanda sati biyu ayi, dan Allah ki dubi maraici na” Nisawa tae “Banida wani gata a duniyar nan sesu mahal, bazan lamunci watsar da dangina akan ka ba, ka sani ni marainiya ce sabida su Baba iro sune iya yena, mahaifina ya rasu bayan nini kadai suka haifa a duniya!! Ya rasu ya barni inada qananun shekaru mahaifiyata er jamhoriyar Niger ce haka bayan rasuwar mahaifina ta auri mahaifin su ummul babu kalar qiyayyar daban ganiba nida ita qarshe ya saketa kuma taso tafiya dani ya hanata, a yanzu haka tana aurenta acen Niger da yaranta uku, ina shiga a Nigeria idan nae rashin su Baba iro? Bayan sune gatana gaskia ka sani wlhy bazan iyaba dan Allah kai hakuri” murmushi ya sakar mata yace “Bazan takuraki ba Nancy amma dai zan baki lokaci zuwa wani satin kiyi nazari akai” shiru ne ya rataa wurin kanta nisa tace “Banaso ka wahalar da kanka wurin neman aurena Mahal, sabida ni bazan tab’a iya aurenka ba har abada” Tana gama fadar hakan tae ciki abinta shi kuwa ya dafe kansa dukda haka bata tsiraba seda sukaci mutuncin ta sosai! ************ Sosai Maheer ya tattare nutsuwar sa yana kallon islam!! Duk ta masa fari tamkar batada jini, tayi baqi da komai…..gyaran zamanta tae kantace “Da farko dai ni sunana Salahatul islam Idris me walda, mahaifina da mahaifiyata haifaffun en sokoto ne acikin qaramar hukumar silame dake cikin jihar ta sokoto, wannan kyawun halittata ta bahaushe ce kawai dani sabida iyayena duka hausawa ne, haka na ganni ina kamada mahaifiyata sosai komai nawa natane, mun taso a unguwarmu dake tudun wada mahaifina walda yakeyi itace ta kawoshi zaman sokoto ma, wannan dalilin ne ya sanya ake ce masa idi me walda, ya taso da matuqar son yaga yaranshi suna karatu sedai bashida qarfi ina da yayyu guda hudu duka maza, biyu uwarmu d’aya ubanmu d’aya biyu kuma yaran kishiyar Mahaifiyatane amma ubanmu d’aya, dukkansu suna fara karatu har matakin jami’a amma da qyar biyu suka qarasa kuma suna nan har yanzu cikin gidan ba aikin ayi tun daga bautar qasa, biyun kuma sune muke uwa d’aya uba d’aya wanda khamis yanzu yake aji hudu shi kuwa Asheer yana gun bautar qasa dalilin dayisa se yanzu suka kai nan shine sabida kosun fara rashin transport kawai seya tsayar dasu, so biyu khamis yana fara zuwa coe rashin transport yana daqushe karatun harya watsar wannan ma dasuka kammala da taimakona ne!!! Nice na taso me nutsuwa acikinsu amma se Allah ya mayar dani haka tunda na soma karatun gaba da secondry school….so da dama nikan tashi agidan mu babu abinda zamuci wani zubin haka zamu wuni ina kallon yaran kishiyar Babarmu suna cin abinci amma bazasu bamu ba… Haka sabida ita en uwanta sunada rufin asiri mukuma bamuda kowa se Allah, bayan dana samu admission a jami’ar usman d’an fodii na soma zuwa school sena soma had’uwa da ibtila’in rayuwa… Wani zubin inaji ina gani lecture zata wuceni sabida rashin transport.. Idan zanje makaranta na dinga kame kame kenan na rashin suturar zuwa makaranta wannan abin yana damuna bame qawance dani sabida hatta turaren sakawa banida shi wani lokacin ma sekaga vaselin dazan shafa ya gagaremu senaje a hakan ta fata duk furfuri!! Haka idan nawa mahaifina zancen siyen handout baya kulawa seyace babu har wani zubin nakanji tamkar indena zuwa makarantar!! Haka dai naketa daurewa har muka qarashe zangon karatunmu na farko,nida Nanuwa ajinmu d’aya kuma mumu kad’aine yaran bayin Allah, abinda na kula dashi shine Ita nanuwa bata sakin fuskarta nima muna qawancene kawai amma befi naga face dibta so biyar ba, wani zubin tare da ita muke soleta har gida qasa, idan mun fita bama rabuwa se munkai dandima se kowa ya dauki hanyar gidansu da qafa, ganin inashan wahala ya sanya mahaiyta tace in dawo hostel da zama na daure haka nan na dawo tare da neman Nancy akan ta dawo amma se Baban ta yaqi yarda, sedai takanzo duk sanda takeda test ta kwana karatu……zamana a hostel ya sanya na had’u da qawaye iri iri kala kala, dana gari dakuma b’ata gari ganin banida gata ya sanya wata qawata danai a hostel me suna jameela ta dinga nunamun hanyar yin zina amatsayin sana’a amma fir senaqi yarda haka ya sanya ta soma rarrashina harna soma kaucewa hanya, wani zubin takanzo da maza muje hira a mota kuma takan bani kyautar sututu da kud’ad’e jamcy na yawan nunamun cewar ina cikin musiba na talauci gashi handout ma ya soma gagarana siya, Namcy ta soma ankaewa da yanayin dana soma shiga na wani sauyi ta matsamun na bata labari ta hau wa’azi da ban baki, harta mun magiya, a haka dai ta saisai toni tayi sa’an rabani da jamcy!!! Bayan nan kuma se Allah ya had’ani da wani saurayi me suna suraj haka na daddage ina qaunar suraj, suraj ya yaudareni har gidan mu yaje ya gayar da iyayena ya kuma tura neman aurena, komai suraj yana mun nafita a qangin talauci har ina samu in taimaki iyayena da qawata Nancy dake shan wahala matuqa agun Qanin mahaifinta dake riqon ta da matar sa, Suraj ya sabarmun da kud’i seya kashemun dubu hamsin a rana qarshen wata yana bani dubu dari yace nai laluran school suraj dan kasuwane kuma d’an siyasa ne riqaqqe!! Katsam rana d’aya suraj ya bijiro mun daneman hadin kaina akan mui zina, na nuna masa muda zamuyi aure menene abin rushing yayi yayi nace harammun bazan ba musamman shida yakeda matansa biyu yaje ya rage zafin sa anan, daganan ya nunamun gini yakeyi kuma yanada kwadayina, dayaga bazan yiba seya dawo rarrashin akan nai hakuri koda wasanni yana tattab’ani munayi tunda ba komai bane, haka na saki jikina dashi ganin kamar a hostel mafi akasarin mata suna yi, inajin suna hira mukanyi wasanni ta hanyar tabawa juna sassan jikinmu…wannan shine babban kuskuren dana tafka!!!! Na saba sosai da wasannin da suraj kemun ganin na fara sabawa ya sanya suran ya qara tadamun maganar zina, nace bazanyiba bece komai ba ya tafi tun daga ranar suraj seda yae watanni uku baya waiwayata ko wayana baya d’auka na shiga damuwa sosai, abubuwa ukune suke neman zautar dani na farko dai Ina matuqar son suraj a rashinsa har rama nai da kuma ciwo, na biyu kuma shine tsantsar talaucin dayamun dirar mikiya nasoma sabawa da kudi a wannan lokacin ina aji biyu kuma tun a zango na biyu na hadu da sura farkonsa kusan shekara munyi rayuwa me ma’ana sosai na shaqu dashi….haka kuma abu na uku shine tsantsar sha’awa na saba da wannan wasannin banzar, sena kasa sukuni inji ina son kasancewa da suraj harna soma jin koma waye zan iya wasannin dashi, adu’a naketayi haja dai har Allah ya karkato da suraj awurina, koda yadawo ko wasanin baya mun yace dani harammune nai hakuri koda wancem yaji wa’azi ya tuba, haka muka qara watanni biyu bama komai daya danganci wannan ko riqen ahnnu bayayi kuma duk abinda yakemun ya linka!! Ranar mukaje shopping akan kayana ya qare yace muje na rakashi yaudai na gayar da mamansa haka mukaje gidan ba komai a raina……”😭😭😭😭😭 shiru tayi tana sharar qwallah kantace cikin raunin murya “Maheer bayan mun shiga gidan har parlor muka zauna wata yarinya dagani er aikin gidance ta wadatani da abubuwan sha shi kuwa ya shiga ciki, nasha lemo da cake da aka ajiyemun dama na kwaso qishiruwa kuma naga alamar ba kowa tunkan suzo naji kunya….haka ta kasance Maheer daganan se farkawa nai na ganni cikin jini da wahala ko yatsana bana iya d’agawa, alamu duk suka nunamun fyad’e suraj yamun tun daga yanayin zogin danaji jiki na yanayi aciki, ina nan kwance ina tunanin meya faru se ganin suraj nai ya shigo dagashi se boxers yana murmushi ina hawaye nace ” suraj mekamun mesa zaka cutar dani?” Dariya yae yace “Soyayyace ta sanya haka Islam kiyi hakuri” kukana ya qaru jinya tabbatarmun na qarasa rufe jikina da bargon dake wurin nace “Wlhy senayi qararka a kotu azzalumi kawai” kallon cikin idona yae yana wani shu’umin murmushi yace “Waye ubanki islam? Me waldar? Me zaku iyayi dani? Aganin bansan darajar kudi na dakuke taci bane islam? Inada hankalina wlhy nasan me nakeyi ki sani ba’a cin kud’ina haka kawai kuma kije kotun qoli shari’a zan iya kune zaku wahala tunda kune talakawa, ina zamana kika zo har gidana kuma waye shedarki? Banza jaka” kukana na tsananta haka na barwa Allah ban gayawa kowaba se kawai na hakura, tsawon watanni biyu suraj ya dena kulani kuma tun daga lokacin da abin ya faru har akai watannin biyu na nemi al’adata na rasa!!! Shiru tai na some seconds tana sharar qwallah kan taci gaba… Koda na ankara na gayawa jamcy setace muje asibiti gwajin farko aka tabbatar inada ciki, da taimakon Allah fad’uwar gaban jin inada ciki shine yayi sanadiyar soma bleading dina har cikin ya b’are nasha wahala seda akamun wankin mara banji ba ban gani ba!!! Daga wannan lokacin kuma se jamcy ta fara tsora tani akan nazo mui karuwanci kota nunawa kowa takartar miscarriage din dan shegen dana samu ya fadi har akamun wankin mara, sabida bazata rufamun asiri haka kawai ba ita idan ta kaini gun manya zata samu kudi, nayi nayi jamcy ta rufan asiri taqi haka na yarda akan zanje so biyu tace itama ta yrda, mutumin farko dana fra had’uwa dashi shine ya bani kyautar miliyan daya, ya baiwa jamcy dubu dari uku, na biyu kamma daya tashi seya 1.5m wannan ya qara bud’e idona tunda nasan dad’in kud’i shi kenan sena manta batun yi so biyu haka na manta haramcin aikata abin,Nancy har kuka takemun akan ma tuba na dena amma Allah be sanya nayi nadama se zuwanka, babu memun fada agidanmu mahaifina be taba bincikar inda na samo kudi ba” …..jin tayi shiru na mintuna biyu ya bashi damar miqewa tsaye ya miyar da hannayensa guda biyu baya yana zagayen parlor d’in yarasa mezece laifin waye to? Iyayen ta ko suraj ko kuma ita kanta? Yafi mintuna talatin yana nazarin maganganun islam se cen ya dawo ya zauna ya muskuta da kyau yae gyaran zamansa yace+ “Amma islam kina cikakkiyar sallah biyar awuni kuwa” dukda bataji dad’in maganar ba amma seta tsinci kanta da bashi amsa kamar haka “Ina yi mana Maheer, meze hana nayi saah na taso agidanmu an koyar dani tsare sallah akowane hali” jinjina kanshi yae alamar gamsuwa “Amma kuma bakyayi akan lokaci islam” shiru ta d’anyi kan tace “Ea to anan bazanyi qaryaba wani zubin se magrib nake yin azahar da la’asar dinma gaba daya senai maja” kalonta ya qarayi “Amma aka gayan miko cewa haka ake sallah? Idan fa kabari lokacin sallah ya wuceka da gangan kashiga uku islma, mesa zaki miyar da rayuwarki kamar ta marasa ilmi? Kina ganin ko wannan rashin kiyaye sllah akan lokaci baze jefaki ajikin ibtila’in rayuwa ba? Ya dace ace kisan cewa ba’awa sllah hakan ai, wanda ma yake hada salloli yaushe zega time din yin adu’a tukunna ma yaushe rabonki dayin azkhar? Kokuma ki zauna kiyi karatun alqur’ani me girma tayaya zakiga haske islam?” Shiru tae tana tunani ita wlhy tun quraninta na islmaiyya bazatace ma ga inda yake ba, ko na app da ake turowa a waya bata taba ajiyewa ba kuma ita abinda yasa bata ajiyewa shine sabida yanayin abubuwan dake kan wayarta, soda yawa idan taje wurin gardawan bariki setayi kallon fina finan batsa takejin sha’awa, sannan wani zubin idan taje wurinau sesu shagala da zancen sallah ta kula dan zaman nan datae agida sosai take sallah sam bata wuceta to kenan duk musababbin shigarta wannan halin hadda mugun abun nan datakeyi….seda ya qara cewa “kinaji kinyi shiru islam nace yaushe rabonki dayin karatun alqur’ani ko Azkhar? Hawayen dake kan fuskarta ne ya sauka tace.. ” bazan iya tuna tuna tun yaushe ba Maheer” nisawa yae yace ” Manta wa da Allah tamkar qulla qawancene da sheda islam, baze taba barinki ki mori tsufanki ba, zega yanda duk zeyi ki lalata quruciyar da hannunki ta yanda tsufanki baze miki kyau ba, kazalika koda kin mutu kafin tsufan ki shige wutar Allah, banji dad’in yanda rayuwarki ta kasance hakan ba, dukda kome kika aikata a rayuwa tare da Suraj za’a raba a baki naki kason shima yaja nashi, ga kuma haqqin ki na cutarwar daya miki gashi shine mutumin farko da kika nemi ya aureki sanda nace kiyi hakan, ki kasance acikin istigfari ako da yaushe kije gida yanzu sena qara neman ki kuma” sakkowa tai tabi gwiwowinta tana kuka tace “Ka taimakeni Maheer ka rufa asirina, ka aureni wlhy idan baka banida amfani” murmushi ya sakar mata yace “Kije gida karki damu My Islam zanzo gidan idan na dawo kinji” godiya ta masa ta miqe yace “Zoki karba ki riqe a hannunki banaso wata buqatar ta taso dazaki nemi wani abu awurin wani” sadda kanta a qasa tae ta kasa koda motsin kirki bare ta karbi kudin seda ya mike ya saqala mata a hannu sannan ta juya Kamala ya dauki hanyar gidansu da ita!!!! ************ Yau auren Ummul saura sati d’aya wannan ne dalilin dayisa gidan nasu ya qara kaurewa da hayaniya da ihun mutanen qauyensu da en uwa dakuma abokanan arziqi!! Ummul na zaune tana d’aye selotop dake tafin qafarta bayan ta gama cire lallin gargajiyar data saka, farar qafarnan ta d’akko jan lalli se sheqi takeyi! Ata gefenta qawar Ummul ce Khadeeja ke mata zuba “Yanzu ke Nancy meya alaqanta ki da lallin gargajiya za’ai biki a gidanku? Bakya jin kunyama kizo muje gun zarah uwar zane mana ranar laraba ta zane mana hannayen mu da qafafuwa dubu uku ce kun rabu lapia” Kallon sosai ta mata tana murmushi “Zanjene ai kurun dai dama dole wannan nake farawa dashi, shisa ma nakeyi da wuri danna cire a tare” murmushi tama tai ta sunkuya sosai tace “Wai nikam Hafsat Anya ke ba balarabiya bace? Wlhy danice ke da duniya seta gama ganin wannan surar tawa, sumar kanki kawai seta b’ata wa mutum lokaci wurin kallon ta nifa aduk cikin jikinki banga inda Allah ya kuskure miki ba dama kuma shiba me kuskure bane yasan daidai…ummul ita muke zuzuta kyawun ta amma wlhy Nancy bawai buzuwa ba babu wanda baze yarda cewar keba balarabiya bace idan ya ganki” sakin lallausan murmushi tae . “Khadeejahh abeg jeki kiyi sallah abinki” ta qarashe maganar tana dariya……itama khadeejan juyawa tae tana fad’ar “Anyi baqi daga Niger naga wata mata me kamarki ga alaama maman kice” murmushi tae ta zata wasa ne yasa bata kulata ba seda ta gama tae alwahala ta nufi d’akin Baba Azumi….. Acen ta tarar mamanta da qannin ta sunzo mata…Baba iro ne ya aika suzo dan ya bata haushi sabida taga yayi kudi data gujesa, acewar sa dan bashida kudine taqi zaman aure dashi yayanshi dayakeda abin hannunsa ai basui haka ba ta zauna….. Murna a wurinta ba’a magana sam, mamanta ma taji dadin ganin ta se yare sukeyi na Buzayen Niger Baba Azumi se harare harare takeyi tana yatsina fuska!!….. ********** Duk saurin datake ya hanata d’aukar niqafin ta ayau dinnan, dama wasu lokutan takan fita acikin unguwarsu hakan……murna sosai takeyi tanaso taje ta siyawa mamanta Lemu tasani akwai lemuka agidan taga ko abinci ba’a baiwa har qannin taba, bazata jira yaran su mutu ba da yunwa murnan ganinsu ya hanata shiga b’acin ran an hanasu abinci…..a qofar gidansu tae karo da Mahal da Maheer a tare suna hira sun haye saman motarsu ta baya sunata tafa hannu suna murna qirjinta ne yae mugun dokawa ganin yanda dukkaninsu suka zuba mata ido tamkar wacce qwai ya fashewa a ciki haka ta dinga wurgo qafarta tana kusanto gate din gidan dauke da ledar lemo a hannunta…kanta qaraso Ameen yayi parking zuqeqiyar motarsa ya fito ga mamakin ta wata qara suka saka shida Maheer ya diro daga motarsa yana ihun “MAZAJE!!!!!” Suka tungume juna bayan sun tafa yace “Ango kasha mai” dariya Amin yae “Tunkan akai Amaryar kake cewa nasha mai ya akai ka gane gidan harka rigani qarasowa” kallon Mahal yae yace “Wannan yaron ne qani nane dan wurin qanwar mahaifina ne anan suke zama shine muna tare dayaji kana kwatantamun yace ya gane wurin” murmushi yae shima “Ohk sannunka shima semuje dashi ai, wannan al’adar ta sakkwatawa dame tae kama ace se an maka taron en mata sun fadi adadin kudaden dasuke so ka basu” dariya Maheer yae yace “Tunda al’adar suce aisemu hakura, namata waya tace suna masaukin baqi na waje muje kawai” wucewar Nancy ne ya dakatar dasu duka ukun suka bita da kallo, dukse ta tsargu aciki Mahal ne kurun yasan fuskarta amma Maheer da Amin basu santa ba bata fata su santa ma se idanta da suke gani….. Maheer da qirjinsa ya ninka dukawa ganij cikin idon daya taba sani yace da Amin1 “Aboki ko wannan ce amaryar?” Dukan bayansa yae “Ko alama tawa matar taci uwar wannan a kyau da komai, baka ganin wannan da yanayin qauyawa” dariya sukai dukkansu ya sake cewa “Qanwar matana ce fa, nasha ganinta da wannan kayan na jikinta so am sure itace ma” kallon sa Maheer yae “Kayan kawai fuskar fa?” Be kulasaba sukai ciki ita kuwa se d’aga qafa takeyi zuwa cikin gidan kamar zata kifa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *