WATA SHARI’A
CHAPTER 13
Bayan sun koma gida sukaci gaba da tattaunawa inda Rabiatu da Zarah suka ringa tsinewa Gentle bayan Ummimah ta basu kaf labarin abubuwan daya samesu har mutuwar Baba, da kuma ta Afrah, ga Amrah maras lafiya bama asan inda take ba.
Sunji haushi sosai kuma suma sukayi fatan samun nasara a wannan shari’ar da ake, saidai kuma a yanda sukaji labarin dukiyar mahaifin Gentle, da kuma babban Barrister din daya daukarmata, sun shiga kokonton samun nasararsu, saidai kuma sunyi fatan Allah yasa dukiyarsu kar ta amfanesu.
Da wannan firar har yamma tayi Sultana da Umar suka dawo gida cike da gajiya, Su kansu a mota firar shari’ar kawai yakeyi, amma shi yanaji ajikinshi next zaman da za’ayi insha Allahu zasuyi nasara bama sai ansha wahala ba.
Koda suka shigo gida Hafsa ta taresu, murna fal a ranta ta gaishe da iyayen nata sannan suka k’arisa daga ciki inda suka samu haryanzu su Zarah basu daina firar abunda ya samu su Gentle ba.
Bayan sun natsu sosai Umarya kira Dr. Rafiq, ya k’ara tabbatar masa da cewa fa ranar Monday next week anada bukatarshi a kotu, ya amsa da ‘insha Allahu zayyi kokari ko zuwa ranar Sunday ya shigo Katsina, saboda ranar Friday zai koma Jalingo’,
Sallama sukayi Umarya kashe kiran, Sultana tace
“To ya maganarwancan ma’aikatan na makarantarsu?”,
“wannan kuma ai bamuda case dasu, kotu zata aika da sammacinta” Umar ya bata amsa
yana kokarin cire suite daga jikinshi. ‘ Taimaka masa tayi ya karisa cirewar, itama ta cire nata sannan suka shiga wanka.
Fitowarsu suka samu abinci jere a dining, murmushi Sultana tayi saboda tasan babu tantama wannan aikin Ummimah ne, tunda suka dawo gidan da zama ta hana Safiyya yin aiki sosai, komai ita takeyi bata gajiyawa.
’Ranar lahadi 02:45pm‘ A daidai wannan lokacin ne Umar ya latsa kiran Dr. Rafiq domin yaji ko ya iso Katsinar amma shiru bata shiga ba, Sake latsa kiran yayi still dai ‘not reachable‘, Hakan yasa ya fuskanci Sultana da itama shi take kallo yace “Ban san mesa ba numbern Dr. Bata shiga, kinga tun yamma naketa fama kiranshi amma duk maganar guda ce”, “Ina tunanin k0 yana hanya ne, wata k’ila kuma hanyar babu network mai kyau” Sultana ta bashi amsa tana kallonshi cikin soyayya.
Basu kawo komai a ransu ba a haka suka bar maganar su a tunaninsu ko yana hanya, dan haka cikin kwanciyar hankali bacci ya d’aukesu mai cike da walwala da nishadi saboda yanda sukejin dad’in zasu shiga kotu da hujjarsu babba, wadda suke ganin da ita wannan
shari’arzata kawo karshe. ‘KOTU’
Yau ta kama ranar Monday bakwai ga watan daya, shekara ta dubu biyu da goma sha
bakwai, Kotu ta cika kamar zaman farko, harma zan iya cewa a wannan lokacin ma tafi cika sosai, Kowa burinsa yaga yanda karshen shari’ar zata kaya.
Bayan mai gabatar da kara ya tashi yace
“Yau 7-1-2017 kotu zataci gaba da sauraron shari‘ar data fara a makon daya wuce, wadda Aishatu Abubakarta kawo Salmah Abubakar k’ara akan zargin da take na sakawa an mata fyad’e wanda yayi silar dakatar da ita daga karatunta”. Alkali yace
“Barr. Umar da Barr. Sultana ku muke saurare, kotu na fatan kun kawo mata shaidun data bukata a zaman farko”,
Shiru ya biyo baya kasantuwar daga Umar din har Sultana basu tattare da natsuwarsu,
Tun shigowarsu kotu suke baza ido dan ganin Dr. Rafiq amma shiru haryanzu baizo ba,
Kuma gashi idan sun kira lambarsa bata shiga,
Baki daya hankalinsu a tashe yake,
Ita kanta Ummumah nata hankalin a tashe yake, barin kawayenta Rabiatu da Zarah da suma basu tattare da tasu natsuwar. ‘
“Barr. Umar!” Alk’ali ya fad’a a hasale saboda yayi tunanin ko yajishi.
Firgigit suka dawo hayyacinsu, A daburce Umar ya mike tsaye dukjikinshi yayi sanyi, Sunan Allah kawai yake ambata a ranshi, saboda yasan matukar Dr. Rafiq baizo ba to shikenan basu ba winning din eannan shari’ar.
Bayan ya tashi tsaye yace “Kotu tana bukatar ganin Sister Maryam, Sister Fatima, Sister Rooth da kuma Sister Ifeoma”.
Wasu mata ne suka taso, biyu daga ciki manyan mata ne akalla zasu kai talatin da biyar zuwa da shida,
Biyun kuma da ganinsu yaran matane, idan sunyi aurema to sabon aure ne, dan babu alamar sun taba haihuwa koda daya ce.
Bayan sun fito sun jera wuri daya rankas Umar yace “Wannan sune nurses na Talented University, wanda sune suka karbi Aishatu a lokacin da aka kaita”.
Qur’ani aka bama musulman sukayi rantsuwa da zasu fad’i gaskiya, Christians d’in kuma aka basu bible sukayi ranstuwa da zasu fad’i gaskiya tsakaninsu da Allah, Hakan yasa Ummimah tadan samu sassauci a zuciyarta.
“Rabiatu da Zarah kawayen Aishatu su fito idan suna kusa” alk’ali ya fada yana kallon ta inda zasu fito d’in.
A hankali suka taso suka iso inda sisters din suke tsaye, Alk’ali ya miyar da kallonshi ga sisters d’in yace “K0 kun shaida wannan ‘yan matan kuwa?”.
Da hanzari Sister Maryam tace “Kwarai kuwa na shaidasu, su suka kawo wannan marar lafiyar mai suna Aisha da wata safiya bazan manta ba”.
lfeoma ma tayi caraf tace “Yes I can recognise their faces”. ‘
“Da kyau, Zarah da Rabiatu zaku iya komawa ku zauna” alk’alin ya fada bayan ya dukar da kanshi yayi rubutu. Umaryace
“Zan fara dake Sister Fatima, a lokacin da suka kawo maku Aisha batada lafiya, zaki iya tuna a yanayin da take kuwa?”,
“Ehh zan iya, sun kawota ita ba matacciya ba ba kuma rayayya ba, amma kumajikinta duk ya baci da jini” ta bashi amsa.
“Saura ke Ifeoma, bayan kun karbeta wane irin treating ne kuka fara bata?” Umar ya tambaya yana yi yana leken kofa ko zaiga shigowar Dr. Rafiq amma babu ko alamarshi.
Cikin dakewa lfeoma tace “Mun fara kokarin bata First aid domin tsayar da jinin dake fita daga kasanta amma kuma abun ya gagara, na kira sauran abokan aiki nawa su tayani amma suma sunce abu yafi karfinsu, gashi kuma babu Dr. K0 guda a asibitin suna huta” ta fada cikin hausarta da bata kware ba.
“Sister Maryam daga nan kuma sai kukayi me? Sannan kuma sai naga jini ne,taya za’ace kuda kuka karanci nursing kuma kun kasa tsayar da jini, ko kunga wani ciwo ko rauni a wurin ne?”.
Saida tadan rarraba ido sannan tace
“Gaskiya babu rauni ko d’aya, kawai dai jinin ne mukaga fitarshi tayi yawa,
Ga dunkule dunkulenshi yana fita,
Muna shirin fita da itane mukaga wani katon jini ya fado, koda muka duba da kyau ashe halittarjariri ce harta fara fita, hankalinmu ya tashi sosai munyi tunanin ko shikenan yanzu jinin zai tsaya, amma kuma bai tsaya ba saboda da alama bajariri d’aya bane a cikin cikinta,
Da sauri muka shiga mota mu duka harda kawayen nata muka tafi Kadraq clinic,
Mun samu Dr. Khalid wanda yake gaeny Dr. Ne sai waai abokinshi shi kuma ba gaeny bane,
Sun duddubata sosai Dr. Khalid ya tabbatar mana da kwayar zubar da ciki ce tasha kuma mai muguwar illah, ta sata ta zubar dajini sosai kuma inhar ba’ayi saurin k’ara mata ba zata iya rasa rayuwarta, kuma….” bata k’arisa maganar da take ba Zarah ta mike a fusace tama manta inda take tace
“Wallahi ku munafukai ne karya kuke, kuji tsoron Allah mana, ku duba darajar rantsuwar da kukayi ku fadi gaskiya, haba bayin Allah! Ya da girmanku zaku zubar dashi
saboda an baku kudi? Kudi masu saurin karewa, ko kun manta da akwai babbar shari’ah ne? Wadda ranar baki da ido zasuyi magana, hannu da k’afa zasuyi magana, dukkan gabobin jikin mutum zasuyi magana, wallahi…”
Da karfi alk’ali ya buga guduma yace
“Ki rufewa mutane baki, nan kotu kike ba wurin shirme ba, ki bari har sai idan kin nemi izini kotu ta baki damar yin magana sannan kiyi”.
Cike da bacin rai da kuka Zarah ta koma mazauninta ta zauna, tana tunanin karairayin da nurses d’in nan suke sharawa, gashi kuma Dr. Raflq d’in da zai fadi gaskiya baizo ba, ta yiwu shima an siyeshi da kudi ne shiyasa yak’i zuwa kuma ya kashe wayarshi, Dr. Khalid kuma yazo tun dazu suka ganshi.
A sabule Barr. Umarya koma ya zauna, Yama rasa abunda zai fada, he has no idea yanzu kam, yasan dole za’ayi winning nasu. lta kanta Sultana kuka take tsabar tashin hankali.
Alk’ali yace “Ko lauya mai kare wadda ake kara yanada tambayar da zai masu?”.
Cike da gadara Barr. Sa’eed ya mike, saida ya kalli Umar yaga tsantsar tashin hankali a bayyane dashi, yaga kuma Sultana ta dage sai uban kuka take marar sautu, Shu’umin murmushi yayi sannan ya isa inda sisters din suke.
“Bayan likitan ya tabbatar maku da Clki ne ta zubar sai kuma me ya faru? Barr. Sa’eed ya
jefo masu tambaya yana kallon Sister Fatima da nufin ita zata amsa masa.
‘Gaskiya munyi mamaki sosai, bamuyi tunanin dalibar wannan jami’ar zatayi wannan ta’asar ba. ganin munyi mamaki yasa Dr. Khalid ya tabbatar mana da wannan ba shine zubarda cikinta na farko ba, saboda yaga alamomin haka da dama a tattare da ita”.
Kallonshi ya miyar ga alkali yace “Ina so kotu ta bani dama domin gabatarda Dr. Khalid idan yana kusa”.
‘Kotu ta baka dama” alk’alin ya fada yana kallon ta inda likitan zai fito.
Dr. Khalid ne ya taso a hankali ya tsaya kusa da sisters din, Qur’ani aka bashi yayi rantsuwa da zai fadi gaskiya sannan Barr. Sa’eed yace “K0 zaka fada mana cikakken sunanka da kuma abunda kayi karatunka a kanshi?”.
Ehh zan fada” Dr. Khalid ya bashi amsa.
“To muna saurarenka”, ‘Sunana Khalid Muhammad Khalid, ni d’an asalin garin Katsina ne amma iyayena suna zama a Jalingo nima din acan nake zama, Ni cikakken likita ne ta fannin abunda ya shafi mata, yanzu haka inada asibiti tawa ta kaina wadda duk fannin mata ne kawai a cikinta”, “Good” Barr. Sa‘eed ya fad’a,
“Ko akwai gyara akan bayanan da sisters din nan sukayi? Ko kuma wani abu wanda ba gasklya ba?”.
Shiru yayi kafin yace “Tabbas babu kari ko d’aya a bayanansu,
Bayan sun kawo Aishatu na dubata sosai na kuma gane irin kwayar data sha wadda ta nemi illaya rayuwarta,
Data farfado ne nake mata fad’a akan dalilinta nayin haka,
Shine ta cemin wai tana kunyar a ganta da cikin ne, saboda ita duk iskancinta da bin mazan da takeyi a gidansu ba’a san tana yinshi ba,
Kuma ta tabbatar min da wannan cikin shine na biyu kuma wancan dinma zubardashi tayi.
Na mata nasiha akan ta daina bin maza amma tace sam bata san wannan ba, ta rigada ta saba da maza dan haka dole sai tabi….” bai karisa maganar da yakeyi ba Barr. Sultana ta mike cikin hawaye tace
“Objection my lord! Bai kamata suna fadin magana irin haka ba, saboda wannan tamkar cin fuska ne”.
Kallonta alk’ali yayi yace “korafl bai karbu ba Barr. Sultana. Dr. Khalid ci gaba”.
Wani wawan murmushi Barr. Sa’eed yama Sultana sannan yace “Munajinka Dr.” Ci gaba da zuba karairayi Dr. Khalid yayi. ita dai Ummimah mutuwar zaune ma tayi, ta rasa abunda zata fad’a sai tsabar mamakin hali irin na mutanen yanzu take, lallai kam yanzu kowa ba abun a yarda dashi bane.
Bayan ya gama duka suka koma suka zauna, Alk’ali ya gyara zaman gilashinshn yace
“Ko akwai mai sauran hujjar da zai gabatar kafin a yanke hukunci?”.
Kai kawai Umar da Sultana suka kada cike da takaici, sun san dole ba zasuci wannan shari’ar ba, saboda duk wasu hujjoji nasu anbi an batasu, wanda suke da hope akanshi shiru baizo ba, idon Sultana harya kumbura tsabar kukan da tasha a kotun, Umar kuwa
tagumi kawai yayi yama rasa abunda ke masa dadi.
Kallonsu suka miyar ga Sultana da Mama da suma hankalin nasu a tashe yake, jin alk’all
ya fara magana yasa suka miyarda hankalinsu a gareshi.
“A bisa hujjoji da suka gabata na wanda Iauyoyi masu kare wadda take kara, da kuma na wanda yake kare wadda ake k’ara suka kawo, Kotu tayi zurfin tunaninta tare da yanke hukunci. Munji yanda kowa ya kawo nasa hujjar. dan haka kotu ta gamsu da kaf bayanan Barr. Sa’eed, Ta kuma wanke Salmah Abubakar a bisa kararta da Aishatu Abubakar data kawo akan ta saka an mata fyad’e. lta kuma Alshar kotu zata daureta har na tsawon watanni bakwai a gidan mata (prison) bisa batawa Salmah suna da tayi, sannan kuma zasu bata tarar naira dubu goma na wahalar zirga zirga data sha, ta baro karatunta ta dawo gida akan wannan shari’ar, Amma kuma Aisha da lauyoyinta sunada damar da zasu d’aukaka kara idan hukuncin bai masu ba. Kooootu!”. Alk’ali ya mlke. “
Kara ta saki da karfi had’e da zubewa kasa,
Mama dake kusa da ita tayi saurin dukawa tana kuka sosai mai tsuma zuciyar mai sauraro,
Zarah da Rabiatu ma tuni suka fashe da kuka, suna bala’in tausayin kawarsu,
Lallai wannan rayuwar ta yanzu abun tsoro ce, dukda cutar Ummimah da akayi amma sai gashi wai ita aka bama rashin gaskiya,
Koda yake bataga Iaifin alk’ali ba, saboda shikam yayi amfani da hujjojin da aka kawo masa ne sannan ya yanke hukunci.
Sulma ma tuni ta fasa kukan mai kara fiye da wanda takeyi d’azu,
Umar nata k’ok’arin rarrashinta dukda shima din karfin hali ne, Tunda yake a rayuwarsa tun fara aikinsa bai taba yin shari‘a maras dadin wannan ba, Tsabar rashin gaskiya yayi yawa a cikinta,
Duk wata hanya da zasubi an dode ta. Cikin rashin imani da rashin tausayi Barr. Sa’eed ya kalli Umar tare da mika masa hannu domin su gaisa, Sam Umar yak’i bashi hannun saboda cike yake da takaicinshi, Hakan yasa Barr. Sa‘eed ya kwashe da dariya yace
“Ka tuna shari’armu ta farko dani wacce ka kayar dani? Baka sani ba tun daga wannan lokacin nakejin haushinka, na kuma kuduri aniyar ka gama kayar dani a shari’ah har abada, Na dad’e ina fatan ‘WATA SHARI’AH’ ta hadani dakai, sai gashi kuwa wannan shari’arta had’amu, na kuma gwada maka cewa nafl karfin karamin lawyer kamarka”.
Cikin dakewa Umar ma ya mik’e tsaye.
“Ido cikin ido ya kalleshi yace “Karka damu da wannan Barr. Sa’eed, ka shirya mu had‘u dakai nan gaba kad’an idan
munyi apeal (d’aukaka shari’ah), mu muna tare da gaskiyarmu kuma Allah ba zai taba barinmu muji kunya ba saboda yana tare da mai gaskiya, dan haka ka sake d’aure
damararka tayin yaki dani, ba komai nayi ba a wannan shari’ar sai idan mun d’aukakara zaka tabbatar da k’aramin
Barr. Irina yafi babban irinka a fanni da yawa” ya miyar masa da murmushin da bai kai zuci ba.
Fuska daure Barr. Sa’eed yabar wurin, Har ga AlIah bayyi zaton zasu daukaka k’ara ba.
Gentle kuwa sai washe hakora take, lyayenta ma haka, sal kallon banza suka watsawa su Sultana.
Suna cikin haka ne ma’aikatan gidan yari mata sukazo sanye da uniforma d’insu kalar
kasa, Daidai inda Ummimah take suka isa da handcuff d’insu wai sunzo su tafi da ita.
Hmm