WATA SHARI’A CHAPTER 14WAT

WATA SHARI’A





CHAPTER 14




Saurin mikewa Umar yayi ya tari gabansu babu haufin komai haka kuma babu ko alamar tsoro a tattare dashi, Kallonshi daya daga cikin matan tayi tare da kara bata fuskanta.
“How dare you malam? Ka barmu akan aikinmu muke” ta fada cikin hausarta da bata kware ba kasantuwar ba bahausa bace, mini skirt din dake bisa makeken kugunta kawai ya isa ya tabbatar da cewa ba musulma bace.
“Hukunci bai yanku ba saboda zamuyi apeal, idan baki yarda ba zaki iya zuwa ki samu alk’ali kuyi magana dashi, bakida hurumin da zaki wani kwaso jiki domin kama Ummimah ku kaita prison, so you better to leave this place because you are just wasting your time, babu inda zaku tafi da ita” Umar ya fada cike da zafin rai.
Jin maganar da Umar yayi yasa ta sauke hannun dake rike da handcuffd’in, Juyawa baya tayi hakan yasa suma sauran suka juya, tunda suka tafi basu sake dawowa ba.
Ummimah kuwa har yanzu bata farfado ba, tana mamaki baki daya hankalinta ya tashi, bata fatan ta rasa ‘yarta kamar yanda ta rasa mijinta da sauran ‘ya’yanta guda biyu.
Zarah da Rabiatu kuwa idonsu har ya kumbure tsabar kukan da suka sha, gasu ga Ummimah inda take kwance sai kara allawadai da wannan al’amarin sukeyi.
Saida Sultana ta gama kwasar kukanta sannan ta taso,
Inda suke ta nufa ta tsuguna tana fadin
“Dukkan tsanani yana tare da sauki, haka zalika komai yayu zafi maganinsa Allah, Ya kamata duk koke koken nan mu ajiyesu,
Muyi k’ok’arin sama mata lafiyarta dan sam bai kamata mu barta anan ba,
Gobe Tuesday insha Allahu zamu d’aukaka kara,
Sai mu dage da addu’ah insha Allahu zamuyi nasarah,
Saboda Allah yana tare da mai gaskiya”.
“Hakane Sultana, Allah yayi mana jagora, Allah kuma ya tashi kafadun Ummimah“ Mama ta fada tare da share hawayen fuskarta.
Zarah da Rabiatu ne suka kinkimi Ummimah,
Kai tsaye bakin motar Umar suka kaita,
Tun daga nesa ya bude masu kasantuwar mai amfani da remote ce,
Bayan sun sakata ya bama Sultana key d’in yace ‘ta tafi dasu gida, saboda shi zaije wurin justice suyi magana dashi akan daukaka k’arar da suke so suyi’.
Har Sultana ta tada mota tabar wurin su Gentle suna tsaye suna kallonsu, Mamaki hade da haushi ne ya mamayesu ganin Ummimah zata tafi ba tare da an tafi da ita prison ba.
A ranar saida Umar ya gama komai daga kotunsu ya miyar da maganar court of apeal, An yankar masu rana talatin ga watan d’aya shekara ta dubu biyu da game sha bakwai zasu fara zaman kotu.
Umaryaji dadin yankar masa kwanakin da akayi da yawa, saboda yana tunanin hakan zai bashi damaryin bincike cikin natsuwa har ya samo manyan hujjojin da zai gabatarwa kotu wanda zasu gamsar da kotu cewa lallai Gentle itace tasa akayiwa Ummimah fyade.
“Dan Allah ku sakarmin uwata hakanan, wallahi ita kad’ai gareni, dagani sai kannena
biyu ta haifa, babanmu ya mutu tun muna yara, itace tasha wahala damu tun daga bokonmu har islamiyyarmu,
Bataki ta rasa farin cikinta amma ta faranta mana ba, Ta rasa komai nata a dalilin karatuna na likitanci,
Ba zanso na rasata ta dalilin aikin likitancina ba, dan Allah ku saketa ni na yarda kuyi min 
duk abunda kukaga dama na amince”. Dr. Rafiq ne ke wannan maganar fuskarshi share share da hawaye. 
Wani mutumi katon gaske kamar basamude ya kyalkyale da dariya kafin daga baya ya daure yace 
Kai ba taurin kai gareka ba? Saida muka gargadeka akan kar kaje Katsina domin ka bada 
shaida amma ka nace sai kaje, gashi nan kai bakaje ka bayar da shaidar ba, kuma zaka rasa uwarka”. 
“Ya salam!” Dr. Raflq ya furta. 
“Wallahi na maku alkawarin indai zasu kylemin mamana ba zakuyi mata komai ba to ba zanje kotu in bada shaida ba kunji na rantse, 
Ban hada umma da kowa ba, bana fatan a dalilina ta rasa rayuwarta, Ina sonta fiye da yanda nake son kaina, 
Dan haka wallahi ba zanje ko Katsinan bama barin in bayar da shaida indai zaku kyaleta”. 
Wani d’aya ya tsuke fuska babu k0 alamar annuri a tattate dashi yace 
“Zamu saketa, amma da sharadin inhar wani abu ya faru tofa zakaga abunda baka so, saboda muna tare da kai, muna sane da duk wani motsinka”. 
Bakin Dr. Raflq har rawa yake yace “Wal…wallahi…wallahi na amince, na amince’. 
ka kyautawa kanka“ wancan dayan basamuden ya fada yana kara zaro mugayen idanuwanshi da sukejajur kamarjan garwashi. 
Wani daki suka shiga wanda yake duhu dundum ko tafin hannu ba za’a iya gani ba, Kwanceta sukayi da muguwar igiyar da suka nadeta, Selotape suka kwance daga bakinta da suka nade dashi, Janta sukayi da k’arfin gaske suka fitar da ita daga cikin dakin, Aikuwa ahakan ne ya bata damar fashewa da kuka tana kara ambatar sunan Allah. 
Daidai inda Dr. Raflq yake sukayi jifa da ita, Saurin kankameta yayi cikin furgici saboda yanda ta koma cikin kwanakin da basu wuce biyu ba amma kamar zautacciya. 
Suna cikin hakane basamuden nan ya daka masu tsawa, ba arzik’i sukayi shiru sai rawa jikinsu yakeyi. ‘ “Gaza d’aure masu fuskokinsu mu fitar dasu daga nan”. 
Wanda aka kira da Gaza d’in ya zaro ido cikin mamaki yace “Ance a kyalesu hakanan ne?”, “Banida lokacin amsarka” basamuden ya fada a kufule. 
Hakan ya tabbatarwa Gaza din cewa an amince a sakesu din ne, saboda wanda ya sakasu aikin bayada babban amini sama da basamude, ya yarda dashi sosai. 
Bakin kyalle ya nema ya daure masu fuskokinsu dashi, cikin motarsu mai tint suka sakasu sannan suka tayar da ita suka bar wajen. 
A daidai GRA suka fiddo Dr. Raflq da Ummanshi sukayi jifa dasu tare da barin wurin a dari uku da hamsin. 
Da kyar da wahala Dr. Raflq ya samu ya warware abunda aka nad’e fuskarshi dashi, Babu wahala kuwa ya kwance na ummanshi ma. 
Kara rungumarshi tayi cike da so da kaunar danta. “Me ka masu ne Raflqu? Me ka masu suke neman su illatani?” Ta sake fashewa da kuka. 
“Ummah muje gida zan miki bayanin komai insha Allahu, karki damu babu abunda zasu kara miki” ya bata amsa cikin sigar rarrashi saboda halin da yaga ta shiga abun tausayi ce. 
Da kyar suka mik’e suka tari napep, har kofar gida ya kaisu Dr. RafIq ya rokeshi da yayi hakuri har ya shiga gida ya fito masa da kud’insa, Bayyi musu ba kuwa hakance ta kasance. 
Bayan sun natsu sosai kannen Dr. Raflq mace da namiji hankalunsu a tashe suka tambayesu inda suka shiga, 
Hakan yasa ya labarta masu komai har case din Ummimah wanda shine silar kama Ummansu da akayi shima kuma suka tsareshi wurinsu kawai dan kar yaje ya bayar da shaida. 
Ya kuma fada masu alkawarin daya d’auka akan ba zaije ko Katsinar bama. 
Kanwarshi mace mai suna Dijah ta share hawaye tace “Gaskiya yaya gwara da kace masu ba zakaje ba, saboda nikam ban goyi bayan zuwankan ba, komai zai iya faruwa idan har kaje ka bayar da shaidar, saboda rayuwar yanzu abar tsoro ce”. ‘Hakane kam Dijah, hausawa sunce ‘zaman lafiya yafi zama dan sarki dan haka mu fita batunsu kawai, idanma shari’ar bata warware ba sai su barsu da Allah shi zai masu sakayya, amma kai kam ka zare hannunka kenan” kaninshi Shureim ya fada yana kallonshi. 
Cike da jarumta ummansu tace 
Na amince koda ace zan rasa rayuwata kaje ka bayar da shaidar duk abunda ka sani, a yanda ka bani labarin na fahimci yarinyar tanada bukatartaimako, kuma idan har gaskiya bata fito ba to za’a iya yanke shari’ar duk yanda akaga dama saboda basuda wata hujja dakai kadai suka dogara, dan haka na amince ka tashi ka tafi Katsina yanzu”. 
Cikin mamaki ya kalli umman tashi yace “Ummah kin amince?“, 
“Ehh na amince Rafiqu, idanma kaga baka yarda daka barni ba sai mu tafl tare, nima zan bada tawa shaidar akan daureni da sukayi kawai dan kar kaje ka bayar da shaida”. 
Kallonta ya sakeyi yace “Amma kuma Ummah ai her an zauna shari’ar tun jiya wata k’ilama har an yanke hukunci”, “Babu komai nidai muje, insha Allahu sai yarinyar tayi nasarah”. 

Hmm

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *